2025-03-28@15:52:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1769
«juyin juya halin Musulunci ya»:
A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda 60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818 sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune, kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
Har ila yau, Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya aike wa hukumomin tsaro wasiƙa yana sanar da shirinsa na gudanar da bikin. Gwamnatin jihar da masarautar Kano har yanzu ba su ce komai ba kan wannan haramci ba. Wannan mataki na zuwa ne bayan da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke shirinsa na yin hawan, yana mai cewa sun ɗauki matakin ne bayan shawarar da malamai da dattawa suka ba shi. “Muna tabbatar muku cewa hawan Sallah ba abu ne na ko a mutu ko a yi rai ba, idan har zai haddasa tashin hankali, wajibi ne a dakatar,” in ji Aminu Ado Bayero. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta haramta gudanar da bukukuwan hawan sallah da aka saba yi na al’ada a faɗin Jihar Kano. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya fitar a wani taron manema labarai da ya gudana a hedikwatar rundunar da ke Bompai a wannan Juma’ar. Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno ECOWAS ta gyara cibiyar magance shan miyagun ƙwayoyi a AKTH CP Bakori ya ce hakan na cikin shawarwarin tsaro da rundunar ta bai wa mazauna jihar gabanin bukukuwan ƙaramar sallah da za a soma ranar Lahadi ko Litinin. Sanarwar ta ce rundunar za ta baza jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da bin doka da oda a...
Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), ta kammala gyara wata cibiya don kula da masu fama da shan miyagun ƙwayoyi a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH) da ke Kano, tare da miƙa ta ga asibitin domin amfanin jama’a. Jami’in ECOWAS mai kula da shirin hana yawaitar shan miyagun ƙwayoyi, Dokta Daniel Akwasi Amankwaah, ya ce wannan cibiya na daga cikin ƙoƙarin ƙungiyar wajen rage yawaitar shan ƙwayoyi da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga masu buƙata. Tinubu zai sake zama shugaban ƙasa a 2027 — Akpabio ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano A yayin bikin miƙa cibiyar, Dokta Amankwaah, ya jaddada aniyar ECOWAS na yaƙi da matsalar shan...
Ina mika sakon gaisuwata ga iyayena da yayyena da kannena, ‘yan uwana maza da mata wadanda muka yi makaranta tare da su, al’ummar Musulmi baki daya, duk ina yi muku fatan alkhairi tare da fatan an yi Juma’a lafiya. Allah ya maimaita mana, ina gaida mijina tare da yi masa fatan alkhairi da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya. Sako daga Yusuf Murtala Assalaikum alaikum, Al’ummar Musulmi, ina yi wa kowa fatan alkhairi tare da fatan an yi Sallar Juma’a lafiya Allah ya maimaita mana. Ina gaida iyayena ina yi musu fatan alkhairi da fatan sun yi Sallar Juma’a lafiya, Allah ya maimaita mana. Sannan kuma ina gaida ‘yan uwana yayyena da kannena da fatan sun yi Sallar Juma’a...
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu nasarar lashe zaɓe don yin wa’adi na biyu a 2027, duk da ƙoƙarin ’yan adawa na ƙalubalantarsa. Yayin da yake jawabi a wajen liyafar buɗa-baki da ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC (PGF) ta shirya a Abuja, Akpabio ya nuna ƙwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulki. Sallah: Hadimin gwamnan Sakkwato ya bai wa magoya bayan APC kyautar N22m ’Yan sanda sun ƙwato wa mutumin da aka sace kuɗin fansarsa a Kano “Za mu dawo a 2027, da sunan Yesu, Amin,” in ji shi. “Za mu yi wa jam’iyyarmu da Shugaban Ƙasa addu’a. Wa’adin mulkinsa na biyu ya tabbata.” Liyafar, wacce gwamnonin APC, ’yan...
Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane Radan a matsayin ranar Kudus ta duniya tun fiye da shekaru 40 da suka gabata, kuma ana ci gaba da gudanar tarukan wannan rana a kowace shekara a Iran da sauran sassa na duniya.
“Jami’an ‘yansanda da ke ofishin ‘yansanda, Mayo Belwa, sun isa wurin, inda nan take suka garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibitin Cottage, Mayo-Belwa, domin kokarin ceton ransa, amma abin takaici, an tabbatar da mutuwarsa a lokacin da ya ke karvar magani.” Kakakin rundunar ‘yansandan ya ce, ya yi saurin shiga tsakanin wanda ake zargin da matasa suka kama shi domin cetonsa daga hannun matsan inda aka garzaya da shi asibiti. Ya ci gaba da cewa wasu matasa a yankin da lamarin ya faru sun bi sawu inda suka kama daya daga cikin wadanda ake zargin ’yan fashi da makami ne kuma suka damke shi. Ya gargadi mazauna jihar kan yin yin hukuncin nan na daukar doka a hannunsu...
A safiyar yau ne aka fara gudanar da jerin gwano na ranar Qudus ta duniya a duk fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda aka samu halartar jama’a da dama karkashin taken “Muna ci gaba da cika alkawarin da muka dauka.” Mahalarta taron za su yi tattaki ne daga masallatai da manyan filaye a birane da kauyukan kasar zuwa wuraren da ake gudanar da Sallar Juma’a. A birnin Mashhad da ke gabashin Iran, tun da sanyin safiya ne aka fara gudanar da jerin gwano a wani bangare na bikin na shekara-shekara. A halin da ake ciki dai jama’a a birnin Tehran sun fara taruwa daga wurare daban-daban a kan titin juyin juya hali domin tunawa da wannan rana. A cewar wakilin...
Shugaba Bola Tinubu da takwaransa na Ghana, John Mahama, sun tattauna batutuwa da dama domin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen yammacin Afirka. An gudanar da ganawar ne a Abuja bayan da Mahama ya kai wa Tinubu ziyarar ban girma domin yabawa da halartar shugaban Najeriya a yayin bikin rantsar da shi a Accra, babban birnin Ghana. Wannan dai ya zo ne watanni biyu bayan rantsar da Mahama bayan day a sake komawa kan karagar shugabancin kasar Ghana. Daga cikin muhimman batutuwa da shugabannin kasashen na Najeriya da Ghana suka yi dubi a kansu, hard a yadda za a kara karfafa alakoki a dukkanin bangaroria tsakanin kasashen biyu. Baya ga haka kuma sun tabo batun rarrabuwar kawuna da aka samua ...
Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci ta duniya (WFP) ta fitar a Nijeriya, na ishara da cewa mutum miliyan 11 ne a fadin jihohi shida na Arewa maso Gabas da Arewa maso Yammacin Nijeriya ke fuskantar matsalar karancin abinci a shekarar 2025. Kazalika, rahoton ya danganta matsalar da rashin tsaro da ake ci gaba da fuskanta, da hauhawar farashin kayan abinci da man fetur, da bala’in yanayi, da kuma matsugunan jama’a, ya sa miliyoyin mutane ke fafutukar samun abinci mai gina jiki. Rahoton UNICEF ya kara bayyana cewa yara ‘yan kasa da shekaru biyar a Nijeriya, kusan miliyan 11, na fama da matsanancin rashin abinci, wanda hakan ya sa kashi 50 cikin 100 na ka fuskantar barazana ga...
