2025-03-30@23:24:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 999
«Allah Ya ba shi»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saïd Iravani, ya bayyana cewa kalaman na Trump na tada hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD. Trump ya ce zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Iran maimakon “harba mata bam fiye da kima,” a wata hira da manema labarai a ranar Asabar. “Na fi son kulla yarjejeniya da ba za ta cutar...
Wakilin LEADERSHIP Hausa Ya Zama Shugaban Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai A Kebbi
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar, inda ya jadadda cewar, Allah SWT ya azurta wannan Yanki na Tafkin Chadi da dimbin filayen noma wanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, na iya ba da gudummawa sosai wajen samar da abinci a yankin har ma da yankuna makwabta. Zulum ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin yankin da abokan haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin kafa gonakin noman...

Jaridar Telegraph Ta Ce; Shugabannin Sojojin Iran Sun Bukaci Jagora Da Ya Soke Fatawar Haramci Kera Makamin Nukiliya
Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin mallakar makaman nukiliya da ya fitar da fatawa kanta a farkon takaddamar Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Jaridar ta ruwaito a cikin wani rahoton da wakilinta na musamman Akhtar Muhammad Makoy ya fitar cewa: Manyan jagororin sojojin Iran sun ce dole ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soke fatawar da ta haramta kera makaman nukiliya matukar gwamnatin Iran na son ci gaba...
Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
Duk da haka, da alama cewa, waɗannan binciken ƙila ba su da isasshen ikon gano bindigogin da suka ɓace. A yanzu haka dai, kwamitin majalisar dattawa yana zaune a Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ba da fifiko kan harkokin tsaro a jihar Zamfara, kuma ta ɗauki matakin da ya dace tun farko cewa sulhu da ‘yan bindiga ba komai ba ne illa ‘je ka na yi ka’. “A cikin hirarraki da manema labarai daban-daban, gwamnan ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta yo sulhu da ‘yan bindigar da ke addabar jihar ba. “Ya kamata a bayyana...

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Tafida, ya bayyana godiyar Gwamna Nasir Idris ga Sakatarorin kan irin gudunmuwar da suka bayar ga inganta bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi da kuma goyon baya ga gwamnatinsa a kan jagorancin al’ummar jihar. Daga karshe, Gwamnan ya gode wa Sakatarorin kan irin yadda suka sadaukar da kansu wajen kawo cigaba a bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi 21 na fadin jihar tare da yi musu fatan alkairi a rayuwarsu ta gaba.
ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN ya ce wannan sabon tsari zai ƙarfafa shigar da sabbin ATM a faɗin ƙasa tare da tabbatar da cewa bankuna suna cajin kuɗin da ya dace.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban kasar ta Amurka wanda yake Magana da ‘yan jarida a ofis dinsa dake fadar White House, ya sake jaddada tsohuwar barazanar da ya yi tun kafin a rantsar da shi, na ce wa zai bude kofofin jahannama idan ba a mayar da fursunonin ba daga Gaza.” Donald Trump ya kara da cewa, ya yi Magana da Benjamin Netanyahu akan wa’adin na karshe a ranar Asabar...
Ɗan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC
Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300. Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki. Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama. Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero Gwamnan Zamfara ya...
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci shi ne kasantuwar kasa ta taka rawar al’umma da kyakkyawar hadin kai. Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa a jawabin da ya gabatar a karshen jerin gwanon na tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Tehran: Ba za su taba mika wuya ga kasashen waje ba. Ko da yake Iran bata neman yaki, amma tun ranar farko makiya suke...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata rana. Trump ya kara da cewa a yayin zantawarsa da Tashar talabijin ta Fox News; Suna da kasa mai kimar gaske mai dauke da ma’adanai na musamman da man fetur da kuma iskar gas, da sauran abubuwa. Trump ya ci gaba da cewa: Yana son dukiyarsu ta kasance cikin aminci, domin suna kashe daruruwan biliyoyin dalolia cikin kasar. Ya karkare furucinsa da cewa; Za su...

Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Murkushe Falasdinawa A Birnin Tulkaram Da Ke Gabar Yammacin Kogin Jordan
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere, a daidai lokacin da sojoji ke ci gaba da barnata kayayyakin more rayuwa da kadarorin jama’a da kuma kame jama’a gami da tilastawa dubban mazauna sansanonin biyu gudun hijira. Sojojin mamayar suna ci gaba da killace sansanonin Tulkaram da Nourul Shams, sannan kuma suna kara yawan sintirin motocinsu da na tankokin yakinsu da kuma sintiri da kafa a yankuna da unguwannin su, a daidai lokacin...
Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya takunkumi har sai ta dawo kan tsarin dimokiradiyya. Maganganun Wilson, wanda ya shahara da kare matakan muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma tsantsar kiyayya ga kungiyoyin gwagwarmaya da dukkan gwamnatocin Larabawa da na Musulunci da suka ki amincewa da Shirin daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ya fuskanci mayar da martani mai yawa a tsakanin ‘yan siyasar Tunisiya da masu fafutuka kare hakkokin dan Adama,...
Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna. Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai. Wannan sabon samfurin yana da Faisal kamar fitilun, da hasken rana mai iya buɗewa, da tayoyin 17-inch alloy. Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza. Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku makiya sun gaza wajen cika yarjejeniyar da suka cimma’’. Hamas ta ce ‘’sakin karin wasu yahudawa na ranar Asabar 25 ga wata an jingine shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran makiya su mutunta yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata. Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar ta Hamas inda a wata sanarwa da ministan tsaron kasar ya...
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu. Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado da Gabas Ta Tsakiya’’ Ya kara da cewa za a iya samun wurare daban-daban har guda shida don Falasdinawa su zauna a wajen zirin Gaza. Ya kuma ce za’a gina wa Falasdinawa gidaje masu kyau da inganci nesa da wajen da suke, saidai bai bayyana takamaiman wuri ba. A wani labarin kuma Donald Trump ya fada a ranar Litinin din nan cewa cewa “watakila” zai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
Kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin, ya ce jarin manyan kadarori da kasar ta zuba a bangaren layin dogo ya kai yuan biliyan 43.9, kwatankwacin dala biliyan 6.12, a watan Janairun bana. A cewar kamfanin, adadin ya karu da kaso 3.7 bisa dari idan aka kwatantan da makamancin lokacin a bara. A wannan lokaci, an gudanar da manyan ayyuka, ciki har inganta layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen Chengdu da Chongqing. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana kayayyaki na ci gaba da samun bunkasuwa. Adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin ya kai kashi 52.5%, a watan Janairun da ya wuce, wanda ya karu da kashi 1.9% bisa na watan Disamban da ya gabata, adadin da ya kai koli a cikin watanni 10 da suka gabata. Sakamakon manufofin tabbatar da tattalin arziki da ingiza bunkasuwa, da ma yadda aka koma aiki bayan hutun...
’Yan bindiga sun kashe wani fasto, Rabaran Bala Galadima yayin harin da suka kai garin Lubo da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma yi fashin kuɗi har Naira dubu 300 a yayin harin da suka kai cikin dare wayewar gari Lahadi. Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan, waɗanda sun kai takwas, sun kai farmakin ne da misalin karfe 1 zuwa 3 na dare, inda suka firgita jama’a da harbe-harbe kafin su kutsa cikin gidan wani mutum mai suna Musa Puma. Majiyar ta ce maharan sun rutsa matar gidan da bindiga inda suka karbi kuɗi naira dubu dari 300 tare da yin garkuwa da ɗaya daga cikin ’ya’yansu da kuma...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma. A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a nan birnin Tehran a safiyar yau Litinin. Ya ce: Halin da sojojin JMI suke ciki yafi na ko wani lokacin kyau, don haka a shirye suke su gudanar da ayyukansu a duk lokacinda bukatar haka ta taso. Dangane da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kuma, Janar Bakiri ya bayyana cewa, jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul...
Yanzu-Yanzu: Ƴan Bindiga Sun Sace Iyali 3 A Filato

Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace
Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar sa kuma tana ci gaba da taimaka mata, har’ila yau yana da yakini Iran zata ci gaba da taimakawa kungiyar Hamas har zuwa nasara. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta watsa jawabin Al-Hay kai tsaye daga birnin Tehran a safiyar yau litinin, inda ya yi Jawabi a dandalin Azadi dake tsakiyar birnin Tehran. Yace, farmakin ‘waadu Sadik na daya da na biyu duk...
Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin kasar Windhoek na kimani makonni 3 amma rai yayi halinsa a daren Asabar da ta gabata ya na dan shekara 95. Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africanews’ ya bayyana cewa kasar Namibia ta sami yencin kanta ne daga hannun gwamnatin wariya ta Afirka ta kudu a shekara 1990. Sannan Nujoma ya zama shugaban kasar na farko na tsawon shekaru 15. Sannan aka zabi shugaba mai...
Duk da cewa, cikakken bayani kan wannan ziyara bai fito fili ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto, LEADERSHIP ta tattaro cewa, ganawar ba za ta rasa nasaba da burin Atiku na tsayawa takarar shugabancin Nijeriya ba a zaben 2027 mai zuwa. Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, manyan ‘yan siyasar ba su kammala ganawar ba.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya. Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar. “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game da tallafin da ya ke bayarwa a jihar mu. Mun jingina da manufofin Bankin Duniya wajen inganta rayuwar al’ummar mu kawar da talauci da ci gaban ayyukan inganta rayuwa. “Muna sane da ƙalubalen da muka fuskanta, wanda ya shafi gudanar da ayyukan ci gaba a jihar Zamfara, musamman waɗanda suka samu matsala wajen aiwatarwa, sakamakon yanayin da aka shiga. Amma, lallai babu shakka muna...
Gwamna Inuwa Yahaya, ya kuma umarci hukumomin tsaro da su bi sawun waɗanda suka aikata wannan aika-aika domin kamu su, kana ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da cocin ECWA, da ɗaukacin al’ummar Kirista, yana mai addu’a ga mamacin.
Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar. Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa. Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi wannan aika-aika. Shaidan wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya yi zargin wata manufar siyasa ce ta sa ’yan daban suka cinna wa gine-ginen wuta. Ya bayyana damuwa kan yawaitar irin wannan aika-aika a ’yan kwanakin nan. Kokarinmu ma ji daga kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Aneneh, bai yi nasara ba, saboda mun kira ta a waya ba ta shiga ba. ’Yan...
An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano. An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka. Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka. Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka. ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi...
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
“Zaben Alhaji Ibrahim Ibn Umar El-Kanemi, a matsayin sabon Shehun Dikwa, an gudanar da shi cikin lumana da hadin kai wanda sarakunan masarautar suka taka rawar gani wajen zakulo wanda ya dace,” in ji Zulum. Ya bukaci sarkin da ya yi ba da jagoranci daidai da irin kalubalen zamani, yana mai jaddada rawar da masarautar ke takawa wajen farfado da Borno daga shekaru masu yawa na rashin tsaro.
’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun buƙaci al’umma su kawo musu rahoton duk wanda aka ga yana sana’ar bola-jari a cikin gari. Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Disu Olatunji, ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Tsaro ta Babban Birnin Tarayya wanda Minista Ezenwo Nyesom Wike ya jagoranta. Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Janairu, 2025 ne Hukumar Babban Birnin Tarayya ta haramta ayyukan ’yan bola-jari a cikin faɗin birnin. Umarnin ya taƙaita ayyukansu ga kan juji da ke ya yankunan da suke wajen birnin. A lokacin zaman ne aka dakatar da ayyukan ’yan gwangwan na tsawon makonni biyu, saboda zargin alaƙarsu da ’yan bola-jari. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizanin tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja, inda ke da mawadata da kuma matalauta. A tsakanin al’umma kuma akwai ajin mutane masu matsakaicin samu waɗanda ake kira “Middle Class”. Akan sanya mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kuɗin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma. Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa. NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’...
Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...

Ministan Mai Na Iran Ya Ce: Hana Iran Fitar Da Man Fetur Zuwa Kasuwannin Duniya Mafarki Ne Na Shugaban Amurka
Siyasar tsananata matsin lamba kan Iran ta gaza cimma buri kuma hana fitar da man da Iran ke fitarwa mafarki ne da ba zai tabbata ba Ministan mai na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana matsayar matsin lamba da Amurka ke yi kan fitar da man kasar Iran a matsayin siyasa ta nuna gazawa, yana mai cewa: Hana fitar da man fetur din Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa wajen kasar, mafarki ne da ba zai taba wanzuwa ba. Ministan mai na Iran Mohsen Paknejad a matsayin mayar da martani ga furucin Trump ta sake dawo da tsananta siyasar matsin lamba da nufin gurgunta harkar tattalin arzikin Iran ta hanyar hana ta fitar da man fetur, a jiya Lahadi ya bayyana...

Kwamnadan Rundunar Sojin Ruwan IRGC Ya Ce: Suna Iya Rufe Mashigar Hormuz Amma Ba Za Yi Hakan Ba Yanzu
Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Za su iya rufe mashigar Hormuz, amma ba za yi hakan a yanzu ba Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Reza Tangsiri ya yi bayani kan irin fitattun abubuwan da jirgin ruwan da Iran ta kera mai suna Shahid Bahman Baqiri, inda ya ce; Wannan jirgi shi ne nau’i daya tilo saboda babu wata kasa a yankin yammacin Asiya da ke da makamancinsa. Birgediya Janar Tangsiri ya bayyana a cikin shirin ”Labarin juyin juya hali” a tashar Al-Alam cewa: Bayan sanarwar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar dangane...

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...

Sharhin Bayan Labarai “Yadda JMI Ta bunkasa Bangaren Gine-Gine Da Masana’antu Da Kamfanonin Tare Da Fasahar Cikin Gida”
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta. Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979, daya daga cikin bangarorin da aka sami gagarumin ci gaba a cikinsa shi ne, bunkasa sana’ar gine –gine da kuma samar da masana’antu, wanda ya kai ga kasar ta kai ga wadata a wannan bangaren, wani abu daga kasashen waje, sai abunda ba za’a rasaba. Har’ila yau wannan ya wadanar da mutane da dama a kasar. Kafin haka idan mun dubi...
Wani babban jami’in Ƴansanda, ASP Shafi’u Bawa, na rundunar 61 Police Mobile Force (PMF), an tsinci gawarsa a dakinsa a garin Kontagora, Jihar Neja, a ranar Asabar, bayan da ake zargin ya kashe kansa. Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano gawar ASP Bawa rataye a saman silin ɗin ɗakinsa. Mahaifinsa, Malam Usman Bawa, ne ya fara gano lamarin kafin ya kai rahoto ofishin ‘yansanda na Kontagora. Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta Abin Fashewa Ya Hallaka Mutum Guda, Ya Jikkata 6 A Neja Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa: “A ranar 8/2/2025 da misalin ƙarfe 2 na rana, an samu rahoton cewa ASP Shafi’u Bawa...
Shugaban kasar Namibia dake kan gado Nangolo Mbumba ne ya sanar a yau Lahadi cewa, jagoran samun ‘yacin kasar Sam Nujoma ya rasu a jiya Asabar da dare, bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin babban birnin kasar Windhoek. Sanarwar da shugaban kasar ta Namibia mai ci a yanzu, ya fitar ya bayyana mutuwar Nujoma da cewa; ginshikin da aka kafa kasar akansa ya girgiza. Sam Nujoma ya jagoranci fadan sama wa kasar ta Namibia ‘yanci daga mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta kudu, a shekarar 1990, sannan kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 15. A lokacin da yake a raye, al’ummar kasar ta Namibia suna girmama shi matuka a matsayin wanda ya jagoranci fadan...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya yi kira da a kafa kawancen duniya da dukkanin kasashen musulmi za su shiga ciki, domin taimakawa mutanen Gaza, da sake gina yanki, tare da cewa, kasashen musulmi kadai za su iya sake gina yankin na Gaza tare da dawo da rayuwa a cikinsa. A ganawar da ya yi da mambobin majalisar jagoranci ta kungiyar Hamas, anan Tehran ya yi jinjina ga shahidan kawancen gwagwarmaya, ya kuma yi murna akan nasarar da ‘yan gwgawarmaya su ka samu akan ‘yan sahayoniya. Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Nasarorin da mutanen na Gaza su ka samu, sun hana makiya ‘yan sahayoniya cimma manufofin da su ka shata, duk da cewa adadin shahidan da aka...
“Da sauri jami’an ‘yansanda suka isa wurin, inda suka gano wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Promise Eze, ‘yar Jihar Ebonyi, daure a wata karamar kujera an rufe bakinta da filasta. An same ta a sume kuma cikin damuwa. Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin gaggawa, inda suka kubutar da ita daga hannun wadanda aka yi garkuwa da su, sannan suka garzaya da ita asibitin gundumar Wuse, inda ta farfado,” in ji sanarwar. Adeh ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa Eze ta leka otal din a safiyar ranar 30 ga watan Janairu tare da Okoro, wanda ta hadu da shi ta intanet. A cewarta, wanda ake zargin ya gabatar da kansa a matsayin ma’aikacin kamfanin...
Wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya ce: Juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon samfuri na hadin kan al’umma Ayatullah Mojtaba Hosseini, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya bayyana muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi da kuma nauyin da ya rataya a wuyan musulmi na daidaiku da na al’umma dangane da manufofin juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon salo na hadin kan al’ummar musulmi. A jawabin da ya gabatar na zagayowar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran da aka gudanar a tsohon gidan da Imam Khumaini (r.a) da ya zaune a birnin Najaf, Ayatullah Husaini ya jaddada muhimmancin hadin...
Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da gwamnatin mamayar Isra’ila a yankin. Jaridar ta bayyana cewa: Runduna ta 162 ta sojojin mamayar ta sake matsawa zuwa kusa da kan iyaka da kuma janyewa daga yankin Netzarim na nufin cewa, babu sojojin mamayar Isra’ila a arewacin...
Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata. Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da...
Ga wasu manyan ‘yan kwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, wadanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu baki daya ko wani daga cikin iyayen ‘yan Nijeriya ne. Jamal Musiala (Jamus) Matashin dan wasa Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen dan kwallon kasar Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta Jamus din kuma yana cikin matasan ‘yan kwallon da suke tashe a duniya a yanzu saboda ba za ka lissafa matasan ‘yan wasa guda biyar ba a duniya ba tare da ka saka sunansa ba. An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin can Nijeriya ne, wanda ya...
Iran ta ce a shirye take ta tallafa wa Burkina faso a yakin da take da ta’addanci. Wannan bayyanin ya foto ne bayan wata ganawa tsakanin Firaministan Burkina Faso Rimtalba Jean Emmanuel Ouédraogo da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Burkina Faso, Mista Mojtaba Faghihi a Ouagadougou. Taron dai ya baiwa mutanen biyu damar sake yin nazari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashensu. A cikin wannan yanayi, Iran ta bayyana aniyar ta na tallafawa Burkina Faso, a kokarinta na dakile matsalar rashin tsaro. Tehran, ta bakin jakadanta, ta kuma bayyana sha’awarta kan sauran fannonin hadin gwiwa, kamar su noma, masana’antu, likitanci da al’adu. Ya ce Iran a shirye take ta ba da dukkan goyon bayan da ya dace ga Burkina...

Xi Jinping: Ya Kamata A Sa Kaimi Ga Aiwatar Da Shirin Farfado Da Arewa Maso Gabashin Sin A Dukkan Fannoni A Sabon Zamani
A yau Asabar, 8 ga wannan wata da safe, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kwamitin JKS da gwamnatin lardin Jilin a birnin Changchun dake lardin Jilin. Bayan kammala sauraro, shugaba Xi ya yi jawabi inda ya jaddada cewa, ya kamata hukumomin lardin Jilin su aiwatar da shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin a dukkan fannoni a sabon zamani da kwamitin tsakiya na JKS ya tsara, da tabbatar da tsaron kasar a fannoni 5, da maida hankali ga aikin samun ci gaba mai inganci, da bin tsarin tunanin sabon ci gaba, da bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a dukkan fannoni,...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025. Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5 Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin Jihar Nadin Na Ibrahim zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Febarairun 2025. Sanarwar nadin ta bayyana cewa an zabi, Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar saboda shafe sama da shekaru talatin ya na aikin gwamnati da tarin kwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban...
“Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.

Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin
Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin
Ibrahim Yucel ya shafe shekaru 20 yana zukar taba sosai a lokacin da ya yanke shawarar ci gaba da zuka sosai. Jarabar son kowane irin abu ba shi da kyau, kuma zukar taba tana cikin mafi muni. Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari Barin shan taba yana da matukar wahala, yana bukatar jajircewa da sadaukarwa. Duk da gagarumin kokarin da suke yi, kadan ne kawai na masu zukar sigari suka sami nasarar shawo kan jarabar son da suke yi mata. Kimanin shekara 11 da suka gabata, labarin wani mutum na kokarin daina shan taba ya shahara a talabijin da sauran kafafen yada labarai lokacin da ya saka...
Manchester City ta tsallake rijiya da baya a gidan Orient, bayan ta doke su da ci 2-1, hakan ya sa ta tsallaka zuwa zagaye na biyar na gasar cin kofin FA ranar Asabar. Kamar kullum, Kevin De Bruyne ne ya fitar da kitse daga wuta ana gab-da za a tashi daga wasan. Mai tsaron ragar Manchester City, Stefan Ortega ne ya ci gida tun a minti na 16 da fara wasan, sabon dan wasan City Khusanov ne ya ci kwallonsa ta farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kafin Kevin De Bruyne ya jefa ta biyu. Mutanen Guardiola kuwa su na matsayi na hudu a gasar Firimiya, hakazalika za su hadu da zakarun Turai, Real Madrid a gasar zakarun Turai...
Ga Yadda zaku hada: Da farko za ku samu Tukunya sai ku zuba sukarin a ciki, ku dora shi a wuta ya narke ya yi zafi ya dan tafasa, sai ku kawo lemon tsami guda daya ku matse a ciki sai ku bar shi ya dan dahu sannan ku sauke. Sai ku samu roba me dan girma, ku zuba fulawar a ciki sannan ku kawo Baikin Fauda ita ma ku zuba sai ku zuba dan Gishiri kadan ba da yawa ba sai ku zuba Bota idan kuma ba kuda Bota za ku iya zuba mai ku kwaba da shi, sai ku kwaba sosai ku juya shi ya juyu sosai, sannan ku samu abin murzawa ku yi ta buga shi,...
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Sayyid Aliyul Khaminae yana cewa tsagaita wuta da aka samu bayan wannan lokaci mai tsawo na fafatawa yayi dai-dai. Tawagar shuraa ta Hamas din dai sun hada da shugaban riko na kungiyar Khalil Al-Hayya, shugaban majalisar shoora ta kungiyar Muhammad Ismail Darwish da sauransu. Jagoran ya kara da cewa nasarar da mutanen Gaza suka samu a kan Amurka da kawayenta misdaki nan a...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshiyan ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata jada baya ba, kuma ba zati yi rauni ba saboda takunkuman zaluncin da kasashen yamma suka dorawa kasar. Ya ce kasar tana da arzikin da zata ci gaba da kasancewa a gaba da kasashen da dama a yankin Asiya ta kudu, duk tare da wadannan takunkuman. Tashar talabijin ta Press tv ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a garin Sirjan, daga na kudu masu gabacin lardin Kerman. Inda ya gabatar da kamfanoni da ayyukan jama’a wadanda aka kammala, wadanda suka hada har da sabbin wuraren yawon bude ido da kuma shakatawa. Shugaban y ace, kasar Iran ba zata jada baya ba, sannan makiyan kasar sun...
Firay Ministan HKI Banyamin Natanyahu ya bawa kasar Saudiya Shawara samarwa Falasdinawa kasa daga cikin hamada mai girma da take da shi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Natanyahu yana fadar haka wa wata tashar talabijin ta HH a safiyar yau Asabar. Amma a maida martani ga Natanyahu, dan majalisar dokokin kasar Burtania a jam’iyyar Larbor Afzal Khan yace, wannan shawarar ta Natanyahu tabbaci ne na laifin fitta mutane daga kasarsu da karfi, don kawai ya na son a kwace zirin gaza daga Falasdinawa. Falasdinawa basa bukatan karin kasa suna son yenci ne a kasarsu. Inji dan majalisar dokoki Kim Johnson na jam’iyyar Lebour.. Kafin haka dai sarki Saman bin Abbdul azizi na kasar Saudiya yace ba...

Thomas Bach Ya Bai Wa Cmg Izinin Sarrafa Watsa Labarun Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Milan Ta 2026
Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin mallakin kasar Sin, wato CMG, Shen Haixiong, don bai wa runkunin na CMG damar tsarawa da kuma sarrafa watsa labarun gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Milan da Cortina d’Ampezzo ta shekarar 2026. Shen Haixiong ya ce, gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya da ake shiryawa a birnin Harbin, wata kasaitaciyyar gasa ce ta kasa da kasa da Sin ta shirya bayan...
Wata ‘yar uwa ana auranta aka kira ta ana yi mata nasiha sai ta ce ni dai kun dame ni da na yi hakuri na yi hakuri, tun da yana sona ina son shi kam ai shike nan, wallahi ko shekara daya ba’a yi ba ran nan na kai mata ziyara sai take cewa Amina ashe da ake cewa na yi hakuri nake ganin an dame ni da gaskiyarsu yanzu wallahi har gani nake hakurin da aka ce na yi ma ya yi kadan. To rayuwar aure sai da hakuri, idan muka yi hakurin nan da ake fada in sha Allahu za mu ga nasararsa a gaba, amma idan ba mu yi hakurin nan da ake fada mana ba za...
A bayan nan ne mahukunta a Ƙaramar Hukumar Agege, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙaramar Hukumar Agege, Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi suka kulle babban masallacin Hausawa na garin, biyo bayan wani rikici da ke da alaƙa da na limanci ya ɓarke a masallacin a ranar Juma’a makon jiya. Rikicin na zuwa ne bayan rasuwar babban limamin garin Agege, Shaikh Sharif Habib Abdul-Majid, wanda ya rasu kwanaki biyu gabanin aukuwar lamarin. Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2 An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na zamani, an ga masallata a cikin masallacin suna kai wa junansu duka, wadanda suka haɗar da ɓangarori uku. Waɗanda suka bai wa...
Yadda ake amfani da shi: Za ku dinga shafa zumar a gabanku, ku barta na tsawon mintuna 30, sai ku wanke da ruwan dumi, sannan ku shafa Man Zaitun. Za ku dinga yin haka safe da yamma kafin kwanciya. Sannan ku dinga dafa ‘ya’yan hulba na tsawon mintuna 10 da ruwan da bai wuce kofi daya ba, sai ku dora shi a wuta ya dan tafasa bayan kun sauke shi sai ku tsiyaye shi sai ku sa masa zuma cokali uku, za ki yi wannan hadin shima safe da yamma. Sai kuma maganin kurajen da kaikayin gaba: Kai tsaye ana cewa sanyin mara shi ne yake jawo wannan matsala, amma abin da ya kamata mu sani shi ne...
Madara muhimmin abinci ne da ake bukata domin samun sinadarai masu ginawa da ƙara ƙarfi da lafiyar jiki. Bincike ya nuna cewa mutane biliyan shida ne ke shan madara a duniya, wanda ya sa shan madarar saniya da kiwon dabbobi ya zama wani vangare na rayuwar ɗan adam. Dubban mata Fulani suna samun kuɗaɗen shiga ta hanyar sayar da madara ga ɗaiɗaikun mutane ko jama’a ko ’yan kasuwa, waɗanda suke sha ko sarrafa shi domin amfanin kasuwanci. Lura da muhimmancin madara ga rayuwar ɗan Adam da kuma ƙoƙarin rage haɗarin da ke tattare da shan ta, Hukumar Haɓaka Noma da Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano (KSADP) ta zuba jarin Dala miliyan 8.03 don gina cibiyoyi 100 na tattara madara...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya sha alwashin gyara wa da faɗaɗa sansanin horas da matasan maus yi wa ƙsa hidima (NYSC) na dindindin a jihar. Da yake karɓar babban Daraktan NYSC, Birgediya Janar Yusha’u Ahmed a Maiduguri, Zulum ya ce gwamnatinsa za ta gaggauta gina sansanin dindindin domin karɓar ƙarin ‘yan bautar ƙasa. Ya kuma yaba da gudunmawar da likitoci da malaman kimiyya ke bayarwa a makarantu. Sin Ta Yi Bikin Tunawa Da Wadanda Aka Hallaka Yayin Kisan Kiyashin Birnin Nanjing Tinubu Ya Amince Da Naira Biliyan 80 Domin Sake Gina Madatsar Ruwa Ta Alau Da Ke Borno Shugaban NYSC ya gode wa gwamnatin Borno bisa tallafin da take bai wa ‘yan bautar ƙasa, ciki har da alawus na...
A gasar Serie A 14:03 – Joao Felix (Chelsea – AC Milan) aro Premier League 01:00 – Adel Disasi (Chelsea – Aston Billa) aro- 00:25 – Marshall Munetsi (Reims – Wolbes) ba a fayyace kudin ba. 00:15 – Carlos Alcaraz (Flamengo – Eberton) aro- 00:00 – Nasser Djiga (Red Star Belgrade – Wolbes) ba a fayyace kudin ba. 23:15 – Ben Chilwell (Chelsea – Crystal Palace) aro- 23:10 – Mathys Tel (Bayern Munich – Tottenham) aro – 23:00 – Nico Gonzalez (Porto – Manchester City) £50m 22:50 – Eli Junior Kroupi (FC Lorient – Bournemouth) ba a fayyace kudin ba. 21:32 – Somto Boniface (Chelsea – Ipswich) ba a fayyace kudin ba. 21:32 – Aled Palmer (West Brom –...
Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a kan dokar da za ta rage tallafin da Amurka ke baiwa Afirka ta Kudu, wanda ake ganin bai rasa nasaba da karar Isra’ila da Afrika ta Kudu ta shigar kan kisan gilla a Zirin Gaza da kuma kwace filaye A ranar Juma’a ne fadar White House ta Amurka ta tabbatar da cewa Trump ya rattaba hannu kan wani kudiri na yanke tallafin kudi ga Afirka ta Kudu, saboda rashin amincewarsa da manufofinta na filaye, har ma da batun shigar da kara kan kisan gillar da ta yi a kotun kasa da kasa (ICJ) kan Isra’ila. Gwamnatin Trump ta ba da misali da shari’ar da Afrika ta kudu ta jagoranta kan Isra’ila a...
Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Sun kai ga nasarar cimma matakin cin gashin kai a kere-keren kayayyakin aikin soja Kwamandan rundunar sojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa: Sojojin saman Iran na ma’aikatar tsaro da taimakon sojojin kasar sun cimma mataki dari bisa dari a fagen gudanar da kere-keren kayayyakin da suke bukata a harkar tsaron kasa, kuma dukkanin kayan aikin wannan runduna an inganta su tare da mayar da su saffarin cikin gida. A ranar Juma’a 7 ga watan Fabrairu, Birgediya Janar Wahidi ya sanar a gaban taron kwamandojin sojojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jagoran juyin juya halin Musulunci a wata hira da aka yi da shi ta...
Manyan jami’an kasar Jordan sun gargadi Amurka cewa: Idan ta janyo hargitsi a Jordan, to zai mamaye dukkan kasashen yankin gaba daya Shugaban majalisar dattijan kasar Jordan Faisal Al-Fayez ya jaddada a ranar Juma’a cewa: Ana daukar kasarsa a matsayin ginshikin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa; Duk wani hargitsin da zai iya faruwa a kasar, zai shafi kasashen yankin baki daya, yana mai jaddada cewa: Kasashen yamma, musamman Amurka, suna da cikakkiyar masaniya game da wannan lamari. Al-Fayez ya bayyana cewa, a cikin hirarsa da tashar talabijin ta masarautar Jordan kan manyan kalubale da kasarsa ta fuskanta a baya, amma ta yi galaba a kansu da karfi da kuma tsayin daka, tare da dogaro da...
Kazalka, matsalar ta sanya wasu iyalai da dalibai da dama a kasar yin kokarin jurewa matsin rayuwar da suke ci gaba da fuskanta, wanda hakan yak e kuma kara zamowa, babbar barazana ga rayuwarsu. Bisa fashin baki da rahoton ya yi ya nuna cewa, a shiyoyi shida na kasar, banbancin hauhawan farashin na kayan abincin, ya sha ban ban, inda a yakin Kudu Maso Yamma, lamarin na hauhawan farashin kayan abincin, ya fi yin kamari.
An yabawa Gwamna Uba Sani saboda tsabtace harkokin hajji da kuma naɗa kwararru don jagorantar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna. Shugaban Kungiyar Yan Jaridu ta Kasa reshen Jihar Kaduna, Alhaji AbdulGafaar Alabelewe, ne yayi yabo yayin da jami’an kungiyar suka kai ziyarar ban girma ga hukumar. NUJ ta kuma bayyana naɗin Malam Salihu S. Abubakar a matsayin Shugaban Hukumar a matsayin wanda ya dace da mukami, inda suka jaddada cewa gaskiyarsa da bin doka da na da matukar muhimmanci wajen ci gaban hukumar. Alhaji AbdulGafaar ya ce hukumar ta samu nasarori masu yawa a lokacin hajjin da ya gabata, ciki har da maidawa kowane mahajjaci dala 50 daga kudin hadaya da suka biya a Najeriya. Ya kuma...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau anan birnin Tehran, Hajjatul-Islam Kazim Saddiki, ya bayyana cewa: Trump yana yin baraza da tsoratarwa da cewa zai rage karfin da Iran take da shi a fagen fasahar Nukiliya da kuma matsayin da take da shi a cikin wannan yankin na yammacin Asiya, sai dai kuma ya kamata ya fahimci cewa kamar yadda shugaban da ya gabace shi ya yi kuskuren lissafi, to shi ma haka yake yi.” Limamin na Tehran ya kuma ce,Kamar yadda shugaban Amurka da ya gabaci Trump bai sami nasara akan Iran ba, shi ma haka ba zai cimma manufarsa ba. Hajjtul-Islam Siddiki ya kuma kara da cewa; Bai kamata ace muna kallon cewa ta hanyar abubuwa na zahiri...
Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun yi awon gaba da wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 a hanyar ruwan daga Bonny zuwa Okrika a Jihar Ribas. Sai dai jami’ai a ƙaramar hukumar Bonny ta ce ta kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ceto sauran. Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Shugaban Ƙaramar hukumar Bonny, Hon Anengi Barasua Claude-Wilcox ya ce, an ceto mutanen tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Claude-Wilcox a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Boma Waribor ya fitar a ranar Juma’a, ya ce direban jirgin...
Kasar Sin ta yi watsi tare da nuna kin amincewarta da tsegumin da aka yi mata daga bangaren Amurka, inda sakataren harkokin wajen Amurkar, Marco Rubio ya yi wasu zarge-zarge marasa tushe balle makama a kan kasar ta Sin, yayin da yake ziyara a yankin Latin Amurka da Caribbean. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan a yau Juma’a, inda ya kara da cewa, kalaman marasa tushe daga bangaren Amurka, wadanda suka karkata zuwa tunanin yakin cacar-baka da nuna son zuciya, zarge-zarge ne kawai na yamadidi a kan kasar Sin da aka kitsa da nufin haifar da sabani tsakaninta da kasashen da abin ya shafa na Latin Amurka da Caribbean, wanda kuma hakan tsoma baki...

Xi Jinping Ya Halarci Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Lokacin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9
An kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta nahiyar Asiya karo na 9 a yau 7 ga wata da dare, a birnin Harbin dake lardin Heilongjiang na kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin tare da kaddamar da gasar a hukumance. (Zainab Zhang)
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
“Babban shugaban sojoji da Babban mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro (NSA) suna aiki ba dare ko rana wajen tabbatar da wannan matakin, kamar yadda kuke gani muna sanya kumaji ga dukkanin rundunoni. “Sannan, an janye takunkumin hako ma’adinai a Zamfara, sannan wannan dalilin ne ya sanya muke ganawa a yau domin duba dukkanin bangarorin, inda muke da matsalar tsaro sosai sai mu ga yadda za mu kwato ayyukan,” Badaru ya shaida.
Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A ci gaba da kokarin da rundunar ‘yansandan Jihar Imo ke yi na dakile ayyukan ta’addanci a jihar, jami’an shalkwatar sashen Okigwe tare da hadin gwiwar mazauna unguwar Ogii a ranar 3/02/2025, sun kama wasu mutum uku da aka samu da kokon mutum, kaza da fararen kaya a kan titin Okigwe-Umuahia Edpressigwe. “Mutum ukun da aka kama—Patrick Okoere, Ifeanyichukwu Anyaemeka, da Chukwuemeka Onyekachi 20—ana kan bincike a halin yanzu. Yayin da ake yi masa tambayoyi, Patrick ya bayyana cewa kawun nasa, Osunta Oko, ya nemi ya sayo kokon kan mutum. Ya yi ikirarin cewa ya same shi ne a bakin kogi a kan babbar hanyar Okigwe-Umuahia, yankin da rundunar ke samun labarin sace-sacen mutane....
Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa. “Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe. “Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi. Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci. Taron na yau ya zo daidai da zagayowar kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma taron tunawa da mubaya’a mai dimbin tarihi ga Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 1979. Don haka a safiyar...

Tsohon Ministan Yakin Isra’ila Ya Ce Sune Suka Ba Da Umarnin Kashe Fursunoninsu Da Ake Tsare Da Su A Gaza
Tsohon ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ba da umarnin sojojinsu su kashe fursunoni yahudawa da masu tsaronsu a Gaza Tsohon Ministan tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da aka kora Yoav Gallant a jiya Alhamis ya yi bayani kan matakan da sojojin mamayar Isra’ila suka dauka na tunkarar fursunonin yahudawan sahayoniyya da masu garkuwa da su a Zirin Gaza. A cewar shafin Falestine Today, Gallant ya ce: “Sun ba wa sojojin mamayar Isra’ila umarnin yin amfani da hanyar Hannibal, wato kashe fursunoni ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su tare da masu garkuwa da su a Gaza.” Ya kara da cewa: A jajiberin fara kai farmaki ta kasa kan...
Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi birnin kawanya daga bangarori hudu. A nata bangaren, Ma’aikatar yada labaran Sudan ta zargi bangarorin waje da jagorantar gudanar da fadace-fadacen da ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa ke yi don samun damar cin gajiyar albarkatun kasar, idan ‘yan tawaye suka yi nasara. Rayuwa ta fara inganta a birnin Omdurman kuma kasuwanni sun fara farfadowa, inda jama’a suke komawa ci gaba da harkokinsu na yau...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta haramta yawon dare, ta hanyar takaita zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa 5 na asubahi. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya sanar a ranar Alhamis cewa dokar za ta fara aiki ranar Juma’a, 7 ga Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa an kafa dokar takaita zirga-zirgar ne bayan samun rahotannin barazanar tsaro. Sanarwar ta ce, “takaita zirga-zirgar na da nasaba da karuwar barazanar tsaro da ke fuskantar al’ummar Gombe,” kuma a shirye rundunar take ta shawo kansu. NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya Mutuwar Almajirai: Tinubu ya buƙaci a samar da matakan kare ɗalibai DSP Buhari ya kara da cewa rundunar za...
Rundunar sojin Najeriya ta ce tana aiki kan hanyoyin da za su yaki ‘yan bindiga da sauran masu tada kayar baya ta hanyar amfani da darussan da aka koya a wajen wani bada horo da ya gudana a Sakkwato. Babban Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayyana haka a Sokoto a wajen wani taron karawa juna sani da nufin tattauna sabbin dabarun murkushe ‘yan bindiga da sauran ayyukan tada kayar baya a yankin Arewa maso Yamma, wanda aka gudanar a Runduna ta 8 ta Sojojin Najeriya dake Sokoto. Wanda ya samu wakilcin babban hafsa Manjo Janar Olusegun Samson Abai, ya ce ziyarar wayar da kan ta taso ne domin inganta aikin da ake yi ta hanyar...
Gwamna Sani ya bayyana zargin da kungiyar ta yi a matsayin maras tushe, yana mai jaddada cewa “Mafi yawan ‘yan siyasar da ke irin wadannan kalamai na iya zama suna magana da kansu ne kawai,” in ji shi. “Mun kasance a cikin jam’iyya daya a wani lokaci, kuma dole ne in ce na yi mamakin abin da suka yi.” Ya kara da cewa kawancen ba shi da wata hujjoji ta gaskiya kan ikirarin nasu. “Fito da zarge-zarge ba tare da hujja ba, wani yunkuri ne kawai na kawar da hankulan ‘yan Nijeriya,” in ji gwamnan. “Yawancin wadannan ‘yan siyasa sun rike mukamai a gwamnati kasa da shekaru biyu da suka gabata. Me suka yi a lokacin da suke kan mulki?”...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauye-sauyen shugabanci a jami’o’in gwamnatin tarayya da dama da suka hada da Jami’ar Abuja wadda a yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon. A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya ce a jami’ar Yakubu Gowon, shugaba Tinubu ya rusa majalisar zartarwa gaba daya tare da sauke Farfesa Aisha Sani Maikudi daga mukaminta na shugabar Jami’ar. Sanata Lanre Tejuoso, wanda a halin yanzu shi ne uban Jami’ar Aikin Gona ta Makurdi ne aka nada shi a matsayin Uban Jami’ar Yakubu Gowon. Sanata Joy Emordi, wacce a yanzu ita ce shugabar jami’ar ilimi ta Alvan Ikoku za ta gaje shi a Makurdi....
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci al’ummar Rimin Zakara da ke karamar hukumar Ungogo domin jajantawa iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin asarar rayuka uku tare da jikkata wasu da dama. A ziyarar tasa, Gwamna Yusuf ya gana da iyalan wadanda suka rasu, inda ya jajanta musu tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta dauki nauyin iyalan mutanen uku da suka rasu. Ya kuma ba da umarnin a gaggauta biyan kudaden jinya ga duk wadanda suka jikkata tare da samar da kayan abinci don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa. A cikin nuna jin kai, gwamnan ya bayyana shirin gina sabon masallacin Juma’a a Rimin Zakara a matsayin sadaqatu jariya (dauwamammiyar...
In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...