2025-04-03@11:29:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 562
«Wannan saboda»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ministan ya bayar da jerin sabbin jami’o’in da suka hada da jami’ar New City, Ayetoro, a Jihar Ogun, jami’ar Fortune, Igbotako, a Jihar Ondo, jami’ar Eranoba, Mabushi, jami’ar Minaret, Ikirun, Osun Anned, jami’ar Abubakar Toyin, Oke-Agba, a Jihar Kwara da kuma jami’ar Southern Atlantic, Uyo, a Jihar Akwa Ibom. Sauran su ne jami’ar Lens, Ilemona a Jihar Kwara, jami’ar Monarch, Iyesi-Ota, Jihar Ogun, jami’ar Tonnie Iredia da za ta koyar da ilimin sadarwa a birnin Benin, jami’ar Isaac Balami Aeronautics and Management, a Jihar Lagos da kuma jami’ar Kebin Eze Mgbowo, ta Jihar Inugu. A cewar Alausa, Shugaban kasa Bola Tinubu ya himmatu wajen kyautata harkokin ilimi da kyautata gine-gine a bangaren ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Hukumar da take yaki da yi wa tattalin arzikin kasar Najeriya zagon kasa, ta yi wa tsohuwar ministar harkokin mata Uju Kennedy,tambayoyi masu alaka da zargin da ake yi mata akan aikata ba daidai ba, da kuma karkatar da wasu kudade da sun kai Naira miliyan 138.4 a karkashin kasafin kudin ma’aikatar tata a 2023. Da safiyar jiya Alhamis da misali 11: na safe ne tsohuwar ministar ta isa babbar shalkwarar hukumar ta EFCC dake birnin Abuja,inda ta amsa tambayoyin da aka yi mata. Majiyar hukumar ta EFCC ta ce da akwai wasu kudade da aka bai wa ma’aikatar a karkashin shirin nan na p-Bat cares, amma sai aka karkata su zuwa asusun tsohuwar ministar. Uju tana cikin minsitocin da ...
Wani mutum mai shekara 52, Salihu Byezhe, ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake Sallar Asuba a wani masallaci da ke ƙauyen Gudaba, a Ƙaramar Hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya, kuma daga baya ya rasu a asibiti. Wani mazaunin yankin, Musa Dantani, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis bayan Byezhe ya yi sahur, ya yi alwala, sannan ya shiga masallaci don yin Sallar Asuba. Majalisar wakilai na shirin ƙwace rajistar jam’iyyu daga hannun INEC NAJERIYA A YAU: Falalar Buɗa-baki Cikin Iyali A Lokacin Azumi “Yayin da ake cikin sallah, kwatsam sai ya yanke jiki, nan take wasu daga cikin masu sallah suka riƙe shi suka kuma gaggauta kai shi asibiti. “Lokacin da suke kan hanyar...

Wang Yi: Diflomasiyyar Kasar Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankalin Da Ake Bukata A Duniya Mai Cike Da Rikici
Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu. Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba. Yana cewa, tu’ammali da maganin Fentanyl a Amurka, matsala ce da ya kamata kasar ta warware da kanta. Ya kara da cewa, ba zai yiwu a yi tunanin za a danne kasar Sin, sannan kuma a ci...
Alkalin kotun ya umarci a kwace kuɗin tare da mika su ga gwamnatin tarayya, bisa tanadin dokar hana safarar kuɗaɗe ta shekarar 2022. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Yansanda A Najeriya Sun Kama Yan Kasar Pakistan Biyu Da Hakanni Wajen Sake Yan Kasashen Waje A Kasar
Yansanda a birnin Lagos na kudancin kasar sun kama wasu yan kasar Pakistan biyu wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin aikin kamawa don neman kudaden fansa daga hannun wani dan kasar ta Pakistan dan shekara 48 a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran sun nakalto daga kafafen yada labaran kasar wadanda suka ji kakakin yansan na jihar Lagos Chief Superintendent Benjamin Hundeyin yana cewa, yan kasar Pakisatn da suka kama a wani dauki da suka wanda aka sace don neman kudaden fansa sun kama a ranar 5 ga watan maris akwia Roman Gull dan shekara 19 da kuma Aftab Ahmed dan shekarera 28 a duniya kuma yan asalin kasar Pakistan ne, wadanda suka hada kansu da wasu...
Jinkirta Sahur Da Gaggauta Buda-baki An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa”, ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi. An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya kara yarda da shi ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Mutane ba za su gushe ba cikin alkairi muddin sun gaggauta yin buda-baki” Ma’anar wannan hadisi, sabida Allah ya fada cikin Alkur’ani “summa atimmus siyama ilallai – sannan ku cika azumi zuwa dare” sai Annabi ya koya mana sunnarshi zuwa dai-dai lokacin da ya dace na buda-bakin (ba cikin dare Allah yake nufi ba),...
Gwamnatin Syria ta ayyana dokar ta-baci a yankuna da dama na kasar bayan da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnatin kasar ke kara murkushe fararen hula. An sanya dokar ta-baci a birnin Tartus da ke arewa maso yammacin kasar da kuma daukacin lardin Homs a daren Alhamis. An kuma sanar da dokar hana fita a Latakia har zuwa karfe 10:00 na safe agogon kasar ranar Juma’a. Dokar hana fita ta biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Alawiyyawa da mabiya Shi’a suka yi, wadanda suka yi Allah wadai da ta’addancin gwamnatin. Sun zargi gwamnatin rikon kwarya ta Syria da fifita mulki kan sake gina al’ummar kasar. Majalisar koli ta addinin musulunci ta Alawite a kasar Syria ta fitar da...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran ta yi watsi da zarge-zargen da jami’an Birtaniya suka yi na cewa Tehran na barazana ga tsaron kasar ta Burtaniya. A cewar jami’an Iran, Ingila na zargin Iran da wani abu da ta yi fice a kai. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya mayar da martani da kakkausan lafazi kan wannan zargi, yana mai cewa wannan maganar banza ce. A cikin wani sako da ya wallafa a shafin X, ya tunatar da cewa ita kanta kasar Birtaniya kwarariya ce wajen tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe. A kwanakin baya ne sakataren tsaron Burtaniya Dan Jarvis ya gabatar da shawarar a gaban majalisar dokokin kasar cewa za a kara sa ido kan gwamnatin...

Nijeriya Za Ta Fara Aiwatar Da Yarjejeniyoyin Haɗin Gwiwa Da Kafofin Watsa Labarai Na Sin – Ministan Yaɗa Labarai
Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan. “NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da tashoshi sama da ɗari a faɗin ƙasar nan, tana isar da shirye-shiryen ta ga sama da mutane miliyan 200. “Hakan ya sa muke da buƙatar amfani da wannan haɗin gwiwa don musayar bayanai da fasaha, tare da amfana da juna.” Ministan ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun haɗa da musayar bayanai, shirye-shirye, da fasaha domin inganta ayyukan gidajen watsa labarai na Nijeriya tare da...
“Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne. Kasancewar Hafsan Sojin Sama a Zamfara na nuna ƙwarewa da kulawa ta musamman. Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da...
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar. Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar Jigawa. AIG Ammani ya yaba da dimbin tallafin da Gwamna Namadi ke bai wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar. Ya bayyana jihar Jigawa a matsayin daya daga cikin jihohin kasar nan masu zaman lafiya. A cewarsa, tun da ya samu mukamin AIG mai kula da shiyya ta 1, bai taba samun rahoton manyan laifuka daga...
Don haka, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda saba ka’idojinta na majalisar dattawa. Bugu da kari, majalisar ta bukaci Natasha da ta maido da duk wani abu mallakin majalisar ga mai kula da Majalisar har sai lokacin dakatarwar ya cika. Sanata Imasuen ya bayyana cewa, “A madadin kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata, da kuma sauraron kararrakin jama’a, muna godiya ga shugaban kasa da manyan abokan aikinmu bisa damar da aka ba mu na yi wa ‘yan Nijeriya hidima ta hanyar wannan kwamiti. Mun gabatar da shawarwarinmu cikin girmamawa don tantancewa da amincewa. Na gode.” Bayan doguwar muhawara kan rahoton da kwamitin ya gabatar, Sanatocin sun amince da dukkan shawarwarin...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya bai wa manema labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, matakin na zuwa ne bayan wani kwakkwaran bincike da kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Bello Abdulkadir Fanini ya gudanar. “Rahoton kwamitin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Bashir Kazaure, biyo bayan sanarwar batun biyan mafi karancin albashi...
Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, na tsawon watanni shida. Wannan hukunci ya biyo bayan amincewa da rahoton Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na Majalisar, wanda ya bincike ta kan zargin karya dokokin majalisar. Tsarin Sufuri: Gwamnatin Kano da kamfanin Stata sun ƙulla yarjejeniya Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Natasha na wata 6 Sanata Natasha ta ƙi bayyana a gaban kwamitin a ranar Laraba, duk da gayyatar da aka yi mata domin ta kare kanta. A sakamakon haka, majalisar ta yanke hukuncin dakatar da ita har na tsawon watanni shida. ’Yar majalisar ta shiga takun saƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan rabon kujeru a zauren majalisar. Haka kuma, Natasha ta zargi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin sun kuma ƙwato makamai masu yawa. Bayan artabun, Boko Haram sun yi yunƙurin kai farmakin ramuwar gayya ta hanyar birne bama-bamai a hanyoyin da sojojin za su bi. Sai dai dakarun sun gano sama da guda 10 daga cikin abubuwan fashewar kuma sun tarwatsa su, wanda hakan ya hana aukuwar asarar rayuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A wani yunkuri na bunkasa sana’o’in hannu da kuma karfafa wa masu bukata ta musamman, wata kungiya mai zaman kanta mai suna Women Farmers Advancement Network (WOFAN) ta kaddamar da wata cibiyar kasuwanci ta mata masu sarrafa kayayyaki tare da baiwa masu bukatar su 450 a yankin Karfi. Wannan yunƙurin na da nufin ƙarfafa su 450 da kayan aikin farawa, wanda zai ba su damar yin aiki mai daraja da riba. Da take jawabi a wajen taron, Daraktar Hukumar WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba, wadda ta samu wakilcin jami’in kula da ofishin na Kano, Alhaji Dayyabu Abubakar, ta jaddada cewa cibiyar kasuwanci za ta baiwa mata damar kula da harkokin kasuwancinsu da kuma amfani da dabarun tattaunawa da suka samu ta...
Kwamandan runduna ta 6 ta sojan Nijeriya a jihar Taraba, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya karbi bakuncin mahalarta kwas din Cibiyar Bayar da Agaji ta Sojojin Najeriya (NARC) karo na 7/2025 a wani rangadin karatu a jihar Taraba a hedkwatar rundunar dake Jalingo. A yayin ziyarar, Janar Uwa ya yi wa mahalarta taron karin haske kan ayyukan gudanar da aiki, nasarori, kalubale, da hasashen da za a yi a nan gaba, inda ya bayyana muhimman nasarorin da aka samu wajen yaki da rashin tsaro a cikin shekarar da ta gabata. Ya yi nuni da cewa al’amuran satar mutane don neman kudin fansa, fashi da makami, da kuma rikicin kabilanci ya ragu matuka saboda jajircewar sojojin. A...
Hukumar LASEMA ta bayyana cewa tawagarta ta fara aikin ceto da bincike tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin agaji. Haka kuma, an tura manyan motocin tono ƙasa don taimakawa wajen share baraguzan ginin da kuma ceto duk wanda ya maƙale a ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Wata Kotu A Iran Ta Ci Taran Gwamnatin Amurka Dala Biliyon $12.6 Saboda Haddasa Mutuwar Masu Fama Da Cutar ‘thalassemia’ A Kasar
Wata koto a nan Tehran ta ci gwamnatin Amurka taran dalar Amurka biliyon $12.6 saboda hana wadanda suke fama da cutar ‘Talamessia” a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA ta shirin Nukliyar kasar sannan ta dorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, wanda ya hada da magungunan cutar Talassemia. Labarin ya kara da cewa Kotu mai lamba 55 wanda yake kula da kararraki na kasa da kasa a jiya Laraba ta yanke hukun kan wasu jami’an gwamnatin Amurka wadanda suke da hannun kasi tsaye na wajen dorawa kasar takunkuman tattalin arziki har da magungun wannan cutar. Kafin haka dai masu fama da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A gefe guda, Akpabio ya musanta duk zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da Majalisar Dattawa ta tura Akpoti-Uduaghan zuwa kwamitin ladabtarwa saboda taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Shugaban Majalisar kan batun sauya wajen zama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar leken asiri ta gwamnatin Isra’ila (Shin Bet) ta amince da gazawarta wajen hana harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Talata, shugaban hukumar ta Shin Bet, Ronen Bar, ya amince da cewa, hukumar ta ” gaza a cikin aikinta” na dakile ayyukan Operation Al-Aqsa, tare da kutsawa manyan sansanonin Isra’ila bayan da sojoji da ‘yan sandan gwamnatin suka yi kaca-kaca da su. Ya ce, da hukumar ta Shin Bet ta yi wani abu daban a cikin shekarun da suka gabata kafin harin da kuma a daren da aka kai harin… da an kaucewa hakan. “A matsayina na shugaban hukumar, zan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance. Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar. Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.” Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta. Martanin Akpabio Sanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin. Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi. Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin...

Taron Kasashen Turai Don Goyon Baya Ga Kasar Ukraine, Ya Watse Ba Tare Da Tsaida Irin Taimakon Da Zasu Yi Mata Ba
Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman kan yadda ya dage wajen kare kasarsa da kasashen Turai a gaban Donal Trum a ranar Jumma’an da ta gabata, ya waste ba tare da kasashen sun bayyana abinda zasu iya yiwa Ita Ukraine a yakin da take ci gaba da fafatawa da Rasha ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa matsalolin da suka taso dangane da dogaron da kasashen turai suke yi kan kungiyar Tsaro ta NATO yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka tattauna. Yakin cacarbakin da shugaba Trump na Amurka yayi da shugaban kasar Ukraine ya zama masomin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da ƙalubale – ba don sun shirya mishi ba kuma ba don sun gaza shiryawa ba. Wani rukunin waɗannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana. Domin sauke shirin, latsa nan
A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu. Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin. Su kuwa sojojin HKI sun sanar da kai hari ne akan wani rumbun makamai dake yankin “Kardaha’. Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na HKI su ka kai hari a garin Tartus ba, a ranar 16 ga watan Disamba ba sun kai wannan irin harin.
Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja. Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa; “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa...
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin nasa, Macron ya ba da shawarar cewa kasashen Turai su kara yawan kudaden da suke kashewa a fannin tsaro da kashi 3 zuwa 3.5 na GDP don mayar da martani ga canje-canjen abubuwan da Washington ta sa a gaba. “Tsawon shekaru uku, Rashawa suna kashe kashi 10% na GDPn su a fannin tsaro; Don haka dole ne mu shirya don abin da ke gaba. »
Kamfanin gungun gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, zai watsa bikin bude zama na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC karo na 14 a gobe Talata 4 ga watan nan. Za a bude taron ne da karfe 3 na rana bisa agogon Beijing. Kuma shugaban majalisar ta CPPCC Wang Huning, zai mika rahoton aikin zaunannen kwamitin koli na majalissar CPPCC. Kazalika a yayin zaman, kafofin rediyo da na talabijin daban daban dake karkashin CMG, za su gudanar da shirye-shirye kai tsaye, kana su ma sabbin kafofin sadarwa na zamani za su shiga a dama da su a wannan aiki. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025 a hukumance, da nufin samar da abincin buda baki ga mabukata 91,000 a fadin jihar. Shirin wanda zai dauki tsawon kwanaki 27 yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa dimbin al’ummarta a watan na Ramadan. Mataimakin gwamnan jihar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda kuma shi ne shugaban shirin, ya kaddamar da shirin a hukumance a cibiyar Dandali dake karamar hukumar Fagge. Ya nuna jin dadinsa da yadda aka gudanar da shirin cikin kwanciyar hankali, tare da yin kira ga kamfanonin da abin ya shafa da su tabbatar da isar da abinci cikin lokaci da inganci a dukkanin cibiyoyin ciyar da abincin. Za...
Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa. Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa. A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘ba zamu tsawaita kashi na farko na yarjeniyar ba, haka ma ba za mu amince da gabatar da sauye –sauye a cikin yarjeniyar ba. Mardawi yace HKI za ta karbi fursinonin da suka rage a hannun Hamas kadai ne, ta hanyar ko tsarin da yarjeniyar ta amince da shi. Ya ce: Benyamin Natanyahu yana, cikin dimwa...
Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu binciken na cewa sun samar da wani sinadari wanda baya sanya ‘magnesium Alloy’ a jikin jiragen sama tsatsa, kuma idan an rufe jikin jirgi da shi zai rage nauyinsa. Banda haka zai kyautata yanda jirage zasu sarrafa makamashin jirgin. Rahoton ya kara da cewa wannan kirkirar ya na da muhimmanci a kamfanonin kera jiragen sama, da kuma samar da injuna, saboda zai kara dadewar jikin jiragen sama, kafin yayi tsatsa. Har’ila yau ya kuma taimaka wajen rage nauyin jikin jirgin. Banda haka sabon...
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a ci gaba da yaki. Sergey Lavro ya kuma ce; tunanin aikewa da dakarun zaman lafiya zuwa Ukiraniya wauta ce. Lavrov ya bayyana shugaban kasar Ukiraniya Zelenskiy da cewa dan Nazi ne, wanda ya ha’inci al’ummarsa.”
Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar. Walid Junbilat wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma bakin Isra’ila a cikin harkokin wannan yankin, musamman abinda yae faruwa a kudancin Syria. Dan siyasar na kasar Lebanon wanda ya yi taron manema labaru a jiya Lahadi ya yi gargadi akan yanayin da ake ciki a yankin “Jabalu-Duruz” da tsoma bakin HKI domin haddasa rashin tsaro a cikin wannan yankin. Haka nan kuma ya yi tuni da yabo akan tarihin gwgawarmayar ‘yan Duruz’ da...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya. Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan, da kuma lokacin da ya kamata a yi Magana da su, ko kuma lokacin da ya kamata a zare musu takobi.” Dukkanin wadannan bayanan suna cikin al’kur’ani mai girma. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karatun alkur’ani mai girma, a jiya Lahadi da dare, ya yi ishara da cutukan ruhi da su ka addabi bil’adama a wannan zamanin da...
Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo da ya gabatar ga taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, kasancewar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Sin da Amurka a duniya, abu ne da ya zama wajibi kuma nauyi ne dake kan wuyansu. Xie Feng ya jaddada cewa, idan kasashen biyu suka dauki juna a matsayin abokan hamayya, kuma suka shiga mummunar gasa, kasashen za su yi rashin nasara, kuma duniya za ta sha wahala. Amma idan suka zama abokan huldar juna, da samun nasara tare, za su samu ci gaba tare, da kuma amfanar da duniya baki daya. Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin...
Kwanan nan, aka wallafa littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1 a kasar Sin, wanda kwalejin nazarin tarihi da adabi na kwamitin kolin JKS ya tace. Littafin “Zababbun rubutu game da tattalin arziki na Xi Jinping” kashi na 1, ya kunshi muhimman ayyuka kuma na asali na rubutun Xi Jinping kan raya tattalin arziki daga watan Nuwamban 2012 zuwa Disamban 2024. An tsara shi bisa tsarin lokaci, kuma ya kunshi rubuce rubuce guda 74 da suka hada da rahotanni, jawabai, laccoci, umarni da sauransu.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su. Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da...
Rahotanni da suke fitowa daga Nijar sun bayyana cewa; Wata kungiyar mai alaka da al-ka’ida ta dauki alhakin kashe sojojin kasar 11 a kan iyaka da Aljeriya. A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai lamarin ya faru,kuma a jiya Asabar ne aka yi jana’izarsu a garin Agadez, kamar yadda wata majiyar watsa labara ta jamhuriyar Nijar ta ambata. Shafin “Air Info” da ya watsa laabrin ya kuma ce; Jami’an soja da dama sun hjalarci jana’izar sojojin da su ka kwanta dama, daga cikinsu har da janar Musa Salih Barmo, babban hafsan hafsoshin sojan kasar. Tashar Radiyo din kasar ta Nijar ta ce, an yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke sintiri akan mahadar iyakaokin kasar, da...
Shugaban Ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce bai ga laifin da ya yi wa Shugaban Amurka Donald Trump, ballantana ya nemi afuwa. Zelensky ya bayyana haka ne bayan zazzafar cacar-baki da ya kaure a tsakaninsa da Trump a ofishin shugaban ƙasar Amurka. A cewarsa, “ina godiya ga Amurka da gudunmuwar da take ba mu,” in ji shi kamar yadda ya bayyana a hirarsa da Fox News. Sai dai ya bayyana cewa musayar yawun ba ta dace ba, sannan ya kara da cewa dangantakar da ke tsakaninsa da Trump za ta gyaru. Tunda farko dai an soke taron manema labarai da aka shirya yi a fadar White House a jiya Juma’a, inda shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza. Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da...
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan Ramadan din ba, kuma mu sa kasar mu cikin addu’a Allah ya bamu dacewa. Sunana Abubakar Ahmad, daga Jihar Nassarawa: Ga me hali ya kan shiryawa gajiyayyu marasa hali, wanda kuma Allah bai hore masa ba ya shiga sahun wanda sai dai a dauka a basu su wadannan ba sa shirya komai face yawan salloli da addu’o’i da neman taimakon ubangiji Allah ya fitar...
Tawagar yan wasan Damben Gargariya ta kasar Iran sun zama zakara a wasan damben da ya gudana a birnin Tirana babban birnin kasar Albaniya a makon da ya gabata, inda suka tashi da lambobin yabo 6 wadanda suka hada da zinari 4 azurfa da tagulla. Wannan nasara da ta maida kasar a matsayin zakara a wannan wata a fagen kasa da kasa. Tawagar damben gargaji ta kasar Iran ita ce zakara a gasar damben na wannan shekara ta 2025 haka ita ce zakara a gasar shekara ta 2024. An gudanar da gasar ne a ranakun 27-28 na watan Fabrayrun wannan shekara, wato 2025UWW, wanda ya jawo hankalin masu shaawar wasan a duniya. Daga cikin yan wasan da suka sami lambar...
‘Fake Inbestment Schemes’: Masu cuta na amfani da shafukan zuba jari na bogi domin damfarar mutane. Ransomware: Wasu barayin yanar gizo na saka kwayoyin cutar kwamfuta domin su hana mutum amfani da na’urarsa sai ya biya kudi. Hanyoyin Kare Kanka Yi amfani da kwayoyin kalmomin sirri masu karfi – A guji amfani da kalmomin sirri kamar sunanka ko shekarunka. Yi amfani da Two-Factor Authentication (2FA) – Wannan yana 1ara kariya ga asusunka. Guji danna hadin gwiwa (links) daga tushe da ba a san su ba – Yawancin wadannan hanyoyin suna da cutarwa. Ka tabbata cewa shafin da kake ziyarta yana da alamar ‘https’ – Wannan yana nuna cewa shafin yana da kariya. Kar ka raba bayanan sirrinka da kowa –...
Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su. Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji shi. Tun da farko dai, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne mahukuntan jami’ar suka rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan abokin aikinsu. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu a Katsina a safiyar ranar Litinin cewa, “wasu jami’an CJTF sun bindige dalibai biyu ne bisa kuskure, suna tunanin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga cikin Kasashen da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan. A nan Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai...
Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka. 2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata. 3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya....
Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka. 2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata. 3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya....
Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan kai alkamar zuwa nahiyar Afirka da su ne fari da ake fama da shi Arewacin Afirka da kuma ambaliyar ruwan sama a yankin Sahel.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%. Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna...

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta ‘Euro-Med Monitor’ Ta Ce Ta Sami Shaidu Wadanda Suka Tabbatar Da Cewa HKI Tana Azabtar Da Fulasdinwa
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa Jami’an gidajen yari da kuma sojjin HKI suna dukan kawo wuka kan falasdinawa da suka shiga hannunsu, sannan suna azabtar da su sosai, daga ciki har tare da yanke yanke wasu gabban jikinsu. Kungiyar ta kara da cewa, mutum yana iya ganin alamun duka da kuma kumburan wurare da dama a jikin Falasdiwa. Banda haka Falasdinawan...
Fadar mai alfarma sarkin Musulmi, ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen Juma’ar nan a Sakkwato. Cikin wata sanarwa da Mai Alfarma Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban. Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446. Nasiru Malami/Sakkwato
“A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...
“PDP jam’iyyar siyasa ce, kuma muddin kuka ci gaba da kai mata hari, ba za ku samu ci gaba ba. Ba za ku iya daukar nauyin ‘yan baranda na siyasa da farfaganda don lalata mana kima ba don kawai burge Shugaba Bola Tinubu saboda ajandar ku ta 2027. “Ba wani dan Arewa mai hakali da zai yi wa APC yakin neman zabe a Arewa. Kasancewar wasu ’yan siyasa suna yi wa jam’iyyar shigo ba zurfi ne domin su sami abun sawa a bakin salati ne kadai amma ba wai za su zabe ta a 2027 bane. “Bai kamata Uba Sani ya bar wasu ‘yan siyasa suna yaudararsa, wadanda ba za su iya amfanar da siyarsa da komai ba. “Saboda haka,...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce inganta hadin kai da alaka tsakanin kasashen musulmi da suka hada da Iran da Malaysia na daga cikin abubuwan da ake bukata a halin da ake ciki a duniya. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ta yi da ministan harkokin wajen Malaysia Dato’ Seri Utama Haji Mohamad Bin Haji Hasan a birnin Tehran a wata ziyara da ya kai kasar Iran. Ya ce a halin yanzu gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana aiwatar da abin da take yin a laifuka da wuce gona da iri a yankin saboda kan musuylmi ba hade yake ba. Ya kara da cewa samar da hadin kai tsakanin jami’ai da ‘yan siyasar kasashen musulmi zai taka...
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar Cibiyar Hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR) sun shirya taron karawa juna sani na tsawon kwanaki uku ga jami’an yada labarai. Taron na da nufin baiwa Jami’an Watsa Labarai dabarun sadarwa na zamani, tare da mai da hankali kan sabbin hanyoyin inganta sadarwar jama’a a zamani. Da yake bayyana bude taron, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jaddada kudirin gwamnati na ganin sun kware a fannin sadarwa. Ya jaddada mahimmancin kayan aikin zamani,tare da haɗin gwiwar kafofin watsa labarun, da sadarwa ta hanyar bayanai don tabbatar da ingantaccen kuma da yada bayanai akan lokaci. Ya kuma bayyana muhimmiyar rawar da...
Har ila yau yana daga hukuncin shari’a, ba a fara azumi da kokwanto, misali ka kwanta bacci sai ka kudirce a ranka cewa in an bayyana ganin wata ina bacci, zan tashi da azumi. Mun gode Allah, yanzu sabida na’u’rar zamani da wuri ake sanar da ganin wata. Lamarin ganin watan Ramadana abu ne mai sauki, sabida galibin Malamai da Shehunnanmu na kasa da waje baki daya suna kan Hadisin Kuraibu da yake cewa “Kowacce kasa da ganin watanta, misalin kasar: Nijer da Ghana, Mali, Togo da dai sauransu duk suna da Sarkin Musulmi kuma shi zai ayyana ganin watan. Amma kuma, in Nijer suka ga watan Ramadana, Sarkin Musulmin Nijeriya in yaga dama zai iya cewa na ga wata...
Shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya a matsayin wakilin na angwaye yayin da Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo Janar Muhammad Iliyasu Bashar murabus ne ya tsaya a matsayin wakilin na amaren. Gwamna Nasir Idris, yayin da yake godewa uwargidansa Hajiya Nafisa Nasir Idris bisa wannan shiri a karkashin gidauniyarta ta “Asusun NANAS ”, ya yi alkawarin bayar da goyon baya da kuma ci gaba da gudanar da shirin na shekara-shekara domin amfanin al’ummar Kebbi, ya kuma shawarci ma’auratan da su kasance masu adalci da mutunta ra’ayin juna. Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku-Bagudu, ya bayyana taron a matsayin tunatarwa ga daidaikun mutane...
Wadanda Suka Yi Nasara Aliyu Usman Adam – Matsayi na daya Aliyu Usman Adam, dan asalin Zariya ta Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya a 2008. Bayan hidimar kasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014. A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TB Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu. Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu Zainab Muhammad, wacce...
Kasar Aljeriya ta yi watsi da barazanar da kuma wa’adin da kasar faransa ta gindaya ma ta na cewa za ta soke yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma ta shekarar 1968 wacce ta ba Aljeriya matsayi na musamman. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ta fitar ta ce “A cikin ci gaba da takun tsakar dake wakana (…) Aljeriya ba ta dauki wani mataki ba, kuma ta bar bangaren Faransa da ta matakin da ya dace. Ita dai Faransa ta yi barazana a ranar Laraba cewa za ta binciki yarjejeniyoyin da ke saukaka yanayin zama, shige da fice da kuma aiki ga ‘yan Aljeriya, dangane da koma bayan da ake samu na tashe-tashen hankula sakamakon wani hari...
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su damar yin fice a tsakanin takwarorinsu. Da yake magana tun farko, Gautier Mignot, jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, kuma jagoran tawagar, ya bayyana cewa, sun zo Kano ne domin halartar bikin baje kolin karatu na Turai da aka shirya yi a ranar 27 ga Fabrairu, 2025 a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
“Mun yi jimamin asarar rai da aka yi, kuma mun yi tattaki zuwa ga iyalan mamacin don jajantawa tare da tabbatar musu da gudanar da cikakken bincike don tabbatar da adalci,” in ji shi. Don haka, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu domin Rundunar tana aiki tukuru don zakulo gaskiyar lamarin tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara. Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi. Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar. Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya ce idan an gan shi, sai a mika bayanan ga Dagaci, Hakimi, Mai Unguwa ko Sarki mafi kusa domin sanarda Mai Alfarma Sarkin Musulmi. Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban wata, yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga daukacin...
Sai dai Bukar ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa ya sanar da shugabansa kuma ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a bi masa haƙƙinsa ba. Ya ce sau da dama an buƙaci ya kawo bayanan asusun ajiyarsa na banki don duba matsalarsa, amma babu wani canji. Duk da cewa shugaban makarantar ya wanke shi daga zargin guduwa daga aiki, har yanzu ba a mayar masa da albashinsa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.” Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin...
Majalisar Dattijan Aljeriya ta “dakatar da duk wata hulda da Majalisar Dattijan Faransa. Majalisar al’ummar kasar, kwatankwacin majalisar dattijai a kasar Aljeriya, ta sanar da cewa ta “dakatar da dangantakarta” da majalisar dattawan Faransa, domin nuna adawa da ziyarar da shugabanta Gérard Larcher ya kai a ranakun Litinin da Talata a yankin yammacin Sahara. Ziyarar ta biyo bayan wani gagarumin sauyi da shugaba Emmanuel Macron ya yi a watan Yulin shekarar 2024, inda ya nuna goyan baya ga shirin cin gashin kan yankin “karkashin ikon mulkin Moroko” wanda ya haifar da fushin Algiers. Yankin da Spain ta yi wa mulkin mallaka na yammacin Sahara, wani yanki ne na hamada da Majalisar Dinkin Duniya ba ta yanke matsayi kansa ba, kashi...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce Gwamna Umar Namadi ya amince da nadin sabbin jami’an cibiyoyi 27 da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce, an zabo sabbin jami’an cibiyar ne daga dukkan kananan hukumomin jihar 27, kuma za su samu horo da jagoranci kan ayyukan da hukumar ta dora musu. Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumar ta gudanar ta taron bita ga dukkan jami’an shiyyar da nufin sanar da jami’an irin ci gaban da aka samu a shirye-shiryen gudanar da aikin hajji mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana jin dadinsa kan yadda...
A yau Laraba, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina bai wa Taiwan makamai, ta kuma guji yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kullum, lokacin da aka tambaye shi game da rahotannin da ke cewa, gwamnatin Trump ta bayar da dalar Amurka biliyan 5.3 na taimakon da kasar ke bai wa kasashen waje da aka dakile a kwanan baya, wanda ya hada da dalar Amurka miliyan 870 da aka kebe a kan sha’anin tsaro na Taiwan. A cewar Lin, Sin ta damu matuka game da ire-iren wadannan rahotanni, yana mai...
Hukumar makamashin Nukliya ta kasar Iran ta kaddamar da kayakin aikin da ake bukata don samar da garin sinadarin (Tellurium Dioxide) wanda ake hada maganin cutar daji wanda ake kira (Iodine-131) da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto majiyar hukumar makamashin nukliyar ta Iran, na cewa ana samar da wannan sinadarin ne tare da amfani da makamashin nukliya. Kuma a halin yanzu kasar Iran zata iya samar da maganin wanna cutar a cikin gida. Labarin ya kara da cewa, idan JMI ta fara samar da maganin, zata bar dogaro da kasashen wajen don magance cutar a cikin gida, sannan wata dama ce ta samun kudaden shiga daga kasashen waje. Don haka a halin yanzu Iran tana...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da aikin soji a yammacin gabar kogin Jordan. Fu Cong ya bayyana cewa, dole ne mulkin Gaza bayan yakin ya bi ka’idar “Falasdinawa su yi mulkin Falasdinu”, kuma ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga sake gina Gaza. Kana kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su kara himma wajen kira ga...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar. Ya...
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin Doron Baga. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun mamaye ƙauyen inda suka tara masuntan waje guda. Majiyar ta ce “sun iso ne da makamai, inda suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. Domin sauke shirin, latsa nan
Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central. Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan. Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano. Bugu da kari, babban daraktan...
Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren. Rasata ta bayyana hakan ne yayin halartar bikin sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tawagogin likitanci ta Sin tsakanin Sin da Madagascar. Ji Ping, jakadan Sin dake Madagascar da Randriamanantany Zelyarivelo, ministan kiwon lafiyar jama’a na Madagascar, suka sa hannu a kan yarjejeniyar. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...

Amurka Za Ta Illata Kanta Bisa Tsara Matakan Kayyade Samar Wa Sin Sassan Na’urorin Laturoni Na Semiconductor
Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Trump ta kasar Amurka tana tsara wasu tsauraran matakan kayyade samar wa kasar Sin sassan na’urorin hada laturoni na semiconductor, da kara matsin lamba ga kasashen kawacenta, tare da bukatarsu da su tsaurara dabaibayi a kan sha’anin samar da fasahar matattarar bayanai ta microchip ga kasar Sin. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau 25 ga wannan wata cewa, kasar Sin ta riga ta sanar da matsayinta ga kasar Amurka kan batun kayyade samar da sassan na’urorin laturoni na semiconductor ga kasar Sin sau da dama. Ya ce, Amurka ta siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri. Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai lauyan masu shigar da kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’ar tare da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali. Mai shari’a Osiagor ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a, sannan ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
A yau Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Sergey Lavrov wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran. Bangarorin biyu dai sun tattauna akan batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma na kasa da kasa. Bugu da kari bangaroin biyu sun tattauna akan alakar kasashen biyu da hanyoyin bunkasa ta.
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu. Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin ya ce; Mu mutane ne da mu ka yarda da tattaunawa,kuma a halin yanzu abinda ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yake yi kenan da kasashen makwabta. Da ya tabo batun takunkuman da Amurka take kakaba wa Iran kuwa, shugaban kasar ta Iran ya ce, babu yadda za a yi a kakaba takunkumin ya yi tasiri akan kasar da take da iyaka mai tsawo da...
Fiye da mutane 7,000 da yawancinsu fararen hula ne aka kashe a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tun daga watan Janairu, in ji Firaminista Judith Suminwa Tuluka a ranar Litinin. Mambobin kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Rwanda sun kwace iko da yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo masu arzikin ma’adinai da suka hada da manyan biranen Goma da Bukavu da ke gabashin kasar. Firayim Minista Judith Suminwa Tuluka ta yi gargadin cewa, halin da ake ciki na tsaro a gabashin DRC ya kai matsayi mai daukar hankali, yayin da take jawabi ga kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Ta ce mutanen da suka mutu sun hada da “fiye da gawarwaki 2,500 da aka binne...
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
Gwamnatin Trump ta saka sabbin takunkumai kan wasu mutane da ke da alaka da wani kamfanin fitar da mai na Iran. Takunkuman sun shafi mutane 22 da jiragen ruwa 13 da ke da alaka da masana’antar mai ta Iran. Wadannan takunkumin wani bangare ne na matsin lamba na shugaban Amurka Donald Trump kan Iran. Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta sanar da cewa, takunkumin na da nufin gurgunta harkokin hada-hadar kudi da kuma cinikin man fetur na Iran, da nufin takaita shirinta na nukiliya. Iran dai na mai kakkausar suka kan takunkuman na Amurka, tana mai kallonsu a matsayin sabawa ka’idojin kasa da kasa.
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.” Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki. Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda ya samu wakilcin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya ce shirin samar da tallafin a mazabu zai kara inganta manufofi 12 na gwamnatin jihar wadanda suka hada da karfafawa al’umma don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a kowane mataki. Ya yi fatan wannan karimcin zai yi kyakkyawan tasiri ga mutane 1,200 da suka ci gajiyar tallafin. A jawabinsa, dan majalisa...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...