2025-02-21@14:43:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1114
«a iskar gas»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.” Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a. “Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.
A yunƙurin daƙile ta’adar garkuwa da mutane, Majalisar Dokokin Jihar Edo, ta amince da dokar zartar da hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin. Majalisar ta amince da ƙudirin ne wanda ta yi wa bita daki-daki yayin zaman da ta gudanar a ranar Talata. USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shugaban masu rinjaye na majalisar, Charity Aiguobarueghian ne ya jagoranci gabatar da ƙudirin wanda shugaban marasa rinjaye, Henry Okaka ya goyi baya. A baya dai Majalisar Dokokin Edo ta ayyana hukuncin ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka tabbatar wa laifin garkuwa da mutane tare da ƙwace duk wani abu...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa a ƙetare har na tsawon kwanaki 90. DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da binciken ne a dalilin ruɗanin da ya dabaibaye duniya wanda ke cin karo da muradun Amurkan. Haka kuma, Shugaba Trump ya ce za a...
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...

Ma’aikatar sharia ta kasar Iran Ta bada sanarwan Kama Yan Kasar Burtaniya 2 Tare Da Tuhumar Leken Asiri
Kakakin ma’aikatan shari’a a kasar Iran ya bayyana cewa jami’an tsaro na kasar Iran sun kama mutane biyu yan kasar Burtaniya tare da tuhumar aikin liken asiri a lardin Kerman na kasa. Kamfanin dillancin labaran (IP) na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen biyu suna tafiye-tafiye zuwa lardunan kasar Iran suna tattara bayanai a cikin watan Jeneru na wannan shekarar a lokacinda suka fada hannun Jami’an tsaron kasar. Labaran sun kara da cewa mutanen biyu sun sauya kamamnci, zuwa kamar masu yawon bude ido suna tsammanin cewa ba za’a ganesu ba. Kakakin ma’aikatar Shari’ar ya bayyana cewa ma’aikatan liken asirin kasashen turai da dama sun fi aiki ne a bangaren karatu a makarantun kasar Iran. Asghar Jahangir ya bayyana cewa...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Mususlunci A Iran IRGC Sun Bada Sanarwan Kai Hari A Kan HKI Karo Na Uku
Burgediya Janar Amir Ali Hajizadeh babban kwamandan sojojin sararin samaniya ya bada labarin cewa sojojinsa, zasu kai farmakin ‘Wa’adusadik na 3 nan ba da dadewa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Ali Hajizadeh yana fadar haka a jiya Talata, a hirar da ta hadashi da wata kafar yada labarai labaran kasar. Ya kuma kara da cewa, zasu kai harin don haka HKI da Amurka kawo mata yaki. Yace wadan nan kasashe suna neman yaki da JMI, amma mafi yawan shirin nasu na farfaganda ne. Amma dolene mu shiga yaki don mu hana yaki faruwa. Ya kuma kammala da cewa sojojin Iran suna yaki ne don ladabtar da HKI don ta gane cewa JMI ba mai sauki....
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma Mali suka fice daga kungiyar sannan suka samar da sabon Passport a tsakanin kasashen uku, sai al-amura suka fara sauyi tsakaninu da Ecowas. Sun fara hana wadanda suke rike da Passpory na kasashen ECOWAS shiga kasashen ba tare da visa ba. Gwamnatin Nijer bata bada sanarwan fara aiki da wannan dokar ba. Kuma wani jami’in shige da fice na Niger ya ce umurnin ne aka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
A ranar 17 ga watan Fabrairu, agogon birnin New York ne, aka yi wani zama na musamman na nuna fim din Nezha 2 a hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin, da babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da kuma kungiyar masu sha’awar karanta littattafai na kasar Sin dake MDD suka dauki nauyin shiryawa tare. Fiye da baki 150 da suka hada da mataimakin babban sakataren MDD Xu Haoliang, da jami’an diflomasiyyar kasashen Faransa, Rasha, Girka, Thailand da sauran kasashe a MDD, da ma’aikatan hedikwatar MDD, da ’yan jarida sun halarci bikin nuna fim din. Xu Haoliang, mataimakin babban sakataren MDD ya bayyana...
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...
Tara Daga N100,000 Kan Amfani Da Mitar Wutar Lantarki Ta Ɓarauniyar Hanya – NERC
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al’umma ta Jihar Kano mai suna ‘Kano State Security Neighborhood Watch.’ Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne tare da wasu ƙarin dokokin guda biyu, waɗanda suka haɗa da dokar gyara hukumar sufuri ta jihar da kuma wadda ta kafa cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta jihar. Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar ta ce gwamnan ya amince da dokokin ne a zaman majalisar zartarwar jihar na 25 da ya gudana a fadar gwamnatin jihar. Hakan na zuwa ne bayan dokar samar da...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaron al’umma ta Jihar Kano mai suna ‘Kano State Security Neighborhood Watch.’ Gwamnan ya sanya hannu kan dokar ne tare da wasu ƙarin dokokin guda biyu, waɗanda suka haɗa da dokar gyara hukumar sufuri ta jihar da kuma wadda ta kafa cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta jihar. Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar ta ce gwamnan ya amince da dokokin ne a zaman majalisar zartarwar jihar na 25 da ya gudana a fadar gwamnatin jihar. Hakan na zuwa ne bayan dokar samar da...
Idan Rana Ta Fito, Tafin Hannu Bai Iya Kare Ta
Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja. Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya. Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci...
An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata. A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar. Ya kuma nuna jin dadinsa da goyon baya da hadin kai da mazauna Kano ke bai wa gwamnatinsa, ya kuma bukace su da su ci gaba da jajircewa kan manufofin gwamnatin.
Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin zaɓe da ya binciki Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC dangane da jinkirin da take yi na gudanar da zaɓen cike giɓin wasu kujerun ’yan majalisar tarayya da na jihohi. Majalisar a wannan Talatar ta kuma bayyana cewa jazaman ne kwamitin ya gayyaci Hukumar INEC domin ta bayar da dalilai kan tsaikon da aka samu da kuma yadda take ƙoƙarin yi wa tufkar hanci. Gubar harsashi ta jikkata mutane dama a Zamfara Da wahala City ta yi nasara a gidan Madrid — Guardiola Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta buƙaci kwamitin ya sauke wannan nauyi tare da miƙa mata rahoton bincikensa nan da makonni huɗu. Wannan dai na zuwa ne bayan ƙorafin da wani...
Yawan kudin tikitin kallon fim din “Ne Zha 2” na kasar Sin da aka saya ya zarce dala biliyan 16 a daren jiya, abin da ya sa ya shiga sahun fina-finai 9 mafi samun yawan kudin tikitin kallon fim dake sahun gaba a duniya. Dalilin da ya sa fim din samun wannan ci gaba shi ne ingancin abin da ya kunsa. Labarin da wannan fim ya gabatar ya yi daidai da wasan yanar gizo mai suna “Black Myth: Wukong”, wanda shi ma na kasar Sin ne. “Ne Zha” da “Wukong” dukkansu jarumai ne dake cikin tatsuniyar gargajiya a dogon tarihin Sin, wadanda ba su mika wuyansu ga makomar da aka tanade su ba, kuma suka yi kokarin rike da kaddararsu...
Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu ba su sanya ido Amerika ta ci karenta ba babbaka, babu shakka su ma za su dauki matakan ramuwar gayya, ta hanyar kakaba haraji a kan kayayyakin da Amerika ke fitarwa. Wannan lamari zai haifar da yakin ta fannin kasuwanci, abin da ba zai amfanawa kowa ba.
’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu da suka samu ƙonuwa da raunika daban-daban. Hotuna da wakilinmu na naɗa ya hasko waɗanda lamarin ya shafa suna kwance ana kawo musu agaji, inda galibi sun ƙone a ƙafafu da cinya har zuwa mazaunai.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Barazanar makiya a kan kasar Iran da al’ummarta ba ta yi nasara ba Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa: Gagarumar zanga-zamga da al’ummar Iran suka gudanar a ranar 22 ga watan Bahman ta tabbatar da cewa barazanar makiya a kan Iran da al’ummarta ba ta cimma nasara ko yin tasiri ba. Jagoran juyin juya halin Musuluncin yayin da yake karbar bakwancin dubban mutane daga lardin gabashin Azarbaijan a Husainiyar Imam Khumaini da ke Tehran fadar mulkin kasar a ranar Litinin din da ta gabata, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar bore mai tarihi na al’ummar Tabriz a ranar 29 ga watan...

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Irin Gagarumar Rawar Da Iran Ta Taka A Fegen Tsaro Yakin Tekun Pasha
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana taka rawa ta musamman wajen wanzar da kwanciyar hankali da tsaron yankin Tekun Pasha Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta hanyar mallakar mafi yawan layukan kan iyaka da tekun Pasha da kuma iko da mashigar Hormuz, ta taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron wannan ruwa da yankunan makwabtanta. Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yayin taron tarihin huldar kasashen waje na Iran karo na 8, mai taken “Manufar harkokin wajen Iran da gabar tekun Pasha a cikin mahallin tarihi,” wanda aka gudanar a safiyar yau Talata a cibiyar nazarin siyasa da kasa da kasa na ma’aikatar harkokin...
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya aikata duk abin yake so Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da wa’adin da ya bayar dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin, yana mai cewa ya shaidawa fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika duk abin da yake so. Trump ya tabo batun mataki na gaba – ana sa ran za a fara tattaunawa nan ba da jimawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar – ya ce: “Ya rage ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan mataki na gaba, tare da tuntubarsa.” An kuma tambayi Trump ko jinkirin jigilar makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila a karkashin Shugaba Biden zai “hana tsagaita...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City, Pep Guardiola, ya ce damarsu ta samun nasara kan Real Madrid ’yar kaɗan ce a yayin da a gobe Laraba ƙungiyoyin biyu za su yi karon-batta a Gasar Zakarun Turai. Ana iya tuna cewa, a karawar farko da ƙungiyoyin suka yi a Talatar makon jiya, Madrid ce ta je har gida ta lallasa City da ci 3-2, minti huɗu kafin a tashi wasan. Hauhawar farashi ya koma kashi 24 a Nijeriya — NBS Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya To sai dai gabanin karawar ta biyu da za a yi a filin wasa na Bernabeu, a wasan neman gurbin tsallakawa zagayen ’yan 16, Guardiola ya ce damar da suke...
Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 3000 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu. Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda...
EFCC Ta Cika Hannu Da Mutane 15 Kan Zargin Zamba Ta Intanet A Abuja

Ministan Harkokin Waje Iran Ya Jaddada Cewa Iran Ba Zata Tattauna Da Amurka A Karkashin Takunkumai ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arazgchi ya kara jadda cewa JMI ba zata zauna a teburin tattaunawa da kasar Amurka ba a karkashin takunkuman tattalin arziki ba. Ya kuma kara da cewa Amurka ba zata iya tursasawa kasar Iran zama da ita ba. Ministan ya kara da cewa, ba zakin baki mukeso ba, sai mun gani a kasa a sanya hannu a dakardu sannan mu gani a kasa. Ministan ya fadawa tashar talabijin ta Al-Alam mai watsa shirye shiryenta da harshen larabcin a nan Tehran, ta kuma bayyana cewa, Trump ya bayyana cewa ya na bukatar tattaunawa da kasar Iran kan shirinta na makamashin nukliya tun watan farkon waten Fabrairu amma ba abinda muka gani a kasa.
Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji. Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa. Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa. A wata wasika da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’el Baghae ya ce gwamnatin kasar Iran zata aika tawaga mai karfi zuwa kasar Lebanon don halattar Jana’izar Sayyid Hassan Nasarallah wanda za’a gudanar a cikin yan kwanaki masu zuwa. Bakha’I ya kara da cewa, zamu halarci Jana’izar a kasar Lebanon, kuma zamu aika da tawaka wacce zata kunshi manya-manyan jami’an gwamnati da kuma malaman addini. A ranar Talatan da ta gabata ce wani jami’an kungiyar ta Hizbullah, ya bada sanarwan cewa baki daga kasashe 79 ne zasu halarci jana’izar. Sheikh Ali Daher shugaba kwamitin gudnar da jana’izar ya kara da cewa, ranar zata kasashen ranar sabonta bai’a da marigayin da kuma wanda ya gaje shi. A ranar 27 ga watan Satumba shekara ta...
Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al-Thani zai fara ziyarar aiki na kwana guda a nan Tehran, don tattauna al-amura masu muhimmanci da Jami’an gwamnati JMI. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbass Aragchi ya bayyana cewa, a gobe muna tare da sarkin Qatar Tamim bin Hamad Athani, inda zamu tattauna al-amura masu muhimmanci a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana fadar cewa kasar Qatar ta taka rawa a tsagaita wuta tsakanin HKI da kuma kungiyar Hamas, sannan tana da dangantaka mai karfi da kasar Iran. Ya ce yankin gabasa ta tsakiya tana fuskantar sauye-sauye masu yawa, da kuma barazana iri-iri, kuma wannan zuwan zai kasance sabonta dangantaka tsakanin kasashen biyu ne. Duk da...
Ministan watsa labarai na kasar Lebanon Mr Paul Marcos ya bada sanarwan cewa sojojin HKI sun fara janyewa daga yankunan da suke mamaye da su a kudancin kasar Lebanon. Wanda kuma zai bada daman ga sojojin kasar su maye gurbinsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana cewa wannan sauyin zai kyautata al-amuran tsaro a yankin. Wanda kuma zai tabbatar da ikon kasar Lebanon a kan dukkan kasar ta. Kafin haka dai majalisar dokokin kasar Lebanon ta bokaci ficewar dukkan sojojin kasashen waje daga kasar. Sannan bisa kudurin mai lamba 1701 na MDD rundunar UNIFIL zata taimaka wa sojojin kasar tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin HKI da kuma kasar Lebanon. Labarin ya kara da...
Jagoran al’umar yankin Neja Delta, Cif Edwin Clark ya rasu yana da shekaru 97 a duniya.
A ranar Asabar din da ta gabata ne shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU, suka zabi shugaban kasar Angola Joao Lourenco, a matsayin sabon shugaban karba-karba na kungiyar da kuma ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Djibouti, Mahamoud Ali Youssouf, a matsayin sabon shugaban hukumar gudanar da ayyukan kungiyar, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasashe biyu masu matukar muhimmanci a nahiyar, wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) da kasar Sudan. Rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kara kamari, bayan samun galaba a wasu yankunan kasar da ‘yan tawayen M23 suka yi, na baya-bayan nan shi ne kwace iko da muhimman wurare da dama a birnin Bukavu, hedkwatar...
Sojojin HKI Sun Bada sanarwan cewa ba zasu bar wasu tuddai guda 5 a kudancin kasar Lebanon ba, har zuwa wani lokacin da basu sani ba, saboda tsaron haramtacciyar kasar. Tashar talabijin ta Almayadin ta kasar Lebanon, ta nakalto cewa tankunan yakin HKI sun kutsa cikin garin kafarshuba na kudancin kasar Lebanon kuma sun kafa sansanin sojojin a garin. A jiya litinin ce yakamata sojojin HKI su fice daga kudancin kasar Lebanon da suka mamaye, amma a jiyan din ne suka bada sanarwan cewa ba zasu fita daga wurare 5 daga kudancin kasar ta Lebanon ba. Kafin haka bayan kwanaki 60 da tsagaita budewa juna wuta ne, yakamata sojojin HKI su fice daga kudancin kasar ta Lebanon, amma tare...
Wasu daga cikin mutanen kasar Afirka ta kudu da suke dauke da cutar HIV suna yin koken cewa janye tallafin da Amurka ta yi a karkashin hukumar nan ta USAID, zai jefa rayuwarsu a tsakanin mutuwa da rayuwa. Da akwai miliyoyin mutane a kasar ta Afirka Ta Kudu da suke dauke da cutar HIV da su ka cutu daga dakatar da ayyukan hukumar USAID akan kiwon lafiya. Yankin KwaZulu-Natal dake kasar Afirka ta kudu, yana da masu fama da cutar ta HIV da sun kai miliyan 1.9 a bisa kididdigar 2022. A fadin kasar kuwa da akwai masu dauke da wannan cutar da sun haura miliyan 7.5 da shi ne adadi mafi girma a duniya.
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3” a lokacin da ya dace. Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba su cimma manufarsu ba. Iran dai ta kai wa HKI hare-hare guda biyu a aka bai wa Sunan “ Wa’adussadik” na daya da na biyu. Hare-haren na Iran dai sun kasance mayar da martani ne akan harin da HKI ta kai wa karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Syria da kuma kashe mata jami’an soja masu bayar da shawara ga gwamnatin Damascuss....
Dakarun “Kassam” na kungiyar Hamas sun sanar da shahadar Muhammad Shahin wanda daya ne daga cikin kwamandojinta da ya yi shahada sanadiyyar harin da HKI ta kai masa a birnin Saida na kasar Lebanon. Sanarwar ta dakarun “Kassam” ta ce, Muhammad Ibrahim Shahin wanda ake yi wa lakabi da Abul-Bara’a ya yi shahada ne a karkashin “Tufan-ak-Aksa” bayan da ‘yan mamayar HKI su ka yi masa kisan gilla a garin Saida dake kudancin Lebanon a jiya Litinin. Har ila yau dakarun Kassam sun yi bayani akan rawar da shahidin ya taka a fagen gwgawarmaya da jihadi akan ‘yan mamaya, tun daga boren Intifada na Aksa, har zuwa farmakin guguwar Aksa. Haka nan kuma bayanin na Kassam ya ce, Abul-Baraa ya...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya ne dai Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro sababbin hukumomin raya shiyyoyin ƙasar nan da nufin kawo musu ci-gaba. Gabanin ƙirƙirar waɗannan hukumomin, gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ce ta fara kirkirar hukumar raya yankin Neja Delta bayan wasu ƙalubale da suka dabaibaye yankin. Na baya-bayan nan ita ce Hukumar Raya yankin Arewa ta Tsakiyar ƙasar nan bayan da ’yan yankin suka nace da yin ƙorafin cewa an mayar da su saniyar ware. NAJERIYA A YAU: Dalilan Saukar Farashin Kayan Masarufi A Kaswanni DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan...
A ranar 15 ga watan Fabrairu, ministocin harkokin waje na kasashen Amurka, Japan, da Koriya ta Kudu sun yi shawarwari a Munich na kasar Jamus. A cikin sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, a karon farko, sun bayyana goyon bayansu ga yadda Taiwan za ta shiga cikin kungiyoyin kasa da kasa da suka dace, tare da jaddada muhimmancin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. Dangane da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Guo Jiakun, ya sake nanata cewa, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi da ita ba, kuma batun Taiwan lamari ne na cikin gidan kasar Sin kawai, kuma ba ta yarda da wata tsangwama daga...
Cibiyar Malam Bukar mai kula da hidimar al’amuran da suka shafi karantar da Alqur’ani da dake Babura ta gudanar da bitar yini 4 ga Malamai masu Tafsiri da Alarammomi a garin Babura dake Jihar Jigawa. Da yake jawabi yayin rufe bitar, Shugaban cibiyar, Sheikh Gwani Dr Murtala Bashari yace an shirya bitar ne da nufin kara zaburar da juna da kuma nusar da masu gabatar da tafsirin Alkur’ani kan maida hankali wajen karfafa bin abin Alkur’ani da Sunnar Manzon Allah don kaucewa fadawa miyagun akidu. Shugaban Wanda jami’in gudanar da Shirin, Dr Ismail Ali kura ya wakilta, ya yabawa mahalarta bitar da jagororinsu bisa kwazonsu. Shi ma a nasa jawabin, bako na musamman Farfesa Muhammad Sani Umar Rijiyar...
Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina. AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuna cewa, an kai harin ta’addanci a wani sansanin PMF da ke cikin al’umma, inda aka ce, ‘yan bindigar sun kashe jami’an PMF biyu da CEC hudu.
Ana fargabar cewa gobara ta yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu a yankin Onipakala da ke Ƙaramar Hukumar Ondo West a Jihar Ondo. Bayanai sun ce musibar ta auku ne da tsakar daren Lahadi yayin da jama’a ke sharar barci, lamarin da ya jefa makwabta cikin zullumi. Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino albarkacin watan Ramadana Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe Aminiya ta ruwaito cewa, zuwa wayewar gari Litinin, matar da ’ya’yanta —Bukola da Ifeoluwa— sun ƙone ƙurmus a sakamakon gobarar. Wani maƙwabcinsu da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun tsakar dare gobarar ta tashi amma ana ji ana gani ta rutsa da mutanen uku...
Kakakin Majalisan ya amince da kudirin dan majalisa mai wakiltar mazabar Keana kuma shugaban Kwamitin Majalisar kan Muhalli, Hon. Muhammed Adamu Omadefu, wanda ya bukaci dakatarwar a yayin tantance kwamishinan a zauren Majalisar da ke Lafiya, babban birnin jihar. Hon. Jatau ya ce, Majalisar za ta sake duba batun tantance shi ne kawai idan ya aika da wasikar neman uzuri mai karfi ga Majalisar kan aikata laifi da rashin biyayya da ya yi lokacin da yake Kwamishina. Ya ce, Majalisar ba za ta bari wani jami’in gwamnati ya zubar da darajar Majalisar ba.

Yawan Tikitin Kallon Fim Din “Ne Zha 2” Da Aka Sayar a Karshen Mako Ya Shiga Sahun Gaba Na Fina-Finai 5 A Arewacin Amurka
Kamfanin dake gudanar da nazari na Comscore na Amurka ya ba da kididdiga cewa, yawan tikitin da aka sayar a karshen mako na kallon fim din kasar Sin mai suna “Ne Zha 2” ya shiga sahun gaba na fina-finai 5 a arewacin Amurka. An yi kiyasin cewa, yawan kudin da aka samu a kwanaki 3 na karshen makon da ya gabata ya zarce dala miliyan 7, inda fim din ya zama mafi shahara a matakin koli da Sin ta gabatar a karshen makon a Amurka. An ce, an fara nuna wannan fim a gidajen sinima 770 dake arewacin Amurka daga ranar 14 ga watan nan da muke ciki, a matsayin fim din da Sin ta gabatar, kana yawan kudin da...
Gwamnatin Tarayya tayi kira don samun tsarin visa mai sassauci ga kamfanonin Najeriya da ke neman kafa masana’antu da kasuwanci a ƙasashen waje. Ministan Yada Labarai da Wayarda Kan Jama’a, Mohammed Idris, shine ya yi wannan kiran a Addis Ababa, Ethiopia, yayin da ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wani taro da mambobin gudanarwa na Al’ummar Najeriya a Ethiopia, a cikin tattaunawa da aka yi a wajen zama na 38 na Taron Shugabannin Kasashe na Tarayyar Afirka (AU). Ya jaddada cewa, yayin da Najeriya ke ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga kamfanonin waje don zuba jari da aiki cikin ƙasar, yana da kyau da kuma amfanar juna ga sauran ƙasashen duniya su ba da...
Ya ce: “A bara, na wakilci Nijeriya a Indonesiya, kuma na gano cewa akwai manyan kamfanoni hamsin daga Indonesiya da ke aiki a Nijeriya, amma ba mu da ko kamfanoni biyar daga Nijeriya da ke aiki a Indonesiya. “Idan suna son zuwa ƙasar mu su yi kasuwanci saboda yawan mutanen mu da kuma damar da muke da ita na sayen kayayyakin su da ayyukan su, to ya kamata a samar da tsarin da zai ba da dama ga kamfanonin Nijeriya su ma. Matsalar ba da biza ga ‘yan Nijeriya na nan a Indonesiya da Habasha.” Dangane da matsalar da ‘yan Nijeriya ke fuskanta bayan da gwamnatin Habasha ta soke tsarin nan na ‘e-visa’ da ‘Visa-on-Arrival’ ga matafiya daga...
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta haramta wa Gwamnatin Tarayya riƙewa ko kuma yi wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi 44 na jihar katsalandan. Mai Shari’a Musa Ibrahim Muhammad ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, biyo bayan ƙarar da wakilan ƙananan hukumomin jihar suka kai na kare ‘yancinsu na cin gashin kai dangane da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayyar ke ware musu. Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina Wannan shari’ar dai ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta dakatar da bai wa ƙananan hukumomin jihar kuɗaɗe, bisa zargin tafka maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomin da...
Nijar ta bayyan fatanta na ganin ta kulla yarjejeniya da kafofin yada labarai na Iran. Wannan bayanin na kunshe ne a bayyannin da jakadan Nijar a Tehran Malam Seydou Ali Zataou, ya yi a ganawarsa da shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin sashen kasashen waje na Iran, Ahmad Norozi a wannan Litinin. Bangarorin sun bayyana kyakyawan fatan musayar bayanai da shirye shirye a tsakaninsu da nufin karya laggon kafofin yada labarai na kasashen yamma dake yada gurbatattun bayanai da rahotanni kan kasashen. jakadan na NIjar, ya kuma yi tinu da irin kyakyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu.
Bisa ga yadda wasu fina-finan kasar Sin ke samun karbuwa a kasuwannin kasa da kasa, ciki har da fim din “Ne Zha 2”, a yau Litinin an kaddamar da bikin “Tafiya a kasar Sin bisa fina-finan kasar” a gidan tarihi na fina-finai na kasar Sin dake nan birnin Beijing, wanda hukumar kula da fina-finai ta kasar Sin da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) suka shirya, kuma gidan talabijin na kasa da kasa na kasar Sin (CGTN) da cibiyar shirye-shirye ta tashar fina-finai suka karbi bakuncinsa. Bikin wanda ya fi mayar da hankali kan gudanar da ayyukan tallata fina-finai da yawon shakatawa ta hanyar nuna fina-finan kasar Sin a ketare, da shirya bikin nune-nunen fina-finan kasar...

Kasar Sin Ta Taya Mahmoud Ali Youssouf Murnar Zabarsa Da Aka Yi A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar AU
A kwanan nan ne dai aka gudanar da taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka wato AU karo na 38, inda aka zabi ministan harkokin wajen kasar Djibouti Mahmoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban hukumar gudanarwar AU na tsawon shekaru hudu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya taya shi murna a yau 17 ga wata, ya kuma jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa tare da Youssouf, da sabuwar hukumar gudanarwa ta AU. Yayin da yake amsa tambayoyi a gun taron manema labaru na yau, Guo Jiakun ya bayyana cewa, kasar Sin tana kallon dangantakarta da AU daga mahanga mai muhimmanci kuma na dogon lokaci. Yana mai cewa “A halin yanzu, zaman lafiya da...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura. Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta da wani tasiri a kan wannan kasa da kuma al’ummarta. Jagoran ya yi ishara da irin gagarumar fitowar al’ummar kasar a cikin jerin gwano da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci, wanda ya hambarar da azzalumar gwamnatin Pahlavi ta tsohuwar gwamnatin Amurka. Ayatullah Khamenei ya sake ba da misali da irin dimbin abubuwan da suka faru a lokacin zagayowar nasarar...
Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin da kasashen Afirka suka dauka a kan Isra’ila da “mummunan” ayyukanta a Gaza. A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce tana adawa da keta dokokin kasa da kasa da kuma “kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da Isra’ila ke yi”. Kungiyar dai ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman...
Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah. Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce kasar za ta halarci gagarumin bikin mai matukar muhimmanci, Tunda farko dai kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan...
Bangaren kungiyar Hamas da ke dauke da makamai ya tabbatar da shahadar wani daga cikin jami’in kungiyar a wani harin Isra’ila. Muhammad Ibrahim Shaheen, ya yi shahada ne a wani harin da wani jirgin yakin Isra’ila ya kai a Sidon. Kassam Brigades ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi tsayin daka kan zalincin Isra’ila, ciki har da lokacin yakin Gaza. Ita ma Isra’ila ta tabbatar da kashe jami’in na Hamas a harin da ta ce ta kai kan a Lebanon Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin ta sama a Sidon, inda suka ce sun kashe wani “dan ta’adda” Bafalasdine. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kokarin ganin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma...
Kungiyar M23 Ta Kwace Wani Birni Na Biyu A Gabashin DR Congo Rahotanni daga Congo na cewa Kungiyar yan tawayen DR Congo ta M23 ta kutsa birnin Bukavu birnin mafi girma a gabashin kasar, inda ta kwace ofishin gwamnan lardin. Bayanai sun ce mayakan sun kutsa cikin birnin ba tare da fuskantar wata tirjiya ba, kuma sun samu tarba mai kayu daga jama’ar yankin. Bukavu shi ne birni na biyu mafi girma a yankin da ƴan tawayen suka karbe bayan Goma mai kunshe da albarkatun kasa. A ranar Juma’a ne mayakan suka kame filin jirgin saman birnin na Bukavu da ke da tazarar kilomita 30 arewa da birnin – daga nan kuma sai suka nufi birnin wanda shi ne babban...
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin. Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar 15 ga watan Fabrairu, inda waɗanda ake zargin suka kai yarinyar wani kango a jeji suka keta mata haddi. Rahoton na cewar, “Hedikwatar ‘yan sandan jihar reshen Ƙaramar Hukumar...
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da Jam’iyyar APC ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar wasu hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da suka hada da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun raba kudi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 da ke Kano a gaban kotu. Sai dai kuma hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke ya tabbatar da hakkin kananan hukumomi na samun kudadensu, tare da hana gwamnatin tarayya ko wasu hukumominta rike kason su. Da yake jawabi bayan yanke hukuncin, lauyan kananan hukumomi 44, Barista Bashir Wuzirchi, ya bayyana matakin a matsayin nasara ga jihar Kano.
Ministan tattalin arziki na kasar Iran Abdunnaser Himmati yana halatan taro dangane da matsaloli da kuma dammakin da kasashen masu tasowa suka fama da su a birnin Riyad na kasar Saudiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa Himmati yana halattan wannan taro na kwanaki biyu ne tare da gayyatar tokwaransa na kasar Saudiya da kuma shugaban asusun lamuni ta duniya wato IMF. Labarin ya kara da cewa gwamnatin JMI dai tana kokarin ganin ta kyautata dangantaka ko ta ina da kasashen larabawa na yankin tekun da sauran makobta. Taron ya hada da ministan kudi na kasar Saudiya, gwamnann babban bankin kasar, da kuma wadanda suke ruwa da tsaki a harkkin kasuwanci na kasar ta saudia, sun...
Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI. Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron su da tawagar kasar ta Amurka a yau. Ya kuma kara da cewa abubuwan da HKI ta sa a gaba sun hada da ganin kasar Iran bata mallaki makaman Nukliya ba, da shafe kungiyar hamas, sakin fursinoni a hannun Hamasa da kuma samar da huldar jakadanci da kasar Saudiya. Wasu kafafen yada labarai sun nakalto wasu manya manyan jami’an sojojin kasar suna tunanin dakatar da...

Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Da Hamas Sun Yi Tirsa Da HKI Kan Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Ofer
Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya. Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kasashen Turai basa cikin tattaunawar tsagaita wuta a Ukraine. Jaridar Daily Mail ya bayyana cewa hankalin shuwagabannin kasashen turai ya tashi a lokacin da JD Vance mataimakin shugaba Trump ya fada masu cewa ba wani shugaba daga cikin shuwagabannin kasashen Turai da zasu halarci taron tsagaita wuta na Ukraine. Wannan labarin ya Eu ta kira taron gaggawa don tattauna wannan batun. Sannan Sir Keir Starmer ya kuma hanya zuwa Amurka da gaggawa. Mataimakin shugaban kuma yakadansa na musamman a kan shirin tsagaita wuta a Ukraine ya bayyanawa Ukrain kan cewa batun shigar Ukraine kungiyar tsaro da NATO bai da wani muhimmanci a wajen shugaba Trump a yanzu. Mr Vances ya bayyana hakane...
Gwamnatin Katsina ta kashe kimanin Naira biliyan 5.4 domin bai wa mata 3,610 tallafin kiwon awakai. Gwamna Dikko Umar Radda ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da shirin raba tallafin awakan a gundumar Dan-Nakolo da ke Ƙaramar Hukumar Daura ta jihar. Ya bayyana cewa, a ƙarƙashin shirin, an raba wa mata 3,610 awakai huɗu-huɗu a gundumomi 361 da ke faɗin jihar. Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri wani ginishiki ne na bunƙasa harkokin noma da kiwo wanda yake da burin ganin Katsina ta zama ja gaba a fannin dogaro da kai a Arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya. A cewar Gwamnan, kiwon awakai yana da muhimmanci kuma ɗaya ne daga cikin muradin gwamnantinsa na bunƙasa harkokin noma da...
Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan hukumar bai tsaya a kan kula da tsaftace muhalli da abinci kadai ba, suna kula da tasirin sauyin yanayi da kuma fadakar da al’umma yadda za su amfana da trallafin sauyin yanayin da ake samu daga Majalisar Dinkin Duniya. A nasa jawabin, Babban Manajan Daraktan kamfanin, Alhaji Mu’azu Elezah ya nuna bukatar hukumar ta kara kaimi wajen yayata wa al’umma ayyukanta domin zuwa yanzu mutane kadan ne suka san kasancewar hukumar da ayyukanta a sassan kasar nan, “Ya kamata ku zuba jari sosai wajen fadakar da al’umma irin ayyukanku, da kuma yadda mutane za su amfana daga tallafin yaki da sauyin yanayi na majalisar dinkin dunuya” in ji shi
Shugaban kasar Sin kuma babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar, Xi Jinping ya halarci wani taron tattaunawa na kamfanoni masu zaman kansu a yau Litinin. Xi, wanda har ila yau shi ne shugaban kwamitin tsakiya na sojin kasar, ya gabatar da muhimmin jawabi bayan sauraron ra’ayoyin wakilan ‘yan kasuwa masu zaman kansu. Li Qiang, firaministan kasar Sin, da Ding Xuexiang, mataimakin firaministan kasar, su ma duk sun halarci taron, wanda Wang Huning, shugaban majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama’ar kasar Sin, ya jagoranta. (Abdulrazaq Yahuza Jere).
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje. Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sada yankuna. Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin. Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su. Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran ...
Gwamnatin Amurka ta fara aiwatar da matakan korar ‘yan Nijeriya daga ƙasar, inda ake sa ran mutane 85 za su iso Lagos, yayin da wasu 116 ke tsare. Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, ya bayyana haka yayin wata ziyarar ban girma da ya kai wa Ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, a Tafawa Balewa House da ke Abuja. Ya bayyana cewa waɗanda ke tsare a gidan yari a Amurka ne za su kasance cikin rukuni na farko na waɗanda za a dawo da su. Ya Kamata Amurka Ta San Ana Barin Halal Don Kunya Amurka Da Isra’ila Sun Sake Barazanar ‘Lugudan Wuta’ A Gaza A nata ɓangaren, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu ta bayyana damuwa kan yadda ake gudanar da...
Kungiyar da Hansi Flick ke jagoranta ta tsallake zuwa matakin zagaye na 16 a gasar zakarun Turai, amma kuma sabon kocin na fatan ganin ya lashe babbar gasar ta kasar Sifaniya.
Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
Shirin Trump Na Gaza Rubio ya bayyana cewa shirin Trump shi ne kaɗai mafita a yanzu, duk da cewa ƙasashen Larabawa da na duniya suna goyon bayan kafa ƙasar Falasdinu tare da Isra’ila. A nasa bangaren, Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya ce kafa ƙasar Falasdinu ce kaɗai hanya ta samar da zaman lafiya a yankin.
Mai Martaba Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya buƙaci a riƙa tona asirin malaman tsubbu a duk inda suke. Sarkin wanda shi ne shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kwara, ya buƙaci malaman Musulunci da su riƙa fallasa duk masu fakewa da rigar malumta suna ayyukan tsubbu. Basaraken ya buƙaci malaman addini da “su tsaftace harkar tasu, tare da tona asirin ɓata-garin cikinsu ga jami’an tsaro kafin miyagun su kai ga aikata munanan ayyukansu ko halaka jama’a.” Ya yi wannan kira ne bayan kisan gillar da wani mai iƙirarin malumta mai suna Abdurrahman Bello, ya yi wa wata ɗaliba ’yar ajin ƙarshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kwara da ake Ilori, mai suna Hafsah Lawal. A cikin sanarwar da basaraken ya...
Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba. Bisa ci gaban Sin cikin sauri, wasu kasashe suna daukarta a matsayin wata “barazana”. Game da hakan, Zardari ya ce, a matsayin makwabciyar kasar Sin, kasar Pakistan ta san a ko da yaushe Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, kila ne a ji tsoron sauran kasashen duniya, amma ba kasar Sin ba. (Safiyah Ma)
Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan. Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin Jordan fiye da wadanda Falasdinawa suke ginawa. Wannan dai shi ne lokacin farko da HKI ta dawo da siyasar rusau a yammacin kogin Jordan tun a 1967. Wannan matakin na HKI yana zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Robio yake ziyara a Tel Aviv, kuma a lokacin da Amurkan ta bai wa HKI bama-baman MK-84 har guda 1,800.
Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin. mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya. Mafi yawancin ‘yan siyasa a birnin sun buya,saboda karatowar ‘yan tawayen cikin birnin. Wasu rahotannin suna nuni da cewa, ‘yan tawayen sun shiga cikin birnin na Bkavu, a jiya Lahadi. Bukavu dai shi ne birni na biyu da ‘yan tawayen su ka kama daga farkon watan Janairu zuwa yanzu, bayan da su ka shiga cikin birnin Goma. An Shiga Rudani A Birnin Bukavu . Sojojin DRC da kawayensu na...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yi kira ga kasasnen larabawa da na musulmi da su nuna cikakken goyon bayansu al’ummar Falasdinu domin dakile makircin hadin gwiwa a tsakanin Amurka da Isra’ila na korar Falasdinawa daga gidansu. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran, Abbas Arakci ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da babban sakataren kungiyar kasashen larabawan yankin tekun pasha a birnin Muscat na kasar Oman a jiya Lahadi. Babban jami’in diplomasiyyar na Iran ya kara da cewa; ya zama wajibi a ji sauti daya daga kasashen musulmi na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falasdinu. Arakci wanda ya yi ishara da ganawa ta farko da aka yi a matakin ministocin kasashen kungiyar larabawa...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya gabatar da jawabi da marecen jiya Lahadi inda ya tabo muhimman batutuwa da su ka shafi kasar ta Lebanon da kuma yammacin Asiya. Sheikh Na’im Kassim ya ce wajibi ne ‘yan sahayoniya su janye sojojinsu daga kudancin kasar ta Lebanon domin babu wani dalili na cigaba da zamansu. Shekih Na’im Kassim ya bayyana ranar 23 ga watan nan na Febrairu ta jana’izar Shahid Sayyid Hassan da kuma shahid Hashim Safiyuddin a matsayin ranar jaddada mubaya’a ga tafarkin da ya tafiyar da rayuwarsa a kansa da shi ne gwgawarmaya. Babban makatakardar kungiyar ta Hizbullah dai ya gabatar da jawabi ne na tunawa da jagororin Hizbullah da su ka gabata, inda...
Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa wa fararen hula bom inda ya kashe fararen hula bakwai a yankin Yani da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina. Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana. Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda biyu da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma na jihar (CWC) sun kwanta dama a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar a ranar Asabar. Wani mazaunin Gundumar Zakka da ke Ƙaramar Hukumar, yankin da abin ya faru, ya bayyana cewa an yi arangamar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda ’yan bindiga suka shirya kai wa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan.
Bishop na Cocin Katolika da ke Kontagora, Babban Rabaran Bulus Yohanna ya gudanar da bikin aure ga ma’aurata ashirin da daya a jihar Neja. A lokacin da yake jawabi yayin bikin daurin aurea cocin St. Mark Catholic da ke Nsanji Nkoso a karamar hukumar Magama ta jihar Neja, Bishop din ya bayyana cewa, bai kamata masoya na zama tare ba har sai coci ya tabbatar da su a matsayin ma’aurata bayan an biya sadaki da kuma bin ka’idoji. A cewar Most Reverend Bulus Yohanna “mafi yawansu sun fi dogaro da auren gargajiya wanda a baya ya basu damar zama tare. “Kuma muna bukatar mu tabbata cewa babu wani daga cikinsu da aka tilastawa”. “Dole ne mu ƙarfafa su su...
Najeriya ta nuna adawa da wani yunkuri na sake fasalin Sashen Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) (PAPS), saboda damuwa game sanadin da ka iya tabarbarewar hanyoyin zaman lafiya da siyasa na kungiyar. Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya sanar da wannan matsayi a madadin Shugaba Bola Tinubu, a lokacin da ake tattaunawa kan ssauye-sauyen kungiyar AU. Shugaban na Najeriya ya kuma yabawa shugabanin kasashen Ruwanda Paul Kagame da William Ruto na Kenya, bisa shawarwarin da suka gabatar na kawo sauyi da nufin ganin kungiyar ta AU ta kara zage damtse wajen magance matsalolin mambobin kungiyar. Shugaba Tinubu ya bayyana goyon bayansa na samar da kwamitin sa ido kan shugabannin kasa da...
Ƙungiyar Gamayyar Jam’iyyun Siyasa ta Ƙasa (IPAC), reshen Jihar Katsina, ta bayyana amincewarta da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Laminu Lawal Boyi, ya bayyana cewa IPAC ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da bai wa dukkanin jam’iyyun siyasa damar shiga zaɓen. Fusatattun matasa sun ƙone ofishin ’yan sanda a Ondo NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya “Baya ga shugabancina a IPAC, ni kuma shugaban jam’iyyar Accord ne, wacce ta shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 34 da kujerun kansiloli 361 a faɗin jihar. “A matsayina na ɗan takara kuma mai ruwa da tsaki, na...
An samar da ruwan sha a yankunan Danbatta, da Makoda da Minjibir dake gundumar Kano ta Arewa bayan kwashe kimanin shekaru goma. Kwamishinan albarkatun ruwa na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana haka a wani rangadin da ya kai kananan hukumomin uku domin tantance yadda ake samar da ruwan sha ga al’umma. Umar Doguwa ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya himmatu sosai wajen samar da ruwan sha a dukkan lungu da sako na jihar Kano. Ya ce an gyara kananan cibiyoyin samar da ruwan sha a yankunan inda ake samar da ruwa babu kakkautawa. Kwamishinan ya ce yanzu haka ana samun ruwan sha a kauyukan kunya, da Kilawa da ,wailare duk a karamar hukumar Minjibir yayin da...
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo. Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu. An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Ana zargin al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, amma ba a samu cikakken bayani ba sai zuwa ranar Lahadi. Wani mazaunin Ifon, wani gari da ke iyaka da Jihar Edo, ya shaida wa Aminiya cewa mutuwar matashin ta sa al’umma da abokansa yin bore. Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rikicin...
Wasu fusatattun matasa sun banka wa ofishin ’yan sanda na yankin Ifon, da ke Ƙaramar Hukumar Ose wuta a Jihar Ondo. Lamarin ya faru ne bayan da ake zargi ’yan sanda da azabtar da wani matashi har ya mutu a hannunsu. An tsinci gawar ɗan sanda a Otal a Ogun NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Ana zargin al’amarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, amma ba a samu cikakken bayani ba sai zuwa ranar Lahadi. Wani mazaunin Ifon, wani gari da ke iyaka da Jihar Edo, ya shaida wa Aminiya cewa mutuwar matashin ta sa al’umma da abokansa yin bore. Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa rikicin...

Kasar Sin Ta Kammala Gina Jirgin Ruwan FPSO Na Farko Na Duniya Mai Karfin Rikewa Da Adana Iskar Carbon
An kammala aikin gina wani jirgin ruwa sabon kira mai bambaro saman ruwa, da samarwa, da adanawa, da saukewa wato FPSO a takaice, wanda ke da na’urar rike iskar carbon da wurin adanawa, a Shanghai, a cewar Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin. Jirgin dai shi ne irinsa na farko a duniya kuma ana shirin isar da shi a karshen watan Fabrairu, a cewar jaridar. Jirgin na FPSO mai tsayin mita 333 da fadin mita 60, yana iya samar da danyen mai har ganga 120,000 a kowace rana. Kana yana iya aiki na musamman wajen rike iskar carbon dioxide da aka samar yayin kewayawa da ayyukan samar da mai. Bugu da kari, yana amfani da makamashin zafi daga iskar...
A watan Janairun wannan shekara ta 2025, an fara fitar da sabbin fina-finan Hausa masu dogon zango sama da 10, wadanda ake nunawa a tasoshin ‘YouTube’ daban-daban, bayan wasu da yawa da aka kwana biyu ana haskawa ta kafar. Manyan fina-finai, musamman masu dogon zango da kamfanin Saira Mobies ke daukar nauyi, mai suna Labarina; na daga cikin fina-finan da ke kan gaba a ‘YouTube’, harkokin fina-finan Kannywood, sun koma wannan kafar ne; tun bayan da tattalin arzikin masana’antar ya tabarbare sanadiyar mutuwar kasuwar CD, sai ake tunanin komawa ‘YouTube’ din zai inganta kasuwancin masana’antar kamar yadda yake a baya. An dade ana shirya fina-finan Hausa masu dogon zango, amma fim din Izzar So, na Lawan Ahmad; na cikin wadanda...
Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, kwamfutar da kasar Sin ta kera da kanta ta zamani na uku mai sarrafa bayanai tare da warware matsaloli cikin matukar sauri ko kwamfutar quantum a takaice, wato Origin Wukong, ta samu masu amfani da ita sama da miliyan 20 daga sassan duniya baki daya, wanda ya kasance wani muhimmin ci gaba a fannin bunkasa ayyukan da suka shafi kwamfutar quantum. A cewar cibiyar nazarin injiniyan kwamfutar quantum ta Anhui, masu amfani daga kasashe ko yankuna 139 sun samu damar shiga Origin Wukong, tare da Amurka, Rasha, Japan da Kanada a matsayin mafi yawan yin amfani da ita. A cikin wadannan kasashe, Amurka ce ke kan gaba a...
An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun. Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas. NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro Ya je otal ɗin Super G Royal da ke rukunin gidaje naAnthony Uzum tare da wata mata da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar. Da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar washegari ne, manajar otal ɗin, Deborah Adejobi, ta gano cewar ɗakin da suka kama ba a kulle yake ba. Lokacin da ta shiga, sai ta tarar da ɗan sandan a kwance babu rai, kuma matar da...
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida. Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta. Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi...
Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba da cewa “Mun san cewa kuskure daya tal zai iya cutar da kungiya. Sakamako da kuma makin da kungiya ke samu na iya sanyawa a kori mai horarwa ko kuma dan wasa ya rasa damarsa a cikin kungiya.”Hakan ya faru ga Erin ten Hag – domin daya daga cikin kurakurai hudu da na’urar VAR ta tafka shi ne bai wa West Ham bugun fanareti a...
Shirin Inganta Muhalli da Samar da Ruwan sha da kuma bunkasa aikin gona ACRESAL a jihar Jigawa yace zai zabo garuruwa masu wahalar shiga guda 6 domin sanya musu fitilun kan titi masu amfani da hasken rana. Shugaban shirin na jihar Jigawa, Alhaji Yahaya Muhamamad Uba Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar. Yana mai cewar, a yanzu haka ma tuni an zabi karin wasu garuruwa 60 domin basu bashin kudi marar ruwa. A don haka, ya bukaci wadanda aka baiwa bashin a baya da su tabbatar sun biya domin wasu su amfana. Alhaji Muhammad Uba yace Gwamna Umar Namadi ya amincewa shirin ACRESAL sayo karin injinan yashe kogi guda 2, wadanda za a...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa. Ya kara da...
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran ya ce: Tuntubar juna tsakanin Iran da Iraki ya zama wajibi don inganta matakan tsaro tsakanin kasashen biyu Mataimakin ministan harkokin wajen Iran kan harkokin siyasa Majid Takht Rawanji ya jaddada da cewa: Ziyarar da ya kai zuwa Iraki ta zo ne bisa tsarin tuntubar juna ta fuskar siyasa da aka saba yi tsakanin kasashen biyu. Rawanji ya kara da cewa: Iran da Iraki sun tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro tsakaninsu a matsayinsu na kasashen ‘yan’uwa da musulmi, tare da jaddada muhimmancin hadin kai da hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a yankin. Ya kara da cewa, tsaron yankin shi ne babban fifiko ga kasashen Iran da Iraki, wanda ya bukaci ci...
Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa. Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma...
Nijar Za Ta Yi Taron Tattauna Batun Komawa Mulkin Siyasa