2025-04-13@05:54:59 GMT
إجمالي نتائج البحث: 304

«bayyana fatan»:

    Wannan gargadi da Sin da EU suka gabatar ga manyan kamfanonin shirya fina-finai da na fasaha na Amurka, na nuna cewa, gangancin da gwamnatin Amurka ke yi na kakaba haraji barkatai, zai ci gaba da illata kashin bayan fannoninta na cinikayya.   Hadin gwiwa tsakanin Sin da Sifaniya, ya kara bayyana yadda Sin ke fatan ci gaba da bude kofarta, da aiki tare da abokan hulda irinsu Sifaniya wajen goyon bayan tsarin cudanyar sassa daban daban, da goyon bayan dunkulewar salon raya tattalin arziki da cinikayya marar shinge, da samar da karin hidimomi, da kayayyaki masu inganci ga kasashen biyu ta hanyar hadin gwiwa da juna, da mutunta juna, da amfanar da al’ummunsu. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta...
    Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya. Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa...
    Manufar “ramuwar gayya” ba za ta daidaita gibin cinikin da kasar Amurka take fuskanta ba, illa ta daga farashin kayan da ake shigarwa kasar daga kasashen waje, da haddasa hadarin hauhawar farashin kaya a kasar, da kawo illa ga zaman rayuwar jama’ar kasar. A karshe Amurka ba za ta cimma burinta na zama a matsayin koli a duniya ba. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      A nata martani kuwa, Okonjo-Iweala ta ce, karuwar takun saka ta fuskar cinikayya ya haifar da babban kalubale ga tsarin bunkasar cinikayya da tattalin arzikin duniya. Don haka ta jaddada muhimmancin rungumar budadden salo na bin ka’idar cudanyar mabambantan sassa, kana ta jaddada wajibcin warware dukkanin takaddama ta hanyar tattaunawa mai ma’ana karkashin dandalin WTO. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Juma’a da daddare, wata fashewar bama-bama a wata shahararriyar kasuwa a titin Kodesoh, Ikeja dake Lagos ta janyo raunuka ga mutane da dama. Shaidu sun bayyana cewa fashewar ta faru ne lokacin da wani mai kula da shagon kyamara ya yi kokarin bude wani kunshin da aka kawo. Hukumar agajin gaggawa, tare da jami’an ‘yansanda daga tashar yankin G, EOD-CBRN Base 23 ta Ikeja, da ma’aikatan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Lagos (LASTMA), sun tura jami’ansu domin gudanar da ayyukan daukar matakai da tsaro a wurin. Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga Ƴan Nijeriya 85 Za Su Iso Lagos Daga Amurka A Yau Wani shaida gani da ido,...
    Hukumar ilimin bai daya ta kasa wato UBEC ta yabawa Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa jajircewar sa wajen inganta ilimi a matakin farko a Jihar. Shugabar Hukumar, Hajiya Aisha Garba, ta bayyana hakan a yayin ziyarar gwamnan zuwa hedikwatar UBEC a Abuja. Hajiya Aisha Garba ta bayyana jihar Jigawa a matsayin abin koyi ga sauran jihohin kasar nan. Kazalika, ta jaddada irin yadda gwamnati ta zage damtse wajen zuba jari a harkar ilmi, tana mai cewa Jihar ta karɓi fiye da Naira biliyan 21 daga tallafin UBEC tun daga shekarar 2004, wanda ya sanya ta cikin jihohin da suka fi cika sharudan samun tallafin UBEC. Ta kuma lissafa wasu daga cikin nasarorin da aka cimma a ƙarƙashin...
    Wata kungiya mai zaman kanta da ke dauke da sunan Kauru Emirate Consultative Initiative (KECI) ta nisanta da yunkurin da wasu ke yi na saka Masarautar Kauru cikin sabon tsarin Jihar Gurara da ake kokarin kirkira daga Jihar Kaduna. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban kungiyar, Malam Isah Mukhtar, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa ‘yan jarida a Zariya. A cewar Malam Mukhtar, ikirarin da wasu ke yi musamman daga yankin Kudancin Kaduna na cewa Masarautar Kauru na son shiga cikin Jihar Gurara ba gaskiya ba ne kuma yana bata suna. “Mutanen Masarautar Kauru ba su da hannu a wannan yunkuri. Muna alfahari da kasancewarmu a cikin Jihar Kaduna, musamman saboda alakar tarihi, al’adu...
