2025-04-03@11:26:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 562

«Wannan saboda»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci. Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa. Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci. Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai...
    (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali.  Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, da tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa samun moriyar kasa da kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya hade kowa da kowa, da neman bunkasa ta bai-daya, tare da samar da moriyar juna da dukkan...
    “Wannan mataki na dokar ta-ɓaci wata dama ce ta kare rayuwar al’umma, tabbatar da tsaron muhimman kadarori, da dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu. Shugaba Tinubu ya buƙaci dukkanin ɓangarori su mara baya ga ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Jihar Ribas tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziƙi da haɗin kan ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar. Ko abin ya tafi kamar yadda Trump ya yi tsamani? Alal hakika, manufofi marasa dorewa da gwamnatin Trump ta dauka na illata amanar Amurka, har ma hakan ya yi ta dakushe kwarin gwiwar masu zuba jari na ketare da na kamfanonin cikin gidan kasar. Babban mizanin wasu muhimman hannayen jarin Amurka ya yi matukar raguwa kwanan baya, abin da ya shaida damuwar masu zuba jari a...
    Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A Ribas? Ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas yana nufin Gwamnatin Tarayya ta ƙwace ikon jihar, kuma hakan na iya kawo cikas ga harkokin siyasa da ci gaban jihar. Masana doka da ‘yan adawa na ganin cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama wata hanya ta take haƙƙin masu mulki da aka zaɓa a jihar. Tun bayan ɗaukar wannan mataki,...
    Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta...
    Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara.   A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13.   A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.   Sanarwar ta bayyana cewa...
    Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya.   Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da ‘yan jarida, yana mai bada tabbacin cewa wannan kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa za su kasance ginshiƙin gudanar da mulki a jihar.   “Mu a Jihar Gombe muna alfahari da daɗaɗɗiyar dangantakar da muka ƙulla da ‘yan jarida; ‘yan jarida abokan aikinmu ne masu ƙima a fagen kawo ci gaba, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ganin sun ci gaba da yin aiki...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, mutane da dama sun fahimci muhimmancin koyan sana’a wajen dogaro da kai, maimakon dogaro da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu masu sana’ar hannu, musamman teloli, da rashin cika alƙawari. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya A mafi yawan lokuta, ana samun matsala da su, musamman a lokutan bukukuwa, inda suke kasa kammala ɗinkin kayan da aka ba su ko suka yi alƙawari. Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi. Domin sauke...
    Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [10] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [9] Fashin Baƙi: Ibn Juzai, ya bayyana nau’ikan rai uku da suka shafi halayyar ɗan’adam, bisa koyarwar addinin Islama. Waɗannan nau’ikan rai suna da nasaba da matsayin mutum a cikin halayensa da alaƙarsa da Allah. Ga cikakken bayani kan kowanne daga cikinsu: 1. Rai Mai Umarni da Mummuna (النَّفْسُ الأَمَّارَةُ بِالسُّوءِ): Wannan ita ce zuciyar da take yawan umartar mai ita da aikata sharri da mugunta, da saɓo. Allah Ya ambaci irin wannan rai a cikin Alƙur’ani inda Ya ce:” Ba kuma ina wanke kaina ba ne. Shakka babu ɗabi’ar rai ce ta umurci mutum da yin mummunan abu, sai fa wanda Ubangiji Ya yi...
    Alakar tattalin arziki da cinikayya bisa daidaito da aminci kuma mai dorewa tsakanin Sin da Amurka ta dace da muhimman muradun kasashen biyu, kuma za ta amfanar da kamfanoni a duk duniya, a cewar mataimakin ministan cinikayya Wang Shouwen yayin wata ganawa da Ramon Laguarta, shugaban kamfanin PepsiCo a ranar Talata. Da yake karin haske kan yadda kasar Sin ke da karfin gwiwar cimma burinta na bunkasa tattalin arzikinta na shekarar 2025 da aka gabatar a cikin rahoton aikin gwamnati, Wang, kuma wakilin harkokin cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin, ya bayyana cewa, wasu jerin tsare-tsare da kasar ta bullo da su na fadada bukatun cikin gida, da sa kaimi ga inganta tsare-tsaren yin sayayya za su samar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata Kungiyar Agaji Mai Zaman Kanta, Ike Odoeme Foundation, ta taimaka wa yankuna biyu a karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa, ta hanyar haka rijiyoyin burtsatse guda bibbiyu a kowane yanki. A yayin kaddamar da ayyukan a kauyukan Facawa da Riniyal da ke  Ringim, jami’ar shirye-shirye ta gidauniyar, Miss Suzie Agas, ta bayyana jin dadinsu na yin tasiri a rayuwar al’ummar yankin.   A cewarta, wannan aikin yana tabbatar da kudirin gidauniyar na tabbatar da cewa kowace al’umma tana da damar samun tsaftataccen ruwa, ba tare da la’akari da matsayinta ko inda take ba. Suzie Agas ta jaddada cewa ruwa yana da matukar muhimmanci ga kiwon lafiya da ci gaban tattalin arziki, amma abin takaici, al’ummomi da dama na...
    Haka kuma, a ranar 3 ga Fabrairu, jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutum uku da bindigogi 10 ƙirar AK-47, inda suka amsa cewa suna sayar da su ga masu aikata laifuka. Rundunar ‘yansanda ta ce za ta ci gaba da yaƙi da fasa-ƙwauri da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A ci gaba da taya Falasdinawa fada da sojojin Yemen suke yi, sun kai wa sansanin jiragen sama na HKI dake saharar “Nakab” hari da makami mai linzami samfurin “Ballistic’ wanda ya fi sauti sauri. A wata sanarwa da sojojin Yemen su ka yi da marecen jiya Talata sun bayyana cewa; a karkashin taimakawa Falasdinawa da ake zalunta, da kuma mayar da martani akan kisan kiyashin da abokan gaba ‘yan sahayoniya suke yi wa ‘yan’uwanmu a Gaza, sojojin Yemen sun kai hari da yardar Allah  akan sansanin sojan sama na Nivatim” da makami mai linzami wanda ya fi sauti sauri, mai suna “Falasdinu 2” sun bisa yardar Allah ya isa inda aka harba shi.” Sanarwar ta kuma ci gaba da...
    Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000.   A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba   A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram.   A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro.   Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya.   Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu   Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci...
    Jaridar Financial Times ta Burtaniya ta bayyana cewa, masu zuba jari na kasashen waje suna kara “gano kasar Sin”, kuma sun yi imanin cewa, kasar Sin za ta iya samar da “kirkire-kirkire da damammaki” masu yawa a wasu fannoni. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana yau Talata cewa, bisa gayyatar da gwamnatin kasar Namibiya ta yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Peng Qinghua, zai halarci bikin rantsar da shugabar kasar Netumbo Nandi-Ndaitwah a birnin Windhoek, a ranar 21 ga watan Maris. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Wannan shi ne karo na biyu, a shekarar da ta gabata dukkanin ƙananan hukumomi a Nijeriya ta hannun jihohinsu sun samu tallafin buhun shinkafa miliyan ɗaya mai nauyin kilogiram 10. Don haka, a wannan shekarar ma muna sake yin makamancin na bara.”   Hashim ya yi tilawar cewa gidauniyar Dangote ta himmatu wajen samar da tallafin kayan abinci ga mabuƙata, tallafi a ɓangaren kiwon lafiya, gina ɗakunan kwanan ɗalibai a jami’o’i, da sauran tallafi ciki har da wanda gidauniyar ta yi a lokacin annobar Korona.   Ya ce tallafin dafawa ne kan ƙoƙarin da gwamnatocin jihohi ke yi wa al’ummarsu, ya yi fatan cewa shinkafar da suka kawo Bauchi ɗin za ta je kai tsaye ga waɗanda aka bayar domin...
    Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji bayan ya tsallake karatu uku a wannan Talatar. Wannan na zuwa ne bayan karatun tsanaki da majalisar ta yi ƙudirin a ranar Alhamis ta makon jiya. Wike ya ƙwace filin Sakatariyar PDP da ke Abuja Janar Tsiga ya shafe kwanaki 40 a hannun masu garkuwa duk da biyan kuɗin fansa Ana iya tuna cewa, a makonnin bayan nan ne kwamitin kuɗi na majalisar ya gudanar da sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin, inda kuma ya tattara ra’ayoyin al’umma ya miƙa wa majalisar. Dokar harajin da majalisar ta amince da ita ta ƙunshi ƙudiri guda huɗu da suka haɗa da ƙudirin dokar tafiyar da haraji da na kafa hukumar tattara haraji mai suna Nigeria...
    Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce, “A daren yau mun koma yaƙi a Gaza.” Hamas ta zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsawon kusan wata biyu, tana mai cewa hakan na barazana ga lafiyar fursunonin da ke tsare a Gaza. Amma Isra’ila ta ce Hamas ce ke ƙin sakin fursunonin tare da bijirewa yarjejeniyar sulhu. A lokacin yarjejeniyar, an yi musayar wasu fursunonin Isra’ila da Falsɗinawa da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila. Sai dai har yanzu kimanin mutum 59 daga cikin fursunonin Isra’ila suna hannun Hamas, kuma ana zargin rabinsu sun mutu. Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta amince da harin da Isra’ila ta sake kai wa Gaza, inda ƙasashen biyu suka sha alwashin yaƙar Hamas, ‘yan tawayen Houthi...
    An shiga wata 11 da Gwamnatin Jihar Sakkwato ƙarƙashin Gwamna Ahmad Aliyu ta tuɓe rawanin wasu sarakuna da take ganin sun yi abin da bai dace ba na shiga siyasa. Tun bayan cire sarakunan, mutane sun yi tsammanin gwamnati za ta nada wadanda take muradi ne kai-tsaye domin su maye gurbin tubabbun sarakunan, amma shiru kamar ba wasu da ke jiran hukunci da sakayyar gwamnati mai ci. Kofin Duniya: ’Yan wasan cikin gida 8 da Super Eagles ta gayyata Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu Har yanzu gwamnati ba ta fito ta fadi dalilin rashin sake nada sababbin sarakunan ba domin ci gaba da wakilcin jama’a, ganin an bar garin kufai ba cikakken basarake. A baya da ma...
    Ya zuwa yanzu dai, Gwamna Fubara bai ce komai ba kan lamarin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dan Mahadi Karubi, wanda  yana  ya jagoranci boren 2009 bayan zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa an daukewa mahaifin nashi daurin talalar da aka yi masa bisa umarnin ma’aikatar sharia. Shi dai Mahadi Karubi an yi masa daurin zaman gidan ne bayan hargitsin da ya jagoranta bayan zaben shugaban kasar da aka yi a 2009. Husain Karubi ya fada wa kamfanin dillancin labarun “IRNA” cewa; An fada wa mahaifina cewa, Daga nan zuwa watan Aprilu zai iya gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da kaidi ba, amma daga yanzu zuwa lokacin zai iya sanar da jami’an tsaro inda yake son zuwa gabanin  kwana daya. Harigitsin day a biyo bayan zaben 2009 a Iran wanda ‘yan takara uku...
    Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [9] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [8] Neman taimako daga Allah yana da nau’i biyu: 1. Taimako na Gaba ɗaya: Wannan yana nufin cewa dukkan halittu suna buƙatar Allah wajen gudanar da rayuwa, kamar samun arziki, da lafiya, da tsira da kulawa, da sauran su. 2. Taimako na Musamman: Wannan kuwa shi ne neman taimako daga Allah wajen yi Masa ibada da biyayya, da bin hanyoyin shiriya, da tabbatar da zuciya a bisa tafarkin daidai har lokacin mutuwa da sauran su. A wurin Allah kaɗai ake neman taimako a cikin ibada. Wannan yana nuna cewa ibada ba za ta cika ba sai da taimakon Allah. Idan mutum yana son ya yi...
    Yau Litinin da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya kira wani taron manema labarai, inda kakakin hukumar kididdiga ta Sin, Fu Linghui ya yi bayani kan yadda tattalin arzikin kasar ke gudana a cikin farkon watanni biyu na bana da suka gabata. Kididdiga na nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Fabrairu na bana, masana’antar samar da kayayyaki na samun saurin bunkasa, inda ribar da kamfanoni da masana’antu da ke iya samun ribar da ta zarce dala miliyan 2.7 a duk shekara, ta karu da kashi 5.9% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, masana’antar ba da hidima ta fi samun bunkasuwa, inda alkaluman ci gabanta suka karu da kashi 5.6% bisa na makamancin lokacin bara, kuma...
    Wasan na tare da jarumai da suka hada da Rekiate Ibrahim-AttahRekiya Attah, Ramadan Booth, Rabiu Rikadawa, da sauran jarumai. ‘MAGGI Tales of Ramadan’ yana kunshe da darussa masu kayatarwa da aka tsara na mako 6 wanda zai fara daga farkon watan Ramadan. A yayin kallon wasan za a fuskanci muhimman abin da zai karfafa soyayya a tsakanin al’umma. Wannan kuma abu ne da ake bukata a rayuwa.   A kowanne shafi na labarin zai fito da cikakken abubuwan da suke tattare da darussan watan Ramadan a tsakanin al’umma gaba daya musamman ganin yadda aka kama baki da rana har aka zo yin buda baki da kuma lokacin da yin sahur.   A jawabinta, shugabar vangaren kula da sarrafa MaGGI na...
