2025-02-28@13:26:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 92
«ga watan Ramadana»:
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi na kulla huldar tattalin arziki da tsaro da kasashen yammacin da tsakiyar Afirka. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya habarta cewa, hamshakin attajirin nan na Rasha Oleg Deripaska ya halarci tattaunawar da shugabannin biyu suka yi. Kafofin yada labarai sun ambato wani minista a Guinea-Bissau, ya ce, Kamfanin aluminium na Rasha Rusal yana sha’awar gina layin dogo da tashar jiragen ruwa a kasar, da kuma...
Har ila yau yana daga hukuncin shari’a, ba a fara azumi da kokwanto, misali ka kwanta bacci sai ka kudirce a ranka cewa in an bayyana ganin wata ina bacci, zan tashi da azumi. Mun gode Allah, yanzu sabida na’u’rar zamani da wuri ake sanar da ganin wata. Lamarin ganin watan Ramadana abu ne mai sauki, sabida galibin Malamai da Shehunnanmu na kasa da waje baki daya suna kan Hadisin Kuraibu da yake cewa “Kowacce kasa da ganin watanta, misalin kasar: Nijer da Ghana, Mali, Togo da dai sauransu duk suna da Sarkin Musulmi kuma shi zai ayyana ganin watan. Amma kuma, in Nijer suka ga watan Ramadana, Sarkin Musulmin Nijeriya in yaga dama zai iya cewa na ga wata...
Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda 100 na kayan ilimi na musamman; 260 na Kula da Yara da sauransu. Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce wannan wani shiri ne a cikin jerin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi wanda ke nuni da fifikon da take da shi na samar da ilimin boko a jihar. A cewarsa...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lin Jian ne ya jaddada cewa, alakar da take a tsakanin Rasha da China ba ta tasirantuwa da shiga tsakanin wani bangare na uku, sannan kuma ya ce, kokarin da Amurka take yi na haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu ba zai yi nasara ba. A wani taron manema labaru da kakakin ma’aikatar harkokin wajen na China ya gabatar, ya bayar da jawabi akan tambayar da aka yi masa akan maganar da ta fito daga bakin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio cewa; Rasha ta dogara ne China, kuma kasashen biyu za su iya hada kai su yi fada da Amurka. Li Jian ya kuma ce; Ba tare da la’akari da sauye-sauyen da za su...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara. Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi. Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar. Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya ce idan an gan shi, sai a mika bayanan ga Dagaci, Hakimi, Mai Unguwa ko Sarki mafi kusa domin sanarda Mai Alfarma Sarkin Musulmi. Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban wata, yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga daukacin...
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada. An gudanar da rabon kayan ne a ɗakin ajiyar abinci na gwamnatin jihar da ke Bulasa. Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a wajen rabon, ya gode wa gidauniyar bisa tallafin da ta ke bai wa mutanen jihar. Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince...
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.” Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin...
Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu. Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko. Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau. A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana...
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage farashin kayan marmari kamar dankalin Turawa da karas da kukumba da latas da koren tattasai da ake fataucin su daga wasu jihohin Arewa zuwa Kudancin kasa. Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno “Za mu yi ragin ne daidai gwargwado daga cikin ribar da muke samu saboda albarkar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin. A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a kasar, Pezeshkian ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da cewa tana kara habaka, tare da jaddada bukatar gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu, musamman ma cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu. Ya ce, “Iran da Rasha suna da rawar gani da za su iya takawa domin inganta hadin gwiwarsu, kuma mun kuduri aniyar karfafa huldar dake tsakanin Tehran da...
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati. Ya furta haka ne a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa ta shirya a cibiyar bunkasa ma’aikata dake Dutse. Ya jaddada cewa, gaskiya, da rikon amana, su ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari. Barista Salisu Abdu, ya...
Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware. Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da Amurka ta zartas kan rikicin Rasha/Ukrain duk kuwa da kauracewar kasashen Turai kwamitin ya kada kuri’ar amincewa da kudurin na Amurka da nufin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi tsakanin Ukraine da Rasha. Kuri’u 10 ne suka amince da kudurin, sabili da haka babu wanda ya ki, ko da yake kasashen Turai biyar a majalisar – Denmark, Faransa, Girka, Birtaniya da Slovenia – sun zabi su kauracewa zaben. Wannan kudurin dai ya tuna da muhimmin kudurin MDD na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da yin kira da a warware takaddama cikin lumana da samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashen...