    Idris ya gode wa kamfanonin Faransa da suka daɗe suna aiki a Nijeriya, irin su TotalEnergies, Lafarge, Peugeot, Danone, Alstom, Schneider Electric da sauran su, saboda gudunmawar da suke bayarwa a sassa daban-daban na ƙasar nan kamar makamashi, ababen more rayuwa, noma, lafiya da masana’antu.   Idris ya ce a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya tana kan “tafarkin sauyi da ba a taɓa ganin irin sa ba” wanda Ajandar Sabunta Fata ke ɗauke da shi.   Ya ce: “Waɗannan sauye-sauyen tarihi na gina tattalin arzikin da ya fi gasa, mai gaskiya da amfanar masu zuba jari, suna mayar da Nijeriya ƙofar shiga kasuwar masu saye ta Afirka wadda ke bunƙasa, ƙarƙashin Yankin Ciniki Cikin ’Yanci na Nahiyar...
      -Mun lura da ilimomin harkokin zamaninmu a cikin Alkur’ani Cikin godiyar Allah, muna mika ziyara ga Shehu Isma’ila Umar Almadda (Mai Diwani) da kuma ban gajiya da gabatar da Tafsirin Alkur’ani mai girma na Azumin Ramadan na bana. Allah ya kai mu na badi albarkar Annabi (SAW) da Shehu (RTA). Ya Shehi, a Tafsirinka na rana ta bakwai mun ji yadda ka yi bayani na ilimomin kiyaye hadurran hanya da ke kunshe a cikin aya ta 63 ta Suratul Furkan (Sura ta 25), “Wa Ibadur Rahman…”. Mun kara fahimtar cewa, ayar tana nusarwa a kan tafiya cikin tsari walau sufuri ne na titin mota, ko na jirgin sama ko na ruwa ko jirgin kasa, da dukkan alamomin da ake...
    Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana gamsuwarta da yadda ake ci gaba da gudanar da ayyukan gina tituna da gyare-gyare a fadin jihar.   Kwamishinan ayyuka da samar da ababen more rayuwa na jihar Alhaji Lawal Barau Bungudu ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar.   Alhaji Lawal Barau Bungudu ya bayyana cewa, tun bayan hawan Gwamna Dauda Lawal mulki, gwamnatin ta ba da fifiko wajen samar da ababen more rayuwa, musamman gine-gine da sake gina tituna, a wani bangare na babban shirinta na sabunta birane da nufin kawo sauyi a jihar da kuma saukaka zirga-zirgar ababen hawa.   Ya ce gwamnatin jihar ta dukufa wajen fadada hanyoyin jihar domin ingantawa...
    Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai. Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa,...
    Kasar Sudan ta kai kukan HDL a gaban kotun MDD cewa ta keta dokar hana kisan kiyashi ta hanyar taimakawa dakarun kai daukin gaggawa. A jiya Alhamis kasar ta Sudan din ta bukaci kotun ta kasa da kasa dake karkashin MDD da  ta ta fitar da hukunci na gaggawa na bayar da umarni ga HDL da ta kawo karshen kisan kiyashin da aka yi wa kabilar Masalit da sauran al’ummu a cikin tsawon shekaru biyu na yakin basasar kasar. Ministan shari’a na kasar Sudan Muawia Usman ya bayyana cewa: Kisan kiyashin da dakarun kai daukin gaggawa su ka yi wa al’ummar Masalit da su ka kunshi larabawan yankin Darfur, ya faru ne ta hanyar taimakon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.” Bayan...
    Ana fargabar matafiya da dama sun rasu bayan kifewar wani  kwalekwale ɗauke da ’yan kasuwa a yankin Kogin Neja. Hatsarin kwalekwalen ya auku ne ƙauyen Sokun da ke yankin Ƙaramar Hukumar Lapai, a sakamakon iska mai ƙarfi da ta haddasa juyawar igiyar ruwan. Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne a yayin da kwalekwalen ke ɗauke da fasinjoji da kuma buhunan shinkafa kimanin 200 daga ƙauyen Bugge na Jihar Kogi a zuwa ƙauyen Sokun na Jihar Neja a ranar Laraba da dare. Wani mazaunin yankin, Baba Alhassan, ya shaida wa wakilinmu cewa, ba a kai ga tantance ainihin yawan fasinjojin da ke cikin kwalwkwalen a lokacin da lamarin ya faru ba, amma an yi asarar duk buhunan shinkafar a hastarin....
    Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Riɓers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da kuma babban birnin tarayya. An kama masu garkuwa da mutane biyu a Yobe Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev, a ranar Alhamis, ya ce za a fuskanci ambaliyar ruwa a gaɓar teku da koguna a wasu sassan yankunan Kudu maso Kudu na...