Mai Bai Wa Gwamnan Sakkwato Shawara kan Harkokin Karkara, Malami Muhammad Galadanchi (Bajare), ya bai wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar, kyautar Naira miliyan 22 domin gudanar da shagalin Sallah Karamar. Yayin bayar da kyautar a ranar Alhamis, Bajare ya ce ya yi hakan ne domin nuna godiyarsa ga jagoran APC a jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, da Gwamna Ahmad Aliyu, bisa damar da suka ba shi don ba da gudunmawarsa ga ci gaban jihar. An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Isuhu Yellow a Zamfara Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu “Wannan tallafi saƙon godiya ne daga shugabanninmu zuwa gare ku. Idan ba su ba mu dama ba, ba za mu iya wannan ba. “Kuma muna shirye mu ƙara...
kungiyar ta koka kan cewa bai dace a yi amfani da EFCC wajen kamun Jami’an gwamnatin jihar Bauchi da nufin nuna yatsa wa Gwamna Bala Muhammad wanda ya kasance mai fitowa da hakikanin gaskiyar halin da talakawa ke ciki da nema musu hakkinsu daga wajen shugaban kasa. kungiyar ta lura da cewa in ana amfani da irin wannan salon lallai za a samu nakasu wajen kyautata demukradiyya a kasar nan domin mutane da dama za su yi shiru kan abubuwan da suke tafiya ba daidai ba domin gudun musgunawa. Eyes on Democracy ta kuma nuna shakku kan yadda aka kama Akanta Janar din a lokacin da yake halartar taron FAAC a Abuja, inda ta bayyana cewa hukumar EFCC ba ta...
Rahoton ya bayyana rashin wadataccen abinci mai gina jiki, da wahalhalun tattalin arziki na iya zama ummul-haba’isin muhimman abubuwan da ke haifar da rashin abinci ga yara. A cikin 2024 kadai, Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce ta yi wa yara sama da 300,000 maganin tamowa, doriyar kashi 25 cikin 100 daga 2023. Daga cikin wadannan kaso, 75,000 na bukatar kulawar rashin lafiya mai tsanani, yayin da 250,000 aka basu kulawa ta hanyar shirye-shiryen sama musu lafiya a fadin jihohi bakwai: Borno, Bauchi, Katsina, Kano, Sokoto, Zamfara, da Kebbi. Wakilin kungiyar ta MSF na kasa Dr Simba Tirima ya shaida wa LEADERSHIP cewa kungiyar agajin ta lura da yadda ake samun karuwar masu dauke da cutar, wanda ya zarce shekarun...
Imam sayyid Aliyul Khamina’ie Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran yayi kira ga mutanen kasar su fito kwansu da kwarkwatansu don halattar zanga-zangar ranar Kududs ta duniya a yau Jumma’a. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jagoran yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Alhahamis da yamma. Ya kuma kara da cewa fitowar zanga-zangar ranar Kudus ta duniya alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, sannan cika alkawali ne ga al-ummar kasar Falasdinu kan cewa mutanen kasar Iran ba zasu taba barinsu su, su kadai ba. Ranar Qudus ta duniya dai, rana ce wacce Imam Khomaini (q) wanda ya kafa JMI ya ware a ko wace ranar Jumma’a ta karshe...

Iran Ta Gudanar Da Faretin Jiragen Ruwa A Tekun Farisa Da Kuma Tekun Caspian Don Raya Ranar Kudud Ta Duniya
Jiragen ruwan yaki na dakarun juyin juya halin musulunci IRGC a nan Iran, kanana da manya-manya, har’ila yau da na masu sa kai sun gudanar da faretin jiragen ruwan yaki don raya ranar Kudus ta duniya kwana guda kafin ranar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto dubban jiragen yaki da na masu sa kai a tekun Farisa da ke kudancin kasar da kuma tekun Caspian da ke arewacin kasar suna jerin gwano a cikin ruwayen yankunansu don raya wannan ranar. Dakarun IRGC sun gudanar da wannan atisai ne a jiya Alhamis, don nuna goyon bayansu ga Falasdinwa musamman a Gaza, wadanda a halin yanzu, sojojin HKI sun yi masau kawayya, sun hana shigowar abinda da abinsha cikin...

Iran Ta Bada Amsa Ga Wasikar Shugaban Kasar Amurka Ta Gayyatar Kasar Zuwa Tattaunawa Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin. Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,...
Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci. A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba voyayayen abu bane, musammamn duba da cewa, yawan aukuwar tashe-tashen hankula, kalubalen rashin tsaro da matsatin tattalin arziki, suna manyan hummulhaba’isin da ke janyo karancin abinci a a cikin alumma. Misali, yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabas, ayyukan ‘yan bindiga daji a yankin arewa masu yamma da kuma rikice-rikicen kabilanci a sauran yankuanan, sun janyo tarwatsa miliyoyin alumomi daga matsugunan su, lalata gonakansu wanda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Lokutan sallah su ne lokuta na farin ciki, godiya ga ni’imar Allah, da kuma ibada. A wannan lokaci, yana da muhimmanci a tabbatar da ayyukan da ake aikatawa sun kasance masu inganci da dacewa da koyarwar addini. NAJERIYA A YAU: Halin Da Matasa Suka Tsinci Kansu A Najeriya NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Amma mene ne ya kamata musulmi su yi kafin da kuma ranar sallah? Ta wacce hanya za a tabbatar da zaman lafiya da tsari yayin bukukuwan sallah? Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari kan muhimman abubuwan da Musulmi ya kamata su aikata kafin da kuma lokacin sallah. Domin sauke shirin, latsa nan
Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17] Fashin Baƙi: Maganar Ibn Juzai tana nuni ne ga girman tasirin salatin Annabi (S.A.W)i a rayuwar Musulumi, musamman dangane da ƙaunar Annabi Muhammad (S.A.W) da bin sunnarsa. Domin cikakken bayani kan wannan batu, bari na ɗan zurfafa bincike a cikin abubuwan da ke cikinsa. Ma’anar Salati A fagen ilimi, salati ga Annabi (S.A.W) na da fassarori da dama: Idan Allah ne Yake yin Salati: Yana nufin yabo da ɗaukaka ga Annabi (S.A.W) da Allah Yake yi masa a wajen mala’iku. Idan Mala’iku ne Suka yi Salati: Yana nufin nema wa Annabi (S.A.W) rahama da ɗaukaka, da daraja da martaba a wurin Allah. Idan Musulumi...

