2025-03-01@17:08:10 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1473

«tabbatar da tsaro»:

    Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Amma duk da haka, hatta wake-wake da raye-raye da kuma abinda ya shafi sinima, tsofaffin jarumai ne su ka kawo su a masana’antar Kannywood, saboda haka ya kasance wani lokaci mai ban sha’awa a tarihi lokacin da Hamisu Lamido Iyan-Tama ya hadu da Hindatu Bashir a kan dandamali don ba shi lambar yabo. Dukkanmu sai muka tuna da fim dinsu na Badakala (wanda wani jarumi Bashir Mudi Yakasai ya shirya), inda suka yi fim mai dauke da rawa da waka na farko a cikin fina-finan Hausa,wato a shekarar 1997 wannan fim ya daga abinda yanzu ake kira Hausa Afropop, domin shi ne wakar fina-finan Hausa ta farko da aka kai wa Rabi’u BK a kasuwar Kofar Wambai domin sayar da...
    Gwamnatin Yobe ta raba wa ma’aikatan gona babura guda 200 domin gudanar da ayyukan kula da harkokin noma a jihar. Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa, Ali Mustapha Goniri ne ya bayyana haka a lokacin da yake miƙa baburan ga waɗanda suka rabauta. Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa Yadda ake ‘Spring rolls’ Ya ce an yi rabon baburan ne domin tallafa wa ayyukan ma’aikatan da kuma bunƙasa noman zamani a jihar ta hanyar sabbin dabaru da kayan aiki. Goniri ya ce ma’aikatar gona za ta sa ido kan yadda ma’aikatan da ke aikin faɗaɗa ayyukan noma ke yi domin tabbatar da cewa manoma a kowane lungu da saƙo na jihar suna noman amfanin gona da iri...
    Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan Ramadan din ba, kuma mu sa kasar mu cikin addu’a Allah ya bamu dacewa. Sunana Abubakar Ahmad, daga Jihar Nassarawa: Ga me hali ya kan shiryawa gajiyayyu marasa hali, wanda kuma Allah bai hore masa ba ya shiga sahun wanda sai dai a dauka a basu su wadannan ba sa shirya komai face yawan salloli da addu’o’i da neman taimakon ubangiji Allah ya fitar...
    C- A nan ganyen zogalen da kika tafasa sai ki zuba a faranti ki yanka tumatir manya guda uku, ki yanka gurji (cocumber) babba guda daya, ki saka magi, gishiri kadan, mai kadan. Kar ki sa wulikuli. Zai yi miki maganin basir da cikowar gaba. Zai kara mi ki ni’ima da dandano sosai. 5) Ruwan Dabino: Ki bare dabinonki rabin kwano, ki jika da ruwa. Idan ya yi luguf sai ki markada a ‘blander’. Za ki gan shi da kauri kirtif. Sai ki ajiye a firinji; duk sanda za ki sha sai ki debi cokali biyu ki zuba a kofi, ki juye madarar ruwa gwangwani daya, ki sa garin minannas karamin cokali ki juya sosai. Idan ya yi kauri da...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan. Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan. “Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar. “Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.” Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar...
    A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA)’ ta haramta amfani da iran wadannan tankunan man ne daga yau Asabar 1 ga watan Maris, saboda ceton rayukan mutanen kasar. Dokar dai zata shafi ayyukan mutanen, don wasu zasu rasa ayyukansu. Dokar ta kara da cewa, daga yau tankunan man masu daukar lita 45,000 zuwa kasa ne kawai za’a a barisu dauki man fetur zuwa wasu wurar daga deport. Sai kuma kungiyar...
    Wata gobara da ta tashi cikin ta lalata wani ɓangare na Asibitin Ago da ke kan titin Ago Palace, Okota, a Jihar Legas. Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Juma’a, inda ta shafi wani sashe na ginin mai bene hawa ɗaya, inda asibitin yake. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Likitoci da marasa lafiya da ke cikin asibitin sun tsere domin tsira da rayukansu yayin da wutar ta bazu. Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Lagos (LASEMA), Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce jami’ansu sun isa wajen gobarar da misalin ƙarfe 8:45 na...
    Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla. Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a wannan wata a fagen kasa da kasa. Tawagar damben gargaji ta kasar Iran ita ce zakara a gasar damben na wannan shekara ta 2025 haka ita ce zakara a gasar shekara ta 2024. An gudanar da gasar ne a ranakun 27-28 na watan Fabrayrun wannan shekara, wato 2025UWW, wanda ya jawo hankalin masu shaawar wasan a duniya. Daga cikin yan wasan da suka sami lambar...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance  matsalar da Falasdinawa suke...
    Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru. Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu. Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya...
    ‘Fake Inbestment Schemes’: Masu cuta na amfani da shafukan zuba jari na bogi domin damfarar mutane. Ransomware: Wasu barayin yanar gizo na saka kwayoyin cutar kwamfuta domin su hana mutum amfani da na’urarsa sai ya biya kudi. Hanyoyin Kare Kanka Yi amfani da kwayoyin kalmomin sirri masu karfi – A guji amfani da kalmomin sirri kamar sunanka ko shekarunka. Yi amfani da Two-Factor Authentication (2FA) – Wannan yana 1ara kariya ga asusunka. Guji danna hadin gwiwa (links) daga tushe da ba a san su ba – Yawancin wadannan hanyoyin suna da cutarwa. Ka tabbata cewa shafin da kake ziyarta yana da alamar ‘https’ – Wannan yana nuna cewa shafin yana da kariya. Kar ka raba bayanan sirrinka da kowa –...
    Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mandalari da ke Konduga a Jihar Borno, ta hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama. Gobarar, ta tashi da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, ta bazu zuwa yankunan da ke da cunkoson jama’a, inda ta cinye matsugunan wucin gadi da kuma kayayyaki masu tarin yawa. Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Sojojin da aka jibge a Konduga, sun kai ɗauki nan take bayan samun labarin tashin wutar. Sun haɗa kai da jami’an agaji da kuma al’ummar yankin domin shawo kan gobarar. Duk da haka, akwai fargabar...
    Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su. Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji shi. Tun da farko dai, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne mahukuntan jami’ar suka rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan abokin aikinsu. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu a Katsina a safiyar ranar Litinin cewa, “wasu jami’an CJTF sun bindige dalibai biyu ne bisa kuskure, suna tunanin...
    Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Lokacin harin, mutum biyu sun jikkata, yayin da ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya rasa ransa sakamakon harbin da wani daga cikin mutanensa ya yi. Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace...
    Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Ƙasa Hidima (NYSC), Manjo Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 22 a hannun ’yan bindiga. An sace shi ne a ranar 6 ga watan Fabrairu, 2025, a gidansa da ke garin Tsiga a Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, yayin da wasu ’yan bindiga suka kai hari. Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250 Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta Maharan sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 250 kafin su sako shi. Sai dai bayan tattaunawa, an biya kuɗin fansa, wanda ya kai ga sakinsa. A halin yanzu, likitoci na kula da shi a wani asibiti da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan. A nan  Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai...
    A jiya Juma’a ne dai aka yi jana’izar shahidan Hizbullah 130 a garuruwan Aytas-sha’ab da Aytarun da suke da kudancin Lebanon. Tashar talabijin din al-manar ta watsa taron jana’izar shahidai 95 da su ka yi shahada watanni uku da su ka gabata a yayin yaki da HKI. A garin Aytrun da shi ma yake a kudancin Lebanon an yi jana’izar shahidai 35. Dukkkanin jana’izar biyu ta sami halartar dububan mutane daga cikin garuruwan da kuma wajensu.  A gefe daya, a daidai lokacin da ake gudanar da jana’izar mutanen a garin Aytatun, sojojin HKI sun kai hari a gefen garin, sai dai babu rahoto akan shahada ko jikkatar mutane. Dan majalisa mai wakilntar Hizbullah a majalisar dokoki Hassan Fadlallah wanda kuma...
    Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya: 1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya: A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100, wanda bukatarsa da ake da ita a Nijeriya a shekara daya, ta kai kimanin tan miliyan 3.4, inda sauran wanda ake bukatar fitarwa waje ya kai kashi 60 cikin 100. 2- Kamun Tarwada A Nijeriya Fitacciyar Sana’a Ce: Samar da Tarwada a Nijeriya, ya karu daga tan miliyan 21,700 a 1999 zuwa tan miliyan 316,700 a 2015, wanda ya karu da sama da kashi 1,400...
    Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara. Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya. Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn Yayin bikin rabon dabinon, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da tallafa wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya. Ya jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da...
    Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru. Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako. Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa,...
    Fira ministan hakar Habasha  Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu. Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta Habasha ya kulla yarjejeniya da yankin Somaliland akan tashar jirgin ruwa. Ita dai kasar ta Habasha ba ta da iyaka da ruwa, don haka take son amfani da mashigar ruwan kasar ta yankin Somaliland. Habashan dai tana son gina wani yanki na kasuwanci a gabar ruwan  ta yankin Somaliland.  Yankin Somaliland na kasar Somaliya ne wanda Mogadishu  take daukar cewa ba kasa...
    Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027. Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasar. Kazalika, ya yaba wa Shugaban Kwamtin kan gundunmawar da ya bayar wajen gainin an samar da wadannan ayyuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Saɓanin shekarun baya, azumin watan Ramadan na bana ya zo a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa farashin kayan abinci na sauka a sassan Najeriya. Kayayyakin masarufi irinsu shinkafa da wake da fulawa na daga cikin waɗanda aka fi sarrafawa a watan na Ramadan, kuma su ne masu gwaggwaɓan kaso a faɗuwar farashin. Farashin kayan masarufi na sauka a wannan karo ne baya kimanin shekara biyu a jere suna tashi a ƙasar. Haka kuma, ana iya cewa ’yan Najeriya sun saba ganin tashin farashin kaya, musamman na abinci, a gabnin watan Ramadan. Duk da mutane suna nuna jin daɗinsu da saukar farashin a wannan karon, amma wasu na cewa hakan bai kawo sauƙi ga talaka ba, a wannan lokaci...
    Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka. 2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata. 3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya....
    Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka. 2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata. 3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya....
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    1.1 Abinci sahur yana da albarka; yin sahur albarka ne, haka ma abincin sahur abinci ne mai albarka. Ana karɓo hadisi daga Miƙdãm ɗan Ma’adikarib Allah ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Ina horonku da cin abincin sahur, domin abinci ne mai albarka” Nasã’i (Almujtabã 4/149 da Sunanul Kubrã 2/115) da Ahmad (Musnad #17192) da salsala ingantacciya. An karɓo daga Abud Dardã’i Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Shi sahur abinci ne mai albarka.”Ibnu Hibban (Al’ihsãn #3464) Ɗabarãni (Mu’ujamul Kabir 17/131 hadisi mai lamba 322). An karɓo daga Irbãdu ɗan Sãriyatu Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya gayyace ni cin...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta duba yiwuwar inganta cibiyar lafiya tare da kafa makarantar sakandare a garin Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da gidan marayu da makarantar islamiyya, wanda dan asalin yankin Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya ya gina a matsayin wakafi ga mahaifinsa. Malam Umar Namadi ya bayyana jin dadinsa bisa wannan  kokari na Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya. Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan matakin domin amfanin talakawa da marasa galihu a cikin al’umma. Ya  jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da irin wadannan mutane...
    Ita kuwa Kasar Algeria, ita ce ta uku; inda ta noma Dabino kimanin tan miliyan 1.25. Hadakar tsakanin Gwamnatin Jigawa da Saudiyya da kuma wani kamfanin aikin noma da ke kasar nan, wato ‘Netay Agro-Tech’, za ta kara taimakawa wajen sake habaka noman Dabinon a jihar. A duk shekara, Nijeriya na noma Dabino kimanin tan 21,000, inda Jigawa ta kasance daga cikin jeren masu noman nasa. A jawabinsa a gidan gwamnatin jihar da ke Dutse, a lokacin da ya karbi tawagar wata babbar gona da ke Kasar Saudiyya, wadda ta kware wajen noman Dabino tare da ba shi kulawar da ta dace, gwamnan jihar, Umar Namadi ya bayyana cewa, sabuwar hadakar za ta bude sabon babi ga noman Dabino a...
    Bayan da Mr. Donald Trump ya sake hawan kujerar shugaban kasar Amurka, ya dakatar da kusan dukkan gudummawar da kasarsa ke samarwa ga kasashen ketare, bisa manufarsa ta wai “Amurka ta zamanto gaba da komai”. Sai dai a kwanakin baya, gwamnatin kasar Philippines ta sanar da cewa, Amurka ba ta dakatar da gudummawar soja ta kimanin dala miliyan 336 a gare ta ba. To, amma me Amurka take iya samu daga gudummawar soja da take samarwa Philippines har ya sa ba ta dakatar ba? Dalili shi ne gudummawar na iya sa sojoji da ‘yan sanda da ma ‘yan siyasa na kasar ta Phillipines su taimaka mata cimma manufarta, musamman ma wajen neman dakile kasar Sin bisa ga yadda suke sa-in-sa...
    Kazalika, wannan kimiyya abar maraba ce ga masu kiwon Shanu, musamman ga wadanda ke bukatar fadada samar da ingantacciya kuma wadatacciyar Madara a guraren kiwonsu. Kirkirar kimiyyar, ta zo kan gaba duba da kokarin niyyar da Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta sanya a gaba, ta zamanantar da kiwon dabbobi da kuma habaka samar da wadatacciyar Madarar Shanu a kasar nan. Ana dai ci gaba da bukatar ingantacciyar Madarar Shanun a fadin wannan kasa, sai dai ana ci gaba da fuskantar kalubalen lafiyayyun Shanun, musamman a kasa irin Nijeriya. Sabuwar kimiyyar za ta bayar da damar saurin sanya ido kan yadda kiwon lafiyarsu ke tafiya, saurin gano ko sun harbu da wata kwayar cuta da kuma kula da lokacin nakudanarsu. “Wannan...
    An shawarci gwamnatin tarayya da ta sanya ido sosai kan yadda za a biya ariyas na kudaden fansho da suka kai biliyan ₦758. Wani masani kan harkokin kudi, Farfesa Yushau Ibrahim Ango ne ya bayar da wannan shawarar a Kaduna yayin da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa PENCOM ta yi alkawarin kammala biyan kudin cikin watanni uku. Farfesa Yushau Ango ya bayyana cewa, takardun lamuni yawanci kayan aikin kudi ne na dogon lokaci da ake samu daga masu saka hannun jari don warware basussukan da ake bin gwamnati, wanda yakan dauki lokacin da aka kayyade. Ya nuna damuwarsa kan cewa bai kamata a rika rike irin wadannan kudade a bankunan kasuwanci da masu kula da fansho...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan 54.99. A ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa. Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki  A baya dai, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin da ya kai Naira tiriliyan 49.7, amma daga bisani aka ƙara adadin kuɗin. Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin a ranar Juma’a, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Kasafin kuɗin na 2025 ya ninka wanda aka yi a bara, wanda ya tsaya a Naira tiriliyan 27.5, da ƙarin kashi 99.96...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da ya kai Naira tiriliyan 54.99. A ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025, Majalisar Dokoki ta amince da kasafin bayan tattaunawa da nazari a kansa. Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Gwamnatin Sakkwato ta nemi malaman Jami’a su janye yajin aiki  A baya dai, Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin da ya kai Naira tiriliyan 49.7, amma daga bisani aka ƙara adadin kuɗin. Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin a ranar Juma’a, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Kasafin kuɗin na 2025 ya ninka wanda aka yi a bara, wanda ya tsaya a Naira tiriliyan 27.5, da ƙarin kashi 99.96...
    Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%. Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna...
    Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki. Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin. An ga watan Ramadan a Najeriya An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya  An gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban. Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed. Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa. Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya....
    Bankin na CBN ya sanar da cewa, daukacin Bankunan, ana sa ran su bi wannan umarnin nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban hukumar IMF Kristalina Georgieva ta fadawa gwamnan babban bankin kasar Lebanon na riko, Wassim Mansouri a wata haduwa da suka y ikan cewa kasarsa zata sami kudaden sake gidan kasar dag wajenta ne, tare da sharudda. Rahoton ya kara da cewa kasashen Lebanon da Siriya zasu sami kudade daga cibiyoyin biyu ne kawaii dan sun samar da dangantakar diblomasiyya da HKI. Sannan kasar...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa Jami’an gidajen yari da kuma sojjin HKI suna dukan kawo wuka kan falasdinawa da suka shiga hannunsu, sannan suna azabtar da su sosai, daga ciki har tare da yanke yanke wasu gabban jikinsu. Kungiyar ta kara da cewa, mutum yana iya ganin alamun duka da kuma kumburan wurare da dama a jikin Falasdiwa. Banda haka Falasdinawan...
    Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah na fadar haka, ya kuma kara da cewa kungiyar ta gabatar da shihidar da dama saboda kare kasarsu, saboda kare kasar Lebanon daga mamayar HKI. Labarin ya kara da cewa an gudanar da jana’izar ne a garuruwan Aitarun da kuma Aita shaab. Inda mutanen da dam dagayankin zuka halarta . Labarin ya kara da cewa Shahidan sun kai ga shahada ne a hare-haren da sojojin HKI suka kai kan kudancin kasar ta Lebanon a cikin watannin Octoba da kuma Nuwamba na shekara ta 2024. Labarin ya kara da cewa a yakin dai mutanen leabin kimani...
    Shuwagabannin Afrika ta Kudu, Malasiya da kuma Colombia sun jaddada matsayinsu nah ana jiragen ruwa dauke da makamai zuwa HKI tsayawa a tashishin jiragen Ruwan kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, Firaiministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim da Shugaban kasar Colmbia Gustavo Petro suna fadar haka a wani rubutun hadin guiwa da aka buga a mujallar ‘Foreign Policy’ na wannan makon. Shuwagabannin sun bayyana cewa yakin da HKI ta durawa Falasdinawa a Gaza, ya nuna yadda tsarin dokokin kasa da kasa suna gaza tabbatar da adalci a duniya. Labarin ya kara da cewa : Ko mu hada kai mu tabbatar da dokokin kasa da kasa, ko kuma dukkan...
    Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara. Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu. Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano Bayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi. Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa. Sai dai dakarun...
    Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Juma’a, wanda hakan ke nufin ranar Asabar, 1 ga watan Maris, ita ce daya ga watan Ramadan 1446 Hijira a Najeriya. A cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmi, ya karanta a fadarsa, ya bayyana cewa an samu sahihan bayanai daga kwamitocin ganin wata da shugabannin addinin Musulunci a sassa daban-daban na kasar nan. An ga watan Ramadan a Najeriya —Sarkin Musulmi Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara a dalilin haka, ya ayyana fara azumin watan Ramadan daga safiyar Asabar. Haka nan, hukumomin Saudiyya ma sun tabbatar da ganin watan, inda suka ayyana Asabar a matsayin daya ga...
    Fadar mai alfarma sarkin Musulmi, ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen Juma’ar nan a Sakkwato.   Cikin wata sanarwa da Mai Alfarma Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.   Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446. Nasiru Malami/Sakkwato
    Shugaban ya kuma yaba da hadar da tuni Hukumarsa ke kan ci gaba da yi da NPA ta kan kayan da ake fitarwa da su zuwa ketare, da ke a gabar ruwa ta Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar. A na sa jawabin Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, Dakta Abubakar Dantsoho, ya bai wa Shugaban na Hukumar Kwastam tabbacin goyon baya da hadin kan NPA, domin Hukumomin biyu, su samu cin nasarar abinda suka sanya a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta buƙaci malaman jami’ar jihar da suka shiga yajin aiki da su koma bakin aiki don ci gaban ilimi a jihar. Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi, Farfesa Isah Muhammad Maishanu ne, ya bayyana haka a taron manema labarai da ya kira a ranar Juma’a, kwana ɗaya bayan da malaman suka fara yajin aiki saboda rashin biyansu haƙƙoƙinsu. An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya  Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara Ya ce: “Muna kira ga malaman da su sake tunani kan matakin da suka dauka. Kada su bari siyasa ko wasu da ba su da kishin jiha su yi amfani da su wajen hana ci gaban ilimi. “Mu na mutunta su, kuma muna...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...
    Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Sergei Shoigu, sakataren majalisar tsaro ta kasar Rasha, a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, Sin da Rasha sun kasance masu tuntubar juna a dukkan matakai, da aiwatar da matsayar da suka cimma da shugaba Putin da hadin gwiwa mai muhimmanci da moriyar juna tare da zurfafa hadin gwiwarsu a kai a kai, domin taimakawa muradunsu na bai daya na samun ci gaba da farfado da kasashen biyu. Ya kara da cewa, ya kamata kasashen 2 su karfafa hadin kai a harkokin da suka shafi yanki da ma duniya, su kuma goyi bayan rawar da kasashen BRICS da kungiyar hadin kai ta Shanghai suke takawa, tare da...
    Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin yau Juma’a. Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025. Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar. Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano Wannan na nufin cewa Musulmai a Saudiyya za su fara azumi a ranar Asabar. Hakazalika, ƙasashen Qatar da Oman sun sanar da cewa za su fara azumin Ramadan a wannan ranar Asabar. A yayin da ake shirin shiga wannan wata mai alfarma, an yi kira ga Musulmai...
      Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna (KSPWA) ta yaba da gudunmuwar da Gwamnatin Jihar Kaduna Malam Uba Sani ya ke badawa wajen samun nasarorin da aka samu kwanan nan.   An bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da Shugaban Hukumar Jindadi Alhazai na Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar ya jagoranta tare da tawagar Kwamitin Musamman na Hajji da shugabannin ga Sarkin Zazzau, Malam Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya.   Babban burin ziyarar shi ne neman ci gaba da samun goyon baya da addu’o’in Sarkin don samun nasarar ayyukan Hajji na shekarar 2025.   Malam Salihu ya nuna godiya sosai ga gudunmuwar da Sarkin ya ba da a baya kan shirye-shiryen Hajji, tare da...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta sanar da naɗin Dakta Mustapha Muhammad Ali, a matsayin sabon Sakataren Hukumar. Sanarwar naɗin na ƙunshe ne a cikin wata takarda da shugaban sashin hulɗa da Jama’a na hukumar, Muhammad Ahmad Musa, ya fitar bayan amincewar kwamitin gudanarwa na NAHCON a taron da aka gudanar na ranar 26 ga Fabrairun 2025, bisa tanadin sashi na 8 na dokar da ta kafa NAHCON ta 2006. NAHCON Ta Tsawaita Wa’adin Biyan Kuɗin Kujerar Aikin Hajjin 2025 zuwa 10 ga Fabrairu Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince Da Kwangilar Aiki Da NAHCON Bayan Sabunta Yarjejeniya  Dakta Mustapha Muhammad Ali, wanda ƙwararre ne wajen tabbatar da gudanarwa da kuma aiwatar da manufofin inganta aikin Hajji a Nijeriya, zai...
    Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara. Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu. Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano Bayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi. Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa. Sai dai dakarun...
    Ya kara da cewa rashin gudunar da daga wurin INEC abu ne mai hadari, wanda ya saba wa dokokin tsarin mulki da dokoki wadanda suka tilas zaben cike gurbi a duk lokacin da aka samu bukatan hakan. Rahotanni sun bayyana cewa a halin yanzu akwai kujeru bakwai a majalisar kasar nan da babu kowa, akwar biyar a majalisar wakilai, sannan akwai biyu a majalisar dattawa. Kujerun da babu kowa a majalisar wakilai akwai a jihohin Edo da Oyo da Kaduna da Ogun da kuma Jigawa, yayin da kujerun majalisar dattawan na jihohin Edo da Anambra. Biyu daga cikin wadannan kujeru sun zama babu kowa ne bayan zaben gwamnan a Jihar Edo, yayin da sauran biyar suka zama babu kowa saboda...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara. Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya. Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki Dokta Taofik, ya ce sun je fadar ne, domin neman albarka da shawarwari kan hanyoyin magance cin zarafin mata. Ya kuma bayyana cewa cibiyar ta ɗauki nauyin malamai da limamai zuwa Jami’ar Al-Azhar da ke Masar...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma Babban Sakataren Tsare-Tsare, Salisu Mustapha, kan badaƙalar zaftare albashin ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba. An umarci Mustapha da ya sauka daga muƙaminsa na Babban Sakataren Tsare-Tsare a Ofishin Shugaban Ma’aikata domin ba da damar gudanar da bincike. A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura Gwamna Abba ya amince da naɗa Malam Umar Muhammad Jalo, Muƙaddashin Babban Sakataren REPA, a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan jihar har zuwa lokacin da za a kammala binciken lamarin. Matakin gwamna ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da dama da ma’aikatan gwamnati suka yi kan rage albashi ba bisa...
    Kasar Sin ce ke da kusan kashi 30 cikin 100 na karuwar tattalin arzikin duniya a bara, wanda ya yi tasiri matuka ga tattalin arzikin duniya. Gudunmawar da kasar Sin ta bayar ta sake tabbatar da matsayinta na kan gaba a fannin tattalin arziki, kuma ta nuna muhimmiyar rawar da take takawa wajen ciyar da harkokin cinikayyar kasa da kasa gaba, da karfafa zuba jari da ingiza kirkire-kirkire na fasaha. Hakazalika, darajar cinikin waje na kasar Sin ta kai wani matsayi mafi girma a shekarar 2024, inda jimilarta ta kai yuan triliyan 43.85, wanda ya karu da kashi 5 cikin dari bisa na shekara 2023. Haka ma yawan kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje ya karu da kashi 7.1...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma babban Sakatare na sashin shirye-shirye, Salisu Mustapha, bisa zargin yin kutse a albashin ma’aikatan gwamnati da rashin biyan wasu daga cikinsu. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar daren Alhamis, an bayyana cewa dakatarwar ta fara aiki nan take, tare da umartar Mustapha da ya sauka daga matsayin babban Sakatare don bai wa kwamitin bincike damar gudanar da aikinsa ba tare da katsalandan ba. Labarin Bukar, Malamin Da Ya Shafe Watanni 20 Ba Tare Da Albashi Ba A Borno Gwamnan Kano Ya Kafa Kwamitin Bincike Kan Zaftare Albashin Ma’aikata A don ci gaba da gudanar da harkokin ofishin, gwamnan...
    Sanata Natasha Akpoti ta zargi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswil Akpabio da neman yin lalata da ita. ’Yar Majalisar Dattawa daga Jihar Kogi ta bayyana cewa mijinta ma shaida ne a kan yunkurin Akpabio ne yin lalata da ita. A wata hira da aka yi da ita a tashar talabijin ta Arise a safiyar Juma’a, Sanata Natasha ta ce tun da ta ki amincewa da buƙatar Shugaban Majalisar ya kafa mata ƙahon zuƙa. A makon da ya gabata ne Natasha ta yinwa Akpabio wankin babban bargo a zauren Majalisar bayan ya sauya mata kujera ba tare da tuntubar ta ba. Shin Kwankwasiyya ta kama hanyar wargajewa ne? NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki Ya ba da umarnin...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce inganta hadin kai da alaka tsakanin kasashen musulmi da suka hada da Iran da Malaysia na daga cikin abubuwan da ake bukata a halin da ake ciki a duniya. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da ministan harkokin wajen Malaysia Dato’ Seri Utama Haji Mohamad Bin Haji Hasan a birnin Tehran a wata ziyara da ya kai kasar Iran. Ya  ce a halin yanzu gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana aiwatar da abin da take yin a laifuka da wuce gona da iri a yankin saboda kan musuylmi ba hade yake ba. Ya kara da cewa samar da hadin kai tsakanin jami’ai da ‘yan siyasar kasashen musulmi zai taka...
    Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi na kulla huldar tattalin arziki da tsaro da kasashen yammacin da tsakiyar Afirka. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya habarta cewa, hamshakin attajirin nan na Rasha Oleg Deripaska ya halarci tattaunawar da shugabannin biyu suka yi. Kafofin yada labarai sun ambato wani minista a Guinea-Bissau, ya ce, Kamfanin aluminium na Rasha Rusal yana sha’awar gina layin dogo da tashar jiragen ruwa a kasar, da kuma...
    Ministar tsaron Habasha Aisha Mohammed ta gana da tawagar sojoji daga Nijar karkashin jagorancin ministan tsaro Salifu Modi, inda bangarorin biyu suka tattauna kan yadda za a inganta hadin gwiwar soja da tsaro. Ministar tsaron Habasha Aisha Mohammed ta jaddada cewa; Afirka na da karfin fuskantar kalubale ba tare da tsoma bakin waje ba. A yayin ganawarta da tawagar sojojin kasar Nijar karkashin jagorancin ministan tsaro Salifu Modi a babban birnin kasar Adis Ababa, Mohammed ta jaddada muhimmancin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu bisa amincewa da mutunta juna. Ta sake jaddada aniyar Habasha na tallafawa zaman lafiyar nahiyar da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka don fuskantar barazanar tsaro tare. A nasa bangaren, ministan tsaron Nijar ya jaddada...
    Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai.   Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani.   Da yake bayyana bude taron, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin sun kware a fannin sadarwa.   Ya jaddada mahimmancin kayan aikin zamani,tare da haɗin gwiwar kafofin watsa labarun, da sadarwa ta hanyar bayanai don tabbatar da ingantaccen kuma da yada bayanai akan lokaci.   Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da...
    Sako daga Alawiyya Jilani Jihar Kano: Ina gaishe da Mummy da Abba, da kannena Zuhra, Sajida, Alhaji, da dukkanin kawayena na islamiyya dana boko wadanda muka kammala dukka, ina gaida Khadija (Sweet Bala), ina gaishe da Siyama Abdul, ina gaishe da Aunty Hajara da sauran ‘yan’uwa da fatan sakon ya iso gare ku kuma da fatan kun yi juma’a lafiya. Sako daga Balaraba Ibrahim Jihar Kaduna: Assalam.. Dan Allah a gaishe mun da Sisi ‘yar fucika uwar tsokana, da Hajiya Hazira, da Aunty Amina mai sakwara, ina gaishe da baby nice, da Binta kwaram da sauran wadanda ban gaisar ba wanda suka sanni. Sako daga Yusuf Uba Muhammad Jihar Kano: Haj. Rabi’at dan Allah a mikan sakon gaisuwata zuwa ga...
    Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya yi wani kakkausan gargadi game da rahotannin rashin biyan albashi da rashin biyan ma’aikatan jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin tauye hakkin ma’aikata da kuma cin amanar jama’a.   Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin bincike mai mutane bakwai, karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdussalam, domin gano musabbabin sabanin.   Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruk ya wakilta, ya ce kwamitin ya hada da manyan jami’an gwamnati da masana harkokin kudi da wadanda suka kware a tsarin biyan albashi.   Yace Membobin Kwamitin sune Abdulkadir Abdussalam_ – Shugaban, Kwamishinan Karkara da Ci gaban Al’umma Dr. Bashir Abdu Muzakkari – memba, mai ba da shawara na musamman kan...
      Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya a matsayin wakilin na angwaye yayin da Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammad Iliyasu Bashar murabus ne ya tsaya a matsayin wakilin na amaren.   Gwamna Nasir Idris, yayin da yake godewa uwargidansa Hajiya Nafisa Nasir Idris bisa wannan shiri a karkashin gidauniyarta ta “Asusun NANAS ”, ya yi alkawarin bayar da goyon baya da kuma ci gaba da gudanar da shirin na shekara-shekara domin amfanin al’ummar Kebbi, ya kuma shawarci ma’auratan da su kasance masu adalci da mutunta ra’ayin juna.   Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku-Bagudu, ya bayyana taron a matsayin tunatarwa ga daidaikun mutane...
    Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar.   Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda 100 na kayan ilimi na musamman; 260 na Kula da Yara da sauransu.   Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce  wannan wani shiri ne a cikin jerin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi wanda ke nuni da fifikon da take da shi na samar da ilimin boko a jihar.   A cewarsa...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta ce daga cikin wuraren kiwo guda 400 da ke jihar, ta duba 57 domin dakile rikicin manoma da makiyaya a jihar.   Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka ne a wajen bude taron tuntubar masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen kiwo tare da hadin gwiwa da kwamitin shugaban kasa na aiwatar da gyara harkokin kiwon dabbobi da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar.   Ya ce baya ga samar da tsarin doka na kare wuraren kiwo, manufar za ta kuma tabbatar da amfani da albarkatun kasa mai dorewa a jihar.   Gwamnan ya ce gwamnatin sa ta kuma dauki ma’aikatan kiwon lafiyar dabbobi 300 na al’umma domin su samar da ayyukan ci gaba ga manoma...
    Wadanda Suka Yi Nasara Aliyu Usman Adam – Matsayi na daya Aliyu Usman Adam, dan asalin Zariya ta Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a 2008. Bayan hidimar kasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014. A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TB Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu. Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu Zainab Muhammad, wacce...
    Har ila yau, a cewarsa; Abiola ya samu mafi yawan kuri’u tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata, domin zama shugaban kasa. “Babu tantama a zuciyata, Abiola ne ya lashe wannan zabe tare da cika dukkanin sharudan da ake bukata”, in ji IBB. Kazalika, ya kuma bayyana farin cikinsa; kan yadda Buhari ya karrama Abiola da lambar yabo mafi girma ta GCFR, wadda ake bai wa shugabannin kasa. “Ko shakka babu, Mashood Abiola shi ne ya lashe zaben shugaban kasa a 1993, da kuri’u sama da miliyan takwas a jam’iyyasa ta SDP, inda ya samu nasara a kan abokin karawarsa, Alhaji Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC”, in ji Babangida. A jawabinsa na godiya, IBB ya bayyana rushe zaben...
    Kasar Masar ta ce an fara tattaunawa tsakanin Isra’ila da Hamas kan mataki na gaba na tsagaita wuta a Gaza. Ma’aikatar yada labaran kasar Masar ta fada a jiya Alhamis cewa, tawagogin Isra’ila, Qatar da Amurka na birnin Alkahira domin tattaunawa mai zurfi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. “Bangarorin da abin ya shafa sun fara tattaunawa mai zurfi don tattaunawa kan matakai na gaba na yarjejeniyar tsagaita wuta, a ci gaba da kokarin tabbatar da aiwatar da fahimtar juna da aka amince da su a baya,” in ji sanarwar. Ta kara da cewa, masu shiga tsakani suna tattaunawa kan hanyoyin da za a iya “inganta isar da kayayyakin jin kai” zuwa yankin Falasdinu da yaki ya daidaita. A...
    Kasar Aljeriya ta yi watsi da barazanar da kuma wa’adin da kasar faransa ta gindaya ma ta na cewa za ta soke yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta shekarar 1968 wacce ta ba Aljeriya matsayi na musamman. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta ce “A cikin ci gaba da takun tsakar dake wakana (…) Aljeriya ba ta dauki wani mataki ba, kuma ta bar bangaren Faransa da ta matakin da ya dace. Ita dai Faransa ta yi barazana a ranar Laraba cewa za ta binciki yarjejeniyoyin da ke saukaka yanayin zama, shige da fice da kuma aiki ga ‘yan Aljeriya, dangane da koma bayan da ake samu na tashe-tashen hankula sakamakon wani hari...
    Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan barazanar soji da Isra’ila ke yi mata, da kuma sukar da kasashen Yamma suka yi kan karfin tsaron kasar a matsayin rashin hankali da wauta. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmaeil Baqaei ya bayyana a jiya Alhamis yayin da jami’an Isra’ila ke ci gaba da yi wa Iran barazanar daukar matakin soji, kasashen yamma na ci gaba da zargin kasar da kara karfin tsaronta. M. Baqaei ya yi nuni da cewa, yankin yammacin Asiya na fama da wata mamaya da ta dade wacce kamu ta wuce gona da iri da rashin bin doka da oda. Don haka ya kara da cewa, wajibi ne kawai Iran ta kara karfin tsaronta. Kalaman nasa sun...
    Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023, jami’an sojin sun amince da cewa sun kasa cika aikinsu a ranar da Hamas ta kai wa Isra’ila hari. Wani jami’in soji ya shaidawa gidan radiyon RFI cewa sojojin sun “kasa cika aikinsu na kare fararen hula Isra’ila” a harin na ranar 7 ga Oktoba, 2023, yayin da aka fitar da babban sakamakon binciken. Ya kara da cewa...
    A wani mataki na nuna kara kusanci tsakanin kasashen Somaliya da Habasha, shugaban kasar Habasha Abiy Ahmed ya ziyarci Somaliya. A Shekara guda da ta wuce, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna. Bayan shafe shekara guda ana zaman dar-dar, a watan Disambar da ya gabata ne a kasar Turkiya, kasashen biyu suka sake kulla huldar jakadanci ta hanyar sanya hannu kan yarjejeniyar Ankara. Shugaban kasar Somaliya Hassan Cheikh Mohamoud ya gabatar a matsayin “mahimmin mataki” na daidaita huldar dake tsakanin kasashen biyu. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar da yammacin jiya Alhamis, an bayyana cewa: Habasha da Somaliya kasashe ne masu dogaro da juna da makoma guda da kuma ra’ayi daya na tabbatar da...
    A 2024, rundunar ‘yansanda ta Abuja, sun kama wani mai suna Nuhu Ezra, a yanikin Lugbe dauke da Kokon kan mutum da Kasuwansa, inda wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa, ya ci karo da Kokon kan mutum da Kasuwan ne, a yayin da yake yin farauta a cikin Dajin Kuje. Kazalika, duk dai a 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar Ondo, sun cafke wani mai suna Yusuf Adenoyin, a yankin Isua, na karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas dauke da Kokon kan bil Adama guda takwas. A Jihar Oyo ma, rundunar ‘yansanda ta jihar ta kama wasu mutane biyu a yankin Amuloko da ke garin Ibadan, bisa zargin samun dauke da danyen Kokon kan wata mata , da ba...
    A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu.  An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.   Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023 Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce,...
    An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...
      Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.   Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.   Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da bukatar zuwa Hajji su tuntubi jami’an hukumar a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar ko su ziyarci hedikwatar hukumar dake kan titin Katsina, a cikin garin Kaduna.   Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa mutum dubu uku da dari hudu da sittin (3,460) ne suka biya kudin Hajji ta hannun hukumar.   Ya kuma kara da cewa kudin Hajji ya kama naira...
    A ranar 27 ga wata ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kaddamar da gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya a birnin Beijing. Babban daraktan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, masana’antar mutum-mutumin inji ta zama wata muhimmiyar alama ta auna matsayin wata kasa ta fuskar kimiyya da fasahar kere-kere da kuma masana’antar kere-kere na babban mataki. Kasar Sin ta zama kasa mafi grima a duniya wajen kera mutum-mutumin inji da yin amfani da su. Ta hanyar dogaro da babban dandalin watsa labaru mai karfi, gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya ta CMG za ta nuna nasarorin da aka samu wajen kera mutum-mutumin inji ta kowane bangare, ta yadda za a hada karfin...
    Taron lakca karo na 22 na kasar Sin da aka yi jiya Laraba a birnin Alkahiran Masar, ya hada malamai Sinawa da na kasar da jami’ai sama da 200, inda suka tattauna don gane da zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika, wajen daukaka zamanantar da kasashe masu tasowa. Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika da cibiyar Confucius ta jami’ar Suez Canal ta Masar ne suka karbi bakuncin taron mai taken “Zurfafa hadin gwiwar Sin da Afrika domin jagorantar zamanantar da kasashe masu tasowa.” Taron ya mayar da hankali ne kan karfafa dangantakar Sin da Masar, da fadada musaya tsakanin masana, da bunkasa tallafin ilimi ga kokarin kasashe masu tasowa na zamanantar da kansu. Tattaunawar ta kuma jaddada batun kara inganta...
    Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su damar yin fice a tsakanin takwarorinsu.   Da yake magana tun farko, Gautier Mignot, jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, kuma jagoran tawagar, ya bayyana cewa, sun zo Kano ne domin halartar bikin baje kolin karatu na Turai da aka shirya yi a ranar 27 ga Fabrairu, 2025 a jihar.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
    Ma’aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gaggauta janye binciken sashe na 232 kan shigo da jan karfe kasarta, inda ta bayyana cewa, zargin da ake yi na cewa kasar Sin na amfani da tallafin gwamnati da karfin samar da hajoji fiye da kima don gurgunta abokan takara kwata-kwata ba ya da tushe. Kakakin ma’aikatar He Yadong ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a lokacin da yake amsa tambaya kan matakin da Amurka ta dauka na kaddamar da binciken sashe na 232 kan jan karfe da aka shigar da su kasar daga kasashen waje. Ya kara da cewa, binciken na Amurka wani aiki ne na kashin kai da kariyar cinikayya wanda ta yi...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya koma gidansa da ke Jihar Kaduna da zama, bayan shafe shekara biyu a Daura, tun bayan barinsa mulki a watan Mayun 2023. Buhari, ya zaɓi yin rayuwa mai sauƙi bayan kammala wa’adin mulkinsa ba tare da shiga harkokin siyasa ba. Gwamnatin Kano ta nemi Tinubu ya kori Aminu Bayero daga fadar Nassarawa Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki Ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da manyan jami’an gwamnati zuwa Kaduna. Daga cikin tawagar da suka yi masa rakiya akwai Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, mataimakan gwamnan Jihar Katsina, Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, wasu tsofaffin ministoci, da wasu daga cikin hadimansa. A lokacin...
    Bugu da kari, masu baje koli na cikin gida za su gabatar da kayayyaki na alfarma da wadanda aka samar a cikin gida, kuma wani bangare na baje kolin zai mayar da hankali ga hada masu sayayya na kasashen ketare da masu samar da kayayyaki na kasar Sin ta hanyoyin da aka tsara na zuba jari. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Kano, ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ɗauki mataki na cire Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, daga Fadar Nassarawa, wanda ta ce zamansa na haddasa tashin hankali a jihar. Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne, ya yi wannan kira. Zargin Almundahana: Kotu ta ba da belin Farfesa Usman Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Fadar Gwamnatin Kano yayin rabon kayan tallafi da ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Tarauni, Hon. Kabiru Dahiru Sule, ya bayar. Ya zargi wasu mutane na amfani da zaman Aminu Ado a fadar Nasarawa don cimma muradun kansu da kuma haddasa rikici a Kano. “Muna kira ga...
    Kazalika sun yi ƙorafi tare da nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnati da majalisar gudanarwar Jami’ar ke tafiyar da al’amuran da suka shafi ci gabanta.   Ƙungiyar malaman ta ce ta kafa wani kwamiti da zai tilasta tare da tabbatar da an bi umarnin yajin aikin da tsayawar harkoki a Jami’ar har sai an cimma matsaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata Babbar Kotu a Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ake tuhuma da almundahana. A ranar Alhamis, Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin sakin Farfesa Usman daga gidan gyaran hali na Kuje bayan an cika sharuɗan belinsa. Boko Haram: An lalata gidaje da makarantu a ƙauyukan Adamawa Malaman Jami’ar Sakkwato sun tsunduma yajin aiki Hukumar EFCC ce, ta gurfanar da shi kan tuhume-tuhume guda biyar da suka haɗa da zargin karkatar da kuɗaɗe. Ana zargin ya amince wajen sayen motoci a kan Naira miliyan 49.2 maimakon Naira miliyan 30 da aka ware a matsayinsa na shugaban NHIS a 2016. EFCC, ta kuma ce Farfesa Usman ya bai...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau ranar 27 ga wannan wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da maida batun samun bunkasuwa a matsayin batu mafi muhimmanci a cikin ajendar kasa da kasa, da bin tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, da zama babbar kasa mai ba da muhimmiyar gudummawa a duniya, don tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin ta kiyaye sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya. A matsayin kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 cikin dari ga bunkasuwar duniya, kana ita ce muhimmiyar abokiya ta...
    Wasu gungun ‘yan Boko Haram ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki cikin dare a garin Kwapre da ƙauyukan da ke gundumar New Yadul a ƙaramar hukumar Hong a Jihar Adamawa. Harin wanda ya fara daga misalin ƙarfe 7:30 na yammacin ranar Talata, 25 ga watan Fabrairu, kuma ya ɓarnata dukiyoyi a tsakiyar daren. Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno Al’ummar yankin sun ce, an ƙona wuraren ibada da makarantu da gidaje da wuraren kasuwanci, sannan an wawushe dukiyoyi na miliyoyin Naira. Mista Joel Kulaha, Hakimin garin Kwapre da Abalis Jawaja, kuma dagacin ƙauyen, ya ce maharan sun farwa al’ummar garin, inda suka...
    Kwanan baya, kwamitin kula da aikin lantarki na duniya (IEC) ya gabatar da ka’idar sarrafa mutum-mutumin inji mai kula da tsoffi. Ka’idar da kasar Sin ta ba da jagorancin tsarawa, ta tabbatar da yadda za a tsara da sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi bisa halayen da tsoffi suke ciki, ta kuma tabbatar da yadda za a gudanar da bincike kan mutum-mutumin inji, yayin ba da izini gare su. Lamarin da ya ba da tabbaci ga bunkasuwar aikin sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi yadda ya kamata. Bayanin ya nuna cewa, an tsara ka’idar bisa bukatun tsoffi a fannonin samun kulawa cikin harkokin yau da kullum, da kiwon lafiya da dai sauransu. Haka kuma, ana fatan tsara mutum-mutumin...
    “Mun yi jimamin asarar rai da aka yi, kuma mun yi tattaki zuwa ga iyalan mamacin don jajantawa tare da tabbatar musu da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da adalci,” in ji shi.   Don haka, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu domin Rundunar tana aiki tukuru don zakulo gaskiyar lamarin tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jiya Laraba ne dai Hukumar da take kula da harkokin jin kai dake karkashin MDD  ( OCHA) ta bayyana cewa; Kusan shekaru biyu na yakin da ake yi a Sudan ya kara tsananta, kuma a halin yanzu yunwa wani abu ne da ya zama dahir ana ganinta a kasa a Sudan. Babbar daraktan  gudanar da ayyukan hukumar agajin ta MDD Edem Wosornu ta fadawa kwamitin tsaron MDD cewa; Da akwai mutane miliyan 12 da aka tarwasta daga gidajensu, daga cikinsu da akwai wasu miliyan 3.4 da su ka tsallaka iyaka. Haka nan kuma fiye da rabin mutanen kasar Miliyan 24.6 suna fama da matsananciyar yunwa.” Haka nan kuma ta kara da cewa; Tsarin kiwon lafiya na kasar ya durkushe...
    Malaman Jami’ar Jihar Sakkwato, sun fara yajin aiki a karon farko tun bayan kafuwar jami’ar sama da shekaru 12 da suka gabata. A wata sanarwa da shugabansu, Saidu Isah Abubakar, tare da Sakataren Jami’ar, Hassan Aliyu, suka fitar, sun bayyana cewa an yanke shawarar shiga yajin aikin ne a ranar Laraba. Kotu ta yanke wa matashi ɗaurin wata 6 kan satar kaza Abba ya ba da umarnin bincike kan rage wa ma’aikatan Kano albashi “Dukkanin harkokin karatu, karantarwa, jarabawa, duba ɗalibai da makin jarabawa sun tsaya har sai an cimma matsaya,” in ji sanarwar. Malaman sun ce sun ɗauki wannan mataki ne domin tilasta wa gwamnatin jihar, biyan buƙatun da suka jima suna gabatarwa. Sanarwar, ta ce ba su gamsu...
    Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu. Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami  ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa: “ Za mu  kara  yawan wutar lantarkin da muke samarwa da  megawati 2000 a kowace sa’a daya  daga nan zuwa karshen zangon na bakwai na tsare-tsaren ci gaba da ake yi a kowace shekara 5. Zangon dai zai kare ne a cikn watan Maris 2029. Salami ya ce za a kara megawati 1,000 a cikin kowace sa’a da hakan zai mayar da abinda ake samarwa zuwa megawati 3,000 a cikin kowace sa’a.