2025-02-21@14:53:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 414

«Jami ar Yakubu Gowon»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Amincewa da Karin kudin dai ya zo ne domin cike gibin da aka samu, bayan da Amurka ta yanke kudaden taimakon da take bayarwa a fagen kiwon lafiya. A shekarar 2023 Kasar Najeriya mai mutane fiye da miliyan 200 tana cikin 10 na farko da su ka fi karbar tallafin hukumar Amurka na raya kasashe ( USAID). Sai dai a halin yanzu shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dakatar da wannan taimakon  na tsawon kwanaki 90. Wani dan majalisar dattijan Najeriya Sen. Adeola Olamkilekan wanda ya yi Magana a yayin zaman majalisar na amincewa da Karin kasafin kudin ya ce; Kasar ta za ji jiki sosai saboda yadda Amurka ta yanke tallafin, musamman a fagen dakile cutuka. Dala miliyan 200...
    Kakakin dakarun rundunar “Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa za su saki fursunoni 3 na “Isra’ilawa” a wannan rana ta Asabar.  A jiya Juma’a ne dai kakakin na dakarun rundunar “ Kassam” ya fitar da sanarwar cewa za saki fursunoni uku da suke rike da su da su ne: Shasha Alexander,Sagi Dikel Hen,Yaei Horun A ranar Litinin din da ta gabata ne dai mai Magana da yawun dakarun na “Kassam” Abu Ubaidah ta sanar da dakatar da duk wani batu na cigaba das akin fursunonin sai illa masha Allahu. Bayyana wancan matakin dai ya biyo bayan yadda HKI take kin aiki da sharuddan yarjeniyoyin sakin furnsunonin ne da su ka hada da hana mutanen arewacin Gaza komawa gidajensu. Haka...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baka’i ya yi tir da harin ta’addancin da aka kai a yankin na Baluchestan na kasar Pakistan wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama. A jiya juma’a ne dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya fitar da sanarwar akan kisan da ‘yan ta’addar su ka yi wa ma’aikatan hako ma’adanai dake yankin Harnai a arewacin gundumar ta Baluchestan. Haka nan kuma ya ce, a duk inda ayyukan ta’addanci suke faruwa jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin Allawadai da shi. Jami’in diplomasiyyar na Iran ya kuma jaddada bukatar ganin an kara samar da hadin kai a tsakanin Iran da kasar ta Pakistan a fagen fada da ayyukan ta’addanci. A...
    Gwamna Dauda Lawal ya mika makaman da gwamnatinsa ta bayar ga rundunar soji domin kafa hedkwatar rundunar Operation Safe Corridor na jihohin Arewa maso Yamma, a karamar hukumar Tsafe domin kwance damarar makamai, da lalata su da kuma shigar da barayin da suka tuba su koma cikin al’umma.   Gwamnan a wajen bikin mika ragamar sansanin da aka samar, ya jaddada aniyar gwamnatin sa na ci gaba da bin sawun ‘yan bindiga har sai an fatattake su da ruguza su da murkushe su.   Dokta Lawal ya ce gwamnatin jihar ta samar da wurin ne a matsayin wani shiri na taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance matsalar ta’addanci da ya addabi Zamfara da Arewa maso Yamma sama da shekaru goma.  ...
    Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53. Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Fim din da aka yi shi da kagaggun hotuna mai suna “Ne Zha 2” ya zama fim din kasar Sin na farko da ya samu zunzurutun kudi har yuan biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.39 bisa jimillar kudadensa da aka samu a duniya, ciki har da na ba da sautonsa, inda ya zarce misalin da aka yi hasashe a ranar Alhamis, bisa bayanan da aka samu daga dandalin sayar da tikiti na Maoyan. Wannan gagarumar nasarar da aka samu a rana ta 16 bayan fitowar fim din a ranar bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin da ta kasance ranar 29 ga watan Janairu, ta shiga jerin ci gaban da fim din ke samu na kafa tarihi....
    CBN ya ci gaba da cewa, dole ne dilolin su sayar da kudaden musayar ga masu hada-hadar sayar da kudaden, daidai da farashin kasuwar musayar kudade ta kasa, wato NFEM, musamman don a tabbatar da ci gaban tafiyar da farashin. Bankin ya kuma sanya kashi daya a cikin dari a tsakanin farashin da masu musayar kudaden, za su iya chazar masu sayen kudaden. “Dole ne dilolin da su gabatar da rahotannin su ga sashen kusuwanci da musayar kudade na CBN, na kudaden da suka sayar ga masu hada-hadar musayar kudaden, inda su kuma masu  hada-hadar musayar kudaden, dole ne su rinka gabatar da ribar da suka samu a kullum ta saye da sayar kudaden, ta hanyar amfani da tsarin cibiyoyin...
    Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, yana mai nuni da hakan a matsayin ci gaba da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon. Baqa’i ya yi nuni da cewa: Barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, wanda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar...
    Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani da kakkausar murya ga kalamai da kuma matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka ta hanyar halartar gagarumar zanga-zangar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran. Ayatullah Khatami ya kara da cewa: A yau daga mimbarin Juma’a da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran yana tabbatar da cewa: Miliyoyin Iraniyawa ne suka halarci...
    Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...
    ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka kaddamar da munanan hare-hare a kan sansanin Jenin sannan wani jirgin yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi luguden bama-bamai kan gidajen Falasdinawa. A gefe guda kuma, ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa sun gudanar da arangamar da sojojin mamayar, a sansanin Askar da ke gabashin Nablus. Yayin da a birnin Nablus aka yi artabu mai tsanani tsakanin ‘yan gwagwarmayar na Falasdinu da sojojin mamayar Isra’ila. A halin da...
    Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da  ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin, Zhang Xiaogang ya fitar da sanarwa kan batutuwan da suka shafi aikin soja a baya-bayan nan. Ya ce, Taiwan wani bangare ne na kasar Sin. Kuma babu wata tsokana da sojojin Amurka za su yi da za ta iya canza wannan lamari, sabanin haka, za ta iya nuna munafuncin da Amurka ta dade ta na yi ga al’ummomin duniya, kuma za ta iya kara karfafa niyyar jama’ar kasar Sin ta kare ikon kasa da cimma cikakkiyar dunkulewar yankunan kasar baki daya. Game da zarge-zarge marasa tushe da sabon ministan tsaron Amurka ya yi kan Sin, Zhang Xiaogang ya ce, Sin na adawa sosai da hakan. Kuma jama’ar kasar Sin na son zaman lafiya....
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya kammala ziyarar da yake yi a Birtaniya. Kakakin ma’aikatar Guo Jiakun ne ya bayyana hakan a yau, inda ya ce ziyarar ta Wang Yi ta cimma nasara da kyawawan sakamako. Ya ce wannan shi ne karon farko da ministan harkokin wajen Sin ya ziyarci Birtaniya cikin shekaru 10, kuma karon farko da Sin da Birtaniya suka gudanar da muhimmiyar tattaunawa cikin shekaru 7, lamarin dake nuna kudurin bangarorin biyu na ci gaba ingantawa da daidaita dangantakarsu. 2027: Ganawar Kwankwaso Da Aregbesola Ta Haifar Da Cece-kuce A Fagen Siyasar Nijeriya Firaministan Sin Zai Halarci Bikin Rufe Gasawar Wasannin Hunturu Ta Asiya Karo Na 9 Yayin taron, Sin...
    Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu. Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin kirkira sun hada da Toru-ebe da za a sassaka daga jihohin Delta da Edo da Ondo na yanzu, da kuma jihohin Ibadan da Lagoon da za a sassaka daga jihohin Oyo da Legas, bi da bi. Sauran sun hada da Jihar Ijebu da za a samar daga Jihar Ogun ta yanzu da kuma jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha da za a kirkiro daga jihohin Ogu da...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) karkashin jagorancin shugaban kasa Alhassan Yahaya, ta jaddada aniyar ta na inganta aikin jarida da kuma jin dadin ‘yan jarida a fadin Najeriya.   Kungiyar tana aiki tukuru don ganin an zartar da kudurin dokar inganta kafafen yada labarai a majalisar dokokin kasar don karfafa masana’antar.   A cikin sanarwar da ta fitar a karshen taron kaddamar da kwamitin koli (CWC), wanda aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, kungiyar na hada kai da Majalisar Dokoki ta kasa, kungiyoyin farar hula, da sauran masu ruwa da tsaki domin ganin an samar da dokar inganta harkokin yada labarai.   Sanarwar ta bayyana cewa, CWC ta yanke shawarar gano harkokin kasuwanci don samun kudaden shiga don...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bibiyar ’yan ta’adda har sai an fatattake su, an ruguza su tare da murƙushe su. Gwamnan ya miƙa kayan aikin da gwamnatin jihar Zamfara ta samar domin kafa hedikwatar tsaro ta dakarun sojin ‘Operation Safe Corridor’ na jihohin Arewa maso Yamma. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa ‘Operation Safe Corridor’ zai ta tabbatar da canja ƙwaƙwale, haɗe kai magance duk al’amuran da suka shafi ’yan bindiga. Sanarwar ta ƙara da cewa, an tsara shirin ne a ƙarƙashin Operation Safe Corridor a yankin Arewa maso Gabas, wanda ya yi nasarar sauya ƙwaƙwalen tsoffin mayaƙan Boko Haram tare...
    Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu. Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace. Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata....
    Manyan jami’an Philippines sun sake ikirarin shirin sayen makamai masu linzami dake cin matsakaicin zango na Amurka tare da hada su da batun tekun kudancin Sin. Hakika matakin na Philippines ya damka muradun kasar na tsaro a hannun kawayenta na yammacin duniya. Dabarar Philippines ta dogaro da kasashen yamma ba za ta samar da tsaro a kasar ba, sai ma akasin hakan. Saboda jibge makamai masu linzamin ya shafi tsarin tsaro na kasashen yankin kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN. A daya bangaren, Philippines na yunkurin cin gajiyar tekun kudancin Sin ta hanyar samun goyon baya daga kasashen dake wajen yankin, inda take ci gaba da takala da tada rikici da ma amfani da batun a matsayin wata dama ta...
    Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA).   A duk duniya, OCHA, wacce ke kula da CERF da Asusun Kula da Ruwa na Kasa (CBPFs) irin su Asusun Ba da Agajin Gaggawa (NHF), tana jagorantar matakai don taimaka wa miliyoyin mutane ta hanyar magance annoba kamar ambaliyar ruwa, fari, da kwalara.   A watan Oktoban 2024, CERF ta saki Dala miliyan 5 domin a kara kaimi wajen magance ambaliyar ruwa da kuma magance muhimman bukatu a jihohin Borno da...
