2025-04-11@14:00:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2640

«shiga wajenta»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Amurka ta kai sabbin munanan hare-hare ta sama har sau 22 a wasu larduna da dama na kasar Yemen, jim kadan bayan kai wa kasar hare-hare da dama makamancin haka. A cewar majiyoyin na Yemen, wadannan sabbin hare-hare na Amurka sun auna yankuna daban-daban a ranar Laraba, ciki har da babban birnin kasar Sanaa da lardin Ibb da ke tsakiyar kasar. A Sana’a, an kai hare-hare ta sama guda takwas. Har yanzu ba a tabbatar da asarar rayuka ba, amma hare-haren sun shafi muhimman ababen more rayuwa, lamarin da ke kara tabarbare yanayin rayuwa ga fararen hula. An sami adadin wadanda suka mutu mafi muni a lardin al-Hudaydah da ke yammacin kasar, inda aka tabbatar da mutuwar fararen hula 6...
    Majalissar Dokokin Rasha ta amince da yerjejeniyar huldar ta shakaru 20 tsakanin kasar da Iran. Wannan na nuna muhimmin mataki na zurfafa dangantakar siyasa, soja da tattalin arziki tsakanin Moscow da Tehran. Yarjejeniyar ta tsawon shekaru 20, wakilan majalisar sun amince da ita ne a kuri’ar da aka kada a ranar Talata ta yadda kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa cikin tsari da inganci. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na kasar Iran Massoud Pezeshkian ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a cikin watan Janairu, da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban da suka hada da tsaro, makamashi, kudi, sufuri, masana’antu, noma, al’adu, da kimiyya da fasaha. Yarjejeniyar ta kuma bada damar zuba jari a...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne sun kashe masunta uku a wani hari da suka kai ƙauyen Sanyinna da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Wata majiyar a ƙauyen ta ce ’yan bindigar sun kashe mutanen ne a lokacin da suka kawo hari da safiyar Talata yayin da mutanen suka fita sana’arsu ta su. Kazalika, majiyar ta ce ko a ranar Litinin da ta gabata ’yan bindigar sun kai hari garin Sutti da Takkau duk a karamar hukumar inda sun jikkata mutum biyu. Mataimaki na musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza kan tsaro, Alhaji Gazali Raka ya tabbatar da faruwar lamarin. Alhaji Raka ya bayyana cewa ’yan bindigar sun sace dabbobi da suka haɗa da Shanu...
    Mutane biyun da suka jikkata na karɓar magani a Asibitin Gwamnati na Tangaza. Raka ya buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa don daƙile hare-haren da ke ƙara yawaita a yankin, tare da dawo da zaman lafiya domin ci gaban al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata. Nijar ta ayyana Hausa a matsayin yaren ƙasa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Ministan ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun wani adadi mai yawa na ƙwararrun likitocin da ke da burin fita zuwa wasu ƙasashen duniya aiki, suna fakewa da matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya. Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya. Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma...
    Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin. Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da suke yia  kan fararen hula a yankuna da dama na Gaza. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da samun sabbin adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda adadin shahidai ya kai 50,810 yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 115,688. Adadin wadanda suka raa...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali.  “An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa.  “Daga shekaru uku baya zuwa yanzu a hankali zaman lafiya ya fara dawowa Borno, amma lamarin ya sauya a ‘yan kwanakin nan,” in ji shi Zulum...
    Wasu ‘yan kasar Amurka uku da aka daure bisa laifin yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, yanzu haka suna hannun Amurka bayan yanke hukuncin da aka yi a kansu a makon jiya, kamar yadda wasu jami’an Amurka da na  fadar shugaban kasar Kongo suka bayyana ga kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan  Talata. A ranar 19 ga Mayu, 2024, wasu ‘yan bindiga sanye da kakin sojoji sun mamaye ofishin shugaban kasar DRC Felix Tshisekedi bayan da suka mamaye gidan ministan tattalin arzikin kasar mai barin gado kuma dan takarar shugaban majalisar dokokin kasar Vital Kamerhe. An bayar da rahoton mutuwar mutane shida da suka hada da jami’an ‘yan sanda biyu a lokacin yunkurin...
    A wani mataki na kara nesanta kanta da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka, Nijar ta ayyana harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci. Kamfanin dillancin labarin kasar AFP ne ya ruwaito hakan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 31 ga Maris. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Tun bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Muhammad Bazoum, Nijar ɗin ke ɗaukar matakan nesanta kanta da Faransa, inda ta fara da korar sojojinta da kuma sauyawa wurare da dama da ke da alaƙa da kasar suna. Bayan haka kuma, Nijar ɗin da sauran ƙasashen da Faransan ta yi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kaka da kakanni an san Hausawa  da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta – shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari. Domin...
    Sai dai ya koka da yadda hare-haren da aka kai kwanan nan, inda aka tarwatsa sansanonin sojoji a Wajirko, Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, Wulgo a Gamboru Ngala, Izge a karamar hukumar Gwoza da sauransu wanda hakan ya yi sanadin kashe mutane ‘yan gari da jami’an tsaro, lallai abun damuwa ne matuka.   Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a wani taro na musamman na tsaro wanda ya samu halartar babban kwamandan runduna ta 7 ta rundunar sojojin Nijeriya, Manjo Janar Abubakar Haruna da kwamandojin sassan rundunar da kwamishinan ‘yansanda na jihar da shugabannin sauran hukumomin tsaro.   Taron ya kuma samu halartar Shehun Borno Alh. Dr. Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi; Shehun Bama, Sarakunan Biu, Uba, Askira, Gwoza, yayin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Declan Rice ne ya jefa ƙwallaye biyu a wasan kafin Mikel Merino ya jefa ta uku kuma ta ƙarshe a wasan, hakan ya sa Rice ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar Zakarun Turai da ya ci ƙwallaye biyu daga bugun tazara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa Real Madrid a daren nan a karawar da suka yi ta kwata-fainal a Gasar Zakarun Turai. Arsenal dai ta doke Real Madrid da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Emirates da ke Landan. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansa An kammala minti 45 na karawar babu ci, sai dai alƙaluma sun nuna Arsenal ta kai farmaki sau huɗu yayin da Real ta kai hari sau biyar. Duk da cewa babu ɓangaren da ya samu nasarar zura ƙwallo amma wasan wanda Irfan Peljto na ƙasar Bosnia Herzegovina ya yi alƙalanci ya yi matuƙar...
    Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Turai su kara mu’amala da juna, da bude kofa ga juna don tabbatar da yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata, ta...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali. Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansa “An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa. “Daga shekaru uku baya...
    Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu.   Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu.   Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar. Daga kanmu, magana ta...
    Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya. Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali. Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58 “Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba. “Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi. Kazalika ya soki shirin ‘yan...
    Tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Nduese Essien, ya ce Ma’aikatun Harkokin Jin-ƙai na tarayya da jihohi sun zamo matattarar cin hanci da rashawa a Nijeriya. Essien, ya kuma zargi ministocin ma’aikatun da karkatar da biliyoyin naira da aka ware domin ‘yan ƙasar da ke cikin mawuyacin hali. Kotu ta daure ango wata 6 saboda likin kudi a bikinsa Gaza: Isra’ila ta kashe Falasdinawa 58 a awa 58 “Wani zai yi tunanin ƙirƙirar ma’aikatun nan zai inganta rayuwa da walwalar al’umma, amma abun takaici sun zamo mazurarar sace kuɗin al’umma ba tare da wata shakka ba. “Dukkanin ministocin ma’aikatun jin-ƙan Najeriya, babu wanda ba a zarga ba da karkatar da kuɗin al’umma.” In ji shi. Kazalika ya soki shirin ‘yan...
    Ya jaddada cewa, taken taron ya dace kuma yazo a kan lokaci “wanda na yi imanin cewa, dandalin zai taimaka wajen gabatar da jawabai a bangarori daban-daban na gyare-gyaren kasafin kudi da shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a karkashin shirin renewed hope.”   Ya ce, jawabin da ake gabatarwa a dandalin zai ba da gudummawa ga kudirin dokar gyaran haraji da ke gaban majalisar dokokin kasar don karfafa tsarin tarayyar Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Kula da Jin DDaɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta ayyana ranar Juma’a 11 ga Afirilun 2025 a matsayin ranar ƙarshe da za a kammala biyan kuɗin aikin hajjin bana ga dukkan maniyyatan jihar. Shugaban hukumar, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da manema labarai a Ilori. Alhaji Abdulkadir ya bayyana cewa jimillar kuɗin aikin hajjin bana ya kai naira miliyan 8,459,000. Ya yi kira ga dukkan maniyyatan da suka  fara biyan kuɗi da su tabbatar sun kammala ragowar kuɗin kafin ranar ƙarshe, wato 11 ga Afrilu, domin ba za a ƙara lokaci ba. Alhaji Abdulsalam ya kuma buƙaci maniyyatan da su gaggauta miƙa fasfo ɗin su na tafiya ƙasashen waje ga jami’ansu domin fara...
    Sojojin HKI sun kara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Falasdinawa a Gaza, a dai-dai lokacinda ake kiranta zuwa tsagaita wuta a gazar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar kare fararen hula ta falasdinawa a Gaza, tana fadar haka a safiyar yau Talata. Ta kuma kara da cewa, Ta kuma kara da cewa a daren jiya kadai jiragen yakin yahudawan sun kashe akalla falasdinawa 19 mafi yawansu yara kanana. Labarin ya nakalto kakakin kungiyar kare fararen hula na Gaza Mhmood Bassal yana fadar haka, ya kuma kara da crawa , a garin Deir Balah jiragen yakin yahudawan sun kai hari a kan wani gida inda suka kashe yara 5 da manyan mutane 4. Sannan sun...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza, ta yi tir da gwamnatin Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, saboda dirar mikiyan da ta yi kan Falasdinawa a yankin wadanda suke zanga-zangar beman HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da ta yi a gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a jiya Litinin ce, Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da aka mamaye, suka rufe shagudansu da harkokin kasuwancinsu da kuma ofisoshinsu don neman HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da suke yiwa yan uwansu kuma yan kasarsu a Gaza. Amma kamar yadda jami’an tsaron HKI ta hanasu zanga zanga a wasu wurare, jami’an tsaron gwamnatin Falasdinawa a yankin ma, karkashun...
    Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar. Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi. Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe yanken Sahel 3 Niger,  Mali da Burkiya faso kan kakkabo jirgin saman yaki wanda bai da matuki wanda ya keta sararin samar kasar ta Aljeriya a makon da ya gabata, wanda ya sa kasashen uku suka janye jakadunsu daga kasar. Gwamnatin kasar Mali dai bata yi magana a kan wannan matakin da gwamnatin kasar ta Aljeriya ta dauka ba. Sai dai dakatar da zirga-zirgan jiragen...
