2025-02-26@13:58:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 25

«rage farashin kayan»:

    Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
    Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
    Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage farashin kayan marmari kamar dankalin Turawa da karas da kukumba da latas da koren tattasai da ake fataucin su daga wasu jihohin Arewa zuwa Kudancin kasa. Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno “Za mu yi ragin ne daidai gwargwado daga cikin ribar da muke samu saboda albarkar...
    Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne da ke kara dagula zaman lafiya a yankin. A yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya, Nebenzia ya ce “daya daga cikin abubuwan da ke nuni da yunkurin dagula zaman lafiya a yankin shi ne yadda Isra’ila ke ci gaba da mamaye yankin Golan na klasar Syria.” Sauran abubuwan da ke haifar da rashin zaman lafiya, a cewar wakilin Majalisar Dinkin Duniya, su ne yadda “Isra’ila” ke hana ‘yan kasar Lebanon da suka rasa matsugunansu komawa gidajensu a Kudancin kasar, da kuma ayyukan tada hankali da ta yi ta hanyar kai farmakin soji a...
    Dalibban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura na daf da fara Jirage da Motoci Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ne ya bayyana haka lokacin da yake magana da Radio Nijeriya Kaduna a ofishinsa na Daura. Ya kara da cewa Jami’ar Sufurin da Gwamnatin Tarayya ta Samar na da manufar Samar da dalibbai masu hazaka da zasu kasance masu kirkire kirkire da manufar ganin ana yaye dalibbai da zasu dogaro da kansu dama taimakawa wajen habakar tattalin arzkin kasa. Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ya Kara da cewa baya ga ilmantar da dalibbai Jami’ar tsaye take wajen ganin sun Samar da dalibbai masu tarbiyya da zasu kasance abin alfahari cikin al’umma. Hakama Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa yanzu...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
    Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza  a jiya Lahadi. Ya kara da...
    Gwamnatin Tarayya, ta bayyana cewa ba ta shigo da kayan abinci daga ƙasashen waje ba, duk da cewa farashin kayan abinci ya ragu a kasuwanni. Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Farfesa Abubakar Kyari, ya bayyana cewa, ko da yake gwamnatin ta yi tunanin shigo da abinci a lokacin da farashinsa ya yi tashin gwauron zabo, daga bisani ta janye wannan shawarar. An ƙwace miliyoyin daloli, gidajen da ke da alaƙa da Emefiele Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu Ministan ya danganta saukar farashin kayan abinci da ƙoƙarin manoma da suka koma gonaki a daminar bara, wanda ya sa amfanin gona ya yi yawa. Ya kuma buƙaci ‘yan kasuwa da su rage farashi domin jama’a...
    “A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari. An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi...
    Wata gobara da ta tashi cikin dare a garin Satigal da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ta ƙone gidaje da dama, dabbobi, da rumbunan ajiyar hatsi guda shida. Sai dai kawo yanzu babu labarin rasa rai a gobarar. Ukraine ce mai laifi a yaƙin da ta ke yi da Rasha — Trump Hana Biza: Najeriya ta cancanci a girmama ta – Babban Hafsan Tsaro A cewar wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na shiyyar Rano, Rabi’u Kura, ya fitar, mazauna yankin sun haɗa kai wajen kashe gobarar da kuma ceton rayuka da dukiyoyi. Bayan haka, an kai rahoton lamarin ga Sarkin Rano, Dokta Muhammad Isa Umaru, a fadarsa. Hakimin Satigal, ya jagoranci wasu mazauna yankin zuwa wajen sarkin,...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da cewa, ta kakkabo jiragen saman marasa matuki 9 da kasar Ukiraniya ta harba mata. Sanawar ta ma’aikatar harkokin tsaron Rasha ta ci gaba da cewa; A daren jiya ne  aka kakkabo jiragen sama  marasa matuki 3 na kasar Ukiraniya da aka harba a kan yankin Biryansk, sai kuma wani jirgin saman guda daya akan sararin samaniyar Tatrastan. Bugu da kari makaman saman na Rasha  sun kakkabo wasu jiragen sama marasa matuki guda 4 a sararin samaniyar “Bahrul-Aswad”, sai kuma jirgi guda daya a saman yankin Tula. A gefe daya  a jiya ne aka bude wani kwarya-kwaryar taro a tsakanin kasashen Amurka da Rasha a kasar Saudiyya domin tattauna hanyoyin kawo karshen yakin Ukinraniya. Sakataren...
    Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
    Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun jari a wasu bangarori na Tashar. Mahukunta a bangaren tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa a fadin duniya, sun dogara ne, wajen samar da kudaden shiga domin su samu damar ci gaba da kula da kayan gudanar da ayyukansu da kuma kara tabbatar da tsaro, a Tashohin Jiragen Ruwan su. Bugu da kari, wasu kararru a fannin sun bayyana cewa, harajin da Hukumar NPA ke karba...
    Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.   Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad ​​Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), ofishin kula da magunguna masu muhimmanci, da gidauniyar REDAID Nigeria Foundation., a Jalingo.   Danburam ya bayyana cewa, wani bincike da aka yi kwanan nan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 18 a kananan hukumomin Ardo-kola, Bali, da Takum, ya nuna cewa kayan gwajin cutar kanjamau sun kare a cibiyoyin.   “Rashin kayan gwajin zai kawo cikas ga kokarin...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta. Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979, daya daga cikin bangarorin da aka sami gagarumin ci gaba a cikinsa shi ne, bunkasa sana’ar gine –gine da kuma samar da masana’antu, wanda ya kai ga kasar ta kai ga wadata a wannan bangaren, wani abu daga kasashen waje, sai abunda ba za’a rasaba. Har’ila yau wannan ya wadanar da mutane da dama a kasar. Kafin haka idan mun dubi...
    Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma. Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni. A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004. Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan...
    Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka. Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da suke guduwa daga filin yaki suna karuwa. Jaridar ta kuma kara da cewa; Babban hafsan hafsoshin kasar ta Ukiraniya ya bayar da umarnin a dauki sojojin sama 5000 a mayar da su na kasa. Da akwai tsoron cewa kasar ta Ukiraniya tana rashin kwararrun sojojinta, da ba za ta iya maye gurbinsu a cikin sauki ba idan har aka tura su zuwa filin daga. A...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara da cewa zai dorawa hatta kayakin da suke shigowa Amurka daga kasashen Turai, nan gaba, sai dai bai sanya lokaci ba. Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa zai dorawa kasar Canada kashi 25% kan dukkan kayakin da suke shigowa kasar. Sai mna Desel, inda zai sanya kashi 10% kacal.
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun ce rundunar kai daukin gaggawa mai fada da sojojin kasar Sudan ta kai wa garin “Tandalti” hari da jirgen sama marasa matuki jim kadan bayan ziyarar shugaba majalisar shugabancin kasar Janar Abdulfattah al-Sisi. Majiyar sojan kasar Sudan ta ce, sun yi amfani da na’urorin kakkabo jiragen sama, akan hare-haren na rundunar kai daukin gaggawa tare da kakkabo da dama daga cikinsu. Wadannan hare-haren dai sun faru ne jim kadan bayan wata ziyara da shugaban majalisar shugabancin kasar ta Sudan janar Burhan Abdulfattah ya kai garin “Um-Ruwabah’ wanda sojojin Sudan din ba su dade da kwato shi ba. A cikin makwannin bayan nan dai sojojin na Sudan suna cigaba da samun nasara akan...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin  kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka  bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis.  Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
۱