    An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta kafofi daban daban sau miliyan 459, karuwar kaso 30 kan na bara. Kana an kalli liyafar ta talabijin har sau miliyan 189, karuwar kaso 12 idan aka kwatanta da bara. Baya ga haka, kallon liyafar kai tsaye ta kafofin zamani, ya kai sau miliyan 270, karuwar kaso 47 idan aka kwatanta da bara. A bangaren kasashen waje kuwa, kafar yada labarai ta CGTN wadda ke...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025. Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya. Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a...
     Wasu manyan malaman yahudawa 350 sun rattaba hannu akan wata wasika da a ciki su ka bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na fitar da Falasdinawa daga yankin Gaza. Wasikar ta kunshi cewa, Yahudawa ba su amince da  kiyan kiyashi ba akan Falasdinawa ba. Jaridar Guardian da ake bugawa a Birtaniya wacce ta dauki labarin tare da ambato wasu fitattun malaman na yahudawa da su ka rattaba hannu akan takardar, daga cikinsu har da Sharon Bruss, Roly Matalon, da Alisa Waiser, sai kuma wasu fitattun yahudawa a Amurkan. Cody Edgerly wanda daya ne daga cikin wadanda su ka rattaba hannu akan takardar, kuma shugaban kiran, ya nuna abinda shugaban na kasar Amurka yake son yi da...
    A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da ke Amurka (CGCC) da aka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka, Xie ya bayyana cewa, barazanar haraji ba za ta taba yin tasiri a kan Sinawa ba, a maimakon haka, masu yi za su buge ne da illata ginshikin yaki da miyagun kwayoyi da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kara tsadar kayayyaki ga iyalan Amurkawa da harkokin kasuwanci...
    A takardar, wadda mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Rabi’u Ibrahim, ya sa wa hannu, Idris ya ce: “Rediyo ko yaushe hanya ce ta samun ingantaccen bayani kuma abin dogaro ne ga al’umma, musamman a lokutan da ake fuskantar matsaloli.   “A ‘yan shekarun nan, rediyo ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan jama’a kan sauyin yanayi da tasirin sa ga duniyar mu. Tare da faɗin isar sa da sauƙin samun sa, rediyo yana da ikon ilimantarwa da ƙarfafa mutane su ɗauki matakan da suka dace don yaƙi da sauyin yanayi.”   Idris ya ambato jawabin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron COP29 na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi wanda aka gudanar a birnin Baku na...
    Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta sanar da cewa, za a ci gaba da musayar fursunoni kamar yadda aka tsara a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa. A yau Alhamis ne dai kungiyar ta Hamas ta sanar da  cewa za ta saki fursunoni kamar yadda yake a jadawalin da aka tsara. Tashar talabijin din Aljazira ta ambato majiyar kungiyar ta Hamas tana cewa, tawagarta tana tattaunawa d a Masar da Katar  a matsayinsu na masu shiga tsakani musamman akan yadda za a kai wa mutanen Gaza, hadaddun matsugunan da za su rayu a ciki da kuma magunguna da sauran bukatu na  kiwon lafiya na gaggawa. Haka nan kuma an warware matsalar kai kayan agaji da za a bari su rika shiga...
     Mutanen Najeriya suna  bayyana fushinsu akan kara kudaden sayen cajin shiga kafar sadarwa na Internet –Data- da manyan kamfanoni irin su MTN da Airtel su ka yi, saboda yadda ake fama da matsalar rayuwa. Kamfanin MTN shi ne mafi girma a tsakanin kamfanonin samar da hidimomi na hanyar sadarwa, inda a yanzu ake sayar da Giga 15, akan Naira 6,000 bayan da a baya take naira 2,000 ( wato daga dala 1.33-3.99) da hakan yake nufin cewa an rubanya farashin sau uku. Shi ma kamfanin Airtel ya kara yawan kudaden cajin nashi da kaso mai yawa. Wannan Karin da kamfanonin su ka yi, ya bakanta ran masu amfani da su, musamman a wannan lokacin da ake fama da yanayi mai...
    An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano. Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi. Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin. Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana: ...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Karfin kariyar Iran abin alfahari ne ga kawayenta yayin da makiyanta suke kara tsoro Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya dauki wannan batu na kare al’umma da tsaron kasar a matsayin muhimmin abu, ya kuma ce: Karfin tsaron da Iran take da shi shi ne abin da ake magana a kai a yau, kawayen juyin juya halin Iran suna alfahari da shi, yayin da makiyan Iran suke kara shiga cikin tsoro. A ganawarsa da safiyar yau Alhamis tare da tawagar malamai, kwararru da jami’ai na masana’antar tsaron kasa, Jagoran juyin juya halin ya dauki ranar 22 ga watan Bahman a matsayin biki mai girma da tarihi...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: ‘Yan Sudan miliyan 30 ne suke bukatar agaji kuma lamarin yana kara ta’azzara Mataimakin shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Edmore Tondlana ya yi gargadin cewa: Al’amura a Sudan suna kara tabarbarewa, yayin da ake ci gaba da fama da tashe-tashen hankula, mutane da dama suna gudun hijira da kuma samun karuwar matsalolin bukatun jin kai.    Tondlana ya nuni da cewa: Akwai matsalolin tsaro a Sudan saboda hau-hau-hawar farashin kayayyakin bukatu saboda rashin zaman lafiya a kasar. Dangane da yanayin yunwa da aka shelanta a wasu yankunan, ya yi gargadin cewa lamarin na kara ta’azzara saboda fadan da ake fama da shi a yankunan da suka hada...
    Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile ayyukan ta’addanci a jihohin Zamfara da Sokoto daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Fabrairun 2025.   A cewar wata sanarwa da kodinetan cibiyar yada labarai na Operation Fansan Yamma Laftanar Kanar, Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce harin ya yi sanadin fatattakar ‘yan ta’adda da dama da suka hada da wasu manyan ‘yan ta’adda.   Ta ce aikin na inganta tsaron rayuka da dukiyoyi a yankin.   Sanarwar ta bayyana cewa, a tsawon wannan lokaci, sojoji sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda da dama da suka hada da sarakuna irin su Kachalla Na Faransa, Dogon Bakkwalo, Auta Gobaje da Dan Mai Dutsi da dai sauransu.   Ya bayyana cewa, an kawar da da...
    Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa. Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano Haruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.
    Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano Ambasada Haruna Zago ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin ma’aikatan hukumar ne ta tabbatar da haka  Hausa rasuwar Haruna Zago a asibiti. A ranar 5 ga watan Yulin shekarar 2023 Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya naɗa Haruna Zago a matsayin Shugaban Hukumar REMASAB
    Har ila yau, ga irin su Apple, Microsoft, da Google da duk sun samu gindin zama a kasar Sin tare da bude ofisoshi da ressan masana’antu a biranen Shanghai, Beijing, da Shenzhen. Haka nan sauran kamfanoni irin su Coca-Cola, da PepsiCo duk sun tsayu da kafafunsu sosai a kasar. Bugu da kari, ga kamfanonin harkokin biyan kudi ta fasahar zamani kamarsu Amazon da PayPal da su ma suka samu hadin kan kamfanonin kasar Sin don fadada kasuwancinsu a cikin kasar. Duka wannan yana nuna yadda Sin ke fada da cikawa ne a kan manufofinta na kara bude kofa ga duniya. Kuma ya dace Amurka ta nuna sanin ya kamata a kan bahaguwar fahimtarta da sake lale kan matakanta na haddasa...
    A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin. Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)  
    Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa. Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.
    Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare. Kimiyya ba ta da iyaka. Idan muka waiwayi ci gaban bil adama, ba a taba raba kowace nasara da aka samu a binciken kimiyya da kirkire kirkiren fasaha da hadin gwiwa da musaya tsakanin kasa da kasa ba. Gwamnatin Sin na goyon bayan ci gaban kimiyya da fasaha ta kowane bangare, kuma a shirye take ta gabatar da gogewarta a fannin ga duniya. DeepSeek, samfurin...
    A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, har’ila yau jawabi ne ga barazanar da makiya JMI suke mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka bayan ya zagaya ya ga sabbin makamai wadanda masana’antun makamai na kasar suka kera. Ya kuma yaba da irin ci gaban da masana’antun suka samu. Imam Khaminae ya kuma yaba da ayyukan da masu...
    Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a lardin Kunduz na arewacin kasar Afganistan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 5 da kuma raunata wasu da dama. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto “Daesh Khorasan” tana fadar haka a shafinta na sadarwa, bayanda wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa a kusa da wani banki a garin Kunduz, wanda ya halaka shi ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar. Labarin ya kara da cewa an kai harin kunan bakin wakenne da misalign karfi 8:35 na safe a yau Laraba, wato 4:05 na safe agogin GMT. Mai gidan bankin da kuma wasu mutane 4 daga cikin akwai fararen hula da kuma wani...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana fadar haka a ganawarsa da Sarkin a birnin Washington a yau Laraba. A nashi bangaren Sarkin kasar ta Jordan ya bayyana cewa yana ganin kasashen larabawa zasu dauki mataki guda ne a cikin wannan al-amarin, sannan zasu ji ta bakin Yerima Muhammad  bin Salman na kasar Saudiya da kuma Shugaba Abdul Fattah Assisi na kasar Masar, wadanda suke...
    Karon Farko A Shekarar 2025: Turken Rarraba Hasken Wutar Lantarki Ya Fadi A Nijeriya
    Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saïd Iravani, ya bayyana cewa kalaman na Trump na tada hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD. Trump ya ce zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Iran maimakon “harba mata bam fiye da kima,” a wata hira da manema labarai a ranar Asabar. “Na fi son kulla yarjejeniya da ba za ta cutar...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar, inda ya jadadda cewar, Allah SWT ya azurta wannan Yanki na Tafkin Chadi da dimbin filayen noma wanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, na iya ba da gudummawa sosai wajen samar da abinci a yankin har ma da yankuna makwabta. Zulum ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin yankin da abokan haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin kafa gonakin noman...
    Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin mallakar makaman nukiliya da ya fitar da fatawa kanta a farkon takaddamar Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Jaridar ta ruwaito a cikin wani rahoton da wakilinta na musamman Akhtar Muhammad Makoy ya fitar cewa: Manyan jagororin sojojin Iran sun ce dole ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soke fatawar da ta haramta kera makaman nukiliya matukar gwamnatin Iran na son ci gaba...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
    Duk da haka, da alama cewa, waɗannan binciken ƙila ba su da isasshen ikon gano bindigogin da suka ɓace.   A yanzu haka dai, kwamitin majalisar dattawa yana zaune a Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.