    Jami’in ya ce, barazanar da Amurka ke yi game da kara tsananta matakin da za ta dauka, kuskure ne dake nuna muguwar aniyarta ta dakile moriyar sauran kasashe, kuma tabbas Sin ba za ta amince ba ko kadan.   Kasar Sin ta sake nanata ra’ayinta cewa, ba wanda zai ci gajiyar tayar da zaune tsaye a goggayar ciniki, da aiwatar da manufar kariyar ciniki, don haka tana kalubalantar Amurka da ta gyara kuskurenta, tare da soke harajin da ta kakkaba mata, da daina matsa mata lamba kan tattalin arziki da ciniki, da warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar shawarwari bisa turbar mutunta juna. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa da ake tuhumar sa, wanda ya saba wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007. Takardar tuhumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, a Cibiyar Bikin Ali Jita da ke Kano, inda aka ga angon a wani bidiyo yana yin kari da Naira dubu dari a takardun Naira dubu daya-daya...
    Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa gare su ba ta hanyar motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan tsaron farar hula. Isra’ila ta kashe mutane 1,449 tare da jikkata wasu 3,647 tun bayan da ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 18 ga Maris, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Ta kara da cewa yawan Falasdinawa da aka kashe a yakin Isra’ila a Gaza zuwa 50,810, wasu 115,688 kuma sun samu raunuka...
    LEADERSHIP tana karrama mutane da ƙungiyoyin da suka taka rawar gani a fannoni daban-daban kamar gwamnati, kasuwanci da al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa gare su ba ta hanyar motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan tsaron farar hula. Isra’ila ta kashe mutane 1,449 tare da jikkata wasu 3,647 tun bayan da ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 18 ga Maris, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Ta kara da cewa yawan Falasdinawa da aka kashe a yakin Isra’ila a Gaza zuwa 50,810, wasu 115,688 kuma sun samu raunuka...
    Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu. Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi. Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria...
    Kasashen Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga kasa Algeria bayan takaddamar da ta barke tsakaninta da Mali. Kasashen uku da ke karkashin mulkin soja sun sanar da daukar wannan matakin hadin gwiwa ne bayan Mali ta zargi sojojin Algeria da harbo wani jirginta mara matuki a sararin samaniyarta a karshen watan Maris. A ranar 1 ga Afrilu, Algeria ta sanar cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki mai dauke da makamai a sararin samaniyarta, amma ba ta yi karin bayanin ba. A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Mali ta ce hukumomi sun tabbatar da “cikakken yakini” cewa an harbo jirgin ne a cikin “A matsayin harin makiya da aka shirya daga gwamnatin Algeria.” Gobara ta...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin wata ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa da manyan kungiyoyi a kasar, inda ya tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen harkokin mulki, da manufofin harkokin waje, da kalubalen tattalin arziki da zamantakewar kasar. Da yake magana game da kalubalen gudanar da harkokin mulki, shugaban na Iran ya bayyana cewa, ba za a iya cimma gyara halayen kungiyoyi da bangarorin gwamnati ta...
    A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi al-Faqawi da wani matashi mai suna Yousef al-Khazindar sun yi shahada, yayin da wasu ‘yan jarida da suka hada da Ahmed Mansour, Hassan Islayh, Ahmed al-Agha, Mohammed Fayek, Abdullah al-Attar, Ihab al-Bardini, Mahmoud Awad, da Majed Qudaih, suka samu raunuka a tashin bam din. Kungiyar Kafafen Yada Labarai ta Falasdinu ta yi Allah wadai da wannan harin da Isra’ila ta kai a kan tantin ‘yan...
    Hajiya Zainab ta kuma tuna da marigayi mijinta, Sam Nda-Isaiah, wanda ya kafa LEADERSHIP a shekarar 2004. “Tun shekaru ashirin da suka gabata, wanda ya kafa wannan jarida ya shigo harkar wallafa da wani babban buri — Don Allah da kuma ƙasar nan. “Wannan buri har yanzu yana jagorantarmu, kuma da yardar Allah za mu isar da shi zuwa ga ƙarni na gaba,” in ji ta. Ta ƙare da jan hankalin kowa da ya yi tunani a kan irin gudummawar da zai bayar wajen gina Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ci gaba da gudanar da  tarurrukan bita ga maniyyata aikin Hajjin bana, bayan  kammala azumin watan Ramadan. Daraktan Hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, hukumar za ta tabbatar da cewa maniyyata sun sami horo da ilimi kan yadda ake aiwatar da aikin Hajji domin dacewa wannan ibada da suka kashe makudan kudade don gannin sun aiwatar da ita. Alhaji Ahmed Umar Labbo ya ce, za a wayar da kan alhazai da kuma koya musu yadda za su kula da kansu da kuma yadda za su aiwatar da aikin Hajji bisa ga koyarwar addini. Ya ce, ana gudanar da...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har...
    An gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wada ta barke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata kungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargadin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta. A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare hakkin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunkurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu dauke da rubutun bayyana buƙatunsu a wasu hanyoyi da ke Ikeja, babban birnin Jihar Legas. A Jihar Ribas kuma,...
    Shugaban sojin ya ce za a kamo waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’asa, kuma za a hukunta su. Haka kuma ya yi alƙawarin tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyi. A nasa jawabin, Manjo Janar Folusho Oyinlola, kwamandan Operation Safe Haven, ya ce za su ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya musamman a lokacin girbin gonaki. Ya bayyana cewa ganawar da shugabannin yankin na zuwa a lokaci mai muhimmanci duba da yadda matsalar tsaro ke ƙaruwa. Dagacin Manguna, Alhaji Alo Raymond, ya ce hare-haren da ake kai musu na da nasaba da yunƙurin karɓe musu filayen gado. Ya roƙi gwamnati ta kare su da gidajensu, tare...
    Wata gobara da ta ɓarke ta cinye garejin gyaran motocin kamfanin sufurin Borno Express na Gwamnatin Jihar Borno, inda ta lalata motocin bas sama da 10 masu daukar mutane 18 kowacce. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Litinin, bayan wani fashewa mai ƙarfi a harabar garejin. Ko da yake babu wanda ya rasa ransa a wannan lamarin, wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ya samu raunuka yayin da yake kokarin kashe gobarar. Wani ganau ya ce, “Gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar tukunyar gas — inda wani kara mai ban tsoro ya sa ma’aikata da matafiya a yankin suka yi ta gujegujen domin tsira.” Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Mahara sun...
    Kotu ta dage shari’ar kisan Manjo Janar Idris Alkali mai ritaya zuwa ranakun 28 da 29 ga watan Mayu, 2025, domin waɗanda ake tuhuma su fara gabatar da shaidunsu. Babbar kotu da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, ta ɗage shari’ar ne biyo bayan bayan ɓangaren masu ƙara su. gabatar da ga Manjo Janar U. I. Mohammed mai ritaya  game da kisan. Janar Alkali, wanda ya kasance tsohon shugaban gudanarwa a Hedikwatar Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, ya ɓace ne makwanni kaɗan bayan ya yi ritaya daga aikin soja, a lokacin da yake hanyar tafiya Bauchi daga Abuja. Mamacin ne yake tuƙa kansa a lokacin da yake tafiyar inda ya biya ta Jihar Filato. A lokacin da ya ba ce...
    Gwamnatin Sakkwato ta yi barazanar sanya ƙafar wando da waɗanda ta yi zargi suna ƙoƙarin kawo mata cikas a yaƙin da take yi da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro a Jihar. Ta gargaɗi mazauna da su shiga taitayinsu game da yin kalamai da za su iya kawo cikas ga ƙoƙarinta na magance matsalar rashin tsaro a jihar. Wannan gargaɗin ya biyo bayan wata sanarwa da ake dangantawa wani mai suna Basharu Altine Guyawa wanda ya yi ƙoƙarin nuna cewa gwamnati ba ta yi abin da ya kamata ba a fannin tsaro. Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman kan harkokin tsaro, Kanar Ahmed Usman mai ritaya, ya yi wannan gargaɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a...
    Mazauna yankin ƙaramar hukumar Funtua ta Jihar Katsina sun ce ’yan bindiga sun shiga wasu ƙauyukan yankin, inda suka kwashi mutane sama da 50 da suka hada da mata da ƙananan yara. Maharan sun kuma kashe akalla mutum shida, inda suka sake kai wani hari a yankin Ƙaramar Hukumar Ɗandume ta jihar. Rahotanni sun ce tun daga ranar Asabar maharan suka shiga yankin kuma ba su fita ba har zuwa ranar Lahadi da rana. Malam Ya’u Ciɓauna mazaunin garin Layin Gara ne na Ƙaramar Hukumar Funtua, kuma ya ce “Misalin 10:30 na dare suka zo kuma sun kwashi maza da mata da ’yan mata da matan aure da kuma ƙananan yara har 53. “Sun kashe mutum a Layin Gara na...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar manyan jami’an tsaro da na shari’a na gwamnatin. Sun kuma yi Allah wadai da sake dawo da yakin kisan kare dangi da ake yi wa al’ummar Gaza. Iyalan ‘yan Isra’ilar da aka yi garkuwa da su a Gaza su ma sun shiga zanga-zangar, inda suka bukaci a kawo karshen yakin da kuma kulla yarjejeniyar tabbatar da sakin mutanen da aka kama. Kungiyar dai ta ce...
    Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta samar sun shaida cewa, ya zuwa karshen watan Maris na bana, yawan kudaden musanyar kasashen waje da Sin ta adana ya kai dala tiriliyan 3.2407, adadin da ya karu da kashi 0.42%, wato da dala biliyan 13.4 bisa na makamancin watan Fabrairu. Hakan ya sa yawan kudaden ya kai fiye da dala triliyan 3.2 a cikin watanni 16 a jere.   An kuma bayyana cewa, a watan da ya gabata, tattalin arzikin Sin ya ci gaba da tafiya yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, inda jerin manufofin da aka bullo da su bisa yanayin da ake ciki da wadanda za a dauka bisa sauye-sauyen da ake fuskanta, na ci gaba...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta...
    Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD da kuma tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban bisa tushen WTO. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da...
    Jam’iyyar Labour (LP) ta yi barazanar dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da ɗan takarar shugaban kasa na 2023, Peter Obi, idan ba su daina abin da aka kira “aikin da ba a goyon baya” ba. Wannan barazanar ta fito ne bayan taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda aka zargi Otti da shirya taron ba bisa ƙa’ida ba da kuma shirin raba jam’iyyar gida biyu. LP ta kuma nuna damuwa kan shirin Otti na kiran wani taron NEC a ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda aka ce zai kawo cikas ga haɗin kai na jam’iyyar. Haka kuma, jam’iyyar ta gargaɗi Peter Obi game da matakan da za su iya kawo rushewar jam’iyyar, tana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A rana ta 21 da Isra’ila ta sake komawa yaki da al’ummar Falasdinu a Gaza, jiragen yakinta sun kai hare-hare munanan a yankin Khan-Yunus da ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama, da kuma jikkata wani adadin Falaasidinawa  mai yawa. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai kungiyar  ta mayar da martini ta hanyar harba makamai masu linzami akan matsugunin ‘yan share wuri zauna a Asqalan da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar ‘yan sahayoniya. A gafe daya ana gudanar da yajin aiki na gama gari a yankin yammacin kogin Jordan saboda nuna kin amincewa da yadda ‘yan sahayoniya suke yi wa al’ummar Falasdinu kisan kiyashi. Kungiyoyin fararen hula ne su kirayi wannan yajin aikin, wanda ya game yankin na...
    Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban  kwamitin siyasar waje na majalsar shawarar musulunci ta Iran ya gabatar da rahoto akan hali na karshe da ake ciki dangane da batun tattaunawa da Amurka. Arakci ya kuma fadawa kwamitin cewa; Mu ma’abota diflomasiyya da tattaunawa ne, amma za mu tattauna da Amurka ne ba kai tsaye ba,kuma duk da hakan ma har yanzu ba mu...
    Ambaliyar da aka samu sanadiyar mamakon ruwan sama ta kashe aƙalla mutum 33 a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo. Ruwan saman kamar da bakin ƙwarya ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgar ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama. Saudiyya ta musanta hana ’yan Nijeriya biza Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna ƙasar yin hijira. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa wasu mazauna yankin na yunƙurin hijira ta cikin ruwa da ninƙaya, wasu kuma sun yi amfani da kwale-kwale....
     Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China da kuma mai masaukin baki Rasha. Buku da kari Baka’i, ya kuma bayyana cewa za a yi wata tattaunawar a tsakanin Iran da tarayyar turai a matakin masana shari’a. A can kasar Rasha mai Magana da yawun harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta fada wa kafafen watsa labarun kasar ta Rasha cewa, a gobe Talata ne za a yi tattaunawar a tsakanin kwararru daga kasashen...
    Kazalika, a cewar kungiyar, matakin takaita fitar da nau’o’in sinadaran ba zai shafi kamfanoni masu bukatarsu ba, muddin ba sa gudanar da wasu ayyuka daka iya zama illa ga tsaron kasar Sin, da ikon mulkin kan kasar, ko moriyar ci gabanta. Har ila yau, matakan ba za su haifar da cikas ga daidaito da wanzuwar tsarin gudanar da masana’antu na kasa da kasa da na rarraba hajoji zuwa sassan duniya ba. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa  ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu. Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas “Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar. Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji....
    Ya kuma kara da cewa, binciken farko ya nuna cewa, da sa hannun ma’aikatan hukumar ake tafka wannan aika-aika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar da kungiyar ‘Take-it- Back Movement’ da kungiyoyin fararen hula suka shirya a fadin kasar ya zo daidai da ranar bikin ranar ‘yansanda ta kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci LEADERSHIP ta tuna cewa, hukumomin ‘yansanda sun yi gargadi...
    Ana fargabar cewa kimanin ’yan sa-kai 13 ne suka rasa rayukansu a wasu hare-hare da wasu ’yan bindiga da ake zargin mayaƙan Lakurawa ne suka kai Jihar Kebbi a jiya Lahadi. Lamarin ya faru ne a yankin Morai na Ƙaramar Hukumar Augie — ɗaya daga cikin yankunan da ake cewa mayaƙan Lakurawa na da sansani. HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Wani mazauni, Malam Ibrahim Augue, ya ce maharan sun kashe mutum shida ne, suka kwashe shanu, sai ’yan sa-kai suka bi su. “A nan suka yi wa ’yan sa-kan kwanton ɓauna, suka buɗe musu wuta, inda suka kashe guda 13 daga cikinsu.” Ƙoƙarin...
    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa. Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama. A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilastawa wasu mazauna ƙasar yin  hijira a yayin da wasu suka yi amfani da kwale-kwale kamar yadda jam’in kamfanin dillancin labaran AFP ya shaida. Wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa, sun maƙale a saman gidajensu bayan da ruwan ya mamaye matakalar shiga gidanjensu. Bugu da...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila. Kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da shirin don kula da lafiyar al’ummar jihar musamman masu karamin karfi. Dr Abdullahi Kainuwa yana mai cewar a yanzu haka gwamnatin jihar tana gudanar da aikin Dandamalin sabon asibitin kashi na garin Gumel kan naira miliyan 380. A cewar sa, za a bada kwangilar sayen kayayyakin asibitin Kashi na naira miliyan dari shida. Kwamishinan ya kara da cewar gwamnatin jihar ta kammala aikin gina dakunan...
    Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi marar matuki na kasar Mali a farkon wannan wata. Aljeriya dai ta kakkabo jirgin sojojin na Mali marar matuki a cikin daren ranar 31 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, matakin da kasashen uku sukayi tir da shi. A cewar gwamnatin Algiers, jirgin mara matuki da ake magana a kai ya shiga cikin kasar ne, saidai sojojin Mali sun tabbatar da cewa jirgin bai shiga...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida kusa da wani asibiti a Khan Younis da sanyin safiyar ranar Litinin din nan. Akalla mutane bakwai ne kuma suka jikkata a harin. A cikin wani rahoto da aka buga a ranar 1 ga Afrilu, Cibiyar Watson ta ce yakin da Isra’ila ta yi a Gaza ya kasance mafi muni ga ma’aikatan yada labarai da aka yi rikodin kuma...
    Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da rubutun bayyana buƙatunsu a...
    Iran ta sake nanata matsayinta na kin shiga shawarwari kai tsaye da Amurka kan shirinta na nukiliya, maimakon haka ta bukaci a ci gaba da shawarwarin ta hanyar masu shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wata tattaunawa da aka da Washington, kuma ba za a yi irin wannan tattaunawa ba sai dai ta hanyar masu shiga tsakani. “Mun bayyana matsayinmu, muna goyon bayan bin hanyoyi na  diflomasiyya da tattaunawa, amma ta hanyar masu shiga tsakani. Tabbas, ba a gudanar da wata tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da Amurka ba, ” in ji Araghchi a cikin wata sanarwa da ya fitar a dandalin Telegram. Kalaman nasa sun zo ne bayan da shugaban...