      Daga nan sai ya ce, kasar Sin na aiwatar da matakan ramuwar gayya na wajibi game da cin zalin Amurka, ba kawai don kare ikon mulkin kanta, da kare tsaro da muradun ci gabanta ba ne, har ma da tabbatar da gaskiya da adalci tsakanin sassan kasa da kasa, da wanzar da tsarin cinikayyar sassa daban daban na duniya, da kuma moriyar bai daya ta dukkanin al’ummun duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Yobe ta bayyana shirinta na mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram cikin al’ummarsu da aka yi wa shirin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyara da sake haɗewa da iyalansu ƙarƙashin rundunar Operation Safe Corridor (OPSC). Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Damaturu lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar rundunar OPSC ƙarƙashin jagorancin babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa. Hisbah ta warware rigingimu 565 da lalata katan 51 na barasa a Yobe Trust Radio 92.7FM za ta fara shirye-shiryen gwaji Gwamna Buni, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta tuntuɓar juna da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da gwamnatin jihar. Ya koka da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda masu safarar mutane ke ƙara amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen yaudarar mutane da kuma yi musu cin zarafi, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana wadda ba ta da iyaka kuma mai saurin yaɗuwa wadda ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa. Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na ƙasa karo na 27 kan safarar mutane da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, Babbar Lauyan Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya ce dole ne Najeriya ta ɗauki mataki ta hanyar zamani daidai yadda matsalar take saurin faɗaɗa. Ministan shari’an ya ce, “Safarar mutane ta koma ta intanet. Dole ne mu gaggauta ɗaukar mataki ko kuma...
    Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya nuna kaɗuwar sa bisa rashin da aka yi na ɗan Majalisar Dokokin jihar, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, ɗan Majalisa mai wakiltar mazaɓar Ƙauran Namoda ta Kudu. Iyalai sun bayyana cewa Hon. Aminu Kasuwar Daji ya rasu ne a cikin barcin sa da asubahin ranar Larabar nan a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa gwamnan ya miƙa ta’aziyyar sa ga Majalisar Dokokin jihar da Iyalan mamacin. Sanarwar ta kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta aika da tawaga ta musamman, ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Mani Mummuni a yayin jana’izar ta marigayi Aminu K/Daji in...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta samu nasarar samo ingantaccen masauki  ga alhazan jihar a birnin Makkah, gabanin gudanar da aikin Hajjin 2025. Daya daga cikin mambobin kwamitin musamman da ke kula da aikin hukumar, Malam Buhari Marabar-Jos ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Kaduna. Buhari Marabar-Jos ya bayyana cewa masaukan sun cika dukkan sharuddan da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya suka gindaya. Ya kuma bayyana cewa wata tawaga ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, tana can ƙasar Saudiyya don kammala sauran shirye-shirye kafin dawowarsu Najeriya. Ya jaddada cewa Gwamna Uba Sani ya  ƙuduri aniyar kula da jin daɗin alhazan jihar, tare...
    An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari.   Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai  a Minna, inda ya bayyana cewa hakan yana da muhimmanci matuka,  domin dakile  rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.   Alhaji Umar Musa Danladi ya bayyana cewa ya gaji filin gonar ne daga mahaifinsa wanda ya rasu kusan shekaru goma da suka gabata, kuma yana da burin barin filin ga ‘ya’yansa su...
    Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata. Nijar ta ayyana Hausa a matsayin yaren ƙasa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Ministan ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun wani adadi mai yawa na ƙwararrun likitocin da ke da burin fita zuwa wasu ƙasashen duniya aiki, suna fakewa da matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya. Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya. Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma...
    A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci. Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazoum, Nijar ɗin ke ɗaukar matakan nesanta kanta da Faransa, inda ta fara da korar sojojinta da kuma sauyawa wurare da dama da ke da alaƙa da kasar suna. Bayan haka kuma, Nijar ɗin da sauran ƙasashen da Faransan ta yi...
    Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Turai su kara mu’amala da juna, da bude kofa ga juna don tabbatar da yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata, ta...
    Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka  fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
    Jami’an yan sanda a birnin Makka sun tsare wata Bafalasdiniya wacce ta baje Jakarta dauke da tutar kasarta Falasdinu tare da zarginta na bayyana wani abu na siyasa a lokacin aikin umran da take yi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Mint-Press yana cewa matar ta shiga masallacin haramin Ka’aba dauke da jakanta mai tutar falasdinu. Kuma bayan sun kamata sun tsare, Bafalasdiniyar wacce har yanzun ba’a bayyana sunanta ba, ta ce masu tana ganin wasu masu aikin umra wadanda suke shigowa masallacin Ka’aba tare da tutocin kasashen su, daga cikinsu akwai yan kasashen Morocco, Turkiyya, da sauransu, don haka itama tana dauke da tutar kasarta ce Falasdinu don nuna daga inda ta fito....
