2025-02-22@22:39:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 238
«Majalisar Dattawa»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri da tsohon Shugaban Ƙasa kuma tsohon uban gidansa, Olusegun Obasanjo. Obasanjo da Atiku sun yi ganawar ne a yayin ziyarar da tawagar Atiku ta kai gidan Obasanjo da ke mahaifarsa a Jihar Ogun. A ranar Litinin ne Atiku tare da rakiyarsa ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kuros Riba, Liyel Imoke, da tsohon Gwamnan Sakkwato Sanata Aminu Waziri Tambuwal da kuma Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya. Isar tawagar Atiku da tawagarsa gidan Obasanjo ke da wuya shugabannin biyu suka sanya labule domin ganawar sirri.
Gwamnatin tarayya ta yabawa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa kammala aikin kaso 97 na ayyukan tituna da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Auyo yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da gwamnati da al’umma a jihar Jigawa. Badaru wanda ya nuna gamsuwarsa matuka, ya ce gwamnatin jihar ta kammala ayyukan tituna guda 23 cikin 26 da ta gada. Ya kara da cewa sauran ayyukan tituna guda uku sun kusa kammaluwa domin amfanin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati mai ci za ta kawo karin ayyukan raya kasa, don haka akwai...
Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi da kasashen Larabawa, ciki har da Falasdinu da ta bukaci gudanar da taron, tare da hadin gwiwar Bahrain. A wani labarin kuma, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya. A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara...
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
Bugu da kari, jami’in ya ce Sin na taimakawa Masar wajen kafa masana’antar samar da ababen hawa a cikin gida, ta hanyar kafa irin wadannan masana’atu a kasar. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gana da tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a birnin Legas. Kwankwaso ya bayyana a shafinsa na X cewa sun tattauna kan batutuwan da suka shafi siyasa da makomar dimokuradiyya a Najeriya. Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari Ɗan sanda ya rataye kansa har lahira a Neja Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun adawa ke kira ga haɗin kai domin fuskantar zaɓen 2027. A watan Oktoban 2024, jam’iyyar APC a Jihar Osun ya dakatar da Aregbesola bisa zargin cin amanar jam’iyya da sukar shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon gwamnan...
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari An tsinci gawarsa rataye a cikin dakinsa. Majiyoyi sun ce mahaifinsa, Malam Usman Bawa ne, ya fara gano abin da ya faru sannan ya kai rahoton lamarin zuwa ofishin ’yan sanda da ke Kontagora. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce: “A ranar 8...
Wani babban jami’in Ƴansanda, ASP Shafi’u Bawa, na rundunar 61 Police Mobile Force (PMF), an tsinci gawarsa a dakinsa a garin Kontagora, Jihar Neja, a ranar Asabar, bayan da ake zargin ya kashe kansa. Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano gawar ASP Bawa rataye a saman silin ɗin ɗakinsa. Mahaifinsa, Malam Usman Bawa, ne ya fara gano lamarin kafin ya kai rahoto ofishin ‘yansanda na Kontagora. Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta Abin Fashewa Ya Hallaka Mutum Guda, Ya Jikkata 6 A Neja Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa: “A ranar 8/2/2025 da misalin ƙarfe 2 na rana, an samu rahoton cewa ASP Shafi’u Bawa...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar da kiran taron kasahen larabawa a karshen wannan watan na Febrairu da ake ciki domin tattauna batun tilasta wa Falasdinawa yin hijira daga Gaza a karkashin shirin Amurka da Isra’ila. Da safiyar yau Lahadi ne dai ma’aikatar harkokin wajen ta Masar ta bayyana cewa za ta karbi bakuncin taron kungiyar kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan nan na Febrairu,domin tattauna sabbin batutuwan da su ka taso dangane da Falasdinu. Har ila yau sanarwar ta ce, Masar din ta yi wannan gayyatar ne bayan tattaunawa da kasar Bahrain wacce a halin yanzu take rike da shugabancin kungiyar kasashen Larabawan, haka nan kuma tuntubar babbar shalkwatar kungiyar. Bugu da kari Masar din ta sanar...
Kungiyar kasashen musulmi ( OIC) ta fitar da bayani da aciki ta yi tir da maganganun shugaban kasar Amurka Donald Trump akan fitar da mutanen Gaza. Kungiyar ta OIC ta bayyana cewa; maganganun na shugaban kasar Amurka suna a matsayin goyon bayan ‘yan mamaya, masu mulkin mallaka domin kwace kasar Falasdinawa da hakan yake a matsayin take dokokin kasa da kasa da kudurorin MDD da su ka hada da kwamitin tsaro na wannan Majalisar mai lamba;2334. Haka nan kuma bayanin na kungiyar kasashen musulmin ya ce, abinda Trump ya furta zai iya hana zaman lafiya wanzuwa a cikin wannan yankin. Wani sashe na kungiyar kasashen musulmin ya bayyana kin amincewa da duk wani yunkuri na sauya tsarin iyaka da mutane...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu. Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen. Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu. Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na...