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin. Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole. Vladimir Putin ya dage kan cewa tattaunawar da Rasha da Amurka suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi A yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan Adam, musamman mai azumi. Domin sauke shirin, latsa nan

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza a jiya Lahadi. Ya kara da...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...
Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo. Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai. A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani...
Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai fam miliyan (£300m) a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa sannan ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe sama da fam biliyan biyu (£2bn), ko kuma a yi wa tsohon filin wasa na Old Trafford kwaskwarima da zai ci Fam biliyan 1.5. Manchester United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai Fam miliyan 113.2 daga ranar 30 ga watan Yunin 2024 kuma kawo yanzu kungiyar tana mataki na 15 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24. Amma kuma har yanzu kungiyar tana buga gasar cin...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da barazanar kai hari kan filin jirgin saman Lebanon da sauran muhimman wuraren kasar ba. Sheikh Damoush ya jaddada a cikin hudubarsa ta Juma’a cewa “ya zama wajibi gwamnati ta magance matsalar jiragen Iran zuwa kasar Lebanon, domin wannan batu na farko da na karshe yana da alaka ne da ‘yancin kai da kuma martabar kasar Lebanon, kuma hakan na nuni da kwace ‘yancin matakin da...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...

Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata. Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari. An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi...
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a. Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh. Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba ɗaya don halartar wannan muhimmiyar tattaunawa da nufin bayyana wa jama’a irin cigaban da gwamnati ke samu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa. Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha, yana mai cewa hakan ya janyo Washington cikin rikicin na shekaru uku. An shirya wa’adin shekaru biyar na Zelensky zai kare a watan Mayun 2024, amma saboda dokar soja da aka kafa a watan Fabrairun 2022, ba za a iya gudanar da zabe ba. Kalaman na Trump sun jawo martani cikin gaggawa daga jami’an Ukraine, inda ministan harkokin wajen kasar Andrii Sybiha ya jaddada cewa...
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a Saudiyya ba. ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa A cewar Trump, Ukraine ce ta jawo wa kanta matsalar. “Da ba ku fara wannan yaƙin ba, da kun cimma yarjejeniya tun farko,” in ji shi. “Da ni ne, da na samo muku mafita, kuma babu wanda za a kashe.”...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na gaba na musayar fursunoni. Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya...
Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.” Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a. “Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...
Kasar Sin na maraba da duk kokarin da ake yi cikin lumana don warware rikicin kasar Ukraine, ciki har da tattaunawa tsakanin Amurka da Rasha, kuma Sin na fatan dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki za su shiga cikin shawarwarin samar da zaman lafiya in lokaci yayi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na yau Talata, yana mai cewa, ko da yaushe kasar Sin tana da yakinin cewa, tattaunawa da yin shawarwari, ita ce hanya daya tilo da za a iya warware rikicin, kuma ta himmatu wajen inganta shawarwari don samar da zaman lafiya. Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga wata tambaya game da ganawar da jami’an...
Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja. Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya. Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci...
Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 3000 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
Ya ce harin da aka kai ta sama ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda da dama tare da dakile harin da suka kai wa jami’an rundunar ‘yansanda (PMF) da jami’an tsaro na cikin unguwanni (Community Watch Corps, CWC) na jihar Katsina. AVM Akinboyewa ya bayyana cewa, an kaddamar da harin ne a matsayin martani ga bayanan sirri da ke nuna cewa, an kai harin ta’addanci a wani sansanin PMF da ke cikin al’umma, inda aka ce, ‘yan bindigar sun kashe jami’an PMF biyu da CEC hudu.
Masu lura da gasar sun ce kwarewar na’urar wajen yanke hukunci ya karu zuwa kashi 96.4 idan aka kwatanta da kashi 95.7% a kakar da ta gabata. “Babu wanda yake shakku kan tasirin da ko da kuskure daya wajen yanke hukunci zai yi,” in ji wani babban jami’in kwallon kafa, Tony Scholes. Ya ci gaba da cewa “Mun san cewa kuskure daya tal zai iya cutar da kungiya. Sakamako da kuma makin da kungiya ke samu na iya sanyawa a kori mai horarwa ko kuma dan wasa ya rasa damarsa a cikin kungiya.”Hakan ya faru ga Erin ten Hag – domin daya daga cikin kurakurai hudu da na’urar VAR ta tafka shi ne bai wa West Ham bugun fanareti a...