    “Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ba da fifiko kan harkokin tsaro a jihar Zamfara, kuma ta ɗauki matakin da ya dace tun farko cewa sulhu da ‘yan bindiga ba komai ba ne illa ‘je ka na yi ka’. “A cikin hirarraki da manema labarai daban-daban, gwamnan ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta yo sulhu da ‘yan bindigar da ke addabar jihar ba. “Ya kamata a bayyana...
    An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
    Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Tafida, ya bayyana godiyar Gwamna Nasir Idris ga Sakatarorin kan irin gudunmuwar da suka bayar ga inganta bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi da kuma goyon baya ga gwamnatinsa a kan jagorancin al’ummar jihar.   Daga karshe, Gwamnan ya gode wa Sakatarorin kan irin yadda suka sadaukar da kansu wajen kawo cigaba a bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi 21 na fadin jihar tare da yi musu fatan alkairi a rayuwarsu ta gaba.
    ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN ya ce wannan sabon tsari zai ƙarfafa shigar da sabbin ATM a faɗin ƙasa tare da tabbatar da cewa bankuna suna cajin kuɗin da ya dace.
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin  Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban kasar ta Amurka wanda yake Magana da ‘yan jarida a ofis dinsa dake fadar White House, ya sake jaddada tsohuwar barazanar da ya yi tun kafin a rantsar da shi, na ce wa zai bude kofofin jahannama idan ba a mayar da fursunonin ba daga Gaza.” Donald Trump ya kara da cewa, ya yi Magana da Benjamin Netanyahu akan wa’adin na karshe a ranar Asabar...
    Ɗan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC
    Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
    ’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300. Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki. Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama. Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero Gwamnan Zamfara ya...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci shi ne kasantuwar kasa ta taka rawar al’umma da kyakkyawar hadin kai. Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa a jawabin da ya gabatar a karshen jerin gwanon na tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Tehran: Ba za su taba mika wuya ga kasashen waje ba. Ko da yake Iran bata neman yaki, amma tun ranar farko makiya suke...
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata rana. Trump ya kara da cewa a yayin zantawarsa da Tashar talabijin ta Fox News; Suna da kasa mai kimar gaske mai dauke da ma’adanai na musamman da man fetur da kuma iskar gas, da sauran abubuwa. Trump ya ci gaba da cewa: Yana son dukiyarsu ta kasance cikin aminci, domin suna kashe daruruwan biliyoyin dalolia cikin kasar. Ya karkare furucinsa da cewa; Za su...
    Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere, a daidai lokacin da sojoji ke ci gaba da barnata kayayyakin more rayuwa da kadarorin jama’a da kuma kame jama’a gami da tilastawa dubban mazauna sansanonin biyu gudun hijira. Sojojin mamayar suna ci gaba da killace sansanonin Tulkaram da Nourul Shams, sannan kuma suna kara yawan sintirin motocinsu da na tankokin yakinsu da kuma sintiri da kafa a yankuna da unguwannin su, a daidai lokacin...
    Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya takunkumi har sai ta dawo kan tsarin dimokiradiyya. Maganganun Wilson, wanda ya shahara da kare matakan muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma tsantsar kiyayya ga kungiyoyin gwagwarmaya da dukkan gwamnatocin Larabawa da na Musulunci da suka ki amincewa da Shirin daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ya fuskanci mayar da martani mai yawa a tsakanin ‘yan siyasar Tunisiya da masu fafutuka kare hakkokin dan Adama,...
    Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna. Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai. Wannan sabon samfurin yana da Faisal kamar fitilun, da hasken rana mai iya buɗewa, da tayoyin 17-inch alloy. Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna  Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza. Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku makiya sun gaza wajen cika yarjejeniyar da suka cimma’’. Hamas ta ce ‘’sakin karin wasu yahudawa na ranar Asabar 25 ga wata an jingine shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran makiya su mutunta yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata. Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar ta Hamas inda a wata sanarwa da ministan tsaron kasar ya...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar  al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu. Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado da Gabas Ta Tsakiya’’ Ya kara da cewa za a iya samun wurare daban-daban har guda shida don Falasdinawa su zauna a wajen zirin Gaza. Ya kuma ce za’a gina wa Falasdinawa gidaje masu kyau da inganci nesa da wajen da suke, saidai bai bayyana takamaiman wuri ba. A wani labarin kuma Donald Trump ya fada a ranar Litinin din nan cewa cewa “watakila” zai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
    Kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin, ya ce jarin manyan kadarori da kasar ta zuba a bangaren layin dogo ya kai yuan biliyan 43.9, kwatankwacin dala biliyan 6.12, a watan Janairun bana. A cewar kamfanin, adadin ya karu da kaso 3.7 bisa dari idan aka kwatantan da makamancin lokacin a bara. A wannan lokaci, an gudanar da manyan ayyuka, ciki har inganta layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen Chengdu da Chongqing. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana kayayyaki na ci gaba da samun bunkasuwa. Adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin ya kai kashi 52.5%, a watan Janairun da ya wuce, wanda ya karu da kashi 1.9% bisa na watan Disamban da ya gabata, adadin da ya kai koli a cikin watanni 10 da suka gabata. Sakamakon manufofin tabbatar da tattalin arziki da ingiza bunkasuwa, da ma yadda aka koma aiki bayan hutun...
    ’Yan bindiga sun kashe wani fasto, Rabaran Bala Galadima yayin harin da suka kai garin Lubo da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma yi fashin kuɗi har Naira dubu 300 a yayin harin da suka kai cikin dare wayewar gari Lahadi. Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan, waɗanda sun kai takwas, sun kai farmakin ne da misalin karfe 1 zuwa 3 na dare, inda suka firgita jama’a da harbe-harbe kafin su kutsa cikin gidan wani mutum mai suna Musa Puma. Majiyar ta ce maharan sun rutsa matar gidan da bindiga inda suka karbi kuɗi naira dubu dari 300 tare da yin garkuwa da ɗaya daga cikin ’ya’yansu da kuma...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma. A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Babban hafsan hafsishin sojojin Iran Manjo Janar Muhammad Bakri ya bayyana cewa sojojin Iran a shirye suke fiye da ko wani lokaci don kare JMI daga makiyanta. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Bakiri ya bayyana haka ne a lokacinda yake tattaki na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a nan birnin Tehran a safiyar yau Litinin. Ya ce: Halin da sojojin JMI suke ciki yafi na ko wani lokacin kyau, don haka a shirye suke su gudanar da ayyukansu a duk lokacinda bukatar haka ta taso. Dangane da tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kuma, Janar Bakiri ya bayyana cewa, jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul...
    Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar sa kuma tana ci gaba da taimaka mata, har’ila yau yana da yakini Iran zata ci gaba da taimakawa kungiyar Hamas har zuwa nasara. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta watsa jawabin Al-Hay kai tsaye daga birnin Tehran a safiyar yau litinin, inda ya yi Jawabi a dandalin Azadi dake tsakiyar birnin Tehran. Yace, farmakin ‘waadu Sadik na daya da na biyu duk...
    Sam Nujoma, dan gwagwarmaya neman yencin kasar Namibiya karkashin gwamnatin wariyar launin fata ta Afrika ta kudu, ya rasu a jiya Lahadi kamar yanda gwamnatin kasar ta Namibi a ta bada sanarwa. Shugaban kasar ta Namibia mai ci, Nangola Mbumba ya ce tsohon shugaban kasar ya na jinya a as wani asbiti a babban birnin kasar  Windhoek  na kimani makonni 3 amma rai yayi halinsa a daren Asabar da ta gabata ya na dan shekara 95. Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africanews’ ya bayyana cewa kasar Namibia ta sami yencin kanta ne daga hannun gwamnatin wariya ta Afirka ta kudu a shekara 1990. Sannan Nujoma ya zama shugaban kasar na farko na tsawon shekaru 15. Sannan aka zabi shugaba mai...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya.   Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar.   “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game da tallafin da ya ke bayarwa a jihar mu. Mun jingina da manufofin Bankin Duniya wajen inganta rayuwar al’ummar mu kawar da talauci da ci gaban ayyukan inganta rayuwa.   “Muna sane da ƙalubalen da muka fuskanta, wanda ya shafi gudanar da ayyukan ci gaba a jihar Zamfara, musamman waɗanda suka samu matsala wajen aiwatarwa, sakamakon yanayin da aka shiga. Amma, lallai babu shakka muna...
    Wasu ’yan daba sun gine-ginen makaranta a yankin Okpoga da ke Karamar Hukumar Okpogwu da ke Jihar. Ɓata-garin sun ƙona gine-ginen ne a Makarantar Sakandaren Central UBE da ke Ogwu-Okpoga da kuma Makarantar Ƙaramar Sakandare s ake Obossa. Wani shaida ya bayyana wa wakilinmu cewa a makon da ya gabata ne ’yan daban suka yi wannan aika-aika. Shaidan wanda bai amince a bayyana sunansa ba, ya yi zargin wata manufar siyasa ce ta sa ’yan daban suka cinna wa gine-ginen wuta. Ya bayyana damuwa kan yawaitar irin wannan aika-aika a ’yan kwanakin nan. Kokarinmu ma ji daga kakakin ’yan sanda ta Jihar Binuwai, Catherine Aneneh, bai yi nasara ba, saboda mun kira ta a waya ba ta shiga ba. ’Yan...
    An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano. An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka. Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka. Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka. ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi...
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
    “Zaben Alhaji Ibrahim Ibn Umar El-Kanemi, a matsayin sabon Shehun Dikwa, an gudanar da shi cikin lumana da hadin kai wanda sarakunan masarautar suka taka rawar gani wajen zakulo wanda ya dace,” in ji Zulum.   Ya bukaci sarkin da ya yi ba da jagoranci daidai da irin kalubalen zamani, yana mai jaddada rawar da masarautar ke takawa wajen farfado da Borno daga shekaru masu yawa na rashin tsaro.
    ’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun buƙaci al’umma su kawo musu rahoton duk wanda aka ga yana sana’ar bola-jari a cikin gari. Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Disu Olatunji, ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Tsaro ta Babban Birnin Tarayya wanda Minista Ezenwo Nyesom Wike ya jagoranta. Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Janairu, 2025 ne Hukumar Babban Birnin Tarayya ta haramta ayyukan ’yan bola-jari a cikin faɗin birnin. Umarnin ya taƙaita ayyukansu ga kan juji da ke ya yankunan da suke wajen birnin. A lokacin zaman ne aka dakatar da ayyukan ’yan gwangwan na tsawon makonni biyu, saboda zargin alaƙarsu da ’yan bola-jari. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Akan karkasa mutane gida-gida a bisa mizanin tattalin arziki, musamman a tsarin jari-hujja, inda ke da mawadata da kuma matalauta. A tsakanin al’umma kuma akwai ajin mutane masu matsakaicin samu waɗanda ake kira “Middle Class”. Akan sanya mutane a wannan aji ne galibi bisa la’akari da aiki ko sana’ar da suke yi, da kuɗin da suke samu, da matakin ilimin da suka kai, da ma matsayinsu a tsakanin al’umma. Sai dai a baya-bayan nan irin wadannan muntane sun bi sahun matalauta wajen korafi game da yadda suke dandana kudarsu saboda tsadar rayuwa. NAJERIYA A YAU: Dalilin Faɗuwar Farashin Tumatur A Kasuwa DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’...
    Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
    Siyasar tsananata matsin lamba kan Iran ta gaza cimma buri kuma hana fitar da man da Iran ke fitarwa mafarki ne da ba zai tabbata ba Ministan mai na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana matsayar matsin lamba da Amurka ke yi kan fitar da man kasar Iran a matsayin siyasa ta nuna gazawa, yana mai cewa: Hana fitar da man fetur din Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa wajen kasar, mafarki ne da ba zai taba wanzuwa ba. Ministan mai na Iran Mohsen Paknejad a matsayin mayar da martani ga furucin Trump ta sake dawo da tsananta siyasar matsin lamba da nufin gurgunta harkar tattalin arzikin Iran ta hanyar hana ta fitar da man fetur, a jiya Lahadi ya bayyana...
    Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Za su iya rufe mashigar Hormuz, amma ba za yi hakan a yanzu ba Kwamandan rundunar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Reza Tangsiri ya yi bayani kan irin fitattun abubuwan da jirgin ruwan da Iran ta kera mai suna Shahid Bahman Baqiri, inda ya ce; Wannan jirgi shi ne nau’i daya tilo saboda babu wata kasa a yankin yammacin Asiya da ke da makamancinsa. Birgediya Janar Tangsiri ya bayyana a cikin shirin ”Labarin juyin juya hali” a tashar Al-Alam cewa: Bayan sanarwar da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar dangane...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta. Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979, daya daga cikin bangarorin da aka sami gagarumin ci gaba a cikinsa shi ne, bunkasa sana’ar gine –gine da kuma samar da masana’antu, wanda ya kai ga kasar ta kai ga wadata a wannan bangaren, wani abu daga kasashen waje, sai abunda ba za’a rasaba. Har’ila yau wannan ya wadanar da mutane da dama a kasar. Kafin haka idan mun dubi...
    Wani babban jami’in Ƴansanda, ASP Shafi’u Bawa, na rundunar 61 Police Mobile Force (PMF), an tsinci gawarsa a dakinsa a garin Kontagora, Jihar Neja, a ranar Asabar, bayan da ake zargin ya kashe kansa. Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gano gawar ASP Bawa rataye a saman silin ɗin ɗakinsa. Mahaifinsa, Malam Usman Bawa, ne ya fara gano lamarin kafin ya kai rahoto ofishin ‘yansanda na Kontagora. Matsalar ‘Yan sandan Amurka Ta Nuna Karfin Tuwo Na Kara Tsananta Abin Fashewa Ya Hallaka Mutum Guda, Ya Jikkata 6 A Neja Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa: “A ranar 8/2/2025 da misalin ƙarfe 2 na rana, an samu rahoton cewa ASP Shafi’u Bawa...
    Shugaban kasar Namibia dake kan gado Nangolo Mbumba ne ya sanar a yau Lahadi cewa, jagoran samun ‘yacin kasar Sam Nujoma ya rasu a jiya Asabar da dare, bayan da aka kwantar da shi a wani asibitin babban birnin kasar Windhoek. Sanarwar da shugaban kasar ta Namibia mai ci a yanzu, ya fitar ya bayyana mutuwar Nujoma da cewa; ginshikin da aka kafa kasar akansa ya girgiza. Sam Nujoma ya jagoranci fadan sama wa kasar ta Namibia ‘yanci daga mulkin nuna wariyar launin fata na Afirka ta kudu, a shekarar 1990, sannan kuma ya jagoranci kasar na tsawon shekaru 15. A lokacin da yake a raye, al’ummar kasar ta Namibia suna girmama shi matuka a matsayin wanda ya jagoranci fadan...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya yi kira da a kafa kawancen duniya da dukkanin kasashen musulmi za su shiga ciki, domin taimakawa mutanen Gaza, da sake gina yanki, tare da cewa, kasashen musulmi kadai za su iya sake gina yankin na Gaza tare da dawo da rayuwa a cikinsa. A ganawar da ya yi da mambobin majalisar jagoranci ta kungiyar Hamas, anan Tehran ya yi jinjina ga shahidan kawancen gwagwarmaya, ya kuma yi murna akan nasarar da ‘yan gwgawarmaya su ka samu akan ‘yan sahayoniya. Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Nasarorin da mutanen na Gaza su ka samu, sun hana makiya ‘yan sahayoniya cimma manufofin da su ka shata, duk da cewa adadin shahidan da aka...
    “Da sauri jami’an ‘yansanda suka isa wurin, inda suka gano wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Promise Eze, ‘yar Jihar Ebonyi, daure a wata karamar kujera an rufe bakinta da filasta. An same ta a sume kuma cikin damuwa. Jami’an ‘yan sanda sun dauki matakin gaggawa, inda suka kubutar da ita daga hannun wadanda aka yi garkuwa da su, sannan suka garzaya da ita asibitin gundumar Wuse, inda ta farfado,” in ji sanarwar. Adeh ta ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa Eze ta leka otal din a safiyar ranar 30 ga watan Janairu tare da Okoro, wanda ta hadu da shi ta intanet. A cewarta, wanda ake zargin ya gabatar da kansa a matsayin ma’aikacin kamfanin...
    Wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya ce: Juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon samfuri na hadin kan al’umma Ayatullah Mojtaba Hosseini, wakilin Jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Iraki ya bayyana muhimmancin hadin kan al’ummar musulmi da kuma nauyin da ya rataya a wuyan musulmi na daidaiku da na al’umma dangane da manufofin juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: juyin juya halin Musulunci ya gabatar da wani sabon salo na hadin kan al’ummar musulmi. A jawabin da ya gabatar na zagayowar samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran da aka gudanar a tsohon gidan da Imam Khumaini (r.a) da ya zaune a birnin Najaf, Ayatullah Husaini ya jaddada muhimmancin hadin...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da gwamnatin mamayar Isra’ila a yankin. Jaridar ta bayyana cewa: Runduna ta 162 ta sojojin mamayar ta sake matsawa zuwa kusa da kan iyaka da kuma janyewa daga yankin Netzarim na nufin cewa, babu sojojin mamayar Isra’ila a arewacin...
    Sojojin Sudan suna kokarin canza ma’aunin yaƙin kasar bayan da suka sun tunkari birnin Khartoum fadar mulkin kasar domin yantar da shi gaba daya Babban birnin kasar Sudan, Khartoum, shi ne tushen rikicin kasar da a halin yanzu aka shafe makonni ana gwabza fada tsakanin sojoji da mayakan dakarun kai daukin gaggawa, amma fadan ya kara kamari a ‘yan kwanakin da suka gabata. Sojoji suna kara ci gaba da tunkarar babban birnin kasar bayan fitattun sojojin kasar da suka hada da sojoji da mayaka masu goyon bayan sojoji da hukumar leken asiri da dakarun tsaron Sudan da suke sansanin Haddab da ke bangaren arewa maso gabashin yankin Gabashin Nilu a arewa maso gabashin Khartoum suka doshi birnin na Khartoum da...
    Ga wasu manyan ‘yan kwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, wadanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu baki daya ko wani daga cikin iyayen ‘yan Nijeriya ne.   Jamal Musiala (Jamus) Matashin dan wasa Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen dan kwallon kasar Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta Jamus din kuma yana cikin matasan ‘yan kwallon da suke tashe a duniya a yanzu saboda ba za ka lissafa matasan ‘yan wasa guda biyar ba a duniya ba tare da ka saka sunansa ba. An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin can Nijeriya ne, wanda ya...
    A yau Asabar, 8 ga wannan wata da safe, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kwamitin JKS da gwamnatin lardin Jilin a birnin Changchun dake lardin Jilin. Bayan kammala sauraro, shugaba Xi ya yi jawabi inda ya jaddada cewa, ya kamata hukumomin lardin Jilin su aiwatar da shirin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin a dukkan fannoni a sabon zamani da kwamitin tsakiya na JKS ya tsara, da tabbatar da tsaron kasar a fannoni 5, da maida hankali ga aikin samun ci gaba mai inganci, da bin tsarin tunanin sabon ci gaba, da bude kofa ga kasashen waje, da yin kwaskwarima a dukkan fannoni,...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Nadin na kunshe cikin wata sanarwar da Kakakin Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yammacin ranar Asabar 08, ga Febarairun 2025. Dalilan Da Suka Sa Gwamnan Kano Sallamar SSG Da Wasu Kwamishinoni 5 Gwamnan Kano Ya Karyata Jita-jitar Rikicinsa Da Sakataren Gwamnatin Jihar Nadin Na Ibrahim zai fara aiki ne daga ranar Litinin mai zuwa 10, ga Febarairun 2025. Sanarwar nadin ta bayyana cewa an zabi, Ibrahim a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar saboda shafe sama da shekaru talatin ya na aikin gwamnati da tarin kwarewar aiki da yake da ita a hukumomi da ma’aikatu daban-daban...
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
    Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
    Jihar Adamawa ta rasa shahararre kuma babban malamin addinin musilunci, Sheikh Ibrahim Abubakar Daware, ranar Juma’a, bayan fama da rashin lafiya. Sheikh Daware ya kasance malami mai karamci wanda yake koyar da darussan addini da kuma gudummawa a kasashen musulmi daban-daban da sassan jihohin Nijeriya da dama. Dauda Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Almajirai 17 Da Suka Rasu A Sakamakon Tashin Gobara A Zamfara Uwargidan Tinubu Ta Kai Wa Gwamnan Jigawa Ziyarar Ta’aziyyar Rasuwar Mahaifiyarsa Da Ɗansa An gudanar da jana’izar malamin kamar yadda addinin musilunci ya tanada a gidansa da ke karamar hukumar Fufore a ranar Asabar. Sheikh Ibrahim Daware, ya rasu ya na da shekaru 71, ya bar matan aure hudu da ‘ya’ya 43 da jikoki 53.
    Xi Ya Umarci Ceto Daukacin Mutanen Da Suka Nutse A Ruftawar Kasar Da Ta Auku A Kudu Maso Yammacin Sin