Kasar Sin Na Adawa Da Kara Yawan Kamfanoninta Cikin Jerin Wadanda Amurka Ta Takaita Fitar Da Kayayyakinsu
Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana cewa, kasar tana matukar adawa da yunkurin Amurka na kara yawan dozin-dozin na kamfanoninta a cikin jerin kamfanonin da aka takaita fitar da kayayyakinsu zuwa kasashen waje. Jami’in, wanda ya bayyana haka a ranar Larabar nan, ya ce, matakin na Amurka ba komai ba ne illa murkushewa da kuma takura wa wasu kamfanonin kasashen ketare, tare da danne hakkokin sauran kasashen duniya na samun ci gaba. Yana mai cewa, hakan zai yi matukar cutar da kamfanonin tare da kawo cikas ga kwanciyar hankali da samun wadataccen tsarin samar da kayayyaki a duniya. Ya kara da cewa, matakin zai yi kafar ungulu ga kokarin warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da...
Kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin He Yadong, ya bayyana a yau Alhamis cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci da ya dace da kasuwa, da doka da kuma mizanin kasa da kasa. He Yadong ya bayyana haka ne a gun taron manema labarai na yau da kullum, inda ya ce, a wannan lokaci da ake ciki, wasu manyan jami’an kamfanonin kasa da kasa na kawo ziyara kasar Sin. Kuma kamfanonin sun yi nuni da cewa, babbar kasuwa, da cikakken tsarin masana’antun samar da kayayyaki, da kuma karfin kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha na Sin, dukkansu babbar dama ce a gare su, kuma zuba jari a Sin yana nufin cin gajiyar wannan dama. Bugu da kari,...
Masu fashin baki da dama na da ra’ayin cewa, tabbas illar wannan mataki na Amurka zai koma kanta, inda wasu daga sassan raya tattalin arzikin kasar kamar na albarkatun gona, da makamashi za su iya fuskantar matsin lamba mai tsanani. Yayin da wasu sassan kamfanonin kasar kuma ka iya fuskantar raguwar ribar da suke samu da kaso mai yawa, sakamakon karin kudaden hajojin da ake samarwa a masana’antun kasashen da Amurkan ta karawa haraji. La’akari da wadannan illoli, kamata ya yi Amurka ta yi karatun ta nutsu, ta dakatar da matakan kakaba haraji marasa ma’ana, kana ta koma teburin tattaunawa, domin warware duk wani sabani na kasuwanci da cinikayya tare da dukkanin sassan da batun ya shafa, ta yadda za...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan ta’addan da suka addabi al’umma a Jihar Zamfara da kewaye, Kachalla Isuhu Yellow ya kwanta dama. BBC ya ruwaito cewa an kashe ƙasurgumin ɗan bindigar ne a yayin wani rikicin cikin gida da ya kaure tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Bayanai sun ce lamarin ya faru da yammacin yau Alhamis, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana wasan ɓuya da jami’an tsaro da wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ’yan bindiga. Ɗan jarida mai bincike kan harkokin ’yan bindiga, Munir Fura-Girke ne ya tabbatar da kashe ɗan bindigar. Isuhu Yellow ya yi fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.

Karfin Lantarki Da Tashoshi Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Ke Samarwa A Sin Ya Kai Kilowatt Biliyan 2
A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu. Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.8 na baki dayan lantarkin da tashoshin samar da lantarki na kasar Sin ke samarwa. Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai...
Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bukukuwan Sallah na bana, saboda bukatar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar. A wata sanarwa da aka fitar, Sarkin ya bayyana takaicinsa kan matakin amma ya jaddada cewa, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne babban abin da ya sa a gaba. Sarkin ya ce, “Bisa umarnin da jama’a suka ba mu da kuma jajircewar da muka yi na ba su kariya, mun ga ya dace mu janye duk wani shiri da aka yi na bukukuwan Sallah bisa la’akari da halin da ake ciki.” Ya kara da cewa, tuntubar da aka yi da manyan malaman addini da sauran masu ruwa da tsaki sun yi tasiri a...
Sojojin Iran sun fitar da bayani a daidai lokacin da ake shirin raya ranar Kudus ta duniya, suna masu bayyana cewa; Hanyar da za ta warware matsalar Falasdinu ita ce yin gwgawarmaya da kuma samun goyon baya daga al’ummun duniya. Bayanin ya kuma kara da cewa; A daidai lokacin da al’ummar Falasdinu suke fuskantar zalunci,ta’addanci, da amfani da karfi a kansu, da kuma yin barna a masallacin Kudus, da majami’u, makarantu, asibitoci da kuma cibiyoyin MDD, da kuma shiru din da duniya ta yi, hakan yana nufin cewa ‘yan sahayoniya masu aiki da duk wata ka’ida ko doka ta kasa da kasa balle kuma halayyar kwarai, a dalilin hakan, hanya daya tilo da za a iya sauya wannan yanayin shi...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dattawa, ta buƙaci Ma’aikatar Sadarwa da ta yi aiki tare da kamfanonin sadarwa domin rage kuɗin data, ta yadda kowa zai iya samun Intanet mai sauƙi a Najeriya. A zaman majalisar na ranar Laraba, Sanata Asuquo Ekpenyong (APC – Kuros Riba), ya nuna damuwa kan yadda farashin data ya ƙaru da kusan kashi 200. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ya ce ƙarin yana hana mutane da dama musamman matasa, samun damar amfani da Intanet. “Ƙarin farashin data ba wai kawai yana hana mutane shiga Intanet ba ne, har ma yana wahalar da matasa ’yan kasuwa da masu aiki daga gida,” in...
Ya kuma yi kira ga iyaye su kula da ’ya’yansu tare da hana su shiga ayyukan da ka iya haddasa tashin hankali. Ya tunatar da al’umma cewa Sallah lokaci ne na zaman lafiya, haɗin kai, da farin ciki, don haka dole ne kowa ya fifita zaman lafiya fiye da bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Rundunar ta kuma samar da lambobin kiran gaggawa don bayar da rahoton abubuwan da ke faruwa a lokacin bukukuwan sallar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasashen Iran, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen sun kaddamar da wani atisayen hadin gwiwa na sojojin ruwa domin nuna goyan baya ga Falasdinawa a zirin Gaza, wadanda ke ci gaba da fuskantar zalinci na gwamnatin Isra’ila. An fara faretin hadin gwiwa a tekun Fasha, da yankin gabar tekun Makran, da kuma tekun Caspian da ke arewaci da kuma kudancin yankin ruwan Iran yau Alhamis gabanin ranar Qudus ta duniya. Kwamandan rundunar sojojin ruwa na IRGC Rear Admiral Alireza Tangsiri ya ce jiragen ruwa masu nauyi da marasa nauyi 3,000 ne ke halartar faretin. Ya kara da cewa, faretin na da nufin nuna karfin ruwa na bangaren ‘yan gwagwarmaya da kuma isar da sako ga miyagu da azzalumar gwamnatin Isra’ila. A...
A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza ko kuma allunan neman tsagaita bude wuta da Hamas cikin gaggawa. Gamayyar kungiyoyin da ke adawa da shugaban majalisar ministocin ne suka shirya zanga-zangar da ta barke a makon da ya gabata, wanda suke zarginsa da matakin korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gida wato Shin Bet, Ronen Bar. Wata Kuri’ar jin ra’ayin jama’a a isra’ila ta nuna cewa yawancin ‘yan Isra’ila na adawa...
