2025-02-21@14:53:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 242

«a yarjejeniyar tsagaita wuta»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Sojojin mamayar Isra’ila sun fara janyewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza Kafofin yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila za su fara ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Zirin Gaza a daren jiya. Jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta watsa rahoton cewa: Rundunar sojin mamayar Isra’ila ta ba da umarnin ficewa daga yankin Netzarim da ke tsakiyar Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar Hamas da gwamnatin mamayar Isra’ila a yankin. Jaridar ta bayyana cewa: Runduna ta 162 ta sojojin mamayar ta sake matsawa zuwa kusa da kan iyaka da kuma janyewa daga yankin Netzarim na nufin cewa, babu sojojin mamayar Isra’ila a arewacin...
    Ga wasu manyan ‘yan kwallo da tauraronsu ke haskawa a duniya, wadanda asalin ‘yan Nijeriya ne, wato ko dai iyayensu baki daya ko wani daga cikin iyayen ‘yan Nijeriya ne.   Jamal Musiala (Jamus) Matashin dan wasa Jamal Musiala, wanda aka haifa a ranar 26 ga Fabrairun shekarar 2003, fitaccen dan kwallon kasar Jamus ne da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta Jamus din kuma yana cikin matasan ‘yan kwallon da suke tashe a duniya a yanzu saboda ba za ka lissafa matasan ‘yan wasa guda biyar ba a duniya ba tare da ka saka sunansa ba. An haife shi ne a garin Stuttgart da ke Jamus, amma mahaifinsa mai suna Daniel Richard asalin can Nijeriya ne, wanda ya...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa da suka miƙa masa takardar amincewarsu ga zaɓen Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Arewa a fadar gwamnati da ke Katsina. Ta kashe saurayinta saboda ya gaisa da tsohuwar abokiyar karatunsa Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da jinjina wa yadda aka gudanar da zaɓen shugabannin Majalisar Sarakunan Yarbawan na Arewa lami lafiya. Ya ce,...
    Iran ta bukaci taron gaggawa na ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, game da shirin shugaba Donald Trump na Amurka na kwace Gaza da kuma korar al’ummar Zirin. Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yana mai jaddada cewa haramtaccen shirin” na shugaban kasar Amurka kan Gaza ya gamu da kakkausan ra’ayi daga kasashe daban-daban, inda ya yi kira da a gudanar da taron gaggawa na ministocin kungiyar ta OIC domin tattaunawa da yanke shawara kan wannan batu. A wata tattaunawa daban daban ta wayar tarho da wasu takwarorinsa a yammacin jiya Asabar ministan harkokin wajen na Iran Sayyid Abbas Araghchi da takwaransa na kasar Masar Badr Abdel-Aty, Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakaninta da Isra’ila “tana cikin hadari” kuma “zata iya rugujewa,” Bassem Naïm, ne wani mamba a ofishin siyasa na kungiyar, ya bayyana hakan ga kamfanin AFP, yayin da tattaunawar da ake yi kan mataki na biyu na tsagaita bude wuta, da ya kamata a fara ranar Litinin, ke ja da baya ba kamar yadda aka fara ba inji shi. Da yake zargin Isra’ila da “jinkiri” wajen aiwatar da kashi na farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta na makonni shida, wanda ya fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu, Bassem Naim ya yi gargadin cewa wannan lamarin ya jefa yarjejeniyar cikin hadari kuma zata iya haifar da rugujewarta....
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
    A daren ranar 6 ga wannan wata, an gudanar da wani biki mai taken “Bikin Bazara Namu” a cibiyar hukumar bunksa ilmi da kimiyya da fasaha da al’adu ta MDD, wato UNESCO dake birnin Paris na kasar Faransa, wanda babban rukunin Sin dake hukumar, da gidan talabijin na lardin Henan na kasar Sin suka karbi bakuncin gudanar da shi, don murnar cewa, Bikin Bazara na al’ummar kasar Sin ya shiga cikin jerin bukukuwan al’adun gargajiya da bil’adama ya yi gado a duniya. Babbar wakiliyar Sin dake hukumar UNESCO, Yang Xinyu ta bayyana cewa, an yi wannan shagali ne don murnar bikin gargajiya na al’ummar kasar Sin don more al’adu tare da sassan duniya, da kara matsa kaimi ga yin hadin...
      Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.   Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a – hanyar Tsangamawa.   Hanyar Tsangamawa da ke Babban Rafi, Karamar Hukumar Danja, Jihar Katsina, ta haddasa mutuwar mata masu juna biyu da jariransu, musamman a lokacin damina.   Duk da yawan koke da rokon gwamnati, har yanzu ba a dauki matakin gyara hanyar ba.   A wata hira da suka yi da Radio Nigeria, wasu daga cikin matan yankin sun bayyana cewa mata masu...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Sayyid Aliyul Khaminae yana cewa tsagaita wuta da aka samu bayan wannan lokaci mai tsawo na fafatawa yayi dai-dai. Tawagar shuraa ta Hamas din dai sun hada da shugaban riko na kungiyar Khalil Al-Hayya, shugaban majalisar shoora ta kungiyar Muhammad Ismail Darwish da sauransu. Jagoran ya kara da cewa nasarar da mutanen Gaza suka samu a kan Amurka da kawayenta misdaki nan a...