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
Iran ta bukaci taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, game da shirin shugaba Donald Trump na Amurka na kwace Gaza da kuma korar al’ummar Zirin. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa haramtaccen shirin” na shugaban kasar Amurka kan Gaza ya gamu da kakkausan ra’ayi daga kasashe daban-daban, inda ya yi kira da a gudanar da taron gaggawa na ministocin kungiyar ta OIC domin tattaunawa da yanke shawara kan wannan batu. A wata tattaunawa daban daban ta wayar tarho da wasu takwarorinsa a yammacin jiya Asabar ministan harkokin wajen na Iran Sayyid Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Masar Badr Abdel-Aty, Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata a fara ranar Litinin, ke ja da baya ba kamar yadda aka fara ba inji shi. Da yake zargin Isra’ila da “jinkiri” wajen aiwatar da kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta na makonni shida, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, Bassem Naim ya yi gargadin cewa wannan lamarin ya jefa yarjejeniyar cikin hadari kuma zata iya haifar da rugujewarta....
Saudiyya Ta Yi Watsi Da Shirin Fitar Da Falasdinawa Daga Gaza
“Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu. Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a – hanyar Tsangamawa. Hanyar Tsangamawa da ke Babban Rafi, Karamar Hukumar Danja, Jihar Katsina, ta haddasa mutuwar mata masu juna biyu da jariransu, musamman a lokacin damina. Duk da yawan koke da rokon gwamnati, har yanzu ba a dauki matakin gyara hanyar ba. A wata hira da suka yi da Radio Nigeria, wasu daga cikin matan yankin sun bayyana cewa mata masu...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Sayyid Aliyul Khaminae yana cewa tsagaita wuta da aka samu bayan wannan lokaci mai tsawo na fafatawa yayi dai-dai. Tawagar shuraa ta Hamas din dai sun hada da shugaban riko na kungiyar Khalil Al-Hayya, shugaban majalisar shoora ta kungiyar Muhammad Ismail Darwish da sauransu. Jagoran ya kara da cewa nasarar da mutanen Gaza suka samu a kan Amurka da kawayenta misdaki nan a...

MDD Ta Ce Masu Fama Da Cutar HIV/AIDS Miliyon 6 Ne Zasu Mutu Saboda Janyewar Amurka Daga Tallafawa Hukumar UNAIDS
Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a ranarsa ta farko na kama aiki a matsayin shugaban kasan Amurka, ya dakatar da dukkan tallafin da Amurka take bayarwa a duniya na tsawon kwanaki 90. Labarin ya nakalto shugaban shirin samar da magunguna HIV/AIDS Christine Stegling tana cewa, duk tare da cewa Amurka ta ci gaba da tallafawa HIV/AIDS na wucin gadi, amma suna ganin cewa da wuya hakan ya ci gaba don tun...
Firay Ministan HKI Banyamin Natanyahu ya bawa kasar Saudiya Shawara samarwa Falasdinawa kasa daga cikin hamada mai girma da take da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka wa wata tashar talabijin ta HH a safiyar yau Asabar. Amma a maida martani ga Natanyahu, dan majalisar dokokin kasar Burtania a jam’iyyar Larbor Afzal Khan yace, wannan shawarar ta Natanyahu tabbaci ne na laifin fitta mutane daga kasarsu da karfi, don kawai ya na son a kwace zirin gaza daga Falasdinawa. Falasdinawa basa bukatan karin kasa suna son yenci ne a kasarsu. Inji dan majalisar dokoki Kim Johnson na jam’iyyar Lebour.. Kafin haka dai sarki Saman bin Abbdul azizi na kasar Saudiya yace ba...
Dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan kasar Jordan da kasar Iraki domin yin Allah wadai da shirin shugaban Amurka Donald Trump na korar Falasdinawa daga yankin Gaza. Masu zanga-zanga a Amman babban birnin kasar Jordan, da kuma wasu garuruwan kasar Larabawa, sun yi zanga-zangar nuna adawa da shirin na tilastawa mazauna zirin Gaza kaura. A Jodan an gabatar da wani sabon daftarin doka a majalisar dokokin kasar da zai haramta tilastawa Falasdinawa komawa Jordan. An kuma gudanar da zanga-zangar adawa da shirin a Bagadaza babban birnin kasar Iraki, baya ga Masar inda aka yi irin wannan zanga-zangar. Yayin ganawarsa da firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Alhamis, Trump ya bayyana shirinsa na kwace yankin Gaza na Falasdinu...
