2025-03-25@21:26:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 90
«Salah al Bardawil»:
Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuraɗiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afirka. Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati Tsohon shugaban na wannan furuci ne a Abuja a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha. Obasanjo ya buga misali da yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuraɗiyya da cewa...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Iran tana cikin shirin ko-ta-kwana akan duk wani abu da zai iya bijirowa, kuma a halin yanzu ba batun yaki ake yi ba. A wata ganawa da ministan harkokin wajen na Iran ya yi da tawagar kungiyar agaji ta “Red Cross” a karkashin jagorancin shugabanta Koliband, ministan harkokin wajen na Iran ya yabawa aikin nasu, tare da cewa; Duk da cewa ana cikin lokacin hutu, amma su a kodayaushe suna cikin shirin ko-ta-kwana domin gabatar da ayyukan agaji da hakan yake nuni da yi wa al’umma hidima ta koli. Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kuma ce: Su ma sojoji da jami’an tsaro kamar ku suke aiki, ba...
Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar Turai sun ce, tsagaita bude wuta nan take a Gaza ya zama dole. Da yake magana a wani taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin babban sakataren majalisar kan harkokin siyasa Khaled Khari, ya ba da rahoto game da tabarbarewar al’amura a Gaza bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni da aka kwashe kusan watanni biyu ana aiki da ita. “A kowace rana, muna kara nisa daga manufar mayar da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su zuwa gidajensu lami lafiya,” in ji Khari, yayin da yake magana kan fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su a Gaza. Babban jami’in kula da harkokin siyasa na Majalisar Dinkin...
Kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta fitar da wata sanarwa dangane da shahadar Salah al-Bardawil, mamba a ofishin siyasa na kungiyar kuma wakilin majalisar dokokin Falasdinu. A rahoton tashar Al-Alam, bayanin Hamas yana cewa: Dr. Salah Al-Bardawil, wanda ya yi fice a fagen siyasa, kafofin watsa labarai, da fagage na kasa da kasa, kuma ake kallonsa a matsayin daya daga cikin manyan kusoshin Hamas, wanda yake a kan gaba wajen gwagwarmaya da sadaukarwa, ya yi shahada a kan tafarkin gaskiya. Bayanin ya ci gaba da cewa: Bai taba gazawa wajen gudanar da ayyukansa na jihadi da hidima ga al’ummar Palastinu ba, ya kuma ci gaba da yin gwagwarmaya kan turba ta gaskiya da neman ‘yanci har zuwa karshen rayuwarsa. Hamas...
4 – Kar ki kasance kullum a cikin bacin rai ko fushi da mijinki, domin fushi kofa ce ta kowane sharri. 5 – Kar ki kasance mai girman kai wajen bashi hakkokin zamanku, abin da yake so ko da baki so matukar bai saba wa addini ba ki yi masa. 6 Ki nuna wa mijinki komai naki nasa ne komai nasa kuma nasa ne, ki nuna baki da iko a kai sai abin da ya yi. 7- Ki kasance mai kula da abubuwan da yake dubawa a jikinki in ya shigo gida, ina idonsa ke kallo a jikinki. Bayan kin yi kwalliya. sai a gyara masa su da kyau domin a dauke masa hankali. In kuma kin tabbatar duk lokacin...
Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka. Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman...
Wani sabon kazamin harin sojojin Isra’ila ya yi sanadin shahadar mutum 40 cikin sa’o’I 24 da suka gabata ciki har da Salah al-Bardawil, dan majalisar Falasdinu kuma mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas. A cikin wata sanarwa da ta fitar yau, Hamas ta ce an kai wa Bardawil hari ne a wani hari na ” yahudawan sahyoniya na ha’inci”, a lokacin da yake gudanar da sallar dare a daren 23 ga watan Ramadan. An kashe shi ne tare da matarsa a wani hari da Isra’ila ta kai ta sama a kan tantinsa da ke yankin al-Mawasi, yammacin birnin Khan Yunis na kudancin Gaza. Kungiyar ta bayyana Bardawil a matsayin “alama ta siyasa, yada labarai,” da ayyukan bunkasa...
Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin He Yongqian, ta ce kasar za ta aiwatar da matakai na kara daidaita manufar jawo jarin waje a shekarar nan ta 2025, da aiwatar da matakan bude kofa a karin sassa, da kyautata yanayin kasuwanci a fannin. He Yongqian, wadda ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Alhamis, ta ce ya zuwa yanzu kasar Sin ta baiwa wasu kamfanoni masu jarin waje 13 damar shiga hada-hadar inganta hidimomin wayar tarho, yayin da aka kaddamar da ayyuka masu jarin waje sama da 40 a fannin fasahar cin gajiya daga halittu masu rai. An kuma amince da fara aikin cikakkun asibitoci 3 masu jarin waje. Jami’ar ta...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sake dawo da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza da kuma hare-haren da Amurka ke kaiwa kasar Yemen. A wata tattaunawa ta wayar tarho a wannan Juma’a, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na UAE Abdullah bin Zayed Al Nahyan, sun tattauna batutuwan da suka shafi yankin, musamman ma ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma hare-haren Amurka a Yemen. Araghchi ya yi kakkausar suka kan kisan gillar da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi wa daruruwan Falasdinawa da ba su ji ba ba su gani ba tun daga ranar Talata, yana mai jaddada cewa yin...
Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar. Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ayyana dokar ta-ɓaci ne kawai a lokuta na matsanancin rikici kamar yaƙin basasa, ko rushewar doka da oda, wanda a cewarsa babu ɗaya daga cikinsu da ya faru a Jihar Ribas. NEF, ta zargi Gwamnatin Tarayya...
Kakakin Rundunar Sojojin Yaman Birgediya Janar Yahya Saree, ya bayyana cewa, Dakarun Yemen sun harba makami mai linzami samfurin Falasdinu-2 a babban filin sauka da tashin jirgin saman Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ben Gurion. Saree ya jaddada cewa, filin jirgin saman Ben Gurion ba shi da aminci ga zirga-zirgar jiragen sama, yana mai gargadin cewa za su ci gaba da kasancewa a fagen daga har sai Isra’ila ta kawo karshen yakin da take yi a kan al’ummar Gaza. Tun da farko dai rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da cewa, an harba makamai masu linzami a yammacin jiya Juma’a a yankuna da dama da ke tsakiyar Falasdinu da ta mamaye, kuma Isra’ila ta tabbatar da cewa an harbo makaman...
Shugaban Riƙo na Jihar Ribas, Ibok Ibas, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa shi ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, wadda ke fama da rikicin siyasa. Da yake jawabi a wani shirin talabijin a daren Alhamis a Fatakwal, Ibas ya bayyana naɗin nasa a matsayin matakin da ya dace don kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya ɗauki kusan shekaru biyu. Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Ya ce rikicin ya hana ci gaban gwamnati, tare da haifar da matsalar tsaro da koma bayan tattalin arziƙi a jihar. “A matsayina na ɗan yankin Neja Delta, na fahimci damuwar mutanenmu. Rashin tabbas a...
Ramadan lokaci ne da ke hada kan iyalai da al’ummomi a fadin duniyar Musulmi. Lokaci ne da masoya ke haduwa tun daga lokacin sahur har zuwa buda-baki, ta hanyar kasancewa tare domin cin abinci mai gina jiki. A wannan lokacin, ba a yin abinci don nishadi kawai, lokaci ne na inganta rayuwa da bayar da labarai na nishadantarwa da zumunta da kuma jin dadin kasancewa tare. A cikin wannan labari mai ban sha’awa na MAGGI mai taken Labarin Ramadan, wasu mata biyar sun yi tafiya ta tsawon wata guda don samar da sauye-sauye, inda suka gano hadaddun girke-girke na sada zumunta da ke da alaka da samar da labarai masu jan hankali, har guda shida. Tare da wasu jaruman wasan...
“Wannan mataki na dokar ta-ɓaci wata dama ce ta kare rayuwar al’umma, tabbatar da tsaron muhimman kadarori, da dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu. Shugaba Tinubu ya buƙaci dukkanin ɓangarori su mara baya ga ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Jihar Ribas tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziƙi da haɗin kan ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan...

Mutane Fiye Da 30 Ne Suka Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Dawkar Gas Ta Yi Bindiga A Abuja Na Tarayyar Najeriya
Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita. Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa...
Fubara ya ƙara da cewa, duk da rikicin siyasar da ake fama da shi, gwamnatinsa tana ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma ana biyan ma’aikata albashinsu tare da ƙaddamar da muhimman ayyuka a jihar. Ya buƙaci al’ummar jihar su ci gaba da bin doka da oda, yana mai cewa za su ci gaba da tuntuɓar hukumomin da suka dace domin tabbatar da cewa dimokraɗiyya ta ci gaba da ƙarfafa a jihar. An fara samun matsala a siyasar Jihar Ribas tun bayan da rashin jituwa ya ɓulla tsakanin Fubara da tsohon gwamnan jihar, wanda yanzu shi ne Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike. Rikicin ya kai ga cewa wasu ‘yan majalisar dokokin jihar masu biyayya ga Wike suka yi barazanar...
A baya-bayan nan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da harkokin gona na kasar Gambiya Demba Sabally, ya bayyana goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin, a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona a kasarsa a ’yan shekarun nan. Idan ana batu na kirkira da amfani da fasahar zamani a duniya, to kowa ya san cewa kasar Sin ta yi zarra a wannan bangare. Haka kuma kowa ya san duk wani ci gaban da Sin take nema ko ta samu, tana yi ne domin jama’arta su kasance cikin walwala, shi ya sa ci gaban Sin a fannin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, ya game kowane bangare na...

Taron Kasashen Iran, Rasha Da China A Birnin Beijing Ya Bukaci A Kawo Karshen Takunkumai Akan Tehran
A yau Juma’a ne aka bude taron kasashen Iran, Rasha da China, a matakin mataimakan ministocin harkokin waje inda su ka tattauna shirin makamashin Nukiliya na Iran. Mahalarta taron sun bukaci ganin an dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata, sannan kuma a warware batun shirinta na makamashin Nukiliya ta hanyar tattaunawa. Kasashen na China, Rasha da kuma Iran sun bayyana takunkuman na Amurka akan Iran da cewa, ba halartattu ba ne. Haka nan kuma sun ce; Tuntubar juna da kuma tattaunawar diplomasiyya bisa girmama juna ne kadai zabin da ake da shi domin cimma manufa. Taron da aka yi a yammacin birnin Beijing ya kunshi mataimakan ministan harkokin wajen Iran Garid Ridh Abadi, Sai Rasha Sergey Ryabkov da...
Sama da mutane 100 ne mazauna garin Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara suka rasa matsugunansu sakamakon ruwan sama ya yi barna a cikin al’umma. Gidan Rediyon Najeriya ya tattaro cewa an lalata cibiyoyin ilimi da gidajen zama da rumfunan kasuwa tare da lalata dukiyoyi. Guguwar ruwan sama ta yi barna a kwalejin Ansar Deen da ke Ijagbo yayin da ajujuwa sama da 10 suka yi lalace, inda dalibai da malamai suka makale. An gano cewa guguwar ta afku ne da misalin karfe 4 na yamma. a ranar Litinin, tare da yaga rufin ajujuwan tare da lalata muhimman kayan koyo da kuma kawo cikas ga ayyukan ilimi. Da suke Magana game da wannan...
Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi. A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da Dodams Medical Equipt don kula da aikin na tsawon shekaru 2. Ya bayyana cewa, a watan Janairun wannan shekara ne aka yi duk wani shiri da kuma biyan kudin jirgi, amma saboda hutun karshen shekara da Kamfanoni suka yi, an samu tsaiko wajen samar da wasu sassa musamman na’urar gudanarda aikin, wanda ya iso a ranar Litinin 10 ga Maris, 2025. Ya ci...
Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki. Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya ce babban aminin Obi, Valentine Ozigbo, ya koma jam’iyyar APC domin yin takarar gwamna. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina “Kun san muna rage ƙarfin jam’iyyar LP kuwa?” in ji Bwala. “Valentine Ozigbo ya shigo jam’iyyarmu, Balami ma haka, Peter Obi ma zai zo....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu? Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya...
Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku. HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda...
’Yan bindiga sun kashe aƙalla manoma 14 yayin wani hari da suka kai yankuna huɗu a Ƙaramar Hukumar Akure ta Arewa da ke Jihar Ondo. Yankunan da abin ya shafa — Aba Alajido, Aba Sunday, Aba Pastor da Ademekun— galibi mazaunansu ƙananan manoma ne. Abba zai naɗa sabon Kwamishina a Kano Yadda za a samu rufin asiri da sana’ar ɗinki — Muhammad Wata majiyar ’yan sanda, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa maharan ɗauke da bindigogi sun auka yankunan ne da tsakar daren ranar Asabar inda suka soma harbe-harbe kan mai uwa da wabi. Majiyar ta ce kawo yanzu dai an tsinto gawawwaki mutum 14 yayin da ake ci gaba laluben wasu. Wani mazaunin ɗaya daga cikin yankunan...
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta,...
Jagoran kungiyar Ansar Allah ta kasar Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya baiwa masu shiga tsakani wa’adin kwanaki hudu na tabbatar da shigar da kayayyakin jin kai a Gaza, yana mai gargadin cewa idan har Isra’ila ta ci gaba da toshe hanyoyin kai kayan agaji a Gaza, to dakarun Yemen za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwa masu alaka da Isra’ila. A cikin wani jawabi da ya yi wanda aka watsa a gidajen talabijin na ciki da wajen kasar Yemen, Al-Houthi ya soki ta’annutin da Isra’ila ke ci gaba da yi wa Falasdinu, yana mai jaddada cewa, rashin aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da kuma hana shigar da kayan agaji a Gaza da kuma ci gaba...
Don haka, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda saba ka’idojinta na majalisar dattawa. Bugu da kari, majalisar ta bukaci Natasha da ta maido da duk wani abu mallakin majalisar ga mai kula da Majalisar har sai lokacin dakatarwar ya cika. Sanata Imasuen ya bayyana cewa, “A madadin kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata, da kuma sauraron kararrakin jama’a, muna godiya ga shugaban kasa da manyan abokan aikinmu bisa damar da aka ba mu na yi wa ‘yan Nijeriya hidima ta hanyar wannan kwamiti. Mun gabatar da shawarwarinmu cikin girmamawa don tantancewa da amincewa. Na gode.” Bayan doguwar muhawara kan rahoton da kwamitin ya gabatar, Sanatocin sun amince da dukkan shawarwarin...
Majalisar Dokokin jihar Jigawa ta yi garambawul ga dokar bada kudaden tallafi ga masu bukata ta musamman domin kara yawan kudaden tallafin daga naira dubu bakwai zuwa naira dubu goma. Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatar da rahoton kwamatin kula da al’amuran mata da cigaban al’umma na majalisar. Da yake gabatar da rahotonsa, shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Birnin Kudu, Alhaji Muhammad Kabir Ibrahim, yace kwamatin ya tattauna da masu ruwa da tsaki domin duba bukatar kara yawan kudaden da ake tallafawa masu bukata ta musamman daidai da halin da rayuwa ta ke ciki a yau. Ya ce gyaran fuskar da aka yiwa dokar ya hada da kara yawan makafi da kurame da kutare da sauran masu bukata ta...

Lin Jian Ya Yi Bayani Kan Takardar Bayani Game Da Shawo Kan Sinadarai Masu Alaka Da Sinadarin Fentanyl Ta Sin
A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa. Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da...
Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya. Haka nan ya ambaci cewa abu mai muhimmanci a wannan lokacin shi ne tabbatar da tsagaita wutar yaki,wanda yake fuskantar keta shi –daga Isra’ila. Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban. Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da shirin na...
A yau Talata, kasar Sin ta bakin ma’aikatar kula da harkokin kasuwanci ta kasar ta bayyana rashin jin dadinta game da karin harajin da Amurka ta yi ikirarin sanyawa kayayyakin kasar, bisa kafa hujja da maganin Fentanyl. Kamar yadda kakakin ma’aikatar ya bayyana, Sin tana daya daga cikin kasashe mafiya tsauraran matakan yaki da miyagun kwayoyi ko sarrafa su. Tabbas kasar Sin kasa ce mai sa ido da daukar tsauraran matakan dakilewa da yaki da tu’ammali da duk wani abu mai illa, musammam miyagun kwayoyi, kuma tana iyakar kokarinta kan wannan batu. Idan ba a manta ba, kasar Sin ce ta jagoranci duniya wajen tsara jerin rukunin kwayoyin Fentanyl da sauran abubuwan da suka jibance shi a watan Mayun 2019,...
Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin, take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa kuma...
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook da dai sauransu a kasar. Ministan sadarwa na kasar Nijer sidi Mohammad Raliyu shi ne ya bayyana hakan, yana me cewa duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya kunshi mutanen 50 zuwa 100 dole ne yayi rajista a wajen hukuma don ci gaba da aikinsa. Ministan ya ce zaurukan whattsap da Facebook na zama hanyoyin kasuwanci da kuma yaƙar gwamnatoci, wannan yasa za ta bullon da sabon shiri tare da wasu ƙasashen Afirka domin sake duba dokar da ta bada damar aiki da shafukan sada zumunta a Kasashen, domin dakile amfani da ita ta hanyar da...
Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa. Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa. A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je...
Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya bayyana cewa matarsa ta taɓa kawo masa ƙorafi game da cin zarafin da ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi mata. A cewarsa, rikicin ya fara tun lokacin da Natasha ta tsaya takarar kujerar Sanata a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, inda ta nemi kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya. Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano A lokacin, Akpabio yana riƙe da mukamin Ministan Neja Delta. “Da kaina na je na same shi na buƙaci ya bai wa matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotar da ke tsakaninmu. “Bayan mun tattauna sai...
Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar. Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma...
Cecekucen dai a tsakanin Donald Trump da kuma Vladmir Zylinesky an yi shi ne saboda banbancin ra’ayin da bangarorin biyu suke da shi akan batun kawo karshen yakin Ukiraniya. Shugaban Amurka Donald Trump dai yana son ganon takwaransa na Ukiraniyan ya amince da kawo karshen yankin da kasarsa take yi da Rasha, yayin da Zylinesky yake Magana akan wasu sharudda kafin hakan ta faru. Shugaban kasar Amurkan ya yi wa shugaban kasar Ukiraniya goron cewa, kasarsa ce take ba su taimakon kudade da makamai, yana mai kara da cewa; Ko dai ya amince da kulla yarjejeniyar kawo karshen yakin ko kuma Amurka ta dakatar da duk wani taimako. Haka nan kuma shugaban na Amurka ya zargi shugaban Ukiraniya da cewa,...
A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu. An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli. Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023 Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce,...
Akwai makoma mai haske wajen raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, wanda tabbas zai taimaka wa Sin da kasashen Afirka wajen gaggauta zamanantar da ayyukan gona, har ma da zamanantar da kasashensu baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Donald Trump ta kawo karshen wani shirin Amurka na bunkasa samar da wutar lantarki a Afirka, wanda aka kaddamar fiye da shekaru 10, in ji Bloomberg. Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kaddamar a shekarar 2013, yana da nufin samar da wutar lantarki ga miliyoyin gidaje a nahiyar Afirka, wanda Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke tafiyar da shi. Wannan na daga cikin shirin Trump na rage kashe kudade na tarayya wanda ma’aikatar ingancin gwamnati ke jagoranta. Kusan dukkanin manufofin shirin “Power Africa” an sanya su cikin jerin shirye-shiryen da za a kawar da su. A ranar 20 ga watan Janairu, ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta dakatar da...
Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da kasa. A makalar da suka rubuta a mujalar harkokin waje, shugabannin sun bayyana cewa “Zabin abu ne mai wuyar gaske: ko dai mu yi aiki tare don tilasta dokokin kasa da kasa ko kuma mu yi kasadar rugujewar sa.” Shugabannin sun kara da cewa “harin da ake kaiwa al’ummar Falasdinu ya yi daidai da ababe marasa dadi da munin tarihin da suka faru a cen baya kan kasashensu”, da suka hada da mulkin mallaka, yaki da ta’addanci da wariyar launin fata. “Muna iya fitowa daga nahiyoyi daban-daban, amma muna da tabbacin cewa rashin tsawatarwa na...
Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar. Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...
Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku kan zargin cin amanarta. Sauran waɗanda jam’iyyar kan zargin cin amana sun haɗa da Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.
Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na Beirut,bayan da aka dauki tsawon yau ana gudanar da jana’izarsa. Dubun dubatar mutanen Lebanon da kuma wasu daga wajen kasar ne su ka halarci taron jana’izar Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin da aka gudanar a cikin birnin Beirtu. Tashar talabijin din al’mayadin ta bayyana cewa bisa kirdado adadin mutanen da su ka halarci jana’izar sun kai mutane miliyan daya da 400,000. Mahalarta jana’izar sun cika filin wasa na birnin Beirut da kuma manyan tituna ta yadda babu masaka cinke, da hakan ya sa motar da take dauke da makararsa da...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta kasa da kasa. Wang, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babbar darektar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, a birnin Johannesburg, birni mafi girma kuma cibiyar hada-hadar tattalin arzikin Afirka ta Kudu. A nata bangaren, Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, a tsakiyar rudanin da duniya ke fama da shi, kasar Sin ta hau kan turba mai kyau,...

Amurka Ta Ce Zata Gabatar Da Nata Shawara Dangane Da Kawo Karshen Yakin Ukraine Ga Babban Zauren MDD
A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD. Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya. Bayan neman albarkatun man fetur da gas, an kuma tsara aikin rijiyar don zurfafa nazarin juyin halittar duniya da kuma zurfafa ilimin binciken kasa. A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da...
“Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025. “Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin da za a iya aiwatar da alkawuran kan biyan hakkokin mambobin kungiyar,” in ji sanarwar.
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida. Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta. Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa. Ya kara da...
Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu. Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin kirkira sun hada da Toru-ebe da za a sassaka daga jihohin Delta da Edo da Ondo na yanzu, da kuma jihohin Ibadan da Lagoon da za a sassaka daga jihohin Oyo da Legas, bi da bi. Sauran sun hada da Jihar Ijebu da za a samar daga Jihar Ogun ta yanzu da kuma jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha da za a kirkiro daga jihohin Ogu da...
Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu. Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace. Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata....
A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da ke Amurka (CGCC) da aka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka, Xie ya bayyana cewa, barazanar haraji ba za ta taba yin tasiri a kan Sinawa ba, a maimakon haka, masu yi za su buge ne da illata ginshikin yaki da miyagun kwayoyi da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kara tsadar kayayyaki ga iyalan Amurkawa da harkokin kasuwanci...
Kwamandan sojan na Iran Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama. A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi. Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Haka kuma, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Bama da kuma dawo da wutar lantarki a yankin. Zulum, ya ƙara da cewa za a ci gaba da tallafa wa masarautar da gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata. Hakazalika,...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba. DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa An harbe ’yan sanda biyu a Yobe Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar...
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano. An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka. Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka. Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka. ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi...
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
Su tsare tsaren anyi shirin tabbatar dukkan makarantu masu zaman kan su da na gwamnati za su fara amfani da tsarin a watan Janairu 2025. Sai dai kuma watan Janairu ya wuce ba tare da samun wani ci gab aba dangane da lamarin. Rahoto ya nuna har yanzu da akwai sauran Rina a Kaba, domin kuwa da akwai karancin makarantu wadanda basu da irin kayan da za ayiu amfani da su wajen aiwatar da sabon tsarin,da kuma yadda za a horar da Malamai, hakan ta sa aka bar masu ruwa da tsaki cikin shakku ko sabon tsarin ilimin za afara amfani da shi. Sabon tsarin ilimin an yi niyyar fara amfanni da shi inda za a koyar da yaddaake sabbin...
A cikin daren nan aka dawo da wutar lantarki a Jihar Kaduna. Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) ya dawo da wutar be bayan kwanaki babu ita. An dauke wutar ne sakamakon yajin aiki da ma’aikatansa suka shiga tsawon kwana biyar. Kaduna Electric ne ke ba da wutar lantarki a Jihar Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi. Ma’aikaran sun janye yajin aikin ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya shiga tsakaninsu da kamfanin.
Sakatariyar kwamitin JKS na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta bayyana a taron hukumomin kwastam na kasar a ranar 7 ga wata cewa, darajar cinikin waje na kasar Sin ta zarce manufar da aka tsara ta yuan triliyan 43 a karon farko a shekarar 2024, inda ta karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023, kuma ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi girma a fannin cinikin kayayyaki a shekaru takwas a jere. A shekarar 2024, an fuskanci karuwar rashin tabbas da rashin zaman lafiya a waje, duk da haka hukumar kwastam ta samar da hidimomi mafi kyau domin saukake da sa kaimi ga inganci da daidaiton yawan...
Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20. Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22. Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5. Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku. Tun a watan Disamba na...
Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa. Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun maslaha.
Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar Ukrain. Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
Da marecen jiya Lahadi ne dai shugaban Majalisar dokokin Iran Mahmud Mashahadani ya iso Tehran domin fara ziyarar aiki da zai gana da jami’an gwamnatin kasar. Mataimakin shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Hamid Ridha Haji Babbayi da kuma shugaban kwamitin kawancen majalisun kasashen biyu ne su ka tarbi Mashhadani a filin saukar jiragen sama na “Mehrbad”
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5 Ya ce hukumar ta karɓo kuɗaɗen daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce kowanne mahajjaci ya samu Naira 61,080. Ya kuma ce an tura wa kuowa kuɗinsa kai-tsaye zuwa asusun bakinsu. “NAHCON ta mayar da waɗannan kuɗaɗen ne saboda matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru...
Kawo yanzu Kano Pillars, wadda take mataki na 10 da maki 29 za ta fafata da Remo Stars a wasan mako na 23.
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
Shugaban Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed ya tabbatar wa mambobin shirin da suke aikin yi wa ƙasa hidima na shekara ɗaya cewa za su fara karɓar Naira 77,000 daga watan Fabrairu. A daidai lokacin da aka sake duba mafi ƙarancin albashi da hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin kuɗaɗen alawus ɗin daga N33,000 zuwa N77,000 duk wata, amma da dama sun nuna damuwarsu kan aiwatar da hakan. Gwamna Buni ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Tafkin Chadi ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara A shekarar bara wani jami’in shirin ya danganta jinkirin aiwatar da biyan kuɗin da rashin kuɗi. Amma yayin da yake bayani ga...
Tsohon shugaban kamfanin Google Eric Schmidt, ya bayyana bullar kamfanin DeepSeek na Sin a matsayin wadda ta kawo muhimmin sauyi ga takara a fagen kirkirarriyar basira ta AI a duniya. Wannan na kunshe ne cikin wani sharhi da jaridar Washington ta wallafa ranar Talata, inda Eric Schmidt ya jaddada cewa, karfin Sin na yin takara da manyan kamfanonin fasaha ba tare da amfani da albarkatu mai yawa ba, ya nuna bukatar da Amurka ke da ita ta karfafa karfinta a bangaren. Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta DeepSeek kamfanin Sin ne dake mayar da hankali kan kirkirarriyar basira ta AI, wanda aka...

Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Amince Da Bukatar Kawo Karshen Rikicin Jin Kai Cikin Gaggawa A Gaza
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15. Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai. A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda...
Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Max Air na tsawon wata uku, bayan ɗaya daga cikin jiragen kamfanin, tayarsa ta yi bindiga yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a daren ranar Talata. Jirgin Max Air ƙirar Boeing 734 mai lamba 5N-MBD ne ya samu matsalar kamar yadda rahotanni suka bayyana. Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Dukkanin fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun kuɓuta cikin ƙoshin lafiya. Wannan shi ne karo na uku da jirgin Max Air ke fuskantar matsala cikin watanni uku da suka gabata. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), ta sanar da...
Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci. Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin. Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin. Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
Sama da ’yan Najeriya 5,000 da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, na fuskantar barazanar dawo da su gida. Daga cikinsu, kusan 1,500 ne ake tsare da su, wanda hakan na daga cikin matakin da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka na korar baƙin haure da masu neman mafaka ba bisa ƙa’ida ba. Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Alƙaluman da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE), ta fitar a watan Nuwamban 2024, sun nuna cewa akwai mutum miliyan 1.445 baƙin haure da ke zaune a ƙasar ba tare da takardun izini ba, ciki har da mutum 3,690...
Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.
Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar. Labarin ya kara da cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...