2025-02-22@06:53:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 409

«tattara madara»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da shirin tallafawa al’umma da Shugaban karamar hukumar Sule Tankarkar ya bullo da shi a yankin. Gwamnan Jihar, Mallam Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron kaddamar da rabon tallafin da aka gudanar a karamar hukumar. Malam Umar Namadi, ya bayyana matukar jin dadinsa bisa wannan gagarumin tallafi, da ya haɗa da bayar da kayayyaki da jari ga rukunin al’umma daban-daban. Yana mai nuni da cewar, wannan mashahurin shiri ya nuna kyakkyawan hangen nesa na Shugaban karamar hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, wajen tallafa wa mutanen karkara da ke fama da kalubale daban daban. Namadi, ya kaddamar da rabon tallafi ga mutane fiye da 350 a karamar hukumar Sule Tankarkar....
    Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya bayyana  wa al’ummar jihar Zamfara da ma kasa baki daya aniyar rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron wasannin rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau. Taro West African Social Activities WASA wani taro ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin  wasannin gargajiya na wannan  yankin na Afirka. Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu  cikin annashuwa domin wasannin al’adun da kuma bikin ƙarshen  shekara. Janar...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
    Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar.   Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi, jihar Bauchi; Usman Umar Danburam, 35, daga Darazo, Jihar Bauchi; Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 50, daga Mina, Jihar Neja; Aminu Mohammed, 40; da Adamu Abdul’aziz mai shekaru 46 daga jihar Taraba, an kama su ne a ranar 17 ga watan Janairun 2025.   An same su dauke da kayayyaki dama da kuma wasu duwatse ake zargin masu daraja ne a wani sansani hakar ma’adinai dake...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce kusan yara miliyan 5.4 ‘yan kasa da shekaru biyar a yankin arewa maso yamma da arewa maso gabas na fama da matsananciyar rashin abinci mai gina jiki, inda aka yi hasashen za a samu Karin masu wannan matsala su miliyan daya nan da watan Afrilun 2025.   Wakiliyar UNICEF a Najeriya Ms Cristian Munduate ta bayyana hakan a wani taron manema labarai kan rikicin da ya addabi miliyoyin yara a jihar Zamfara da kuma fadin Najeriya da aka gudanar a Gusau babban birnin jihar Zamfara.   Ms Munduate wadda ta yi tsokaci kan halin da kananan yara ke ciki a Zamfara, ta ce jihar na da yara miliyan...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
    Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...