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Litinin 31 ga watan Maris da Talata 1 ga watan Afrilu a matsayin ranakun hutun karamar Sallah. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida wadda babbar sakatariyar ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu. A cikin sanarwar, ministan harkokin cikin gida na Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya buƙaci dukkanin Musulmai su rungumi tausayawa da karamci da zaman lafiya, inda ya jaddada muhimmancin nuna soyayya da yafiya da haɗin kai domin gina alumma mai cike da zaman lafiya. Ya kuma buƙaci alummar Musulmi su yi wa Najeriya addu’ar ɗorewar zaman lafiya da samun ci gaba, kuma ya yi kiran gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai har iyakar Bachaka da ke Ƙaramar Hukumar Argungu a Jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin garin. Harin ya faru ne kwana guda bayan da dakarun tsaro suka kashe wasu dakarun Lakurawa a yankin. Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi, ta tabbatar da faruwar harin, inda ta ce ba a tantance sunayen jami’an Kwastam da aka kashe ba. “Eh, an kai hari, kuma ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an Kwastam biyu da wani mazaunin Bachaka,” in ji kakakin rundunar, Nafiu Abubakar. Bayan...
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC a jihar Zamfara sun bayar da wa’adin kwanaki 14 ga gwamnatin jihar, inda suka bukaci da a kawo karshen kura-kuran da aka samu wajen aiwatar da mafi karancin albashi na N70,000. An sanar da wa’adin ne a wani taron manema labarai a Gusau bayan wani taron gaggawa da kungiyoyin kwadago suka yi. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar NLC na jihar Zamfara, Malam Sani Halliru, ya bayyana rashin jituwar da ake samu wajen biyan albashin watan Maris a matsayin abin bakin ciki da damuwa ga ma’aikatan gwamnati. “Ya zama dole mu kira wannan taron manema labarai saboda mun ji takaicin yadda gwamnatin jihar ke aiwatar da mafi karancin albashi,”...
Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke bikin Sallar Eid-el-Fitr Durbar, saboda matsalar tsaro da ya sa aka dakatar da shirye-shiryen. Sarkin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa ta karamar hukumar Nasarawa da ke Kano. Ya kuma jaddada cewa zaman lafiya a tsakanin jama’a ya fi muhimmanci fiye da bikin Durbar. Bayero ya yi nuni da cewa manyan Malaman addinin Musulunci da dattawa da masu ruwa da tsaki da ‘yan majalisarsa suka bada shawarar a soke bikin domin a samu zaman lafiya. Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci al’ummar Kano da su yi amfani da lokacin bukukuwan Sallah wajen ziyartar...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa. A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya. “Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kira ga al’ummar kasar da su nuna hadin kai a yayin bukukuwan ranar Kudus ta duniya wato ranar JUma’ar kashe ta watan Ramadana da ke gabatowa, yana mai jaddada cewa hakan zai nuna matukar goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga al’ummar Falastinu. Pezeshkian, ya bayyana hakan ne a yayin taron majalisar ministocin kasar na farko sabuwar shekarar kalandar farisa, inda yake cewa “Ina fatan tare da halartar al’ummar kasar, za a gudanar da ranar Kudus mai daraja, kuma a wannan rana al’umma za su nuna hadin kai ga duniya.” Ranar Kudus ta duniya dai marigayi Imam Khumaini ne ya ayyana ta kuma ana gudanar da ita a kowace shekara a ranar Juma’ar...
Babban hafsan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya shelanta ‘yantar da Khartoum Babban birnin kasar. Wannan na zuwa ne bayan da tun da farko ya sanar da cewa dakarunsa sun kwato filin jirgin saman babban birnin, wuri mai matukar mahimmanci daga hannun dakarun ‘yan tawaye na RSF. “An ‘yantar da Khartoum, an gama,” in ji shugaban na Sudan daga fadar shugaban kasa a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na kasar. Kazalika, wata sanarwa da sashen watsa labarai na majalisar rikon kwarya mai mulkin kasar ta fitar, ta ce Al-Burhan ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Khartoum ta jirgi mai saukar ungulu a jiyan, jirgin da ya zamo na farko da...
Kantoman Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya dakatar da dukkanin masu riƙe da muƙaman siyasa da jami’an gwamnatin jihar nan take. A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ibas, ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bisa izinin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata ranakun hutun sallah Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da Sakatare na Gwamnatin jihar, Shugaban Ma’aikata, Kwamishinoni, shugabannin hukumomi, da masu ba da shawara na musamman. Ya umarci duk waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar ayyukansu ga sakatarorin ma’aikatunsu. Ya ce hukumomin da babu sakatare, sai a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sarkin Kano 15, Aminu Ado Bayero, ya soke shirinsa na gudanar da bikin hawan salla bayan shawarwari da dattawa da malaman addini suka ba shi. Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan buƙatar tabbatar da zaman lafiya a jihar, biyo bayan shiga ruɗani da jama’a suka yi. Hadimin Gwamnan Kano Tanka Galadanci ya rasu Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Wannan na zuwa ne yayin da aka shiga ruɗani a Kano saboda rikicin masarauta, biyo bayan mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano. Tun farko, duka sarakunan biyu – Sanusi II da Aminu Ado Bayero, sun shirya gudanar da hawan salla, lamarin da ya haddasa fargaba a tsakanin al’umma. A cikin wata...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, da dama daga cikin matasan Najeriya na fama da matsaloli masu tarin yawa, musamman wajen ciyar da kansu da biyan buƙatunsu na yau da kullum. Wannan na faruwa ne sakamakon halin da tattalin arziƙin ƙasa ke ciki, rashin aikin yi, da kuma tsadar rayuwa. NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu Wasu daga cikin matasan sun kammala karatu, wasu kuma suna da sana’o’in hannu, amma duk da haka, rashin samun aikin da zai biya musu buƙatunsu yana ƙara jefa su cikin mawuyacin hali. Wannan matsala na ci gaba da haddasa damuwa ga matasan ƙasar, inda da...
Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [18] Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17] Fashin Baƙi: Wannan magana ta Ibnu Juzai al-Kalbi Allah Ya ji ƙan sa tana bayani ne a kan istigfari ( wato nema gafarar Allah) da sakamakonsa a rayuwar mutum. Domin fahimtar wannan tasa dalla-dalla, zan yi bayani a matakai uku: Ma’anar Istigfari da Muhimmancinsa: Istigfari na nufin neman gafarar Allah Ta’ala bisa zunubai da aka aikata. Ana yin hakan ta hanyar faɗin “Astaghfirullah” da sauran lafuzza masu kama da hakan. Allah Maɗaukakin Sarki ya yawaita umurni da a yi istigfari a cikin Alƙur’ani, kamar yadda ya ce: ” sai na ce: Ku nemi gafarar Ubangijinku, lalle Shi Ya kasance Mai ywana gafara ne” Suratu...
Kamfanin Hisense South Africa, da kamfanin CNBM, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa bisa matsayin koli, ta gudanar da aikin samar da hidimomin kyautata amfani da makamashi mai tsafta a Afirka ta kudu. Kamfanonin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a jiya Talata, a birnin Johannesburg, yayin bikin baje hajojin da suka shafi sabbin makamashi, daya daga baje koli mafi girma da ake gudanarwa a nahiyar Afirka a fannin makamashi mai tsafta, wanda ke gudana yanzu haka a birnin. Bayan sanya hannu kan yarjejeniyar, babbar manajan sashen lura da hadin gwiwar kamfanin CNBM a kasashen ketare Jiang Fei, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, sabon hadin gwiwar zai taimakawa Afirka ta kudu, da...
Sanarwar ta umarci dukkanin waɗanda abin ya shafa da su miƙa ragamar aiki ga Sakatarorin ma’aikatun da suke jagoranta. Idan babu Sakatare, sai miƙa ragamar ga babban Darakta mafi girma ko Shugaban Harkokin Gudanarwa. Wannan umarni zai fara aiki daga ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari. An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Sanata Lawan, ya jajanta wa mutanen da suka yi asarar dukiya sakamakon gobarar. Ya ce haƙƙinsu ne su taimaka wa juna, kuma zai ci gaba da ƙoƙari don ganin cewa wadanda abin ya shafa sun samu tallafin da ya dace. Ya bayyana cewa wannan tallafin zai ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin da...

Sabbin Nasarorin Rigakafi Da Warkar Da Cutar TB Na Kasar Sin Sun Kara Kuzarin Dakile Yaduwarta Duniya
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sojojin mamayar HKI sun kai sabbin hare-hare a wasu yankuna na gabashin kasar Lebanon, adaidai lokacin da take ci gaba da kai wa yankin yammacin kogin Jordan wasu gare-haren. Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa; Sojojin mamayar sun kame Falasdinawa 5 a garin al-Khalil dake kudancin yammacin kogin Jordan. Haka nan kuma sun kama wasu Falasdinawa 8 a garin Nablus. A garin Bireh da wasu yankuna na Ramallah, sojojin mamayar sun kai wasu hare-haren a yau Laraba. A cikin watannin bayan nan, sojojin HKI sun rushe gidajen Falasdinwa 79 a cikin yankin yammacin kogin Jordan, tare da tilastawa mazaunan gidajen kusan 40,000 yin hijira. A ranar 22 ga watan Maris ne dai jiragen yakin HKI su ka kai hare-hare...

Sojojin Sudan Sun Kwace Wuri Na Karshe Da Yake A Hannun “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” A Cikin Birnin Khartum
Rundunar sojan Sudan ta sanar da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa. Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kasar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an shimfida iko a cikn filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na birnin Khartum. Har ila yau yau kwamandan sojan ya kuma bayyana cewa, a yanzu haka suna cigaba da faraurar mayakin “Rundunar Kai Daukin Gaggawa”da su ka saura a cikin binin Khartum. Tun da safiyar yau Laraba ne dai sojojin na Sudan suka sanar da cewa suna samun Karin nasara akan abokan fadansu. Wata majiyar ta shaida...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
Aƙalla mutum biyu ne suka rasu, yayin da wani ya jikkata a wani hatsarin mota da ya auku kusa da Sinimar Eldorado da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta tabbatar da faruwar lamarin. Gidauniyar Daily Trust da WRAPA sun ’yanta fursunoni 21 a Kaduna da Katsina Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:15 na safiyar yau Laraba, inda ya haɗa wata babbar mota ƙirar DAF da babur ƙirar Jincheng. Mai magana da yawun FRSC, Abdullahi Labaran, ya ce tuƙin ganganci ne ya haddasa hatsarin. “Daga cikin mutum shida da hatsarin ya shafa, biyu sun rasu, yayin da ɗaya ya...
NCDC, ta ce yawan masu kamuwa da cutar a bana ya fi na shekarar da ta gabata, inda a lokacin aka samu mutum 506 kacal. Hukumar ta shawarci al’umma suke shan sha ruwa mai tsafta, su riƙa wanke hannu da sabulu, su ci abinci mai kyau, tare da tabbatar da tsaftar muhalli don guje wa kamuwa da cutar kwalara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Mataimaki na Musamman kan Harkokin Rediyo ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu. Ya rasu ne a ranar Laraba 26 ga watan Maris, 2025, bayan gajeriyar rashin lafiya a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano. Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4 Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da rasuwar cikin wata sanarwa da ya fitar. Sanarwar ta bayyana marigayin a matsayin ƙwararren ɗan jarida da ya taka rawar gani wajen inganta harkokin sadarwa a jihar. Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin yau Laraba a Filin Masallacin Galadanchi da ke kusa da...
Gidauniyar Daily Trust (DTF) tare da haɗin gwiwar ƙungiyar WRAPA, Hamu Legal, da Bahama Chambers, sun biya tarar fursunoni 21 domin su samu damar fita daga gidajen gyaran hali a Jihohin Kaduna da Katsina. A Kaduna, an ’yanta mutum 17 bayan da DTF da abokan aikinta suka biya tarar su har Naira miliyan biyu da dubu dari biyu. Ministan tsaro ya yi alƙawarin kawo sauyi a cibiyar horar da sojoji ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Laifuffukan da aka yanke musu hukunci sun haɗa da sata, shiga da karɓar kayan sata. Da yake jawabi ga waɗanda aka fitar, Daraktan Gidauniyar Daily Trust, Dokta Theophilus Abbah, ya ce manufar shirin shi ne rage cunkoson fursunoni...
Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura. Yace, an sami gudunmawar kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah. A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu, Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
Ministan Tsaro, Mohammed Abubakar Badaru, ya ziyarci Cibiyar Horar da Sojoji da ke Zariya, inda ya yi alƙawarin samar da ƙarin kayan aiki da ci gaba da inganta horon kuratan sojoji domin su dace da buƙatun zamani. A lokacin ziyarar, Ministan ya bayyana gamsuwarsa da horon da kurata na kashi 88 ke samu, inda ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya na bunƙasa kayan horo da samar da ingantattun makamai da kayan aiki ga dakarun sojoji. Kakakin ’yan sandan Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Badaru ya yi alƙawarin tuntuɓar Gwamnatin Jihar Kaduna, domin kammala ginin Makarantar Sakandaren Chindit, wadda ba a kammala ta ba tsawon lokaci. Ya kuma bayar da tabbacin...
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, SP Abdulahi Usman, ya rasu bayan fama da doguwar jinya. Kakakin rundunar ’yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne, ya tabbatar da rasuwarsa cikin wata sanarwa a ranar Laraba. ’Yan fashi 4 sun mutu yayin tsere wa ’yan sanda a Nasarawa Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ya bayyana Usman a matsayin jajirtaccen ɗan sanda kuma gada tsakanin jami’an tsaro da al’umma. “SP Usman ya shafe shekaru uku yana ƙarfafa hulɗa tsakanin ’yan sanda da jama’ar Taraba. “Ƙwarewarsa, mutuntaka da jajircewarsa wajen neman adalci sun an samu tasiri,” in ji Adejobi. Ya ƙara da cewa rasuwar Usman babban rashi ne ga rundunar ’yan sanda, abokan aikinsa...