Mataimakin shugaban ya umarci shugabannin NAHCON da su gaggauta daukan kwararan matakan da suka dace domin tabbatar da kare martabar dukkanin maniyyatan Nijeriya. Da yake magana kan soke kwantiragin da suka yi da kamfanin kasar Saudiyyan, shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya ba da tabbacin cewa lamarin ba sai shafi kowani maniyyancin Nijeriya ba. “Ba wani abun damuwa kwata-kwata. Ba wani maniyyancin Nijeriya muddin an masa rajista da za a bar shi,” Usman ya shelanta. Ya kuma yi watsi da zargin da kungiyar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi (FSPWA) ke yi na cewa takaddamar kwangilar na iya kawo cikas ga aikin hajjin.
Jakadan Amurka na musamman kan kasashen Rashad Ukraine ya bayyana cewa Amurka tana kokarin ganin ta kawo karshen dukkan dangantakar da ke tsakanin kasashen China da Rasha da kuma JMI. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto, Keith Kellogg ya na fadar haka a taron Munich na tsaro a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa gwamnatin Trump tana aiki dare da rana don ganin ta wargaza dukkan dangantaka da ke tsakani Iran da Rasha da kuma China. Jakadan ya kara da cewa dangantaka da ke tsakanin wadannan kasashen da JMI babu ita a shekaru 4 da suka gabata. Amma shugaba Donal Tromp yana aiki a kan haka. don ganin an katse dangantakar wadannan manya-manyan kasashe da JMI....
Rahoton ya ce an fara badakalar ne a ranar 10 ga watan Disamba a lokacin da kamfanin harhada magunguna ya samu sakon imel dake nuna wani mai sayar da shi, Accent Pharma, yana neman a biya shi wani sabon asusun ajiya na banki. Ba tare da sanin sakon imel din na yaudara ne ba, ana zargin kamfanin harhada magunguna ya aika Rs 11.76 lakh, kamar yadda PUNCH Metro ta fahimci. Wakilinmu ya ruwaito cewa kamfanin ya gano cewa an yi kutse ne bayan an biya kudin da kuma tantancewa. Wannan ya haifar da kwakkwaran bincike daga sashin damfarar intanet na kasar. Rahoton ya kara da cewa, “Masu bincike sun binciki email din da aka yi wa kutse zuwa Nijeriya inda...
Babban jami’i mai kula da harkokin Syria a ma’aikatar harkokin wajen Iran, Muhammad Ridha Ra’uf Shaibani ya sanar da cewa, sun yi musayar sakwanni da kasar Syria, kuma sun bude kafar ttataunawa ta kai tsaye. Ra’uf Shaibani wanda ya kai ziyara kasar Rasha domin ttataunawa da mahukuntan kasar, ya fada a jiya Juma’a da marece cewa, Muna cikin shiri da tanadin sake dawo da alaka da kasar Syria anan gaba. Har ila yau. Shaibani ya ce; Muna bin diddigin abubuwan da suke faruwa a Syria, kuma za mu dauki matsaya a lokacin da ya dace.” Haka nan kuma ya ce; Muna kallon Syria ne a matsayin kasa wacce take da matsayi a cikin yankin yammacin Asiya, kuma mun yi imani...
Jami’ar Tarayya ta Lafia ta yi bikin rantsar dalibai 8,000 da suka sami gurbin karatu a sassan 76 a tsakanin tsangayoyin jami’ar 12. Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul-Rahman, ya sake jaddada matsayar hukumar a kan duk wani nau’i na rashin da’a da kuma shiga kungiyoyin asiri. Shugaban jami’ar wanda mataimakin shugaban jami’ar na sashen koyarwa, Farfesa Alemchi Chuku ya wakilta ya ci gaba da cewa basu da hakuri ga duk wani nau’i na rashin da’a kuma za su yi kakkausar suka ga munanan dabi’u. Ya kuma bukaci sabbin daliban da su mutunta juna da kuma ma’aikatan jami’ar da malamai na jami’ar domin ganin zamansu ya kasance mai amfani. “Ba...

