2025-04-02@15:12:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 274

«ficewar ƙasashen»:

    Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa. Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace. Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi. Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi. Shugaban...
    Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...
    Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito. Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile shigar baƙin haure cikin ƙasar. Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta Faeser ta ce gwamnatin na ci gaba da daukan matakin mayar da baƙin haure ƙasashen da suka fito, inda yanzu haka aka samu raguwar masu ajiye takardun neman mafaka a ƙasar, mafi ƙarfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Turai. Faeser ta...
    A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yankin Xizang a bude yake ga kowa da kowa, kuma ba a hana baki daga kasashen waje shiga ba, inda ya kara da cewa, yankin yana karbar dimbin matafiya da sauran al’ummomi da dama daga sassa daban-daban a kowace shekara, domin ko a shekarar...
    A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri. Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL A jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya kasance wani babban mataki na bude kasuwar kasar Sin ga kwayoyi dangin gyada na kasar Zambiya, wanda zai amfanar da manoman kasar nan gaba ba da jimawa ba. Ya kara da cewa, baya ga wannan yarjejeniyar...
    Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita. Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi.   Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali.   An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare.   A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai.   Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe...
    Da safiyar Yau Talata jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan unguwar Dhahiya dake Beirut tare da bayyana cewa ta kai wa wani kusa ne a kungiyar Hizbullah hari. Harin na yau shi ne irinsa na biyu da HKI ya kai a unguwar Dhahiya tun daga tsagaita wutar yaki a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata. Jiragen yakin na HKI sun yi shawagi a kasa-kasan birnin Beirut kafin aji karar fashewar abubuwa masu karfi. Kafafen watsa labarai sun ambaci cewa jiragen sun kai harin ne akan wani dogon gini a cikin unguwar. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa ya zuwa yanzu mutane 3 ne su ka yi shahada,yayin da wasu 4 su ka jikkata. Masu...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iyayen Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda aka sace tare da mahaifinsa a Jihar Katsina, sun bayyana cewa sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba. Abdulsalam, wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Kebbi, an sace shi tare da mahaifinsa da wasu makonni biyu da suka gabata, bayan Gwamnan Katsina ya karrama shi. Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi. Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi Mahaifinsa, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya shaida cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban ɗan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karɓe su da ƙarfi. “Ya yi...
    Rahotanni sun ce, wani ɗan kasar China ya kama matarsa tana cin amanarsa da wanda ya ba ta aiki a lokutan aiki ta hanyar amfani da wata na’urar ɗaukar hoto ta jirgi mara matuƙi da ake sarrafa ta daga nesa, tana leƙen asiri daga nesa. Mutumin mai hazaka da aka fi sani da Jing ya fara zargin cewa, matarsa na yin wata alaƙa ne bayan ta yi nisa sosai da shi kuma ta canza mu’amalarta sosai, ciki har da ziyartar iyayenta fiye da kowane lokaci da kuma kawo uzuri a duk lokacin da ya yi mata rakiya da kuma ƙarin lokaci a wurin aikinta. Ladubban Ranar Idin Karamar Sallah Abubuwan da ya kamata Musulmi ya yi a ranar Karamar...
    Kamfanin hakar ma’adinai mai suna RUSAL na kasar Rasha ya aika da tawaga zuwa kasar Saloyo a yammacin Afirka don nazarin yiyuwar fara hakar ma’adinin bauxite a kasar nan gaba. Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jakadan kasar Rasah a Saliyo yana fadar haka. Labarin ya nakalto Mohammad Yongawo wani jami’in gwamnatin kasar ta Saliyo yana cewa kasarsa a shirye take ta kammala yarjeniya tsakanin kamfanin Rusal na kasar Rasha don fara aiki a yankunan da ske da ma’adinin bauxite. Ya kuma kara da cewa a halin yanzun bangarorin biyu suna cikin tattaunawa a tsakanionsu. Sannan yana fatan daga karshen gwamnatin kasar zata bawa kamfanin lisisin fara hakar ma’anin a kasar nan ba da dadewa ba. Kafin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa na Janhuriyar Congo Jean-Claude Gakosso, jiya Juma’a a birnin Beijing, inda suka yi alkawarin hada hannu wajen inganta raya dangantakar Sin da Afrika. Wang Yi wanda kuma mamba ne na ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce dangantakar dake tsakanin Sin da Janhuriyar Congo, ta zama misalin hadin gwiwa da goyon baya dake tsakanin Sin da Afrika. Wang Yi ya kuma yi kira ga kasashen Sin da Afrika da su hada kai da kara hadin gwiwa domin kare muradun kasashe masu tasowa, da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a duniya yayin da ake fuskantar hargitsi. A nasa bangare, Jean-Claude Gakosso, ya ce...
    An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.  
    An ga jinjirin watan Shawwal a Nijeriya da ke tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana. Ɗaya daga cikin ’yan kwamitin duban wata a Nijeriya (NMSC), Malam Simwal Usman Jibrin ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X. Sai dai ya ce ana dakon sanar da ganin jinjirin watan a hukumance daga Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Islama a Nijeriya da ke ƙarƙashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi. Hakan ya tabbatar da ƙarewar watan azumi na Ramadanan bana, saboda haka gobe Lahadi take Sallah a Nijeriya.  