Wasu mutane huɗu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun mutu a sakamakon hatsarin mota a Jihar Nasarawa. Kakakin rundunar ‘yan sanda jihar SP Nansel Rahman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce lamarin ya auku ne lokacin da ‘yan fashin ke ƙoƙarin tserewa jami’an. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati “A ranar 25 ga watan Maris ne rundunarmu ta samu wani kiran gaggawa kan wasu ‘yan fashi na tsaka da ta’asa a bayan filin wasa na ƙaramar hukumar Keffi. “Bayan samun kiran ne kwamishinan ‘yan sanda Shettima Jauro Mohammed ya ba da umarnin bin bayan ‘yan fashin nan take. “Suna cikin guje...
Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in kasar Iran a baya-bayan nan, ba a samu wani ci gaba kadan ba a cikin binciken nukiliyar da aka shafe shekaru ana yi kan kasar Iran, yana mai jaddada bukatar gaggauta warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin Tehran da Washington. A wata hira da Bloomberg babban darektan hukumar Rafael Grossi ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai koma Tehran domin ci gaba...
Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa. Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Har ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 ƙaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na’urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar. Wani jami’in Ma’aikatar Kare...
Ƙungiyoyin ƙwadago reshen Jihar Ribas sun yi barazanar ɗaukar mataki muddin gwamnatin Nijeriya ba ta janye dokar-ta-ɓacin da ta ayyana a jihar ba. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwar gamayya da ƙungiyoyin ƙwadagon na NLC, TUC da JNC suka fitar a ranar 24 ga watan Maris. Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Kwamishinan Abba ya yi murabus bayan watanni 7 da naɗinsa Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na jihar sun nuna damuwa kan tasirin dokar-ta-ɓacin a kan tattalin arzikin jihar da kuma nuna rashin dacewar ta a hukumance. A cewarsu, wannan matakin ya sanya an kasa biyan albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar. ’Yan ƙwadagon sun bayyana cewa dakatar da zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da rashin biyan...
Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus. Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin. Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar. Sanarwar ta ce Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da murabus ɗin Kwamishinan yana kuma yaba masa kan ƙwazon da ya yi wajen sauke nauyin da aka ɗora masa. Kazalika, gwamnan yana yi wa Manjo-Janar Idris fatan samun nutsuwa da kwanciyar hankali a ritayar da ya yi. Aminiya ta ruwaito cewa tun a ranar 16 ga watan Agustan bara ne aka rantsar da Manjo-Janar Muhammad...
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II ya ce duk wani mai ƙoƙarin ja da hukuncin Allah to ba zai taba wanyewa lafiya ba. Sanusi II ya ce duk wani mai ƙoƙarin kawo tazgaro ga zaman lafiyar Jihar Kano a ƙarshe aniyyarsa ce za ta koma kansa. SSarkin ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan rediyon Premier da ke Kano, inda yake roƙon al’ummar jihar su zamo masu bin doka da oda, da kuma gudun aikata abubuwan da ka iya ta da hankali. Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kazalika ya bayyana masu ƙalubalantar kasancewarsa Sarki a matsayin masu yaƙi da...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya sanar da cewa har yanzu Iran ba ta mayar da martani kan wasikar da shugaban Amurka Donald Trump ya aike kan shirin nukiliyar Iran ba. Sai dai ya ce ana shirin mayar da amsa kuma za a mika ta hanyoyin da suka dace nan ba da jimawa ba. Da yake magana a wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da ministan harkokin wajen Armeniya Ararat Mirzoyan a Yerevan, Araghchi ya nanata cewa Iran ba za ta shiga tattaunawa kai tsaye da Amurka ba a karkashin yanayin matsin lamba da barazanar soji, da kuma kakaba takunkumi. Sai dai kuma ya tabbatar da cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai...
Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar. Duba daga rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan watan na Maris. Wani jirgin ruwa, Hafnia Andromeda, ana kyautata tsammanin zai isa tashar Everglades a ranar 29 ga Maris tare...
Hukumar kula da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen ƙetare (NIDCOM), ta bayyana cewa an kuɓutar da ‘yan Nijeriya 956 daga gidajen yarin Libya tare da mayar da su gida cikin watanni ukun farkon shekarar 2025. Shugabar hukumar, Hon. Abike Dabiri-Erewa, ta ce waɗanda aka dawo da su sun haɗa da mata 683, maza 132, yara 87, da jarirai 54. An samu nasarar mayar da su ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin NIDCOM, Hukumar ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) da kuma Hukumar Kula da Baƙin Haure da waɗanda rikici ya raba da matsugunansu (NCRMI). A cewar sanarwar da NIDCOM ta fitar, an dawo da su ne kashi-kashi daga watan Janairu zuwa Maris 2025. A ranar 28 ga Janairu, an dawo da mutum...
Dakarun (RSF) sun sanya sabbin takunkumai kan isar da kayan agaji a yankunan da ke karkashin ikonsu, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar ayyukan jin kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Matsalolin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar RSF ke kokarin kafa gwamnatin daga bangarenta a yammacin kasar ammacin Sudan, duk da fatattakarsu sojojin kasar suka yi daga babban birnin kasar, Khartoum, lamarin da ke barazana ga rarrabuwar kawuna a kasar da yaki ya daidaita. Matakan da kungiyar ta dauka na hana gudanar da ayyukan agaji na barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutane a yankin na Darfur, wadanda da dama daga cikinsu sun riga sun rasa matsugunansu sakamakon tashe-tashen hankula a baya. A...
1. Gibɗa a cikin Addini: Wannan ya ƙunshi yin gasa a ibada kamar sallah, ko azumi, ko karatun Alƙur’ani, da sadaka, ko mutum ya so ya zama hamshaƙin mai kuɗi da zai rinƙa taimaka wa addini da bayin Allah. Ko kuma mutum ya nemi ya zama malami ko jagora a addini don ya koyar da mutane. 2. Gibɗa a cikin Duniya: Wannan shi ne mutum ya so samun ilimi irin na wasu don ya amfanar da kansa da al’umma. Ko kuma son ya zama attajiri ko ɗan kasuwa ko mai wata sana’a da zai rinƙa ba wa mutane horo saboda ya ga wani yana yi shi ma ya so ya ƙware ya taimaka domin samun lada a wurin Allah. Haka...
Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka. Kazalika a shekarar 2023, dogaron sassan kasa da kasa kan kasar Sin ta fuskar samar da matsakaitan hajoji ya kai kaso 16 bisa dari, sama da na yankin arewacin Amurka mai kaso 15 bisa dari. Bugu da kari, rahoton...
A yanzu nan ne Aminiya take samun labarin rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdullahi Shu’aibu wanda aka fi sani da Baba Ƙarƙuzu ko Ƙarƙuzu na Bodara. Hakan dai na kunshe ne cikin wani sako da jarumi a masana’antar Kannywood kuma Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Kano, Abba El-Mustapha, ya wallafa a shafinsa na Instagram. SShi ma dai fitaccen jarumin Kannywood kuma Shugaban Hukumar Fina-finai ta Nijeriya, Ali Nuhu, ya wallafa hoton marigayi Ƙarƙuzu a shafinsa na Facebook yana mai roƙon Allah Ya jikansa. Ƙarƙuzu dai tsohon jarumi ne a masana’antar Kannywood da ya yi tashe tun a shekarun 1980. Ana iya tuna cewa wata hira da ya yi da Zinariya TV kuma Mujallar Fim ta wallafa a shekarar 2023, Ƙarƙuzu...
