2025-04-19@01:20:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1328

«Allah Ya ba»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Sarkin tare da tawagarsa sun fita a ciki jerin gwanon motoci zuwa gidan gwamnati, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya tarbe su. Bikin bana ma ya sha bamban da na baya, domin an sauya hanyoyin da ake bi a baya. Duk da hakan, jama’a da dama sun fito suna murna da jin daɗi yayin da motocin Sarkin ke wucewa. Duba hotunan hawan a ƙasa: Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi. Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin. HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi “A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na...
    Wasu gidajen na ‘yan kasuwa ma sun bi sahu wajen ƙara farashi, wanda hakan ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziƙi. A halin yanzu, hauhawar farashin man fetur na nufin za a ƙara kudin sufuri da kuma farashin kayan masarufi, wanda zai ƙara jefa al’umma cikin kunci. Masana harkar man fetur sun yi gargaɗin cewa, idan ba a magance rikicin da wuri ba, farashin mai na iya haura Naira 1,000 a wasu yankuna. Gwamnatin Tarayya ta taɓa bayar da umarni cewa a sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da Naira domin daidaita farashin mai, amma yarjejeniyar ta ƙare a watan Maris 2025. A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya. A yayin da...
    Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita. Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane...
    Haka kuma, an Ƙwato bindiga ƙirar gida da Naira miliyan 4.84 da ake zargin kuɗin fansa ne. An ceto Dokta Yushau ba tare da wata matsala ba. A wata arangama daban, jami’an ‘yansanda sun kama wani Kafinta Musa a Jihar Taraba bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. An ƙwato bindiga ƙirar AK-49 a hannunsa, kuma ana ci gaba da bincike don kama sauran miyagun da ke tare da shi. Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da wannan aikin tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka. Daga kanmu, magana...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.   Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.   Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
    Game da aka yi wa mafarauta 16 a Udune Efandion, karamar hukumar Uromi ta jihar Edo, gwamna Monday Okpebholo ya yi kakkausar suka ga wannan aika-aika na rashin hankali, yana mai bayyana hakan a matsayin “wani abu da kuma muguwar dabi’a.     Okpebholo, tare da Gwamna Abdullahi Yusuf na Jihar Kano, sun yi addu’a ga rayukan wadanda abin ya shafa a kauyen Bunkure na jihar Kano inda wadanda abin ya shafa suka fita tare da kuma da bada tabbacin ga iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a gurfanar da masu laifin gaban kuliya.   Allah wadai da gwamnan ya biyo bayan harin da wasu gungun ’yan bindiga suka kai wa mafarautan, wadanda aka yi kuskuren cewa masu garkuwa...
    Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Okpebholo bisa tattaunawarsa da shugabannin al’ummar Hausa a Edo domin hana rikici da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan. “Biyan diyya da aka alƙawarta abu ne mai kyau, amma dole ne a tabbatar da hakan cikin gaggawa domin taimaka wa iyalan da suka rasa masu ɗaukar nauyinsu,” ya ƙara da cewa. A nasa ɓangaren, Gwamna Okpebholo ya nuna matuƙar damuwarsa kan wannan kisa, inda ya tabbatar da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata laifin. “Ina samu labarin abin da ya faru, na garzaya zuwa Uromi. Na gana da al’ummar Hausa a wajen, kuma mun yi ƙoƙarin kwantar da tarzoma. “Ina tabbatar muku da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa,”...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa “ Amnesty International” ta zargi fira ministan HKI da cewa, mai aikata laifin yaki ne, da kuma amfani da yunwa a matsayin makamin yaki akan fararen hula. Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta bayyana cewa a cikin ganganci Netanyahu yake kai wa fararen hula harer-hare da kuma aikata laifuka akan bil’adama. Haka nan kuma kungiyar ta yi gargadi akan ziyarar da Netanyahu zai kai wata kasa daga cikin wadanda su ka rattaba hannu a yarjejeniyar kafa kotun duniya ba tare da an kama shi ba. Kungiyar “Amnesty Interational” ta ce rashin kama Fira ministan na HKI zai kara ba shi karfin gwiwar ci gaba da aikata laifuka. Dangane da gayyatar da kasar...