    Ofishin jakadancin Amurka da ke Damascus ya fitar da wata sanarwar gaggawa, inda ya yi kira ga daukacin Amurkawa da su gaggauta ficewa daga kasar Syria, sakamakon karuwar hare-haren da ake kai wa a lokacin bukukuwan sallar Idi, wanda ke kawo karshen azumin watan Ramadan mai alfarma. A cikin wata sanarwa da ta fitar ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta daukaka tafiye-tafiye zuwa Syria zuwa mataki na 4 mafi girman inda aka gargadi, Amurkawa da kada su je kasar Siriya bisa kowane dalili. Ofishin jakadancin ya gargadi ‘yan kasar game da yiwuwar kai hari kan “ofisoshin jakadanci, kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin jama’a na Syria” a Damascus. Halin tsaro a Syria ya tabarbare bayan da kungiyoyin ‘yan ta’adda, karkashin jagorancin...
    Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.   A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da yunwa da kuma samar da abinci ga al’umma. A cewar sa, karamar Hukumar ta ware wasu yankunan Sahara domin fara noman rani a karo na farko dan fadada harkar noma a kan Tudu.   Alhaji Jamilu Danmalam yace an zabi kauyen Tunubu dake mazabar Kanwa domin fara noman Rani. Ya kara da cewar, wadanda suka anfana da tallafin za su ci moriyar kaso...
    Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum.   2-Maganin Hawan Jini (Hypertension) Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini. Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma.   3-Maganin Basir Sadidan Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo. Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki...
    A cikin shekaru da ya yi a masana’antar, Karkuzu ya nuna ƙwarewa wajen kawo canji da kuma nishaɗantar da al’umma. A madadin gwamnatin Kano da al’ummar jihar, gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamacin, ‘yan Kannywood, da masana’antar. Ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya jiƙan jarumin, Ya kuma Aljanna Firdausi ta zama makomarsa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818  sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune,  kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
    Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin  raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
    Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fargaba kan yadda ake ci gaba da samun karuwar matsalar jin kai a zirin Gaza, inda ta bayar da rahoton cewa akalla Falasdinawa 142,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin mako guda kacal saboda tsanantar hare-haren bama-bamai na Isra’ila. Kakakin MDD Stephane Dujarric, ya bayyana a wani taron manema labarai a jiya Laraba cewa, hare-haren da kuma umarnin gudun hijira, tare da hana kayan da ke shiga Gaza da kuma hana ayyukan jin kai a cikin yankin, suna yin mummunan tasiri ga daukacin al’ummar sama da miliyan biyu. Dujarric ya yi nuni da cewa, yayin da rikicin ya tsananta, ana sa ran adadin mutanen da suka rasa matsugunansu zai karu sosai. A yammacin ranar Talata,...
    Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi alkawarin inganta sansanin horas da kuratan sojoji dake Zaria wato Depot domin baiwa hukumar Soji damar ci gaba da aikin horaswa a wajen.   Ministan ya yi wannan alkawarin ne a lokacin da ya kai ziyarar tantance sojojin Najeriya da ke Chindit Cantonment a Zariya.   Ministan ya kuma ce, ma’aikatar tsaro ba za ta bar wani abu ba, wajen tabbatar da cewa makarantar firamare ta Chindit ta samu ingantuwar kayan aiki don dacewa da tsarin zamani a matsayin hanyar kara kwarin gwiwa na hafsoshi da sojoji na Kantoment da ke amfana da wajen.   Ya kara da cewa ofishin sa zai hada kai da gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an kammala makarantar...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har ila yau, masu bincike sun gano wasu tsoffin dabarun hana koguna da madatsun ruwa ambaliya da yadda aka tsaga manyan hanyoyin ruwa da aka yi amfani da su shekaru 5,000 da suka gabata, a wani tsohon yanki na Zhejiang ta hanyar amfani da kayan binciken muhalli. Binciken ya fayyace wayewar kai na tsara birane da kula da koguna da hanyoyin ruwa irin na Liangzhu a tsohon zamani. Babu shakka, amfani da wayewar kan magabata a zamaninmu na yanzu yana daga cikin sirrin nasarorin da Sinawa ke samu ta fuskar wayewar kai da bunkasa ci gaban kimiyya da fasaha da kere-kere da kirkire-kirkire. Ina fatan kasashenmu na Afirka su dau hannu domin jifar tsuntsu biyu da dutse daya, tabbatar da...
    Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in kasar Iran a baya-bayan nan, ba a samu wani ci gaba kadan ba a cikin binciken nukiliyar da aka shafe shekaru ana yi kan kasar Iran, yana mai jaddada bukatar gaggauta warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin Tehran da Washington. A wata hira da Bloomberg babban darektan hukumar Rafael Grossi ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai koma Tehran domin ci gaba...
    A gun taron manema labarai na musamman da ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta gudanar a yau Talata, jami’ai masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa, yayin da manufofi da matakai daban daban na fadada kashe kudi ke ci gaba da yin tasiri a bana, kasuwannin kayayyakin masarufi na kasar Sin baki daya, sun ci gaba da nuna yanayin bunkasa bisa daidaito. Jami’an sun kuma ce ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta inganta ayyuka na musamman don bunkasa kashe kudi, da gudanar da ayyuka a fannoni hudu, wato inganta yadda ake amfani da kayayyaki, da fadada amfani da hidimomi, da samar da gajiya daga sabbin kayayyaki, da kuma kirkirar sabbin yanayin cimma gajiya. Ma’aikatar kasuwancin ta kuma bayyana cewa,...
    A kwanakin nan, birnin Beijing na Sin ya karbi tarin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwar kasar Sin dake kawo ziyara kasar, sai dai kuma idan an yi la’akari da yanayin yakin cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa dake wakana yanzu haka, a iya cewa ziyarce-ziyarcen sun zo da mamaki. Yayin da gwamnatin Amurka ke matsa kaimi wajen ingiza yakin cinikayya, ‘yan siyasa da wakilan manyan kamfanonin Amurka na haye wahalhalu inda suke ta kawo ziyara Sin, wanda hakan ke nuni ga matukar goyon baya da salon bude kofar cinikayyar duniya ke samu, da kuma fatan da ake yi na samun cikakken daidaito, da hadin gwiwar raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ko shakka babu, matakin Amurka na...
    Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen duniya da su fadada zuba jari a kasar Sin, domin zurfafa samun moriyar juna da samun nasara tare. He ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugabannin manyan kamfanoni na duniya a nan birnin Beijing, yayin da suka yi musayar ra’ayi kan yanayin tattalin arzikin duniya da na kasar Sin, da hadin gwiwar Sin da Amurka a fannin tattalin arziki da cinikayya, da fadada zuba jari a kasar Sin. He ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da karfin juriya, da fa’ida mai yawa, da wadataccen...
    Kungiyar da ke sa ido da kare hakkin dan adam ta Syria (SOHR) ta fitar da fayafan bidiyo guda hudu da ke dauke da hotunan azabtarwa da kisa da jami’an tsaron sabuwar gwamnatin kasar  karkashin kungiyar Tahrir Sham  suke aiwatarwa a kan fararen hula tsiraru marasa rinjaye a kasar. Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama a Syria ta bayyana a ranar Lahadi cewa, ta samu faifan bidiyo guda hudu ne da ke nuna yadda ake aiwatar da hukuncin kisa kan wasu matasa da ba sa dauke da makamai daga ‘yan Alawiyya, da jami’an tsaro suka aiwatar a kauyen al-Shir da ke yankin Latakia a ranar 7 ga watan Maris. A cewar kungiyar, faifan bidiyon ya kara...
    Wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin da ta ke sauke mai a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, a Jihar Neja. Lamarin ya faru ne da da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Lahadi kusa da Asibitin Gaba. Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Shaidu sun ce gobarar ta fara ne yayin da ake sauke man fetur, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba kasancewar sauran tankunan mai maƙare suke da fetur. Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen don shawo kan lamarin, amma har yanzu wutar na ci gaba da yaɗuwa. “Babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa,...
    Gwamnonin Arewa sun aike wa Gwamna Dikko Umar Radda na Jihar Katsina, saƙon ta’aziyya game da rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Baribari, wadda ta rasu tana da shekaru 93. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana Hajiya Safara’u a matsayin uwa mai tausayi da riƙon gaskiya, wadda ta rayu bisa turbar Allah da hidima wa al’umma. ’Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 10, sun jikkata 14 a Zamfara Mahaifiyar Gwamnan Katsina ta rasu A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya, ya iyalanta da shugabanni za su yi kewarta. Ya kuma buƙaci Gwamna Radda da iyalansa da su ci gaba da girmama tarihinta ta...
    A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata. Kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ita ma ta shaida wannan yanayi, a farkon watanni biyu na shekarar bana, yawan kudin kayayyakin da aka sayar a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 8 da...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a jiya cewa, kasar Sin na dora muhimmanci sosai kan hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kuma tana da kwarin gwiwa kan hakan. Wang ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron firaministan kasar Japan Shigeru Ishiba a birnin Tokyo tare da ministocin harkokin wajen kasashen Japan da Koriya ta Kudu. Yana mai cewa, an fara hadin gwiwa tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu da wuri, inda aka samu sakamako da dama, kuma tana da babban tasiri, wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen inganta fahimtar juna da hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar...
    Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta bayyana a jiya Juma’a cewa, fadin yankin kasar dake fama da zaizayar kasa ya ragu zuwa murabba’in kilomita miliyan 2.6019 a shekarar 2024, wanda ya samu raguwar murabba’in kilomita 25,700, idan aka kwatanta da na shekarar 2023. Wadanann alkaluman wani bangare ne na sakamakon aikin sa ido kan zaizayar kasa a kasar Sin a shekarar 2024, wanda aka kammala a kwanan nan. Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Sin Ta Ba Da Jawabi A Kwamitin Kare Hakkin Bil’adama Na MDD A Madadin Kungiyar Abokantaka Ta Inganta Hakkin Bil’adama Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu ya nuna cewa, ana samun ci gaba bisa...
    Gwamnatin Jihar Borno, ta ɗauki matakin hukunta wasu ma’aurata, Mamman Sheriff da matarsa, da aka kama suna cin zarafin wata yarinya a unguwar Pompomari Bypass da ke Maiduguri. Bayan bayyanar faifan bidiyon da ya nuna ma’auratan suna dukan yarinyar, mutane da dama sun yi tir da abin a shafukan sada zumunta. Majalisar Wakilai ta musanta karɓar kuɗi kan dokar ta-ɓaci a Ribas Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia Wannan ya sa Hukumar Tsaron Sibil Difens (NSCDC) ta cafke su nan take. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa gwamnati ba za ta musu sassauci ba. Ya ce ma’aikatun shari’a, ilimi, da harkokin mata sun haɗa kai domin ganin an hukunta waɗanda suka aikata laifi. Yarinyar, wacce...
    Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan  harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita. “A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza. Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin...
    A cewarsa, tun da farko mun kau da kai ga barin sanya hannun jari a shiyyar kasuwanci ta Olokola (OKFTZ), amma saboda manufofinku da kuma yanayin da masu zuba jari ke da shi, ina so in ce mun dawo kuma za mu yi aiki tare da gwamnatin jihar don komawa Olokola, kuma ana shirin gina tashar jiragen ruwa mafi girma a kasar. Da yake karin haske kan ayyukan da kamfanin ke gudanarwa a Jihar, Dangote ya ce sabbin layukan biyu masu karfin metric tan miliyan 6.0 a kowace shekara na kamfanin siminti an gina su a Itori, yayin da kamfanin siminti na metric ton miliyan 12 a kowace shekara kuma yana nan a Ibeshe. Bayan kammala aikin, Dangote ya ba...
    A ranar Juma’a aka rantsar da sabuwar shugabar ƙasar Namibia, Netumbo Nandi-Ndaitwah domin jagorantar ƙasar wadda aka ruwaito na fuskantar ƙalubale na rashin aikin yi da talauci. Kasancewar Netumbo Nandi-Ndaitwah mace ta biyu da aka taɓa zaɓa a matsayin shugabar ƙasa a nahiyar Afirka, kuma ta farko a Namibia na iya fuskantar ƙalubale. “Idan komai ya tafi daidai, wannan zai zama kyakkyawan misali,” kamar yadda Netumbo Nandi Ndaitwah ta shaida wa shirin Podcast na BBC Africa. “Amma idan wani abu ya faru, kamar yadda zai iya faruwa ga kowace gwamnati ko da a ƙarƙashin namiji ne, akwai waɗanda za su ce: ‘saboda ni mace ce!’” Sabuwar shugabar, mai shekara 72 a duniya ta lashe zaɓen qasar ne a watan Nuwamba...
    An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa.   Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin.   A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa.   Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
      Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Uba Sani, ta raba kayan abinci da tufafi ga marayu, mabukata da malamai a Hayin Na’iya dake Kaduna. An gudanar da taron ne a makarantar Ummul Muminina Hafsat Islamic Academy da ke Hayin Na’iya, Kaduna. Hajiya Hafsat Uba Sani, wacce Hajiya Aisha Idris Maman ‘Yan Uku ta wakilta, ta jaddada bukatar ganin masu hali su tallafa wa talakawa da mabukata a cikin al’ummarsu. “Uwargidan gwamnan ta yi imanin cewa marayu da mabukata suna bukatar soyayya, kulawa da tallafi kamar kowane yaro,” in ji ta. “Wannan shiri ba wai kawai don samar da abinci da tufafi ba ne; yana nufin nuna musu cewa ana kaunarsu kuma ba a manta da su ba.” “Muna...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar zagayowar lokacin bukukuwan Nowruz na sabuwar shekarar hijira shamsiyya da ake amfani da itya a hukumance a kasar Iran. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa al’ummar kasar ta gidan telebijin na murnar shiga sabuwar shekara ta Farisa a yammacin wannan Alhamis. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada bukatar gwamnati da al’ummar kasar su ci gaba da zuba jari don karfafa azamarsu wajen tunkarar takunkumai na zalunci da masu girman kai na duniya suka kakaba ma kasar. Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa samar da kayayyaki na samun bunkasuwa ne idan aka ba da tallafin jari mai karfi. Jagoran ya kuma...
    Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida a fashewar tankar man fetur da ya afku a yankin Karu da ke Abuja a daren Laraba. Rundunar ta kuma ce motoci 14 ne suka kone a mummunan hatsarin. Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, rundunar ta yi matukar jimamin hatsarin motar da ya afku a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin karfe 6:58 na yamma kafin gadar Nyanya. Ta kuma ce, ofishin hukumar na Karu ya samu...
    Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci da ke kan gadar, lamarin da ya haddasa gobara. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da dama, yayin da mutane da yawa suka samu munanan raunuka. Shugaban Sashen Ɗaukar Matakan Gaggawa na Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa (FEMA), Mista Mark Nyam, ya...
    Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako. Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin. “Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe. “Sun tilasta Shugaban Kasuwa...
    Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a hanyar Karu zuwa Nyanya dake birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da wata mummunar gobara da ta rutsa da motoci da dama, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a yammacin ranar Laraba. Har zuwa yanzu  dai ba a tantance musabbabin fashewar tankar man ba. Cikakken bayani na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majiyar ‘yan aware ta kasar Mali ta sanar da cewa wani hari da sojojin gwamnati su ka kai a arewacin kasar ya yi sanadiyyar kashe mutane 18 a arewacin kasar Yemen, sai dai sojojin gwamnatin ta ce, ‘yan aware ta kai wa hari. Kungiyar Azbinawa ‘yan aware ta ce sojojin gwamnatin kasar sun kai hari ne a garin Lerneb mai nisan kilo mita 50 daga birnin Timbuktu, a ranar Litinin da ta gabata kuma bayan mutane 18 da su ka kwanta dama, wasu 7 sun jikkata. Kungiyar ta Azbinawa ta bayyana abinda ya faru da cewa; “Dabbanci” ne irin na zamanin jahiliyya. Sai dai sojojin gwamnatin kasar ta Mali sun wallafa a shafinsu na X cewa; sun kai harin ne...
    Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano. Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC. Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri. Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu...
    Gwamnatin HKI ta bayyana damuwarta da jibge sojojin da gwamnatin kasar masar take yi a yankin Sinaa kusa da kan iyakar kasar da HKI. Tun bayan da gwamnatin HKI ta gama lalata makaman gwamnatin kasar Siriya bayan ta taimaka ta kawo dan Daesh kan kujerar shugabancin kasar ta Siriya, kuma ta bayyana cewa yankunan da ta mamaye a kasar Siriya sun zama HKI ne har abada.take nuna damuwa da kasar Masar. Banda haka mun ga yadda sabon shugaban kasar ta Siriya  Julani ya yi shiri da bakinsa a kan mamayar da HKI takewa kasar Siriya da kuma yadda ta kai hare-hare fiye da dubu guda kan kasar tana lalata makamanta, ko wa ya fahinci cewa, siriya ta gama yawo,. Kuma...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin hukumar raya hadin gwiwar neman ci gaban kasa da kasa ta kasar Sin (CIDCA), Li Ming, ya bayyana a gun taron manema labaru na yau Litinin cewa, rage yawan tallafin kasashen waje da Amurka ta yi, da rage fiye da kashi 90 cikin 100 na ayyukan da take yi, sun sabawa alkawuran da ta dauka, da kuma nauyin da ke bisa wuyanta a karkashin tsarin MDD, kuma hakan wani yunkuri ne na ja da baya, wanda kasashen duniya ba sa goyon baya. Li Ming ya jaddada cewa, alkawarin da kasar Sin ta yi na kara yawan albarkatu ga hadin gwiwar ci gaban duniya, ba zai canza ba. Ya kara da cewa, ka’idojin kasar Sin na kin tsoma baki cikin...
    Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari. A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz ta kammala karatu a Makarantar Hartford Public High School da ke Hartford, a Jihar Connecticut, inda aka karama ta, har ma ta samu gurbin karatu a kwaleji, amma yanzu ta kai karar tsohuwar makarantarta saboda sakacinta. Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira Matashiyar mai shekara 19 tana zargin makarantar da ta...
    An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim. An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan  tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari. Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru 63 da kafuwar gidan rediyon a watan Maris na shekarar 1962. Sun bayyana godiyarsu ga rawar da FRCN Kaduna ya taka tsawon shekaru duk da kalubalen aiki, wanda suka bukaci mahukunta su magance. A sakon taya murna daban da suka aiko, Sanata Salisu Musa Matori, da Alhaji Umar Dembo, da Alhaji Umar Iya Gulak, da Alhaji Garba Baba da Alhaji Muhammad Damak Abubakar, sun jinjinawa...
    An yi kira ga gwamnatocin jihohin Arewacin Najeriya da su tabbatar da dorewar tashar Rediyon Nigeria (FRCN) Kaduna a matsayin abim tunawa da marigayi Firimiyan  tsohuwar jihar Arewa, Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto, ya bari. Masu sauraron tashar sun yi wannan kira a cikin bayanai daban-daban yayin da suke tsokaci kan bikin cika shekaru 63 da kafuwar gidan rediyon a watan Maris na shekarar 1962. Sun bayyana godiyarsu ga rawar da FRCN Kaduna ya taka tsawon shekaru duk da kalubalen aiki, wanda suka bukaci mahukunta su magance. A sakon taya murna daban da suka aiko, Sanata Salisu Musa Matori, da Alhaji Umar Dembo, da Alhaji Umar Iya Gulak, da Alhaji Garba Baba da Alhaji Muhammad Damak Abubakar, sun jinjinawa...
    A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a daurin auren. Kafin ɗaurin auren ne Abba Musa da Maryam Sulaiman amarya da kuma Rainahatu Sulaiman (’yar uwar amarya) da Misbahu Ahmad (abokin ango) da direban motar sun tafi garin Murno da ke da nisan kilomita 5 daga Boto domin gaisawa da ’yan uwan amaryar kamar yadda aka saba a al’adar Hausawa. Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa Nijar ta kori...
    Kafofin yada labaran kasar Rasha sun yi ta jinjina wa wani sojan kasar a matsayin jarumi saboda ci gaba da fafatawa a yankin Kursk tsawon mako guda bayan harbin da aka yi masa a ka. Mutumin da ba a bayyana sunansa ba, wanda aka ruwaito cewa yana cikin Brigade na 155 na Marine na Rukunin Pacific Fleet na Rasha, ya ci gaba fafatawa da sojojin Ukraine a Kursk lokacin da aka harbe shi. Nijar ta kori wasu kamfanonin China 3 daga ƙasar Faɗuwar farashin kayan abinci a watan azumi ta shammace mu – ‘Yan kasuwa A lokacin an harbi hular kansa, amma yana tunanin tabbas harsashin ya huda cikinta. Ya samu kumburi a saman idonsa, wanda daga ƙarshe ya sa...
    Ya kara bayanin cewar Jami’ar za ta dauki sahun dalibanta na farko wato shekarar karatu ta 2025, inda ya kara jaddada aniyar gwamnati ta bada damar samun yin karatu na ilimi mai zurfi tare da bunkasa shi. Ministan har ila yau ya ce zai taimaka wajen tabbatar da cewar Jami’ar ta samu nata kason daga Hukumar kula da ilimin manyan makaratun ta kasa, domin hakan zai taimakawa bunkasa Jami’ar cikin wani lokaci nan gaba. Ya ci gaban da bayanin “Zan tabbatar da cewar Jami’ar ta samu taimako na gidauniya kula da ilimi mai zurfi ta lamurran manyan makarantu ta samun kudade daga wurinta wannan shekarar. Don haka wannan rana ce ta farin ciki ga al’ummar Kudancin Kaduna, al’ummar Jihar Kaduna,...
    ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.  Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye tun a lokacin kaka, da nufin rubanya kudinsu idan farashinsa ya yi tashin gwauron zabo daga musamman a lokaci irin wannan na azumin watan Ramadan, da wasu bayin Allah suke saya don raba wa mabukata. ’Yan bindiga na neman N30m domin fansar gwarzon gasar Al-Qur’ani a Katsina ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Kudin hatsi irin su shinkafa da...
    ’Yan bindigar da suka yi garkuwa da wani gwarzon musabaƙar karatun Al-Qur’ani a Jihar Katsina, Abdulsalam Rabi’u Faskari, suna neman naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa Da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a, Kwamishinan watsa labarai da al’adu na Katsina, Bala Salisu-Zango ya ce Abdulsalam da mahaifinsa da ɗan uwansa da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su, suna nan da ransu a hannun ’yan bindiga, ba a kashe su ba. ’Yan Nijeriya su ƙara haƙuri kan matakan da muke ɗauka — Tinubu Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC Ya ce “Gwamnati ta samu labarin wani saƙon jaje da ake yaɗawa wanda mai ba gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin watsa labarai ya sa...
    Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
    “Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.” Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta. Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci. Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki. Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada...
    Wani jami’in yada labarai na babban yankin kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a amince da duk wani mahaluki ko wata runduna da za ta raba yankin Taiwan da kasar Sin ba, kuma babu yadda za a yi a lamunce da ayyukan “ballewar Taiwan” ta ko wace hanya. Jami’in yada labarun, da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Chen Binhua ya kara da cewa, matukar dakarun ‘yan awaren suka kuskura suka bari tura ta kai bango, za a dauki kwararan matakan mayar da martani a kansu. Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta...
    Shugaban kungiyar agajin Falasdinawa ta “UNRWA’ wacce MDD ta kafa, ya yi gargadin rushewarta da hakan zai hana Falasdinawa na yanzu samun ilimi, haka nan kuma bayar da kayan agaji da bukatun yau da kullum ga mutane miliyan 6 a Falasdinu. Shugaban kungiyar Agajin Philippe Lazzarini ya fada wa kamfanin dillancin labarun Faransa cewa; Da akwai hatsari da gaske da kungiyar take fuskanta na rushewa, da hakan zai kara dagula yanayin da al’ummar Falasdinu suke ciki.” Philippe Lazzarini ya kara da cewa; Idan hakan ta faru, to mun sadaukar da falasdinawan da suke rayuwa a wannan lokacin da hana su ilimi. Tun bayan farmakon Aksa 2023 ne dai  HKI da Amurka su ka dauki matakin haramta kungiyar da dakatar da...
    Babban abin da ya bai wa Sin nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri shi ne yadda gwamnati ta maida hankali wajen gina manyan ginshikai da tattalin arziki ke dogara da su domin samun ci gaba mai dorewa. Misali, irin layukan dogon da aka shimfida da suka sada ko wane lungu da sako a duk fadin kasar, da zamanantar da harkar sufurin jiragen sama da na ruwa, gami da bunkasuwar harkar yawon shakatawa ya janyo hankulan kasashen duniya tare da ba su kwarin gwiwa wajen rige-rigen zuwa Sin domin zuba jari. Tattalin arziki na zamani yana tafiya tare da fasahar zamani, kuma a fannin kirkirarriyar fasaha, kasar Sin tana a sahun gaba. Domin idan ba’a manta ba, a kwanakin baya Sin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban abin da ya bai wa Sin nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri shi ne yadda gwamnati ta maida hankali wajen gina manyan ginshikai da tattalin arziki ke dogara da su domin samun ci gaba mai dorewa. Misali, irin layukan dogon da aka shimfida da suka sada ko wane lungu da sako a duk fadin kasar, da zamanantar da harkar sufurin jiragen sama da na ruwa, gami da bunkasuwar harkar yawon shakatawa ya janyo hankulan kasashen duniya tare da ba su kwarin gwiwa wajen rige-rigen zuwa Sin domin zuba jari. Tattalin arziki na zamani yana tafiya tare da fasahar zamani, kuma a fannin kirkirarriyar fasaha, kasar Sin tana a sahun gaba. Domin idan ba’a manta ba, a kwanakin baya Sin...