    Jamhuriyar Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin na kasa, yayin da Faransanci ya zama harshen aiki mai sauki, don haka, Faransanci ba yaren hukuma ne ba. Matakin dai ya dogara ne da shawarwarin da babban taron kasar ya gabatart a watan Fabrairu, wanda kuma shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya amince da shi a ranar 26 ga Maris.   A yanzu sabon kundin tsarin mulkin kasar ya jera harsuna goma sha daya da ake magana da su na Nijar, inda ya amince da Hausa a matsayin harshen kasa.   Harshen Hausa dai shi ne yaren da aka fi amfani da shi a duk fadin Nijar. A kwanakin baya sabbin hukumomin kasar da ke da suka raba gari da kasar...
    Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD da kuma tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban bisa tushen WTO. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kuma jaddada cewa, manufofin kasar Sin na jan hankalin jari daga waje ba su sauya ba, kuma ba za su sauya ba.   Tattaunawar na zuwa ne yayin da ake tsaka da shiga wani sabon zagayen zullumi dangane da cinikayya a duniya inda a baya-bayan nan Amurka ta kara haraji kan abokan cinikayyarta, ciki har da Sin.   Ling Ji ya soki wannan mataki, yana mai kiransa da wanda ya yi matukar keta ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa, haka kuma ya keta hakkokin sauran kasashe. (Fa’iza Mustapha)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa  ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu. Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas “Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar. Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji....
    Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an soke gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin. Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban. Idan...
    Wannan ya haifar da wani rikici, wanda ya jawo mutuwar Usman Sagiru da raunata wasu da dama. Wannan shi ne abin da ‘Yansanda suka yi ƙoƙarin hana faruwa, kuma sun ɗauki matakan gaggawa bayan wannan al’amari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya soke gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an soke gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin. Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban.  ...
    Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwi, Manguna, Daffo, Josho da Hurti. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin rashin hankali da tausayi. Ya ce an kashe mutane da dama ciki har da mata da yara, yayin da wasu da dama suka jikkata. Ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare na barazana ga zaman lafiya da haɗin kan yankin Arewa. A wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya...
    Nemi adalci maimakon babakere. Cin zali ta hanyar kakaba haraji da Amurka ke yi, ya haifar da suka da adawa da martani daga kasashe da dama. Takarda mai dauke da matsayar kasar Sin da aka fitar dangane da cin zalin ta samu goyon bayan daga kasa da kasa. Sakamakon wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya, ya nuna wadanda suka amsa nazarin na kira ga kasashen duniya su hada hannu su dauki mataki domin bijirewa salon cin zali irin na Amurka, su kare hakkokinsu da kuma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya. Bisa fakewa da daidaito da adalci, Amurka na son cin riba daga faduwar wasu, inda take sanya muradunta sama...
    Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.   Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a amince da shi ba ne, bai dace ba, kuma babban abin damuwa ne,’ in ji Sakataren Harkokin Waje David Lammy, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.” Lammy wanda ya bayyana cewa Birtaniya tana tuntuɓar ‘yan majalisar domin ba su goyon baya, kuma ya bayyana wa hukumomin Isra’ila ƙarara cewa “ba haka ake yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya mu’amala ba.” “Abin da gwamnatin Birtaniya...
    Sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya ce ba wanda zai ci ribar yakin cinikayya a yayin da ake ta cacar baka kan harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa duniya.  Antonio Guitess ya yi wannan gargadin ta bakin kakakinsa inda ya yake bayyana cewa, “ba wanda ke yin nasara a yakin na cinikayya. ” Yana mai cewa, a yayin da ake samun karuwar adawa daga sassa daban daban, shugaban Amurka Donal Trump a ranar Laraba ya rattaba hannu kan wani umarnin zartarwa kan abin da yake kira “harajin fito na ramuwar gayya,” wanda ya sanya kashi 10 cikin dari na mafi karancin harajin fito, da karin sama da haka kan wasu abokan cinikayyar kasar. A wani...
    Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman A. Tar ta fitar, gwamnatin ta yi Allah-wadai da irin munanan kalamam da suke yi da kan iya haifar da barazana. An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe ’Yan sanda sun gayyaci Sarki Sanusi domin amsa tambayoyi Inda ta yi nuni da cewa, waɗannan kalaman sun saɓawa al’adunmu da tsarin rayuwarmu, musamman a shafukan sada zumunta na...
    Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da sanya harajin fito na ramuwar gayya kan dukkan kawayen cinikayyarta a ranar 2 ga wata, inda kasar Sin ta mayar da martani nan take, da zummar kiyaye halastaccen hakkinta. Daga baya a ranar 3 ga wata, Sin ta sanar da wasu jerin matakai, ciki har da kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, da shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka, gami da kara wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin sunayen kamfanonin da ta dauki matakin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kansu, matakan da suka janyo babbar raguwar darajar takardun hannayen jari...