Yau Asabar shugabannin kasashen raya tattalin arzikin kasashen Gabashi da Kudancin Afrika EAC da SADC za su gana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya domin tattauna rikicin gabashin DRC. Shugaban kasar Kenya, William Ruto, dake jagorantar kungiyar EAC, ya sanar da halartar takwarorinsa na Congo da Rwanda. Tun da farko a ranar Juma’a, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana domin samun nasarar wannan tattaunawar, inda fadar shugaban kasar ta Kwango ta gabatar da bukatunta da suka hada da : tsagaita bude wuta nan take, janyewar dakarun M23 da na Rwanda daga yankin Congo, da sake bude filin jirgin saman Goma, da mayar da birnin ga hannun halastattun hukumomi. A ranar Juma’a, a wani taro a Malabo, Kungiyar...
Kazalka, matsalar ta sanya wasu iyalai da dalibai da dama a kasar yin kokarin jurewa matsin rayuwar da suke ci gaba da fuskanta, wanda hakan yak e kuma kara zamowa, babbar barazana ga rayuwarsu. Bisa fashin baki da rahoton ya yi ya nuna cewa, a shiyoyi shida na kasar, banbancin hauhawan farashin na kayan abincin, ya sha ban ban, inda a yakin Kudu Maso Yamma, lamarin na hauhawan farashin kayan abincin, ya fi yin kamari.
Shirin Inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya raba katinan cire kudi na ATM a kananan hukumomi 10 daga cikin 27 domin al’umma su sami tallafin naira dubu saba’in da biyar biyar na gwamnatin Tarayya. Shugaban shirin na jihar, Malam Mustapha Umar Babura ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Yayi bayanin cewar, ana rabon katinan karbar kudin ne ga wadanda za su sami tallafin inganta rayuwa na naira dubu sabain da biyar. A cewarsa, duk da korafe korafen da ake samu wajen rabon katinan, aikin na cigaba da gudana yadda ya kamata. Mustapha Umar Babura ya ce ana ta kokarin warware duk matsalolin da ma’aikatan suke cin karo da su wajen rabon katinan ga al’umma....
MA’aikatar harkokin wajen kasar Venezue ta sanar da cewa; Abinda Amurkan ta yi sata ce a tsakar ranar Allah da ta yi wa dukiyar al’ummar Venezueal, tare da cewa za ta dauki dukkanin matakan da su ka dace domin sake dawo da jirgin saman nata.” Sanarwar ta kuma zargin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio da cewa shi ne ya bayar da umarnin kwace jirgin na Venezuela. Haka nan kuma ta kara da cewa; Kiyayyar da Robio yake yi wa kasar Venezuela ce ta sa shi kwace jirgin, da hakan ya mayar da shi zama barawon jiragen,alhali a baya, ba shi da wani aiki sai cusa kiyayya da gaba. Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Venezuela ta bukaci ganin an dawo...
Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa. “Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe. “Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi. Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci. Taron na yau ya zo daidai da zagayowar kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma taron tunawa da mubaya’a mai dimbin tarihi ga Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 1979. Don haka a safiyar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran ya sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai da sabbin takunkuman da Amurka ta kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa sun sabawa ka’idojin dokokin kasa da kasa. Baqa’i ya yi nuni da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na kakaba takunkumi kan wasu kungiyoyi da cibiyoyi masu gudanar da ayyuka na dabi’a da al’adu na kasa Iran bisa zarginsu da hannu wajen sayar da danyen man fetur na Iran, a matsayin mummunan matakin da bai dace ba, kuma ya jaddada cewa hakan ya sabawa ka’idojin kasa da kasa. Ya kara da...
Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi birnin kawanya daga bangarori hudu. A nata bangaren, Ma’aikatar yada labaran Sudan ta zargi bangarorin waje da jagorantar gudanar da fadace-fadacen da ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa ke yi don samun damar cin gajiyar albarkatun kasar, idan ‘yan tawaye suka yi nasara. Rayuwa ta fara inganta a birnin Omdurman kuma kasuwanni sun fara farfadowa, inda jama’a suke komawa ci gaba da harkokinsu na yau...
A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
Ministan yaki na HKI Israel Kant ya umurci jami’an gwamnatin kasar su fidda wani tsari wanda zai bawa falasdinawa damar ficewa daga yankin Gaza a radin kansu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan ya na haka bi sa umurnin da shugaba Trump na Amurka ya bayar na cewa ‘zai kwace Gaza’. Yace Palasdinawa a Gaza su na so ko basa so za su bar Gaza, a bisa radin kansu ko kuma da karfi. Shugaban kasar Amurka yace ya dauki nauyin fidda Falasdinawa daga gaza, don wurin ya zama na yahudawan sahyoniyya kadai. Wasu masana suna ganin mai yuwa wannan shirin zai kawo karshen zaman lafiyan da aka samu, bayan yaki na watanni 15 da suka gabata....
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar. Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809. A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana. Don...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya tattalin arziki, da kuma kyakkyawar makomar bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin. Saboda haka, kasar Sin tana lale marhabin da baki daga daukacin fadin duniya su zo su ga kyawawan al’adun Sinawa tare da more wa abin. Kididdiga ta nuna cewa, ya zuwa ran 5 ga watan Fabrairu, adadin kudin da aka samu na tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun Bikin Bazarar, ya zarce Yuan...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa : Gabadayen Falastinu tun daga kogi har zuwa teku ta al’ummar Falasdinawa ce. Jagoran ya jaddada goyon bayan Iran ne ga gwagwarmayar Falasdinawa kan kasarsu mai dimbin tarihi, tun daga kogin Jordan zuwa tekun Bahar Rum, kamar shafin offishin jagoran ya sanar. Kallaman Jagoran na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da wata shawara mai cike da cece-kuce na kaurar da Falasdinawa daga zirin Gaza da kuma sanya Amurka ta karbe yankin da yaki ya lalata. Ta hanyar yada wannan sako a cikin harsuna da dama, Iran ta nanata kudurinta na tabbatar da Falasdinu. Shugaba Trump na Amurka ya tsaya...
Ministan tsaron Isra’ila, Isra’ila Katz ya umarci sojojin gwamnatin kasar da su shirya wani shiri na “ficewar” Falasdinawa daga zirin Gaza. Umarnin Katz ya biyo bayan shawarar Shugaba Donald Trump na tilastawa Falasdinawa Gaza barin zirin da kuma sanya Amurka ta mamaye yankin da yaki ya lalata. “Na umurci IDF da su shirya wani shiri don ba da damar ficewa na radin kan mazauna Gaza,” in ji kakakin na Isra’ila a cikin wata sanarwa. Katz ya bayyana cewa ya fadawa sojojin Isra’ila da su yi shirin da “zai ba da damar duk wani mazaunin Gaza da ke son barin yankin zuwa, ga duk wata kasa da yake son karba.” Ministan tsaron Isra’ila ya kara da cewa “Tsarin zai hada da...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa da ta wakilai. A cikin wasikar da aka karanta yayin zaman majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce an sami karin kudin ne sakamakon karin kudaden shigar da hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta samu na Naira tiriliyan 1.4, yayin da hukumar hana fasakwabri ta kasa ta tara Naira tiriliyan 1.2, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka tara. A don...
Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan shekarar ta 2025, inda ta buga wasanni da dama ba tare da tayi rashin nasara ba tun bayan shigowar sabuwar shekara, kuma daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da ta samu ya zuwa yanzu a bana shi ne wanda ta doke Valencia da ci 7-1 kwanaki 10 da suka gabata. Har Yanzu Arsenal Ta Na Iya Lashe Gasar Firimiya Ta Bana – Alan Shearer Ba...
Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamamd Riza Arif ya bayyana cewa, A halin yanzu ba ya cikin shirin gwamnatin Iran yin ganawa a tsakanin shugaban kasa Mas’ud Fizishkiyan da takwaransa na Amurka Donald Trump. A jiya Laraba ne mataimakin shugaban kasar Iran Riza Arif da ya yi Magana da ‘yan jarida inda yake mayar da martani akan fatan shugaban kasar Amurka Donald Trump na ganawa da shugaba Mas’ud Fizishkiyan na Iran, yana mai kara da cewa hakan ba ya cikin shirin gwamnati a wannan lokacin. Mataimakin shugaban kasar ta Iran ya kuma ce, ya kamata Trump ya san cewa, bisa fatawa ta addini da jagoran juyin musulunci ya fitar, Iran ba za ta mallaki makamin Nukiliya ba. Riza Arif ce Iran...
Hukumar Kula da Magunguna ta Najeriya (PCN) ofishin Kano ta kai ziyarar gani da ido ga hukumar samar da magunguna ta jihar Kano (DMCSA). Wannan ziyarar alama ce ta farkon tsarin ba da izini ga DMCSA don zama cibiyar rarraba magunguna ta mega da cibiyar bada horo. Jami’ar Jihar Kano mai kula da ofishin PCN Kano Pharmacist Hasiya Abubakar Ladan ce ta jagoranci tawagar da suka kai ziyarar. Wannan ziyarar wani mafari ne na tantancewa da wata tawagar kwararru daga hedikwatar PCN ta kasa da ke Abuja. Ta bayyana cewa ziyarar na da nufin tantance yadda DMCSA ke bin ka’idoji, don ba da Takaddar Rijistar wuraren sayarda magunguna. Pharmacist Ladan ta yabawa shugabannin DMCSA bisa...
Mataimakin shugaban kasar Iran kan al-amuran na Musamman Muhammad Javad Zareef ya bayyana cewa tattaunawa kadai da Amurka, ba zai warware matsalolin Iran ba. Kamfanin dillancin labarum IP na kasar Iran ya nakalto Zareef ya na fadar haka a taron majalisar ministocin da aka gudanar a jiya Laraba a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iram ya kuma nakalto mataimakin shugaban kasar yana cewa, maslahar daga Amurka Itace ta dagewa takunkuman tattalin arziki. Wasu masana dadama, sun bayyana cewa idan trump ya na son tattaunawa da Iran to da dole ne ta farko Amurka ta dorawa iran sannan a yi maganar tattaunawa. A jiya ne shugaban Trump ya bayyana anniyarsa ta shiga tattaunawa da kasar Iran yana kuma...
Shugabannan Palasdinawa daga cikin har da kungiyar Hamas da Jahadul Islami duk sun ki amincewa da shirin trump na sake kwace Gaza, kafin haka kuma shugaban ya ce dole Falasdinawa su daga yankin kafin ya kwace shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shuwagabannin Palasdinawan suna allawadai da shugaban, sun kuma kara da cewa abinda HKI bata samu da yakin wattnin 15 ba, shugaba Trump ya na ya ba su da sauki da kuma wayon da za’a yiwa yaro. A ranar talata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa zai kwace Gaza a hannun Palasdinawa sannan ya sake gina shi. Falasdinawa kimani 61,700 suka rasa rayukansu a yayin da fiye da 100,000 ji rauni a...

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Amincewa Da Tsarin Bada Tallafi A Mazabu
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta yabawa Gwamna Umar Namadi bisa amincewarsa ga manufar majalisar, ta bullo da tsarin bada tallafin sana’oi na mazabu ba tare da jinkiri ba. Shugaban Majalisar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya bayyana haka a lokacin da yake kaddamar da rabon tallafi wanda wakilin mazabar Kanya a majalisar dokokin jihar,Alhaji Ibrahim Hashim Kanya, ya bai wa al’ummar garin Kanya dake karamar hukumar Babura. Yana mai cewar, majalisar ta bullo da tsarin bada tallafin domin mara baya ga Kudurorin Gwamna Umar Namadi guda goma sha biyu, ta fuskar bunkasa tattali da samar da ayyukan yi ga jama’a. A jawabinsa, wakilin mazabar Kanya Alhaji Ibrahim Hashim Kanya, ya ce mutane 1,350 ne za su amfana da tallafin...
Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025. Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan lokaci. Nijeriya Na Iya Fuskantar Ƙarancin Maniyyata A Hajjin Bana EFCC Ta Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar ₦144m A Gombe Farfesa Usman ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da ya gudana a manhajar ‘Zoom’ a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, 2025, tare da masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji. Shugaban Hukumar NAHCON ya yi kira ga Sakatarorin...

Mutanen Amurka Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Goyin Bayan Falasdinawa Bayan Tattaunawar Trump Da Natanyahu Dangane Da Gaza
Mutanen kasar Amurka sun fito zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da korar Falasdinawa daga Gaza ne, bayan taron da yan jaridu na Trump Da Natanyaho a birnin washintong a jiya Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu zanga-zangar su na rera taken cewa “gaza ba na sayarwa bane”. Maganganun Trump a baya-bayan nan, dangane da yankin Gaza dai, ya jawo cece-kuce da dama kan al-amiran a duniya, A birnin Washington dai mutane sun yi ta kawo batun kare hakkin ‘yan kasa’ da kuma tauya hakkin wata al-umma wacce ta yi shekarun fiye 75 tu na neman hakkinta na komawa kasarta, daga kasashen da suke rayuwa, rayuwa irin ta yan gudun hijira na lokaci mai tsawo. A lokacin...
Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da tsawaita wa’adin karɓar kuɗin aikin Hajjin bana. NAHCON ta ce daga yanzu zuwa 10 ga watan Fabrairu ƙofa a buɗe take ta ci gaba da karɓar kuɗin kujera ga maniyyatan da ke son sauke farali a bana. Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka Ana iya tuna cewa, da misalin ƙarfe goma sha biyun daren ranar Juma’a 31 ga watan Janairun 2025, ne wa’adin biyan kuɗin kujerun aikin hajjin bana ya cika. Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar NAHCON ta ƙasa, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce tsawaita wa’adin wata dama ce ga maniyyatan da ba...
A kwanakin baya Hausawa mazauna Jahar Imo suka yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri Fadar Gwamnatin Jihar Imo da ke yankin Kudu maso Gabas yankin da ake kira da Ibo. Hausawa mazauna Jihar Imo da ke Owerri babban birnin jahar a kwanan baya sun yi bikin cika shekara 153 da zuwa Owerri, Jahar Imo da zama domin gudanar da harkokin na kasuwanci. DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Sarki Sanusi ya ziyarci unguwar da mutane suka rasu a dalilin rusau Yawancin garurukan Asaba da Benin da Obudu a Jihar Kuros Riba su ne mazaunin Hausawa na farko a Jahar Kuros Riba sai kuma garin Alele a Jihar Ribas mai iyaka...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF. Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa. A cewarsa, gwamnatin jihar tana sane da muhimmancin da asusun ke da shi, musamman ga ma’aikatan da aka horas da su domin samun kwarewa a fanninsu. Dagaceri, ya tabbatar wa shugaban asusun cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da hadin kai ga sabon ofishin na ITF da aka kafa a yankin Jigawa. Tun da farko, Shugaban Asusun na Arewa maso...
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata. Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja Wasiƙar shugaban ta kare matakin da ya ɗauka na ƙin amincewa bisa la’akari da tanadin da sashe na 22 da ke cikin ƙudirin kafa jami’ar ya yi. Ya yi bayanin cewa sashen ya yi tanadin cewa filin da za a gina jami’ar zai kasance a ƙarƙashin ikon Gwamnatin...

Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa. Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.” A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai...
Ministocin harkokin wajen 5 na kasashen larabawa tare da hadin gwiwar jami’an Falasdinawa sun rubuta wa ministan harkokin wajen Amurka Marco Antonio Rubio wasiki da a ciki suke nuna kin amincewa da shirin korar Falasdinawa zuwa wajen Falasdinu. Kasashen da su ka rubuta wasikar sun kunshi Saudiyya, HDL, Katar, Masar da Jordan, sai kuma mai bai wa shugaban gwamnatin Falasdinu shawara Husain Sheikh, sun kuma mika wannan wasikar ne ga mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Amurka mai kula da yankin gabas mai nisa. A ranar 25 ga watan Janairu da ya shude, shugaban kasar Amurka ya gabatar da shawarar cewa kasashen Masar da Jordan su karbi bakuncin Falasdinawa daga Gaza. Tare da cewa Trump din ya ce zaman na...

Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Fara Tattaunawa, Marhala Ta Biyu Na Tsagaita Wuta A Gaza
Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta kammala ɗaukar tsohon ɗan wasan Real Madrid Marco Asensio daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. Asensio wanda ya bar Real Madrid a shekarar 2023 ya na ɗaya daga matasan ƴan wasa da tauraruwarsu ke haskawa a harkar ƙwallon ƙafa a yanzu. PSG Na Neman Dauko Lamine Yamal Daga Barcelona A Kan Yuro Miliyan 200 Wannan Ita Ce Shekarata Ta Karshe A PSG —Mbappe Aston Villa ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa cewa Asensio ya rattaɓa hannun komawa ƙungiyar a matsayin aro daga PSG har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. Asensio ne ɗan wasa na biyu da Villa ta ɗauka aro bayan Marcus...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
Mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata a sanadiyyar wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tireloli uku waɗanda suka yi karo da juna ’yar tazarar mitoci ƙalilan zuwa garin Agaie. Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar Ebola Wani mazaunin yankin, Baba Yakubu ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tirelolin da lamarin ya shafa ta ɗauko lodin dabbobi da suka haɗa da shanu da awaki Shi ma Darekta Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullah Baba Arah, ya...
Ƴansanda Sun Kashe Mutum Ɗaya Kan Zargin Garkuwa Da Mutane A Adamawa
Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren wurin shan shayi da taliya na zamani a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari. Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin. Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari. An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i. Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa,...

Wasu Hukumomi A MDD Sun Bada Sanarwan Cewa HKI Ta Fadada Yaki Kan Falasdinawa Daga Gaza Zuwa Dukkan Kasar Falasdinu
Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai rabi da rabi, a wasu wuraren ma dai sai dai kasusuwa. Ya zuwa yanzu dai an sami gawawwakin da sun kai 458 kamar kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu Dr. Khalil Dakran ya ambata. Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa tana kirdadon cewa za a iya samun gawawwakin da suke tsakanin 4000, zuwa 5000 a karkashin baraguzai a fadin Falasdinu.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a jiya Lahadi Fira minista Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin a rushe gidajen na Falasdinawa. Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa wannan shi ne hari irinsa na farko da aka rushe gidaje 100 a lokaci kadan. Masu bin diddigin abinda yake faruwa suna cewa, da alama HKI tana son shafe sansanin ‘yan hijirar na Jenin ne baki daya. Kungiyoyin Falasdinawa da su ka hada da Hamas sun yi kira da a takawa HKI akan wannan irin barna da take yi.
Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a ragar Manchester City bayan da ɗan wasan baya Nathan Ake ya tafka kuskure. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates Duk da ƙwallon da Haaland ya ci bai hana Arsenal raga raga da City a wasan mako na 24 na gasar Firimiyar ba, wannan sakamakon ya sanya magoya bayan ƙungiyar sa...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita. A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya yi tir da irin wadannan shawarwari a matsayin “abin dariya kuma maras amfani,” yana mai cewa, “Abin da mamayar Isra’ila ta kasa cimma da karfi, ba zai samu ta hanyar makircin siyasa ba.” Abu Zuhri ya kara da cewa, “Sanarwar da Amurka ta nanata na raba Falasdinawa da gidajensu da nufin sake gina yankin zirin Gaza na nuni da yadda kasar ke da hannu wajen aikata laifukan da suka shafi yanki.” Kana, ya yi gargadin cewa, “aikin kwashe mazauna Gaza” wani...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10. Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Aminiya ta ruwaito cewa, an bayar da lambobin yabon ne ga fitattun mutanen maza da maza a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Kano ranar Asabar da daddare. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce waɗanda suka samu lambobin yabon sun yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa kuma a dalilin haka an samu ci...
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Sudan sun ce rundunar kai daukin gaggawa mai fada da sojojin kasar Sudan ta kai wa garin “Tandalti” hari da jirgen sama marasa matuki jim kadan bayan ziyarar shugaba majalisar shugabancin kasar Janar Abdulfattah al-Sisi. Majiyar sojan kasar Sudan ta ce, sun yi amfani da na’urorin kakkabo jiragen sama, akan hare-haren na rundunar kai daukin gaggawa tare da kakkabo da dama daga cikinsu. Wadannan hare-haren dai sun faru ne jim kadan bayan wata ziyara da shugaban majalisar shugabancin kasar ta Sudan janar Burhan Abdulfattah ya kai garin “Um-Ruwabah’ wanda sojojin Sudan din ba su dade da kwato shi ba. A cikin makwannin bayan nan dai sojojin na Sudan suna cigaba da samun nasara akan...
Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga karatu har na tsawon shekaru biyu. Labarin ya nakalto hukumomin Jami’ar na cewa, wadannan daliban sune suka shirya zanga-zanga a cikin Jami’ar, inda suka maida ita cibiyar goyon bayana Falasdinawa a Gaza. Ta kuma kara da cewa wannan kin kabilar samiyawa ne. Jami’ar ta sa an kama wasu malaman jami’ar, ta kuma dakatar da wasu daga karantarwa, sannan wasu kuma an koresu daga jami’an kwatakwata....
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya raba fiye da Naira Miliyan 75 ga masu karamin karfi. Malam Umar Namadi, ya yaba da tsarin bada tallafin ga al’ummar karamar hukumar ta Miga. A cewarsa, tsarin bada wannan tallafi da kakakin majalisar ya yi ya dace da kudirorin gwamnatin jihar 12. Yana mai nuni da cewar, a kowacce Karamar Hukuma za a kaddamar da irin wannan tallafi domin bunkasa tattalin arzikin...
Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja. Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa. Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi...
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmaki kan birnin Tulkarm da sansaninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun shiga rana ta shida suna kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkarm da sansaninsa, inda yanayin tsoro da tarwatsa gine-gine suka lullube mazaunan yankunan, adaidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da kai hare-hare da kutsawa cikin gidajen Falasdinawa, lamarin da ya yi sanadin barnatar da dukiyoyin Falasdinawa da dama tare da tilastawa iyalai masu yawa tsarewa zuwa gudun hijira. Sojojin mamayar Isra’ila suna gudanarda sintiri da kafa ta hanyar gudanar gudanar da yawo a kan tituna a cikin birnin musamman a yankunan yamma, kudanci da kuma gabas, inda...
Sojojin Sudan sun kwace iko da wani birni da ke arewacin Kordofan daga hannun ‘yan tawayen kasar na Rapid Support Forces Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta sake kwace iko da birnin Umm Rawaba, birni na biyu mafi girma a arewacin jihar Kordofan da ke kudancin kasar daga hannun dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce: Godiya ta tabbata ga Allah da yardarSa, sojojin sun tsarkake birnin Umm Rawaba daga hannun mayakan dakarun kai dauki gaggawa da sojojin hayarsu, tare da janyo musumunanan hasarori masu yawa. A cewar shafin yanar gizo na Arabi 21, Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun mamaye birnin...
Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita. “A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in ji shi. Ya ci gaba da cewa, Allah ya albarkaci Arewacin Nijeriya da kasar nomad a kuma yanayi mai kyau, musamman ma Karamar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, inda ake iya shuka wannan Iri na Inibi, ya girma; a kuma amfana da shi. Shugaban ya sanar da cewa, kimanin kashi 85 cikin 100 na Inibin da ake nomawa a kasar nan, na fitowa ne daga...

Limamin Juma’ar Tehran Ya Jinjinawa Wanda Ya Assasa Juyin Musuluncin A Iran Marigayi Imam Khumaini ( R.A)
Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin. Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da falsafa. Limamin juma’ar na Tehran wanda yake jawabi dangane da zagayowar cikar shekaru 46 daga dawowar Imam Khumaini Iran bayan zaman hijira na shekaru 15 a kasashen waje, ya ce abin alfahari ne yadda wannan rana ta zagayo a daidai wannan lokacin da kungiyoyin gwgagwarmayar musulunci suke kara bunkasa da daukaka a duniyar musulunci. Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma bayyana cewa abinda yake...
Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi. Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa. Shekara guda bayan binne shi,...
Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...

Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya. Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar Isra’ila Inbar Lipman Garden, cewa ya yi A wannan rana mai girma muna tuna Yahudawa maza da mata da yara miliyan shida da aka kashe a cikin Holocaust tare da miliyoyin wasu da ke shan wahala a ƙarƙashin mulkin Nazi. Muna girmama abubuwan tunawa da su ba wai kawai nuna rashin jin dadi ba a a har ma da sake tabbatar da aniyarmu...
Wata tankar mai cike da fetur ta yi bindiga a cikin wani gidan mai da ke garin Dutse, hedikwatar Jihar Jigawa. A safiyar Juma’a ne kakakin ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Shiisu Adamu, ya sanar cewa lamarin ya faru ne a gidan mai na Shakkato da ke kan hanyar Kiyawa. Hakan na zuwa ne yayin da aka samu karuwar fashewar tankoki dauke da man fetur a Najeriya, wanda mafi muninsu a baya-bayan nan ya yi ajalin sama da mutum 100 a Jihar Neja. Ko a shekarar da ta gabata, irin haka ya faru a Jihar Jigawa, inda sama damutum 100 suka rasu. Seaman Abbas da Hussaina: An dakatar da shirin Brekete Family Hausa An ɗaure zawarawa a gidan yari...
Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin Qatar, Doha a jiya Alhamis. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, tawagar kungiyar ta hada da shugabannin Khalil Al-Hayya, Hussam Badran, Izzat Al-Rishq da Basem Na’im. Darwish ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tallafa wa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yancin kai, yana mai jaddada cewa: “Harin Daukan Fansa naAmbaliysar Al-Aqsa Mai Albarka” wani ci gaba ne a yunkurin al’ummar...
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan mamayar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan sahayoniyya, tare da yin nuni da cewa, za ta ci gaba da kokarinta ba tare da wata matsala ba, domin kubutar da su ta kowace hanya. Kungiyar Hamas ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a a yayin bikin sakin wani sabon rukunin fursunonin Falasdinu, tana jaddada cewa: Hamas ta sake sanar da babban alfahari da girmamawa ga al’ummar Falastinu masu tsayin daka,...
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa. Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F. Sandy, a fadar gwamnati. Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya. Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa ’yan Najeriya suna...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar dabbobi. Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdulkadir Tukur mai shekara 35 da Ibrahim Saidu mai shekara 20. KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An same su da tumaki 28 da awaki 57, jimillar dabbobi 85 da ake zargin da sato su. An kama su ne a ranar 25 ga watan Janairu, 2025, bayan da Dagacin Tulmi a Ƙaramar Hukumar Akko, Abubakar Umar, ya kai wa ‘yan sanda rahoto. Wani mafarauci mai suna Yayaji Muhammad ne ya tare su a garin Tulmi, inda suka kasa bayar da cikakken bayani kan...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...

An Tsamo Gawakin Mutane 30 A Karon Da Wani Jirgin Fasinja Ya Yi Da Wani Jirgi Mai Saukar Ungulu A Birnin Washinton
Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da wadanda suke da rai zuwa neman gawaki kawai, tunda ana ganin da wuya a sami wani da rai a cikin fasinjojin jirgin. Ya zuwa yanzu dai an tsamo gawakin mutane 30, kuma suna ci gaba da aikin gano wasu karin gawakin. Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa jirgin fasinjar ya rabu zuwa kasha ukku sannan ya fada cikin wani ruwa mai zurfin mita 7....
Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio. Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin. Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok Hisbah Ta Kama Matashi Da Matashiya Kan Yin Aure Saɓanin Dokokin Musulunci A Kano Yarjejeniyar tsagaita wutar an ƙulla ta ne don bayar da damar musayar fursunonin da Hamas ke riƙe da su da kuma waɗanda ke tsare a Isra’ila. Sai dai wannan matakin ba zato ba tsammani ya haifar da rashin tabbas kan ci...
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara. Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga. “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame. “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar, hukumar bunkasa tattalin arziki ta jihar ce ta fitar da ta hannun shirin farfadowa daga annobar cutar corona. A cewar sa, kusan mutane dubu ashirin da uku ne za su amfana da tallafin naira dubu saba’in da biyar a jihar. Yana mai cewar, hakan na daga cikin kudirin shugaban kasa na Renewed Hope agenda...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Amince Da Bukatar Kawo Karshen Rikicin Jin Kai Cikin Gaggawa A Gaza
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15. Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai. A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda...
Ministan Harkokin Wajen Benin Ya Yi Wa Sinawa Gaisuwar Sabuwar Shekara
Yayin da dokar haramtawa hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA) yin aiki a Isra’ila ke gab da fara aiki, kwamitin sulhu na majalisar ya kira wata budaddiyar muhawara dongane da batun, inda wakilin Sin da wakilan sauran kasashe suka sake bayyana goyon bayansu ga hukumar. Wakilin Sin na dindindin a MDD Fu Cong, ya yi kira ga Isra’ila da ta daina dakatarwa da kai wa hukumar hari, kana ta dakatar da zartar da dokoki masu ruwa da tsaki, yana mai kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyon bayan hukumar wajen gudanar da ayyukanta da marawa MDD da kwamitin sulhun baya, wajen daukar matakan gaggawa domin tabbatar da hukumar ta gudanar da ayyukanta. Yankin Gabashin...