    Ta ce tallafin zai taimaka wajen bai wa mata damar zama masu dogaro da kansu a fannin tattalin arziƙi. An raba kuɗin ne ga kungiyoyin mata manoma daga ƙananan hukumomi 13 a faɗin jihar, inda kowacce ƙungiya ta samu Naira miliyan biyu. Haka kuma, ƙungiyoyin matasa manoma su ma sun amfana da tallafin don bunƙasa ayyukansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya bar jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari. El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook. ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga a Abuja Ya ce bai gamsu da yadda ake tafiyar da APC ba cikin shekaru biyu da suka gabata. Yayin da yake zantawa da BBC Hausa, El-Rufa’i ya bayyana cewa ya sanar da Buhari kafin ya fice daga APC. “Na faɗa masa game da shawarar da na yanke a ranar Juma’a. Ina yawan tuntuɓarsa kan harkokin siyasata,” in ji shi. El-Rufa’i ya kuma tuna cewa...
    ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi, a Jihar Kebbi. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su. “Malam Rabe da ’ya’yansa biyar,...
    Kasashen Iran da Belarus, sun rattaba hannu kan wani daftari na bunkasa alaka ta haddin  guiwar tsaro a tsakaninsu. Ministan tsaron kasar Iran Aziz Nasirzadeh da takwaransa na kasar Belarus Viktor Khrenin ne suka rattaba hannu kan wata takarda kan fadada hadin gwiwar tsaron kasashen biyu. An rattaba hannu kan takardar ne a wata ganawar da ministocin biyu suka yi a Minsk, babban birnin kasar Belarus, inda bangarorin biyu suka kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaro da kuma hanyoyin zurfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu da inganta hadin gwiwar soji. A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan batutuwan da suka shafi tsaro tare da yin musayar ra’ayi kan hanyoyin zurfafa dangantakar dake tsakaninsu. A yayin...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
    Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna cewa, mutane na bayyana shakku kan manufofin haraji na sabuwar gwamnatin Amurka, kuma sun damu ainun da mummunan tasirinta kan kasuwar hannayen jari ta kasar dake tafiyar hawainiya. Wani mai bayar da amsa cikin nazarin ya kuma bayyana cewa, sanya haraji kan dukkan kayayyakin kasashen wajen, bai taba haifar da da mai ido ba. A baya bayan nan, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa,...
    Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama. Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da sauran sassan ƙasar. HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juyawa domin kai gas ɗin wani gidan mai, inda a nan ne ta faɗi ta yi bindiga. Mutane da dama da suka shaida lamarin sun ce ya ƙazanta, sakamakon...
    Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar. Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin ciyarwar. A yayin ziyarar, kwamitin ya duba yadda ake gudanar da shirin a kananan hukumomin Birniwa da Kirikasamma da Guri da Hadejia, inda aikin kwamatin ya mayar da hankali ga tantance nasarar shirin da gano matsalolin da ke bukatar gyara. A karshen ziyarar, Alhaji Yahaya Andaza wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, ya bayyana damuwa kan wasu kura-kurai da aka samu a cibiyar...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10. Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu. Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari. Wani ganau da ya buƙaci a sakaya...
    Domin tabbatar da zaman lafiya, an tura ƙarin jami’an tsar tare da haɗin gwiwar sojoji domin daƙile tashin hankali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024. Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya. A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta...
    An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar Talata. Lakurawa sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Kebbi Tsohon shugaban Philippines ya faɗa komar ’yan sanda Kwamishinan ya yi bayanin cewa ya zama wajibi duk wasu alamomi da aka gani a ɗauka a shiga da su ɗakin gwaje-gwaje a bincika domin a tabbatar ko ƙoshin lafiyar al’umma. Dakta Faruk Umar ya ce ma’aikatarsa za ta saka ido kan jami’an lafiya na gwamnati da masu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumomi sun tabbatar da cewar lamura dun daidaita a yankin, yayin da ‘yansanda suka miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masana na gargaɗin cewa idan NNPC ta daina sayar wa matatar Dangote mai a naira, hakan na iya haifar da hauhawar farashin man fetur, maimakon rage farashin da ake tsammani. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.   “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar bayar da bayanan sirri don cimma nasarar ayyukanmu,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a wajen taron manema labaru na ministan harkokin waje da aka shirya a harabar manyan tarukan kasar Sin guda biyu, lokacin da yake magana kan batun Taiwan cewa: suna daya tilo na Taiwan a Majalisar Dinkin Duniya shi ne “Lardin Taiwan na kasar Sin”. Kuma wasu sun yi amannar cewa, hakan ne ya sa manufar babban yankin kasar Sin a kan Taiwan ta zama mai tsaurin gaske. Da take mayar da jawabi game da wannan batu, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning, ta bayyana a wani taron manema labarai da aka saba gudanarwa da ya gudana yau 10 ga wata cewa, wannan shi ne daidaitaccen matsayin...