    Hedikwatar ’yan sandan Nijeriya ta gayyaci Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan wani lamari da ya faru a lokacin bikin Sallah a Kano. A baya dai rundunar ’yan sanda tare da sauran wasu jami’an tsaro a jihar sun soke duk wani hawan bikin Sallah, musamman jerin gwanon dawakai a jihar, saboda dalilan tsaro. Motar fasinja ta kama wuta wasu sun tsallake rijiya da baya Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang Sai dai a yayin da Sarkin ke tattaki domin halartar Sallah a filin Idi na Ƙofar Mata a ranar 30 ga watan Maris, an caka wa wani ɗan banga da ke kare Sarkin wuƙa har lahira, yayin da wasu...
    Wani jami’in ’yan sanda ya shaida wa Leadership cewa: “Duk da haramta bukukuwan sallah, an gudanar da hawa a motocin Sarkin a rana ta uku bayan Sallah, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce.” Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wani bayani daga fadar Sarkin Kano game da gayyatar da aka yi masa. Ga hoton takardar gayyatar da ‘yansandan suka fitar: Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba.  Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin...
    Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa, inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki kuma jajirtacce. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda Oladunjoye ke yi wa aiki a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce rasuwarsa babban rashi ne. Ya ce Oladunjoye mutum ne mai kishin jam’iyya, jajirtacce, kuma ya taka rawar gani...
    SShugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana  alhininsa bisa rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a yana mau shekaru 68 a duniya.   Mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan Harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da sanarwar, inda ya jaddada muhimmancin gudummawar Dr. Abdulaziz wajen koyar da addinin Musulunci da kuma ci gaban matasa.   Shugaba Tinubu ya yabawa ƙoƙarin marigayin wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da rikicin Boko Haram tun farkon bayyanar kungiyar. Ya ce al’ummar Musulmi sun yi babban rashi bisa mutuwar Dr. Abdulaziz wanda kan jajirce kan gaskiya da ɗa’a.   Shugaban ya kuma yi addu’a ga Allah Ya jikansa, tare da...
    Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya. Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da...
    Ya roƙi Allah da Ya ji ƙansa, tare da bai wa iyalansa da almajiransa haƙurin rashinsa. Hakazalika, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana kaɗuwarsa game da fitaccen malamin. Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta. “Ina miƙa ta’aziyya ta ga iyalai da almajiran Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi. “Dokts Dutsen Tanshi ya kasance abin tunawa saboda jajircewarsa wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci. “Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdausi,” in ji Kwankwaso. Dokta Abdulaziz ya kasance mashahurin malami wanda aka san shi wajen faɗar gaskiya, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman...
    Kotun Ƙoli ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja, ta yanke wanda ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar LP na ƙasa. A ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙoli, ya ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta da hurumin yanke hukunci kan shugabancin jam’iyyar. APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027 NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Alƙalai sun bayyana cewa batun shugabanci al’amari ne da ya shafi cikin jam’iyya, kuma ba kotu ke da ikon yanke hukunci a kai ba. Kotun ta kuma ce wa’adin mulkin Julius Abure a matsayin shugaban jam’iyyar ya ƙare tun da farko. Kotun ta amince da ƙarar da...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara. Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
    Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira ga duniya da ta bayyana goyon bayanta ga al’ummar Palasdinu ta hanyar daukar matakan gaggawa da suka hada da dukkanin hanyoyin soja, tattalin arziki, da diflomasiyya mai  inganci. Dangane da haka ne kungiyar ta yi kira ga limaman masallatan Juma’a a fadin duniya da su sadaukar da hudubar sallar Juma’a na gobe don magana kan wajabcin magance wahalhalu da...
    Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin. Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Wani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce, “Tun a ranar Asabar muka samu bayanai cewa Turji zai ziyarci Gatawa, kuma mun sanar da hukumomi. “Duk da haka, shi da mutanensa sun bi ta ƙauyukanmu, sun yi bikin sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai.” Ɗan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
    Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda yake ɗaya daga cikin masu naɗa Sarki a Kano. Alhaji Sunusi, ya rasu yana da shekaru 92 bayan fama da doguwar rashin lafiya. Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Basakkwacen da ya yi ridda ya sake karɓar addinin Musulunci Ya rasu ya bar ’ya’ya da jikoki da dama, ciki har da Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kano. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari da ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin gargajiya. Ya ce gudunmawar da ya bayar za a ci...
    Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...
    A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy  Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, mai yuwa yayi tasiri a barazanar da kasar Iran take fuskanta na kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar. Aragchi ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran na zaman lafiya ne, kuma har yanzun kasar Iran tana kan bakanta na aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya don kare hakkinta na mallakar fasahar makamashin nukliya wannan dokokin kasa da...
    A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yankin Xizang a bude yake ga kowa da kowa, kuma ba a hana baki daga kasashen waje shiga ba, inda ya kara da cewa, yankin yana karbar dimbin matafiya da sauran al’ummomi da dama daga sassa daban-daban a kowace shekara, domin ko a shekarar...