Malaman Yahudawa Fiye Da 300 Sun Rattaba Hannu Akan Takardar Kin Amincewa Da Shirin Donald Trump A Yankin Gaza
Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya wacce ta dauki labarin tare da ambato wasu fitattun malaman na yahudawa da su ka rattaba hannu akan takardar, daga cikinsu har da Sharon Bruss, Roly Matalon, da Alisa Waiser, sai kuma wasu fitattun yahudawa a Amurkan. Cody Edgerly wanda daya ne daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan takardar, kuma shugaban kiran, ya nuna abinda shugaban na kasar Amurka yake son yi da...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Bayyana Rashin Amincewarta Da Shiga Tattaunawa Karkashin Matsin Lamba
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba, tana mai jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa tsarinta na asali a ko da yaushe tana goyon bayan samar da hanyoyin diplomasiyya kan batutuwa daban-daban da suka hada da batun Shirin makamashin nukiliya, kuma tana goyon bayan warware al’amura ta hanyar diflomasiyya ciki har da batun Shirin makamashin nukiliyarta, sannan ta tabbatar da hakan a tsawon shekaru fiye da ashirin na yin riko da...
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa. Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano Haruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.

Amurka Tana Son Ta Maida Rasha Da China Gefe A Duk Wata Tattaunawa Ta Shirin Makamashin Nukliyar Kasar Iran
Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya. Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba...
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci a kan lamarin. Har ila yau, ya yi kira ga hukumar makarantar da ma Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), da su girke tudu-tudu na rage gudu a kusa da makarantar domin kaucewa irin hatsarin nan gaba.
Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa. Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba. “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu yana da yawa, farashin sa yana sauka da kan sa.” Ministan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannin tsaro, inda ya ce a shekarar 2024 jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 8,000, sun kama mutum 11,600, tare da ƙwato makamai fiye da 10,000. Ya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ake yi yana sa hanyoyi na ƙara...
Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata rana. Trump ya kara da cewa a yayin zantawarsa da Tashar talabijin ta Fox News; Suna da kasa mai kimar gaske mai dauke da ma’adanai na musamman da man fetur da kuma iskar gas, da sauran abubuwa. Trump ya ci gaba da cewa: Yana son dukiyarsu ta kasance cikin aminci, domin suna kashe daruruwan biliyoyin dalolia cikin kasar. Ya karkare furucinsa da cewa; Za su...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma. A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin kasar Windhoek na kimani makonni 3 amma rai yayi halinsa a daren Asabar da ta gabata ya na dan shekara 95. Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africanews’ ya bayyana cewa kasar Namibia ta sami yencin kanta ne daga hannun gwamnatin wariya ta Afirka ta kudu a shekara 1990. Sannan Nujoma ya zama shugaban kasar na farko na tsawon shekaru 15. Sannan aka zabi shugaba mai...
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa, an tabbatar da sallamar Ari a matsayin Kwamishinan zaɓen jihar Adamawa bayan da Majalisar wakilai ta tarayya ta amince da buƙatar sallamarsa da shugaban ƙasa ya yi, biyo bayan zarginsa da aka yi da karya ƙa’idojin aiki da shigo da shakku yayin gudanar da aikin zaɓe da ayyana sakamakon zaɓe ba daidai ba, lamarin da har ya kai an gurfanar da shi a kotu. Ari ya nuna damuwarsa kan yadda hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da kotun sauraron ƙararrakin zaɓe suka shafa wa idanunsu toka suka ƙi hango hujjojinsa da ya gabatar na kura-kuran da aka tafka a lokacin zaɓen. Hudu wanda ya ɗauki Alkur’ani mai girma yayin hirar, ya rantse da...
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu. Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
Shugaban Ukraine, Bolodymyr Zelensky ya ce duk wata tattaunawa da za a yi kan makomar kasarsa, wajibi ne a sanya kasashen yamma da Amurka da Rasha da kuma Ukraine din a ciki. A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, Bolodymyr Zelensky ya ce a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugaba Bladimir Putin, idan har hakan ne zai kawo karshen yakin da suka kwashe kusan shekara uku suna gwabzawa. Sai dai shugaba Zelensky ya sake nanata bukatarsa ta karin makamai domin ci gaba da samun nasara kan Rashar.
Gwamnatin Amurka ta sanar da janye tallafin da take bai wa Afirka ta Kudu yayin da alaƙa tsakanin ƙasashen biyu ta lalace a dalilin dokar karɓe gonakin fararen fata da Shugaba Cyril Ramaphosa ya amince da ita. Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta katse duk wani tallafin da take ba wa Afirka ta Kudu ciki har da na kuɗi a wani mataki na nuna adawa da dokar kwace filayen noma da Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar ya rattabawa hannu. Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2 Shugaba Trump ya ce Amurka ba za ta taimaka wa gwamnatin Pretoria ba, duba da yadda take ci gaba da take...
