2025-04-15@20:17:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1351
«Iran da Amurka»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland. Shugaba Donald Trump yana kokarin kawo karshen yakin Ukraine da aka shafe fiye da shekaru uku anayi tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cimma nasarar warware matsalar ba. Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta dauki karin nauyi...
Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata. Nijar ta ayyana Hausa a matsayin yaren ƙasa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Ministan ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun wani adadi mai yawa na ƙwararrun likitocin da ke da burin fita zuwa wasu ƙasashen duniya aiki, suna fakewa da matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya. Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya. Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma...
Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin. Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da suke yia kan fararen hula a yankuna da dama na Gaza. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da samun sabbin adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda adadin shahidai ya kai 50,810 yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 115,688. Adadin wadanda suka raa...
An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda. An fitar da Neguise daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar Tarayyar Afirka bayan da kasashe da dama suka nuna rashin amincewarsu da halartarsa a taron shekara-shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. Jakadan na Isra’ila ya shiga wurin taron ne ba zato ba tsammani, ba tare da an gayyace shi ba, a cewar majiyoyin diflomasiyyar da suka halarci taron. Majiyar ta kara da cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewa da zuwansa, lamarin da ya sa aka dakatar da taron...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali. “An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa. “Daga shekaru uku baya zuwa yanzu a hankali zaman lafiya ya fara dawowa Borno, amma lamarin ya sauya a ‘yan kwanakin nan,” in ji shi Zulum...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta – shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari. Domin...
Duk da matsin lambar da Amurka ke yi, kasar Sin tana da dabararta, za ta ci gaba da mai da hankali kan ayyukanta, za ta kuma rika bude kofarta ga ketare. Har kullum kasar Sin na ganin cewa, ainihin huldar da ke tsakaninta da Amurka ita ce samun moriyar juna da nasara ga ko wane bangare. Ya kamata a daidaita sabanin ciniki ta hanyar tattaunawa cikin adalci. Amma idan Amurka ta fara dora harajin da ta yi shelar dauka, to, kasar Sin za ta dauki wajibabbun matakai, domin kiyaye halastattun hakkokinta. (Tasallah Yuan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Declan Rice ne ya jefa ƙwallaye biyu a wasan kafin Mikel Merino ya jefa ta uku kuma ta ƙarshe a wasan, hakan ya sa Rice ya zamo dan wasa na farko a tarihin gasar Zakarun Turai da ya ci ƙwallaye biyu daga bugun tazara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta lallasa Real Madrid a daren nan a karawar da suka yi ta kwata-fainal a Gasar Zakarun Turai. Arsenal dai ta doke Real Madrid da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Emirates da ke Landan. Boko Haram na sake ƙwace ikon wasu yankuna a Borno — Zulum Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansa An kammala minti 45 na karawar babu ci, sai dai alƙaluma sun nuna Arsenal ta kai farmaki sau huɗu yayin da Real ta kai hari sau biyar. Duk da cewa babu ɓangaren da ya samu nasarar zura ƙwallo amma wasan wanda Irfan Peljto na ƙasar Bosnia Herzegovina ya yi alƙalanci ya yi matuƙar...
Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Turai su kara mu’amala da juna, da bude kofa ga juna don tabbatar da yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata, ta...
Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali. Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansa “An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa. “Daga shekaru uku baya...
Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai. Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma...
Ya ce karin wa’adin na baya-bayan nan ya biyo bayan cikar wa’adin farko na ranar 1 ga Afrilu, 2025, wanda aka sanya tun da farko a ranar 24 ga watan Janairu. Umar ya kara da cewa, duk da wannan karin wa’adin, amma an ci gaba da samun karancin fitowar masu filaye domin sabunta takardunsu. Domin tabbatar da bin ka’ida, kwamishinan ya yi gargadin cewa, nan ba da jimawa ba, za a buga sunayen wadanda ba su bi ka’ida ba a jaridun kasar nan da kuma nuna su a allunan sanarwa a muhimman wuraren gwamnati da suka hada da dakin karatu na jihar Kano, Sakatariyar Audu Bako, Gidan Murtala, da kuma babbar kotun jihar. Daga kanmu, magana ta...
Sojojin HKI sun kara yawan hare-haren da suke kaiwa kan Falasdinawa a Gaza, a dai-dai lokacinda ake kiranta zuwa tsagaita wuta a gazar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kungiyar kare fararen hula ta falasdinawa a Gaza, tana fadar haka a safiyar yau Talata. Ta kuma kara da cewa, Ta kuma kara da cewa a daren jiya kadai jiragen yakin yahudawan sun kashe akalla falasdinawa 19 mafi yawansu yara kanana. Labarin ya nakalto kakakin kungiyar kare fararen hula na Gaza Mhmood Bassal yana fadar haka, ya kuma kara da crawa , a garin Deir Balah jiragen yakin yahudawan sun kai hari a kan wani gida inda suka kashe yara 5 da manyan mutane 4. Sannan sun...
Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar. Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi. Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe yanken Sahel 3 Niger, Mali da Burkiya faso kan kakkabo jirgin saman yaki wanda bai da matuki wanda ya keta sararin samar kasar ta Aljeriya a makon da ya gabata, wanda ya sa kasashen uku suka janye jakadunsu daga kasar. Gwamnatin kasar Mali dai bata yi magana a kan wannan matakin da gwamnatin kasar ta Aljeriya ta dauka ba. Sai dai dakatar da zirga-zirgan jiragen...
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa da ake tuhumar sa, wanda ya saba wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007. Takardar tuhumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, a Cibiyar Bikin Ali Jita da ke Kano, inda aka ga angon a wani bidiyo yana yin kari da Naira dubu dari a takardun Naira dubu daya-daya...
Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa gare su ba ta hanyar motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan tsaron farar hula. Isra’ila ta kashe mutane 1,449 tare da jikkata wasu 3,647 tun bayan da ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 18 ga Maris, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Ta kara da cewa yawan Falasdinawa da aka kashe a yakin Isra’ila a Gaza zuwa 50,810, wasu 115,688 kuma sun samu raunuka...
Akalla Falasdinawa 58 ne aka kashe tare da jikkata wasu 213 a cikin awa 24 da suka wuce a hare-haren da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza. Ma’aikatar lafiya ta yankin ta sanar cewa wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun makale a karkashin baraguzai da kuma kan tituna, ba za a iya isa gare su ba ta hanyar motocin daukar marasa lafiya da kuma ma’aikatan tsaron farar hula. Isra’ila ta kashe mutane 1,449 tare da jikkata wasu 3,647 tun bayan da ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta a ranar 18 ga Maris, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Ta kara da cewa yawan Falasdinawa da aka kashe a yakin Isra’ila a Gaza zuwa 50,810, wasu 115,688 kuma sun samu raunuka...
Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu. Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi. Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin wata ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa da manyan kungiyoyi a kasar, inda ya tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen harkokin mulki, da manufofin harkokin waje, da kalubalen tattalin arziki da zamantakewar kasar. Da yake magana game da kalubalen gudanar da harkokin mulki, shugaban na Iran ya bayyana cewa, ba za a iya cimma gyara halayen kungiyoyi da bangarorin gwamnati ta...
A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi al-Faqawi da wani matashi mai suna Yousef al-Khazindar sun yi shahada, yayin da wasu ‘yan jarida da suka hada da Ahmed Mansour, Hassan Islayh, Ahmed al-Agha, Mohammed Fayek, Abdullah al-Attar, Ihab al-Bardini, Mahmoud Awad, da Majed Qudaih, suka samu raunuka a tashin bam din. Kungiyar Kafafen Yada Labarai ta Falasdinu ta yi Allah wadai da wannan harin da Isra’ila ta kai a kan tantin ‘yan...
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar karshe da duk wani bako da ke kasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta dauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga kasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta jaddada cewa duk wanda aka samu ya ci gaba da zama a kasar har...
Sai an ga yadda za ta kaya a Emirates yau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Haka kuma, an gargaɗi kamfanonin da ke da alhakin kawo mutane Umrah cewa idan suka ƙi bayyana sunayen waɗanda suka ƙi dawowa gida, za a ci su tara har riyal 100,000. Ma’aikatar ta buƙaci kowa ya bi doka domin guje wa hukunci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jamhuriyar musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta fata tattaunawa wacce ba ta kai tsaye ba da Amurka a ranar Asabar mai zuwa a kasar Oman. Ministan harkokin wajen Iran din ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan a shafinsa na ‘’X’’ a safiyar Talata. “Iran da Amurka za su gana a Oman ranar Asabar don tattaunawa mai zurfi, inji ” Araghchi. “Wannan wata dama ce, kuma kwallo yana hannun Amurka,” ta nuna da gaske ta ke in ji shi. Kalaman Araghchi na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa Amurka da Iran suna tattaunawa kai tsaye, bayan ganawa da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Washington. Shugaban na Amurka ya ce tattaunawar da za a yi...
A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo bayan kakkabo jirginta marar matuki. Haka zalika ma’aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen da ke zuwa kasar Mali”, ba tare da bayar da wani karin bayani ba, wanda ke nuni da cewa jiragen farar hula na kasuwanci da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa su ma abin ya shafe su. Takaddama dai ta yi zafi tsakanin Aljeriya...
Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin. Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a Gaza kuma ya nuna damuwar da kasashen duniya ke ci gaba da yi kan tashe-tashen hankula da rikicin jin kai a Gaza. Haka kuma sanarwar wadannan kasashe uku ta nuna muhimmancin hanyar diflomasiyya na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A baya dai shugaba Macron ya nuna adawarsa da mamaye yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta yi. Macron ya kuma kira sabbin hare-haren da Isra’ila ta...
A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar manyan jami’an tsaro da na shari’a na gwamnatin. Sun kuma yi Allah wadai da sake dawo da yakin kisan kare dangi da ake yi wa al’ummar Gaza. Iyalan ‘yan Isra’ilar da aka yi garkuwa da su a Gaza su ma sun shiga zanga-zangar, inda suka bukaci a kawo karshen yakin da kuma kulla yarjejeniyar tabbatar da sakin mutanen da aka kama. Kungiyar dai ta ce...
Aƙalla mutane biya ne suka mutu, 19 suka yi munanan raunuka a dalilin hatsarin mota da ya rutsa da su a Kasuwar Damagum da ke kan babbar hanyar Kano-Maidugri a Jihar Yobe. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi. Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Wani da lamarin ya faru a idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa, gudun wuce sa’a da wani direban bas ke yi ne ya janyo hatsarin, inda ya afka wa mutanen da ke tsaye a bakin titi ana tsaka da cin kasuwar. “Direban ya ɗauko fasinjoji ne zuwa Damaturu, kuma da alamu Potiskum ya nufa,” in ji shi. Kwamandan hukumar kiyaye haɗura...
Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta...
Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD da kuma tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban bisa tushen WTO. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da...
Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin siyasar waje na majalsar shawarar musulunci ta Iran ya gabatar da rahoto akan hali na karshe da ake ciki dangane da batun tattaunawa da Amurka. Arakci ya kuma fadawa kwamitin cewa; Mu ma’abota diflomasiyya da tattaunawa ne, amma za mu tattauna da Amurka ne ba kai tsaye ba,kuma duk da hakan ma har yanzu ba mu...
Ambaliyar da aka samu sanadiyar mamakon ruwan sama ta kashe aƙalla mutum 33 a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo. Ruwan saman kamar da bakin ƙwarya ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgar ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama. Saudiyya ta musanta hana ’yan Nijeriya biza Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilasta wa wasu mazauna ƙasar yin hijira. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa wasu mazauna yankin na yunƙurin hijira ta cikin ruwa da ninƙaya, wasu kuma sun yi amfani da kwale-kwale....
Kasashen Uku Suna Yin Taron ne dai a matsayin kwararru domin tattauna batutuwa da dama daga cikinsu da akwai na shirin Nukiliya na Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Baka’i ne ya sanar da cewa za a yi wannan taron ne a birnin Moscow wanda kuma ya kuma kunshi wakilai daga kasashen Iran, China da kuma mai masaukin baki Rasha. Buku da kari Baka’i, ya kuma bayyana cewa za a yi wata tattaunawar a tsakanin Iran da tarayyar turai a matakin masana shari’a. A can kasar Rasha mai Magana da yawun harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ta fada wa kafafen watsa labarun kasar ta Rasha cewa, a gobe Talata ne za a yi tattaunawar a tsakanin kwararru daga kasashen...
Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu. Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas “Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar. Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji....
Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar da kungiyar ‘Take-it- Back Movement’ da kungiyoyin fararen hula suka shirya a fadin kasar ya zo daidai da ranar bikin ranar ‘yansanda ta kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci LEADERSHIP ta tuna cewa, hukumomin ‘yansanda sun yi gargadi...
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa. Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama. A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilastawa wasu mazauna ƙasar yin hijira a yayin da wasu suka yi amfani da kwale-kwale kamar yadda jam’in kamfanin dillancin labaran AFP ya shaida. Wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa, sun maƙale a saman gidajensu bayan da ruwan ya mamaye matakalar shiga gidanjensu. Bugu da...
Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi marar matuki na kasar Mali a farkon wannan wata. Aljeriya dai ta kakkabo jirgin sojojin na Mali marar matuki a cikin daren ranar 31 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, matakin da kasashen uku sukayi tir da shi. A cewar gwamnatin Algiers, jirgin mara matuki da ake magana a kai ya shiga cikin kasar ne, saidai sojojin Mali sun tabbatar da cewa jirgin bai shiga...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar Hungary duk da sammacin kame shi da kotun ICC ta bayar kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama da gwamnatinsa ta yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce : Sammacin kame jami’an gwamnatin Isra’ila da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi na nuni da yadda duniya ke nuna bacin rai kan kisan kiyashi, laifukan yaki, da...
Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Yemen, inda ta kai sabbin hare-hare ta sama a yankuna daban-daban na kasar a baya bayan nan. Kafar yada labaran kasar Yemen ta bayyana cewa, Amurka ta kai akalla hare-haren jiragen yaki guda uku a gundumar Bani Matar da ke lardin Sanaa. Akalla fararen hula hudu ne suka mutu sannan wasu 25 suka jikkata, ciki har da mata 11 da yaro daya. Hakazalika jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare guda hudu a tsibirin Kamaran da ke al-Hudaydah a yammacin kasar Yemen. Wasu hare-hare uku na Amurka sun kai hari a lardin Hajjah da ke yammacin kasar Yemen. Amurka da kawayenta sun zafafa kai hare-hare kan kasar Yemen bayan da ta koma yaki...
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida kusa da wani asibiti a Khan Younis da sanyin safiyar ranar Litinin din nan. Akalla mutane bakwai ne kuma suka jikkata a harin. A cikin wani rahoto da aka buga a ranar 1 ga Afrilu, Cibiyar Watson ta ce yakin da Isra’ila ta yi a Gaza ya kasance mafi muni ga ma’aikatan yada labarai da aka yi rikodin kuma...
Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da rubutun bayyana buƙatunsu a...
Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji tare da rasa mayaƙansu da dama. Rahotanni na cewa harin ya auke ne da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi a lokacin da ’yan ta’addan suka mamaye sansanin sojin Nijeriya da ke garin Izge. Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back An sayar da kare mafi tsada a duniya Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa Aminiya cewar wani soji mai muƙamin Kyaftin da kuma Kofur na daga cikin waɗanda suka kwanta dama, yayin da sojoji suka yi nasarar hallaka mahara da dama a yayin arangamar. Shugaban ƙaramar...
Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba. Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya. Rundunar ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai...
Iran ta sake nanata matsayinta na kin shiga shawarwari kai tsaye da Amurka kan shirinta na nukiliya, maimakon haka ta bukaci a ci gaba da shawarwarin ta hanyar masu shiga tsakani. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya bayyana hakan, yana mai cewa babu wata tattaunawa da aka da Washington, kuma ba za a yi irin wannan tattaunawa ba sai dai ta hanyar masu shiga tsakani. “Mun bayyana matsayinmu, muna goyon bayan bin hanyoyi na diflomasiyya da tattaunawa, amma ta hanyar masu shiga tsakani. Tabbas, ba a gudanar da wata tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da Amurka ba, ” in ji Araghchi a cikin wata sanarwa da ya fitar a dandalin Telegram. Kalaman nasa sun zo ne bayan da shugaban...
A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, a yayin bikin ranar yara kanana ta duniya a Falasdinu, cibiyoyi masu fafutuka kan harkokin fursunoni sun sanar da cewa: Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana ci gaba da tsare kananan yara Palastinawa sama da 350 a gidajen yari da wuraren da ake tsare da fursunoni. Sanarwar hadin gwiwa da hukumar kula da harkokin tsare-tsare, da “Kungiyar Fursunonin palasdinu”, da kuma “Cibiyar Kare Hakkokin Bil Adama ta Al-Dameer” suka fitar, ta bayyana cewa, yaran na fuskantar matsaloli Ciki har da azabtarwa, yunwa da gangan, da rashin kulawar likita. Wadannan cibiyoyi sun jaddada cewa yaran Palasdinawa su ma suna fuskantar tauye hakkinsu, wanda irin wannan hali ne ya yi sanadin shahadar wani yaro a cikin makon...
Fulham ta kawo ƙarshen wasanni 26 da Liverpool ta yi a jere ba tare da rashin nasara ba a gasar Firimiyar Ingila ta wannan kakar. Fulham ta yi nasarar doke Liverpool da 3-2 a Craven Cottage ranar Lahadi a wasan mako na 31. Liverpool ce ta fara zura ƙwallo a ragar Fulham ta hannun Mac Allister minti 14 da fara wasa kafin Ryan Sessegnon ya rama wa Fulham a minti 23. Fulham ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai da ta ƙara wa Liverpool ƙwallo ɗaya a lokacin da ɗan wasan Nijeriya, Alex Iwobi ya zura ƙwallo a ragar Liverpool a minti 32 da fara wasa. Yayin da ake tunanin cewa Liverpool za ta iya ramawa, sai Fullham ta...
Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata, da kuma fasahar kera makamin idan tana bukatar yin hakan. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Agentina a yan kwanakin da suka gabata. Ya kuma kara jaddada cewa a halin yanzu JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana da abinda ake kira “sinadarin Uranium da ta gasa, wanda yawansa zai iya samar da makaman nukliya har zuwa 6-ko 7, amma dai bata kera makamin ba. Abinda tambaya a nan itace tunda hukumar ta tabbatar da cewa...
Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila. Hakan ya sa ta kasance kungiya ta farko a tarihin gasar da ta koma baya (relegation) bayan buga wasanni 31 kacal, Southampton ta samu maki 10 a wasanni 31 an zura mata kwallaye 74 a raga sannan kuma ta zura kwallaye 23 kacal a bana. Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028 Ramsdale tsohon mai tsaron ragar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024. Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana zuwa 1.43 ya taimaka wajen sanya sashin mai a matakin ci gaba na dan kadan a maimakon yin kasa sosai. A gabaki-daya, sashin mai ya taimaka da kaso 00.7 cikin 100 na ci gaban tattalin arziki cikin gida (GDP) a tsawon wannan lokacin. “Vangaren da ba na mai ba wanda ya samu tagomashi, ya samu saurin havaka da kaso 3.69 idan aka kwatanta da na...
Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 177 dubu dari 615 da 840 daga wani babban kantin da ke Millenia a birnin Orlando da ke Jihar Florida a Amurka a ranar 26 ga Fabrairu. A cewar sashen ’yan sanda na Orlando, Glider ya dauki matakin da ba a saba gani ba na haɗiye ’yan kunnayen da ya sace. A cewar rahoton ’yan sanda da kafar yada labarai ta...
Ganduje Ya Nada Tsohon Kwamishinansa Garba, Shugaban Ma’aikatan Jam’iyyar APC Kamshin Jiki Da Cikar Hankalin Manzon Allah (SAW) Maimakon mu guje wa matsalolin da muke fuskanta, ya kamata mu nemi shawarar magance su. Idan kuka bi ka’idodin hakan zai taimaka muku ku magance matsalolinku. Ku tattauna matsala: Akwai lokacin magana, Ku tabbata cewa kun tattauna matsalar sosai. Ka gaya wa matarka ainihin abin da ke zuciyarka da kuma ra’ayinka a kan batun. A kowane lokaci, ku gaya wa junanku gaskiya, ko da abin vacin rai ya faru kada ku yi fada. Idan ka yi maganar da za ta sanyaya zuciyar matarka ba za ku yi gardama ba. Ko da ba ku jitu a kan wannan batu ba ku ci gaba...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana sharuddan da Tehran ta gindaya na ci gaba da tattaunawa kan shirinta na nukiliya, yana mai jaddada aniyar kasar ta fuskar diflomasiyya tare da tsayawa tsayin daka kan muradun kasa. Da yake magana a wani taron sabuar shekarar Nowruz tare da jami’an Iran, jakadu, da wakilan kasa da kasa a daren ranar Asabar, Araghchi ya jaddada daukar nauyin Iran kan harkokin duniya. Ya lura cewa martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump an yi shi ne don dacewa da sauti da kuma abin da ke cikin saƙon na asali, ta hanyar buɗe hanyoyin diflomasiyya. Araghchi ya yi nuni da cewa, yin cudanya kai tsaye da jam’iyyar da ke ci gaba da...
Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo, gami da cewa motocin daukar marasa lafiya ba su da haskensu na gaggawa, kuma sojojin Isra’ila sun shiga wuta. Rahoton sojojin Isra’ila daga baya ya yi ikirarin cewa sojojin na Isra’ila sun boye gawarwakin da motocin daukar marasa lafiya a karkashin yashi “don hana namun daji cinye su.” Wannan tsari dai ba a saba gani ba ne ga dakarunsu na aikata kisan kiyashi tare da...
Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a amince da shi ba ne, bai dace ba, kuma babban abin damuwa ne,’ in ji Sakataren Harkokin Waje David Lammy, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.” Lammy wanda ya bayyana cewa Birtaniya tana tuntuɓar ‘yan majalisar domin ba su goyon baya, kuma ya bayyana wa hukumomin Isra’ila ƙarara cewa “ba haka ake yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya mu’amala ba.” “Abin da gwamnatin Birtaniya...
Tsohon Gwamna Jihar Oyo, Omololu Olunloyo ya riga mu gidan gaskiya. Wata sanarwa da iyalansa suka fitar ta ce ya rasu yayin da rage kwanaki tara kacal ya cika shekaru 90 a doron ƙasa. Finafinan Kannywood da suke tashe da kuma manyan marubutansu An yi wa wata mata ƙarin jini sau 36 Tsohon gwamnan wanda aka haifa a ranar 14 ga watan Afrilun 1935, ya rasu ne da misalin ƙarfe 1:40 na daren ranar 6 ga watan Afrilun 2025. Bayanai sun ce a bayan nan ya yi ’yar taƙaitacciyar jinya da ke da alaƙa da mutanen da shekarunsu suka ja. Olunloyo ya riƙe muƙamin Gwamnan Oyo daga ranar 1 ga watan Oktoban 1983 zuwa 31 ga watan Disamban 1983 lokacin...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya soki abunda ya danganta da barazanar Amurka ga Teheran, yana mai cewa kasarsa a shirye take ta shiga tattaunawa ta hakika ba tare da barazana ba. “Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana neman tattaunawa ta gaskia, a yayin da suke barazana ga Iran a daya bangaren kuma suna neman yin shawarwari,” in ji Pezeshkian a ranar Asabar. “Idan kuna neman shawarwari, to me yasa kuke yin barazana? A yau, Amurka ba wai kawai ta wulakanta Iran ba har ma da duniya, kuma wannan hali ya saba wa bukatar tattaunawa,” in ji shi. Kalaman na Pezeshkian sun zo ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga Tehran da ta shioga shawarwari kai tsaye...
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kisan da Isra’ila ta yi wa ma’aikatan agaji a zirin Gaza, bayan da wasu sabbin hujjojin bidiyo suka nuna yadda sojojin Isra’ila suke harbin motocin daukar marasa lafiya. Bidiyon da ya ci karo da wani nau’in lamarin da sojojin Isra’ila suka yi cewa “an gano wasu motoci marasa da yawa suna tunkarar sojojin Isra’ila ba tare da fitillu ko alamun motocin ambullance na gaggawa ba”. Shugaban kungiyar agajin ta Falasdinu Younes al-Khatib, ya bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan kashe-kashen, yana mai jaddada cewa ba za a iya amincewa da binciken da sojojin Isra’ila ke jagoranta ba. “Ba mu amince...
Sanannen abu ne cewa irin shagulgulan da ake gudanarwa a lokacin bukukuwan sallah a Kano na samar da nishaɗi da walwala ga mazauna jihar da ma baƙi da ke zuwa kallo daga sassa daban-daban na duniya. Haye-hayen Sallah da Sarkin Kano da hakimansa da sauran ’yar majalisarsa ke yi na daga cikin abubuwan mafi bankaye da sanya farin ciki da annashuwa a zukatan dubban mutane a yayin shagulgulan. Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya (2) An kai wa motar haya hari an kashe mutum 2 da sace wasu a Benuwe Rashin gudanar da hawan a bara saboda hanawar da ’yan sanda suka yi sakamakon Dambarwar Sarautar Kano, ta sa umarnin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar...
Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times” masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.” Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abindaya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da cewa sojojin Isra’ilan suna yin abinda suke yi ne a tsare,kuma duniya ta yi shiru.” Jaridar “New York Times” ta watsa faifen bidiyo dake dauke da muryar wani ma’aikacin agaji wanda daya ne daga cikin wadanda aka sami gawawwakinsu a cikin wani babban kabari a yankin Rafaha. Bidiyon ya nuna yadda sojojin Isra’ila su ka kai wa masu aikin agaji hari da gangan, sun kuma...
A wata sanarwa da kungiyar ta malaman addinin musulunci ta duniya ta ce wajibi ne akan kowane musulmi wanda yake da iko a fadin duniyar musulunci da ya taimakawa mutanen Gaza da makamai da kayan yaki domin dakile ta’addancin Isra’ila da yake cigaba. A jiya Juma’a ne kungiyar malaman addinin musuluncin ta duniya ta fitar da wannan fatawa wacce ta kunshi yin kira ga daidaikun musulmi da kuma gwamnatocinsu da su bai wa kungiyoyin gwgawarmaya makamai da kayan yaki da kuma bayanai na sirri akan abokan gaba. An gina fatawar ne akan cewa matakin farko na wajabcin jihadin akan al’ummar Falasdinu, sannan kasashen dake makwabtaka da Falasdinu da su ka hada Masar, Jordan da kuma Lebanon, sannan kuma dukkanin kasashen...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, ta ceto fasinjoji 14 da wasu ’yan bindiga suka sace yayin da suke tafiya a kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo. Sai dai uku daga cikin fasinjojin sun rasu, ciki har da direban motar. Sabon harajin Trump zai jefa tattalin arziƙin duniya cikin matsala — WTO Ɗalibai za su koma makaranta ranar Lahadi da Litinin – Gwamnatin Kano A cewar sanarwar da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, CSP Catherine Anene, ta fitar a ranar Juma’a, lamarin ya faru ne a ranar 3 ga watan Afrilu, 2025. Wasu ’yan bindiga sun farmaki motar a yankin Otukpo Burnt Bricks, inda suka buɗe wa direban da wani fasinja da ke gaba wuta, lamarin da ya tilasta direban tsayawa. ’Yan...
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa Euro-Med ta ce Laifukan da Isra’ila ta aikata a Gaza sun zarce na kungiyar Daesh. A rahoton data fitar Euro-Med ta ce, tawagoginta sun tattara dubban laifukan da sojojin Isra’ila suka aikata, wadanda suka zama shaidu masu yawa na cin zarafi. “Wadannan laifuffukan suna wakiltar yanayin tashin hankalin da ba a taba gani ba a baya baya nan, saboda laifuka ne da akayi da gangan, da kuma manufar kisan kiyashi. ” Dole ne a yi tir da yanayin laifukan da Isra’ila ta aikata a cikin yankunan Falasdinawa, saboda girman wadannan laifuffukan, wanda ya zarce na kungiyar Daesh. Har ila yau Euro-Med ta jaddada bukatar gaggawar daukar matakin da ya dace na kasa...
Madugun kungiyar Ansarallah ta kasar Yeman ya yi ikirarin cewa, zafafan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kasar Yemen, ya kasa dakatar da ayyukan gwagwarmayar Yeman na goyon bayan al’ummar Gaza ko kuma kare jiragen Isra’ila a tekun Bahar Rum. A wani jawabi da ya yi a ranar Juma’a, Abdul-Malik al-Houthi ya ce Amurka ta zafafa kai hare-hare a kan kasar Yemen, inda wasu lokutan ta kai hare-hare sama da 90 a kowace rana, a wani bangare na goyon bayan da take baiwa kasar Isra’ila a yakin kisan kare dangin da ta ke yi a zirin Gaza. Duk da haka, ya jaddada cewa, hare-haren na Amurka “sun kasa dakatar da ayyukan soji da ke tallafawa al’ummar Falasdinu,...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Abdallah Usman zai jagoranci kungiyar a karon farko cikin makonni 5 a wasan da Pillars zasu kara da Haertland Owerri. Wasan na mako 32 a gasar Firimiya ta Nijeriya da za a buga a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano, zai zama wani mataki da Abdallah zai sake kwantar da hankalin magoya bayan ƙungiyar bayan hatsaniyar da su ka samu a ƙarshen watan Fabrairu. Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi? Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Pillars na mataki na 8 da maki 44 a wasa 31 da su ka buga, yayinda Heartland Owerri ke matsayi na...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce Iran ba ta neman yaki da kowace kasa, amma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare kanta saboda tana da kyakkyawan shiri a kan hakan. Da yake magana a wata tattaunawa ta wayar tarho da yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta shiga yin shawarwari don warware wasu matsaloli, bisa maslaha da mutunta juna, inda ya kara da cewa: “Ba ma neman yaki da wata kasa, amma ba mu da wani shakku wajen kare kanmu, kuma mun riga mun shirya tsaf dangane da hakan.” Shugaba Pezeshkian ya mika sakon taya murna ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya,...
Mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Ogun, Tunde Oladunjoye, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Afrilu, 2025, yayin da yake jinya a ƙasar waje kan wata rashin lafiya da ba a bayyana ba. An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi Iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa, inda suka bayyana shi a matsayin mutumin kirki kuma jajirtacce. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda Oladunjoye ke yi wa aiki a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce rasuwarsa babban rashi ne. Ya ce Oladunjoye mutum ne mai kishin jam’iyya, jajirtacce, kuma ya taka rawar gani...
Dubun-dubatar al’ummar kasar Aljeriya sun gudanar da wani gagarumin gangami da jerin a wannan Juma’a a birnin Algiers babban birnin kasar, domin yin Allawadai da laifukan yaki da Haramtacciyar Kasar Isra’ila take aikatawa a kan al’ummar yankin zirin Gaza. Kamar yadda kungiyar Movement of Society for Peace ta yi kira, dubban ‘yan kasar Aljeriya ne suka fito domin nuna goyon baya ga al’ummar Palasdinu a gaban hedikwatar jam’iyyar da ke unguwar al-Mouradia, babban birnin kasar Aljeriya. Sai dai hukumomin Aljeriya sun kewaye masu zanga-zangar don hana fadada zanga-zangar zuwa wuraren da jama’a ke taruwa. Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken nuna rashin amincewarsu da kisan kiyashin da “Isra’ila” ke yi a Gaza, inda suka yi Allah wadai da saka...
Cibiyar da ke sa ido kan tsattsauran ra’ayi da ke karkashin cibiyar ilimi ta Al-Azhar ta Masar, ta fitar da wata sanarwa da ta yi kira da a kame firaministan Haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a matsayin mai laifin yaki. Shafin sawtbeirut.com ya bayar da rahoto kan sanarwar da ke cewa, cibiyar yaki da tsattsauran ra’ayi ta Al-Azhar, ta yi Allah wadai da tarbar da kasar Hungary ta yi wa firaministan Isra’ila, wanda ke fuskantar sammaci na kasa da kasa da kotun ICC ta bayar, ta kuma sanar da cewa: “Manufar wannan mataki shi ne tauye matsayin kotun kasa da kasa da kuma keta hurumin ta.” Sanarwar ta ce: Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa alama ce ta...
An kashe wani kusa a kungiyar Hamas Hassan Farhat, wanda aka fi sani da Abu Yasser, da wasu mutane biyu a wani hari da jiragen yakin Isra’ila suka kai a wani gida a birnin Sidon, dake kudancin kasar Lebanon, a safiyar jiya Juma’a. A cewar Al-Mayadeen, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wani hari ta sama kan wani gida da ke birnin Sidon da ke kudancin kasar Lebanon, inda harin ya kashe babban kusa na Hamas Hassan Farhat da wasu mutane biyu daga cikin iyalansa. A cewar rahoton, sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari a Al-Naqoura, Nabatiyeh, da Sidon a kudancin kasar Lebanon a yammacin ranar Alhamis, inda suka yi barna a yankunan da aka kai harin....
A wani muhimmin mataki na karfafa zaman lafiya da sulhu, gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da kwamitocin zaman lafiya da sulhu a kananan hukumomin Jahun da Miga. A lokacin bikin kaddamarwar, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, ya bayyana aikace-aikacen da aka dora wa kwamitocin. Ya jaddada bukatar kwamitocin su gano musabbabin rikice-rikicen da suka addabi wasu sassan yankunan. A cewarsa, wannan mataki yana nuna kudurin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummar jihar. Ya ce an dora wa kwamitocin nauyin tantance tasirin wadannan rikice-rikice a tsakanin iyalai daban-daban, bayar da shawarwari masu inganci, tare da sanar da gwamnati duk wani muhimmin abu da ke bukatar daukar mataki. Malam Bala Ibrahim ya ce,...
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Juma’a, ta haramta wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio tattaunawa da manema labarai yayin da ’yar majalisar ta shigar da ƙara a gaban kotu. Mai shari’a Binta Nyako ce ta yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan ƙorafin da lauyan da ke kare Akpabio ya yi cewa Natasha na bin daga wannan gidan talabijin zuwa wancan, don tattaunawa da manema labarai kan shari’arsu, duk da cewa batun yana gaban kotu. ’Yan sanda ku yi amfani da iko cikin adalci — CP Wakili An ceto yara ’yan Taraba da aka yi safararsu zuwa Kudu Kotun ta ce daga yanzu babu wani ɓangaren da zai tattauna da manema labarai...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan birnin Tehran Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi Fard; Duniyar musulmi tana fuskantar jarabawa mai girma da ita ce kare al’ummar Falasdinu, da takawa masu girman kai na duniya birki,haka nan ‘yan Sahayoniya ‘yan daba. Limamin na birnin Tehran ya jaddada muhimmacin fuskantar ‘yan sahayoniya ‘yan daba a cikin wannan yankin na yammacin Asiya. Limamin ya tabo zagayowar ranar kafa tsrin jamhuriyar musulunci na Iran da kaso 98% na al’ummar kasar su ka kada kuri’ar amincewa da shi a 1979, yana mai jaddada cewa an kafa tsarin jamhuriya a Iran ne bisa koyarwa ta musulunci.
Ta ce, “Abin da nake gani shi ne, INEC na taimaka wa masu shigar da kara kan yadda za su kammala ayyukansu na haram. “Wannan shi ne karon farko da aka gabatar da koken, ba su da adireshi, lambobin waya, duk da hana amma INEC ta shiryar da su yadda za su gabatar da bayanan da za su kammala kokensu. “Masu shigar da kara, ‘ya’yan jam’iyyar APC a yanzu suka mika takarda mai dauke da adireshin da babu shi domin ganin an yi min kiranye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Ya kara nuna shakku kan dalilin da ya sa aka kafa dokar ta-baci a Jihar Ribas, yana mai cewa rashin tsaro ya addabi wasu sassan kasar nan, amma ba a kakaba dokar ta-baci ba ko kuma wani abu makamancin haka. “Idan shugaban kasa ya ce saboda rashin tsaro ne, saboda sun fasa bututun mai, yaya batun sassan kasar da ake fama da rashin tsaro? Shugaban kasar yana cewa su ma su kafa masa dokar ta-baci a kansa. Ba za su iya ba, saboda shi shugaban kasa ne da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, babu wanda zai iya sanya masa dokar ta-baci, saboda akwai rashin tsaro mai tsanani a arewa maso gabas, arewa maso yamma, hatta a kudu maso gabas da...
Adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren baya-bayan nan a ƙaramar hukumar Bokkos da ke Jihar Filato ya kai 52 kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana. Hakan ya biyo bayan sake gano wasu gawarwaki 40 ne a ranar Laraba da Alhamis da daddare yayin da masu aikin ceto suka ci gaba da kutsawa cikin dazuka don nemo waɗanda suka ɓata. Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno Yadda aka yi jana’izar Dokta Idris Dutsen Tanshi a Bauchi Shugaban Ƙungiyar al’adu ta Bokkos Cultural Development Council (BCDC) Vanguard, Farmasum Fuddang, ya shaidawa tashar Talabijin Channels cewa an yi jana’izar mutane 31 a ranar Alhamis tare da wasu yara biyar da suka ƙone ƙurmus a ƙauyen Hurti. An kashe...
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz. Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike Ya je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan. Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa. An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village. Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa...
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar shahararren malamin addinin Musuluncin nan kuma Babban Limamin Masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi da ke Bauchi, Sheikh Dokta Idris Abdulaziz. Malamin ya rasu ne a ranar Alhamis a gidansa da ke Bauchi bayan fama da doguwar rashin lafiya. Kotun ƙoli ta sauke Julius Abure daga shugabancin jam’iyyar LP Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike Ya je ƙasashen Masar da Saudiyya domin neman magani kafin watan Ramadan. Tun da safiyar ranar Juma’a, ɗaruruwan ɗalibansa da mabiyansa daga Bauchi, maƙwabtan garuruwa da kuma wasu jihohi sun taru a gidansa domin halartar jana’izarsa. An gudanar da sallar jana’izar a ranar Juma’a a filin Idi na Games Village. Manyan malamai, ’yan siyasa, ’yan uwa...
Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama. Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin. An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba. Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu. A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman ya taya shi murnin salla karama ya kuma yiawa dukkan kasashen musulmi fatan alkhairi. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, JMI bata neman yaki da kowa amma kuma a shirye take ta kare kanta a duk lokacinda wani ya takaleta. Pezeshkiyan ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya ne, kuma wannan kamar ydda hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA ta tabbatar. Banda haka kamar yadda yake a shekarum baya, hukumar zata ci gaba da bincike don tabbatar da hakan. A wani bangare na maganarsa shugaban...
Jakadan kasar Iran a cibiyoyin MDD a kasashen Turai ko Geneva Ali Gahraini ya yi tir da amincewar da hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta yi da zargin kasar ta take hakkin bil’adama a taronta na baya-bayan nan abirnin Geveva. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baraini yana cewa, hukuncin da hukumar ta yanke a kan JMI na son zuciya ne kuma saboda siyasar JMI a duniya ne. Bahraini ya kara da cewa, wannan hukuncin ya taba mutucin hukumar ta yin adalci ga wasu kasashen a duniya. Bahraini ya kara dan cewa, abin mamakoi shigha ba’a taba jin wannan hukumar ta yankewa HKI irin wannan hukuncin ba, duk tare da cewa duk duniya tana ganin yadda...
“Malam bisa kyakkyawar mu’amalarsa duk da cewa ya kasance dodon yaki da Bidi’a ba zallar almajiransa ba ne suka halarci wannan jana’izar ka ga dai jama’a to ko’ina. Muna kyautata masa zato duk da an ce da kalmar shahada ya cika,” Aminu Sani, wani almajiransa. Daga cikin wasiyoyin da Malamin ya yi sun haɗa da bai yarda da ɗauke-ɗauken hotuna wajen Janazarsa ba; babu zaman Makoki; ba turereniya wajen ɗaukar gawarsa sannan kuma babu shiga makabarta da takalmi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yayin gabatar da rahoton an raba lambar yabo ga Hakiman da aka fi samun gudunmawar Zakkar daga gundumominsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dokta Hakeem Baba-Ahmed, ya yi murabus daga matsayin mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa. Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da cewa ya aike da takardar murabus ɗinsa kimanin makonni biyu da suka wuce, inda ya ce dalilansa na ƙashin kai ne. Batun na yanke jiki na faɗi ƙarya ce — Wike NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Har yanzu ba a tabbatar da ko fadar shugaban ƙasa ta amince da murabus ɗin ba. An naɗa Baba-Ahmed a watan Satumban 2023 a matsayin mai bai wa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, shawara kan harkokin siyasa. A lokacin da yake riƙe da muƙamin, ya wakilci gwamnati a taruka da...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje. Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta Fitaccen malami Dokta Idris Dutsen Tanshi ya rasu Wike, ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Alhamis yayin da ya kai ziyara wajen wani aiki da ake shirin ƙaddamarwa a watan gobe domin bikin cikar Shugaba Bola Tinubu shekara biyu a mulki. A wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Anthony Ogunleye, ya fitar, Wike ya ce waɗanda ke yaɗa wannan labari suna ƙoƙarin...
Jiragen yakin Isra’ila sun kai karin hare-hare ta sama kan kasar Siriya, inda suka bijirewa gargadin Majalisar Dinkin Duniya game da hadassa asarar fararen hula yayin da suke ci gaba da kai wa kasar ta Larabawa hare-hare. Rahotanni sun ce a ranar alhamis, jiragen saman Isra’ila sun kai hare-hare a kalla sau biyu a kan wuraren da sojoji a kusa da birnin Damascus, inda bayanai suka ce sun kai hari a yankunan Al-Kiswah da Al-Muqaylibah. Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka. Hare-haren sun zo ne kasa da kwana guda bayan hare-haren da Isra’ila ta kai makamancin haka inda ta kashe mutane 13. Fararen hula 9 ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani hari da jiragen...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi kira ga kasashe mambobi kungiyar hadin guiwa ta Shanghai da ta yi Allah wadai da barazanar Trump ta baya baya nan kan kasar. A taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da aka gudanar a birnin Moscow a ranar Alhamis, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht Ravanchi, ya yi kira ga mambobin kungiyar SCO da su yi Allah wadai da kalaman da shugaban na Amurka Donald Trump ya yi a baya-bayan nan kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, lamarin da ya ce yana da hadari. Majid Takht Ravanchi ya yi kakkausar suka ga barazanar harin bam da Trump ya yi a wata hira da tashar NBC News, inda ya ce, hakan ya keta...
Kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi Isra’ila game da harin da ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan ceto a Gaza yana mai cewa hakan zai iya kasancewa ‘lafin yaki’. Ma’aikatan agaji 15 ne suka ras arayukan a wani kazamin hari da Isra’ila ta kai kan motocin daukar marasa lafiya a Gaza wada ya fiddo a fili irin ” laifuffukan yaki da sojojin Isra’ila suka kwashe tsawon lokaci suna aikatawa a zirin Gaza”. Kafin hakan dama hukumar kula da hakkin bil adama ta MDD ta amince da kudurin dake kira ga Isra’ila da kada ta aikata kisan kiyashi a zirin Gaza. An amince da kudurin ne ranar Laraba yayin taron hukumar na 58, bayan ya...
Fitaccen malamin addinin Islama da ke Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ya riga mu gidan gaskiya. Almajiransa sun tabbatar wa Aminiya cewa ya rasu ne a gidansa da ke Bauchi inda za a yi jana’izarsa a safiyar wannan Juma’ar. Malamin ya yi fama da rashin lafiya inda gabanin watan Ramadana ya fita neman magani a ƙasashen Masar da Saudiyya. Fitowarsa ta ƙarshe ita ce ranar Idin ƙaramar Sallah da ta gabata, inda ya yi huɗuba kan muhimmanci haɗin kai a tsakanin musulmi.
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare da wani tsohon Ambasada da sauran waɗanda ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su. Gobara ta lalata wani ɓangare na gidan Ado Bayero Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Aminiya ta ruwaito yadda aka yi garkuwa da tsohon shugaban Hukumar NYSC daga mahaifarsa a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina, a ranar 5 ga Fabrairu, 2025. Da yake jawabi gabanin miƙa su a...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito, da mutunta juna ta yadda bangarorin za su ci moriyar juna. Guo ya bayyana hakan ne a taron manema labarai na yau, a matsayin martani ga wata tambaya game da sanarwar da Washington ya yi na kakaba “harajin ramuwar gayya” kan manyan abokan cinikiayya. Yana mai cewa, a karkashin manufar “ramuwar gayya”, Amurka ta sanya karin harajin fito kan kayayyakin da ake fitarwa daga kasar...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari idan har ta kasa cimma matsaya da Washington kan shirinta na nukiliya. Ryabkov ya ce, “Hakika ana jin barazanar, ana kuma jin bayanai kan abubuwan da suka dace,” in ji Ryabkov, yana mai cewa “Sakamakon hakan, musamman idan harin ya kasance kan kayayyakin nukiliya, na iya zama bala’i ga daukacin yankin.” Ya ce sabbin kalaman na Trump za su kara...
Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree ya tabbatar da cewa, sojojin Yaman sun gudanar da wani shiri na soji na hadin gwiwa, inda suka yi arangama da jirgin ruwan Amurka Harry Truman da jiragen yakin da yake dauke da su a arewacin tekun Bahar Maliya. Saree ya ci gaba da cewa, a harin an yi amfani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuka, kuma harin...