2025-03-20@17:50:37 GMT
إجمالي نتائج البحث: 60
«siyan ɗanyen mai da»:
Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya. Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da ‘yan jarida, yana mai bada tabbacin cewa wannan kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa za su kasance ginshiƙin gudanar da mulki a jihar. “Mu a Jihar Gombe muna alfahari da daɗaɗɗiyar dangantakar da muka ƙulla da ‘yan jarida; ‘yan jarida abokan aikinmu ne masu ƙima a fagen kawo ci gaba, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ganin sun ci gaba da yin aiki...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira. Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da Ribas An ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai...
Gidauniyar Sheikh Ɗahiru Bauchi ta buƙaci Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya nemi afuwar ɗaliban malamin bisa abin da ta kira rashin adalci da aka musu. Idan kuwa bai yi hakan ba kafin ƙarshen watan Ramadan, za su maka shi a kotu. An sanya dokar hana fita bayan kashe sabuwar amarya a Jigawa HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Wannan na ƙunshe ne a wata takarda da gidauniyar ta fitar, wadda Sayyadi Aliyu Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya sanya wa hannu. A cewar takardar, dole ne El-Rufai ya fito ya yarda da laifinsa sannan ya nemi afuwar gidauniyar, ɗalibanta da jagoranta, Sheikh Ɗahiru Bauchi. Gidauniyar ta zargi tsohon gwamnan...
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri kan matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin kawo ci gaba a ƙasar. Tinubu ya ce duk da cewa gwamnatinsa mai sauraron koken jama’a ce, amma yana so a ƙara haƙuri domin akwai haske nan gaba. Minista ya caccaki El-Rufai kan sukar Tinubu da APC Sojoji sun hallaka shugabannin ’yan bindiga 2 da wasu a Katsina Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ta ruwaito Tinubu yana wannan furuci ne a ranar Juma’a, yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar fastocin Cocin Katolika ta Catholic Bishop’s Conference of Nigeria (CBCN) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Ya bayyana wa malaman cocin cewa ya ɗauki matakai masu...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba. Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar. MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja Ya jaddada cewa kawai Kotun Ƙoli ce ke da ikon sauya hukuncin mayar da Sanusi kan karagar mulki. “Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke hukuncinta na baya ba. Kawai dai ta dakatar da aiwatar da shi har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci na ƙarshe,” in ji Dederi yayin da yake magana...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai domin tabbatar da kyakkyawan makoma ga ƙasar. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Kano: Gobara ta kashe mutum 7 da lalata kadarorin N50m a Fabrairu “Tsawon shekaru 50, Najeriya na kashe kuɗin ’ya’yanmu wajen samar da man fetur ga maƙwabtan ƙasashe. Dole ce ta sa muka tsara makomar yaranmu,” in ji shi. Shugaban ya amince da cewa ana fuskantar ƙalubale...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh, a wani artabu da suka yi da shi a dajin Gidan-Abe da ke kan iyakar Bwari da Kaduna. Sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan shigowar ‘yan bindiga yankin daga Kaduna. NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, Olatunji Rilwan Disu, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane, ƙarƙashin jagorancin Mustapha Muhammed, sun tare hanyar ’yan bindigar, inda suka yi musayar wuta da su. “Mun yi nasarar...
Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46. Tinubu ya bai wa Farfesa Jega muƙami a gwamnatinsa PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani...
Ya bayyana cewa samun damar karɓar baƙuncin wannan babban taro wata gagarumar nasara ce ga Nijeriya, kasancewar ita ce ƙasar Afirka ta biyu da za ta karɓi baƙuncin taron. Ya ce: “Wannan babban cigaba ne ga Nijeriya kuma yana da alaƙa da manufofin gwamnatin mu na inganta martabar ƙasar a idon duniya. A daidai lokacin da muke aiwatar da muhimman sauye-sauye da ƙarfafa matsayar mu a duniya, karɓar baƙuncin WPRF wata alama ce cewa duniya tana kallon Nijeriya. “Gwamnati za ta bayar da cikakken goyon baya don tabbatar da nasarar wannan taro.” Ya kuma bayyana wata muhimmiyar nasara, inda ya ce Nijeriya ta samu damar karɓar baƙuncin Cibiyar UNESCO ta Mataki na Biyu kan Ilimin Kafofin Watsa...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Ta buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba. A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma. Ta tunatar da mahalarta...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da iyalin su al’ada. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shin ko mene ne matsayin buɗa-baki tare da iyali a watan Ramadana? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da...
Daliban da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Tarayya ta Joseph Sarwuan Tarka da ke Jihar Binuwai sun kubuta. Daliban sun lubauta ne bayan shafe kwanaki takwas a hannun ’yan ta’addan.
Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba. Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar. Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni. “Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya...
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta samu sahalewar Shugaban Ƙasa na ƙara daukar sabbin ma’aikata. Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Aifi, na ya sanar da haka, a yayin ƙaddamar da Baban Ofishin Yanki na Hukumar a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya a ranar Laraba. “Nan gaba kaɗan za mu ɗauki ’yan Najeriya masu kyawawan ɗabi’u a matsayin jami’ai a Sibil Difens, kuma muna godiya ga shugaban ƙasa bisa wannan dama da ya ba hukumar,” in ji shi. Ya bayyana cewa Hukumar ta fara shirye-shiryen ɗaukar sabbin, amma sai nan gaba za ta sanar da ranar fara ɗaukar tasu. An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna An kama korarren jami’in tsaro da...
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) ta samu sahalewar Shugaban Ƙasa na ƙara daukar sabbin ma’aikata. Babban Kwamandan Hukumar, Ahmed Aifi, na ya sanar da haka, a yayin ƙaddamar da Baban Ofishin Yanki na Hukumar a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke yankin Babban Birnin Tarayya a ranar Laraba. “Nan gaba kaɗan za mu ɗauki ’yan Najeriya masu kyawawan ɗabi’u a matsayin jami’ain Sibil Difens, kuma muna godiya ga shugaban ƙasa bisa wannan dama da ya ba hukumar,” in ji shi. Ya bayyana cewa Hukumar ta fara shirye-shiryen ɗaukar sabbin, amma sai nan gaba za ta sanar da ranar fara ɗaukar tasu. An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna An kama korarren jami’in tsaro da ke...
Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince da yi wa dokar da ta kafa Hukumar Tace Fina-finai ta jihar gyare-gyare. Ɗaya daga cikin sabbi gyaran da aka yi mata shi ne na wajabta wa masu wuraren bukukuwa da taruka yin rajista da hukumar. Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa Kwamitin majalisa ya yi watsi da ƙorafin Natasha a kan Akpabio Wannan mataki ya zo ne saboda yadda ayyukan hukumar ke jan hankali, inda sau da yawa ake samun saɓani tsakaninta da wasu. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawal Husaini Dala ne, ya bayyana cewa an yi wannan dokar gyara ne don daidaita harkokin ɗaukar fina-finai da kare addini da al’adu. Ya ce daga yanzu...

A ɗakin otel muka tsinci gawar tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya — ’Yan sanda
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano. Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da kuma tsarin zamantakewar al’ummar jihar. ’Yan TikTok ɗin da suka haɗa da Ahmad Isa da Maryam Musa waɗanda dukansu ’yan unguwar Ladanai ne da ke yankin Hotoro ne. Sun gurfana a kotu ne bayan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta cika hannunta da su. Jami’an tsaro sun hana jama’a kwasar mai bayan hatsarin tanka a Taraba Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina. ’Yan bindigar sun sace daliban ne a ɗakunan kwanansu da ke yankin Paris Quarters a garin na Dutsinma. Maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kutsa yankin ne da misalin ƙarfe 4 an asubahin ranar Lahadi, suka yi awon gaba da ɗaliban. Jami’an tsaro sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, amma kafin su isa wurin ’yan bindigar sun riga sun riga sun tsere da ɗaliban. Dutsinma na daga cikin ƙananan hukumomin Jihar Kastina da suka fi dama da matsalar ’yan bindiga da ke satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, duk kuwa da matakan da gwamnati da kuma hukumomin...
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki. Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi. Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan Ramadana Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.” ’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi...
Wata kotun majistare da ke zamanta a Ago Iwoye, Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 21, Adebanjo Segun, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kaza. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar tsaro ta Civil Defence , Dyke Ogbonnaya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. An ce an fara samun matsalar ne a ranar Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025, kan Adebanjo mai shekara 21 a lokacin da aka kama shi da laifin satar kaza. Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sanda Ogbonnaya ya bayyana cewa, “Bayan an yi nazari...
An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda. An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba. An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa An maye gurbinsa da Mojisola Meranda, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar kai a majalisar da kuma jam’iyyar APC mai mulki a Jihar. Rahotanni sun nuna cewa an matsa wa Meranda da ta sauka daga muƙaminta, bayan da ake zargin cewa Shugaba Bola Tinubu bai gamsu da sauke Obasa daga muƙaminsa ba. A safiyar ranar Alhamis, labari ya...
Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan ya faɗo daga benen wani katafaren kanti. Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Cikin wani dogon saƙo da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin. “Muna baƙin ciki da samun labarin mutuwar Abubakar Lawal. Wannan lamari ne...
Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a. A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna. Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina A yayin da mu’amala tsakanin jinsi ɗaya ta halasta a wasu yankunan ƙasar mafi rinjayen musulmi a duniya, sai ɗabi’ar ta haramta a lardin Aceh da aka ayyana dokokin shari’ar Musulunci. Tun a watan Nuwamban bara ne dai ’yan sanda masu ɗabbaka shari’a suka kama mazajen biyu da ke karatu a wata jami’a suna aikata wannan alfasha a wani...
A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun tsayar da su domin tuhuma bisa zargin cewa masu yi wa ’yan bindigar daji leƙen asiri ne. NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji Wannan harbin da suka yi ya yi sanadiyar mutuwar wannan ɗalibi mai suna Saidu Abdulkadir. Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya an kama wani ɗalibin jami’ar yana safarar makamai....
Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda. Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya. Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya ce dubun dan shekara 65 din mai suna Nehemiah Sunday Udo ne a ranar Asabar baya al’ummar kauyen Ekpene Obo da ke Ƙaramar Hukumar Esit Eket sun ritsa shi. John ya ce bayan samun kira daga al’ummar yankin ne ’yan sanda suka kai samame inda suka samu mutanen sun kai wanda ake zargin fadar basaraken yankin. Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan...
Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai mai hankali da zai goyi bayan APC a zaɓen 2027. PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, baya aikin komai sai ɗumama kujera. Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Haka kuma, ana zargin gwamnatin Jihar Kaduna da dakatar da rarraba kayayyakin koyarwa da Sanata Lawal Adamu ya saya domin amfanin makarantun jihar. Yusuf Dingyadi, Mataimaki na Musamman na Shugaban PDP kan Yaɗa Labarai, ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta haɗa kai da wakilan jama’a don ci...
Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu. An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe Gini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini. Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa. Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta...
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa a ƙetare har na tsawon kwanaki 90. DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da binciken ne a dalilin ruɗanin da ya dabaibaye duniya wanda ke cin karo da muradun Amurkan. Haka kuma, Shugaba Trump ya ce za a...
Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sake jaddada cewa ƙasashen waje ne ke tallafa wa ’yan ta’addan Boko Haram da kuɗi da makamai. A wata hira da ya yi da Al Jazeera, Janar Musa ya nuna damuwa kan yadda ƙungiyar ke ci gaba da aikata ta’addanci sama da shekaru 16, duk da ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi na daƙile. Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Ya bayyana cewa an kama wasu ’yan Boko Haram ɗauke da maƙudan kuɗaɗe da ke da alaƙa da ƙasashen ƙetare. Ya nuna cewa akwai ƙasashen da ke taimaka wa ƙungiyar daga waje. Janar Musa ya yi tambaya cewar: “Ta...
Wani ɗan Nijeriya ɗan asalin Jihar Yobe, Saidu Abdulrahman, ya lashe kambun lambar yabo ta Kundin Bajinta na Duniya a matsayin wanda ɗaukar hotuna kai tsaye cikin sa’a ɗaya. Bayanai sun ce a cikin mintuna 60 Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotuna 897 masu ɗaukar hankali a watan Satumba na bara, lamarin da ba shi damar doke wanda ya lashe kambun na bara da hotuna 500. Makwabta sun kai karar ma’aurata saboda carar zakaransu Kasuwanci: Yadda matan Arewa ke samun arziki daga cikin gidajensu Da wannan ƙwazo ne Kundin Bajinta na Duniya wata Guinness World Records (GWR) ya karrama matashin da lambar yabo. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, matashin ya bayyana cewa, “ina...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su. Lardin Balochistan mai albarkar ma’ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.
An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano. Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi. Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin. Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana: ...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin. An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin. Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
Kotu ta tsare wani ɗan fashi da ya yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe. Matashin da dubunsa ta cika yi wa ɗaliban fyade ne a yayin wani fashi a ɗakunan kwanan ɗalibai mata a cikin dare. Ya yi musu wannan aika-aika tare da yunƙurin kisa ne a daƙinsu kwanan ɗalibai mata da ke wajen harabar jami’ar a yankin Malete a ranar 2 ga watan Disamba, 2024. A yayin gurfanar da matashin a gaban Kotun Majiatare ta Jihar Kwara da ke birnin Ilorin, an tuhume shi da yin amfani da makami wajen yi wa ɗaliban munanan raunuka, tare da yi musu fyaɗe da kuma sace wayoyin iPhone 13 PronMax da iPhone 11 Pro Max. ’Yan sanda na...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ’yan matan. ’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Mazauna yankin sun ce, maharan da suke da yawa sun shiga cikin unguwar ne daga yankin Birnin Gwari, ta Kwalejin fasaha ta Mamman Kontagora da ke Pandogari. Majiyoyi sun ce an kai ’yan matan da...
Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Rundunar ’yan sandan Jihar Alaska ta sanar da cewa, jirgin samfurin Cessna Caraɓan mai fasinjoji tara da matuƙin jirgi ɗaya ne, an samu rahoton ne ranar Alhamis. Jirgin da ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da ƙarfe 4:00 na yamma agogon Alaska (0100 GMT) da ya ɓace. Biranen biyu suna da nisan mil 146 (kilomita 235)...
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron. DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta. An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata...
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe. Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya. Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku...
Hukumar ICPC ta samu gurfanar da Mohammed Idris, wani jami’i a ƙofar shigen shiga wurin Hajji da ɗiban kaya na filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas, kan laifin bayar da bayanan ƙarya da kuma cin da kuɗaɗen haram. A gaban Mai shari’a O.A. Fadipe na kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja, lauyan ICPC, Yvonne Williams-Mbata, ta gabatar da shaida kan yadda bincike ya gano ɓacewar kuɗi har Naira miliyan goma sha ɗaya da dubu ɗari biyu da talatin da huɗu (N11,234,000) a ƙarƙashin kulawar wanda ake tuhuma daga watan Fabrairu 2001 zuwa Afrilu 2021. Yadda Tayar Jirgin Saman Max Air Ta Kama Da Wuta Yayin Sauka A Kano Fashewar Tayar Jirgi A Kano: Gwamnatin Tarayya Ta...
Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna. A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da ɗan wasan ya shigar bayan da ɗan jaridan ya zarge shi da naushin sa. Wannan dai na zuwa ne bayan da ɗan jarida Bozduman ya zargi Osimhe da cin zaraginsa, bayan tashi wasa 3-3 tsakanin ƙungiyarsa ta Galatasary da kuma Dynamo Kyiv. Yanzu haka dai Osimhen na fuskantar bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kai. A makon da ya gabata ne...
A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron. Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya? Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi. Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa. Shekara guda bayan binne shi,...
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya samu rauni a gwiwar dama a lokacin atisayen safiyar Talata, wanda ya hana shi tafiya Spain don buga wasan da ƙungiyarsa ke neman cancantar shiga zagayen 16 na ƙarshe. Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Daƙile Satar Yara A Bauchi Duk da cewa kulob ɗin bai bayyana tsawon lokacin da Lookman zai...
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar. Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari ’Yan sanda sun yi ƙarin haske kan barazanar harin ’yan ta’adda a Kano Ana kuma ci gaba da jefa ayar tambaya ko shin tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi suna haifar da ɗa mai ido ta hanyar kalato wa ƙasar wata riba. Sai dai...
Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada. Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni. Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na...