    Yakin cinikayya ba zai taba durkusar da kasar Sin ba, sai dai kaikayi ya koma kan mashekiya. Yayin da wasu kasashen ke aiwatar da kariyar cinikayya da kokarin rufe kofarsu ga sauran sassan duniya, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kuma maraba da ’yan kasuwa daga kasa da kasa. Maimakon kawo cikas, kasar Sin za ta lalubo hanyoyin samun karin ci gaba ga kanta da sauran sassan duniya, kuma kariyyar cinikayya da ake yi, zai rikide ya zamo alheri a gare ta.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Mai Martaba Idi Chiroma, Sarkin Gassol a Jihar Taraba, ya ce Musulmin da suka gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 2025 sun nuna tsayin daka wajen sadaukarwa ga addini.   Chiroma ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi ga al’ummar Musulmi a wani bangare na bikin Sallar karama a karamar hukumar Gassol da ke jihar.   Ya kuma ja hankalin al’ummarsa da su jure duk wani kalubalen da suka fuskanta yayin da suka jure mawuyacin hali na baya-bayan nan domin ibada.   Chiroma ya bayyana cewa wadanda za su koma ga tsohon halin da suke ciki na iya zama ba tare da albarkar da ke tattare da azumin watan Ramadan ba.  ...
    Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Okpebholo bisa tattaunawarsa da shugabannin al’ummar Hausa a Edo domin hana rikici da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan. “Biyan diyya da aka alƙawarta abu ne mai kyau, amma dole ne a tabbatar da hakan cikin gaggawa domin taimaka wa iyalan da suka rasa masu ɗaukar nauyinsu,” ya ƙara da cewa. A nasa ɓangaren, Gwamna Okpebholo ya nuna matuƙar damuwarsa kan wannan kisa, inda ya tabbatar da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata laifin. “Ina samu labarin abin da ya faru, na garzaya zuwa Uromi. Na gana da al’ummar Hausa a wajen, kuma mun yi ƙoƙarin kwantar da tarzoma. “Ina tabbatar muku da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa,”...
    Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Malam Tanko Isiyaka, shugaban fulani na gundumar Bondon, ya bayyana cewa marigayin ya fito ne daga jihar Bauchi.   Ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin tare da yin kira da a yi addu’a tare da tallafa wa iyalan mamacin. An yi jana’izar mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su guji cin mutuncin shugabanni yayin da suke bayyana matsalolinsu, inda ya jaddada cewa girmamawa da ladabi suna fi tasiri wajen samun mafita. “Idan ka zagi shugabanka, ta yaya kake so ya taimaka maka?” in ji shi. Masar ta miƙa wa Hamas da Isra’ila tayin tsagaita wuta Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar Sallah “Amma idan ka yi magana da ladabi, zai saurare ka kuma ya ɗauki mataki.” Da yake jawabi bayan sallar Idi a Sakkwato, Sarkin Musulmi, ya buƙaci ’yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma zaman lafiya da ci gaban ƙasa. “Ku yi wa Shugaban...
    Kungiyar Hamasa a gaza ta bada sanarwan cewa ta amince da shawarar da kasashen da suke shiga tskaninta da HKI kan cewa ta amince da kafa gwamnatin hadin kan Falasdinawa, amma ba zata taba mika makamanta ga wani ba ko waye shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Kungiyar Khalil Al-Hayya yana fadar haka a jiya Asabar a wani jawabin da ya gabatar da faifen bidiyo. Al-Hayya ya kara da cewa muna karban dukkan shawarori masu ma’ana idan an bijirosu gare mua. Amma batun makamanmu, ba zamu taba kyale mutanemmu a hannun yahudawan sahyoniyya ko kuma wasu shuwagabannin Falasdinawa wadanda zasu mika su ga yahudawa ba suna ta yawo da hanka;linsu ba. Yace fatammu ne gwamnatin...
    Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana. Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa...
    Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia. Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa. Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu. “Kamar yadda aka...
    Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na  harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari. Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana. Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai. Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa...
      Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, tare da hadin gwiwar First Impression Communication Limited, ta shirya wani taro kan shirin Samar da Ruwa Mai Tsafta a Birane da Karkara da Tsabtace Muhalli da Kiwon Lafiya (SURWASH) da ya gudana a Arewa House, a Kaduna.   Da yake bude taron, Kwamishinan Ayyuka da Samar da Kayayyakin More Rayuwa, Dakta Ibrahim Hamza, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na magance matsalar karancin ruwa a jihar.   Kwamshinan wanda Mataimakin Daraktan Albarkatun Ruwa, David Roven Aliyu ya wakilta, ya bayyana kokarin da gwamnati ke yi, ciki har da gina rijiyoyin burtsatse a wasu al’ummomi domin inganta tsaftar muhalli da kiwon lafiya.   “Shirin SURWASH na Najeriya wani shiri ne da Asusun...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
    Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan da suka fito daga sassan masana’antu da cinikayya na kasa da kasa a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi ya jadadda cewa, a cikin shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin musamman ma cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta cimma gaggaruman nasarori wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da dorewar walwalar al’umma dogaro da jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato jKS da kokarin al’ummar Sinawa cikin hadin kai, kuma ba za a raba wadannan nasarori da taimakon da kasashen duniya ke ba ta ba, cikin hadda gudunmawar da kamfanonin ketare dake kasar Sin suke bayarwa....
    A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
    Gwamnatin Jihar Gombe, ta tabbatar da mutuwar mutum uku daga cikin 33 da suka kamu da cutar sanƙarau a jihar. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Habu Dahiru ne, ya bayyana hakan yayin ƙarin haske game da ɓullar cutar a jihar. Majalisa ta janye ƙudirin tuɓe wa matakaimakin shugaban ƙasa da gwamnoni rigar alfarma Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi Yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa an samu rahoton mutum 53 da ake zargi sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi hudu: Kaltungo, Yamaltu Deba, Billiri, da Gombe. A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum uku daga ƙananan hukumomin Kaltungo, Yamaltu Deba, da Billiri. A Shongom kuwa, daga cikin mutum huɗu da ake zargi...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin. Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
    Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na bunƙasa kayan horo da samar da ingantattun makamai da kayan aiki ga dakarun sojoji. Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Badaru ya yi alƙawarin tuntuɓar Gwamnatin Jihar Kaduna, domin kammala ginin Makarantar Sakandaren Chindit, wadda ba a kammala ta ba tsawon lokaci. Ya kuma bayar da tabbacin...
    Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.” Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya. Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ya bayyana ganawar da suka yi da Amurkawa a ranar Lahadi a matsayin...
    A kwanakin nan, birnin Beijing na Sin ya karbi tarin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwar kasar Sin dake kawo ziyara kasar, sai dai kuma idan an yi la’akari da yanayin yakin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa dake wakana yanzu haka, a iya cewa ziyarce-ziyarcen sun zo da mamaki. Yayin da gwamnatin Amurka ke matsa kaimi wajen ingiza yakin cinikayya, ‘yan siyasa da wakilan manyan kamfanonin Amurka na haye wahalhalu inda suke ta kawo ziyara Sin, wanda hakan ke nuni ga matukar goyon baya da salon bude kofar cinikayyar duniya ke samu, da kuma fatan da ake yi na samun cikakken daidaito, da hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ko shakka babu, matakin Amurka na...
    Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayya ta ce ta kama damin alburusai 488 da aka ɓoye a jarkar manja a tashar mota. Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sintiri na musamman a Abuja, DCP Ishaku Sharu, ne ya bayyana hakan lokacin da yake holen wanda ake zargin a ofishin rundunar a ranar Litinin. Matasa sun daka wawa kan kayan abincin da Seyi Tinubu zai raba a Gombe Gwamnonin PDP sun garzaya Kotun Ƙoli kan dakatar da Gwamnan Ribas Ya ce rundunar ta samu nasarar kama wanda ake zargin ne bisa tallafin wasu jami’an ƙungiyar masu sufurin motocin haya (NURTW). Kazalika, ya ce sun kama wanda ake zargin ne ɗan asalin Jihar Katsina, ɗauke da harsashi 488 na bindigogin AK-47...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin manyan kamfanoni na duniya a nan birnin Beijing, yayin da suka yi musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, da fadada zuba jari a kasar Sin. He ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da fa’ida mai yawa, da wadataccen...
    Sanata mai wakilatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta bai wa Majalisar Dattawa haƙuri. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Natasha ta ce tana na kan batunta, kuma ba za ta taɓa bai wa majalisar haƙuri a kan gaskiyarta ba. Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — Zulum Idan za a tuna dai majalisar ta dakatar da Natasha tsawon watanni shida tare da dakatar da albashi da alawus-alawus ɗinta ne bisa saɓa wa dokokin majalisar da kwamitin ƙorafi da ladabtarwa ya tabbatar. Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kuma Sanata Natasha take ci gaba da zargin...
    Ƴansandan sun gayyaci Sanata Sunday Karimi domin bayani kan zarginsa na cewa ƙungiyar leƙen asirin ƙasar Rasha ta KGB ta samu shiga cikin Majalisar Dokoki, wanda ke barazana ga tsarin dimokuraɗiyya a Nijeriya. Zargin ya samo asali ne daga rahoton da Sanata Karimi ya raba akan ƙungiyar ta WhatsApp a Majalisar Dattijai a ranar 23 ga Fabrairu, 2025. Rahoton, wanda aka wallafa ta gidan jaridar The Reporters, ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin Majalisar, inda Sanata Natasha H. Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar, ta shigar da buƙatar yin bincike ga Shugaban ‘Yansanda. Fiye Da Dalibai 4,200 Suka Amfana Da Tallafin Ilimi Na Sanata Solomon Adeola Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha A cikin ƙarar da ta...
    A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin manufofinta na tattalin arziki. Sai dai a daya hannun, kasar Sin na kara fadada bude kofarta. Ya ce Amurka na ingiza salon rufe fasahohinta, yayin da Sin ke kara gabatarwa duniya da fasahohin ci gaba. Dukkanin wadannan na nufin Sin za ta zamo mai cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin duniya a shekaru masu zuwa. Daga nan sai mista Jeffrey ya nuna damuwa game da...
    Kasar Rasha ta bayyana cewa dole Moscow da Beijing su shiga shawarwarin tattaunawar nukiliya da Iran. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova ta bayyana cewa, Moscow a shirye take ta samar da ingantacciyar hadin gwiwa da dukkan bangarorin kan batun yarjejeniyar nukiliyar Iran. “ Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ya aike da wasika zuwa Tehran domin fara tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran; yayin da shi da kansa ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a wa’adinsa na farko. A halin da ake ciki dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa...
    A kokarin Gwamnatin Jihar Jigawa na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwa, ta kaddamar da shirin noman rani na Lallashi da ake amfani da rijiyoyin burtsatse a Karamar Hukumar Maigatari ta jihar. Rahoton na nuna cewa, an yi aikin ne domin canza salon noman rani da sauran ayyukan noma a yankunan da galibi hamada ce. A cewar rahoton, wannan shiri ana yin amfani da makamashin hasken rana da kuma amfani da na’urori masu rahusa tare da dabarun noman rani don samar da harkokin noman rani mai inganci cikin sauki. Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum...
    Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana uku bayan an kashe fararen hula 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai. Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan talabijin na ƙasar a ranar Juma’a. An yi wa wata karya tiyatar ceton rai Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun kashe fararen hular ne a lokacin da suka afka cikin wani masallaci a ƙauyen Fombita da ke Kokorou inda suka far wa masallata. Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da harin inda ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An kuma sanar da ma’aikata masu zaman kansu da ‘yan kwangila na kasa da kasa kan dakatar da ba da tallafi. A lokaci guda kuma, an daina ba da tallafi na tarayya ga gidajen Rediyon ‘Free Asia da Rediyo Free Europe/Radio Liberty’. Daraktan Muryar Amurka, Mike Abramowitz, ya ce shi da kusan dukkan ma’aikatansa 1,300 an ba su hutun biyan albashi biyo bayan umarnin. Har ila yau, umarnin zartarwa ya shafi wasu hukumomi, ciki har da Ma’aikatar Sasanci da Shiga Tsakani ta Tarayya; Hukumar Yada Labarai ta Duniya ta Amurka; Cibiyar Nazarin Duniya ta Woodrow Wilson, Cibiyar Smithsonian; Cibiyar Gidan Tarihi da Ayyukan Laburare; Majalisar Sadarwar Amurka; Asusun Ci gaban Al’umma na Cibiyoyin Kudi; da Hukumar Bunkasa kananan Kasuwanci. ...
    Allah Ya yi wa Alhaji Nasiru Ahali, Shugaban Kamfanin Mainasara & Sons, rasuwa. Marigayin wanda yake shahararren masanin masana’antu ne ya rasu yana da shekara 108. Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP A cewar majiyoyin na kusa da iyalan marigayin ɗan kasuwar ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano a daren ranar Alhamis. Ana girmama Ahali a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan masanin asalin masana’antu a Kano. Ya yi ƙoƙari ya kafa tsarin kasuwanci na yau da kullun. A tattaunawarsa da Daily Trust a shekarar 2018, marigayi Ahli ya bayyana cewa sana’arsa ta haɗa da buga littattafai, bugu takardu, masana’antar bulo, sana’ar...
    Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta samu nasarar kammala rijistar maniyyata aikin hajjin bana 3,155.   Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Danbappa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kano a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar Hukumar Shige da Fice a ofishinsa.   Danbappa ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye da suka hada da kwasa-kwasan horas da aikin hajji, da takardu da kuma tattara kayanai.   “Yanzu haka hukumar ta fara bayar da biza ga maniyyatan da suka yi rijista.   Ya yabawa gwamnatin jiha bisa yadda take ci gaba da tallafawa kokarin hukumar na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki.  ...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace. Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) jiya Alhamis. Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari. Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.” A cewar Araghchi, tilas ne a gudanar da shawarwari...
    Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci. Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa. Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci. Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai...