2025-04-13@12:15:16 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1158
«Barau Bungudu»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Lahadi, ta laƙume ƙauyukan Wanori, Sarari, da Nuguri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Aminiya ta rawaito cewa gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu, da kuma raba daruruwa da muhallin su. Saudiyya ta musanta hana ’yan Nijeriya biza Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi Lamarin dai ya tilasta mazauna ƙauyen Wanori yin ƙaura domin gujewa gobarar da ke ci gaba da yaɗuwa. Ibtila’in da ya zuwa lokacin wallafa wannan rahoton ba a gano musabbbinsa, ya ƙara dagula wa al’ummar ƙauyen lissafi, kasancewar an samu makamancin hakan a baya, ga kuma ‘yan ta’addan Boko Haram da ke tilasta su yin gudun hijira. Duk ƙoƙarin da manema labarai suka...
Jam’iyyar Labour (LP) ta yi barazanar dakatar da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da ɗan takarar shugaban kasa na 2023, Peter Obi, idan ba su daina abin da aka kira “aikin da ba a goyon baya” ba. Wannan barazanar ta fito ne bayan taron kwamitin zartarwa na Jam’iyyar (NEC) da aka gudanar a Abuja, inda aka zargi Otti da shirya taron ba bisa ƙa’ida ba da kuma shirin raba jam’iyyar gida biyu. LP ta kuma nuna damuwa kan shirin Otti na kiran wani taron NEC a ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda aka ce zai kawo cikas ga haɗin kai na jam’iyyar. Haka kuma, jam’iyyar ta gargaɗi Peter Obi game da matakan da za su iya kawo rushewar jam’iyyar, tana...
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin alkahira a jiya Lahadi, inda ya sami kyakkyawar tarba daga Abdulfattah al-Sisi. Ziyarar ta shugaban kasar Faransa a Masar tana a karkashin tattaunawar da aka bude ne a yau Litinin da kasar Jordan ta kuma ita kanta mai masaukin baki akan halin da Gaza take ciki. Yin wannan taron dai ya biyo bayan sake dawo da yaki da HKi ta yi ne a Gaza, saboda ta ki amincewa da bude shafi na biyu yarjejeniyar tsagaita wutar yaki. A yau Litinin shugabannin kasashen na Masar da kuma Faransa sun yi tir da sake dawo da yaki da Isra’ila ta yi a zirin Gaza, haka nan kuma kin amincewa da shigar da kayan agaji...
Rahotanni da suke fitowa daga yankin ‘Sahalul-Khayam na kasar Lebanon sun ce, wasu ‘yan asalin kasar Syria su 2 sun yi shahada sanadiyyar harin da Isra’ila ta kai da jirgin sama maras matuki sa’o’i 2 da su ka wuce. Da safiyar yau Litinin ma dai wani karamin jirigin ‘yan sahayoniya ya jefa bom akan wata mota da take tafiya a garin “Beit-Lif” a kudancin kasar da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar wanda ke cikinta. Hare-haren da HKI take kai wa a kudancin Lebanon din dai yana a karkashin keta hurumin kasar da kuma kin aiki da kudurin MDD mail amba 1701 na tsagaita wutar yakin da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na wannan shekara ta 2025.
Hukumar Yaƙi Da Cututtuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya, NCDC ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar sanƙarau a Nijeriya ya kai 151. Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna ƙaruwar waɗanda suka kamu da cutar daga 74 zuwa 156 a jihohin ƙasar 23. Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back Jihohin da aka fi samun yawan mace-macen sun haɗa da Kebbi, da Sakkwato da Katsina da Jigawa da Yobe da Bauchi da Gombe da Borno da Kano da Adamawa da kuma Oyo. NCDC ta ce ta tabbatar da kamuwar wasu mutum 126 daga cikin mutum 1,858 da aka...
Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23. Fulham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa. Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta...
Aƙalla mutane 30 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne, sun mutu a wani mummunan hari da kungiyar ‘yan sa kai ta cikin gari ta yi a yankin Dansadau na karamar hukumar Maru, jihar Zamfara. Kamar yadda wani masani kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana daga bayanan sirri, harin ya faru ne a kimanin karfe 2 na rana a ranar Alhamis, 4 ga Afrilu. Mun Rage Tasirin ‘Yan Bindiga A Kebbi Da Zamfara – Sojoji Nasara A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda: Tattalin Arziƙin Jihar Zamfara Na Ƙara Haɓaka – Gwamna Lawal An ce ‘yan fashin suna kan hanyarsu ta kai hari wani kauye kusa da su, amma sai suka yi kicibus da ‘yan sa kai na yankin,...
Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko. Ya tabbatar da cewa kwasa-kwasai har guda 78 ne jami’an NBTE suka nazarta a yayin wannan ziyararz, “Tawagar sun gama aikin su na ziyarar, yanzu haka muna zaman jiran sakamakon bincike da bin sawun nasu ne,” ya ƙara shaida. A nata ɓangaren, Dakta Fatima Umar, daraktan shirye-shiryen kwalejoji kuma jagorar tawagar na NBTE, ta buƙaci kwalejin Kimiyya da fasaha na gwamantin tarayya da ke Bauchi...

Trump Ya Yada Hutunan Bidiyo Wadanda Suka Nuna Yadda Sojojin Amurka Suka Kashe Mutanen Yemen Wadanda Suke Bukukuwan Salla Karama
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya yada wasu hutunan bidiyo wanda yayi kama da na jiragen yakin kasar ne kan kasar Yemen, inda suka yi ruwan boma bomai a kan su a matsayin yan ta’ada wadanda suke shirin yakar Amurka, amma daya baya shaidu sun ta tabbatar da cewa taron ta yan kasar ta Yemen ne a birnin Hudaida wadanda suke bukin sallah karamar da ta gabata a ranar 4 ga watan Afrilun da muke ciki. Labarin ya kara da cewa wannan aikin na sojojin Amurka ya na iya zama laifin yaki wanda ana iya gurfanar da gwamnatin Amurka kan laifukan yakin da ta ke aikatawa a yake-yakenta na kasashen waje. Wannan zargin yana cewa ne bayan da sojojin Amurka...
Dakarun Soji Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai. Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa. Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani A cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa. Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske. Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna...
Dakarun Soji Operation WHIRL STROKE (OPWS), sun kashe ’yan bindiga uku a Ƙaramar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba, tare da lalata sansanoninsu da kuma ƙwato makamai. Wannan harin ya faru ne ranar 5 ga watan Afrilu, kamar yadda kakakin rundunar, Olubodunde Oni, ya bayyana a wata sanarwa. Fasinja ya yi ƙoƙarin buɗe ƙofar jirgi a sararin samaniya Abin da ya sa ba ma cin naman Akuya — Fulani A cewarsa, da sojoji suka isa yankin Chibi, sai ’yan bindigar suka fara tserewa. Amma sojojin sun bi sahunsu, suka yi musayar wuta da su, har suka kashe uku daga cikinsu, sannan suka lalata maɓoyarsu tare da ƙwato makamai masu hatsarin gaske. Sanarwar ta kuma ce sojojin sun daɗe suna...
A bisa wannan dalili ne yasa akwai bukatar mutane su rungumi fannin noman Aya, duba da cewa; hanya ce ga wanda ya zuba jarinsa a fannin, zai iya kara samar wa da kansa kudaden shiga. Sai dai, akasari an fi yin nomanta a Arewacin Nijeriya, musamman ma kuma a Jihar Katsina. Haka zalika, fannin na samar da ayyukan yi kodai na kai tsaye ko kuma wanda ba na kai tsaye ba. Bugu da kari, Aya na taimawa wajen inganta lafiyar jikin Dan’adam, kara karfafa kashin jikin mutum, daidaita sigan da ke jikin bil Adama da dai sauran makamantansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba. Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan tare da addu’ar Allah ya karvi ibadu. “Ina addu’ar Allah ya ci gaba da ba mu zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da hadin kai a tsakani. Za mu ci gaba da shaidar bukukuwan Sallar. “Ina kuma gode wa shugabannn addininmu bisa koyar da mu alkur’ani mai girma. Ina fatan wasu shekarun za su samemu cikin kwanciyar hankali,” Sanwo-Olu ya shaida. Ita kuma a nata vangaren, matar gwamnan jihar, Dakta Ibijoke Sanwo-Olu, ta nuna farin cikinta kan yadda ake gudanar da shagulan salla a jihar cikin kwanciyar hankali tare da yin kira ga mutanen Legas da su ci gaba da nuna soyayya da kauna ga wadanda ba su da...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana sharuddan da Tehran ta gindaya na ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya, yana mai jaddada aniyar kasar ta fuskar diflomasiyya tare da tsayawa tsayin daka kan muradun kasa. Da yake magana a wani taron sabuar shekarar Nowruz tare da jami’an Iran, jakadu, da wakilan kasa da kasa a daren ranar Asabar, Araghchi ya jaddada daukar nauyin Iran kan harkokin duniya. Ya lura cewa martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump an yi shi ne don dacewa da sauti da kuma abin da ke cikin saƙon na asali, ta hanyar buɗe hanyoyin diflomasiyya. Araghchi ya yi nuni da cewa, yin cudanya kai tsaye da jam’iyyar da ke ci gaba da...
Gwamnatin kasar Sin ta yi kakkausar suka da bayyana adawarta ga matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya.” A cikin wata sanarwar da ta fitar, ta yi Allah-wadai da matakin na Amurka, wanda ya kasance daukar mataki bisa radin kai, da kuma kariyar cinikayya da cin zarafin tattalin arziki. Sanarwar ta kara da cewa, ta hanyar fakewa da abin da take kira “ramuwar gayya” da “adalci,” a zahiri dai Amurka ta tsunduma a aiwatar da dabarun danniya da babakere, tana neman cimma manufarta ta “Amurka na gaba da komai” da kuma “Amurka ta fi kowace kasa.” Har ila yau, Amurka na amfani da harajin fito don kawo cikas ga tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa,...
Sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya ce ba wanda zai ci ribar yakin cinikayya a yayin da ake ta cacar baka kan harajin fito da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa duniya. Antonio Guitess ya yi wannan gargadin ta bakin kakakinsa inda ya yake bayyana cewa, “ba wanda ke yin nasara a yakin na cinikayya. ” Yana mai cewa, a yayin da ake samun karuwar adawa daga sassa daban daban, shugaban Amurka Donal Trump a ranar Laraba ya rattaba hannu kan wani umarnin zartarwa kan abin da yake kira “harajin fito na ramuwar gayya,” wanda ya sanya kashi 10 cikin dari na mafi karancin harajin fito, da karin sama da haka kan wasu abokan cinikayyar kasar. A wani...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya soki abunda ya danganta da barazanar Amurka ga Teheran, yana mai cewa kasarsa a shirye take ta shiga tattaunawa ta hakika ba tare da barazana ba. “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman tattaunawa ta gaskia, a yayin da suke barazana ga Iran a daya bangaren kuma suna neman yin shawarwari,” in ji Pezeshkian a ranar Asabar. “Idan kuna neman shawarwari, to me yasa kuke yin barazana? A yau, Amurka ba wai kawai ta wulakanta Iran ba har ma da duniya, kuma wannan hali ya saba wa bukatar tattaunawa,” in ji shi. Kalaman na Pezeshkian sun zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Tehran da ta shioga shawarwari kai tsaye...

Gwamnatin Kasar Sin Ta Caccaki Matakin Kakaba Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba Da Amurka Ta Dauka, Ta Kuma Sha Alwashin Kare Moriyarta
Ta kuma bukaci Amurka da ta daina amfani da harajin fito a matsayin makami don dakile ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, da kuma tauye hakkin samun halaltacciyar ci gaba na al’ummar Sinawa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu nay au zai yi magana kan cewa “Amurka ba zata taba zama mai sulhuntawa tsakanin HKI da Falasdinawa ba” wanda ni tahir amin zan karanta. A dai dai lokacinda rikicin gaza ya zama matsalar ta duniya a halin yanzu, da dama daga cikin masana suna ganin gwamnatin Amurka wacce ta kasance mai goyon bayan HKI na asali ba zata kuma zama mai shiga tsakanin don kawo karshen rikicinta da falasdinawa ba. Dangane da wannan shafin yanar gizo mai suna “Alkhanadik’ ya rubuta wani sharhi dangane da yakin na gaza a jiya Asabar yana cewa, a dai dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka ta kasance bangare babba a cikin haddasa matsaloli ga al-ummar Falasdinu na...
Malamai magada Annabawa ne, dole ka yarda ko ka zama jahili, da yawa daga cikin masu rike da mukaman da suke hana mu zaman lafiya shekarunsu sun tafi sun girma, ko ammanta sittina ko saba’una ake yi yanzu, daga karshe muna rokon ku da kanku ku nemawa jihar abun da za ta yi alfahari da ku bayan babu ku, domin Dole za ku mutu ku bar jihar da mutane a ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times” masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.” Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abindaya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da cewa sojojin Isra’ilan suna yin abinda suke yi ne a tsare,kuma duniya ta yi shiru.” Jaridar “New York Times” ta watsa faifen bidiyo dake dauke da muryar wani ma’aikacin agaji wanda daya ne daga cikin wadanda aka sami gawawwakinsu a cikin wani babban kabari a yankin Rafaha. Bidiyon ya nuna yadda sojojin Isra’ila su ka kai wa masu aikin agaji hari da gangan, sun kuma...
Gwamnatin kasar Amurka ta sanar da sanya harajin fito na ramuwar gayya kan dukkan kawayen cinikayyarta a ranar 2 ga wata, inda kasar Sin ta mayar da martani nan take, da zummar kiyaye halastaccen hakkinta. Daga baya a ranar 3 ga wata, Sin ta sanar da wasu jerin matakai, ciki har da kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, da shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka, gami da kara wasu kamfanonin Amurka a cikin jerin sunayen kamfanonin da ta dauki matakin hana fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje a kansu, matakan da suka janyo babbar raguwar darajar takardun hannayen jari...

Ofishin Jakadancin Sin Da Ke Amurka Da Jakadan Sin A Burtaniya Sun Nuna Adawa Da Matakin Harajin Fito Na Ramuwar Gayya Da Amurka Ta Dauka
A ranar Alhamis ne, ofishin jakadancin kasar Sin da ke Amurka da jakadan Sin a Burtaniya Zheng Zeguang, suka bayyana matukar kin amincewa da harajin fito “na ramuwar gayya” da Amurka ta kakaba. Suna masu nuni da cewa, Amurka ta sanar da karin harajin fito kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashe da dama ciki har da kasar Sin, ta hanyar fakewa da abin da take kira ramuwar gayya, ofishin jakadancin Sin da ke Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, matakin ya saba wa ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kuma ya saba wa ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban. Kana, ya bukaci Amurka da ta gyara kurakurenta, tare da warware sabanin cinikayya tsakaninta da kasar Sin...
Direba da kwandastan motar bas sun tsere domin tsira da rayukansu, inda suka bar fasinjoji a ciki yayin da wata motar bas ta BRT ta kama wuta a Maryland da ke Jihar Legas da safiyar ranar Asabar. Majiyar Channels TV da ke wajen da lamarin ya faru, ta ce motar ta taso ne daga yankin Ikorodu tana kan hanyar zuwa CMS a lokacin da lamarin ya faru. Rashin tsaro a Filato ya wuce rikicin manoma da makiyaya – Muftwang An ceto fasinjoji 14 a hannun ’yan bindiga, 3 sun rasu a Benuwe Ya zuwa lokacin da aka gabatar da wannan rahoton, masu bayar da agajin gaggawa da suka haɗa da jami’an ’yan sandan Nijeriya, da hukumar kula da zirga-zirgar ababen...
Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji. La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani savani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za...
Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO) da asusun lamuni na duniya (IMF) sun nuna damuwa game da tabarbarewar tattalin arziki daga sabbin harajin da gwamnatin Trump ta laftawa duniya, suna masu gargadin cewa hakan zai iya kawo cikas ga harkokin kasuwanci da kuma ci gaban tattalin arzikin duniya. A cikin wata sanarwa da ta fitar, WTO ta yi hasashen cewa harajin Amurka da ya hada da wanda aka gabatar a farkon wannan shekara zai iya rage cinikin hajoji a duniya da kashi 1 cikin 100 a shekarar 2025, wanda zai kaucewa hasashen da ta yi a baya na fadada cinikayya. Rahoton ciniki na duniya na WTO, wanda aka fitar a watan Oktoban bara, ya yi hasashen cinikin kayayyaki a duniya zai...
Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana damuwa kan sabon harajin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya saka kan kayayyakin da ke shiga da su ƙasar daga ƙasashen duniya. Wannan haraji ya haɗa har da kashi 14 cikin 100 na kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga Najeriya. Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu A cewar sanarwar da WTO ta fitar a ranar Alhamis, hukumar na nazari da bibiyar matakin domin fahimtar yadda zai shafi cinikayya da kuma ci gaban tattalin arziƙin duniya. Okonjo-Iweala, ta ce wasu ƙasashe mambobin WTO sun nuna damuwa kan wannan lamari, inda suka buƙaci ɗaukar matakan rage...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Wasu da ake zargin Boko Haram ne sun kai hari sansanin horas da ‘yan sanda na PMFTC da ke Limankara, a Gwoza, inda suka kashe Sufeton ’yan sanda guda ɗaya. Sun kai harin da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, yayin da jami’an tsaro suka fita sintiri a ƙafa. Kakakin APC na Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Sufeto Andrawus Musa daga rundunar 6PMF da ke Maiduguri ya samu rauni a harin, inda maharan suka ƙwace bindigarsa ƙirar AK-47. An kai shi asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), amma rai ya yi halinsa. Rundunar dai na gudanar da bincike kan hari, tare da ƙoƙarin...
Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun hakkoki da muradun kasashe mambobin WTO, kuma ya matukar dagula ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa. Bugu da kari, hukumar harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka,...
Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa, inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki kuma jajirtacce. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda Oladunjoye ke yi wa aiki a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce rasuwarsa babban rashi ne. Ya ce Oladunjoye mutum ne mai kishin jam’iyya, jajirtacce, kuma ya taka rawar gani...
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari’arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu. ’Yan sanda ku yi amfani da iko cikin adalci — CP Wakili An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da zai tattauna da manema labarai...

Kasar Sin Za Ta Kara Sanya Harajin Fito Na Kaso 34% Kan Dukkan Kayayyakin Da Take Shigowa Daga Amurka
Kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, ta shigar da kara a gaban kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kan matakin da Amurka ta dauka na kakaba harajin kwastam kan abokan cinikayyarta. A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta ce, harajin kwastam da Amurka ta kakaba, ya matukar take halaltattun hakkoki da muradun kasashe mambobin WTO, kuma ya matukar dagula ka’idojin tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban da kuma tsarin tattalin arziki da cinikayyar kasa da kasa. Bugu da kari, hukumar harajin kwastam ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, kasar Sin za ta kara sanya harajin fito na kaso 34% kan dukkan kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka,...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi Fard; Duniyar musulmi tana fuskantar jarabawa mai girma da ita ce kare al’ummar Falasdinu, da takawa masu girman kai na duniya birki,haka nan ‘yan Sahayoniya ‘yan daba. Limamin na birnin Tehran ya jaddada muhimmacin fuskantar ‘yan sahayoniya ‘yan daba a cikin wannan yankin na yammacin Asiya. Limamin ya tabo zagayowar ranar kafa tsrin jamhuriyar musulunci na Iran da kaso 98% na al’ummar kasar su ka kada kuri’ar amincewa da shi a 1979, yana mai jaddada cewa an kafa tsarin jamhuriya a Iran ne bisa koyarwa ta musulunci.
Ta ce, “Abin da nake gani shi ne, INEC na taimaka wa masu shigar da kara kan yadda za su kammala ayyukansu na haram. “Wannan shi ne karon farko da aka gabatar da koken, ba su da adireshi, lambobin waya, duk da hana amma INEC ta shiryar da su yadda za su gabatar da bayanan da za su kammala kokensu. “Masu shigar da kara, ‘ya’yan jam’iyyar APC a yanzu suka mika takarda mai dauke da adireshin da babu shi domin ganin an yi min kiranye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP). Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba. Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52 Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safarar su zuwa jihohin Kudu maso Gabas. Ta ce, sun...
Matakan harajin fito na Amurka na haifar da koma-bayan tsarin cinikayyar duniya. Game da wannan batu, kafar CGTN ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta gudanar da wani binciken jin ra’ayin al’umma ga masu amfani da intanet na sassan kasa da kasa, inda suka yi tir da irin wannan abun da Amurka ta yi, al’amarin da a cewarsu, ka iya janyo ramuwar gayya daga kasashe daban-daban, har ma zai iya ta’azzara yakin harajin fito a duniya, da kawo babbar illa ga tattalin arzikin duniya. Kashi 82.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyinsu sun nuna cewa, yayin da ake fuskantar rashin daidaiton ci gaba da karfin tattalin arziki tsakanin kasa da kasa, neman cike gibin cinikayya da...
An kashe wani sufeton ɗan sanda a yayin wani kwanton ɓauna da wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a kwalejin horar da rundunar ’yan sanda (PMFTC) Camp Limankara, Gwoza a Borno. Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa majiyar Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 0600 a ranar 3 ga Afrilu, 2025, yayin da tawagar jami’an tsaro da suka haɗa da na makarantar horas da ’yan sanda ta Mopol Gwoza da wasu sassan rundunar ’yan sanda ke sintiri a ƙafa. Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi APC ta ƙaryata jita-jitar sauya Shettima kafin zaɓen 2027 Sufeta Andrawus Musa da ke aiki a rundunar 6PMF a Maiduguri ya samu munanan raunuka...
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da hukumar ta yanke a kan JMI na son zuciya ne kuma saboda siyasar JMI a duniya ne. Bahraini ya kara da cewa, wannan hukuncin ya taba mutucin hukumar ta yin adalci ga wasu kasashen a duniya. Bahraini ya kara dan cewa, abin mamakoi shigha ba’a taba jin wannan hukumar ta yankewa HKI irin wannan hukuncin ba, duk tare da cewa duk duniya tana ganin yadda...
Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen duniya na ci gaba da mayar da martini tare da shan alwashin ramuwar gayya game da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya lafta musu kankan kayayyakin da ake shigowa da su kasar. Gwamnatoci da kamfanoni da dama sun sanar da matakan gaggawa na samar da matakan dakile matakin da Amurkan ta dauka kansu. A ranar Laraba ne, ya sanya harajin kan duk kayayyakin da ake shigowa da su Amurka da kuma karin haraji kan wasu manyan abokan kasuwancin kasar. Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kira ga kamfanonin Turai da su dakatar da shirin zuba jari a Amurka. “Ina ganin abin da ke da muhimmanci, shi ne a dakatar da saka hannun jarin da za a cikin ‘yan...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da aka samar ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da Bankin Raya Musulunci (IsDB) na Saudiyya domin kafa ingantattun abubuwan more rayuwa ga masu zuba jari da manoma a fannin sarrafa nama da madara. Dakta Isiaka, wanda ya jaddada muhimmancin wannan aiki, ya bayyana cewa wannan ne karon farko da wani gwamna mai ci ke jagorantar kwamitin da ke kula da irin wannan babban shiri....
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Rahoton na cewa gobarar ta shafi wani sashe na sashen ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa na jami’ar. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara amma abin ya ci tura domin an kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ta wayar salula zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu. “Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce...
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka. “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin fasahohin haƙar ma’adinai don tabbatar da gudanar da ayyuka masu inganci. “Lokacin da ya je masana’antar, Gwamna Lawal ya zagaya wurare da dama, inda ya fara tun daga magudanar ruwa da zuwa duka sassan injina da kayan aiki. “Gwamna Lawal ya kuma ziyarci wurare daban-daban a cikin masana’antar, ciki har da gidan wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga ɗaukacin kamfanin,...
An shiga firgici da safiyar Alhamis ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata. Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin ruwan. Wutar ta bazu cikin masaukin fasinjoji da sauri ta kama wasu fasinjojin da ke ciki. Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye “Akwai wani babban abin fashewa daga ɓangaren injin jirgin wanda hakan ya haifar da gobara wadda ta laƙume jirgin. Majiyar ta ƙara da cewa, “har yanzu ba a san...
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar wa ɗalibai da ma’aikata hanyar sufuri mafi aminci, mafi dacewa, da sauƙaƙe ƙalubalen da ke tattare da zirga zirga tsakanin sassan jami’ar. Shugaban jami’ar wanda ya samu rakiyar magatakarda Haruna Aliyu da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Haruna Musa da shugaban dakin karatu na jami’ar Dr. Kabiru Dahiru Abbas da shugaban hulda da jama’a na jami’ar Lamara Garba da Farfesa Yakubu Magaji Azare, Shugaban jami’ar ya...
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida. “Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da...
Daga ƙarshe, ya buƙaci sojojin da su ƙara ƙwazo domin tabbatar da cikakken tsaro da zaman lafiya a yankin Arewa maso Yamma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare da sauran abokan hulda. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su. Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba. Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Rikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba. Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar. Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata, wanda ya wanke gadar wucin gadi da mutanen yankin suka gina a matsayin madadi. Wakilin LEADERSHIP a wurin gadar da sanyin safiyar Larabar nan, ya gano cewa, hanyar wucin gadi da mazauna kauyen suka gina, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya wanke ta, lamarin da ya sa masu ababen hawa da matafiya suka makale a gaɓar...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban tattalin arziki a duniya. Don haka, ana kyautata tsammanin cewa, wannan sabon tsarin harajin zai sake fasalin yanayin kasuwanci a duniya, ganin cewa, wasu masana’antu za su fuskanci tsadar kayayyaki da kuma durkushewar hanyoyin samar da kayayyaki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau Laraba zuwa Paris, na ƙasar Faransa, domin ziyarar aiki ta makonni biyu. A cewar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu zai yi bitar mulkinsa na rabin wa’adi, inda zai tantance nasarorin da ya cimma da kuma irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa. Haaland Zai Ziyarci Likita Saboda Raunin Da Ya Samu A Ƙafa Sanarwar ta ce wannan lokaci zai ba shi damar tsara hanyoyin da za su inganta ci gaban ƙasa yayin da yake shirin cika shekaru biyu a kan mulki. Duk da kasancewarsa a waje, Onanuga ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati tare da tuntuɓar manyan jami’ansa har zuwa lokacin...
A wannan Larabar Shugaban Kasa Bola Tinubu zai tafi ziyarar aiki ta makonni biyu a ƙasar Faransa. Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce a yayin ziyarar shugaban ƙasar zai yi bitar ƙwazo da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...

Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya. A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin. Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko’ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta...
Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro. Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu. Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara Wang, ya yi...
“Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa. “Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi. Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu. Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara cafke wadande ake zargi da aikata wannan aika-aika. “An riga an kama kimanin mutane 14 da ake zargi, za mu ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an gurfanar da su a gaban kotu an yi wadanda aka kashe adalci”. In ji Okpebolo Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wasu gidajen na ‘yan kasuwa ma sun bi sahu wajen ƙara farashi, wanda hakan ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziƙi. A halin yanzu, hauhawar farashin man fetur na nufin za a ƙara kudin sufuri da kuma farashin kayan masarufi, wanda zai ƙara jefa al’umma cikin kunci. Masana harkar man fetur sun yi gargaɗin cewa, idan ba a magance rikicin da wuri ba, farashin mai na iya haura Naira 1,000 a wasu yankuna. Gwamnatin Tarayya ta taɓa bayar da umarni cewa a sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da Naira domin daidaita farashin mai, amma yarjejeniyar ta ƙare a watan Maris 2025. A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya. A yayin da...
Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita. Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane...
Jami’an tsaro sun bazama akan titunan manyan garuruwan kasar Zimbabwe domin dakile zanga-zangar da ake shirin yi domin yin kira ga shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya yi murabus. Tsofaffon sojoji da mayakan da su ka samarwa kasar ‘yanci ne dai suka yi kiran a yi zanga-zangar, saboda kin amincewa da shirin shugaban kasar na tsawaita wa’adin mulkinsa. A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai jam’iyyar ZANU-Party, mai mulki a kasar ta sanar da cewa tana son Mnangagwa ya ci gaba da rike mukamin shugaban kasar har zuwa 2023. Mnangagwa dai ya hau karagar mulkin kasar ta Zimbabwe ne tun a 2017,bayan sauke Robert Mugabe daga kan karagar mulki cikin ruwan sanyi. Shugaban mayakan nemawa kasar ‘yanci Blessed Geza...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa iyalai da yan uwan mafarautan nan guda 16 da aka kashe a Jihar Edo. Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya. Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya “Wannan ziyara ba kawai ta jaje da ta’aziyya ba ce, a’a ta nuna tabbacin ƙoƙarin samar da adalci. “Iyalan waɗannan mamata na buƙatar abin da ya...
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan. Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara. Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya. Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
Mai Martaba Idi Chiroma, Sarkin Gassol a Jihar Taraba, ya ce Musulmin da suka gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 2025 sun nuna tsayin daka wajen sadaukarwa ga addini. Chiroma ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake jawabi ga al’ummar Musulmi a wani bangare na bikin Sallar karama a karamar hukumar Gassol da ke jihar. Ya kuma ja hankalin al’ummarsa da su jure duk wani kalubalen da suka fuskanta yayin da suka jure mawuyacin hali na baya-bayan nan domin ibada. Chiroma ya bayyana cewa wadanda za su koma ga tsohon halin da suke ciki na iya zama ba tare da albarkar da ke tattare da azumin watan Ramadan ba. ...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi. Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali. An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare. A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai. Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe...
Sanata Abdul’aziz Yari, mai wakiltar Zamfara ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana shirin tallafa wa marayu 20,000 a faɗin Jihar Zamfara. Yayin da yake magana bayan cin abincin Sallah tare da marayu 500 a gidansa da ke Talata Mafara, Sanata Yari ya ce an shafe watanni tara ana tantance marayun daga ƙananan hukumomin jihar domin tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne za su amfana da shirin. Abba Ya Nemi Gwamnatin Edo Ta Biya Diyyar Matafiyan Da Aka Kashe A Uromi Nijar Ta Fice Daga Rundunar Tsaro Ta Haɗin Kai MNJTF Ya bayyana cewa shirin tallafin wanda zai fara aiki kafin Idin Babbar Sallah, inda za a ware duk abin da marayun ke buƙata don kyautata rayuwarsu. “Mun shirya...
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya. Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar. Da yake...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari. Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka “Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi. Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na Switzerland, wanda kasarsa ke wakiltar muradun Washington a Tehran, yau Litinin. Kameli ya mika gargadin na Iran a hukumance ga wakilin kasar Switzerland dangane da duk wani aiki na barna tare da bayyana aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na mayar da kakkausan martani cikin tsauri kan duk wata barazana. Jami’in diflomasiyyar na Iran yayi tir da kalaman tunzura tashe-tashen hankula wandanda kuma suka sabawa dokokin...
A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027. An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi. An tuhumi Le Pen tare da wasu manyan yan jam’iyyar tata guda 20 da daukar masu taimaka musu aiki wadanda suka yi wa jam’iyyarta aiki maimakon Majalisar Turai wadda ita ce ke biyan ma’aikatan albashi. Ms Le Pen, mai shekaru 56, ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2027 ba, inda a yanzu ake ganin ita...
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike. A yayin ziyarar, Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa —Gwamnatin Kano Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar...
“Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban. A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda ’yan banga suka tare su. Daga nan ne, shugaban ‘yan bangar ya fara yi wa direban tambayoyi game da kayan da ya dauko da kuma fasinjojin sa. Duk da gabatar da takardar sahalewar hanya amma shugaban ‘yan bangar ya nuna zargi kan mafarautan, musamman saboda makamansu da karnukan da su ke tare da su a cikin motar. Saboda haka, “Shugaban ‘yan bangar bai amince...
Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah. A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi dakon wadanda ke haye-hayen dawakan a gefen titi su ma suna yi wa Sarki gaisuwar ban girma. Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana Sarki yakan jagoranci tawagar masarautar ta Zazzau inda zai ratsa ta cikin garin Zazzau sannan ya shiga unguwar Sabon Gari inda zai ziyarci...
Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan daga baya ya sauka don ya sake dawowa da hanyar zabensa ya fara yakin neman zabe a jiya, inda yake kira ga mutanen kasar su zabe shi saboda kyautatuwar kasar Gabon. A cikin watan Augustan shekara ta 2023 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya gaji babansa Umar Bongo bayan rasuwarsa ba tare da zabe ba. A halin yanzu dai yan takara...
Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da kuma Omman an tashi da ci 8-1. Wannan nasarar dai ta tabbatar wa kasar Iran fifiko a wannan wasar har saw hudu a jere. Kuma ba’a taba samun nasara a kan ta gaba daya a dukkan wasannin da ta yi a duk tsawon gasar ba. Mai horar da yan wasan Iran a wannan gasar Ali Nadiri ya bayyanawa IP kan cewa nasarar da JMI ta...
Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan. A cewar ’yan sanda yaron dan shekara 4 ya yi kururuwa, inda ya kira ’yan sanda bayan mahaifiyarsa ta shanye masa ice cream dinsa. Sarkin Gombe ya nemi manoma da makiyaya su zauna lafiya Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano Al’amarin ya faru ne a cikin a garin Mount Pleasant, Wisconsin — mai nisan kilomita bakwai, yamma da Racine — lokacin da yaro dan shekara 4 ya...
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa shugabanni jagorancin don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru. Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi. Dangane da...
Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin Naira. Gwarzon gasar Alƙur’ani ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga a Katsina Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi Wannan ya sa gidajen mai suka ƙara farashi daga Naira 860 zuwa Naira 930 a Legas, da Naira 940 a yankin Kudu maso Yamma da Kwara, sannan Naira 960 a jihohin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas. Rahotanni sun nuna cewa farashin...