2025-03-24@14:02:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 572
«Naira tiriliyan»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ’yan ƙauye su goma daga wasu unguwanni uku da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar, da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare inda wasu gungun ’yan bindiga suka kai farmaki a unguwar Unguwan Yashi-Maraban Kajuru tare da yin garkuwa da mutane shida. Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don arzuta kansu — Obasanjo Waɗanda aka sace su ne: God-Dream Ladan, Lady God-Dream, Philip Mudakas, Mercy Philip, Bitrus Philip, da Gmen Philip. Hakazalika, a ƙauyen Makyali, wasu mutane biyu sun samu raunuka na...
Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan Najeriya sun fara samun sauki yayin da farashin kayan abinci ke raguwa da farashin fetur ke daidaita, kuma naira ke karɓar ƙarfi. Da yake magana a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu a Abuja, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohamed Idris, ya ce ci gaban, suna nuna cewa gyare-gyaren tattalin arziki na Shugaba Bola Tinubu na yin tasiri. Ya amince da wahalhalun da ‘yan Najeriya suka sha amma ya tabbatar da cewa hakan ya fara wucewa. Mohamed Idris ya ce Gwamnatin Tarayya tana nan daram wajen daidaita tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma. A jawabinsa, Ministan Ilimi, Dr. Maruf Alausa, ya ce kudaden da aka...
Ta ce tallafin zai taimaka wajen bai wa mata damar zama masu dogaro da kansu a fannin tattalin arziƙi. An raba kuɗin ne ga kungiyoyin mata manoma daga ƙananan hukumomi 13 a faɗin jihar, inda kowacce ƙungiya ta samu Naira miliyan biyu. Haka kuma, ƙungiyoyin matasa manoma su ma sun amfana da tallafin don bunƙasa ayyukansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu. Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar. Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya. “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba. “tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?” “Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar jama’a na duniya.” Inji jagoran. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a...
Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Wakilai ta umarci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya dakatar da sabon tsarin ƙarin caji kan cire kuɗi ta na’urorin ATM. Wannan umarni ya biyo bayan wata sanarwa da CBN ya fitar, inda ya ƙuduri aniyar fara cajin Naira 100 kan duk cire Naira 20,000 daga ATM a banki, daga ranar 1 ga watan Maris, 2025. Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Zulum ya bai wa ƙananan ’yan kasuwa tallafin 1bn a Borno Ɗan majalisa Marcus Onobun (PDP, Edo) ne, ya jagoranci ƙudirin da ya buƙaci a dakatar da wannan tsari, inda ya bayyana cewa tsarin zai ƙara jefa ’yan Najeriya cikin wahala. Ya bayyana cewa, a shekarar 2019, an rage cajin cire kuɗi ta...
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba wa ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita su 9,403 a ƙananan hukumomin Biu da Hawul, tallafin Naira biliyan ɗaya. Wannan tallafi na da nufin ƙarfafa kasuwanci, haɓaka tattalin arziƙi, da rage talauci a yankunan. Dan ta’adda zai biya tarar miliyoyi bayan shan dukan kawo wuka a Katsina Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha A Biu da Hawul, gwamnan ya raba Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603, inda kowane mutum ya samu Naira 100,000. Hakazalika, ya raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da magidanta 1,800 a Biu da kuma ’yan kasuwa 2,000 a Hawul. Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata. “Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.” Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump,...
Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
Ukraine ta amince da kudurin tsagaita wuta na wata guda a yaƙin da ta shafe shekaru uku tana fafatawa da kasar Rasha. Matakin na zuwa ne bayan tattaunawar da wakilan ƙasar ke ci gaba da yi yanzu haka da Amurka a birnin Jedda na Saudiya. Matashin da ke ƙera jiragen sama da bindigogi daga robobi Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ne ya sanar da haka da maraicen Talata bayan shafe wuni guda jami’an Ukraine da na Amurka suna tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine din da Rasha. Rubio ya ce makasudin gabatar da kudurin shi ne na dakatar da bude wuta da kashe...