    Gwamna Okpebholo ya bayyana takaicinsa kan lamarin, yana mai cewa tuni an kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za su fuskanci hukunci. Bayan tattaunawa, Gwamna Abba ya jagoranci Gwamna Okpebholo zuwa ƙaramar hukumar Bunkure don jajanta wa iyalan mamatan. Gwamnan Edo ya sha alwashin ganin an yi adalci ga mamatan da iyalansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al-Qur’ani mai girma a cikin suratul Baqarah, Allah Ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharuɗan azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha faɗi, wannan wata na ɗauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika, hadisai sun ruwaito falalar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, watan da ke biye da Ramadan. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar da ke akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Litinin, hukuma mai kula da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare, ta bayyana cewa, yanzu haka ana share fagen gudanar da bikin yadda ya kamata, inda yawan fadin shagunan da kamfanoni daban-daban suka kulla kwangilolin baje kolin kayayyakinsu a ciki ya kai muraba’in mita dubu 240, kuma ya kai 2/3 na fadin wurin da aka tanada. Bikin nan da za a gudanar da shi a karo na 8, zai samu ci gaba a bangarori hudu. Na farko, za a tabbatar da fadin wurin bikin da ya kai muraba’in mita dubu 360, don baje kolin kayayyakin zamani. Na biyu, za a samar da dandaloli masu kyau ga mu’ammalar jami’an gwamnati da ‘yan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai martaba Sarkin Lere dake Kaduna Alhaji Sulaiman Umaru ya amince da nadin Sani Ahmed Lere Sardaunan Matasa zuwa Falakin Lere.   Hakan na kunshe ne a cikin takardar nadin da Sakataren Majalisar kuma Sadaukin Lere Alhaji Muhammad Lawal Ahmed ya sanya wa hannu. Alhaji Muhammad Lawal Ahmed yace sabon nadin ya fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa nadin Sani Ahmed Lere a matsayin Falakin Lere daga matsayinsa ne daga Sardaunan Matasan Lere wakilin Matasa a Masarautar zuwa Falakin Lere dan Majalisar Sarki kuma PPS ga Sarki.
    Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike. A yayin ziyarar, Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun...
    Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron. Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a kokarin da kwamitin ya yi na kiyaye muhalli. Dole ne a nace ga jagorancin da JKS ta bayar a wannan bangare, da ma sauke nauyin dake wuyan hukumomin wurare daban-daban karkashinta. Taron ya kuma jadadda cewa, ya kamata a kara karfin sa ido a siyasance, da mai da hankali kan yadda ake tabbatar da manufofi da tsare-tsaren kwamitin, ta yadda za a ba da tabbaci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban.   A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda ’yan banga suka tare su. Daga nan ne, shugaban ‘yan bangar ya fara yi wa direban tambayoyi game da kayan da ya dauko da kuma fasinjojin sa. Duk da gabatar da takardar sahalewar hanya amma shugaban ‘yan bangar ya nuna zargi kan mafarautan, musamman saboda makamansu da karnukan da su ke tare da su a cikin motar.   Saboda haka, “Shugaban ‘yan bangar bai amince...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan Tehran dubban daruruwan mutanen suka fito zuwa babbar masallacin Imam Khumaini dake tsakiyar birnin Tehran inda suka gudanar da sallah mai raka’o’I biyu tare da jagorancin Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Imam Sayyid Aliyul Khamina’e. Duk da cewa ana samun babbanci tsakanin musulmi kan ranar ajiye azumun amma akalla ba wanda zai yi azami kasa da kwanaki 29. A cikin watan dai, musulmi...
    Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan daga baya ya sauka don ya sake dawowa da hanyar zabensa ya fara yakin neman zabe a jiya, inda yake kira ga mutanen kasar su zabe shi saboda kyautatuwar kasar Gabon. A cikin watan Augustan shekara ta 2023 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya gaji babansa Umar Bongo bayan rasuwarsa ba tare da zabe ba. A halin yanzu dai yan takara...
    Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko ta fannin a duniya. Har wa yau, daga cikin tashoshin jiragen ruwa 10 da suka fi hada-hadar kayayyaki a duniya, akwai tashoshin jiragen ruwan kasar Sin guda 8, ta fannin hada-hadar kwantenoni kuma, guda 6 na kasar Sin ne. (Mai fassara: Bilkisu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
    Watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo ni’imomi masu Yawa wanda matasa da sauran mutanen kasa sun amfani da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’I mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu. Amma a wani bangare a cikin wannan Ramadan, duk tare da jin dadin da muka samu, amma watan yana tattare da dacinsa, kissan mutanen Falasdinu, tare da goyon bayan Amurka. Kasashen yamma suna tuhumar Iran tana amfani da sojojin wadanda suke wakiltantan a abinda yake faruwa a yankin. Amma gaskiyar al-amarin sune suke da wakili a wannan yakin, kuma itace HKI, wacce taek wakiltansu a ayyukan ta’addanci da take yi...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka amsar wasikar da ta aiko mana, inda a cikinta, muka kara jaddada cewa babu wata tattaunawa kai tsaye da Amurka, kuma an tura wasikar ta inda na Amurkan ta fito wato ta kasar Omman. Don haka muna jiran matakan da Amurka zata dauka a kan amsar. Daga karshe shugaban ya kammala da cewa duk wata mu’amala da gwamnatin kasar Amurka ba zai taba yiyuwa kai...
    Asbitin ‘Mount Sinai’ (Dotsen Sinaa’ a kasar Amurka ta salami wata likita daga aiki, bayan da aika da wani rubutu da hoto a shafukan yanar gizo tana, wanda Asbitin tana cewa ai Musanta hare-haren ranar 7th ga watan Octoba ne’. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta bayyana cewa Dr Leila Abbasi,diyar shekara 46 a duniya, ta aika sako cikin shafinta na yanar gizo inda take goyon bayan kungiyoyin Hamas da Hizbullah na kasar Lebanon sannan tana allawadai da kuma aibata HKI kan kissan yara da take yi a Gaza.   Gwamnatin kasar Amurka dai tana ganin kanta a matsayin kasa wacce take gaba wajen kare hakkin fadin albarkacin baki, amma idan al-amarin ya shafi HKI sai ta nuna...
    Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har  13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har da Yankunan  Malikah da Sarf na birnin San’aa babban birnin kasar. Wasu kafafen yada labaran kasar Yemen sun bayyana cewa, kafin haka jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare a kan kasar ta Yemen wadanda suka kai ga shahadar fararen hula 12 da kuma raunata wasu 2 a birnin San’aa babban birnin kasar. Washington ta bada sanarwan cewa ta na kai hare-haren don tabbatar da tsaron...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya taya al’ummar Musulmi murna bisa kammala azumin watan Ramadan lafiya, tare da kira garesu da su rungumi koyarwar Annabi Muhammadu (S.A.W) a cikin rayuwarsu ta yau da kullum. Ya bayyana hakan ne a sakon sa na Sallah ga al’ummar jihar. Malam Umar Namadi ya yi addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya karɓi azumi da addu’o’in al’ummar Musulmi da suka yi a watan  na Ramadan. Haka kuma, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da yi wa  shugabanni jagorancin  don yin abin da ya dace domin jin daɗin al’umma. Namadi ya kuma yi addu’ar samun  zaman lafiya, da hadin kai, da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. ...
    Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 20, Usman Sagiru, bisa zargin kashe wani ɗan Bijilanti a tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bayan Sallar Eid. Iftila’in ya faru ne da ƙarfe 12:40 na rana a Lahadi, lokacin da ayarin Sarkin Kano ke watsewa daga filin Sallar Idin. A cewar kakakin Ƴansanda SP Haruna Kiyawa, ana zargi Sagiru da wasu da suka tsere da soka makami ga wani ɗan sa kai mai suna Surajo Rabiu daga unguwar Sabon Titi Jaba, wanda ya mutu sakamakon raunin. Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II Wani ɗan Bijilanti, Aminu Suleman daga...
    Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare. Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru. Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi. Dangane da...
    Akwai karin tawagogin ceto da dama na kasar Sin da suka shiga ayyukan ba da agaji tare da takwarorinsu na Myanmar. Girgizar kasar mai karfin maki 7.7 ta afku a kasar ce da ke kudu maso gabashin Asiya, a ranar Jumma’ar da ta gabata. A jiya Asabar da dare, tawagar yada labarai ta majalisar gudanarwar kasar ta bayyana cewa, sama da mutum 1,700 ne suka mutu, kana sama da 3,400 suka jikkata, yayin da kuma kimanin 300 suka bace, a kakkarfar girgizar kasar da ta faru a kasar ta Myanmar. A yinin yau Lahadi kuma, wani jirgin saman kamfanin China Eastern Airlines ya tashi daga Kunming, babban birnin lardin Yunnan na kudu maso yammacin kasar Sin, dauke da kayayyakin agaji...
    Mai martaba Sarkin zazzau,kuma shugaban majalisar sarakunan jihar kaduna, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya bukaci Dagatan da ke masarautar zazzau da su rinka sanya ido sosai akan zirga-zirgar bakin fuskokin da ba su gane ba a cikin su. Ya yi kiran ne a sakon sa na sallah bayan kammala azumin watan Ramadan a fadar sa dake Zaria. Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana cewa harkar tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a hakki ne na kowa amma ba gwamnati ita kadai ba,a don haka akwai bukatar ganin an hada karfi da karfe domin samun nasara a game da tsaron. Mai martaba Sarkin ya kuma bukaci Dagatan da su rinka kai rahoton zuwan duk wani bako ko bakuwa da kuma dalilin zuwan. Ya ce...
    Ya ce: “Ya ‘yan uwa Musulmi na Jihar Zamfara da ma sauran wurare, ina miƙa saƙon barka da Sallah tare da taya mu murnar kammala azumin shekarar Hijira ta 1446, wannan wata mai alfarma ta kasance lokaci na sadaukarwa ga Allah (SWT).   “Yayin da muke gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah, ina kira ga kowannenmu da ya ci gaba da ayyukan ƙwarai, da haƙuri, da karamcin da aka yi a watan Ramadan.   “Ƙalubalan da ke gabanmu suna da yawa kuma suna buƙatar haɗin kai don ganin an magance su, don haka mu ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu yi aiki tare a matsayin al’umma ɗaya, mu goyi bayan ajandar gwamnati na ceto da sake gina jiharmu.   Gwamna Lawal...
    Sarkin Kano mai daraja ta daya wanda ya bayyana zaman lafiya a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, don haka, ya amince da janye duk wasu shirye-shiryen bikin hawan Sallah mai ban sha’awa, wanda ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da al’adu (UNESCO) ta bayyana a matsayin gadon bil’adama mara misaltuwa.   LEADERSHIP ta rawaito cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya sanar da dakatar da bikin hawan Sallah, saboda barazanar tsaro da jami’an leken asiri suka rahoto a jihar.   Dangane da haka, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda...
    A jiya Asabar dubun dubatar ‘yan hamayyar siyasa su ka yi gangami a birnin Stanbul bayan da jam’iyyar “National Party” ta gayyace su, domin ci gaba da yin tir da kamun da aka yi wa Akram Imam Uglu wanda shi ne magajin garin na Stanbul. Shugagan jam’iyyar “Turkish National Party’ ta adawa, Uzgur Ozil ya bayyana cewa adadin wadanda su ka halarci gangamin sun kai miliyan 2.2. Daga cikin mahalarta gangamin da akwai mata da mahaifan Akram Ima wadanda su ka rika bayar da taken cewa za a ci gaba da yin gwgawarmaya ako’ina.” Tun da asubahin jiya Asabar ne dai mutane su ka fara yin tururuwa a cikin birnin na birnin Sitanbul suna dauke da tutocin turkiya da kuma...
    A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30. Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya. Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama. A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi. Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan...
    Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite. Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba. Kafin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban majalisar dokokin kasar Fiji Filimone Jitoko, ya ce yadda kasar Sin ta samar da nagartattun manufofi, da samun nasarar kawar da fatara, da inganta tsarin dimokradiyya, ta yadda za ta shafi dukkan bangarorin zaman al’umma, sun kasance abin koyi ga kasarsa. Filimone Jitoko, ya bayyana hakan ne kwanan nan yayin zantawarsa da wata wakiliyar CMG a birnin Beijing, lokacin da ya ziyarci kasar Sin a karon farko, inda ya ce ziyarar ta ba shi damar samun karin ilimi, da kuma yin tunani mai zurfi. Ya kara da cewa, kasar Fiji na godiya ga kasar Sin bisa yadda take fahimtar bukatun kananan tsibiran dake yankin tekun Pasifik ta fuskar tinkarar sauyin yanayi, kuma Fiji na fatan zurfafa hadin gwiwa da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rikicikin ya turnuke jam’iyyar SDP a yayin da aka samu shugabanni bangare biyu a Jihar Kogi, rikicin ya kunno kai ne bayan da wani bangare ya kaddamar da kwamitin gudanarwa a Lakwaja. Taron da aka gudanar a sakateriyar jam’iyyar na jihar, an zabi tsohon shugaban sashi na APC, Hon. Ahmed Attah a matsayin sabon shubagaba, tare da Alhaji Idris Sofada a matsayin sabon sakatare na jam’iyyar a jihar. Wakilai 3,890 ne daga kananan hukumomi 21 na jihar suka zabi shugabanni 21 na jam’iyyar. Sannan kuma jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) sun kasance a wannan wuri lokacin zaben. A jawabinsa na farko, Attag ya yi alkawarin zai yi gaskiya da adalci tare da daga martabar jam’iyyar SDP...
    Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia. Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa. Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu. “Kamar yadda aka...
    Kungiyar JIBWIS a Karamar Hukumar Giwa ta bukaci al’ummar Yakawada da su ci gaba da rungumar koyarwar Al-Qur’ani a rayuwarsu ta yau da kullum. Mataimakin Shugaban kungiyar, Malam Ibrahim Mustafa Shatiman Giwa, ya yi wannan kira ne yayin bikin rufe Tafsirin Ramadan na bana da aka gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Yakawada. Malam Ibrahim Mustafa ya bayyana jin daɗinsa kan goyon baya da jajircewar al’ummar Yakawada a duk tsawon Tafsirin. Ya jaddada muhimmancin kiyaye darussan da aka koya a cikin Ramadan tare da amfani da su a rayuwa bayan karewar watan mai alfarma. A nasa jawabin, Sheikh Suleman Abdulkarim Fatika ya nuna godiyarsa ga dukkan mahalarta Tafsirin da suka daure suka halarta tun daga farkon watan Ramadan...
    ’Yan Sanda sun kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan matafiya 16 ’yan Arewa a kan titin Uromi zuwa Obajana, a Jihar Edo. Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya yi tir da wannan hari, kuma ya bai wa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Hedikwatar Rundunar da ke Abuja, yin bincike. Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki An cafke mutum 19 bayan arangama tsakanin sojoji da ’yan shi’a a Abuja Bayan faruwar lamarin, rundunar ’yan sandan Jihar Edo, ta tura jami’anta zuwa yankin domin wanzar da zaman lafiya. Har ila yau, ana ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere. Kakakin rundunar ’yan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya ce Sufeto-Janar ya ba da...
    Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...
    Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can. Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen...
    Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a cikin tekun farisa wanda aka sanyawa suna Shahid Baghiri mai kuma  tsawon mita 180. Sannan   Labarin ya kara da cewa gwamnatin shugaba Donal Trump na kasar Amurka ta bawa Iran razarar watanni biyu ta amince da zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ta yi shirin yaki da kasar ta Amurka. Dakarun...
        Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta yi ala wadai da kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, Jihar Edo, a ranar 28 ga Maris, 2025.   Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano lokacin da aka kai musu farmaki, aka sare su, sannan aka banka musu wuta a abin da gidauniyar ta bayyana a matsayin abin “aikin rashin imani” na tashin hankali bisa la’akari da bambancin kabilanci.   A cikin wata sanarwa da Darakta-Janar na gidauniyar, Injiniya Dakta Abubakar Gambo Umar, ya fitar, gidauniyar ta nuna damuwarta kan yadda hare-haren da ake kai wa ‘yan Arewa ke ƙaruwa a wasu sassan Kudancin kasan nan, tana...
    Wannan ya sa murnar da wasu ke yi ta komawa da haska finafinan Hausa masu dogon zango a tashar YouTube ta fara komawa ciki. Me ya sa ba a gamawa din? BBC Hausa ta ci gaba da cewa wani faifan bidiyo na wata tattaunawa da jagoran shirin Izzar so, Ahmad Lawan ya yi a tasharsa ta Bakori TV, ya ce masu kallo ne ba su gaji da kallon shirin ba, shi ya sa ba zai daina ba. Ya ce kasancewar Youtube ya dade kudu, amma bai je arewacin Nijeriya ba ne ya sa su ka gwada domin su koya wa mutanen arewa kallon fim a YouTube, shi kuma wannan fim din ya na ciki, ko in ce shi ne daya...
    Ya kara da cewa cire Jami’oi daga tsarin albashi na (IPPIS),wanda hakan ne ya ba su Jami’oin tsayawa da kansu kan lamarin da ya shafi ayyukansu wanda har ila yau hakan ya sa ayyukamsu suka kara ingantuwa. Wike ya yi karin bayani,“akwai maganar amincewa da maganar kudaden bincike na Hukumar TETFund a cikin wasu makarantu, hakan ya kar bunkasa lamarin daya shafi bincike  da kirkiro wasu abubuwa.” Su wadannan lamurran na ci gaba sun kara daidaita Jami’oi su maida hankali kan ilimin da suke samarwa domin  ya cimma matsalolin da ake fuskanta a karni na ashirin da daya. da yake bayyana yadda ya ji dangane da karramawar da Hukumar Jami’ar kalaba ta yi masa na ba shi digirin digirgir,Wike ya...
    Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai  cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu. An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin shugaban kasa na farko Riek Machar daurin talala a cikin gidansa. Babban magatakardar MDD ya yi kira ga ‘yan siyasar kasar ta Sudan  ta Kudu da su ci gaba da riko da yarjejeniyar sulhu da zaman lafiya,inda ya ce: “ A dawo da gwamnatin hadin kan kasa, da aiki da alkawullan da aka yin a zaman lafiya da sulhu, da hakan ne kadai hanyar dawo...
    Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya bayyana sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da yake ziyarar aiki a kasar Guyana da cewa, sakarai ne. A yayin ziyarar da sakataren na  harkokin wajen Amurka ya kai zuwa kasar Guyana mai makwabtaka da Venezuela, ya ce, Amurka za ta mayar da martani mai karfi akan Venezuela idan har ta kai wa Guyanan hari. Rubio ya kara da cewa; Idan haka ta faru, to kuwa Venezuela za ta gwammace kida da karatu a wannan rana. Amurkan dai ta kulla yarjejeniyar tsaro da kasar ta Guyana a yayin ziyarar da Rubio ya kai. Shi kuwa shugaban kasar ta Venezuela da yake mayar da martani ya ce; Marco Rubio wawa, ya zo yana yi wa...
    Yau Juma’a, shugaban babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG Shen Haixiong, ya gana da ministar raya al’adu ta kasar Rasha Olga Lyubimova dake ziyara a kasar Sin. Shen Haixiong ya ce, yana maraba da Rasha ta shiga a dama da ita cikin bikin fina-finai na kasa da kasa da 0za a yi a kasar Sin a bana. A nata bangare, Olga Lyubimova ta ce, a shekarun baya bayan nan, Rasha da Sin suna kara musaya a fannoni daban-daban, ciki har da fina-finai, kuma sun samu kyawawan sakamako. Ta kara da cewa, tana fatan bangarorin biyu za su zurfafa hadin gwiwarsu. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma. A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma wanda ake samarwa a cikin kasar, ya ragu da tan miliyan 1.4. Kazalika, a gonar da ake noman Kwakwar Manja, za a iya samar da tan 12.5 a kowace hekta daya a duk shekara. Misali, a 2023 a heckta 20 a cikin shekara daya, an girbe Kwakwar da ta kai kimanin tan 250, inda akalla aka samu ribar kimanin Naira 150,000 na kowanne tan daya,...
    A yau Juma’a aka kammala taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na kasashen Asiya na Boao. Cikin kwanaki 4, kimanin wakilai 2,000 daga kasashe da yankuna sama da 60 ne suka hallara a lardin Hainan na kasar Sin tare da musayar ra’ayi mai zurfi karkashin jigon na “Gina makomar asiya a duniya mai sauyawa.” A matsayinta na mai masaukin bakin, kasar Sin ta gabatar da shawarwari 4 da suka yi daidai da ra’ayin mahalarta taron. Shawarwarin sun hada da karfafa hadin kai da hadin gwiwa wajen inganta aminci, da inganta dunkulewar tattalin arzikin duniya ta hanyar bude kofa da dunkulewa, da samar da ci gaba da wadata na moriyar juna, da kiyaye zaman lafiya da tsaro da zaman jituwa. Alkaluma sun...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Barcelona za ta yi asarar maki saboda saɓa dokar FIFA a wasanta da Osasuna Girgizar ƙasa ta kashe mutum 150 a Myanmar da Thailand Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Tuni dai gwamnatin Edo ta yi Allah wadai da lamarin wanda ya faru a ranar Alhamis...
    Shugaban ƙasar ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, da shugabannin al’ummar Uromi bisa matakin da suka ɗauka domin daƙile yiwuwar tashin hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da safiyar yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da wakilan da suka fito daga sassan masana’antu da cinikayya na kasa da kasa a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi ya jadadda cewa, a cikin shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama’ar Sin musamman ma cikin shekaru 40 da aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, Sin ta cimma gaggaruman nasarori wajen samun saurin bunkasuwar tattalin arziki da dorewar walwalar al’umma dogaro da jagorancin jam’iyyar kwaminis ta Sin wato jKS da kokarin al’ummar Sinawa cikin hadin kai, kuma ba za a raba wadannan nasarori da taimakon da kasashen duniya ke ba ta ba, cikin hadda gudunmawar da kamfanonin ketare dake kasar Sin suke bayarwa....
    Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Fred Itua, ya bayyana cewa waɗanda aka kashe sun fito daga Fatakwal, a Jihar Ribas, amma ‘yan banga sun ɗauka cewa ‘yan ta’adda ne. Gwamna Okpebholo ya kai ziyara wajen da lamarin ya faru, inda ya jaddada cewa za a gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta masu hannu a kisan. Amnesty International da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi kira da a tabbatar da an yi adalci. Gwamnan Edo ya yaba wa shugabannin Arewa bisa yadda suka kwantar da hankula tare da guje wa ɗaukar fansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp...
    A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki, musamman ma a irin wannan lokaci da ake samun tsadar rayuwa a cikin kasar nan. Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargadin cewa dokar ta-vaci na iya haifar da mummunan sakamako na tattalin arziki, tana mai jaddada muhimmancin da Jihar Ribas ke da ita ga tattalin arzikin Nijeriya da yankin Neja Delta gaba daya. Ta ce da ma can kasar nan ta riga ta fuskanci hauhawar farashi,...
    Kwankwaso ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da cewa an hukunta masu laifin. “Ina kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike a kan wannan lamari mai tayar da hankali tare da tabbatar da an hukunta masu hannu a ciki,” in ji shi. Tsohon gwamnan ya kuma miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, da gwamnatin Kano da sauran jihohin da abin ya shafa, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansu. Kisan ya haifar da cece-ku-ce kan hatsarin da ke tattare da ɗaukar doka a hannu, tare da buƙatar a ƙara inganta tsaro don hana irin haka faruwa a gaba. Jagororin siyasa da na al’umma da dama...
    Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin. Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba. Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke shirinsa na yin hawan, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne bayan shawarar da malamai da dattawa suka ba shi. “Muna tabbatar muku cewa hawan Sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, idan har zai haddasa tashin hankali, wajibi ne a dakatar,” in ji Aminu Ado Bayero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar. Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH CP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin. Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a...
    Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun  2025, wanda ya kai yawan Ganga  1,465,006 da ake hakowa a  kullum. A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a  gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Yadda Ake Ba Da Ita Ana ba da ita kafin a fita zuwa Sallar Idi ko kafin Ranar Sallah da kwana daya ko biyu. Abin da ake bayarwa shi ne Muddan Nabiyy (mudun awo ne dan madaidaici wanda za a iya auna shi da cikin tafukan hannun mutum mai matsakaicin tsawo) guda hudu a kan kowane mutum. Ana fitarwa daga dukkan nau’in abinci, kamar mu a nan mu ce shinkafa, masara, doya, dawa, dauro, cukwi, nono da duk dai abin da galibin mutane suke amfani da shi a matsayin abinci. Malaman kasar Maroko wadda kasa ce ta Malaman Musulunci kuma ‘yan’uwanmu ne Malikawa; sun yi fatawa cewa ya halasta a ba da kudi a madadin abinci a Zakkar. Za a...
    Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
    A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali. Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.” Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya  Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah. Yadda ake fitarwa Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda...
    Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano,m, ta ƙwato kuɗi Naira 4,850,000 tare da mayar da su ga wani mutum da aka sace, bayan sun ceto shi. A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an yi garkuwa da mutumin ne a garin Zakirai, a Ƙaramar Hukumar Gabasawa. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Lakurawa sun kashe jami’an Kwastam 2 a Kebbi Masu garkuwar sun fara neman kuɗin fansa Naira miliyan 15 kafin daga bisani jami’an tsaro suka shiga lamarin. “Bayan samun labarin garkuwar, jami’anmu sun ƙaddamar da bincike, inda suka kama mutum biyar da ake zargi, sannan suka ceto wanda aka sace a ranar 17 ga watan Maris,” in ji sanarwar....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada. A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini. NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Amma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah? Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
    Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa. He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin. Kuma kamfanonin sun yi nuni da cewa, babbar kasuwa, da cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki, da kuma karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin, dukkansu babbar dama ce a gare su, kuma zuba jari a Sin yana nufin cin gajiyar wannan dama. Bugu da kari,...
    Yau Alhamis, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da ministan kasar Faransa mai kula da harkokin Turai da sauran kasashen waje, Jean Noel Barrot a birnin Beijing. Yayin ganawar, Wang Yi ya ce a lokacin da duniya take fama da yanayi mai cike da sauye-sauye da hargitsi, ya kamata kasashen biyu su nuna sanin ya kamata a matsayinsu na manyan kasashe tare da karfafa hadin gwiwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na daukar Faransa a matsayin babbar abokiyar huldar cimma ci gaba mai inganci. A nasa bangare, Jean Noel Barrot ya ce Faransa ta kuduri niyyar raya dangantaka mai karko da dorewa da kyakkyawar makoma da kasar Sin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana...
    A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu. Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.8 na baki dayan lantarkin da tashoshin samar da lantarki na kasar Sin ke samarwa. Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai...
    Ana kuma sa ran tattaunawar za ta kunshi ci gaban yankin a cikin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, inda shugabannin biyu suka yi alkawarin ciyar da zaman lafiya da gudanar da mulkin dimokradiyya.   A baya, Mahama ya ziyarci shugaba Tinubu jim kadan bayan lashe zaben shugaban kasa a watan Disamba na 2024. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin da ake tunkarar bikin ƙaramar sallah, hankalin Musulmi a ko ina a duniya, ya karkata zuwa ga hidimar wannan rana ta musamman, musamman a fannin ado da sabbin kaya. A wata ziyarar da Aminiya ta kai babbar kasuwar tufafi da kayan ado ta Kwari da ke Kano, ta tarar da kasuwa cike maƙil da mata da maza, kowanne na ƙoƙarin sayen sabbin kaya. Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano Kayayyakin da aka fi saya sun haɗa da atamfofi, mayafai, adire, dogayen riguna, leshi, sarƙoƙi, yadi, da sauran kayan ado.   Kasuwanni sun cika maƙil da masu...
     Jiniyar gargadi ta kada a cikin sassa masu yawa na Falasdinu dake karkashin mamaya  bayan harbo makami mai linzami da mutanen Yemen su ka yi. Kafafen watsa labarun HKI sun ce, jiniyar gargadin ta kada a cikin garuruwa 255 a HKI daga cikin har da birnin Kudus. Jaridar “Yediot Ahronot” ta buga labarin dake cewa, wasu barguzan makami mai linzamin sun fada a unguwar “Mifo Hurun”. Har ila yau harba makami mai linzamin daga Yemen ya sa an dakatar da zirga-zirgar jirage a filin saukar jiragen sama na “Ben Gorion”. Jaridar “Yesrael Home” ta ce miliyoyin mutane ne su ka shiga dakunan boya saboda kaucewa makami mai  linzamin da aka harbo daga Yemen. A jiya Laraba Sayyid Abdulmalik al-Husi, jagoran...
    Ya kuma yi kira ga iyaye su kula da ’ya’yansu tare da hana su shiga ayyukan da ka iya haddasa tashin hankali. Ya tunatar da al’umma cewa Sallah lokaci ne na zaman lafiya, haɗin kai, da farin ciki, don haka dole ne kowa ya fifita zaman lafiya fiye da bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Rundunar ta kuma samar da lambobin kiran gaggawa don bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa a lokacin bukukuwan sallar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    FRSC, ta miƙa lamarin ga ‘yansanda don bincike, tare da yin kira ga direbobi su kiyaye dokokin hanya domin guje wa irin wannan hatsari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bikin Sallar Eid-el-Fitr Durbar, saboda matsalar tsaro da ya sa aka dakatar da shirye-shiryen.   Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa ta karamar hukumar Nasarawa da ke Kano.   Ya kuma jaddada cewa zaman lafiya a tsakanin jama’a ya fi muhimmanci fiye da bikin Durbar.     Bayero ya yi nuni da cewa manyan Malaman addinin Musulunci da dattawa da masu ruwa da tsaki da ‘yan majalisarsa suka bada shawarar a soke bikin domin a samu zaman lafiya.   Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar Kano da su yi amfani da lokacin bukukuwan Sallah wajen ziyartar...
    Babban hafsan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya shelanta  ‘yantar da Khartoum Babban birnin kasar. Wannan na zuwa ne bayan da tun da farko ya sanar da cewa dakarunsa sun kwato filin jirgin saman babban birnin, wuri mai matukar mahimmanci daga hannun dakarun ‘yan tawaye na RSF. “An ‘yantar da Khartoum, an gama,” in ji shugaban na Sudan daga fadar shugaban kasa a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na kasar. Kazalika, wata sanarwa da sashen watsa labarai na majalisar rikon kwarya mai mulkin kasar ta fitar, ta ce Al-Burhan ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Khartoum ta jirgi mai saukar ungulu a jiyan, jirgin da ya zamo na farko da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta umarci dukkanin waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga Sakatarorin ma’aikatun da suke jagoranta. Idan babu Sakatare, sai miƙa ragamar ga babban Darakta mafi girma ko Shugaban Harkokin Gudanarwa. Wannan umarni zai fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Darakta a ofishin lura da harkokin waje na kwamitin kolin JKS, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya gana da mataimakin shugaban kwamitin kasa na Amurka mai lura da alakar Sin da Amurka Evan Greenberg. Yayin da suke zantawa a yau Laraba, Wang ya jinjinawa Greenberg, bisa tsawon lokaci da ya shafe yana ingiza tattaunawa, da hadin gwiwa tsakanin bangaren Sin da na Amurka, yana mai fatan kwamitin kasa na Amurka mai lura da alakar Sin da Amurka, da sauran kwararru daga dukkanin fannonin rayuwa na Amurka, za su bayar da sabbin gudummawa don wanzar da daidaito, da tabbatar da kyakkyawar alakar Sin da Amurka yadda ya kamata. A nasa bangare kuwa, mista Greenberg ya ce alakar Sin da...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar sojan Sudan ta sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa. Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kasar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an  shimfida iko a  cikn filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na birnin Khartum. Har ila yau yau kwamandan sojan ya kuma bayyana cewa, a yanzu haka suna cigaba da faraurar mayakin “Rundunar Kai Daukin Gaggawa”da su ka saura a cikin binin Khartum. Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin na Sudan suka sanar da cewa suna samun Karin nasara akan abokan fadansu. Wata majiyar ta shaida...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya amince da bukatar ma’aikatar shari’a na yin afuwa ga wasu fursunoni sannan kuma da rage yawan shekarun wasu na zaman gidan kurkuku. Yin afuwar ga fursunonin dai ya zo saboda shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta 1404 da kuma karatowar karamar salla ra 1446. Bugu da kari a wannan tsakanin ne ake bikin kafa tsarin jamhuriyar Musulunci na Iran. Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran Hujjatul-Islam Wal Muslimin Gulam Muhsin Eji ne ya gabatar da bukatar neman afuwar ga fursunonin ta mutane 1526, wanda kuma ya sami amincewar jagoran. A kowace shekara a lokutan bukukuwan addini da nasa ana yi wa fursunoni masu kananan laufuka afuwa, yayin da ake rage wa...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har ila yau, masu bincike sun gano wasu tsoffin dabarun hana koguna da madatsun ruwa ambaliya da yadda aka tsaga manyan hanyoyin ruwa da aka yi amfani da su shekaru 5,000 da suka gabata, a wani tsohon yanki na Zhejiang ta hanyar amfani da kayan binciken muhalli. Binciken ya fayyace wayewar kai na tsara birane da kula da koguna da hanyoyin ruwa irin na Liangzhu a tsohon zamani. Babu shakka, amfani da wayewar kan magabata a zamaninmu na yanzu yana daga cikin sirrin nasarorin da Sinawa ke samu ta fuskar wayewar kai da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kere-kere da kirkire-kirkire. Ina fatan kasashenmu na Afirka su dau hannu domin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, tabbatar da...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
    Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
    Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati “A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi. “Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take. “Suna cikin guje...
    Ya ce, “Da misalin karfe 7:28 na safe ne wasu da ke sharar masallacin suka ga mutumin a kwance a cikin masallacin, sai suka yi kokarin tayar da shi domin su yi shara amma shiru.   Nan da nan, sai mutanen suka sanar da Musulman yankin lamarin, inda suka garzaya da shi zuwa asibiti, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.   Musa ya ce, daga bisani aka mika gawar marigayin ga ‘yan uwansa domin yi masa jana’iza. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Ƙungiyoyin ƙwadago reshen Jihar Ribas sun yi barazanar ɗaukar mataki muddin gwamnatin Nijeriya ba ta janye dokar-ta-ɓacin da ta ayyana a jihar ba. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar gamayya da ƙungiyoyin ƙwadagon na NLC, TUC da JNC suka fitar a ranar 24 ga watan Maris. Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Kwamishinan Abba ya yi murabus bayan watanni 7 da naɗinsa Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na jihar sun nuna damuwa kan tasirin dokar-ta-ɓacin a kan tattalin arzikin jihar da kuma nuna rashin dacewar ta a hukumance. A cewarsu, wannan matakin ya sanya an kasa biyan albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar. ’Yan ƙwadagon sun bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da rashin biyan...
     Kwamishinan tsaron cikin gida da ayyuka na musamman na jihar Kano, Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris (mai ritaya), ya yi murabus daga mukaminsa. An tabbatar da murabus din nasa ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar. Ya ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus din a hukumance, inda ya nuna jin dadinsa da irin gudunmawar da Janar din sojan ya bayar a lokacin da yake gudanar da aikinsa. Rasha Da Ukraine Sun Amince Da Tsagaita Wuta A Tekun Black Sea Kasuwar Kayayyakin Masarufi Ta Sin Za Ta Ci Gaba Da Nuna Yanayin Bunkasa Bisa Daidaito A Bana LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Manjo janar Idris (mai ritaya) shi ne...