    Wani mamba na kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar ta Lebanon ya soki hare-haren da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila take kai wa a kudancin kasar Lebanon da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta, yana mai jaddada cewa Amurka ce ke da alhakin kai hare-haren wuce gona da iri na sahyoniyawan. A cewar Al-Mayadeen, mazauna kudancin kasar Lebanon sun binne gawawwakin shahidan Hizbullah 14 a garin Blida a wani gagarumin biki. Hassan Fadlallah, wakilin kungiyar Hizbullah a majalisar dokokin kasar Lebanon ya bayyana a yayin jawabinsa cewa: Gwamnatin Sahayoniya tana cin gajiyar raunin gwamnatin Lebanon ta yi, kuma muna bukatar matsayin da ya kunshi ayyuka na zahiri, hatta a matakin siyasa da diflomasiyya. Ya kara da cewa: “Muna kira ga gwamnatin...
    Edwin Wagensfeld, mai tsattsauran ra’ayi mai tsattsauran ra’ayi kuma mai magana da yawun kungiyar Pegida ta kasar Holland, ya kona kur’ani a gaban zauren majalisa a birnin Amsterdam, a wani mataki na nuna kyama ga Musulunci, kuma wannan matakin ya haifar da fushin ‘yan siyasa da ‘yan kasar ta Holland. A cewar gidan talabijin na Aljazeera, wannan mataki na nuna kyama ga addinin musulunci, wanda ya gudana a yammacin ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu, ya janyo cece-kuce da suka da yawa. Wagensfeld dai ya shahara da matsananciyar adawa da Musulunci, kuma wannan matakin ya zo daidai da kalaman nasa inda ya yi ikirarin cewa an aiwatar da wannan aiki (kona kur’ani) ne sakamakon karin matsin lamba da aka fuskanta...
    A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
    Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da wadannan hare-hare tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin jama’ar Jihar Filato. ACF ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da hada...
    Kwanan nan wani mai kiwon karnuka a Indiya ya biya Rupee miliyan 500 — kwatankwacin Naira biliyan 8 da miliyan 949 da dubu 481 da 589 domin sayen wani karen kerkeci na jinsin karen Shephard Caucasian, wanda hakan ya sa karen ya zama mafi tsada a duniya. Karen mai suna Cadabomb Okami, an bayar da rahoton cewa, an yi kiwon karen mafi tsadar ne a Amurka kuma S. Satish, wani mai sha’awar kiwon kare a birnin Bengaluru da ke Indiya kuma shugaban kungiyar masu kiwon karnukan Indiya ne ya saya. NAJERIYA A YAU: Mene ne Tasirin Shirin NYSC Bayan Shekaru 50 Da Kafa Shi? ACF ta nemi Gwamnatin Tarayya ta kawo ƙarshen kisan jama’a a Filato Ya shahara saboda tarin...
    Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23. Fulham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa. Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta...
    Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an soke gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin. Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban. Idan...
    Aƙalla mutane 30 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun mutu a wani mummunan hari da kungiyar ‘yan sa kai ta cikin gari ta yi a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru, jihar Zamfara. Kamar yadda wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana daga bayanan sirri, harin ya faru ne a kimanin karfe 2 na rana a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu. Mun Rage Tasirin ‘Yan Bindiga A Kebbi Da Zamfara – Sojoji Nasara A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda: Tattalin Arziƙin Jihar Zamfara Na Ƙara Haɓaka – Gwamna Lawal  An ce ‘yan fashin suna kan hanyarsu ta kai hari wani kauye kusa da su, amma sai suka yi kicibus da ‘yan sa kai na yankin,...
    Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da ƙananan yara. ’Yan sanda sun soke gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da waɗannan hare-hare tare da miƙa sakon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma ɗaukacin jama’ar Jihar Filato. Ƙungiyar...
    Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko. Ya tabbatar da cewa kwasa-kwasai har guda 78 ne jami’an NBTE suka nazarta a yayin wannan ziyararz, “Tawagar sun gama aikin su na ziyarar, yanzu haka muna zaman jiran sakamakon bincike da bin sawun nasu ne,” ya ƙara shaida. A nata ɓangaren, Dakta Fatima Umar, daraktan shirye-shiryen kwalejoji kuma jagorar tawagar na NBTE, ta buƙaci kwalejin Kimiyya da fasaha na gwamantin tarayya da ke Bauchi...
    Game da matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya”, kasar Sin ta gabatar da jerin matakai don mayar da martani, da kuma bayyana ra’ayin gwamnatin kasar na kin amincewa da sabon tsarin haraji na kasar Amurka. Cikin bayanin da Sin ta fitar a ranar 5 ga wannan wata, ta yi nuni da cewa, kasar Amurka ta yi amfani da haraji a matsayin makamin matsawa sauran kasashe lamba da neman samun moriya ita kadai, wanda mataki ne da aka dauka bisa ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya da cin zarafin tattalin arziki, kuma Sin ta jaddada cewa, ba ta jin tsoron tinkarar wannan batu, kuma za ta ci gaba da aiwatar da manufofin cinikayya masu inganci...
    An gudanar da taro na farko na kwamitin raya cinikayya da kiyaye muhalli na hukumar kula da cinikayya ta duniya wato WTO na shekarar 2025 a birnin Geneva dake kasar Switzerland a kwanakin baya, inda tawagar wakilan kasar Sin ta karbi bakuncin taron tattaunawa kan hadin gwiwar fasaha da cinikayya da sana’o’i masu kiyaye muhalli, inda aka gabatar da dabarun Sin na raya sana’o’i da fasaha masu kiyaye muhalli. A cikin jawabansu, masanan Sin sun yi amfani da ayyukan samar da makamashin da ake iya sake amfani da su, a kasashen Habasha da Sri Lanka da kuma aikin daidaita matsalar wutar lantarki na Afirka da sauransu a matsayin misalan dabarun Sin na hadin gwiwar fasaha. Fasahohin Sin sun kunshi fannnoni...
    Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya soke gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, kan hawan sallah. Maimaikon ya Sarkin ya je Abuja domin yi masa tambayoyi, Sufeto Janar ya umarci rundunar ’yan sandan jihar, yi wa Sanusi II tambayoyi. Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da hare-haren Filato, sun nemi a yi adalci Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Kakakin ’yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne, ya bayyana hakan, inda ya ce an soke gayyatar ne bayan da wasu manyan mutane a ƙasar suka shiga lamarin. Ya ƙara da cewa ’yan sanda na son kauce wa duk wani da zai danganta lamarin da siyasa ko wani abu daban.  ...
    Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata,  da kuma fasahar kera makamin idan tana bukatar yin hakan.   Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Agentina a yan kwanakin da suka gabata. Ya kuma kara jaddada cewa a halin yanzu JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana da abinda ake kira “sinadarin Uranium da ta gasa, wanda yawansa zai iya samar da makaman nukliya har zuwa 6-ko 7, amma dai bata kera makamin ba. Abinda tambaya a nan itace tunda hukumar ta tabbatar da cewa...
    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila. Hakan ya sa ta kasance kungiya ta farko a tarihin gasar da ta koma baya (relegation) bayan buga wasanni 31 kacal, Southampton ta samu maki 10 a wasanni 31 an zura mata kwallaye 74 a raga sannan kuma ta zura kwallaye 23 kacal a bana. Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028 Ramsdale tsohon mai tsaron ragar...
    Gwamnatin Kasar Iran ta bada sanarwan samun sabbin ci gaba a fagen fasaha da kuma kayakin da suka shafi makamashin Nukliya, wanda za’a baje kolinsa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekarar , wato ranar makamashin Nukliya ta kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasa kuma shugaban hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran Mohammad Eslami yana fadar haka a yau Lahadi. Ya kuma kara da cewa, masana fasahar nukliya ta kasar sun samar da sabbin ci gaba a fagen makamashin nukliya wadanda suka hada da magungun wadanda suka yi amfani da sinadarin Nkliya don samar da su, da kuma ci gaba a fannin ilmi da dama, duk tare da fasaha da kuma...
    Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF), ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wasu ƙauyuka na Ƙaramar Hukumar Bokkos da ke Jihar Filato. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Ruwi, Manguna, Daffo, Josho da Hurti. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana waɗannan hare-hare a matsayin rashin hankali da tausayi. Ya ce an kashe mutane da dama ciki har da mata da yara, yayin da wasu da dama suka jikkata. Ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare na barazana ga zaman lafiya da haɗin kan yankin Arewa. A wata sanarwa da kakakinsa, Ismaila Uba Misilli, ya...
    Nemi adalci maimakon babakere. Cin zali ta hanyar kakaba haraji da Amurka ke yi, ya haifar da suka da adawa da martani daga kasashe da dama. Takarda mai dauke da matsayar kasar Sin da aka fitar dangane da cin zalin ta samu goyon bayan daga kasa da kasa. Sakamakon wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin masu amfani da intanet a fadin duniya, ya nuna wadanda suka amsa nazarin na kira ga kasashen duniya su hada hannu su dauki mataki domin bijirewa salon cin zali irin na Amurka, su kare hakkokinsu da kuma tsarin cinikayya da tattalin arziki na duniya. Bisa fakewa da daidaito da adalci, Amurka na son cin riba daga faduwar wasu, inda take sanya muradunta sama...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yada wasu hutunan bidiyo wanda yayi kama da na jiragen yakin kasar ne kan kasar Yemen, inda suka yi ruwan boma bomai a kan su a matsayin yan ta’ada wadanda suke shirin yakar Amurka, amma daya baya shaidu sun ta tabbatar da cewa taron ta yan kasar ta Yemen ne a birnin Hudaida wadanda suke bukin sallah karamar da ta gabata a ranar 4 ga watan Afrilun da muke ciki. Labarin ya kara da cewa wannan aikin na sojojin Amurka ya na iya zama laifin yaki wanda ana iya gurfanar da gwamnatin Amurka kan laifukan yakin da ta ke aikatawa a yake-yakenta na kasashen waje. Wannan zargin yana cewa ne bayan da sojojin Amurka...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa ta ware kudade don gina kananan cibiyoyin kiwon lafiya a duk fadin kasar. Jaridar daily Trust ta Najeriya ta nakalto mataimakin shugaban kasa Alhaji Shetima yana fadar haka a ranar Asabar a lokacinda yake kaddamar da cibiyar yaki da cutar daga a cikin asbitin koyon aikin likitanci ta OOUTH dage birnin shagamu na jihar Oyo. Mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa shirin gina wadannan kananan cibiyoyin kiwon lafiya dai yana daga cikin babban shirin gwamnatin mai ci na kyautata cibiyoyin kiwon lafiya a kasar gaba daya.
    Dakarun Soji  Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai. Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa. Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani A cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa. Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske. Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna...
    Dakarun Soji  Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai. Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa. Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani A cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa. Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske. Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna...
    Kakakin rundunar tsaron teku ta kasar Sin Liu Dejun, ya bayyana a yau Lahadi cewa, an kori wani jirgin kamun kifi na kasar Japan da ya shiga yankin ruwan kasar Sin na tsibirin Diaoyu Dao ba bisa ka’ida ba. A cewarsa, rundunar ta dauki matakan da suka dace bisa doka, ta gargadi jirgin sannan ta kore shi, bayan ya shiga yankin ruwan kasar Sin tsakanin ranar Asabar da Lahadi. Sau Biyu Ake Yin Girbin Aya A Shekara – RMRDC Gwamnatin Yobe Ta Ƙaryata Rahoton Bayyanar Boko Haram A Babban Birnin Jihar Da yake bayyana tsibirin na Diaoyu Dao da tsibiran dake karkashinsa a matsayin mallakin kasar Sin, Liu Dejun ya bukaci Japan ta gaggauta dakatar da ayyukanta da suka saba...
    Jirgin da ke ɗauke da mutane sama da 200 daga Bali a ƙasar Indonesia zuwa Ostireliya, ya yi juyawar dole bayan wani fasinja ya yi yunƙurin buɗe ƙofarsa yayin da jirgin kamfanin Jetstar ke shawagi a tekun Indiya. “Mun samu wani jirgin sama ya koma Denpasar (filin jirgin sama na Bali) a daren Talata bayan wani ruɗaɗen fasinja ya yi yunƙurin buɗe ɗaya daga cikin kofofin jirgin kuma ya ci zarafin ma’aikatanmu,” a cewar wata sanarwa da kamfanin jirgin sama ya fitar game da lamarin a daren Litinin, 31 ga Maris. Ɓarawo ya haɗiye ɗan kunnen Naira biliyan ɗaya Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya Hukumomin yankin Bali ne suka fitar da fasinjan daga cikin jirgin. A...
    A bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar mutane su rungumi fannin noman Aya, duba da cewa; hanya ce ga wanda ya zuba jarinsa a fannin, zai iya kara samar wa da kansa kudaden shiga. Sai dai, akasari an fi yin nomanta a Arewacin Nijeriya, musamman ma kuma a Jihar Katsina. Haka zalika, fannin na samar da ayyukan yi kodai na kai tsaye ko kuma wanda ba na kai tsaye ba. Bugu da kari, Aya na taimawa wajen inganta lafiyar jikin Dan’adam, kara karfafa kashin jikin mutum, daidaita sigan da ke jikin bil Adama da dai sauran makamantansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024. Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana zuwa 1.43 ya taimaka wajen sanya sashin mai a matakin ci gaba na dan kadan a maimakon yin kasa sosai. A gabaki-daya, sashin mai ya taimaka da kaso 00.7 cikin 100 na ci gaban tattalin arziki cikin gida (GDP) a tsawon wannan lokacin. “Vangaren da ba na mai ba wanda ya samu tagomashi, ya samu saurin havaka da kaso 3.69 idan aka kwatanta da na...
    Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.   Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, wasu Fulani daga Karamar Hukumar Jahun ta Jihar Jigawa sun yi imani cewa, idan suka ci naman akuya, maza za su kamu da cututtukan da suka shafi maraina, musamman ciwon mara da aka fi sani da ƙaba ko kumburin maraina, yayin da mata kuma za su kamu da ƙuraje a fatar jikinsu. Malam Aminu Muhammad Jahun ya shaida wa wakilinmu cewa, tun yana yaro yake guje wa cin naman akuya, yana mai bayyana cewa, yawancin Fulani a yankinsu ba sa cin naman akuya, kuma idan aka ci, za a kamu da ciwon ƙaba. Tsohon Gwamnan Oyo Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36...
    Olunloyo ya jagoranci jihar Oyo tsakanin 1 ga Oktoba, 1983 zuwa 31 ga Disambar 1983.   Rasuwar marigayi dan siyasar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da tsohon Editan jaridar Nigerian Tribune, Barista Oladapo Ogunwusi ya fitar a ranar Lahadi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya karvi ibadu. “Ina addu’ar Allah ya ci gaba da ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da hadin kai a tsakani. Za mu ci gaba da shaidar bukukuwan Sallar. “Ina kuma gode wa shugabannn addininmu bisa koyar da mu alkur’ani mai girma. Ina fatan wasu shekarun za su samemu cikin kwanciyar hankali,” Sanwo-Olu ya shaida. Ita kuma a nata vangaren, matar gwamnan jihar, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, ta nuna farin cikinta kan yadda ake gudanar da shagulan salla a jihar cikin kwanciyar hankali tare da yin kira ga mutanen Legas da su ci gaba da nuna soyayya da kauna ga wadanda ba su da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana sharuddan da Tehran ta gindaya na ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya, yana mai jaddada aniyar kasar ta fuskar diflomasiyya tare da tsayawa tsayin daka kan muradun kasa. Da yake magana a wani taron sabuar shekarar Nowruz tare da jami’an Iran, jakadu, da wakilan kasa da kasa a daren ranar Asabar, Araghchi ya jaddada daukar nauyin Iran kan harkokin duniya. Ya lura cewa martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump an yi shi ne don dacewa da sauti da kuma abin da ke cikin saƙon na asali, ta hanyar buɗe hanyoyin diflomasiyya. Araghchi ya yi nuni da cewa, yin cudanya kai tsaye da jam’iyyar da ke ci gaba da...
    Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo, gami da cewa motocin daukar marasa lafiya ba su da haskensu na gaggawa, kuma sojojin Isra’ila sun shiga wuta. Rahoton sojojin Isra’ila daga baya ya yi ikirarin cewa sojojin na Isra’ila sun boye gawarwakin da motocin daukar marasa lafiya a karkashin yashi “don hana namun daji cinye su.” Wannan tsari dai ba a saba gani ba ne ga dakarunsu na aikata kisan kiyashi tare da...
    Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.” A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki. Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa,...
    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a amince da shi ba ne, bai dace ba, kuma babban abin damuwa ne,’ in ji Sakataren Harkokin Waje David Lammy, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.” Lammy wanda ya bayyana cewa Birtaniya tana tuntuɓar ‘yan majalisar domin ba su goyon baya, kuma ya bayyana wa hukumomin Isra’ila ƙarara cewa “ba haka ake yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya mu’amala ba.” “Abin da gwamnatin Birtaniya...