Alamomin cutar sun haɗa da ciwon kai mai tsanani, ciwon wuya, tari, da amai. Yaɗuwar cutar a Kebbi na iya shafar sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita, musamman Zamfara, Sakkwato, da Neja, inda ake yawan tafiye-tafiye tsakanin jihohin. Hakan na nuni da buƙatar gaggauta ɗaukar matakan kariya don hana cutar yaɗuwa zuwa sauran yankuna. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Malam Yunusa Alfazazi, dan kimanin shekara 35 kuma mazaunin Kafanchan da ke Karamar Hukumar Jema’a ta Jihar Kaduna, ya kafa tarihi a duniyar fasaha da kirkire-kirkire, inda yake kera jiragen sama da bindigogi da sauran na’urori daga robobi da filastik. Allah Ya albarkaci Nijeriya da mutane masu fasaha da baiwar kera kayayyaki ba tare da samun horo na musamman ba. Misali, Malam Yahaya Makera da ya kafa tashar rediyo mai aiki a Kaduna da kayan aikin daba su taka kara sun karya ba. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 450 a Pakistan DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa? Haka nan, Mansur Nuhu Bamalli ya samu nasarori a fannin injiniyanci duk da karancin kayan aiki da suke...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata. Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.” Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu...
Fim din na “Habibullah” wanda Adnan Zandi ya fitar da shi, ya sami kyautar ne a wurin bikin baje kolin fina-finai karo na 28 a Poland. Wannan bikin baje kolin na fina-finai mafi girma da ake yi a kasar Poland domin tsamo fina-finan masu kima ta fuskar fasaha. Labarin fim din na “Habibullah’ an gina shi ne akan wani mutum da ya manyanta, amma yake jajurcewa wajen
Hukumar da take fada da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya ta’annatii ta kwato da kudaden da sun kusa dalar Amurka miliyan 500. Haka nan kuma hukumar ta kwato man fetur da sauran dangoginsa da sun kai ton 931,000, sai kuma gidajen da sun kai 975. A cikin rahoton da ta fitar a ranar litinin hukumar ta EFCC ta bayyana cewa, ta sa an hukunta masu laifi har su 4,000 wanda shi ne adadi mafi girma tun kafa ta. Tuni an zuba wasu kudaden da aka kwato a cikin ayyukan gwamnati. A karshen rahoton hukumar “Transparency International” ta bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 140, a jerin masu fama da cin hanci da rashawa, bayan da a baya ta kasance...
Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a wasu jihohin ƙasar na tsawon kwanaki huɗu. Wata sanarwa da Nimet ta fitar ranar Litinin a Abuja, ta ce mutane su guji fita cikin tsananin zafi musamman daga karfe 12 na rana zuwa karfe 3. Ainihin abin da ke kawo wa Manchester United koma baya ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ Hukumar ta ce mutane za su ji sauyin al’amura a tsawon lokacin da za a kwashe ana tsala zafin ranar. Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar yanayi na zafin rana sun haɗa da Neja da Kwara da...
Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka. Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da...
Wani babban jami’in ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta Indiya ya bukaci musulmi da su yi sallar Juma’a a gida. A cewar radiyon gwamnatin Pakistan, Firimiyan Jihar Uttar Pradesh Yogi Adityanath ya kare kalaman jami’in ‘yan sandan game da musulmi, inda ya ce, “A yayin da ake gudanar da bukukuwan Holi sau daya a shekara, ana gudanar da sallar Juma’a a duk mako.” Ya bayyana jami’in a matsayin gwarzo jarumi, tare da bayyana cewa wannan ra’ayi nasa daidai ko da kuwa hakan ya bakantawa wasu. Ya kara da cewa: “Bikin Holi ya fi sallar Juma’a muhimmanci, amma ana gudanar da shi sau daya ne kawai a shekara, don haka gudanar da shi yana da fifiko a kan Jum’a.” Jami’in...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin. Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya. A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila...
