2025-02-20@08:54:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 46
«rajistar layin»:
Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ( IRGC) ta yaye kallabin sabbin makamai a atisayen soja mai yaken “Rasulul-A’azam” da suke ci gaba da yi a halin yanzu. Daga cikin makaman da aka kaddamar da akwai makamai masu linzami dake cin dogon zango, sai kuma jiragen sama marasa matuki da kuma makaman Atilare. A jiya Laraba ne dai aka kaddamar da sabbin makamai masu linzamin wanda ya sami halartar manjo janar Muhammad Bakeri da shi ne babban hafasan hafsoshin sojan kasar Iran. Shi kuwa janar Ali Kuhistani da shi ne mataimakin kwamandan rundunar ta IRGC a fagen kayan yaki, ya ce; Sabbin makamai sun kunshe da kayan aiki na zamani masu muhimmanci da aka hade su wuri daya....
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin ta yi hira da shugaban Pakistan, Asif Ali Zardari, dake ziyarar aiki a kasar Sin, a baya bayan nan a birnin Beijing. Yayin hirar, Zardari ya bayyana cewa, ci gaban kasar Sin al’amari ne mai kyau, kuma Sin ba ta taba zama mai mamaya ba. Bisa ci gaban Sin cikin sauri, wasu kasashe suna daukarta a matsayin wata “barazana”. Game da hakan, Zardari ya ce, a matsayin makwabciyar kasar Sin, kasar Pakistan ta san a ko da yaushe Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, kila ne a ji tsoron sauran kasashen duniya, amma ba kasar Sin ba. (Safiyah Ma)
Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, yana mai nuni da hakan a matsayin ci gaba da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon. Baqa’i ya yi nuni da cewa: Barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, wanda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar...

Shugaban kasar Iran Ya Jaddada Matsayin Kasarsa Na Rashin Son Shiga Yaki Amma Tana Shirye Wajen Fuskantar Barazana
Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ba su neman yin yaki, amma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fuskantar duk wata barazana Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran ba za ta mika kai ga duk wata barazana ba, kuma ba za ta ja da baya ba wajen fuskantar matsin lamba, yana mai jaddada cewa; Kasarsa ba ta neman yaki da wata kasa, sai dai tana kokarin karfafa dangantakar abokantaka da kasashen makwabta. Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da ya kai lardin Bushahar inda ya gana da al’umma tare da jinjinawa sadaukarwar shahidai musamman shahidan wannan lardin, a daidai lokacin da ake cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci,...
Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa. Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba. DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa An harbe ’yan sanda biyu a Yobe Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar...
Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.

Shugaban Kungiyar Hamas Yace: Iran Bata Gusheba Tana Taimaka Mana, Kuma Shirin Trump Na Kwace Gaza Zai Ya Lalace
Khalilul Hay, shugaban kungiyar Hamas a Gaza, wanda ya halarci gangamin bikin cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran, ya bayyana cewa yakin Tufanul Aksa ya na matsayin mataki na farko ne na kwatar kasar Falasdinu daga hannun wadanda suka mamayeta. Ya kuma kara da cewa JMI ta taimakawa kungiyar sa kuma tana ci gaba da taimaka mata, har’ila yau yana da yakini Iran zata ci gaba da taimakawa kungiyar Hamas har zuwa nasara. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta watsa jawabin Al-Hay kai tsaye daga birnin Tehran a safiyar yau litinin, inda ya yi Jawabi a dandalin Azadi dake tsakiyar birnin Tehran. Yace, farmakin ‘waadu Sadik na daya da na biyu duk...
Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...

Ministan Mai Na Iran Ya Ce: Hana Iran Fitar Da Man Fetur Zuwa Kasuwannin Duniya Mafarki Ne Na Shugaban Amurka
Siyasar tsananata matsin lamba kan Iran ta gaza cimma buri kuma hana fitar da man da Iran ke fitarwa mafarki ne da ba zai tabbata ba Ministan mai na kasar Iran Mohsen Paknejad ya bayyana matsayar matsin lamba da Amurka ke yi kan fitar da man kasar Iran a matsayin siyasa ta nuna gazawa, yana mai cewa: Hana fitar da man fetur din Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa wajen kasar, mafarki ne da ba zai taba wanzuwa ba. Ministan mai na Iran Mohsen Paknejad a matsayin mayar da martani ga furucin Trump ta sake dawo da tsananta siyasar matsin lamba da nufin gurgunta harkar tattalin arzikin Iran ta hanyar hana ta fitar da man fetur, a jiya Lahadi ya bayyana...

Kwamandan Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Ya Ce: Hamas Ta Yi Rawar Gani Wajen Kare Kanta
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
An bude atisayen soja kan teku bisa hadin gwiwar wasu kasashe a birnin Karachi na kasar Pakistan, a ranar 7 ga wata. Asitayen sojan da kasar Pakistan ta tsara ya samu halartar jiragen ruwan soja daga kasashe sama da guda 10, wadanda suka hada da Sin, da Indonesiya, da Japan, da Italiya, da Malasiya, da kuma Amurka da dai sauransu. Haka kuma, sauran kasashe sama da guda 40 sun tura masu sa ido wajen atisayen. An raba atisayen sojan zuwa matakai guda biyu. Mataki na farko shi ne tsakanin ranaku 7 zuwa 9 ga watan Fabrairu, inda za a yi atisayen soja kan tashar jiragen ruwa, da tattaunawa kan atisayen, da tattaunawa kan ayyukan musamman tsakanin bangarori daban daban da...
Wani Mataimakin Sufeton ’Yan Sanda (ASP), Shafi’u Bawa, da ke aiki da Rundunar 61 Police Mobile Force a Kontagora da ke Jihar Neja, ya hallaka kansa har lahira. Wani jami’in dan sanda ya shaida wa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne a ranar Asabar. Gwamnatin Kano ta dakatar da wani fim mai suna Zarmalulu Aisha Binani ce ta lashe zaɓen Adamawa, ina da ƙwararan hujjoji – Ari An tsinci gawarsa rataye a cikin dakinsa. Majiyoyi sun ce mahaifinsa, Malam Usman Bawa ne, ya fara gano abin da ya faru sannan ya kai rahoton lamarin zuwa ofishin ’yan sanda da ke Kontagora. Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce: “A ranar 8...
Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma. Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni. A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004. Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan...
Kwamandan rundunar sojin saman Iran ya bayyana cewa: Sun kai ga nasarar cimma matakin cin gashin kai a kere-keren kayayyakin aikin soja Kwamandan rundunar sojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa: Sojojin saman Iran na ma’aikatar tsaro da taimakon sojojin kasar sun cimma mataki dari bisa dari a fagen gudanar da kere-keren kayayyakin da suke bukata a harkar tsaron kasa, kuma dukkanin kayan aikin wannan runduna an inganta su tare da mayar da su saffarin cikin gida. A ranar Juma’a 7 ga watan Fabrairu, Birgediya Janar Wahidi ya sanar a gaban taron kwamandojin sojojin saman Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Jagoran juyin juya halin Musulunci a wata hira da aka yi da shi ta...
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin EDR Takale Uma, ya bayyana a ranar Alhamis cewa, kamfanin layin dogo na Ethio-Djibouti (EDR), yana samun ci gaba mai kyau, tare da kara karfinsa na jigilar kayayyaki zuwa kasashen waje. Uma ya bayyana a shafinsa na X cewa, “Tare da karin kan jiragen kasa da taragu, yanzu mun samu damar baiwa karin wurare hidima, mun fadada zirga-zirga daga Indode da Adama zuwa Mojo, Dire Dawa, da kuma wurin ajiye kaya na Sabata.” Uma ya kara da cewa, EDR yana maye gurbin tsoffin kayayyakin aiki da sabbi, da kuma gyara wadanda suka lalace, kana ya kara yawan jiragensa daga jiragen kasa takwas zuwa 21 da taragu 892 zuwa 935. Yana mai cewa “Jajicewar da muka...
Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji. Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa. “Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan rashi, Allah ya sa wannan ya zama na karshe a cikin irin wannan mummunan lamari a cikin al’ummarmu,” inji...

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Iran Ya Sanya Sheikh Na’im Kasim A Matsayin My Wakiltarsa A Kasar Lebanon
A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai ya taka rawar a zo a gani wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
Ancelotti ya shaidawa manema labarai ranar Talata cewa “Bellingham ya samu rauni yayin atisaye amma kuma Vinicius Jr zai buga wasan gobe duk da cewar har yanzu ya na kan murmurewa daga raunin da ya ji a watan jiya Ya kuma ce Mbappe ya yi atisaye kamar yadda aka saba a yau, amma gobe ba zai samu damar buga wasan ba, Madrid ce kan gaba a teburin La Liga da maki 49 a wasanni 22, maki daya tsakaninsu da Atletico Madrid wadda zasu hadu ranar Asabar a Santiago, bayan nan kuma zasu ziyarci zakarun Ingila, Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar 11 ga Fabrairu.
Sojojin sama na JMI sun sami nasarar kakkabo jiragen yaki na makiyan da aka sawwara, tare da amfani da makami mai suna Majid a cikin atisayen sojojin sama da suke gudanarwa a kudu masu yammacin kasar. Jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa dai, suna da masu muhimmanci a yakin zamani a halin yanzu, don haka sojojin sama na kasar suka bawa al-amarin muhiommanci. Banda haka tana da makiya wadanda suke da su a yankin wadanda suek amfani da irin wadannan makamai. A atisayen dai an sawwara jiragen makiya da dama a sararin samaniya, wadanda suke kokarin fadawa kasar, sannan aka cilla makaman garkuwan sararin samaniya samfurin Majid wadanda suka kakkabosu gaba daya.
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya kasance daga cikin shirye-shiryen kasar na shirin kare sararin samaniyar kasar ta sama. Labarin ya kara da cewa a wannan karom ma sojojin Iran da kuma dakarun juyin juya halin musulunci zasu yi atisayen hadin giwa ne don gwada karfin sojojin kasar da kuma IRGC na kare sararin samaniyar kasar. Kafin haka dai sojojin sun gwada karfinsu a bangarori daban daban na sojojin kasar don...
Babbar Kotun Jihar Kogi ta tsige Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga kujerarsa ta Ohinoyi na Ƙasar Ebira. Kotun ta soke naɗin Alhaji Ahmed Muhammed ne a ranar Litinin, shekara guda bayan fara aikin basaraken. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Salisu Umar, ya kuma dakatar da basaraken daga gabatar da kansa matsayin Ohinoyi, har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe. Kotun ta bayar da umarnin ne bayan ƙarar da Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutum biyu suka shigar. Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba Sun shigar da...

Limamin Juma’ar Tehran Ya Jinjinawa Wanda Ya Assasa Juyin Musuluncin A Iran Marigayi Imam Khumaini ( R.A)
Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin. Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da falsafa. Limamin juma’ar na Tehran wanda yake jawabi dangane da zagayowar cikar shekaru 46 daga dawowar Imam Khumaini Iran bayan zaman hijira na shekaru 15 a kasashen waje, ya ce abin alfahari ne yadda wannan rana ta zagayo a daidai wannan lokacin da kungiyoyin gwgagwarmayar musulunci suke kara bunkasa da daukaka a duniyar musulunci. Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma bayyana cewa abinda yake...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi. Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?. A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda...
Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar hankali. Yayin bikin, hukumomin kula da layin dogo na sassan kasar sun kara karfin aiki a wuraren da aka fi amfani da su, da inganta karfin ba da hidimmomin jiragen kasa da tashoshi, da aiwatar da matakan saukakawa jama’a, da kuma kokarin samar wa fasinjoji ingantacciyar hanyar tafiya. Alal misali, reshen Beijing na kamfanin kula da layin dogo na kasar Sin, ya kara tashoshin caji...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace. Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci...
Liverpool, Barcelona, Arsenal, Inter Milan, Atletico Madrid, Bayer Leverkusen, Lille, Aston Villa. Ƙungiyoyin Dake Jiran Tsammani Atalanta, Borussia Dortmund, Real Madrid, Bayern Munich, AC Milan, PSV, Paris St-Germain, Benfica, Monaco, Brest, Feyenoord, Juventus, Celtic, Manchester City, Sporting, Club Brugge. Ƙungiyoyin Da Aka Kora Dinamo Zagreb, Stuttgart, Shakhtar Donetsk, Bologna, Sparta Prague, Leipzig, Girona, Red Star Belgrade, Sturm Graz, Salzburg, Slovan Bratislava, Young Boys.
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa. Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...

Hukumar Gidagen Radiyo Da Talabijin Na Kasar Iran Ta Bada Sanarwan Kama Dan Rahotonta A Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye
A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....
Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar. Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai...
Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40. Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci. Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci. Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina. Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba. “Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba. “Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko. “A yanzu na ƙara...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
Real Madrid za ta fafata da Leganes, yayin da Barcelona za ta je Valencia a zagayen kwata fainal a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin. Wani wasan da zai yi zafi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Getafe, yayin da za a yi tata-ɓurza tsakanin Real Sociedad da Osasuna. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu Ana sa ran buga wasannin da za a gudanar ranar 5 ga watan Fabrairu. A jadawalin ya bayar da damar sake buga El Clasico wato karawar hamayya tsakanin Real da Barcelona a wasan ƙarshe da suka daɗe ba su haɗu a gasar tsawon shekaru. An haɗu...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025. Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja, ya ce hakan ya nuna kwazon hukumar a karkashin ma’aikatar filaye da gidaje na tallafa wa tattalin arzikin jihar. Malam Saidu Bakuwai, ya ba da karin haske kan ayyukan hukumar da suka hada da alhakin duk wasu takardu da suka shafi filaye, tsarawa da bayar da takaddun kowane gida, sake tantancewa, daidaitawa, da kuma tsarin rajistar kadarorin. Sauran su ne Gudanarwa da Rajista...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi. Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.