Su tsare tsaren anyi shirin tabbatar dukkan makarantu masu zaman kan su da na gwamnati za su fara amfani da tsarin a watan Janairu 2025. Sai dai kuma watan Janairu ya wuce ba tare da samun wani ci gab aba dangane da lamarin. Rahoto ya nuna har yanzu da akwai sauran Rina a Kaba, domin kuwa da akwai karancin makarantu wadanda basu da irin kayan da za ayiu amfani da su wajen aiwatar da sabon tsarin,da kuma yadda za a horar da Malamai, hakan ta sa aka bar masu ruwa da tsaki cikin shakku ko sabon tsarin ilimin za afara amfani da shi. Sabon tsarin ilimin an yi niyyar fara amfanni da shi inda za a koyar da yaddaake sabbin...
Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata. Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun zama dala biliyan $39.723 daga ranar 31 ga watan Janairu 2025. An bayyana koma bayan ne a kudaden waje na ajiya da babban bankin kasar yake da su, da ya kamata ace a ranar 4 ga watan Febrairu ne za a fitar da kididdiga akan halin da kudaden wajen suke ciki,amma ba a yi ba. Bugu da kari wannanbayanin ya fito ne daga kamfanin dake...
Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20. Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22. Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5. Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku. Tun a watan Disamba na...
A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa. Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun maslaha.
A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi. A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da gargaɗin da mahaifiyarta ta yi mata. Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga “Lokacin da mahaifiyar ta samu ’yarta a bakin kogin, sai ta fusata. Duk da gargaɗin da aka yi mata na ƙauracewa kogin, Rachael ta ƙi, wanda hakan ya sa mahaifiyar tashin hankali ta fusata,” in ji wani ganau. A cikin fushi,...
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu da bai wa ‘yan’uwansu haƙurin jure wannan babban rashi, har ila yau gwamna Dauda Lawal ya yi addu’ar Allah ya bai wa wadanda suka samu raunuka lafiya. Gwamnati za ta yi bincike domin ta gano dalilin afkuwar wannan gobara, domin kaucewa hakan a nan gaba. A karshe ya ce gwamnati za ta bayar da duk wani taimakon da ake bukata da tallafi ga iyalan mamatan da kuma na asibiti.
Hukumar kula da aikin Hajji ta kasa NAHCON ta sanar da a ci gaba da yi wa maniyyata rajista har zuwa ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu, 2025. A daren Talata 4 ga watan ne hukumar ta amince da kara lokacin a taron da ta yi da shugabannin hukumomin alhazai na jihohi. Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Jin Dadin Alhazzai ta Jihar Kaduna Yunusa Mohammed Abdullahi ya fitar, ya ce shugaban hukumar Malam Salihu S. Abubakar ya yi kira ga maniyyatan jihar ta Kaduna da su yi amfani da wannan damar wajen yin rajista ta hanyar tuntubar jami’anmu da ke kananan hukumomi don su cika kudadensu, ko karbar sabuwar telar banki don su biya kafin a...
Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun. Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a...

Sheikh Na’im Kassim: Za A Yi Jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Rana 23 Ga Febrairu Da Ake Ciki
Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon. Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken...
Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Ukraine da aka dakatar a yakin da ake yi da Rasha, suna bukatar a gduanar da su. “Yawancin kasashen dimokuradiyya suna gudanar da zabe a lokacin yakinsu. Ina ganin yana da mahimmanci su yi haka,”in ji Kellogg. Kamfanin dillancin labaran reuters ma ya rawaito wasu jami’an fadar White House sun tattauna batun matsawa...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba. Sannan, shin su wa ke amfani da kudaden fansar da ake biya ga masu garkuwa da mutanen? Hasashe ya nuna cewa, mai yiwuwa a yi amfani da kudaden don kara sayen bindigogi da sauran makamantansu. Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Bukatar Warwarewa A cikin wannan rudani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester. Mece Ce Matsalar Manchester United? AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin...
Shi ma da yake jawabi, shugaban kungiyar masu tuka ‘yar kurkurar, Jamilu Isyaku ya bayyana jin dadinsa ga Gwamna Radda bisa amsa kiran da suka yi masa na biya masu bukatunsu kan sama masu da keke napep mai amfani da lantarki da kuma ba da tabbacin yin amfani da su yadda ya kamata.
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi. Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?. A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda...
Sarkin ya yi addu’a Allah ya jiƙansa, ya gafarta masa, kuma ya bai wa iyalansa haƙuri.

Tunawa Da Ranar Wadanda Aka Yi Wa Kisan Kiyashi: Majalisar Dinkin Duniya Ta Wayar Da Kan Dalibai A Abuja
Ishara ”Kada Mu Manta” taron, ya ba da haske game da lokutan soyayyar dangi da alakar kud da kud da ke wanzuwa a cikin iyalai na Yahudawa da al’ummomin kafin Holocaust da alhakinmu na kare hakkin kowa na rayuwa cikin mutunci da zaman lafiya. Da yake gabtar da jawabi a yayin taron jakadan kasar Isra’ila Inbar Lipman Garden, cewa ya yi A wannan rana mai girma muna tuna Yahudawa maza da mata da yara miliyan shida da aka kashe a cikin Holocaust tare da miliyoyin wasu da ke shan wahala a ƙarƙashin mulkin Nazi. Muna girmama abubuwan tunawa da su ba wai kawai nuna rashin jin dadi ba a a har ma da sake tabbatar da aniyarmu...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba. Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba. Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa...
Shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan dokar ba da damar tsare bakin haure kusan 30,000 a sansanin Amurka da ke tsibirin Guantanamo Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana son gidan kurkukun sojoji da ke Guantanamo Bay, wanda aka kebance domin tsare fursunonin da ake zargi da ta’addanci, ya kasance a shirye domin karban bakin haure kusan 30,000 da suka shiga cikin Amurka ba bisa ka’ida ba. Trump yana cewa: “A yau zai rattaba hannu kan wani umarni na zartarwa wanda ke umurtar ma’aikatar tsaro da tsaron cikin gida da su shirya wata cibiya da za ta karbi bakin haure 30,000 a tsibirin Guantanamo Bay,” Trump ya kara da cewa: Guantanamo zai karbi “masu aikata laifuka” a cikin...
Sabbin waɗanda aka rantsar sun haɗa da Hon. Sanusi Khalifa, babban mashawarci kan albarkatun ƙasa; Hon. Haladu Ayuba, Mai Bada shawara kan daidaita ɗabi’un jama’a; Hon. Jidauna Tula, babban shawarcesa kan harkokin Shari’a da kuma Hon. Adamu Bello da aka sanya a matsayin babban mashawarci a ɓangaren kasuwanci da masana’antu. Sauran sun haɗa da Alh. Danladi Mohammed Danbaba, babban mai bada shawara kan harkokin jin-ƙai; Hon. Sani Mohammed Burra, babban mai bada shawara kan harkokin majalisar dokokin jihar da na tarayya; Hon. Yakub Ibrahim Hamza, babban mai bada shawara kan ilimi mai zurfi da kuma Hon. Shitu Zaki da ya zama babban mai bada shawara kan harkokin siyasa. Ƙarashin su ne Usman DanTuraki, babban mai bada shawara kan...
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40. Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci. Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci...

Sojojiun HKI A Kudancin Kasar Lebanon Sun Kashe Mutane Fararen Hula Wasu Kuma Suka Ji Rauni A Yau Lahadi
Ministan kiwon lafiya na kasar Lebanon ya bada sanarwan cewa sojojin HKI a kudancin kasar sun kashe fararen hula 15 sannan wasu 83 suka ji rauni a safiyar yau. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana cewa mutanen kudancin kasar Lebanon sun komawa gidajensu da suke kudancin kasar kan iyaka da kasar Falasdinu da aka mamaye ne, sai sojojin yahudawan, suka bude masu wuta suka kashe wannan adadin. A yau Lahadi ne 26 ga watan Jeneru ne, wa’adin ficewar sojojin HKI daga kasar Lebanon yake cika kamar yadda ya zo cikin yarjeniyar da suka sanyawa hannu da kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata. Wannan bas hi ne kate hurumin yarjeniyar da aka sanyawa hannu da...

Falasdinawa Sun Gudanar Da Bukukuwan Tarbar Fursunonin Falasdinawa 114 Da Aka Sako Daga Gidan Yarin Isra’ila
Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.