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar. Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta...
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...

Iran Ta Ce Shirinta Na Makamashin Nukliya Na Zaman Lafiya Ne, Kuma Ba Zata Tattauna Da Amurka Karkashin Barazana Ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...

Sojojin Ruwa Na Kasashen Rasha Da China Sun Shigo Kasar Iran Don Fara Atisayen Sojojin Ruwa Mai Suna “Damarar Tsaro 2025”
Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
Yau Litinin, aka rufe taro na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin wato CPPCC karo na 14 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran manyan jami’an gwamnati da jami’yyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, sun halarci taron. A gun bikin rufe taron, an zartas da kudurin rahoton aikin kwamitin dindindin na taron, da rahoton da kwamiti mai kula da kudurori ya gabatar game da bincike kan kudurorin da aka gabatarwa taron, kana da kudurin siyasa na taron da dai sauran muhimman takardu. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Jam’iyyar APC ta yi kira ga Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara da ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi. Shugaban APC na Jihar Ribas, Tony Okocha ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai yau Litinin a birnin Fatakwal. An cafke mutum uku kan satar wayoyin lantarki a Adamawa Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai Okocha ya ce gayyatar da Fubara ya aika wa ’yan majalisar dokokin jihar domin ya gana da su akwai lauje cikin naɗi. “Hukuncin Kotun Ƙoli ne ƙarshe babu wani abu da wani zai iya yi. Abun da ya rage wa gwamnan shi ne ko dai ya sauka, ko kuma a tsige shi,” in ji Okocha. Tun...
Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel. Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin...
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi, Cif Patrick Adaba ya riga mu gidan gaskiya. An ruwaito cewa Cif Adaba wanda ya shafe shekaru 78 a doron ƙasa ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a Abuja. Abba ya ƙaddamar da bincike kan zaftare albashin ma’aikatan Kano Blatter da Platini sun sake gurfana a kotu kan zargin cin hanci Wata majiya daga iyalansa ta ce tsohon Mataimakin Gwamnan ya rasu ne cikin daren ranar Lahadi. Cif Patrick Adaba shi ne ya yi wa Prince Abubakar Audu mataimakin gwamna bayan samun nasara a Zaɓen 1999. Tsohon Mataimakin Gwamnan wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Adavi da ke Jihar Kogin, ƙani ne ga tsohon Darekta Janar na Hukumar Kula da Kafofin Watsa Labarai...
Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan dukkanin cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. Jakadan dindindin na Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Jasem Yacoub al-Hammadi, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce “Al-Hammadi ya jaddada bukatar kasashen duniya da cibiyoyinta su tabbatar da alkawurran da suka dauka a karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD, da babban taron...
Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in ji jaridar Prompt News. Shakirat Moshood ce ta jefa wa Nijeriya ƙwallon farko a wasan cikin mintuna 20 kacal da farawa, Harmony Chidi ta ninka damar da Nijeriya ke da ita daga bugun fanareti mintuna biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci. Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu Afrika ta...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya ce manufar Iran ta ginu ne kan samar da hadin kai a yammacin Asiya, kamar yadda kuma ta yi imanin cewa duk wani rikici da tashin hankali a yankin to zai illata kowa. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da Firaministan Norway Jonas Gahr Støre a yammacin waannan Lahadi, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa ad suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu, da kuma sauran batutuwa na yankin da kuma na kasa da kasa. Shugaban na Iran ya kara da cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila na neman yada karya dangane da batun ayyukan nukiliyar Iran a matsayin tushen rashin tsaro a yankin. Har ila yau ya jaddada cewa Iran ba ta taba...
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan fararen...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin...
A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai. Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata su samu sana’a da za ta rage musu dogaro da wasu. PDP ta sake ɗage babban taronta zuwa Mayun 2025 An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba “Wannan tallafi yana da muhimmanci domin zai taimaka wa mata su kula da kansu da iyalansu ba tare da jira komai daga mazajensu ba. “Wannan kuma wani yunƙuri ne na taimakon jama’a kamar yadda maigidana, Hon....
Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta. A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa. Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi...
Isyaku Mahmud, makaho ne dan shekara 28 da ke sana’ar sayar da data a yankin Kudancin Kaduna. Ya shaida wa Aminiya cewa har sana’ar hada-hadar kudi ta POS yana yi a baya, amma yanzu ba shi da jari. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Aminiya ta ga yadda makahon yake sarrafa manhajojin WhatsApp is Fesbuk kuma yake sayar da data kai tsaye daga wayarsa ta hanyar amfani da tsarin Smart Cash tare da tura kudi da wayar tasa, kamar yadda ya gwadawa wakilinmu. Dan asalin garin Yalwa da ke Karamar Hukumar Tudun Wada (Dan Kadai) da ke Jihar Kano ne, ya kwashe shekaru kusan biyar yana zuwa yawon bara...
Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci daya wanda aka fi sani da tsarin kasa biyu – kasar Falasdinawa da kuma ta Isra’ila. Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan itace kadai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka dade ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kawayensa sun yi watsi da batun. Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin...
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar ta kasar Iran. Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku. Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne...
Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
A karon farko alkaluman ta’addaci a yankin Sahel da ke nahiyar Afirka ya zarce na jimillar sauran sassan duniya, a cewar rahoton cibiyar GTI mai bincike kan ta’addanci a matakin duniya. Rahoton ya nuna yawan kashe-kashe masu alaka da ta’addanci a Sahel, “ya zarce rabin jimillar adadin a duniya.” Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano Alkaluman sun nuna an kashe mutane 3,885 a yankin daga cikin mutane 7,555 da aka kashe a fadin duniya a dalilin ta’addanci. Rahoto ya kara da cewa a yayin da adadin a matakin duniya ya ragu daga kimanin 11,000 a shekarar 2015, lamarin ya ninku sau 10 a yankin daga shekarar 2019,...
Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi. Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata...
A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-hare a kan cibiyoyin makamashin Nukliyar kasar ba zasu dakatar da ayyuka a cibiyoyin ba. Sai dai yin haka zai kara yada yaki a yankin kudancin Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa cibiyoyin nukliya na kasar Iran suna da kekyawar kariya daga makamai. Don haka da sauki makiyammu ba zasu cutar da cibiyoyin ba. Ministan ya bayyana haka ne a taron kasashen musulmi na OIC wanda aka gudanar a birnin Jedda na kasar Saudiya a yau Asabar. Ya ce iran zata ci gaba da neman fahintar juna ta hanyar diblomasiyy, Amma idan sun dage zasu yi amfani da karfi to Iran a shirye...
Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Nijeriya, NMDPRA, ta bayar da lasisin kafa sabbin matatun man fetur uku a wasu jihohin ƙasar uku. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, wadda shugabanta, Farouk Ahmed ya bayyana ta nuna. Dalilin da muka dakatar da Sanata Natasha — Majalisar Dattawa Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol NMDPRA ta ce ta bayar da lasisin gina sabbin matatun man ne a jihohin Abia da Delta da kuma Edo. “Za a buɗe Matatar Eghudu wadda za ta iya tace ganga 100,000 a kullum a Jihar Edo. “Za kuma a buɗe Matatar MB wadda za...
Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar. “An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne...
Kasashen Iran da kuma Iraki sun nuna damuwa kan tashe tashen hankulan dake faruwa a Siriya. A wata sanarwa da ta fita ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana matukar damuwarta kan yadda tashe-tashen hankulan da ke yaduwa a fadin kasar ta Siriya, tana mai gargadin cewa, wannan yanayi mara kyau zai share fagen rashin zaman lafiya a yankin da kuma kara tunzura Isra’ila. Kakakin ma’aikatar Esmail Baghai ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran na nuna damuwa kan rashin tsaro, tashe-tashen hankula, zubar da jini da cutar da al’ummar Siriya da basu ji basu gani ba. Ita ma ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta bayyana matukar damuwarta kan halin da ake ciki a makwabciyarta Syria, tana mai jaddada cewa...
Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila. A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba...
Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi. Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan harkokin satar ma’adinai. A cewar gwamnatin, cikin wadanda aka kama 320, kusan mutum 150 a halin yanzu suna fuskantar shari’a kuma wasu guda tara an dauresu, inda su kuma mutum hudu ‘yan kasar wajen aka dauresu a gidan yari. Ministan bunkasa albarkatun kasa, Dele Alake, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labarai a karshen zaman majalisar zartarwa na tarayya...
Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai. A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani. Alake ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta karfafa aikin hadin gwiwa a tsakaninta da gwamnatin jihohi a yankunan da ake hakar ma’adinai domin dakile ayyukan masu haka ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da cewa kasar na morar albartun da Allah ya huwace mata. Da yake magana kan takardar da ya gabatar a gaban majalisar, ministan ya ce takardar ta tsara yadda za a shawo kan...
Shugaba Zelensky na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha. Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, sannan kuma tawagar da zai je da ita, za ta ci gaba da zama a can Saudiyya din saboda yin aiki tare da mutanen Saudiyya da kuma Amurka.” Zelensky ya kara da cewa; Kasarsa Ukiraniya tana son ganin an sami zaman lafiya mai dorewa. Bugu da kari shugaban na kasar Ukiraniya ya ce; Matakin farko da kasarsa ta gabatar a matsayin shawarar...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata masu dogaro da Amurka su kwana da sanin cewa, haka makomarsu za ta kasance, domin haka halayyar girman kai take.” Haka nan kuma limamin na Tehran ya ce; tare da cewa jagoran juyin musulunci na Iran ya sha jaddada cewa, babu aiki da tunani a cikin tattaunawa da Amurka, kuma ba abu ne na girma ba, sai dai kuma da akwai wadanda ba su nuna...
Shugaban Rukunonin Kamfanin Flour Mills Mista John Coumantaros ne, ya tarbi Dantsoho, a lokacin ziyarar aikin, inda suka tattauna kan ci gaban da ake ci gaba da samu da kuma yadda za a mayar da hankali, wajen zuba hannun jari kan aiki, musamman domin Tashoshin Jiragen Ruwan, su raba. A na sa martanin Dantsoho, ya bayyana cewa, wannan ci gaban mai alfanu, ya yi daidai da sahalewar Gwamnatin Tarayya na aikin bunkasa kasuwanci wato NSW. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani mutum mai shekara 52, Salihu Byezhe, ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake Sallar Asuba a wani masallaci da ke ƙauyen Gudaba, a Ƙaramar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya, kuma daga baya ya rasu a asibiti. Wani mazaunin yankin, Musa Dantani, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis bayan Byezhe ya yi sahur, ya yi alwala, sannan ya shiga masallaci don yin Sallar Asuba. Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi “Yayin da ake cikin sallah, kwatsam sai ya yanke jiki, nan take wasu daga cikin masu sallah suka riƙe shi suka kuma gaggauta kai shi asibiti. “Lokacin da suke kan hanyar...
Tsohon Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Dakta Doyin, Okupe, ya rasu. Dakta Doyin Okupe ya rasu ne bayan fama da jinya a sakamakon cutar kansa. Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da rasuwar Doyin Okupe ta wata sanarwa a safiyar Juma’a.

Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka
Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...

Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya
Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin Hukumar wani kokari ne na karin kudin wutar lantarki na sauyawa masu amfani da wuta daga tsarin da suka saba amfani da shi mai sauki zuwa ga wanda zai kasance wanda yake mai tsada. A sanarwar da aka fitar Shugaban kungiyar da Sakatarenta Kwamrade Joe Ajaero Komrade Emmanuel Ugboaja wadda ta ce tsarin da ake shirin yi tamkar “yin laifi ne ga tattalin arzikin kasa.”...
Ana ci gaba da takun saka tsakanin Rasha da Faransa biyo bayan kalaman Emmanuel Macron na baya-bayan nan game da kayyade makaman nukiliya. Moscow ta dauki wadannan kalamai a matsayin barazana kai tsaye, yayin da Paris ke kare matsayinta ta hanyar jaddada bukatar kare Turai, Wanda ya nuna yadda ake samun rashin jituwa sosai kan batun Ukraine. Moscow ta yi imanin cewa Emmanuel Macron, wanda ya yi Allah wadai da “tashin hankali” na Rasha yayin jawabinsa a yammacin Laraba, yana son “yakin (a Ukraine) ya ci gaba.” Ministan harkokin wajen Rasha ya yi la’akari da cewa kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya nuna yuwuwar kariyar Turai da laima ta nukiliya “barazana” ce ga Rasha. A sa’i daya kuma, Sergei...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya. A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi kan wannan zargi, yana mai cewa wannan maganar banza ce. A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, ya tunatar da cewa ita kanta kasar Birtaniya kwarariya ce wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe. A kwanakin baya ne sakataren tsaron Burtaniya Dan Jarvis ya gabatar da shawarar a gaban majalisar dokokin kasar cewa za a kara sa ido kan gwamnatin...

Nazarin CGTN: Manufar Sanya Muradun Amurka Gaba Da Komai Na Lalata Dangantakar Dake Tsakaninta Da Turai
Wani nazari da kafar yada labarai ta CGTN ta gudanar, wanda mutane 15,257 daga fadin kasashe 38 suka bayar da amsa, ya bayyana cewa manufar sanya muradun Amurka gaba da komai tana da mummunan tasiri kan dangantakar Amurkar da Turai, yayin da adadin wadanda suka aminta da Amurka daga kasashe kawayenta daga cikin masu bayar da amsa a nazarin, ya ragu. A cewar nazarin, kaso 62.9 na masu bayar da amsa sun yi Allah wadai da manufar sanya muradun Amurka gaba da komai, inda suka soki manufar suna cewa, ta yi watsi da hakkoki da muradun sauran kasashe. Adadin wadanda suka bayar da wannan amsa daga nahiyar Turai ya kai kaso 67.7. Baya ga haka, kaso 55.1 na masu bayar...
Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu. Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya. A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su...
Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.” Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy? Kwanakin baya...
Allah Ya yi wa babban malamin Musulunci a Najeriya Sheikh Sa’idu Hassan Jingir rasuwa, bayan fama da rashin lafiya. Marigayi Sheikh Sa’idu Hassan Jingir shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II na Ƙasa Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bida Wa Iqamatis Sunan (JIBWIS). Ana sa rana gudanar jana’izarsa da misalin ƙarfe biyu 2:00 na rana a Masallacin Santa, Unguwar Rimi cikin birnin Jos.
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani da makamin siyasa.
Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan kasar ya zama abin dariya ba, kamar a kwanaki kadan da su ka gabata da ya mike a gaban majalisa ya yi barazanar aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya. Haka nan kuma ta zargi Fira ministan kasar da cewa za su yi amfani da batun kara yawan taimakon soja ga Ukiraniya domin kara haraji a cikin gida. Tun bayan da aka yi cacar baki a...
Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba. Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su 450 da kayan aikin farawa, wanda zai ba su damar yin aiki mai daraja da riba. Da take jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba, wadda ta samu wakilcin jami’in kula da ofishin na Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar kula da harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa da suka samu ta...
Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki. Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa musamman a lokacin azumin Ramadan, a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya, sun bayyana rashin jin dadinsu da tashin gwauron zabi. ‘Ya’yan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu a lokacin azumi, amma farashin na kara zama wanda ba zai iya jurewa ba,” in ji su. Malam Ado Shehu, jami’in hulda da jama’a na kasuwar ‘ya’yan itacen Naibawa,...
An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki. Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara. Ya ce a lokacin azumi da ake tsananin zafi a hankali ruwan jiki yana raguwa. A cewarsa karuwar cin ‘ya’yan itatuwa daban-daban zai yi matukar amfani ga musulmi mai azumi. Farfesa Afolabi ya bayyana cewa a lokacin azumin watan Ramadan musulmi sun kaurace wa abinci da abin sha, tare da hana jikinsu cin abinci da suka saba. Ya ba da shawarar a kara amfani...
An yanke wa wasu mutum uku da aka kama da laifin fyaɗe hukuncin ratayewa da kuma dandaƙewa a Jihar Kaduna. Kwamishinar Kula da Walwalar Jama”a, Hajiya Rabi Salisu, ta bayyana fatan cewa hukuncin da kotu ta yanke wa masu laifin zai zama darasi ga masu muguwar ɗabi’ar ta fyaɗe. Da take sanar da hakan a ranar Laraba, kwamishinar ta bayyana cewa Ma’aikatar ta yi nasara a Shari’o’i uku da ta shigar da ƙara kan masu aikata fyaɗe a shekara gudanar ta gabata. Ta bayyana cewa daga cikin mutanen akwai wanda Mai Shari’a Nana ta Babbar Kotun jihar ta yanke masa da hukuncin dandanƙewa da kuma kisa ta hanyar rataya, a watan Yuni shekarar 2024. An kama korarren jami’in tsaro da...
Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su, Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba. Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya. Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
Wani gini mai hawa biyu ya rufta a yankin Lekki da ke Jihar Legas wanda ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu shida. Jami’an bayar da agaji daga hukumomin LASEMA da NEMA sun ceto waɗanda suka jikkata kuma an kai su Babban Asibitin Marina domin kula da lafiyarsu. Majalisar Kano ta yi wa dokar hukumar tace fina-finai gyaran fuska Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Tun da farko, ’yan sanda sun ce an ceto mutum 14 daga wajen da ginin ya rufta. Sakataren hukumar LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa ana bincike don gano musabbabin rushewar ginin. “Zuwa yanzu mun gano gawarwakin mutum biyu daga...
Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi matukar birge ’yan kallo na ciki da wajen kasar. Bugu da kari, a karon farko, mutum-mutumi za su shiga a dama da su a wasan gudun fanfalakin da za a gudanar cikin watan Afrilu mai zuwa a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ake sa ran mutum-mutumin nan da aka saka masa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, Tian Kung wanda cibiyar bunkasa kere-keren mutum-mutumi masu...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya ba da gudummawar Riyal biliyan 40 ga wata kungiyar agaji da mai rajin ganin an sako fursunoni mabukata da aka samu da laifin aikata laifuffuka wandanda ba na son rai. A duk shekara, a cikin watan Ramadan, wannan kungiya mai zaman kanta ta kan kaddamar da kiraye-kirayen bayar da tallafi don tara kudade da biyan Diya, ta yadda za a saki fursunonin da ake yanke musu hukunci bisa aikata laifukan da ba da gangan ba. Taron dai ya hada jami’ai da masu ba da agaji a Tehran babban birnin kasar da kuma garuruwa daban-daban na kasar duk shekara. Diya wani hakki ne da ake biya ga wanda aka...
Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, ta shigar kan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, inda ta zarge shi da cin zarafinta. Kwamitin ya bayyana ƙorafin a matsayin “mattacen ƙorafi tun kafin a duba shi.” Zargin Cin Zarafi: Natasha ta gabatar wa majalisa ƙorafinta game da Akpabio Matashi ya hallaka mahaifiyarsa da duka a Bauchi A ranar Laraba, kwamitin ya bayyana cewa ƙorafin bai cika ƙa’ida ba. Shugaban kwamitin, Sanata Neda Imasuen, ya ce Natasha ce da kanta ta sanya hannu a kan ƙorafin, maimakon wani ya sa mata hannu, wanda hakan ya sa ya zama mara inganci. Haka kuma, ya bayyana cewa batutuwan da ke cikin ƙorafin tuni suna gaban kotu,...
Bayan wannan jawabi, Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi bisa dokar majalisar, imda ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da matsayinsa ba daidai ba. Ta kuma nemi izinin miƙa ƙorafin ga majalisar a hukumance. Majalisar ta tura ƙorafin zuwa Kwamitin ladabtarwa domin ci gaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma bukaci kwamitin da ke da alhakin rabon kayayyakin da su hada kai da shugabannin al’umma da na addini a yankunansu domin ganin an raba kayan abincin yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel kan zargin almundanar naira biliyan 700. EFCC ta tsare tsohon gwamnan ne bayan ya amsa gayyatar ta a ranar Talata domin amsa wasu tambayoyi kan zargin karkatar da kuɗi da wata ƙungiya mai rajin yaƙi da masu zamba ta yi masa. ’Yan sanda sun ceto wani mutum da aka yi garkuwa da shi a Gombe Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Ƙungiyar ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya karɓi naira tiriliyan uku daga asusun Gwamnatin Tarayya a tsawon shekara takwas da ya yi yana mulki, amma ya bar wa jihar bashin naira biliyan 500 da rashin biyan...
Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
“Wannan kasafin kuɗin ya nuna sabon gagarumin fifiko a kan harkar tsaro, ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, ma’adanai, noma, da sauran sassa masu matuƙar tasiri kan jin daɗin al’umma da cigaban tattalin arzikin su.” Ya ƙara da cewa shekarar 2025 ita ce “shekarar tabbatar da cigaba,” inda sauye-sauyen da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta fara aiwatarwa za su fara haifar da ainihin sauyi ga al’umma. Ya kuma jaddada cewa tun tuni aka fara ganin sauƙin farashin kayan abinci, wanda ke samar da sauƙin rayuwa ga ‘yan ƙasa. Ministan ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata domin tabbatar da ingantaccen tasirin sa a rayuwar...
Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba. “Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.” A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya. Daga kanmu, magana...
Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin, take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa kuma...
Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green Horizon, Farfesa Muhammed Sabiu (SAN) ne ya jagoranci taron wanda shirin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila ta shirya. Tun da farko a jawabinsa na bude taron, Sarkin Katsina, Dokta Abdulmuminu Kabir Sarkin Fulani Hamceta Alhaji Aminu Lawal Bagiwa ya wakilta, ya ja hankalin mahalarta da su tsaya domin sanin abin da za a ilmantar da su kasancewarsu na shugabannin al’umma kuma na farko da ake kawo...
Yayin da al’ummar Musulmai a Najeriya da duniya ke fara azumin watan Ramadan, Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta aike da sakon fatan alheri, tana kira da a yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen sabunta zukata da nuna tausayi da karfafa hadin kai a kasa. A cikin wata sanarwa da Daraktan Janar na gidauniyar, Abubakar Gambo Umar ya sanya wa hannu, ta jaddada bukatar kyautata dabi’u da wanzar da zaman lafiya da adalci a kasuwanci a lokacin azumi. Gidauniyar ta yi kira ga malaman addini da su ci gaba da yada sakonnin tsoron Allah da hakuri da kaunar juna, domin karfafa darussan Ramadan na sabunta imani da hadin kan al’umma. Hakazalika, gidauniyar ta...
Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata. Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar. Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi...
Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja. Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa; “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa...
A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83. Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.” Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi wannan kiran ne bayan wata maganan da ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya yi dangane da kasar Iran. Labarin ya kara da cewa, Hakan Fiddan ya bayyana cewa shirye-shiryen JMI a kasar Siriya masu rusa kasar ne, kafin juyin mulkin da Turkiyan ta dauki nauyinsa a baya-bayan nan a kasar Siriya. Ya ce: Fidan yana magana kan gagarumin taron Jana’izar Shahid Sayyid Hassan...
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja Bayan murabus ɗin nata, nan take ’yan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Nijeriya. ’Yan majalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayin mace ta farko kakakin majalisa. Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan ’yan jam’iyyar APC...