Nasarar da Afirika Ta Kudu ta samu akan kasar Benin ya sa ta hada maki 13 a wasanni 6, kuma ta baiwa Nijeriya dake matsayi na 4 tazarar maki 6. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta gamu da cikas a ƙoƙarinta na neman yankar tikitin shiga Gasar Kofin Duniya ta baɗi, bayan da ta tashi canjaras 1-1 da Zimbabwe. Victor Osimhen ne ya fara ci wa Nijeriya kwallo a minti na 74 a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom. Masu neman yi wa Natasha kiranye ba su cika ƙa’ida ba — INEC Dalilin da dimokuraɗiyya ta gaza kawo ci gaba a Afirka — Obasanjo Sai dai Zimbabwe ta farke ana daf da tashi a minti na 90 ta hannun ɗan wasanta na gaba, Taranda Chirewa. Wannan sakamako na nufin cewa Nijeriya na matsayi na huɗu a rukunin C, inda Ghana ke gabanta a...
A shekarar 2024 da ta gabata, kamfanonin kasar Sin da masu bincike na kasar, sun gabatar da sabbin bukatun neman ikon mallakar fasaha har 20,081 ga ofishin rajistar ikon mallakar fasaha na Turai ko EPO, kamar dai yadda alkaluman shekarar 2024 da ofishin ya fitar a yau Talata suka nuna. Wannan adadi ya kai kaso 10.1 bisa dari na jimillar neman izini da ofishin na EPO ya karba a bara, wanda hakan ya tabbatar da Sin a matsayi na 4 cikin jerin kasashe mafiya gabatar da bukatar ga ofishin a duniya baki daya. A jerin kamfanoni dake cikin jadawalin na EPO, kamfanin Huawei na Sin na matsayi na biyu, da bukatun neman ikon mallakar fasaha har 4,322. Baya ga Huawei,...
Amurka ta shigo da sama da ganga miliyan biyu na man jiragen sama daga matatar Dangote a watan Maris. Matatar ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, inda ta ce hakan ya tabbatar da “nagartar da ba ta misaltuwa” na kayayyakin matatar da kuma aminci da kasashen duniya suka bai wa matatar. Nijeriyar Jiya Da Yau: Kiki-Kakar Sabgar ‘Yan Majalisu Alamar Deepseek” Ta Bude Kofar Gyara Na Kara Kunno Kai A Harkokin Duniya Duba daga rahoton ma’aikatar sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta Kpler, ta ce jiragen ruwa shida dauke da kusan ganga miliyan 1.7 na man jiragen sama daga matatar Dangote sun isa tashoshin jiragen ruwa na Amurka a wannan...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya ce a jiya Litinin, ma’aikatar harkokin wajen Sin ta gudanar da taron karawa juna sani na kasa da kasa, mai taken “Karfafa rawar da MDD ke takawa, tare da habaka ra’ayin cudanyar bangarori daban daban” a nan birnin Beijing. Guo ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na yau da kullum da ya jagoranta a yau Talata, inda ya ce daukacin mahalarta taron na karawa juna sani sun yi imanin cewa, a halin da ake ciki, ya kamata a karfafa ayyukan MDD, da inganta hadin kai da hadin gwiwa, da kuma tinkarar kalubale daban daban da ake fuskanta a duniya. Kazalika, mahalarta taron sun jinjinawa rawar da kasar Sin ta taka...
A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro. Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike musu kugu ne, ta yadda za a ga ba su da wani tasiri ko katabus, wajen zuwa da kyawawan manufofi, don ciyar da jama’arsu gaba. Yanzu kuwa, za a iya yi wa wadannan “yan majalisun uzuri?. Shin, suna da cikakken ikon gudanar da aiyukan nasu ko babu?. Babu shakka, duk wani irin iko da ake da bukata da tsarin mulki zai ba da, ya jima...
Sai dai, tabbas za a karya tsarin, ganin yadda ba a samun adalci a ciki. Mun san kasar Sin daya ce daga cikin kasashen da suka warware dabaibayin hana ci gaba da kasashen yamma suka daura musu, inda ta raya tattalin arzikinta, tare da taka muhimmiyar rawa a cikin tsarin duniya ta fuskar samar da kayayyaki. Daga bisani me kasar Sin ta yi? Ta samar da tunanin gina al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai-daya, inda aka nanata bukatar ba sauran mutane damar jin dadin zaman rayuwa, matukar wani mahaluki na son samun zaman rayuwa mai inganci. Bisa wannan tunani ne, kasar Sin ta samar da jerin shawarwari masu alaka da ci gaban tattalin arziki, da tsaro, da cudanyar mabambantan...

Iran Ta Turkiyya Sun Bukaci kasashen Musulmi Su Magance matsalar Jinkai A Kasar Palasdinu Da Aka Mamaye
A zantawa ta water tarho ministocin harkokin waje na kasashen Iran da Turkiya sun bukaci kasashen musulmi su magance matsalar jinkai da kayakin agaji na Falasdinawa a kasarsu da aka mamaye. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Hakan Fidan na kasar Turkiya da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi suna fadar haka a jiya Litinin. A lokacinda yake Magana a kan rikicin da ke faruwa a kasar Turkiyya Abbas Aragchi ya bayyana cewa, rikici ne na cikin gida, kuma yana fatan gwamnatin kasar zara iya magancece ta yadda ta ga ya dace, kuma yana da imani zata iya magance matsalar. Aragchi ya kara da cewa, wannan shi ne matsayin iran a cikin al-amuran da ke faruwa a...

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Zargin Kasar Amurkan Dangane Da Kamfanonin Man Fetur Na Kasar Ba Gaskiya Bane
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya musanta zargin kasar Amurka na cewa wasu jiragen ruwan JMI suna amfani da tudan kasar Iraqi sun kai kawo a ruwayen yankin. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fadawa Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran, kan cewa Aragchi yana fadar haka ne a jiya litinin, a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Iraki Fu’ad Hussain. Kafin haka ministan ya nakalto korafin da jami’an gwamnatin kasar Amurka suka gabatarwa gwamnatin kasar Iraki na cewa jiragen ruwan kasar Iran na amfani da takardun bugi na kasar Iraki don gudanar da harkokinsu a yankin. Aragchi ya musanta hakan ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son raba JMI...
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan tsaron kasar Muhammad Badaru yana fadar haka a lokacinda yake kaddar da wani bangaren na rundunar a barikin Kabala da ke barikin Jaje a kusa da birnin Kaduna daga arewacin kasar a jiya Litinin. Badaru ya kara da cewa gwamnatin kasar tag a akwai butara da samar da irin wannan rundunar, saboda magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda aka dade ana fama das u, ko kuma wadanda suke tasowa nan da ca. Ya kara da cewa rundunar da aka kaddamar a jiya litinin bangare ne na runduna mai sojoji 800 da za’a...
