2025-04-12@21:57:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 79

«da mu awiya»:

    108-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin al-kur’ani  mai girma ko cikin wasu littafan wadanda suka hada da Littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawi na maulana Jalaluddin Rumi, ko kuma cikin wasu littafan. Da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///.. Madalla, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun ci gaba da kawo maku sirar Imam Alhassan lamami na biyu daga limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All…(s) kuma da na farko ga Fatimah (s) diyar manzon All..(s). A cikin shirimmu da ya gabata...
    Sojojin HKI wadanda suka yi ritaya da kuma masu jiran aiki ko Reserv sun watsa wata bukata da suka rubuta ta kawo karshen yakin da Benyamin Natanyahu yake jagoranta a Gaza. Sojojin sun kara da cewa a halin yanzu yakin yana cimma manufar Natanyahu ne kawai, ba don manufar HKI ake yins a ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kafin su watsa takardar bukatar a yau Alhamis, babban kwamnadan sojojin sama na HKI Major General Tomer Bar ya ja kunnen sojojin kan cewa kada su watsa takardan, kuma y ace duk wanda ya sanya hannu a kan takardan yana iya korarsa daga rundunar sojojin sama na HKI. Amma sojojin sun kammala da cewa a...
    Ta kara da cewa, “Ta hanyar hada tsarin horaswa na ayyukan masana’antu a cikin tsarinmu na TVET, muna rage gibin rashin kwarewar da bude kofa ga sana’o’i masu kyau a fannin fasahar sadarwa na zamani na Kenya,” (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Cikin Gida ta Amurka, Tammy Bruce, akwai damuwa kan taimakon da ke iya faɗa wa hannun ƙungiyoyin Taliban da Houthi, waɗanda ke iko da mafi yawan yankunan waɗannan ƙasashe. A baya-bayan nan, Hukumar Yaƙi da Yunwa ta Duniya (WFP) ta bayyana cewa katse tallafin Amurka tamkar “hukuncin kisa ne” ga miliyoyin mutane da ke fuskantar matsananciyar yunwa a faɗin duniya, musamman a yankunan da ake rikici. Masu fashin baƙi na ganin wannan mataki na iya taimaka wa dubban mutane, amma kuma har yanzu ana buƙatar a duba inda taimakon ke zuwa don tabbatar da cewa yana taimaka wa mabuƙata ba tare da faɗa wa hannun ‘yan tada ƙayar baya ba. Daga kanmu,...
    Kungiyar Tuntuba ta Arewacin Najeriya (ACF) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Kungiyar ta bayyana bakin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da kananan yara. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da wadannan hare-hare tare da mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan wadanda suka rasu da kuma daukacin jama’ar Jihar Filato. ACF ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta ayyana dokar ta-baci a wuraren da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga tare da hada...
    Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ɗauki matakin gaggawa wajen kawo ƙarshen hare-haren da ake kai wa al’umma a Jihar Filato. Ƙungiyar ta bayyana baƙin cikinta matuƙa kan harin da aka kai yankin Bokkos da Mangu a ranar 28 ga watan Maris, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama ciki har da ƙananan yara. ’Yan sanda sun soke gayyatar da suka yi wa Sanusi II kan hawan sallah Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Taraba A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Farfesa T.A. Muhammad-Baba ya fitar, ACF ta yi tir da waɗannan hare-hare tare da miƙa sakon ta’aziyyarta ga iyalan waɗanda suka rasu da kuma ɗaukacin jama’ar Jihar Filato. Ƙungiyar...
    Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
    Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kai wadannan hare-hare ne a garin Rasul Isa da lardin Salif a yammacin birnin Hudaida na kasar ta Yemen. Sannan tashar talabijin ta Almasirah ta bayyana cewa akalla mutum guda ne ya rasa ransa a wannan harin sannan wani guda ya ji rauni. Har’ila yau jiragen yakin Amurkan sun kai hare-hare kan yankin...
    A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar ‘ya’ya da jikoki da dama. Mu Leka Shirin “Bunkasa Tagomashin Kirkirarriyar Basira Ta AI” Na Kasar Sin Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Daga cikin ‘ya’yansa akwai Alhaji Abdullahi Abbas, shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano. Kano, jiha ce da hamayyar siyasa da rikicin masarauta ya dabaibaye ta. Akwai hamayyar siyasa tsakanin shugabannin jam’iyyun NNPP mai mulki a jihar da takwararta ta...
    Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka. Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka na da hannu a ayyukan haramtacciyar kasar Isra’ila na yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin. A wata ganawa da ya yi da Hans Grundberg, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen a birnin Tehran, Araghchi ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren soji da Amurka ke kaiwa sassa daban-daban na kasar Yeman, wanda ke sanadin mutuwar fararen hula da kuma lalata kayayyakin more rayuwa. Ya kara da cewa: Hare-haren da sojojin Amurka suke kai wa kasar Yamen, wanda ya zo daidai da irin yadda gwamnatin sahyoniyawan ke ci gaba da aiwatar da kisan gilla a zirin Gaza da kuma hare-haren da take kaiwa kasashen Lebanon...
    Tsadar rayuwa tun daga wancan lokacin ne bayan cire tallafin mai,da kwana daya kawai zuwa biyu sai rayuwar wasu dole ta fara sauyawa,kaya ko kayayyakin da ake saya a farashi na kashi 75 zuwa 100 sai abin ya koma farashin wasu har sai da,ya kai kashi 200 zuwa kashi 300 kai wani abin ma, har ya zarce haka,kuma kamar yadda Hausawa suka ce dole ce kanwar na ki ta sa hakan ta kasance,wannan kuma haka ne. Dole ce tasa haka saboda har an kai ga ganin abinda ya cirewa Buzu nadi wato wahala ke nan.Kuma dole ne cin kasuwa da makiyi wasu abubuwan abin ba,a  iya cewa komai sai dai ayi gum da Baki kawai. Matsalar tsaro Ko shakka babu...
    Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na bunƙasa kayan horo da samar da ingantattun makamai da kayan aiki ga dakarun sojoji. Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Badaru ya yi alƙawarin tuntuɓar Gwamnatin Jihar Kaduna, domin kammala ginin Makarantar Sakandaren Chindit, wadda ba a kammala ta ba tsawon lokaci. Ya kuma bayar da tabbacin...
    Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025. Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87, da jarirai 54. An samu nasarar mayar da su ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin NIDCOM, Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da kuma Hukumar Kula da Baƙin Haure da waɗanda rikici ya raba da matsugunansu (NCRMI). A cewar sanarwar da NIDCOM ta fitar, an dawo da su ne kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris 2025. A ranar 28 ga Janairu, an dawo da mutum...
    A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320. Hon. Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici. Ta kuma jaddada cewa wajibi ne ‘yan Nijeriya su bi hanyoyin da doka ta tanada idan suna son yin hijira, domin guje wa hatsarin da ke tattare da tafiya ta haramtacciyar hanya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    A kwanakin nan, birnin Beijing na Sin ya karbi tarin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwar kasar Sin dake kawo ziyara kasar, sai dai kuma idan an yi la’akari da yanayin yakin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa dake wakana yanzu haka, a iya cewa ziyarce-ziyarcen sun zo da mamaki. Yayin da gwamnatin Amurka ke matsa kaimi wajen ingiza yakin cinikayya, ‘yan siyasa da wakilan manyan kamfanonin Amurka na haye wahalhalu inda suke ta kawo ziyara Sin, wanda hakan ke nuni ga matukar goyon baya da salon bude kofar cinikayyar duniya ke samu, da kuma fatan da ake yi na samun cikakken daidaito, da hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ko shakka babu, matakin Amurka na...
    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita. “A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza. Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin...
    Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan kusoshin Hamas, wanda yake a kan gaba wajen gwagwarmaya da  sadaukarwa, ya yi shahada a kan tafarkin gaskiya. Bayanin ya ci gaba da cewa: Bai taba gazawa wajen gudanar da ayyukansa na jihadi da hidima ga al’ummar Palastinu ba, ya kuma ci gaba da yin gwagwarmaya kan turba ta gaskiya da neman ‘yanci har zuwa karshen rayuwarsa. Hamas...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka.  Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman...
    Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani hari na ” yahudawan sahyoniya na ha’inci”, a lokacin da yake gudanar da sallar dare a daren 23 ga watan Ramadan. An kashe shi ne tare da matarsa ​​a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa da ke yankin al-Mawasi, yammacin birnin Khan Yunis na kudancin Gaza. Kungiyar ta bayyana Bardawil a matsayin “alama ta siyasa, yada labarai,” da ayyukan bunkasa...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen. A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE  Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen. Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa  da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin...
    Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar. Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ayyana dokar ta-ɓaci ne kawai a lokuta na matsanancin rikici kamar yaƙin basasa, ko rushewar doka da oda, wanda a cewarsa babu ɗaya daga cikinsu da ya faru a Jihar Ribas. NEF, ta zargi Gwamnatin Tarayya...
    Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da tashin jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ben Gurion. Saree ya jaddada cewa, filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci ga zirga-zirgar jiragen sama, yana mai gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa a fagen daga har sai Isra’ila ta kawo karshen yakin da take yi a kan al’ummar Gaza. Tun da farko dai rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu  linzami a yammacin jiya Juma’a a yankuna da dama da ke tsakiyar Falasdinu da ta mamaye, kuma Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman...
    Shugaban Riƙo na Jihar Ribas, Ibok Ibas, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa shi ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, wadda ke fama da rikicin siyasa. Da yake jawabi a wani shirin talabijin a daren Alhamis a Fatakwal, Ibas ya bayyana naɗin nasa a matsayin matakin da ya dace don kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya ɗauki kusan shekaru biyu. Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Ya ce rikicin ya hana ci gaban gwamnati, tare da haifar da matsalar tsaro da koma bayan tattalin arziƙi a jihar. “A matsayina na ɗan yankin Neja Delta, na fahimci damuwar mutanenmu. Rashin tabbas a...
    Ramadan lokaci ne da ke hada kan iyalai da al’ummomi a fadin duniyar Musulmi. Lokaci ne da masoya ke haduwa tun daga lokacin sahur har zuwa buda-baki, ta hanyar kasancewa tare domin cin abinci mai gina jiki. A wannan lokacin, ba a yin abinci don nishadi kawai, lokaci ne na inganta rayuwa da bayar da labarai na nishadantarwa da zumunta da kuma jin dadin kasancewa tare. A cikin wannan labari mai ban sha’awa na MAGGI mai taken Labarin Ramadan, wasu mata biyar sun yi tafiya ta tsawon wata guda don samar da sauye-sauye, inda suka gano hadaddun girke-girke na sada zumunta da ke da alaka da samar da labarai masu jan hankali, har guda shida. Tare da wasu jaruman wasan...
    Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa  ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
    Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan...
    Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a  jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita. Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa...
    Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar. Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar. An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike. Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar...
    A baya-bayan nan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da harkokin gona na kasar Gambiya Demba Sabally, ya bayyana goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin, a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona a kasarsa a ’yan shekarun nan. Idan ana batu na kirkira da amfani da fasahar zamani a duniya, to kowa ya san cewa kasar Sin ta yi zarra a wannan bangare. Haka kuma kowa ya san duk wani ci gaban da Sin take nema ko ta samu, tana yi ne domin jama’arta su kasance cikin walwala, shi ya sa ci gaban Sin a fannin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, ya game kowane bangare na...
    A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa dole ne Rasha ta mayar da yankunan da ta ƙwace. Tun a shekarar 2014, Rasha ta ƙwace yankin Crimea, sannan a shekarar 2022 ta mamaye wasu yankuna huɗu na gabashin Ukraine. Yanzu dai ana fatan wannan tattaunawa za ta kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana ci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi.   A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da Dodams Medical Equipt don kula da aikin na tsawon shekaru 2.   Ya bayyana cewa, a watan Janairun wannan shekara ne aka yi duk wani shiri da kuma biyan kudin jirgi, amma saboda hutun karshen shekara da Kamfanoni suka yi, an samu tsaiko wajen samar da wasu sassa musamman na’urar gudanarda aikin, wanda ya iso a ranar Litinin 10 ga Maris, 2025.   Ya ci...
    Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki. Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya ce babban aminin Obi, Valentine Ozigbo, ya koma jam’iyyar APC domin yin takarar gwamna. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina “Kun san muna rage ƙarfin jam’iyyar LP kuwa?” in ji Bwala. “Valentine Ozigbo ya shigo jam’iyyarmu, Balami ma haka, Peter Obi ma zai zo....
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu? Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba wa ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita su 9,403 a ƙananan hukumomin Biu da Hawul, tallafin Naira biliyan ɗaya. Wannan tallafi na da nufin ƙarfafa kasuwanci, haɓaka tattalin arziƙi, da rage talauci a yankunan. Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha A Biu da Hawul, gwamnan ya raba Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603, inda kowane mutum ya samu Naira 100,000. Hakazalika, ya raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da magidanta 1,800 a Biu da kuma ’yan kasuwa 2,000 a Hawul. Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan...
    Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku. HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda...
    Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu. Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3. Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da...
    An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, lamarin da ya ba ta damar buga Gasar Europa a kakar bana. ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ An hana tashe bana a Kano — Nalako Kungiyar Old Trafford ta koma matsayi na 14 a kasan teburin Firimiya da maki 34, bayan da ta ci...
    ’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...
    Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.   Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar kawar da barazanar masu tada kayar baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta,...
    Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila. A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da  Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba...
    Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya. Haka nan ya ambaci cewa abu mai muhimmanci a wannan lokacin shi ne tabbatar da tsagaita wutar yaki,wanda yake fuskantar keta shi –daga Isra’ila. Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban. Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da  shirin na...
    Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin,  take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa  kuma...
    Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya bayyana cewa matarsa ta taɓa kawo masa ƙorafi game da cin zarafin da ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi mata. A cewarsa, rikicin ya fara tun lokacin da Natasha ta tsaya takarar kujerar Sanata a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, inda ta nemi kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya. Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano A lokacin, Akpabio yana riƙe da mukamin Ministan Neja Delta. “Da kaina na je na same shi na buƙaci ya bai wa matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotar da ke tsakaninmu. “Bayan mun tattauna sai...
    Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar. Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma...
    Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru. Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako. Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa,...
    A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu.  An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.   Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023 Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce,...
    Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.  Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...
    Ƙaramin Ministan Gidaje da Tsara Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a Zaɓen 2023 Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara. Sai dai Ministan ya ce ƙaddarar hukunci daga Allah ne ya sanya a yanzu haka ba shi ke riƙe da madafan iko a Jihar Kanon ba. Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Ata ya faɗi hakan ne yayin da yake barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddin ake sake naɗa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano. Ministan ya ce kalaman da shugaban jam’iyyar ya riƙa furtawa su ne dalilin da Allah Ya ƙwace mulkin jihar...
    A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD. Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu...
    Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
    Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya. Bayan neman albarkatun man fetur da gas, an kuma tsara aikin rijiyar don zurfafa nazarin juyin halittar duniya da kuma zurfafa ilimin binciken kasa. A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da...
    Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...
    Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida. Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta. Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa. Ya kara da...
    Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu. Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin kirkira sun hada da Toru-ebe da za a sassaka daga jihohin Delta da Edo da Ondo na yanzu, da kuma jihohin Ibadan da Lagoon da za a sassaka daga jihohin Oyo da Legas, bi da bi. Sauran sun hada da Jihar Ijebu da za a samar daga Jihar Ogun ta yanzu da kuma jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha da za a kirkiro daga jihohin Ogu da...
    Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu. Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace. Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata....
    A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da ke Amurka (CGCC) da aka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka, Xie ya bayyana cewa, barazanar haraji ba za ta taba yin tasiri a kan Sinawa ba, a maimakon haka, masu yi za su buge ne da illata ginshikin yaki da miyagun kwayoyi da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kara tsadar kayayyaki ga iyalan Amurkawa da harkokin kasuwanci...
    Kwamandan sojan na Iran  Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya  janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama. A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi. Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Haka kuma, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Bama da kuma dawo da wutar lantarki a yankin. Zulum, ya ƙara da cewa za a ci gaba da tallafa wa masarautar da gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata. Hakazalika,...
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
    Su tsare tsaren anyi shirin tabbatar dukkan makarantu masu zaman kan su da na gwamnati za su fara amfani da tsarin a watan Janairu 2025. Sai dai kuma watan Janairu ya wuce ba tare da samun wani ci gab aba dangane da lamarin. Rahoto ya nuna har yanzu da akwai sauran Rina a Kaba, domin kuwa da akwai karancin makarantu wadanda basu da irin kayan da za ayiu amfani da su wajen aiwatar da sabon tsarin,da kuma yadda za a horar da Malamai, hakan ta sa aka bar masu ruwa da tsaki cikin shakku ko sabon tsarin ilimin za afara amfani da shi. Sabon tsarin ilimin an yi niyyar fara amfanni da shi inda za a koyar da yaddaake sabbin...
    A cikin daren nan aka dawo da wutar lantarki a Jihar Kaduna. Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) ya dawo da wutar be bayan kwanaki babu ita. An dauke wutar ne sakamakon yajin aiki da ma’aikatansa suka shiga tsawon kwana biyar. Kaduna Electric ne ke ba da wutar lantarki a Jihar Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi. Ma’aikaran sun janye yajin aikin ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya shiga tsakaninsu da kamfanin.
    Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20. Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22. Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5. Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an  yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku. Tun a watan Disamba na...
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
    Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar  Ukrain. Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
    HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan  yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da  duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
    Sama da ’yan Najeriya 5,000 da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, na fuskantar barazanar dawo da su gida. Daga cikinsu, kusan 1,500 ne ake tsare da su, wanda hakan na daga cikin matakin da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka na korar baƙin haure da masu neman mafaka ba bisa ƙa’ida ba. Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Alƙaluman da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE), ta fitar a watan Nuwamban 2024, sun nuna cewa akwai mutum miliyan 1.445 baƙin haure da ke zaune a ƙasar ba tare da takardun izini ba, ciki har da mutum 3,690...
    Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.
    Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar. Labarin ya kara da  cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan  birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
۱