    An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987.   Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005.   A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka.   Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci...
    Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan alherai goma ga ma’aurata cikin Ramadan. 4. Salon buɗa baki Ma’aurata za su yi amfani da lokacin buɗa baki don ƙara kusanci, farfaɗo da shau’uka cikin zuciya da ɗumama sha’awa. Ma’aurata su tsara buɗa bakinsu ta yadda za su zama kamar dai su sabbin masoya ne da suka sami kansu tsundum cikin sabuwar soyayyar juna. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa Suna buɗa bakin cikin wasa da raha da tsokanar juna, ciyar da juna a baki, kallon marmasa soyayya da...
    Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi.   Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa. A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa...
    A bara, alkaluman tattalin arziki na GDP na kasar Sin sun kai yuan triliyan 134.9, inda aka samu karuwar kaso 5 cikin dari, lamarin da ya sa shi kasancewa tattalin arziki mafi saurin ci gaba cikin kasashen duniya masu karfin tattalin arziki. Ci gaban da ake samu na ingantuwar tattalin arzikin kasar ya haifar da tarin alfanu ga jama’a. Wani nazari da ya samu amsa daga mutane 25,883 daga kasashe 41 da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, ya nuna cewa, sama da kaso 80 na wadanda suka bayar da amsa, sun yaba da tsarin ci gaban kasar Sin dake mayar da hankali kan moriyar al’umma, tare kuma da amincewa da ingancin salon shugabancin gwamnatin kasar Sin. A shekarar...
    Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wasu masu kiwon, suna zuwa shagunan sayar da magani ne su sayo su rika bai wa dabbobin da suka harbu da wata kwayar cuta, ba tare da yin la’akari kan adadin magungunan da ya kamata su ba su ba”, in ji Ngulukun. Ana kuma bukatar masu kiwon su dakar da bai wa dabbonin nasu magunguna daidai da lokacin da misali, kajin gidan gona ke shirin fara yin kwai ko kuma lokacin da shanu ke shirin fara samar da madara, domin kare lafiyar mutane. Sai dai, abin takaici shi ne, akasarin masu kiwon; ba sa kiyaye irin wadannan lokuta, wanda hakan ke shafar lafiyar mutanen da suka yi amfani da irin wadannan dabbobi. Kazalika, yawan bai wa dabbobin magungunan barkatai don...
    Manyan Wuraren Da Cutar Ta Bulla Da Kuma Kididdigar NCDC Kamar yadda muka lakanto daga jaridar Blueprint, bincikensu ya nuna cewa, an samu bullar cutar zazzabin Lassan a shekarar 1970 a Nijeriya, inda sama da mutum 100 suka kamu da cutar. A tsakanin 1989 zuwa 1990, bullar annobar cutar a Nijeriya, ta yi sanadiyyar kamuwar mutane akalla sama da 1,000. Haka nan kuma, a shekarar 2018 an sake samun bullar cutar a kasar, inda mutane sama da 1,500 suka kamu da cutar, sannan adadin wadanda suka kamun sun doshi kashi 20 cikin 100. Kwana-kwanan ne, NCDC ta bayar da rahoton mutuwar mutum 80 daga cikin 413 da aka tabbatar sun kamu da cutar a cikin fadin jihohi 11 cikin mako...
    Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR. Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka...
    Aƙalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu a ranar Talata sakamakon fashewar wata tankar mai da ta tashi a Jihar Neja, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da lalata filayen noma a cikin unguwanni. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Ƙaramin Rami da ke ƙaramar hukumar Mashegu da misalin ƙarfe 6:30 na yamma. An yi garkuwa da ɗan uwan ​​Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna Najeriya ta kama hanyar gyaruwa – Remi Tinubu Rahotanni sun bayyana cewa haɗarin ya afku ne lokacin da wata motar ɗaukar kaya ta yi yunƙurin kaucewa wasu munanan hanyoyi. Waɗanda fashewar ɗin ta rutsa da su sun haɗa da: Rafiatu Sahabi da Ramlat Shehu da Rashida Abdullahi da Raliya Abdulrahman...
    Hukumar da take yaki da yi wa tattalin arzikin kasar  Najeriya zagon kasa, ta yi wa tsohuwar ministar harkokin mata Uju Kennedy,tambayoyi masu alaka da zargin da ake yi mata akan aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da wasu kudade da sun kai Naira miliyan 138.4 a karkashin kasafin kudin ma’aikatar tata a 2023. Da safiyar jiya Alhamis da misali 11: na safe ne tsohuwar ministar ta isa babbar shalkwarar hukumar ta EFCC dake birnin Abuja,inda ta amsa tambayoyin da aka yi mata. Majiyar hukumar ta EFCC ta ce da akwai wasu kudade da aka bai wa ma’aikatar a karkashin shirin nan na p-Bat cares, amma sai aka karkata su zuwa asusun tsohuwar ministar. Uju tana cikin minsitocin da ...
    Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp