2025-02-22@15:45:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 286

«jiragen yaki»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya ce kasashen turan guda uku wadanda suka hada da Jamus, Faransa da Ingila sun aiko masa da sako inda suke tabbatar haka. A cikin shugaban Muhammad Eslami ya fadawa tashar talabijan ta Presstv irin ci gaban masu yawa wadanda JMI ta samu a cikin shekarun da suka gabata. Shugaban ya kara da cewa sakon da EU3 ya nuna irin yadda rikicin shirin Nukliyar kasar Iran...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara da cewa zai dorawa hatta kayakin da suke shigowa Amurka daga kasashen Turai, nan gaba, sai dai bai sanya lokaci ba. Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa zai dorawa kasar Canada kashi 25% kan dukkan kayakin da suke shigowa kasar. Sai mna Desel, inda zai sanya kashi 10% kacal.
    Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai  rabi da rabi, a wasu wuraren ma dai sai dai kasusuwa. Ya zuwa yanzu dai an sami gawawwakin da sun kai 458 kamar kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu Dr.  Khalil Dakran ya ambata. Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa tana kirdadon cewa za a iya samun gawawwakin da suke tsakanin 4000, zuwa 5000 a karkashin baraguzai a fadin Falasdinu.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan da Gwamnatin Kano ta sanar cewa ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aura da ’yan mata da zawarawa a jihar batun ke ta shan suka daga ɓangarori daba-daban. Wasu na ganin jihar na da wasu buƙatun da suka fi auren gatan muhimmanci da ya kamata gwamnatin ta fi mayar da hankali a kansu. NAJERIYA A YAU: Anya Jam’iyyar PDP Za Ta Kai Labari A Fagen Siyasar Najeriya Kuwa? DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya A Yau na wannan rana ya yi nazari ne kan dalilan da Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan biyu da rabi don aurar da ’yan mata da...
    Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a ragar Manchester City bayan da ɗan wasan baya Nathan Ake ya tafka kuskure. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates  Duk da ƙwallon da Haaland ya ci bai hana Arsenal raga raga da City a wasan mako na 24 na gasar Firimiyar  ba, wannan sakamakon ya sanya magoya bayan ƙungiyar sa...
    Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Ukraine da aka dakatar a yakin da ake yi da Rasha, suna bukatar a gduanar da su. “Yawancin kasashen dimokuradiyya suna gudanar da zabe a lokacin yakinsu. Ina ganin yana da mahimmanci su yi haka,”in ji Kellogg. Kamfanin dillancin labaran reuters ma ya rawaito wasu jami’an fadar White House sun tattauna batun matsawa...
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da kasar ke yi na karfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk kasashen da suka nemi tsoma baki a harkar kasarsa. Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama...
    Allah Ya yi wa mahaifin ma’aikacin Aminiya, Abubakar Abdurrahman Adoro, rasuwa. Mahaifin nasa, Farfesa Abdurrahman Lawal Adoro, ya rasu ne a gidansa da ke garin Batagarawa a Jihar Katsina, ranar Litinin 27 ga watan Janairu, 2025, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Katsina, ya yi fama da jinya na wani lokaci. Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja Marigayi Shehin Malami a Sashen Harshen Larabci na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina, inda a nan ya samu matsayin Farfesa. Ya kasance Shugaban Sashen Larabci (HOD) na Jami’ar na farko tun da aka kirkiro ta a shekarar 2006, inda ya yi wa’adi biyu...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
    A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba. Sannan, shin su wa ke amfani da kudaden fansar da ake biya ga masu garkuwa da mutanen? Hasashe ya nuna cewa, mai yiwuwa a yi amfani da kudaden don kara sayen bindigogi da sauran makamantansu.   Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Bukatar Warwarewa A cikin wannan rudani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati...
    Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja. Binciken da wakilinmu ya yi ya nuna cewa, ’yan gudun hijirar sun fito ne daga sassan jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sakkwato a yankin Arewa-maso-Yamma da jihohin Adamawa da Borno da Yobe a yankin Arewa-maso-Gabas. Dangote ya karya farashin man fetur An miƙa wa Majalisar Kano ƙorafin ƙara wa’adin manyan ma’aikatan gwamnati A yanzu haka galibinsu sun fada barace-barace da kananan ayyuka ko sana’o’in da ba...
    Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man fetur daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita a yammacin wannan Asabar.
    An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu. A cikin wata wasika mai kwanan wata 6 ga Janairu, 2025, Sani Usman DanAbdullo, Esq., Daraktan Gudanarwa da Harkokin Gabaɗaya na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), ya buƙaci Majalisa da ta kare doka da oda, tare da dakatar da abin da ya bayyana a matsayin rashin amfani da ikon zartarwa yadda ya kamata. An aike da ƙorafin ne...
    Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa bayyanar irin girman da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suke da shi ya sanya makiya takaici. Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Manjo Janar Baqiri ya aike da sakon murna ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Hossein Salami, a yau Asabar, dangane da bukukuwan watan Sha’aban, ciki har da zagayowar ranar haihuwar Imam Husaini (a.s), wanda ya zo daidai da ranar dakarun kare juyin juya halin Musulunci. Yana mai jaddada cewa; Yana da...
    ‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara. Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin Doga. Ministan ya kara da cewa gwamnatocin Amurka da suka shude daga ciki har da gwamnatin Trumps suka yi a baya musamman ficewarta su daga yarjeniyar JCPOA.  Abbas Argchi ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci wanda dole ne Amurka ta yi idan tana son jawo hankalin iran dangane da tattaunawa da ita shi ne sako kudaden ta masu yawa wadanda ta hana a yi amfani...
    Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran,  shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Asabar ce shugaban kasar Iran, Masuod Pezeshikyan tare da majalisar ministocinsa suka kara sabonta bai’a wato marigayi Immam Khomani (q).   Labarin ya kara da cewa Sayyid Hassan Khomani, jikan Imam(q) wanda kuma yake kula da hubbaren nasa ne, ya tarbi shugaban kasar ya kuma jagorance su zuwa hubbaren kakansa Imam Khumaini(q). Imam Khomani (q) ne ya jagoranci mutanen kasar...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda zasu nunasu nan ba da dadewa ba. Sannan ya kara da cewa dukkan jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aiki na zama, wanda sabbin jiragen saman yakin da ake kerasu a wasu kasashen basu yi gaba da su a wani daga cikin a kayakin aiki na zamani ba. Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda ya nakalto babban kwamnadan...
    “Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da aka kai Legas, ya kai ga kama skunk mai nauyin kilogiram 47, wani nau’in tabar wiwi, da kuma Nitrous Odide mai nauyin kilogiram 25.46 da aka fi sani da dariya a unguwar Akala da ke Mushin,” Babafemi ya kara da cewa. A Jihar Ekiti, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Adepoju Taiwo, dauke da kilo 1.950 na...
    Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya. Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya. Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da  duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
    Bisa alkaluman da hukumar kula da zirga-zirgar layin dogo ta kasar Sin ta bayar, tun daga kaddamar da zirga-zirgar fasinjoji a lokacin bikin bazara na Sin daga ranar 14 zuwa ranar 30 ga watan Janairu, yawan fasinjojin da jiragen kasa suka dauka ya kai miliyan 206 a kasar, kuma an yi zirga-zirgar fasinjojin cikin kwanciyar hankali. Yayin bikin, hukumomin kula da layin dogo na sassan kasar sun kara karfin aiki a wuraren da aka fi amfani da su, da inganta karfin ba da hidimmomin jiragen kasa da tashoshi, da aiwatar da matakan saukakawa jama’a, da kuma kokarin samar wa fasinjoji ingantacciyar hanyar tafiya. Alal misali, reshen Beijing na kamfanin kula da layin dogo na kasar Sin, ya kara tashoshin caji...
    Bugu da ƙari, Naira miliyan 267.6 an ware su domin shirye-shiryen Addinin Musulunci da tallafa wa waɗanda suka Musulunta, yayin da Naira miliyan 589 za a yi amfani da su wajen bincike kan harkokin tsaro da kuma yaƙi da bara a tituna. Jimillar kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719.75, wanda ya karu da kashi 31 daga asalin kuɗin da aka gabatar da farko, kuma ya fi na shekarar 2024 da kashi 65.
    Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga jirgin saman Air France da ya dawo da Imam Khumaini gida daga gudun hijira na sama da shekaru 14 wanda ya kai ga kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin bukukuwan al’ummar Iran suna halartar taruka daban-daban har zuwa zagayowar ranar 22 ga watan Bahman wato 10 ga watan Fabrairu, wato ranar tunawa da juyin juya halin Musulunci. Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai...
    Ana zargin wani ɗan ƙabilar Ibo mai suna Oguchwku da yin lalata yaran makarantar Firamare masu shekaru 9 da 10 da haihuwa, kuma ‘ya’yan Hausawa ne. Aminiya ta bibiyi lamarin a inda ta garzaya Cibiyar Kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Ƙofar Gayan Zariya a Jihar Kaduna. Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya Tankar fetur ta yi bindiga a gidan mai Jigawa Daraktan cibiyar Salama Centre da ke Asibitin Gambo Sawaba ƙofar Gayan Zariya, Hajiya Aishatu Ahmad, ta shaida wa Wakilin namu cewar a ranar 27 ga watan ɗaya na wannan shekarar ne hukumar ‘yan sanda da ke Kasuwar Mata a ƙaramar hukumar Sabon Gari ta kawo wani mai suna...
    Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya jaddada muhimmancin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci da kasar Kazakhstan a wata ganawa da firaministan kasar Kazakhstan Olzhas Bektenov. A yayin taron na ranar Alhamis, Aref ya bayyana bukatar samar da karin kwamitocin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. Bayan goron gayyata day a samu a hukumance daga Bektenov, mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya isa kasar Kazakhstan a ranar Alhamis domin halartar taron koli na shugabannin gwamnatoci mambobi a kungiyar tattalin arzikin Eurasia (EAEU) da taron Almaty Digital Summit 2025, wanda aka shirya gudanarwa daga ranar 31 ga watan Janairu zuwa 1 ga Fabrairu. Iran wadda a baya-bayan nan ta samu matsayin mamba mai sanya ido a...
    Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta kwashe yara 2,500 da suka jikkata a yakin da Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi a Gaza domin samun kulawar gaggawa. Rokon nasa ya biyo bayan ganawar da ya yi da likitocin Amurka ne wadanda suka yi gargadin cewa yaran na fuskantar barazanar mutuwa a makonni masu zuwa. Likitocin hudu, wadanda suka yi aikin sa kai a Gaza sun bayyana mummunan halin da yanayin  kiwon lafiyar yankin ke ciki, wanda yakin ya yi wa illa. Guterres ya ce ya ji dadin matuka  bayan tattaunawarsa da likitocin Amurka ranar Alhamis.  Ya kuma”Dole ne a kwashe yara 2,500 ba tare da bata lokaci ba, tare da ba...
    Dakta Tingilin ya ce a cikin wannan shekarar, gwamnatin Jihar Katsina ta yi kasafin kudi na naira miliyan dubu 50 domin tabbatar da samar da tsabtataccen ruwan sha a kananan hukumomi 20 na cikin jihar. Ya kara da cewa kwamitin karbar korafe-korafe da aka kafa, an kafa shi ne domin duba aikace-aikacen shirin SURWASH da ake gudanarwa ga al’ummar a jihar.
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada aniyar Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a dukkan fannoni Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a fannoni daban daban. Wannan ya zo ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi a birnin Doha a jiya Alhamis, tare da fira ministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani. Taron ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi bangarorin biyu, da suka hada da ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yankin,...
    Adadin jigilar fasinjoji da jiragen kasa masu zirga zirga cikin biranen kasar Sin suka yi a shekarar 2024, ya karu da kimanin biliyan 2.8 ko kuma kaso 9.5 a kan na shekarar 2023. A cewar ma’aikatar kula da sufuri ta kasar, a baran, jimilar jigilar fasinjoji da jiragen suka yi ya kai biliyan 32.24. Zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2024, tsawon tafiyar da jirage 325 suka yi a fadin birane 54 na kasar Sin, ya kai kilomita 10,945. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar. Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su. Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a Sweden Kwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi. Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma. Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a...
    Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
    Sowore, wanda ya taɓa tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa, na fuskantar tuhume-tuhume guda 17 daga rundunar ‘yansanda, ciki har da laifi a kafafen sada zumunta da kuma kiran Shugaban ‘Yansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, da “IGP na ƙarya.”
    An harbe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani, Salwan Momika, ɗan asalin ƙasar Iraƙi mai shekaru 38, a gidansa da ke Södertälje, kusa da birnin Stockholm a Sweden. A harbe shi lokacin da yake ƙoƙarin wallafa bidiyo a kafar TikTok. Sarkin yaƙin Zazzau ya rasu ana tsaka da taro  Hisbah ta kama masoya kan yin aure ba tare da amincewar iyayensu ba Salwan Momika, ya ƙone Al-Ƙur’ani a 2023 a wajen Babban Masallacin Birnin Stockholm, lamarin da ya jawo cece-ku-ce da zanga-zanga a ƙasashen Musulmi. Lamarin ya haifar da rikicin diflomasiyya, ciki har da kai hari ofishin jakadancin Sweden da ke Bagdad, da kuma korar jakadan Sweden da ke Iraƙi. A halin yanzu, ’yan sanda sun kama mutum biyar da ake...
    Masarautar Zazzau, ta sanar da rasuwar Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro. Marigayin, ya rasu ne a Asibitin Gambo Sawaba lokacin da ya halarci taro a asibitin. Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a Tiktok Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Masarautar, ta bayyana cewa za a yi jana’izarsa a gidansa da ke Rimin Doko, Unguwar Kaura, cikin Birnin Zariya.   Cikakken bayani na tafe…
    Hukumomi a birnin Quetta na Ƙasar Pakistan, sun kama wani mutum mai shekaru 50, kan zargin kashe ’yarsa mai shekaru 15 a duniya, saboda ta ƙi daina ɗora bidiyonta a kafar TikTok. Rahoton ’yan sanda ya nuna cewar, mutumin ya dawo da iyalinsa daga Amurka zuwa Pakistan kwanan nan kafin aikata kisan. Hisbah ta kama masoya kan yin aure ba tare da amincewar iyayensu ba Wata uku uami’o’i ba su da wutar lantarki —SSANU Ya amsa laifin harbe ’yarsa, inda ya ce tana aikata abubuwan da ba su dace da addini da al’ada ba, ta hanyar saka bidiyo a TikTok. An kuma kama ɗan uwansa kan zargin taimaka masa wajen aikata laifin. Dukkaninsu sun nuna rashin amincewa da yadda matashiyar...
    An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC. Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare. Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye. DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen...
    An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC. Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare. Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye. DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen...
    Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba. Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi. Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta. “Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.” An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran. “A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta...
    Kungiyar fursunonin Falasdinu ta ce za a sako wasu karin Falasdinawa 110 daga gidajen yarin Isra’ila a yau Alhamis a mataki na uku na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas. Ana sa ran galibin Falasdinawan da aka ‘yantar za su isa yankin Radana na Ramallah da ke yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye da misalin karfe 12:00 na safe agogon kasar, in ji kungiyar fursunonin Falasdinu. Wannan ba zai hada da fursunoni 20 da za a tura gudun hijira a wajen Falasdinu ba. Kungiyar ta kuma fitar da jerin sunaye da shekarun fursunonin da za a saki wadanda suka hada da akalla yara 30. Sakin da za’ayi wa Falasdinawan 110 a yau zai sanya...
    Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba. Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na Naira dubu 70 da sauran sauye-sauye da ke tattare da shi zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar nan ta 2025.   Shugaban Ƙungiyar SSANU ta Kasa, Kwamred ohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a yayin taron Majalisar Tuntuba ta Ƙasa (NAC) da ƙungiyar ta gudanar a Abuja. Kwamred Ibrahim ya bayyana cewa har yanzu Gwamantin Tarayya da na wasu jihohi ba...
    Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu. A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji. A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wasu gidaje da rumbun ajiya a sansanin Tulkaram a Gabar yamma da Kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa gidaje da rumbun adana kayayyaki a sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkarm da ke Gabar yammacin Kogin Jordan a cikin daren jiya, inda haka ya yi sanadiyyar tashin gobara. Shafin watsa labaran Falasdinawa na yanar gizo ya bayyana cewa: Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun tarwatsa wani rumbun ajiyar kaya da ke kasan benen wani ginin da ke unguwar Al-Wakala a tsakiyar sansanin, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara mai tsanani ta ya shafi wani shagon sayar da silinda gas da ke yankin da wasu gidaje da yawa...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan yi rangadi a wurare daban daban kafin bikin bazara na kasar, kana kafin bikin na wannan shekara, shugaban ya ziyarci lardin Liaoning dake arewa maso gabashin Sin. Sai dai wadanne fannonin ya mai da hankali a kai, yayin wannan ziyara? Abu na farko da shugaba Xi ya lura da shi, shi ne aikin sabunta fasahohin masana’antu. A rangadinsa na wannan karo, shugaban ya ziyarci wata masana’antar sarrafa kayayyakin karfe, inda ya duba yadda ake kokarin amfani da sabbin fasahohi a wurin, kana ya nanata bukatar samar da kayayyaki masu inganci, wadanda ba za su gurbata muhalli ba. Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari Gwamna Nasir Ya Ƙaddamar da Aikin Titin Koko–Zuru...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Ya gargaɗi kamfanonin da suka samu kwangilar da su tabbatar da ingantaccen aiki, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗan aikin. Sannan, ya buƙaci direbobin manyan motoci da su guji lodin da ya fi ƙarfin titin domin kare lafiyar matafiya da rage hatsari. Don haka, gwamnati za ta kafa kwamiti don tabbatar da bin doka da oda a kan titin. Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Abdullahi Umar Faruk, ya bayyana cewa kashi 40 na kuɗin aikin an riga an biya. Ya ce an biya kamfanonin kuɗin kamar haka: Kamfanin ZBBC zai shimfiɗa titin daga Dabai zuwa Mahuta (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18. Kamfanin Habib Engineering LTD zai yi aikin daga Mahuta zuwa...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Dole ne kasashen duniya su gane irin wahalhalun da al’ummar Iran ta sha wajen yaki da ta’addanci Jakadan kasar Iran na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya aike da wasika ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dangane da laifukan da kungiyar ta’addanci ta munafukai {MKO} ta aikata, wanda ya yi sanadin shahadan mutane 23,323, Irawani ya bukaci kungiyoyin kasa da kasa sun yi furuci da ire-iren wahalhalun da al’ummar Iran suka sha tsawon shekaru da dama da kuma wadanda suka yi shahada a fagen yaki da ta’addanci. A cikin wannan sakon, Irawani ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta himmatu wajen aiwatar da dokokin kasa da kasa...
    Majalisar Dokokin Amurka zata dauki matakin fitar da dokar da zata hukunta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya saboda kotun ta tabbatar da zarge-zargen manyan laifukan gwamnatin mamayar Isra’ila Ana sa ran nan kusa kadan Majalisar Dattawan Amurka za ta fara kada kuri’a kan kakaba takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta duniya da ke birnin Hague, bayan da kotun ta tuhumi fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohun ministan yakinsa Yoav Gallant a watan Mayu da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a Zirin Gaza. A cewar jaridar Washington Post, ‘yan majalisar dokokin Amurka suna matsawa wajen zartar da dokar, wadda za ta sanya takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa, yayin...
    Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...
    Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya samu rauni a gwiwar dama a lokacin atisayen safiyar Talata, wanda ya hana shi tafiya Spain don buga wasan da ƙungiyarsa ke neman cancantar shiga zagayen 16 na ƙarshe. Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Daƙile Satar Yara A Bauchi  Duk da cewa kulob ɗin bai bayyana tsawon lokacin da Lookman zai...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke dasu da kuma cikakken goyon bayan Amurka. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : tsayin daka da aka fara a Iran din, ya jawo farkawar wasu al’ummar musulmi kuma durkusar da Isra’ila a Gaza da Labanon misali ne. Jagoran ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ganawa da jakadun kasashen musulmi a birnin Teheran, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar aiko da sakon annabta ga Manzon Allah Muhammad (SAW). Jagoran ya ce “A yau, bayanin da muke bayarwa na mulkin mallaka da girman kai yana bayyana gaba daya...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna. Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi hare-hare. Sojoji sun ƙwato tarin makamai a Zamfara Tankar mai ta sake fashewa a Neja Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja a ranar Talatar nan, mai magana da yawun rundunar, Benneth Igweh, ya ce sun samu nasarar ce ta hanyar bayanan sirri, inda suka cafke wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Igweh ya bayyana...
    Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang ya ce, ya kamata kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sudan, inda kuma ya bukaci gamayyar kasa da kasa da ta kara taka rawar gani wajen sasanta rikici a kasar. Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya, yayin wani taro da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira don tantance rahoton da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta gabatar dangane da batun Darfur na kasar Sudan. A cewar Geng, yayin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke gudanar da bincike a kasar Sudan, ya kamata ta yi mu’ammala sosai da gwamnatin kasar Sudan, kafin daukar wani mataki, ta yadda za a tabbatar da...
    A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma  kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne. Sannan hukumar ta fara kokarin ganin an sake shi. Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa duk wani hari kan daya daga cikin cibiyoyin Nukliyar kasar Iran daga HKI ko Amerika, wannan wata musiba ce da yankin, kuma wadanda suka kai harin zasu gamu da maida martani ba tare da jinkiri ba. Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a wata hirar da ta hada shi da tashar talabijin ta Sky News a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa, ban tsamman zasu yi haka ba. Amma idan sun, to kuwa ba zasu ji ta da dadi ba. Yace: JMI ta rattaba hannu a kan yarjeniyar Nukliya da manya-manyan kasashe 6 a duniya kan shirin ta na makacin Nukliya wanda...
    Bayan hare haren da mutane suka kai kan ofisoshin jakadancin kasashen Ugandan, Rwandan, Kenyan, Japan, Amurka da kuma Faransa a birnin Kinshasa na kasar Democradiyya Congo masu zamga-zanga sun fara kwasar ganima a manya-manyan shaguwa a birnin. Masu zanga-zangar sun fara tada hankali a kasar ne saboda irin saurin ci gaban da yan tawayen M23 suke mamayar kasar. Kuma suna ganin wadannan kasashe suna da hannu a tallafawa yan tawayen wadanda suke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun sojojin Gwamnati. Labarin ya kara da cewa an ga hayaki na tashi a ofishin jakadancin kasar Faransa a Kinshasa, kuma suna yin haka ne don nuna turjiya ga halayen mulkin mallaka na kasar faransa, wacce take daga cikin wadanda suke goyon...
    Ga shirin “the pen writes the dragon and snake”(shirin da ya nuna fasahar rubutu na Sinanci da wasan Kunfu) na cikin Shagalin Bikin Bazara na CMG, zai kayatar da ku.
    Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran zai karbi bakwancin tawagar jami’an kasar da jakadun kasashen musulmi A cikin sa’o’i masu zuwa ne Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei zai karbi bakwancin wasu tawagogin jami’an kasar, baya ga wakilai da jakadun kasashen musulmi. Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa: Wannan taro ya zo ne domin murnar tunawa da zagayowar ranar aiko fiyayyen halitta, Manzon Tsira Muhammadu dan Abdullahi (s.a.w) da sakon addinin Musulunci ga dukkan talikai wanda ya yi daidai da yau Talata 28 ga watan Janairu, kuma daidai da ranar 27 ga watan Rajab shekara ta 1446 bayan hijira.
    Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci. A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza...
    A cim ma burin Gwamna Umar Namadi na ci gaban bil’adama a cikin ajandar mai dauke da abubuwa 12, majalisar zartaswar jihar Jigawa ta kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin samar da hanyoyin da za a bi wajen nemo masu hazaka domin karfafa kirkire-kirkire a tsakanin matasa masu tasowa a jihar.   Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka bayan taron majalisar da aka gudanar a Dutse.   Ya ce, kwamitin ya kunshi kwamishinonin lafiya, muhalli, kananan hukumomi yayin da kwamishinan ilimi mai zurfi zai zama shugaba.   Sauran mambobin sun hada da masu ba da shawara kan fasaha, ICT da tattalin arziki na dijital, ilimi mai zurfi, aikin gona,...
    Babban Kotun Jihar Kano ta rundunar ’yan sanda sake kamawa, gayyata ko tsare Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jihar Jihar Kano (PCACC), Magaji Rimingado. Kotun ta ba a da umarnin ne bayan  ƙarar da Babban Lauyan jihar Kano da hukumar PCACC da kuma Magaji Magaji Rimingado suka shigar. Waɗanda ake ƙara su ne rundunar ’yan sandan Najeriya, Sufeto-Janar na ’yan sanda da Mataimakinsa Ma kula da Shiyya ta Ɗaya da Kwamishinan ’Yan Sanda Kano da ASP. Ahmed M. Bello da Bala Muhammad Inuwa. Kotun ta ɗage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairu, 2025. A ranar Juma’a ’yan sanda sun kama shugaba na hukumar da yamma, inda suka tsare shi na tsawon awanni, daga baya ba...
    Wani shaida ya bayyana wa kotu yadda tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Sanata Hadi Sirika ya ba wa kamfanin da bai cancanta ba aikin gyaran Filin jirgin Katsina a kan Naira biliyan 2.8. tsohon Daraktan Sayayya ne a ma’aikatar, Musa Obinyan ya bayyana wa kotu cewa a lokacin da Hadi Sirika yake ministan ba wa Kamfanin Al Buraq Investment Ltd, aikin gyaran filin jirgin, alhalin kamfanin bai cancanci a ba shi aikin ba. Musa Obinyan ya shaida wa Babbar Kotun Abuja cewa rufa-rufa aka yi aka ba wa Al-Buraq, sannan nemo kuɗin aikin aka yi daga wani wuri aka biya. Ya ba da shaida ne a ci gaba da sauraron shari’ar da Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin (EFCC)...
    Ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar da cewa Falasdinawa kusan 300,000 da suka rasa matsugunansu ne suka koma gida a gabar tekun a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma da kungiyar Hamas. “Wannan ya zo ne bayan kwanaki 470 na kisan kiyashi da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi,” in ji sanarwar, wanda ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 47,000 tare da lalata wargaza yankin Falasdinawan. An bayyana cewa sama da kashi 90%, yankin ya lalace sakamakon hare haren Isra’ila. An ruguza duk wasu wurare da cibiyoyi masu matukar mahimmanci kama daga asibitoci, makarantu, gidajen jama’a wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki. A yanzu Falasdinawan dake komawa wannan yankin...
    Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci. Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina. Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba. “Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba. “Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko. “A yanzu na ƙara...
    A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano Shugaba Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) kuma shugaban kwamitin tsakiya na sojojin kasar ya kara da cewa, “a cikin shekarar dabbar Dragon, mun nuna kuzari da ruhi mai karfi na iya aiwatarwa. Mun...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci: An murkushe dukkanin daidaito a gaban mutanen kudancin Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana abin da ya faru a kudancin kasar Lebanon a matsayin murkushe dukkanin daidaito na siyasa da lissafin abin duniya. A cikin wani rubutu a dandalin “X”, Ayatullahi Sayyid Khamenei ya nuna cewa an murkushe wadannan daidaito a gaban mutane masu aminci da aminci a kudancin Lebanon. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la’akari da cewa: Al’ummar kudancin kasar Labanon ba su damu da sojojin yahudawan sahayoniyya da suka yi kaca-kaca da su ba, suna kuma kai rayukansu zuwa fagen fama da rashin son kai da kuma dogaro da alkawarin Ubangiji.
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kera wani jirgi maras matuki ciki mafi girman da suka Sanya masa suna “Gaza” A jiya Lahadi, a gefen atisayen soji mai taken “Manzon Allah Mai Girma na 19” da aka gudanar da gwajin makamansu, sun samu nasarar gwajin sabon jirgin sama maras matuki ciki mai suna “Gaza” wanda ake daukansa a matsayi mafi girman jirgin saman maras matuki ciki da zai iya yin luguden wuta mafi girma da tsanani, jirgin yana cin dogon zango kuma shi ne mafi girma da Iran ta kera wajen kai farmakin da zai jefa bama-bamai 8 akan wurare 8 a kasa. Jirgin Gaza maras matuki (wanda ake kira Shahed 149) shi ne jirgi mara matuki...
    Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya baiwa al’ummar jihar Zamfara aniyar rundunar sojojin Najeriya wajen ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.   Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau.   Kungiyar WASA wani taron ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin murnar dimbin al’adun gargajiya na wannan kasa mai girma.   Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu a cikin annashuwa don bikin da kuma nuna ƙarshen ayyukan shekara.   Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon. ‎Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar...
    Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe. An gurfanar da masoyan da suka kai wa malami hari a Kano Kotu ta ɗaure matashi shekara 2 kan satar wayoyi a Kano Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wasu nakiyoyi da wani mutum ya ɓoye a wajen domin aikin haƙar ma’adinai. Lamarin ya yi sanadin lalacewar gidaje kusan 12 a yankin, inda ya jefa al’umma cikin tashin hankali. Fatima Sadauki ta rasa ranta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi  wanda ya jagoranci tawagar yan siyasa da kuma tattalin arzikin kasarsa zuwa birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan, a yau Lahadi sun tattauna al-amura masu muhimmanci  tsakaninsu da kuma yanking aba daya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa ministan ta hadu da tokwaransa na rikon kwarya Amir Khan Muttaki a birnin Kabul inda suka tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu. Wadanda suka hada da al-amuran kan iyakokin kasashen biyu, tsaro, ruwa da hakkin ko wace kasa kan ruwan da ke kwarara daga kasar Afganistan zuwa kasar Iran. Da batun miliyoyin yan kasar Afgansitan wadanda suke rayuwa a kasar Iran na shekaru kimani 50. Ministocin biyu sun tattauna al-amura...
    Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey  Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...
    Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada. Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni. Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na...
    Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
    Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
    Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.