2025-03-16@08:28:40 GMT
إجمالي نتائج البحث: 117
«farashin kayan abincin»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...
Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa. Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami. Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar cewa wata shida bayan kammala ba su horo da sauya tunanin tsofaffin mayaƙan, amma har yanzu babu labarin ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya yi tubar muzuru. Shugabar Sashen Daƙile Rikice-rikice Masu Alaƙa da Tsattsauran Ra’ayi (PVEA) ta Cibiyar, Ambasada Mairo Musa Abbas, ce ta bayyana haka a yayin taron gwamnonin yankin Tafkin Chadi a Maiduguri, Jihar Borno. NAJERIYA...
Gwamnati Ta Sake Haɗa Tubabbun Mayaƙan Boko Haram 5,000 Da Iyalansu

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta. A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan. Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba. A halin yanzun babu wata kasa, ya...
Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki. Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba. Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin. A ranar Litinin din da ta gabata...
Dakarun rundunar Operation Fansar Yamma sun ce sun ƙwato tarin makamai a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda na Jihar Zamfara. Dakarun tare da haɗin gwiwar jami’an tsaron farin kaya (DSS), sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan masu safarar makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya. Tankar mai ta sake fashewa a Neja Jadawalin Gasar AFCON 2025 da za a fafata a Morocco Wata sanarwa da jami’in yaɗa labaran rundunar, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce sun ƙaddamar da farmaki ranar 27 ga watan Janairun 2025, abin da ya kai ga ƙwato makaman kan hanyar Namoda zuwa Zurmi. Ya ce waɗanda ake zargin sun tsere zuwa cikin daji tare da barin motarsu bayan artabu da sojoji. Kanal Abubakar ya...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin. ///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen wadannan yankuna suka kwarara zuwa gidajensi, amma ko da suka isa sai suka ga cewa sojojin kasar Lebanon sun sha shinge don hana mutane wucewa zuwa wadannan wurare, don har yanzun akwai sojojin HKI a yankin suna iya kashe su. Banda haka sojojin HKI sun kara wayoyin wasu daga cikin mutanen wadannan yankuna, suna fada masu cewa kada su kuskura su shiga wadannan yankuna. Amma...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan. Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron Maulidin Shehu Ibrahim Inyass na ƙasa da aka gudanar ranar Asabar a jihar. Ɗan shekara 30 ya mutu a kududdufi a Kano ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike “Mun ankarar da jama’a sannan muka ɗauki matakan da suka dace domin tunkarar lamarin,” in ji CP Garba. Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin dangane da lamarin...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
Gomman sojoji da mayaƙan sa-kai na Sibiliyan JTF sun kwanta da dama a wata arangama da mayaƙan Boko Haram a yankin Mai-saleh da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe. Majiyoyin tsaro sun bayyana ce ’yan na Boko Haram sun kai wa jami’an tsaron hari ne bayan da jami’an tsaron sun kwace wani babban sansaninsu da ke Mai-Saleh a tsakanin jihohin biyu. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro mai barin gado, Manjo-Janar Edward Buba, ya tabbatar da rasuwar sojoji 22 a harin. “Jimillar sojoji 22 ne suka rasu wasu da dama sun jikkata a yayin artabun,” in ji Edward Buba. Amma wasu majiyoyi sun ce sojojin da suka kwanta dama sun haura 27. Mace ta rasu, wasu sun jikkata yayin da...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...
Majiyoyin leken asirin da suka tabbatar da harin, sun kara da cewa maharan sun kai hari sansanin ne dauke da muggan makamai, inda suka ce ‘yan ta’addan sun lalata gine-gine da dama da kuma motocin aikin soji a yayin harin.
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...