A ranakun 11, 19, da 25 ga Fabrairu, an dawo da mutum 484. A ranakun 4 da 18 ga Maris, an dawo da mutum 320. Hon. Dabiri-Erewa ta ƙara da kira ga ‘yan Nijeriya da su guji tafiya ƙetare ta ɓarauniyar hanya, musamman ta Libya, wacce ke fama da matsaloli da rikici. Ta kuma jaddada cewa wajibi ne ‘yan Nijeriya su bi hanyoyin da doka ta tanada idan suna son yin hijira, domin guje wa hatsarin da ke tattare da tafiya ta haramtacciyar hanya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne a daidai lokacin da Ibas ya amince da murabus ɗin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, George Nwaeke, yana mai gode masa bisa gudunmawar da ya bayar a lokacinsa. Ibas ya ce naɗin Farfesa Worika ya yi...
Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo. Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan. Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da? Sai dai har yanzu wasu na yi wa ƙungiyar kallon hadarin kaji, kan zargin ta gaza cimma wasu muradu da aka kafa ta a kai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kasar Rasha ta bayyana a wannan Talata cewa tana nazarin sakamakon tattaunawar da ta yi da Amurka kan Ukraine a Saudiyya, Rasha ta ce ba wani bayyani da za’a fitar game da tattaunawar, kuma ba wani lokaci da aka a sanya na ranar da za a sake ganawa da Amurkawa ba. “An ba da sakamakon tattaunawar da aka yi a manyan biranen, Kuma “Ana nazarin su,” in ji mai magana da yawun shugaban kasar Rasha Dmitry Peskov yayin jawabinsa na yau da kullun. Rahotanni sun ce ana tattaunawa tsakanin Amurka da Ukraine har zuwa yau Talata. Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a...
Wasu lauyoyi 77 a Jamus sun bukaci gwamnatin kasar da ta mutunta sammacin kotun hukunta manya laifuka ta duniya ICC, na cafke firaministan Isra’ila Banjamin Netanyahu. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da da suka fitar, fitattun lauyoyin 77 sun kuma bayyana yiwuwar kasancewar Netanyahu a Jamus a matsayin take doka da kuma hakkin kasar. Lauyoyin sun soki Friedrich Martin Josef Merz, dan siyasa kuma shugaban gwamnati a nan gaba, saboda sanarwar da ya yi a lokacin yakin neman zabe cewa zai samo hanyar gayyatar firaministan Isra’ila da kuma tattaunawa ta wayar tarho da Netanyahu bayan nasararsa. Lauyoyin sun kuma yi Allah wadai da halin wasu jami’o’in da suka soke jawabin da Francesca Albanese mai kula da harkokin kare hakkin...
Za a ɗauko hayar ƙwararrun sojoji daga ƙetare domin horar da sojin ƙasar aikin ƙundumbala wajen tunkarar ’yan ta’adda da kuma ƙwato mutanen da aka yi garkuwa da su a Nijeriya. Ministan Tsaron Nijeriya, Badaru Abubakar ya sanar da haka lokacin ƙaddamar da aikin horar da sojojin 800 a Jaji da ke Jihar Kaduna. Gaskiyar abin da ake faɗa kan ’yan fim — Samira Sani Mutum 2,000 za su riƙa kamuwa da cutar HIV duk rana a duniya — MDD Abubakar ya ce baya ga horaswar, gwamnati za ta samar wa dakarun kayan aiki na zamani da za su yi amfani da su wajen daƙile matsalolin tsaron da ake samu. Ministan ya ce a karon farko, sojojin 800 za su...
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Duba da yanayin kiwon lafiya a duniya tun bayan ɓullar cututtuka kamar sanƙarau da Shan Inna, wajibi ne mu bi ƙa’idojin kiwon lafiya na Saudiyya. “Dole ne mu tabbatar da cewa dukkanin alhazai sun samu takardun rigakafi da katin shaidar lafiya,” in ji shi. Ministan, tare da rakiyar wasu manyan jami’an ma’aikatar lafiya, sun duba motocin ɗaukar marasa lafiya na NAHCON, kayan magani, da shirye-shiryen kiwon lafiya a asibitocin Nijeriya da ke Saudiyya. Sun gano muhimman wuraren da ake buƙatar ingantawa, ciki har da wadatar magunguna, alluran rigakafi, na’urorin likitanci, da motocin ɗaukar marasa lafiya. Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya yaba da shirin Ministan, inda ya ce: “Ziyararku ta ƙara mana ƙwarin gwiwa a ƙoƙarin da muke yi...
Sai dai duk da yaba wa Amurka bisa irin taimakon da ta bayar a baya, Byanyima ta nuna damuwa kan yadda aka dakatar da tallafin kwatsam ba tare da shiri ba. Wannan na iya haddasa koma baya a ƙoƙarin da aka shafe shekaru ana yi na rage yawan masu kamuwa da cutar, musamman a yankunan da ke fama da talauci da ƙarancin kayan kiwon lafiya. Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa, idan ba a samu sabbin hanyoyin tallafi ba, yiwuwar ƙaruwar mace-mace sakamakon cutar HIV na da matuƙar girma. Hakan na iya rusa nasarorin da aka samu a yaƙin da duniya ke yi da cutar. Ana ci gaba da kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin agaji da su ceto shirin...
Kungiyar ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Kebbi ta raba kayan abinci da kudi ga iyalan mambobinta da suka rasu a lokacin da suke kan aikin jarida, a matsayin kyautar azumin Ramadan. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kungiyar na Jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar, ya ce suna gudanar da wannan shiri a duk shekara, tun bayan kaddamar da shi da tsohon shugaban kungiyar na jiha Alhaji Aliyu Jajirma ya yi, domin faranta ran iyalan abokan aikinsu da suka rasu. Kwamared Sarki Abubakar ya bayyana cewa dukkan shugabannin kungiyar da suka gabata sun tabbatar da ci gaba da gudanar da wannan shiri a duk lokacin azumin Ramadan domin rage wa iyalan mamatan radadin wahalhalun rayu. Ya sanar...
Samira Sani ‘yar asalin garin Kano ne da ta shigo Masana’anrtar Kannywood a 2022. A tattaunarta da Aminiya, ta ba da tarihinta da kuma yadda ta daɗe tana mu’amala da ‘yan Kannywood kafin ta fara fitowa a fim: Za mu so ki gabatar da kanki? Suna na Samira Sani, jaruma a Masanartar Fim ta Kannywood. Mene ne tarihinki a takaice? To ni ‘yar asalin garin Kano ne. An haife ni a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano. Na yi makarantun firamare da sakandare duk a Dakatsalle, bayan na gama sakandare sai aka yi min aure, daga baya Allah Ya kawo ni cikin birnin Kano. Ke nan kin taɓa yin aure? Eh na taɓa yin aure,...
“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba. “Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam....