2025-02-21@14:57:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 231

«biyan haraji»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
    Kasuwannin hatsi a Jihar Neja suna fama da matsalar faduwar farashi amfanin gona, sakamakon shigo da hatsi daga kasashen makwabta kamar Chadi da Ghana da Jamhuriyar Benin da Burkina Faso. Wannan yanayi ya haifar da yawan kaya, wanda ke shafar manoma da ‘yan kasuwa da masu samar da kayayyaki a yankin. Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi Manoman da suka tara hatsi don cin riba sun shiga damuwa saboda shaguna da kasuwanni sun cika da buhunhunan hatsi, amma babu masaya. Wasu daga cikin manoma da ’yan kasuwa sun bayyana wa wakilinmu cewa, wannan yanayi ya rikitar da harkar kasuwanci, inda suke fama da karancin riba saboda farashin...
    Ibrahim Yucel ya shafe shekaru 20 yana zukar taba sosai a lokacin da ya yanke shawarar ci gaba da zuka sosai. Jarabar son kowane irin abu ba shi da kyau, kuma zukar taba tana cikin mafi muni. Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari Barin shan taba yana da matukar wahala, yana bukatar jajircewa da sadaukarwa. Duk da gagarumin kokarin da suke yi, kadan ne kawai na masu zukar sigari suka sami nasarar shawo kan jarabar son da suke yi mata. Kimanin shekara 11 da suka gabata, labarin wani mutum na kokarin daina shan taba ya shahara a talabijin da sauran kafafen yada labarai lokacin da ya saka...
    A daren ranar 6 ga wannan wata, an gudanar da wani biki mai taken “Bikin Bazara Namu” a cibiyar hukumar bunksa ilmi da kimiyya da fasaha da al’adu ta MDD, wato UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda babban rukunin Sin dake hukumar, da gidan talabijin na lardin Henan na kasar Sin suka karbi bakuncin gudanar da shi, don murnar cewa, Bikin Bazara na al’ummar kasar Sin ya shiga cikin jerin bukukuwan al’adun gargajiya da bil’adama ya yi gado a duniya. Babbar wakiliyar Sin dake hukumar UNESCO, Yang Xinyu ta bayyana cewa, an yi wannan shagali ne don murnar bikin gargajiya na al’ummar kasar Sin don more al’adu tare da sassan duniya, da kara matsa kaimi ga yin hadin...
    Madara muhimmin abinci ne da ake bukata domin samun sinadarai masu ginawa da ƙara ƙarfi da lafiyar jiki. Bincike ya nuna cewa mutane biliyan shida ne ke shan madara a duniya, wanda ya sa shan madarar saniya da kiwon dabbobi ya zama wani vangare na rayuwar ɗan adam. Dubban mata Fulani suna samun kuɗaɗen shiga ta hanyar sayar da madara ga ɗaiɗaikun mutane ko jama’a ko ’yan kasuwa, waɗanda suke sha ko sarrafa shi domin amfanin kasuwanci. Lura da muhimmancin madara ga rayuwar ɗan Adam da kuma ƙoƙarin rage haɗarin da ke tattare da shan ta, Hukumar Haɓaka Noma da Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano (KSADP) ta zuba jarin Dala miliyan 8.03 don gina cibiyoyi 100 na tattara madara...
    A cewar Maiha, kafa wajen bayar da horo da kamfanin na ABIS ya yi, zai cike gibin da ake da shi a fannin kiwo da kuma bayar da gudunmawa wajen kara habaka tattalin arzikin fannin. Ministan ya kara da cewa, bayar da ingantaccen horo a fannin bunkasa kiwo, zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci da kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar, musamman ma matasa. Maiha, ya kuma bai wa kamfanin na ABIS tabbacin cewa, ma’aikatarsa, za ta bai wai kamfanin goyon bayan da ya dace, domin samar da kwararru a fannin bunkasa kiwon kasar. Da yake yin tsokaci kan jajircewa da mayar da hankali na kamfanin na ABIS, Maiha ya bukaci kamfanin ya yi hadaka da ma’aikatarsa,...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Idan Amurka ta yi barazana ga tsaron kasar Iran, to lallai Iran ta kalubalance ta Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa: Tattaunawa da Amurka ba wayo ba ce, kuma ba hikima ba ce, kuma gogewa ta tabbatar da hakan. Yayin ganawarsa da tawagar kwamandojin sojojin sama da na sararin samaniya na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada cewa: Idan Amurkawa suka yi barazana wa Iran, to lallai za su fuskanci mayar da martani, idan kuma suka aiwatar da wannan barazanar, to za su fuskanci mayar da martani Iran mai gauni, kamar yadda idan suka kawo hari kan kasar Iran, za...
    Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
    Xi Da Mai Dakinsa Sun Shirya Liyafar Maraba Da Manyan Baki A Birnin Harbin
    Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25  yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A cewar tata, tarin yawan nasa ne ya sa aka samu faduwar farashinsa a kasuwanni, wannan dalili ne ma ya sanya, don gudun kada manoman su yi asara; suke sayar da shi kan farashi mai sauki. “Daga watannin Janairu, Fabrairu zuwa Maris; ana samun kwantan Tumatir, yanzu kuma muna da injinoni masu kyau na sarrafa Tumatirin, wanda hakan zai sa a samu raguwar farashin”, in ji...
    Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
    Mayaƙan Lakurawa sun kashe farar hula ɗaya tare da jikkata wasu shida a yankin Gulma da ke Karamar Hukumar Argungua Jihar Kebbi. Da misalin ƙarfe 11 na dare ne maharan suka suka wa yankin yayin da mazauna suke tsaka da barci a ranar Alhamis suna harbe harbe-harbe. Shugaban Ƙaramar Hukumar Argungu, Aliyu Sani Gulma, ya bayyana cewa waɗanda maharan suka yi raunin harbi suna samun kulawa a Asibitin Tarayya da ke Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
    Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa. “Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe. “Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi. Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar...
    Majalisar Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Kastina ta biya wa al’ummarta kudin wutar lantarki a kowane wata. Shugaban Hukumar, Alhaji Bishir Sabi’u na cewa nan gaba za a kammala aikin layin da aka ware musu na musamman na Kamfanin Wutar Lantarki ta Kasa (TCN). Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito shi yana cewa karamar hukumar ta riga ta hada garin Jibia da layi na musamman na TCN domin garin ya rika samun wutar yadda ya kamata. Ya ce, “duk da cewa an yi gwajin wutar, amma ba a riga an kammala aikin layin na TCN ba, kuma da ya fara aiki, al’ummar garin za su fara samun wutar lantarki tsawon awa 24.” ’Yan sanda sun sa dokar hana yawon...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala. A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya. Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe. Rashin...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama.   A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan mutanen uku da suka rasu.   Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.   A cikin nuna jin kai, gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya (dauwamammiyar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi sun koma sayen na gwangwani ko na leda. NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Wannan ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan yankin da Jami’ar Bayero. Gwamnan ya yi kuma alkawarin samar da Asibitin sha-ka-tafi da samar musu da hanya da kai hasken wutar lantarki da rijiyoyin burtsatsai da bai wa iyalan mamatan jari da daukar dawainiyar karatun yaransu gwargwadon iko da kuma daukar nauyin jinyar wadanda suka ji rauni a yankin a yayin rusau da aka yi a makon da ya gabata.
    A ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Adamu, ta ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji. An ƙaddamar da tsarin ne a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da ke cikin babbar kasuwar Gombe. Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti Hajiya Aisha ta jinjina wa haɗin kan ’yan kasuwa, musamman, Alhaji Sanusi Abdullahi Mai Rediyo. Ta ce kuɗaɗen haraji suna da muhimmanci wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa don amfanin al’umma. Ta yi kira ga ’yan kasuwa da su dage wajen biyan harajinsu na shekara-shekara, wanda kowane mai shago zai biya sau ɗaya kawai. Hajiya Aisha...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana a ranar 6 ga watan nan cewa, shaharar da kallon fina-finai na lokacin hutu na Bikin Bazara na al’ummar Sinawa ya yi manuniya ce a kan dimbin albarkar da kasuwar masarufi ta kasar Sin ke da ita, da karfin kasar na raya tattalin arziki, da kuma kyakkyawar makomar bunkasar tattalin arzikin kasar ta Sin. Saboda haka, kasar Sin tana lale marhabin da baki daga daukacin fadin duniya su zo su ga kyawawan al’adun Sinawa tare da more wa abin. Kididdiga ta nuna cewa, ya zuwa ran 5 ga watan Fabrairu, adadin kudin da aka samu na tikitin kallon fina-finai a lokacin hutun Bikin Bazarar, ya zarce Yuan...
    Yayin da ake fuskantar matakan cin zarafi daga wata kasa daya tilo a duniya, kasar Sin ta lashi takobin daukar kwararan matakai don kare hakkoki da muradunta, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, He Yongqian ta bayyana a yau Alhamis. Mai magana da yawun ma’aikatar ta fada a wani taron manema labarai da aka gudanar cewa, kakaba karin haraji da Amurka ta yi ita kadai, ta yi matukar saba wa ka’idojin kungiyar kasuwanci ta duniya, wato WTO, wanda ke nuni baro-baro a fili da ra’ayi na kashin kai da gicciye kariyar ciniki. Don haka, a cewar jami’ar ma’aikatar, yunkurin na Amurka ya yi matukar kawo cikas ga tsarin gudanar da ciniki a tsakanin bangarori daban-daban,...
    Ƙungiyar Malamai ta Najeriya NUT reshen Jihar Ebonyi ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ƙananan hukumomi bakwai na jihar sakamakon rashin biyan albashin watanni. Yankunan da abin ya shafa sun haɗa da: Ebonyi, Edda, Ezza South, Ezza North, Ivo, Ishielu da Ƙaramar Hukumar Ohaukwu. Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa Ƙungiyar ta koka kan rashin biyan albashin sama da watanni uku ga malaman da ke Ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar, Bassey Asuquo kuma aka rabawa manema labarai a Abakiliki babban birnin jihar a ranar Alhamis. Sanarwar...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kudirin kasafin kudin shekarar 2025 daga naira tiriliyan 49.7 zuwa naira tiriliyan 54.2, yayin da majalisar dokokin kasar ke kokarin ganin an zartar da shi kafin karshen wata. Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da karin kasafin ta hanyar wasiku daban-daban da shugaba Tinubu ya aikewa majalisar dattawa da ta wakilai. A cikin wasikar da aka karanta yayin zaman majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya ce an sami  karin kudin ne sakamakon karin kudaden shigar da hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta samu na Naira tiriliyan 1.4, yayin da hukumar hana fasakwabri  ta kasa ta tara Naira tiriliyan 1.2, da kuma Naira tiriliyan 1.8 da wasu hukumomin gwamnati suka tara. A don...
    Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Tsiga da ke karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda suka yi garkuwa da tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yi wa kasa hidima  NYSC, Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutum takwas. Majiya mai tushe ta bayyana hakan ga gidan rediyon Najeriya a wata hira da manema labarai, yayin da ‘yan sanda ba su tabbatar da faruwar lamarin ba. Wani shaidan gani da ido ya bayyana yadda gungun  ‘yan bindigan  suka afkawa al’ummar a kan babura da misalin karfe sha biyu na dare. “Da misalin karfe 12 na dare ne ‘yan bindigar suka shigo garin na tsiga a bisa babura, inda suka rika harbi a sararin samaniya,...
    Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025. Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria. Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya yi addu’ar Allah ya bai iyalan hakurin rashin sa,kuma ya sa a rinka tunawa da kyawawan dabi’un sa na taimakawa marasa karfi da kuma Dora al’umma akan turbar kasuwanci. Ya kuma roki Allah da ya sanya shi a aljannar firdausi. Da ya ke jawabi a masadin iyalan,Alhaji Hassan Abdulwahab ya yi bayanin cewa marigayi Albabello ya sadaukar da rayuwar sa ce wajen hidimtawa al’umma. Cikin...
    Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
    Wata gobara da ta tashi a Ƙauyen Zago da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta a Jihar Kano, ta ƙone gidaje, amfanin gona, da dabbobi, lamarin da ya janyo wa mazauna ƙauyen asara mai tarin yawa. Gobarar, ta fara ne da safiyar ranar Laraba, inda ta ƙone gidaje da dama tare da lalata hatsi da sauran amfanin gona. An yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar NYSC Janar Tsiga Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai Har ila yau, ta kashe shanu da sauran dabbobi mallakin mazauna ƙauyen. Wasu daga cikin mazauna ƙauyen, Hayyo Zago da Abdulrahman Zago, sun ce gobarar ta ci gaba da ci har zuwa rana kafin jami’an kashe gobara su iss, inda suka yi nasarar...
    An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron. DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta. An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata...
    Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).   Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji.   Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa.   “Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan rashi, Allah ya sa wannan ya zama na karshe a cikin irin wannan mummunan lamari a cikin al’ummarmu,” inji...
    Kwanan baya, kasar Amurka ta sanar da kara harajin kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar, tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl. Bayan haka, nan take kasar Sin ta sanar da daukar matakan mayar da martani a kan karin harajin Amurka domin kare hakki da moriyarta yadda ya kamata. Saan nan, a ranar 4 ga wata, Sin ta gabatar da cewa, tun daga ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 2025, za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka. A sai daya kuma, kasar Sin ta shigar da kara kan matakan da Amurka ta dauka na karin haraji a...
    Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe. Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya. Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku...
    “Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in ji sanarwar. Tabbas! abin da manoman suka fada gaskiya ne, domin ko a shekarar 2018, karin harajin da Amurka ta kakkaba a kan kayayyakin kasar Sin, ya janyo kasar ta Sin wadda a baya ita ce ta fi shigo da wake na Amurka, ta sanya karin harajin kashi 25 cikin 100 na ramuwar gayya kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa. Kuma a yanzu ma, Sin...
    An Samu Yuan Biliyan 9.51 Daga Sayen Tikitin Kallon Fina-Finai A Lokacin Hutun Bikin Bazara A Kasar Sin
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji. Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025. Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya  Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn “Shugaban ƙasa na cewa yaushe matsalar tsaro za ta ƙare, saboda lokacin da ya kamata ta ƙare ya yi. “A wani zama da muka yi da shi da shugabannin hafsoshin tsaron, an tattauna sosai, kuma shugaban ya ce su faɗa masa yaushe matsalar za ta ƙare, suka ce da yardar Allah zuwa ƙarshen shekarar nan,” in ji shi....
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci a ƙara adadin kasafin kuɗin shekarar 2025 daga Naira tiriliyan 49.7 zuwa Naira tiriliyan 54.2. Wannan buƙata na ckkin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Laraba. Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana A baya, Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki kasafin Naira tiriliyan 49.7 a ranar 18 ga watan Disamba. 2024. Sai dai a cikin wasiƙarsa, ya bayyana cewa ƙarin da aka yi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga da hukumomin gwamnati suka tara. Wannna ya haɗa da Naira tiriliyan 1.4 da Hukumar Tara Haraji ta...
    Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU). A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin...
    Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU). A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin...
    A yayin da farashin buhu daya na danyar citta da ke a matsayin iri ya yi tashin gwauron zabon da ba a taɓa ganin irin sa ba, inda ake sayar da shi a kan Naira 210,000 kowane buhu, shi kuwa busasshen buhun citta ana sayar da shi ne daga Naira dubu 500,000 zuwa Naira 550,000 a yankin Kudancin Jihar Kaduna da aka fi noman ta a Nijeriya. Hakan ba ya rasa nasaba da matsalar kwayoyin cutar da suka lahanta mafi yawan cittar da aka noma a 2024, wanda ya yi sanadiyyar karancin irin cittan da kuma hauhawar farashin taki da magunguna da sauran ayyukan noman cittar. Hausawa sun yi bikin cika shekara 153 da zama a garin Owerri DAGA LARABA:...
    Jaridar Politico ta buga wani rahoton dake cewa sojojin kasar Ukiraniya suna fuskantar matsin lamba mai yawa, da kuma rashin kwararrun mayaka. Wannan matsin lambar da sojojin kasar suke fuskanta ya sa ana tunanin mayar da sojojin sama zuwa na kasa da tura su filin daga. Har ila yau jaridar ta ambaci yadda sojojin da suke guduwa daga filin yaki suna karuwa. Jaridar ta kuma kara da cewa; Babban hafsan hafsoshin kasar ta Ukiraniya ya bayar da umarnin a dauki sojojin sama 5000 a mayar da su na kasa. Da akwai tsoron cewa kasar ta Ukiraniya tana rashin kwararrun sojojinta, da ba za ta iya maye gurbinsu a cikin sauki ba idan har aka tura su zuwa filin daga. A...
    Rahotanni  sun ambaci cewa bayan ficewar sojan Faransa na karshe daga sansanin Abaci dake gabacin kasar Chadi,kasar Turkiya tana shirin maye gurbinta. Wata majiyar kasar Turkiya ta shaidawa wata kafar labaru ta Afirka cewa, Ankara tana shirin girke jiragen yaki marasa matuki a cikin sansanin dake kan iyaka da kasar Libya akokarin da take yi na cike gurbin da Faransa ta bari, da zummar tabbatar da kanta a cikin wanann yankin na Afirka. Gwamnatin Chadi ta bai wa Turkiya sansanin na Abaci a karkashin yarjejeniyar da kasashen biyu su ka cimmawa a tsakiyar watan da ya gabata,bayan doguwar tattaunawa da aka yi a tsakanin jami’an gwmanatocin kasashen biyu. Haka nan kuma rahoton ya ce, kasar Turkiya ta bai wa gwamnatin...
    Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025.   Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
    Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa.   An tsare Iyalin har tsawon kwanaki 60 a tsakanin dajin Buruku da Sabo Birni.   Da yake tabbatar da rawar da ya taka a wannan aika-aika, Haruna ya ce, “Ni manomi ne kuma dan banga. Gaskiya ni ne na kai ‘yan bindiga gidan Alhaji Anas. Anas dana ne – dan yayata. Na san daya daga cikin ‘yan fashin da ya ce in nuna musu gidan...
    Wasu ma’aurata ’yan kasar Australia da suka yi aure kuma suka sake rabuwa da juna har sau 12 a cikin shekaru 43 da suka gabata, a yanzu ana gudanar da bincike a kan zargin zamba tsakaninsu. ’Yan sanda a birnin Vienna na kasar Australia a halin yanzu suna gudanar da bincike a kan wani lamari mai ban mamaki, inda wasu ma’aurata da suka yi aure sannan suka rabu har sau 12 a tsawon shekaru 43, domin yin amfani da wata doka da ta ba su damar karbar makudan kudade. Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna Ana zargin tsofaffin ma’auratan da laifin kitsa kowace...
    Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar  Ukrain. Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.
    An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara.  Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun. Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan haramtacciyar kasar, Benjamin Netanyahu zuwa birnin Washington na Amurka, ya dauki wata hanya ta musamman, domin ya gwammace ya kaucewa wucewa ta sararin samaniyar kasashe wadanda suka tabbatar da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da sammacin kama Netanyahu idan ya shiga sararin samaniyarsu. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba...
    A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar Sin ta ce za ta kai kara ga kungiyar WTO, gami da daukar matakan da suka wajaba wajen kare moriyarta. A ganin kwararru masu nazarin al’amuran duniya, dalilin da ya sa sabuwar gwamnatin kasar Amurka daukar matakin nan na sanya karin haraji shi ne domin neman tilastawa sauran kasashe su biya kudi, ta yadda kasar Amurka za ta samu damar sassanta matsalar tattalin arziki da...
    Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren  wurin shan shayi da taliya na zamani  a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari.   Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin. Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari.   An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i. Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa,...
    Gwamnatin Tarayya ta sanar das shirye-shiryenta na sake kara kudin wutar lantarki nan da watanni masu zuwa. Ta bayyana cewa ana tsara karin ta yadda zai zo da tallafi ga masu karamin karfi cikin masu amfani da wutar. Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Makamashi, Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan a Babban Taron Shugabannin Lantarki na Kasashen Afirka da ke gudana a Dar es Salaam, hedikwatar kasar Tanzania. A yayin taron ta gabatar wa mahalarta da shirin na Najeriya na kashe Dala biliyan 32 domin inganta wutar lantarki zuwa shekarar 2030. Batun karin na zuwa ne bayan a bara gwamnatin ta yi ninka kudin wuta sau uku ga kwastomomi da ke amfani da Band A. A yanzu kuma kamfanonin rarraba...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara da cewa zai dorawa hatta kayakin da suke shigowa Amurka daga kasashen Turai, nan gaba, sai dai bai sanya lokaci ba. Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa zai dorawa kasar Canada kashi 25% kan dukkan kayakin da suke shigowa kasar. Sai mna Desel, inda zai sanya kashi 10% kacal.
    Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai  rabi da rabi, a wasu wuraren ma dai sai dai kasusuwa. Ya zuwa yanzu dai an sami gawawwakin da sun kai 458 kamar kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu Dr.  Khalil Dakran ya ambata. Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa tana kirdadon cewa za a iya samun gawawwakin da suke tsakanin 4000, zuwa 5000 a karkashin baraguzai a fadin Falasdinu.
    Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Ukraine da aka dakatar a yakin da ake yi da Rasha, suna bukatar a gduanar da su. “Yawancin kasashen dimokuradiyya suna gudanar da zabe a lokacin yakinsu. Ina ganin yana da mahimmanci su yi haka,”in ji Kellogg. Kamfanin dillancin labaran reuters ma ya rawaito wasu jami’an fadar White House sun tattauna batun matsawa...
    Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a taron shugabannin ƙasashen Afrika kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya, inda Nijeriya ta gabatar da shirin dala biliyan 32 na faɗaɗa samar da wuta zuwa shekarar 2030. An Sace Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki 18 A Cikin Kwanaki 6 – TCN Jami’in Kenya: Fasahar Sin Na Ingiza Samar Da Wutar Lantarkin Kenya Ta ce duk da...
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano ya fitar saboda magance barazanar tsaro da yake fuskanta, ya fara aiwatar da dokar hana motoci masu baƙin gilas wato tinted glass shiga harabar asibitin. Mahukuntan asibitin sun bayyana cewa, motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su iya shiga, amma sai an bi ka’idojin tsaro na musamman. Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani A wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na asibitin, Usman Rabiu Mudi ya fitar, ya ce, an kafa dokar hana motocin masu baƙin gilashi shiga ne saboda wasu munanan abubuwan da suka faru. Ya bayyana irin munanan ababen kamar yunƙurin sace mutane...
    Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa. Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci. Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja Marigayi Shehin Malami a Sashen Harshen Larabci na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina, inda a nan ya samu matsayin Farfesa. Ya kasance Shugaban Sashen Larabci (HOD) na Jami’ar na farko tun da aka kirkiro ta a shekarar 2006, inda ya yi wa’adi biyu...
    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za a ci gaba da bada tallafi ga al’umma a dukkan mazabu 30 na ‘yan majalisar dokokin Jihar. Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi ya bada wannan tabbacin a lokacin da yake kaddamar da bada tallafi ga al’ummar karamar hukumar Miga wanda Shugaban majalisar dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya raba fiye da Naira Miliyan 75 ga masu karamin karfi. Malam Umar Namadi, ya  yaba da tsarin bada tallafin ga al’ummar karamar hukumar ta Miga. A cewarsa, tsarin bada wannan tallafi da kakakin majalisar ya yi ya  dace da kudirorin gwamnatin jihar 12. Yana mai nuni da cewar, a kowacce Karamar Hukuma  za a kaddamar da irin wannan tallafi domin bunkasa tattalin arzikin...
    A yau Asabar, bayanai a hukumance sun nuna cewa, fiye da fasinjoji tsakanin yankuna miliyan 304 ne suka yi zirga-zirga a fadin kasar Sin a ranar Juma’a, rana ta hudu ta hutun bikin bazarar bana, yayin da aka samu yawan ziyarce-ziyarcen iyalai wanda ya ingiza yawon shakatawa. Wannan dai shi ne karo na farko na zirga-zirgar bikin bazara na bana, wanda kuma aka fi sani da chunyun, da adadin tafiye-tafiye tsakanin yankuna ya zarce miliyan 300, a cewar wata tawagar ma’aikata ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirga a lokacin chunyun. Adadin tafiye-tafiye ta mota ya karu da kashi 6.9 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, inda ya kai miliyan 288.44...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
    Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man fetur daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita a yammacin wannan Asabar.
    An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu. A cikin wata wasika mai kwanan wata 6 ga Janairu, 2025, Sani Usman DanAbdullo, Esq., Daraktan Gudanarwa da Harkokin Gabaɗaya na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), ya buƙaci Majalisa da ta kare doka da oda, tare da dakatar da abin da ya bayyana a matsayin rashin amfani da ikon zartarwa yadda ya kamata. An aike da ƙorafin ne...
    Kasar Kenya na amfani da damar ci gaban fasahar kasar Sin don kara dogaro da samar da wutar lantarki a kasar. Darektan ma’aikatar kula da harkokin rarraba wutar lantarki ta kasar Joseph Siror ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, ababen more rayuwa a fannin samar da wutar lantakin kasar na kunshe da dimbin kayayyakin aiki daga kamfanonin kasar Sin irin su Huawei da rukunin Yocean. An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa Ƴansanda Za Su Fara Tilasta Yin Insuran Motoci Daga 1 Ga Fabrairu “Sashen wutar lantarki na Kenya ya kuma ci moriyar musayar fasaha da...
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara. Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma...
    Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024. Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024. Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma...
    Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya. Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya. Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan...
    Shugaban ya kara da cewa, a shekarar farko ne ake fara girbe reshensa, sannan kuma bishiyar tasa na daukar tsawon shekara 50 ana amfana da ita. “A shekara, sau biyu ake girbe Inibi, sannan idan aka ajiye ganyensa a kan tebur, yana shafe daga kwana 45 zuwa 50 ba tare da ya lalace ba”, in ji shi. Ya ci gaba da cewa, Allah ya albarkaci Arewacin Nijeriya da kasar nomad a kuma yanayi mai kyau, musamman ma Karamar Hukumar Kudan ta Jihar Kaduna, inda ake iya shuka wannan Iri na Inibi, ya girma; a kuma amfana da shi. Shugaban ya sanar da cewa, kimanin kashi 85 cikin 100 na Inibin da ake nomawa a kasar nan, na fitowa ne daga...
    Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar hankali. Yayin bikin, hukumomin kula da layin dogo na sassan kasar sun kara karfin aiki a wuraren da aka fi amfani da su, da inganta karfin ba da hidimmomin jiragen kasa da tashoshi, da aiwatar da matakan saukakawa jama’a, da kuma kokarin samar wa fasinjoji ingantacciyar hanyar tafiya. Alal misali, reshen Beijing na kamfanin kula da layin dogo na kasar Sin, ya kara tashoshin caji...
    A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen man da sauki daga gun matatun main a Dangote da kuma na MRS. A cewarsa, a yanzu haka ‘ya’yan IPMAN na yin dakon man daga gun wadannan matatun biyu, ba tare da matatun sun yi masu karin farashin man ba, inda ya shawarci sauran ‘ya’yan kungiyar da su je su yi rijista da wadannan matatun, domin su rinka sawo man da sauki.
    Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga jirgin saman Air France da ya dawo da Imam Khumaini gida daga gudun hijira na sama da shekaru 14 wanda ya kai ga kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin bukukuwan al’ummar Iran suna halartar taruka daban-daban har zuwa zagayowar ranar 22 ga watan Bahman wato 10 ga watan Fabrairu, wato ranar tunawa da juyin juya halin Musulunci. Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai...
    “Kamafanin na LNG na kasa, na bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunkasa tattalin azrikin Nijeriya da kuma kara bayar da goyon baya wajen ganin ana fitar da kaya zuwa ketare, kuma zamu tabbatar da cewa, an kara karfafa hadaka a tsakanin Hukumar da Kamfanin.” Inji Dantsoho. “Rarar da Nijeriya ta samu na hada-hada ta kai ta Naira tiriliyan 5.81 wacce ta yi daidai da dala biliyan 3.7, a zango na uku hudu a 2024.” Kamar yadda rukunonin taron bunkasa tattalin arziki na Nijeriya NESGya ruwaito. Rahoton ya sanar da cewa, an samu wannan nasarar ce, biyo bayan amfanin da Tashoshin Hukumar Jiragen Ruwa ta Kasa NPA.
    Wasu sojoji da har yanzu ba a tantance adadinsu ba sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka bayan da wani da ake zargin wani direba da ya bugu cikin barasa ne ya kutsa cikin su a yankin Shomolu da ke Jihar Legas. Lamarin ya faru ne ’yan mintuna kaɗan bayan da sojojin suke kan hanyarsu daga Barikin Myoung da ke yankin Marocco a Shomolu. Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa a Adamawa Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Waɗanda suka samu raunuka suna jinya a asibitin sojojin Nijeriya da ke Yaba, yayin da aka ajiye gawarwakin sojojin da suka rasu a ɗakin ajiye gawa a asibitin. Hedikwatar Runduna ta 81 ta Sojojin Nijeriya,...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a samu a hukumance daga Bektenov, mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya isa kasar Kazakhstan a ranar Alhamis domin halartar taron koli na shugabannin gwamnatoci mambobi a kungiyar tattalin arzikin Eurasia (EAEU) da taron Almaty Digital Summit 2025, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 1 ga Fabrairu. Iran wadda a baya-bayan nan ta samu matsayin mamba mai sanya ido a...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin  kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka  bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis.  Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
    A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
    Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa. Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami. Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar cewa wata shida bayan kammala ba su horo da sauya tunanin tsofaffin mayaƙan, amma har yanzu babu labarin ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya yi tubar muzuru. Shugabar Sashen Daƙile Rikice-rikice Masu Alaƙa da Tsattsauran Ra’ayi (PVEA)  ta Cibiyar, Ambasada Mairo Musa Abbas, ce ta bayyana haka a yayin taron gwamnonin yankin Tafkin Chadi a Maiduguri, Jihar Borno. NAJERIYA...
    Karamar Hukumar Birnin kudu ta jihar Jigawa ta bada tabbacin hada kai da duk wata hukuma ko kamfani dake da muradin cigaban yankin. Shugaban karamar hukumar, Dr. Muhammad Uba Builder ya bada wannan tabbacin lokacin da wakilan rukunin kamfanonin kasar Sin wato China suka ziyarce shi a ofishinsa. Yace karamar hukumar Birnin kudu tana sahun gaba wajen zaman lafiya da karbar baki a fadin jihar. Mista Sheng ya shaidawa shugaban karamar hukumar niyyar sa ta kafa kamfanin sarrafa takin zamani a yankin domin bunkasa aikin gona. Yana mai cewar zai samar da kamfanin yin kujeru da gado da sauran kayayyaki domin bunkasa al’amuran kasuwanci a yankin. Yace zai kuma samar da sinadarin da zai taimakawa manoma wajen samun amfanin gona...
    Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya. Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu. Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje A ranar Talata kuma, shugaban Angola...
    Masarautar Zazzau, ta sanar da rasuwar Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro. Marigayin, ya rasu ne a Asibitin Gambo Sawaba lokacin da ya halarci taro a asibitin. Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a Tiktok Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Masarautar, ta bayyana cewa za a yi jana’izarsa a gidansa da ke Rimin Doko, Unguwar Kaura, cikin Birnin Zariya.   Cikakken bayani na tafe…
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi da ‘yan bindiga.   “Dole ne in yaba wa sojoji, DSS, da ‘yan sanda, musamman ma Hukumar Tsaro Ta Farin Kaya, bisa nasarar aiwatar da wannan gagarumin kame.   “Ina so in jaddada cewa waɗannan nasarori da aka samu tare da wasu na daƙile ‘yan bindiga a jihar, sun samo asali ne daga haɗin kai da goyon bayan da gwamnatin jihar Zamfara ke baiwa ɗaukacin...
    Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu. A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji. A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
    An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce, shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed al-Sharaa (al-Jolani) ya gabatar da jawabi na samun nasara bayan ganawa da shugabannin bangarorin soja a birnin Damascus fadar mulkin kasar, a gaban dandazon bangarori da dakarun Siriya. A yayin jawabinsa na nasara, Al-Sharaa ya ce: A yau kasar Siriya tana bukata abubuwa fiye da kowane lokaci, yana cewa, kamar yadda suka kuduri aniyar ‘yantar da kasar a baya, wajibi...
    Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
    Hukumar Alhazan Jihar Kaduna ta Kaddamar da shirin bada horo da fadakarwa ga maniyatan bana Jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa an gabatar da wannan bitar ko horon ne a cibiyar hukumar alhazai ta jihar Kaduna da ke unguwar Dogarawa a karamar Hukumar Sabon Garin Zaria. Shugaban hukumar na jihar Kaduna Malam Salihu Abubakar yace bitar wani jigo ne ga kokarin da ake wajen ilmantar da maniyata yadda zasu sauke farali salun alun. Za a fadakar da maniyatan game dukkanin abubuwan da suka shafi aikin hajji domin fuskantar kowane irin kalubalen da zai taso lokacin aikin hajji mai zuwa. Malam Abubakar ya roki mabiyatan su kammala biyan kudin aikin bana kafin cikar wa’adin da...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake  gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki. Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba. Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin. A ranar Litinin din da ta gabata...
    Bikin bazara shi ne biki mafi dadewa da muhimmanci a bukukuwan gargajiya na Sin. Kuma bikin na ci gaba da kara bazuwa da samun karbuwa a fadin duniya. A kwanakin baya-bayan nan, kasashe da hukumomin kasa da kasa da dama sun gudanar da shirye-shirye da nune-nunen dake da alaka da bikin bazara, kuma jama’a a fadin duniya sun hadu domin a dama da su cikin bikin murnar sabuwar shekarar ta Sin. A wannan lokaci, 1 bisa 5 na al’ummar duniya ne ke murnar bikin ta mabanbantan hanyoyi, lamarin da ya mayar da bikin bazara zuwa wata al’adar gargajiya ta duniya tare da inganta fahimta da abota tsakanin jama’ar dukkan kasashe. Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025...
    A ɗaya bangaren, sojoji sun tabbatar da cewa suna ci gaba da neman Bello Turji, wanda ke jagorantar hare-haren ‘yan bindiga a yankin. Turji ya tsere daga maɓoyarsa, amma jami’an tsaro sun ce ba za su daina nemansa ba har sai an kama shi. Sojojin sun tabbatar da cewa suna ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya a yankunan da ‘yan bindiga suka addaba.
    Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama hari a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC). An bayar da rahoton cewa, fusatattun masu zanga-zangar sun kai wa ofisoshin jakadancin Amurka, Faransa, Belgium, Rwanda, Uganda, Kenya da Afirka ta Kudu hari. Masu zanga-zangar dai na neman hadin kan kasashen waje da yunkurin kasa da kasa na shiga tsakani na soji da kuma dakatar da ‘yan tawayen M23 da ke ci gaba da mamaye wasu sassan yankin gabashi. ‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa amma masu zanga-zangar sun samu damar shiga sassan harabar, inda suka yi banka wuta. Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi da kungiyar ta M23 ya yi Kamari a baya bayan...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna. Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi hare-hare. Sojoji sun ƙwato tarin makamai a Zamfara Tankar mai ta sake fashewa a Neja Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja a ranar Talatar nan, mai magana da yawun rundunar, Benneth Igweh, ya ce sun samu nasarar ce ta hanyar bayanan sirri, inda suka cafke wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Igweh ya bayyana...