2025-02-01@22:07:12 GMT
إجمالي نتائج البحث: 207
«ya kamata a»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Hukumar kula da gandun daji na Hadejia ta ce wuraren shakatawa na kasa suna taka rawar gani ta fuskar kiyaye halittu, da magance matsalolin sauyin yanayi, da inganta bincike, da ci gaba, gami da samar da ayyukan yi a Najeriya. Mukaddashin jami’in kula da gandun dajin, Mista Jonah Moses ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar neman shawarwari ofishin wayar da kan jama’a na kasa da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya nanata cewa al’umma za su kara fahimtar fa’idojin irin wadannan wurare ne kadai idan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA, ta taimaka wajen fadakarwa ko ilmantar da jama’a. Jonah Moses ya bayyana cewa, sun kawo ziyarar ce domin ganawa da masu ruwa...
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya kasa da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar tun hawansa karagar mulki, a sassan jihar ta Jigawan. Yana mai cewar sun ziyarci jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan ta’aziyyar rashin da aka masa. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba musu bisa wannan ziyara tare da fatan za su koma jihohinsu lafiya. Usman Mohammed Zaria
Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane 300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
Gwamnatin jihar Kwara ta ce ta samar da matakan dakile yawaitar kauran likitocin daga jihar zuwa wasu kasashe, domin neman ingantacciyar rayuwa. Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam ta bayyana haka, a lokacin da ta karbi bakuncin shugabannin kungiyar likitoci ta kasa, a Ilorin. A cewarta gwamnatin ta amince da biyan Asusun Horar da Likita masu neman kwarewa da sauran abubuwan karawa likitoci gwarin gwiwa. Dokta El-Imam ta bayyana cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarinta wajen ganin dukkan ma’aikatan jinya sun yi fice a aikin da suka zaba, domin dakile yawan barin kasan nan da likitoci ke yi zuwa kasashen waje. Kwamishinan, ya yi kira ga kungiyar da ta ziyarce ta, da ta fahimci...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025. Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.