    “Za a lika sunayen tare da albashin ma’aikata a wurare masu mahimmanci a cikin harabar ma’aikatu, ofisoshin gwamnati da sakatariyar kananan hukumomi 44 na jihar don sauƙaƙe aikin,” in ji Faruk. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar ta Amurka Donald Ttump ya kara yawan kasashen da ya sa wa takunkumin shiga cikin Amurka zuwa kasashe 43. Daga cikin kasashen da ya sa wa sharuddan shiga cikin kasar Amurka sun hada guda 11 da su ne; Somaliya, Sudan, da Libya. Sai kuma Afghanistan, Cuba, Iran, Korea Ta Arewa, Syria, Venezuela da kuma Yemen. A lokacin zangonsa na farko Trump matakin nasa ya ja hankalin duniya saboda yadda ya hana ‘yan hijira daga kasashen Iraki,  Libya, Somaliya, Sudan da Yemen shiga cikin kasar. An kalubalanci matakin na shugaban kasar Amurka a wancan lokacin a kotu saboda yadda ya shafi mafi yawancin kasashen musulmi. Bayan da Joe Biden ya zama shugaban kasa ya soke wancan matakin na Donald...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.” Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili da kuma abinda wasikar tasa ta kunsa. Dr. Baka’i ya kuma kara da cewa; Bayan yin nazarin wasikar da abinda ta kunsa za mu bayar da jawabi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kore cewa ziyarar da ministan ma’aikatar tasu Abbas Arakci ya kai zuwa kasar Oman yana da alaka da bayar da jawabin wannan wasikar ta shugaban kasar Amurka. Da yake mayar...
    Kasar Yemen ta sanar da cewa Amurka da ta sake kai wasu hare-haren a gundumar Hudaidah akan wani kamfani na auduga. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto majiyar Ansarullah ta  kasar Yemen din tana cewa; Sojojin na Yemen sun kai hare-hare da makamai masu linzami har 18 akan jiragen ruwa na dakon jiragen yaki “USS Troman” hari. Kakakin sojan kasar Yemen ne janar Yahya Sari ya sanar da kai hare-hare na martani akan jiragen yakin Amurka. Tun daga ranar Asabar din da ta gabata ne dai jiragen yakin Amurka da na Birtaniya su ka rika kai wa Yemen hare-hare da sun yi sanadiyyar shahadar mutane da dama. Yankunan da harin ya shafa sun hada biranen San’aa da kuma...
    Mataki na Uku: Kare kai daga shubuha; wato matakin tsantseni, shubuha na nufin abubuwan da ba a tabbatar da halacci ko haramcinsu ba. Akwai wani mataki da ya fi kauce wa haram, wato kauce wa abubuwan da ke da shakku. Annabi (SAW) ya ce: ” Lalle halal a bayyane take, kuma lalle haram a bayyane yake, amma akwai wasu abubuwa masu rikitarwa a tsakanin su waɗanda mutane da yawa ba su san su ba, wanda ya nisanci shubuha, to ya kare addininsa da mutuncinsa.” Bukhari da Muslim ne suka ruwaito. Saboda haka, matakin tsantseni yana nufin mutum ya kiyaye kansa daga duk wani abu da zai iya kai shi ga haram, koda kuwa ba a tabbatar da haramcinsa ba. Mataki...
    A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar. Hakan na kunshe cikin wata ’yar takaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar. Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “dan siyasar wariyar launin fata mai kyamar Amurka,” lamarin da ya kara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria. A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Afirka ta Kudu, sakamakon...
    Sama da shekaru 80 kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40. Shugaba Donald Trump na Amurka ya ba da umarnin dakatar da ayyukan wasu hukumomin ƙasar guda shida da rushe wasu baki daya, ciki har da kafar yaɗa labarai ta Voice of America wato VOA. Sauran hukumomin sun hada da gidajen adana kayan tarihi da ɗakunan karatu da bangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna. Daga ciki har da hukumar US Agency for Global Media wadda gidan rediyon Muryar Amurka wato VOA ke karkashinta da Radio Free Europe da Asia da Radio Marti wadda ke yaɗa labarai da Sifaniyanci a Cuba. Haka kuma tuni Trump din ya soma daukar wasu matakai wadanda suka...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta yi martani kan korar jakadanta daga Amurka Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA “A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo. “Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.” Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin Nukliya, da hadsa fitina a kudancin Asia. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yace dukkan wadannan zarge-zarge basa da toshe. Sannan ya zargi kasashen kungiyar na G7 da goyon bayan HKI a kissan kiyashin da ta aikata a Gaza. Kafin haka dai kasashen kungiyar ta G7 sun kammala taronsu a kasar Canada a ranar jumma’ar da ta gabata inda suka, suka fidda bayanin bayan...
    Saboda haka ne, hukumar ta shawarci manoman da ke da ra’ayin noma a kakar noman ta bana da su tabbatar sun tuntube ta, ko kuma tuntubar sauran hukumomin da ke hasashen yanayi, domin sanin lokacin da ya ya fi dacewa su yi shuka. Hukumar ta yi hasashen cewa, jihohin Zamfara, Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Filato, Bauchi, Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Neja, Kwara, Kogi, Abuja, Ekiti da kuma Ondo, za su fuskanci daukewar ruwan sama da wuri, inda aka kwatanta da na dogon zango da aka samu a daminar bara. Haka zalika, hukumar ta yi hasashen cewa; za a samu jinkirin ruwan sama a wasu sasssan jihohin Kaduna, Nasarawa, Benuwe, Legas, Kwara, Taraba, Oyo, Ogun, Kuros Riba, Delta, Akwa Ibom, Ebonyi,...
    Duk da kokarin da ma’aikatan asibitin suka yi na ceto shi, rahotanni sun ce ya samu raunuka da dama ciki har da guda daya a zuciya. Jaridar Irish Mirror ta ruwaito cewa ‘yansanda suna tsare da Eghomwanre har zuwa lokacin da zai gurfana a gaban alkali Michele Finan a kotun gundumar Dublin. A yayin shari’ar, Garda Grainne Collier ya bayar da rahoton kama Eghomwanre, tuhuma, da kuma taka tsantsan. An ce wanda ake zargin yana fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka hada da cin zarafin Babatunde a titin Anne South, da laifin cin zarafin abokinsa, Adetola Adetuilehin, a layin Duke, da kuma tashin hankali. Alkalin kotun mai shari’a Finan ya ba shi taimakon shari’a, inda aka tsare shi a gidan...
    Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran manjo  janar Salami wanda ya gabatar da jawabi a wurin tunawa da shahid Mahadi Bakiri a garin Tabriz ya bayyana cewa;; Babu yadda za ayi jamhuriyar musulunci ta Iran ta bude tattaunawa da Amurka a karkashin barazana, yana mai kara da cewa; yin gwawarmaya da jajurcewa a gaban masu girman kai da daga hanci, yana daga cikin muhimman koyarwar alkur’ani mai girma da kuma tsarin musulunci. Manjo janar Salami ya kara da cewa; ta hanyar tsayin daka da dunkulewar al’umma wuri daya, za a kai ga samun nasara. Haka nan ya kara da cewa; A tsawon shekaru 46 da su ka gabata, al’ummar Iran ta kasance a cikin fadaka wajen fuskantar duk wata...
    Daga ranar 2 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2024, an gudanar da taron kasa da kasa na “Fahimtar kasar Sin” a birnin Guangzhou. A yayin taron, fiye da baki 600 na kasar Sin da kasashen waje, ciki har da tsohon firaministan kasar Lebanon Hassan Diab, sun hallara don tattaunawa da yin musayar ra’ayi kan taken “Yin gyare-gyare-zamanintarwa irin ta kasar Sin da sabbin damammakin ci gaban duniya”, inda suka samu ra’ayin bai daya na gudanar da hadin gwiwa. A tattaunawar da ya yi da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, Hassan Diab ya bayyana cewa, fahimtar kasar Sin yana da matukar muhimmanci, domin kasar na bude kofarta ga duniya. A cikin...
    Cibiyar da take fitar da amfanin gona zuwa waje ta kasar Rasha, ta sanar da cewa; a cikin shekarar 2024 an sami karuwar kayan abincin da take fitarwa zuwa wasu kasashen Afirka da kaso 19% da kudin da su ka hau da dala biliyan 7. Wasu kasashen da Rashan za ta linka yawan alkamar da take aikewa su ne Moroko, Najeriya da kuma Kamaru. Yawan alkamar da kasar Rashan za ta aike zuwa Moroko ta kai ton 124,000,a 2024 kuwa yawan alkamar da ta aikewa ita ton 54,000. Ita kuwa kasar Najeriya yawan alkamar da Rashan ta aike mata ta tashi daga ton 48,000 zuwa ton 131,400. Alama ce muhimmin kayan abincin da kasar Rasha take aike wa nahiyar Afirka....
    Ma’aikatar harkokin wajen tarayyar Najeriya a Abuja ta musanta zargin da cewa ana kishe kiristoci a kasar. Jaridar Premium timnes ta Najeriya ta nakalto ma’aikatar na fadar haka a jiya Jumma’a ta kuma kara da cewa rahotannin da suka yada wannan karaiyar sun son ingiza gwamnatin Amurka ta dauki Najeriya a cikin jerin kasashen da suke nuna bambanci a cikin mutanen kasashensu. Wanda ba hakaba. A ranar laraban da ta gabata ce kwamiti mai kula da al-amuran Afirka a majalisar dokokin kasar ta bukace gwamnatin Amurka ta dauki mataki a kan Najeriya saboda abinda ya kira kissan kiristoci a Najeriya . Shugaban karamin kwamitin Chris Smith yayi kira ga shugaba Trump ya dorawa Najeriya takunkuman tattalin arziki masu tsanan kan...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye ta bada sanarwan cewa a shirye take da saki fursinonin HKI da Amurka, har ma da gawakin wasu 4, idan HKI ta dawo kan ci gaba da aiwatar da abubuwan da yarjeniyar tsagaita wuta a tsakaninta da HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani Jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Jumma’a. Ya kuma kara da cewa, wasu daga cikin wadanda suke tsakanin kungiyar da HKI ne ya bata wannan shawarar, sannan ya kara da cewa, sai dai wannan matakin yana da sharudda, kuma sune HKI ta amince ta dawo kan tattaunawa marhala ta biyu don aiwatar da yarjeniyar da aka cimma...
    Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya. Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci. A...
    1. Godiya da harshe: Wannan yana nufin yabon Allah da faɗar ni’imominsa da kuma ambatonsa a cikin kalmomi. Wannan yana da muhimmanci saboda yana nuni da cewa mutum ya gane cewa Allah ne mai bayar da ni’ima. Hadisin da aka kawo yana nuna cewa mutum idan ya bayyana ni’imomin Allah, to yana cikin masu godiya. Wannan na iya kasancewa ta hanyar zikirai, du’a’i, da yabonsa da albarkar da yake bayarwa, da cewa Allah Ya yi min ni’ima iri kaza da kaza. 2. Godiya da gaɓɓai: Wannan yana nufin amfani da dukkan gabban jiki wajen yin biyayya ga Allah da nisantar saɓon Sa. Misali, idan mutum yana da lafiyar jiki, to ya yi amfani da lafiyar wajen aikata kyawawan ayyuka kamar...
    Wani jami’in yada labarai na babban yankin kasar Sin ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a amince da duk wani mahaluki ko wata runduna da za ta raba yankin Taiwan da kasar Sin ba, kuma babu yadda za a yi a lamunce da ayyukan “ballewar Taiwan” ta ko wace hanya. Jami’in yada labarun, da ke aiki a ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin, Chen Binhua ya kara da cewa, matukar dakarun ‘yan awaren suka kuskura suka bari tura ta kai bango, za a dauki kwararan matakan mayar da martani a kansu. Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya Yadda Nijeriya Ta Zarce Yawan Man Da OPEC Ta...
    A jawabinsa na godiya a wurin taron, dan majalisar dokokin ya bayyana godiya ga al’ummar Funtuwa, ya ce zai ci gaba da kawo ayyukan alheri tare da abubuwan jin dadin more rayuwar ga al’ummar mazabunsa na Funtuwa da kewayenta gaba daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An tabbatar da mutuwar wata mata da har yanzu ba a bayyana sunan ta ba bayan ta yi tsalle ta faɗa kogin Legas daga gadar Third Mainland a Jihar Legas. Majiyar PUNCH ta ruwaito hakan ne daga wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Juma’a cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 4 na yamma kusa da bakin ruwan kogin da ke hanyar jami’ar Legas. Direba ya murƙushe yarinya ta mutu a artabu da jami’an tsaro a Edo Lakurawa: Gwamnan Kebbi ya nemi a kafa sansanin soji a jihar “Tawagar ’yan sandan ruwa da ke aiki a wurin sun gano ta gaɓar ruwan da ke hanyar jami’ar Legas...
    Sabon kocin Ingila, Thomas Tuchel ya cire ɗan wasan bayan Ingila Harry Maguire cikin jerin ƴanwasan Ingila da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026. Cikin jerin ƴan wasa 26 da sabon kocin ƙasar Thomas Tuchel ya fitar, ranar Juma’a ya sanar da sunan Marcus Rashford bayan cire shi a wasannin baya. Haka ma kocin ya saka sunan tsohon ɗan wasan Liverpool da ke taka leda a ƙugiyar Ajax, Jordan Henderson cikin tawagar. A karon farko mai tsaron ragar Burnley, James Trafford da ɗan wasan bayan Liverpool, Jarell Quansah za su iya samun damar buga wa babbar tawagar Ingila ƙwallo ba a ke cikin tawagar A ranar Juma’a, 21 da watan Maris ne tawagar Ingila...
    Ya ce: “Bari in ce mun tsallake tudu, kuma wahalhalun da aka sha a baya suna raguwa yayin da tasirin waɗannan sauye-sauye suke fara bayyana.   “A halin yanzu, muna gani muraran yadda farashin kayan abinci yake saukowa, farashin musayar kuɗaɗe yake daidaituwa, kuma farashin man fetur yana raguwa. Waɗannan duk alamu ne cewa ayyukan garambawul da ake aiwatarwa suna haifar da sakamako mai kyau.”   Ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da suke da ma’ana ba su zuwa da sauƙi, domin suna buƙatar haƙuri, juriya, da kuma sadaukarwa don cimma cigaba mai ɗorewa.   “Ƙasar mu tana kan wani muhimmin mataki yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake aiwatar da sauye-sauye masu ƙarfi domin gina sabuwar Nijeriya. Tarihi ya...
    Hukumar EFCC ta kama wata mata da mijinta bisa zargin yin sojan gona da sunan mai ɗakin Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Fatima Dikko Radda, wajen damfarar kuɗi Naira miliyan 197.75. An gurfanar da su a gaban babbar kotun Jihar Kaduna, tare da wasu mutum biyu da ake zargi suna taimaka musu wajen aikata laifin. ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Kaduna, sun sace matasa 3 NAJERIYA A YAU: Rashin Aikin Yi Da Hanyoyin Magance Ta A Najeriya EFCC ta ce mutanen huɗu sun haɗa kai wajen amfani da sunan Hajiya Fatima Dikko Radda don samun canjin dala daga wani mai sana’ar canji. Matar ta gabatar da kanta a matsayin Fatima Dikko Radda, tana buƙatar a yi mata canjin dala. Mijinta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi  wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya. Baya ga tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan yankin, na samu wasikar shugaban kasar Amurka. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar. Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako...
    Motocin dai, an bai rundunar soji Uku, yayin da rundunar ‘yansanda ta Mopol ta karbi daya. Kwamandan Barikin Soji na Birnin Kebbi, Manjo A. P. Azubuine, ya bayyana godiyarsa na goyon baya da gwamnatin ke basu wajen yaki da ‘yan ta’adda a fadin jihar.   Shi ma a nasa bangaren, ACP Aliyu Jega, kwamanda Mopol 36 da ke Birnin Kebbi, ya mika godiyarsa ga gwamnan, inda ya kara da cewa, Motar za ta taimaka musu wurin sauke nauyin da ya rataya akansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi akan cewa; Wata sabuwar yunwa za ta  bulla a Gaza saboda yadda HKI take ci gaba da killace yankin da hana shigar da kayan agaji hatta a cikin watan Ramadan. Kakakin kungiyar ta Hamas Abdullatif al-Qa’uni wanda ya fitar da wani bayani ya ce; Falasdinawa a yankin Gaza an killace su, makonni biyu a jere, kuma sojojin mamaya sun hana a shigar da kayan abinci,magunguna, da makamashi, wanda hakan yake a matsayin amfani da yunwa a matsayin makamin. Qa’ani ya kara da cewa; Abinda ‘yan mamaya suke yi, shi ne jefa Falasdinawa cikin yunwa. Haka nan kuma ya ce;  A nan gaba kadan kayakin da ake da su na bukatun yau da...
    Ta ce tallafin zai taimaka wajen bai wa mata damar zama masu dogaro da kansu a fannin tattalin arziƙi. An raba kuɗin ne ga kungiyoyin mata manoma daga ƙananan hukumomi 13 a faɗin jihar, inda kowacce ƙungiya ta samu Naira miliyan biyu. Haka kuma, ƙungiyoyin matasa manoma su ma sun amfana da tallafin don bunƙasa ayyukansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majiyoyi sun bayyana cewa Donald Trump na shirin tattaunawa da Vladimir Putin a cikin makon nan domin ƙara fahimtar juna dangane da wannan shiri. Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, na kira ga ƙasashen Turai da su haɗa kai domin tallafa wa Ukraine wajen tabbatar da tsaron ƙasar bayan wannan tsagaita wuta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa.   Gwamnan, ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje sansanin ‘yan gudun hijira da ke Kangiwa da Lakurawa suka kai musu hari tare da raba su da muhallansu a kauyukan Birnin Debe, Dan Marke da Tambo.   Gwamnan ya ce, ya kai ziyarar ne domin jajanta wa wadanda abin ya shafa tare da ba shi damar samun rahoton halin da ake ciki a kan wannan mummunan...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, tawagar ta Zamfara ta yi hulɗa da kamfanonin Zhong Zhao International Group, Phoenix Wings, Shenzhen HighGreat Innovation Technology Development Co., Ltd, da Xiamen Magnetic North Technology Co., Ltd yayin da suke ƙasar Sin.   Tang Zhangwei, ya jagoranci wasu kamfanoni zuwa jihar Zamfara, domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a sassa masu muhimmanci, domin bunƙasa tattalin arziki.   A nasa jawabin, gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin da kamfanonin ƙasar Sin ke yi na tabbatar da nasarar haɗin gwiwarsu.   “Ina so in yi muku barka da zuwa Jihar Zamfara. Muna maraba da ku. A watan Fabrairu, na jagoranci wata tawaga zuwa ƙasar Sin don ganawa da kamfanoni a sassa daban-daban da kuma gano...
    Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani jami’an gwamnatin kasar UAE ne zai isar da sakon shugaban kasar Amurka Donal Trump zuwa Tehran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghani ya na fadar haka. Ya kuma kara da cewa a halin yanzu mai bawa shugaban kasa shawara na kasar UAE Anwar Gargash yana kan hanyarsa ta zuwa Tehran dauke da wasikar, don isar da ita ga  jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei. Labarin ya kara da cewa Gargash zai hadu da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi da farko bayan isarsa birnin Tehran. Kafin haka dai Majid Takht-Ravanchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran kan al-amuran siyasa, wanda ya je kasar UEA...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
    Mohammad Reza Aref mataimakin shugaban kasa na farko a nan JMI ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba zata karbi umurni daga wata kasa dangane da shirin makamashin nukliya ta zaman lafiya na kasar ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Aref yana fadar haka a jiya Talata, ya kuma kara da cewa, JMI ta na ci gaba da jajircewa da takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma suka dora mata, dangane da shirin kasar na amfani da fasahar Nukliya. Sai dai har yanzun ba zata nemi shawara ko karbi umurni daga wata kasa a kan amfani da wannan fasaha mai dimbin amfani ba. Mataimakin shugaban kasar ya ce, sinadarin Nukliya ya na da matukar amfani kuma...
    Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta fitar da sunayen kamfanonin jiragen sama da za su yi jigilar Alhazan bana. Bayanin ya ƙunshi sunayen jiragen da kuma adadin mahajjatan da aka ware wa kowannensu. Kamfanin Fly Nas zai yi jigilar Alhazai 22,893, kashi 32.12 bisa dari kenan na maniyyatan Najeriya a bana, yayin da Kamfanin Air peace ya sami Alhazai  9,145 , kashi 12.83. Sauran su ne Max Air Ltd da aka warewa Alhazai 23,343, kashin 32.75 kenan bisa dari, sai kamfanin Umza Air Ltd an ware  da ya sami 15,893 wato kashi 22.30 bisa 100, wanda ya kawo adadin maniyyata 71,274 da ake sa ran za su sauke farali a bana. Hukumar ta NAHCON ta ce za a fara jigilar...
    Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
    Duk da raguwar hare-haren da kashi 2.19 idan aka kwatanta da Janairu, har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da zama barazana ga al’umma a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10. Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu. Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari. Wani ganau da ya buƙaci a sakaya...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta soki kalaman sakataren baitul-malin Amurka da ya bayyana dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu a matsayin zamba. An shafe gomman shekaru ana huldar cinikayya tsakanin bangarorin biyu, a gani na, idan har akwai zamba a ciki, ba na jin huldar za ta kawo matakin da take kai a yanzu. Abun da Amurka ta kasa ganewa shi ne, ita kanta da sauran duniya sun fi bukatar Sin. Idan Amurka ta ci gaba da ta da yakin cinikayya, sai ta fi kowa dandana radadin matakanta, la’akari da yadda kayayyakin kasar Sin suka bunkasa sayayya a kasar. Kana masana sun yi hasashen munanan matakan, za su haifar da raguwar GDPnta da hauhawar farashin kayayyaki da rashin...
    Majalisar Wakilai ta bai wa Hukumar Sadarwa ta NCC umarnin rufe duk wasu shafukan intanet masu nuna batsa a Nijeriya. Majalisar ta ba da wannan umarni yayin zamanta na yau Talata, inda ta nemi hukumar sadarwar ta umarci duk kamfanonin da ke samar da intanet su rufe duk wasu shafukan intanet da ke nuna hotuna ko bidiyon batsa cikin gaggawa. Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi Wannan umarni na zuwa ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa daga Jihar Katsina, Dalhatu Shehu Tafoki, ya gabatar. Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Nijeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar...
    Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba.   Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin su fuskanci hukunci.   Idan ba a manta ba a kwanaki kaɗan da suka wuce gwamnatin Jihar Filato, ta sanar da sanya haramci kan harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar saboda...
    Tare da cewa Rasha ta sanar da kakkabo jiragen sama marasa matuki fiye da 60 da Ukiraniya ta harba, sai dai an sanar da mutuwar mutum daya a birnin Moscow. Kantoman yankin Moscow  Andrey Vorobyov ne ya sanar da cewa mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu 3 su ka jikkata, sanadiyyar hare-haren da Ukiraniya ta kai wa birnin da makamai masu linzami masu yawa da safiyar yau Talata. Kantoman Mascow ya rubuta a shafinsa na “Telegram’ cewa; “ ya zuwa yanzu an sami labarin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu 3 a garin Fidnoveh a kudancin Moscow.” Sai dai daga baya wasu kafafen watsa labarun Rasha sun ambaci cewa adadin wadanda su ka jikkata din ya karu...
    Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ambaci cewa kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shugaban gwamnatin Syria, Julani sun fara dauke gawawwakin mutanen da su ka yi wa kisan kiyashi zuwa wasu wurare da ba a san ko’ina ne ba. Saboda yadda fushin kasashen duniya yake karuwa akan kisan kiyashin da ‘yan ta’adda su ka yi a gabar ruwan Syria, masu mulki a Damascuss suna boye gawawwakin gabanin isar tawagar MDD zuwa yankin. Mafi yawancin mutanen da aka yi wa kisan gillar a yankin gabar ruwan Syria, fararen hula ne wadanda aka fito da su daga cikin gidajensu,yayin da wasu kuma aka yi musu kisan gilla a gaban iyalansu. Ya zuwa shekaran jiya ana maganar cewa an...
    Duk da haka, kungiyar za ta ci gaba da amfani da Old Trafford har sai an kammala sabon filin wasan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Haka kuma, an bukaci su riƙa shan isasshen ruwa, amfani da fanka ko na’urar sanyaya ɗaki, da kuma zama a wurare masu inuwa don kaucewa illar zafi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mayar da hankali kan taruka biyu na kasar Sin, wato taron majalisar wakilan jama’ar kasar (NPC) da kuma taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar (CPPCC), muhimmin abu ne ga manyan shugabannin kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin. Zuwa karshen shekara ta 2024, adadin kamfanonin da baki ’yan kasashen waje suka zuba jari don kafa su a kasar Sin, ya zarce miliyan 1.239. A matsayinsu na wadanda ke gane wa idanunsu, da wadanda ke bayar da gudummawa, gami da wadanda ke cin moriya, daga harkokin yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje na kasar Sin, kamfanonin jarin waje sun riga sun bada hadin-kai tare da samun ci gaba tare da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. A...
    Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha. Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018,...
    Tawagar matasan yan wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta mata (Flamingos) ta yi nasarar doke mai masaukin baƙi Bantwana ta Afrika ta Kudu da ci 3-1 a wasan farko na gasar cin kofin duniya na mata ‘yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025 a filin wasa na Lucas Moripe, Pretoria a ranar Asabar, in ji jaridar Prompt News. Shakirat Moshood ce ta jefa wa Nijeriya ƙwallon farko a wasan cikin mintuna 20 kacal da farawa, Harmony Chidi ta ninka damar da Nijeriya ke da ita daga bugun fanareti mintuna biyar kafin a tafi hutun rabin lokaci. Cinikayyar ‘Yan Kwallon Da Aka Yi A Watan Janairu Hadin Gwiwar Sin Da Nijeriya Za Ta Ba Mata Damar Cimma Burikansu Afrika ta...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa, gwagwarmayar al’ummar kasar Lebanon na nan da karfinta, duk da asarorin da ta yi da kuma sadaukarwa. A wata hira da yayi da tashar talabijin ta Al Manar, Sheikh Qassem ya bayyana cewa, ‘yan gwagwarmaya a kasar Lebanon sun yi nasarar cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta kawo karshen hare-haren da Isra’ila a lokacin da suke kara jajircewa. Ya jaddada cewa “a koyaushe ana ci gaba da tuntubar juna tsakaninsu da shugaban majalisar Nabih Berri, kuma ba mu yi wata tattaunawa a cikin rauni ba.” Sheikh Qassem ya tabbatar da cewa, muddin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ci gaba da mamayar yankunan Lebanon, to dole ne a tunkare ta ta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumi lokaci ne da akan samu wasu ma’aikatu sun sassauta wa ma’aikata ta hanyar yi musu rangwame kamar rage musu yawan sa’o’in aiki. Sai dai a lokacin da waɗannan mutane suke samun rangwame, akwai waɗanda suke ayyuka ko sana’o’in da suka dogara da su ciyar da iyalansu. Sau da dama irin waɗannan mutane sai sun fita sun yi aiki a rana, duk da suna azumi, suke samun abin da za su saka a bakin salati. NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin ladan da masu aikin...
    Shehun malami al-Imam Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama, ya bayyana cewa babban dalilin da ya sa Alƙur’ani ya sauka shi ne kira ga bautar Allah da shiga cikin addininsa. Wannan magana tana da tushen ilimi mai zurfi wanda ke da nasaba da tauhidi da shari’a, da hikimar shiriya. 1. Tauhidi a Matsayin Asalin Kiran Alƙur’ani: Manufar farko da Alƙur’ani ya zo da ita; ita ce tabbatar da tauhidi, wato bautar Allah Shi kaɗai ba tare da sanya masa abokin tarayyaba. Wannan ita ce mafi girman sako da dukan annabawa suka zo da shi. Allah ya ce: “Kuma babu wani Manzo da Muka aiko a gabaninka face sai Mun yi masa wahayi cewa: Lallai babu abin bautawa da gaskiya...
    Wani mutum wanda yake nuna kin amincewa da zaluncin da HKI yake yi wa mutanen Gaza, ya hau kan hausumiyar agogon “ Big-Bang”   a birnin London dauke da tutar Falasdinu. An sami cunkuson motoci a yankin Westminster dake birnin London a jiya Asabar,yayin da masu ceto suke kokarin isa ga mutumin domin sauko da shi daga kan hausmiyar agogon. Jami’an ‘yan sandan sun sanar da samin rahoton abinda ya faru da misalin karfe 7 na safe,kuma sun fara aiki domin ganin an sauko da mutumin cikin lafiya. Jami’an tsaro sun sanar da cewa an rufe hanyar da take zuwa majalisar saboda abinda ya faru. Haka nan kuma gadar da take zuwa Wesminster  da sauran hanyoyin da suke yankin duk an...
    Tashar talbijin din ‘almayadin’ mai watsa shirye-shirye daga Lebanon ta ambaci cewa; Wasu kauyuka na mabiya mazhabar Alawiyya dake Tartus, da kuma Lazikiyya, sun fuskanci hare-hare daga masu dauke da makamai. A yau Lahadi, masu dauke da makaman sun kutsa cikin wasu kauyukan Ramilah, Naq’a dake kusa da Jabalah. Daga jiya zuwa yau masu dauke da makaman sun yi kisan kiyashi a wurare  fiye da 10. Majiyar Almayadin ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda aka kashe bisa bangaranci sun kai 1000. Sai dai kuma tshohon mai bai wa shugaban majalisar ‘yan Alawiyya shawara Muhammad Nasir, ya ce, adadin wadanda aka kashe din sun kai 1,700. Hare-haren sun hada da kona kauyuka 6 a yankin gabar ruwan Midtreniya na kasar...
    A wajen Arteta, wasan na ranar Lahadi a gidan Manchester United ba kawai wasa ne na samun maki uku ba, har ma game da bikinshi na wasa 200 a matsayin kocin Arsenal a gasar Firimiya, kocin dan kasar Sifaniya zai shiga cikin jerin jiga-jigan masu horarwa da su ka samu wannan nasara, inda ya zama na 13 kacal da ya yi hakan da kulob guda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kuturta zuwa Najeriya. Wannan dai na zuwa ne bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwajen da hukumar ke gudanarwa, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba. Kakakin hukumar ta WHO ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewar, an samu ƙarancin maganin cutar ta kuturta a Nijeriya. Ya ce hukumar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta miƙa buƙatar ganin an samu izinin shigar da maganin cikin ƙasar akan lokaci, kuma a watan Janairu aka amince da hakan. Nijeriya wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi yawan jama’a na bayar da...
    Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi. “A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan...
    Minnaro kafin mutuwarshi shi ne babban likitan kungiyar ta Barcelona, kungiyar ta fitar da sanarwar mutuwarshi ana dab da fara wasan, hakan ne ya sa aka dakatar da wasan domin nuna girmamawa gareshi da kuma jajantawa yan uwa da abokan arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari da Iran na yi ne don neman amfanin kansu. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan jami’ai na bangarori uku na gwamnati a ranar Asabar. Jagoran ya ce “Dagewar da wasu gwamnatoci suka yi kan yin shawarwari ba wai don warware al’amura ba ne, a’a yana nufin aiwatar da abin da suke so.” Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: ” Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da abin da suke tsammani ba.” Wadannan gwamnatocin da suke cin zalin ba sa neman yin shawarwari kan batun nukiliya...
    Senegal ta karbi wasu sansanonin soja na faransa a kasar a wani bangare na janye sojojin faransar daga kasar ta Yammacin Afirka. Ofishin jakadancin Faransa a Dakar ya sanar da cewa an mika wurare da gidaje a yankunan Marechal da Saint-Exupery na Dakar ga hannun gwamnatin Senegal. Sauran kuma “za a mika su ne kamar yadda bangarorin biyu suka amince da jadawalin da suka sanya wa hannu”. A ranar 12 ga Fabrairu Faransa ta sanar cewa ta kafa wani kwamiti na hadin gwiwa da Senegal da zai shirya tsare-tsaren ficewar sojojin Faransa da kuma mika sansanonin zuwa karshen shekarar nan.  “Kwamitin ya kuma kaddamar da aikin yin garen-bawul ga hadakar tsaro,” a cewar sanarwar. A watan Nuwamban 2024 ne Shugaba...
    Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna: Muhimmancin sadaka na da yawa baya ga kariya da take yi, sadaka tana hana bambancin da ake yi tsakanin mai kudi da kuma talaka, sadaka tana hada kan al’umma musulmi guri daya, tana taimakawa marayu, masu takaba da manya wadanda suka manyanta wajen nuna musu cewar suma suna da gata, tana kuma kusanto mutum da Allah ta’alla. Wadanda ya kamata a bawa sadaka; Marayu, iyalai masu karamin karfi, masu takaba, ‘yan gudun hijra, dalibai da sauransu. Hanyoyin bada sadaka na da dumbin yawa kamar; bada sadaka ta hanyar bada kudi, yinta ta hanyar dauke abu daga kan hanya wanda zai cutar da dan’Adam, hada kungiya ko kirkirar kungiya ko bada gudunmawa a kungiyar...
    SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1 BUƊA-BAKI [Falalarsa Da Lokacinsa] Na 1 Sharhi: Shehun malami Ibnu Juzai (Allah ya yi masa rahama) yana bayani a nan game da ma’anar Tafsiri, wanda ke nufin fassara da ƙarin bayani kan ma’anonin ayoyin Alƙur’ani. A bisa wannan magana, ana iya fahimtar cewa: 1. Tafsiri yana nufin bayani da sharhi na Alƙur’ani – Wato fassara da bayanin ma’anar ayoyi domin su fi zama a fili ga masu karatu da sauraro, don su fahimci saƙon da ke cikinsu. 2. Tafsiri yana bayyana ma’anar ayoyi dalla-dalla – Manufarsa ita ce kawar da ruɗani da kuma hana kuskuren fahimta. 3. Hanyoyin bayani a tafsiri suna da matakai daban-daban: Ta lafazin ayar kai tsaye (بِنَصِّهِ) – Wato bayani...
    A yau Asabar ne aka gudanar da zama na biyu na taro na uku, na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. Zaman da babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping ya halarta. Albarkacin kasancewar yau ranar bikin mata ta kasa da kasa, a madadin tawagar shugabannin taron, zaman ya mika fatan alheri ga mata daga dukkan kabilu, da dukkan bangarorin kasar Sin, da mata na dukkan kasashen duniya. Bugu da kari, rahoton ayyukan zaunannen kwamitin NPC ya nuna cewa, ana shirin bitar dokoki 34 a shekarar nan ta 2025, wadanda suka hada da samar da wata doka, don inganta hadin...
    Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi Khaminae wasika, inda a ciki yake kiransa zuwa tattaunawa da Amurkan a kan shirin makamashin Nukliyar kasar Iran. Har’ila yau shugaban ya bayyana haka wa tashar talabijin ta Fox news. Iran dai ba ta son tattaunawa kai tsaye da Amurka saboda rashin gaskiya a cikin al-amuransu. Musamman shi Donal Trump, sabo da shine ya fidda kasarsa daga yarjeniyar JCPOA tun farko sannan ya dage sai...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta sanar a Asabar din nan cewa, za ta kara haraji kar kaso 100 kan wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga Canada, bayan da ta kammala bincike kan batun nuna banbanci a hada-hadar cinikayya. Harajin zai fara aiki ne tun daga ranar 20 ga watan nan na Maris, zai kuma kunshi karin kaso 100 bisa mai rapeseed, da tunkuza, da waken peas, yayin da kuma albarkatun teku, da naman alade da ake shigarwa Sin daga Canada, aka yi musu karin harajin kaso 25 bisa dari. Mahukuntan kasar Sin sun ce matakin ya biyo bayan binciken da aka gudanar game da nuna banbanci a hada-hadar cinikayya, wanda ya tabbatar da cewa, matakan da...
    “Wasu masu kiwon, suna zuwa shagunan sayar da magani ne su sayo su rika bai wa dabbobin da suka harbu da wata kwayar cuta, ba tare da yin la’akari kan adadin magungunan da ya kamata su ba su ba”, in ji Ngulukun. Ana kuma bukatar masu kiwon su dakar da bai wa dabbonin nasu magunguna daidai da lokacin da misali, kajin gidan gona ke shirin fara yin kwai ko kuma lokacin da shanu ke shirin fara samar da madara, domin kare lafiyar mutane. Sai dai, abin takaici shi ne, akasarin masu kiwon; ba sa kiyaye irin wadannan lokuta, wanda hakan ke shafar lafiyar mutanen da suka yi amfani da irin wadannan dabbobi. Kazalika, yawan bai wa dabbobin magungunan barkatai don...
    Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, a safiyar ranar Juma’a sojojin gwamnatin Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu masallatai shida na birnin Nablus, inda suka hana gudanar da salla. Har ila yau, sun kame wasu Falasdinawa uku a lokacin da suke kutsawa cikin Nablus. Rahotanni sun ce sojojin na Isra’ila sun harba harsasai masu rai, da gurneti da bama-bamai masu guba a yayin da dakarunsu suka mamaye wasu unguwanni a birnin. Ko a ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ci...
    “Bisa ga ajandar sabunta fata na Shugaba Tinubu, mun himmatu wajen tabbatar da manufofi da ka’idojin da suka jagoranci hukumar tsawon shekaru. “Ina kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya, musamman maniyyatan da suka yi niyyar zuwa aikin hajjin 2025, za su gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da NAHCON bisa sakamakon aikin hajjin 2025. “Shugaban kasa yana tsayawa kan Magana daya. Yana ba mu dukkan goyon bayan da ya kamata. Ba za mu ci amanarsa ba. Ba za mu sauka daga kan manufarmu ba. “A kan wannan, dole ne mu gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima bisa yadda suka ba mu amanar tafiyar da harkokin aikin hajji. “Hukumar ta samu wasu nasarorin da suka shahara...
    Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila. A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da  Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba...
    Rundunar hadaka ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun yi nasarar hallaka  wani kasurgumin jigon kungiyar Lakurawa da aka fi sani da  Maigemu a jihar Kebbi. Sanarwar da Daraktan Tsaron, Alhaji AbdulRahman Usman Zagga, ya fitar, ta ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan musayar wuta da jami’an tsoro. Sanarwar ta ce, wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a yankin karamar Hukumar Arewa, domin jajantawa al’ummar yankin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa ne suka yi. An bayyana cewa, matakin da gwamnan jihar ya dauka kan...