    Amurka Ta Tasa Keyar Indiyawa Kusan 100 Zuwa Gida
    An dakatar da Dagacin Karagawal da ke Jihar Gombe, Usman A. Bello, daga kujerarsa, har sai an kammala bincike kan zargin da ake masa na saran wani maraya da adda har sau bakwai. A baya Aminiya ta ruwaito yadda jikin marayan, mai suna Adamu Muhammad mai shekara 15 ya fara ɗoyi saboda rashin samun kulawa bayan asibiti sun ƙi karbarsa saboda rashin kuɗi, sakamakon raunukan da yake zargin dagacin ya yi masa. A yayin hirar da Aminiya ta yi da shi a lokacin, Dagacin ya musanta sarar yaron, inda ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin kare kansa ne bayan varayi ɗauke da makami sun shiga gidansa. Lamarin da ya faru a farkon watan Disamba na shekarar 2024, wanda ya haifar...
    Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183 yau Asabar, a madadin wasu mutanenta uku daga cikin wadanda kungiyar Hamas ke garkuwa da su a Gaza a wani bangare na aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza da suka cimma. Kamar dai a makon da ya gabata, za a yi musaya ta biyar a wurare biyu a zirin Gaza a jere inji rahotanni. A maimakon haka, Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinawa 183, ciki har da 18 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai, ciki har da wasu fitattun mutane irin su Iyad Abu Shidam, wanda Isra’ila ta yankewa hukuncin daurin rai da rai a Beersheva a shekara ta 2004. Bayanai sun ce kimanin 111 daga cikin wadannan...
    Yau Asabar shugabannin kasashen raya tattalin arzikin kasashen Gabashi da Kudancin Afrika EAC da SADC za su gana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya domin tattauna rikicin gabashin DRC. Shugaban kasar Kenya, William Ruto, dake jagorantar kungiyar EAC, ya sanar da halartar takwarorinsa na Congo da Rwanda. Tun da farko a ranar Juma’a, ministocin harkokin wajen kasashen biyu sun gana domin samun nasarar wannan tattaunawar, inda fadar shugaban kasar ta Kwango ta gabatar da bukatunta da suka hada da : tsagaita bude wuta nan take, janyewar dakarun M23 da na Rwanda daga yankin Congo, da sake bude filin jirgin saman Goma, da mayar da birnin ga hannun halastattun hukumomi. A ranar Juma’a, a wani taro a Malabo, Kungiyar...
    Bangarori mabanbanta na kasar Lebanon suna mayarwa da ‘yar sakon Amurka martani saboda tsoma baki da ta yi a kan yadda za a kafa gwamnati a kasar. Morgan Ortagus wacce ta gana da jami’an kasar Lebanon ta bayyana cewa, bai kamata a kafa gwamnati a kasar ta wakilan kungiyar Hizbullah a ciki ba. Kungiyar malaman addinin musulunci ta fitar da bayani da a ciki ta ce; “Furucin mataimakin manzon Amurka a gabas ta tsakiya, Morgan Ortagus wacce ‘yar sahayoniya ce,tsoma baki ne a harkokin cikin gidan Lebanon wanda ya tsallake ka’idojin aikin diplomasiyya.” Ita ma gwamnatin kasar ta Lebanon ta fitar da bayani tana mai cewa abinda Ortugas din ta furta, ra’ayinta ne, bai shafi gwamnatin Lebanon ba. Shi kuwa...
    Bayanin da babban bankin kasar ta Najeriya ya fitar, ya bayyana cewa an sami wannan koma bayan ne a cikin makwanni uku da su ka gabata. Bayanin na babban bankin na Najeriya ya ci gaba da cewa, kudaden ajiyar Najeriya na waje da a cikin watan Disamba sun kai dala biliya 40,887, sun ragu, sun zama dala biliyan $39.723 daga ranar 31 ga watan Janairu 2025. An bayyana koma bayan ne a kudaden waje na ajiya da babban bankin kasar yake da su, da ya kamata ace a ranar 4 ga watan Febrairu ne za a fitar da kididdiga akan halin da kudaden wajen suke ciki,amma ba a yi ba. Bugu da kari  wannanbayanin  ya fito ne daga kamfanin dake...
    Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20. Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22. Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5. Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an  yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku. Tun a watan Disamba na...
    Wasu da ake zargin ’yan fashi ne sun yi awon gaba da wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 20 a hanyar ruwan daga Bonny zuwa Okrika a Jihar Ribas. Sai dai jami’ai a ƙaramar hukumar Bonny ta ce ta kuɓutar da tara daga cikin fasinjojin yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don ceto sauran. Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Shugaban Ƙaramar hukumar Bonny, Hon Anengi Barasua Claude-Wilcox ya ce, an ceto mutanen tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro. Claude-Wilcox a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Boma Waribor ya fitar a ranar Juma’a, ya ce direban jirgin...
    Gidauniyar ‘TY Buratai Literary Initiative (TYBLI)’ ta kaddamar da shirye-shiryen tallafinta na 2025 wanda ta kudiri aniyar bunkasa ilimi da tsarin koyo a tsakanin daliban Nijeriya. Shirin wanda gidauniyar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya) ta kirkiro kuma ta dauki nauyin wannan shiri na da nufin kwadaitar da koyon Adabin rubutu da kuma bai wa daliban da suka fi hazaka tukuici a fadin kasar nan. Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kashe Naira Tiriliyan 4.2 Don Aikin Manyan Hanyoyi Da take jawabi a wani taron manema labarai, Dokta Lizi Ben-Theanacho, shugabar Gidauniyar ta TYBLI, ta jaddada kudirin Gidauniyar na bunkasa adabin rubutu ta hanyar samar da littattafai...
    Bama-bamai da mayakan Boko Haram suka binne sun kashe mutane biyu a hanyarsu ta zuwa kasuwa a Jihar Adamawa. Kakakin ’yan sanda a jihar Borno, ASP Kenneth Daso, ya ce mutane shida ne a cikin motar a lokacin motar da ta taka bam din a ranar Talatar bayan ta taso daga Karamar Hukumar Hawul ta Borno zuwa Kasuwar Garkida ta jihar Adamawa. “Ana zargin cewa ’yan Boko Haram ne suka dasa bama-baman, kuma motar da ke jigilar mutanen kauyen zuwa kasuwa a Garkida ta taka ta kuma ta fashe. “Wani dan shekara 25 ya mutu nan take, amma sauran fasinjojin an garzaya da su asibiti domin yi musu magani,” inji shi. Shugaban karamar hukuma ya biya wa al’ummarsa kudin wutar...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci. Taron na yau ya zo daidai da zagayowar kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma taron tunawa da mubaya’a mai dimbin tarihi ga Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 1979. Don haka a safiyar...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na korar Falasdinawa daga zirin Gaza karkashin dabarar gudun hijira. Tajani ya bayyana cewa: Ba za a tilastawa Falasdinawan shiga kowane irin zabi ba, yayin da yake magana kan shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar na neman kwace yankin Zaga. A cikin wani yanayi mai alaka da wannan batu, ministan harkokin wajen kasar Spain José Manuel Albares ya bayyana rashin amincewarsa da shawarar da...
    Tsohon ministan yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta ba da umarnin sojojinsu su kashe fursunoni yahudawa da masu tsaronsu a Gaza Tsohon Ministan tsaron gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da aka kora Yoav Gallant a jiya Alhamis ya yi bayani kan matakan da sojojin mamayar Isra’ila suka dauka na tunkarar fursunonin yahudawan sahayoniyya da masu garkuwa da su a Zirin Gaza. A cewar shafin Falestine Today, Gallant ya ce: “Sun ba wa sojojin mamayar Isra’ila umarnin yin amfani da hanyar Hannibal, wato kashe fursunoni ‘yan uwansu da aka yi garkuwa da su tare da masu garkuwa da su a Gaza.” Ya kara da cewa: A jajiberin fara kai farmaki ta kasa kan...
    Wannan ya hada da kilomita 65 daga Legas zuwa Ogun da wani karin da zai tashi daga Kalabar ta Akwa Ibom, wanda titin zai ginu a karkashin ‘Engineering, Procurement, and Construction’ (EPC) da tsarin za su kula da shi na tsawon shekaru goma bayan ginawa. Majalisar zartarwar ta amince da kashe naira biliyan 470.9 domin gina hanyar da ta nausa Jihar Delta da kuma wani naira biliyan 148 don gina hanya a Jihar Anambra zuwa gada ta biyu a Neja. Shi kuma babban hanyar Lagos zuwa Ibadan ya samu amincewar naira biliyan 195 domin a gina shi a karkashin asusun shirin inganta hanyoyi na shugaban kasa (PIDF), da ke da manufar rage cunkoso da inganta sufuri a manyan hanyoyin da...
    Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan ƙungiyar Ruben Amorim ya bayyana a matsayin babbar matsala. A ranar Alhamis ƙungiyar ta ce har yanzu ana duba yanayin raunin domin sanin yadda ya fi dacewa a yi masa magani da kuma tsawon lokacin da zai ɗauka yana jinya. Sanarwar ta ce kowa a ƙungiyar yana yi wa Lisandro Martinez fatan warkewa sarai, kuma za su ci gaba da tallafa masa a kodayaushe. Rashin...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe, yayin da rahotanni ke cewa faɗa na kara yaɗuwa zuwa wasu sassan ƙasar, sannan take hakkin ɗan’adam na ƙara munana. Jakadan Congo a Geneva ya ce gwamnatin ƙasar na buƙatar MDD ta gudanar da cikakken bincike kan hakan. Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan’adam sun yi amannar cewa ƴan tawayen M23 da sojojin Rwanda da na Congo duk sun aikata munanan laifuka. Sai dai har yanzu Rwanda...
    Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi, ta gargadi ma’aikatan Cibiyar Reformatory Institute ta Kiru da su guji karkatar da kayayyakin da aka ware domin gina cibiyar.   A yayin ziyarar duba aikin gyare-gyaren, kwamishina Amina ta jaddada muhimmancin yin amfani da kudaden da aka ware wajen abubuwa masu inganci a wannan cibiyar.     Cibiyar da aka sabunta za ta ƙunshi abubuwan more rayuwa na zamani, waɗanda suka haɗa da dakunan kwanan dalibai, asibiti, wurin shakatawa, wuraren aikin kafinta da walda, ɗakin cin abinci.   Kwamishina Amina ta yabawa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa na inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.   Ana sa ran kammala aikin gyaran nan ba da jimawa ba, daga nan...
    In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
    Mahukunta gidan Radiyon tarayya na kaduna sun kai wa iyalan Alhaji Bala Albabello ta”aziya wanda Allah ya yi wa rasuwa ranar litini 3 ga watan fabrairu na shekarar 2025. Shugaban gidan Radion, Malam Buhari Awwalu ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan marigayin dake Tudun Jukun a zaria. Malam Buhari Awwalu ya jajantawa iyalan marigayin,inda ya yi addu’ar Allah ya bai iyalan hakurin rashin sa,kuma ya sa a rinka tunawa da kyawawan dabi’un sa na taimakawa marasa karfi da kuma Dora al’umma akan turbar kasuwanci. Ya kuma roki Allah da ya sanya shi a aljannar firdausi. Da ya ke jawabi a masadin iyalan,Alhaji Hassan Abdulwahab ya yi bayanin cewa marigayi Albabello ya sadaukar da rayuwar sa ce wajen hidimtawa al’umma. Cikin...
    Babban jami’in jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Cai Qi, ya yi kira a ranar Laraba, da a ci gaba da yin kokari wajen kawar da ayyukan da ba su da ma’ana, da rage nauyin da ke wuyan jami’an kananan matakai, don tabbatar kyakkyawan salon aiki tsakanin ’yan jam’iyya da jami’ai wajen cimma burin da aka sa a gaba a cikin shirin shekaru biyar-biyar karo na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025. Cai, wanda kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ne, kuma mamba a sakatariyar kwamitin kolin JKS, ya bayyana hakan ne a wani taro na matakin koli game da wannan batu. Taron ya bayyana cewa, ya kamata a mayar da hankali wajen...
    A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi. A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da gargaɗin da mahaifiyarta ta yi mata. Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga “Lokacin da mahaifiyar ta samu ’yarta a bakin kogin, sai ta fusata. Duk da gargaɗin da aka yi mata na ƙauracewa kogin, Rachael ta ƙi, wanda hakan ya sa mahaifiyar tashin hankali ta fusata,” in ji wani ganau. A cikin fushi,...
    An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa  tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. ’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya, kasancewar mahaifiyarsa da mahaifin sun rabu. Bayanai sun nuna cewa duk da cewa kakar ta ki amincewa, amma sai da matar ta nace ta dauki yaron da cewa za ta kula da shi, bayan nan ne kuma sanya masa tafasasshen ruwa a gaban nasa, maimakon ruwan dumi. Duk da raunin da tafasasshen ruwan ya yi  masa kuma, sai aka kai shi wurin mai maganin gargajiya...
    An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa  tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. ’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya, kasancewar mahaifiyarsa da mahaifin sun rabu. Bayanai sun nuna cewa duk da cewa kakar ta ki amincewa, amma sai da matar ta nace ta dauki yaron da cewa za ta kula da shi, bayan nan ne kuma sanya masa tafasasshen ruwa a gaban nasa, maimakon ruwan dumi. Duk da raunin da tafasasshen ruwan ya yi  masa kuma, sai aka kai shi wurin mai maganin gargajiya...
    Sojojin HKI sun sanar da cewa a Yau Alhamis biyu daga cikinsu sun halaka, yayin da wasu 8 su ka jikkata sanadiyyar abinda su ka kira faduwar injin daukar abubuwa masu nauyi akansu, a kusa da Gaza. Sanarwar sojojin na mamaya ta kuma ce, biyu daga cikinsu suna da mukamai da suke a karkashin bataliyar rundunar Gulani ta 51.
    An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron. DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta. An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata...
    Mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a zaman lafiya da hakuri a tsakanin al’ummar garin Rimin Zakara sakamakon rikicin filaye da ya barke tsakanin al’umma da Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).   Sarkin ya yi wannan roko ne a ziyarar da ya kai yankin bayan dawowarsa daga aikin hajji.   Da yake jawabi ga al’ummar yankin, Sarkin ya jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a rikicin tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa.   “Dole ne mu yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan rashi, Allah ya sa wannan ya zama na karshe a cikin irin wannan mummunan lamari a cikin al’ummarmu,” inji...
    Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya gana da masu ruwa da tsaki a harkokin sufuri domin tattauna yadda ake ci gaba da aiwatar da aikin inshorar motoci na wasu motocin da ke bin hanyoyin jihar Kano.   Taron wanda ya samu halartar shuwagabannin kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa (NURTW), kungiyar masu safara a tituna ta Najeriya (NARTO), kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (RTEAN), da kuma shugaban tashar motocin Kano Line da nufin tabbatar da bin ka’idojin inshora.   CP Dogo ya yabawa masu ruwa da tsaki bisa hadin kan da suka bayar, inda ya ce sama da kashi 85% na masu ababen hawa sun mallaki takardar inshorar motocin da ake bukata daga ranar farko da...
    A wani umurnin da ya bayar Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran, Imam Aya. Sayyid Alilul Khami’nae ya sanya babban sakataren kungiyar Hizbullah a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Bayan shahadar Sayyed Hassan Nasarallah da kuma Sayyed Hashim safiyuddeen An zabi sheikh Na’em Kasim a matsayin babban sakataren kungiyar ta Hizbullah a kasar Lebanon. Kafin haka dai Shahid Sayyed Hassan Nasarallah ne mai wakiltar jagoran a kasar ta Lebanon. Sheikh Qasim dai  ya taka rawar a zo a gani  wajen yakin da kungiyarsa ta shiga da HKI na watanni 15.. Kuma ana saran shi ne zai zama mai fitar da kungiyar zuwa tudun na tsira daga halin da ta shiga ciki ya kuma ci gaba da yakar kungiyar.
    Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe. Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya. Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku...
    Sakamakon yadda kasar Sin take ci gaba da zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, da kyautata bude kofa ga ketare bisa matakin koli, ya sa kasar ta Sin za ta ci gaba da kara azama kan bunkasar tattalin arziki. Za kuma ta ci gaba da nuna kuzari kan raya kanta tare da amfanar da duniya baki daya. (Tasallah Yuan)    
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya nada Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah Sheikh Na’im Qassim a matsayin wakilinsa a kasar Lebanon. Marigayi Sayyid Hassan Nasrullahi tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah da ya yi shahada, a yakin baya-bayan nan kan kasar Lebanon, shi ne tsohon wakilin mai martaba Imam Khamenei a kasar Lebanon kafin shahadarsa.
    Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
    Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar Rundunar sojin Sudan ta sanar a yau jiya Talata cewa: Sojojinta da mayakan da suke goya musu baya sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar, kuma babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar Janar Abdul-Fattah Al-Burhan ya yi alkawarin samun nasara a nan kusa kadan kan wadanda ya kira ‘yan tawaye. Sojojin Sudan sun watsa labarin ta hanyar kafofin Facebook da Instagram tare da wallafa faifan bidiyon yadda al’ummar birnin suka fito kan tituna suna bayyana murnarsu da ‘yantar da birninsu daga hannun ‘yan tawaye tare da bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba ga sojojin Sudan. A nasa...
    Bisa wannan batu za mu iya ganin cewa, a wannan zamanin da muke ciki na samun ci gaban fasahohi cikin matukar sauri, ya kamata a kara nuna ra’ayi na bude kofa, da karfafa hadin gwiwa da cudanya da juna, maimakon nuna ra’ayin ‘yan mazan jiya da kasar Amurka da wasu kasashe suke yi, inda suke neman yin amfani da takunkumi da babakere wajen kiyaye fifikonsu a bangaren kimiyya da fasaha, matakin da ya raunana su ta fuskar karfin kirkiro sabbin fasahohi, abin da ya zama “Don auki ake yin kunu, ya koma ya rasa auki” ke nan. Sai dai ko da yake batun nan ya kasance gargadi ga kasar Amurka da wasu, zai karfafa gwiwar ‘yan Afirka. A ganin masaniyar...
    A yau ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a wata ziyarar kashu kai, inda daga nan zai wuce Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a birnin Addis Ababa, shugaba Tinubu zai bi sahun shugabannin Afirka a zaman taron majalisar zartarwa karo na 46 da kuma zaman taro na 38 na shugabannin kasashen kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU, wanda aka shirya daga ranar 12 zuwa 16 ga watan Fabarairun 2025. Shugaban zai isa Addis Ababa a farkon mako mai zuwa don halartar taron kungiyar  ta AU. Yayin da yake...
    Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar zai bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU). A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin...
    Shugaba Bola Tinubu a wannan Larabar ya bar Nijeriya zuwa ƙasar Faransa domin kai wata ziyara ta ƙashin kai. Daga nan kuma Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Habasha inda zai halarci taron gamayyar ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU. NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana Dalilin da farashin citta ya yi tashin gwauron zabo Mai bai wa Tinubu shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga a shafinsa na X, ya ce Tinubu zai tafi Paris ɗin ne gabanin tafiyar da zai yi zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha domin taron ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU). A lokacin taron da za a yi a birnin na Addis Ababa a farkon mako mai zuwa, Shugaba Tinubu zai gana da shugabannin ƙasashen Afirka domin...
    Kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 ta sanar da tsagaita wutar yaki a garin Goma da take rike da shi, saboda dalilai na jin kai. Kungiyar wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda wacce ta kwace iko da birnin Goma da shi ne birni mafi girma a gabashin wannan kasa, ta sanar da tsagaita wutar yaki ta gefe daya saboda abinda ta kira samar da damar gudanar da ayyukan agaji. Kungiyar ta ce, ta amince da tsagita wutar yakin ne domin amsa kiran da aka yi dangane da hakan, saboda a taimaka wa dubun dubatar mutanen da suke a tarwatse saboda yaki. Ya zuwa yanzu dai babu wani furuci da ya fito daga gwamnatin kasar DRC akan batun tsagaita wutar...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Amurka da ta kama Fira ministan “Isra’ila” Benjamin Netanyahu da yake ziyarar aiki a kasar. A wasu jerin sakwanni da kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta duniya ta wallafa a shafinta na X, ta bayyana cewa; Yadda Amurka ta karbi bakuncin Benjamin Netanyahu alhali ana zarginsa da manyan laifuka, yana nuni da cewa ta raina kotun ta kasa da kasa. Har ila yau kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta kuma kara da cewa; Gwamnatin da ta gabata ta Amurka a karkashin Joe Biden ta yi watsi da duk wani yunkuri na shimfida adalci a duniya, kuma shi ma shugaba Trump abinda yake yi kenan a yanzu. Wannan...
    Masana kimiyyar kasar Sin sun kirkiro wani sabon samfurin kirkirarriyar basira ta fasahar AI domin yin hasashen zuwan mahaukaciyar guguwa, wanda hakan ya ba da sabuwar fa’ida da kara haskaka hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i a duniya. A kwanan baya, masu bincike daga cibiyar nazarin teku a kwalejin kimiyya ta kasar Sin sun wallafa wannan binciken a cikin mujallar da ke wallafa harkokin kimiyya ta kasar Amurka, watau “Proceedings of the National Academy of Sciences.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
    Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta sanar da fara shawarwarin tsagaita wuta a mataki na biyu tsakaninta da Isra’ila. Kakakin Abdul Latif al-Qanou ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a kafar sadarwar zamani. A cikin wata sanarwa da ta fitar a tashar ta Telegram mai magana da yawun kungiyar Abdel Latif al-Qanoua ya zargi Isra’ila da “jinkirta aiwatar da ka’idojin jinƙai a yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma dakatar da aiwatar da hukuncin kisa.” Ya ce har yanzu kungiyar Falasdinu ta damu da batutuwa da dama da suka hada da matsuguni ga mutanen Gaza, da kuma kayan agaji da kuma kokarin sake gina yankin. Al-Qanou ya kuma zargi Isra’ila da “katse” ka’idojin jin kai da ke...
    Kasar Kenya mai rike da shugabancin kungiyar kasashen gabashin Afirka ta EAC, ta sanar cewa za’a gudanar da wani taron hadin gwiwa da kungiyar raya kasashen yankin kudancin Afirka ta SADC a ranar Juma’a a Dar es Salaam, babban birnin kasar Tanzania. Taron na kwanani biyu zai samu halartar shugabannin kasashen Rwanda da Kongo, Paul Kagame da Félix Tshisekedi. Al’amura sun dagule a yankin na gabshin Kongo bayan harin da ‘yan tawayen M23 – da Rwanda ke marawa baya suka kai a Goma, babban birnin Kivu ta Arewa, a makon jiya, da kuma fadan baya-bayan nan a Kudancin Kivu. A cikin ‘yan kwanakin nan, kungiyoyin biyu da ke da ra’ayi daban-daban kan yadda za a warware rikicin, sun bayyana fatan...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, an kashe sojoji 2 a yankin kusa da Tubas dake Arewacin yammacin kogin Jordan. Kafafen watsa labarun sun kuma ce,  maharin ya isa wani shinge na soja dake kusa da Tayasir, ya kuma boye a cikin hasumiyar da masu tsaro ke zama a ciki, sannan ya bude wa sojoji wuta daga sama. Har ila yau  maharin ya yi bata-kashi da sojojin da suke a wajen, sai dai a karshe sun ci karfinsa, da hakan ya yi shahadarsa. A bayanin da kungiyar Hamas ta fitar ta jininawa maharin tare da cewa, abinda hakan yake nufi shi ne cewa hare-haren da ‘yan sahayoniya suke kai wa ba za su tafi haka kawai ba tare da...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
    Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya kasance daga cikin shirye-shiryen kasar na shirin kare sararin samaniyar kasar ta sama. Labarin ya kara da cewa a wannan karom ma sojojin Iran da kuma dakarun juyin juya halin musulunci zasu yi atisayen hadin giwa ne don gwada karfin sojojin kasar da kuma IRGC na kare sararin samaniyar kasar. Kafin haka dai sojojin sun gwada karfinsu a bangarori daban daban na sojojin kasar don...
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf a wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Iraki Mahmoud al-Mashhadani, ya bayyana cewa: Kasashen Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Iran da kawarta Iraki sun kuduri aniyar marawa bangaren gwagwarmaya baya domin kare Musulunci da martabar al’ummar musulmi. Baqir Qalibaf ya kara da cewa: Sun ba da muhimmanci wajen raya hanyar layin dogo, musamman sabuwar...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan haramtacciyar kasar, Benjamin Netanyahu zuwa birnin Washington na Amurka, ya dauki wata hanya ta musamman, domin ya gwammace ya kaucewa wucewa ta sararin samaniyar kasashe wadanda suka tabbatar da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da sammacin kama Netanyahu idan ya shiga sararin samaniyarsu. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba...
    Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna adawa da yadda ake ci gaba da ruruta wutar rikici a shiyar gabashin kasar. Shafin sadarwa na yanar gizo na Russia Today ya bayyana cewa: Al’ummar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da suke cikin fushi sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashen Rwanda da Faransa da Belgium da kuma Amurka, yayin da hayaki ke tashi daga ginin ofishin jakadancin Faransa. Masu zanga-zangar sun kona tutar Amurka tare...
    Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna. Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da...
    Hukumar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta ce an yi wa wani mutum mai shekara 59 tiyata domin ciro sunƙin hodar ibilis 57 cikin guda 81 da ya haɗiye kwanaki bakwai da suka gabata a Addis Ababa da ke kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ta ce an kama mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjoji bayan isar su filin jirgin sama na Murtala Muhammad daga Habasha a ranar 26 ga watan da ya gabata. Kakakin hukumar ya ce bincike ya gano cewa mutumin wanda ya yi iƙirarin ɗan kasuwa ne a yankin Oshodi da ke jihar Lagos, ya tafi Addis Ababa inda ya haɗiyi sunƙi...
    Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid  Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon. Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken...
    Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik al-Husi ya  yaba wa yadda kungiyar Hamas ta jajurce da ci gaba da wanzuwa a dunkunle duk da cewa kwamandan dakarunta Muhamamd Dhaif ya yi shahada. Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya gabatar da jawabi ne na tunawa da zagayowar lokacin shahadar Salih al-Simad wanda daya ne daga cikin manyan shugabannin Ansarullah, ya kara da cewa, ci gaba da wanzuwar kungiyar ta Hamas yana daga cikin muhimman ayyukan da Muhammad Dhaif ya aiwatar a lokacin rayuwarsa. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya mika sakon ta’aziyyar shahadar Muhammad Dhaif ga kungiyar ta Hamas, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagorori abin koyi saboda ruhinsa na imani mai karfi, azama da ruhi na...
    Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa ido da masu shiga tsakani don dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” in ji shi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin dazu. Sheik Qasem ya ce kungiyar Hizbullah na taka-tsan-tsan don bai wa gwamnatin Lebanon damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Faransa da Amurka suka shiga tsakani...
    A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin. Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda ba zai ba da damar daidaita matsalar da kasar Amurka ke fuskanta ba, maimakon haka, zai lalata huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Ban da haka, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta ce, kasar Sin za ta kai kara ga kungiyar cinikayya ta duniya, da daukar matakai don mayar da martani ga matakin Amurka....
    Kasashen 3 na yankin sahel sun kafa ta su kungiyar mai suna “Kawancen Sahel” (AES). Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata kungiyar Ficewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga kungiyar Ecowas a ranar Laraban nan bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakanin kungiyar da kasashen guda uku, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga cigaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas. A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da kungiyar Ecowas a hukumance dangane da bukatar ficewar tasu. To sai dai bisa dokokin Ecowas, kasashen na bukatar sanar da kungiyar shekara guda kafin amincewa...
    Tashar Talabijin din “ Almanar” ta sanar da cewa, da marecen yau Lahadi ne babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim sai yi jawabi akan muhimman abubuwan da suke faruwa a Lebanon da kuma wannan yankin. Har ila yau, Almanar ta ce babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim zai yi bayani akan lokacin da za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah ya yi shahada ne a sanadiyyar hare-haren masu muni da jiragen yakin HKI su ka kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beiruta. Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce sun jefa bama-bamai da su ka nai nauyin tan 85 akan ginin da Shahid Sayyid Hassan Nasrallah yake ciki.
    Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
    Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
    Kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid ta zargi Manchester City da karfafa gwiwa ga daya daga cikin ‘yan wasanta, Juma Bah domin ya soke yarjejeniyarsa ya koma buga Premier League da buga wasa. Dan wasan mai tsaron baya, ya sanar da kungiyar ta Sifaniya ranar Talata cewar yana so ya katse yarjejeniyarsa, saboda ya koma Manchester City kan kankanin kudi. Tun a baya Manchester City ta nemi izinin Balladolid, domin tattaunawa kan sayen matashin mai shekara 18, domin ya koma buga mata wasa amma sai kungiyar ta ce tana son dan wasanta kuma ba na sayarwa bane. Bah bai halarci atisaye ba ranar Laraba ba, inda hukumar kwallon kafar Sifaniya ta tabbatar cewar ya biya sauran kunshin kwantiraginsa a kungiyar,...
    Shuwagabannin kungiyar kasashen raya tattalin arziki da kuma tsaron kasashen Afrika da kudu ta ce zasu ci gaba da wanzar da sojojinsu a kasar Congo duk tare da sauye-sauyen da kungiyar yan tawaye na M23 suka yi a yankin arewacin KIVU. Shafin yanar gizo na Labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa shuwagabannin kungiyar sun bada wannan sanarwan ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a kasar Zibabwe a ranar Jumma’an da ta gabata. Shugaban kungiyar na riko-riko kuma shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya yim kira ga kungiyar ta kasance mai nuna karfi da da kuma juriya kan abubuwanda da ke faruwa a arewacin congo. Sojojin tabbatar da zaman lafiya na kungiyar a cikin makonnin da suka gabata sun...
    Gwamnan ya kara jaddada Gwamnatinsa ta maida hankalin ta ne kan irin ayyukan da za ta yi wa al’umma, inda ya yi kira kamata ya yi koda wane lokaci Shugabanni su rika tunawa da al’umman da suka zabe su, suna yi ma su aiki. Da yake kara yin bayani Gwamna Ododo ya ba kungiyar mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi kan kudurin sa na ci gaba da kammala duk bada wadansu mukamai na magoya bayan sa fda suke a Karkara. Ya yi kira da mambobin kungiyar da wadanda suka amfana da taimakon kungiyar,su ci gaba da aiwatar da abubuwan da suka sa a gaban su, saboda ayyukan alkahairin da suka fara zai samar da babbar gudunmawar ci gaba a wasu shekaru ma...
    Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran,  shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Asabar ce shugaban kasar Iran, Masuod Pezeshikyan tare da majalisar ministocinsa suka kara sabonta bai’a wato marigayi Immam Khomani (q).   Labarin ya kara da cewa Sayyid Hassan Khomani, jikan Imam(q) wanda kuma yake kula da hubbaren nasa ne, ya tarbi shugaban kasar ya kuma jagorance su zuwa hubbaren kakansa Imam Khumaini(q). Imam Khomani (q) ne ya jagoranci mutanen kasar...
    “Sauran abubuwan baje kolin da aka kwato daga hannun mutanen biyu sun hada da: bindigogi guda uku da aka kera a cikin gida; bindiga guda da aka yi a gida guda biyu; bindigar zamani guda daya; bindigar gida guda daya; cartridges guda uku da 9mm mara komai da gatari mai kan karfe. “Wani farmakin da aka kai Legas, ya kai ga kama skunk mai nauyin kilogiram 47, wani nau’in tabar wiwi, da kuma Nitrous Odide mai nauyin kilogiram 25.46 da aka fi sani da dariya a unguwar Akala da ke Mushin,” Babafemi ya kara da cewa. A Jihar Ekiti, Babafemi ya ce jami’an NDLEA sun kama wani matashi dan shekara 26 mai suna Adepoju Taiwo, dauke da kilo 1.950 na...
    Har ila yau, sun bayar da wannan shawara ce, duba da irin rawar da wadannan kalubale biyar ke takawa a lokacin kakar noma ta 2023 da kuma ta 2024. 1- Kalubalen Rashin Tsaro: Wannan matsalar na jawo wa manoma da sauran masu son zuba hannun jari a fannin koma baya, musamman duba da yadda ‘yan bindigar daji ke halaka manoma da kuma yin garkuwa da su da dama a 2024. Hakan ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da ya kai kimanin kashi 39.84, musamman a watan Disambar 2024. Kwararrun sun bayar da shawarar cewa, idan har ana bukatar samar da wadataccen abinci a 2025, ya zama wajbi a dauki matakan da suka dace, don kare rayukan manoma da kuma...
    Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga  babban birnin kasar Kinsasha. Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu  ita ce, muna yin yaki ne saboda kishin Congo, ba muna yaki ne saboda samun ma’adanai ba, babu wani dalili na daban da ya sa muke yaki.” Da akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa, ‘yan tawayen na M 23 sun kama hanyar zuwa Bukavu, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a yankin. Nangaa ya ce babu wata gwamnati tsayayya a kasar Congo, domin Tshikedi ya riga ya...
    A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif  tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da  suka taka a fagen gwagwarmaya. Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa da kuma al’ummar Falasdinu. Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta mika sakon ta’aziyyar ga iyalan shahidan. Kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Lebanon ta kuma ambaci cewa, Muhammad Dhaif ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne wajen fada da ‘yan sahayoniya da kwankwasar kansu, musamman ma dai a yayin farmakin Aksa, da ya kasance daya daga cikin fitattun wadanda...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi. Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?. A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda...
    A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...
    Gwamnonin tafkin Chadi da suka haɗa da Nijeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, sun zaɓi gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin sabon shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin. Sanarwar na cewar, an zaɓi Gwamna Buni ne a ranar Juma’a a ƙarshen taron ƙungiyar gwamnonin tafkin Chadi karo na 5 da aka gudanar a Maiduguri. ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas Tun farko shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne wanda mataimakin shugabansa Kashim Shettima ya wakilta ya bayyana buɗe taron da gwamnatin Jihar Yobe ta shirya. Gwamna Buni a jawabinsa na karramawa ya yaba wa shugaba Tinubu bisa yadda ya samar da jagoranci ga ƙasa da...
    A kan yawan samun hauhawan farashin man Garima yace kungiyar na samun saukin farashin sawo man man daga matatar Dangote Refinery da ta MRS duba da cewa, farashinsu na da sauki sosai. Garima da yake yin tsokaci a kan yawan samun hauhawan farashin man a kasar nan, ya bayyana cewa, ‘ya’yan kungiyar na samu sayen man da sauki daga gun matatun main a Dangote da kuma na MRS. A cewarsa, a yanzu haka ‘ya’yan IPMAN na yin dakon man daga gun wadannan matatun biyu, ba tare da matatun sun yi masu karin farashin man ba, inda ya shawarci sauran ‘ya’yan kungiyar da su je su yi rijista da wadannan matatun, domin su rinka sawo man da sauki.
    An bayyana dangantakar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika a matsayin wadda ta taimaka wajen gaggauta ci gaba da samar da irin zamanantarwar da nahiyar ke bukata domin ta kasance cikin takara a duniya. Muya Guo, shugabar sashen Sin a bankin Stanbic na Kenya ne ta bayyana haka yayin wata hira a Nairobin Kenya, inda ta ce dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Afrika tare da jarin da kasar ta nahiyar Asiya ke zubawa, sun dora nahiyar kan tafarkin samun ci gaba, yayin da ta zamanantar da muhimman bangarori kamar na kere-keren kayayyaki. ‘Yan Adawa Sun Caccaki Buhari Kan Kalamunsa Na Cewa, ‘Allah Ne Kadai Zai Iya Gyara Nijeriya’ Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa...
    Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga jirgin saman Air France da ya dawo da Imam Khumaini gida daga gudun hijira na sama da shekaru 14 wanda ya kai ga kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin bukukuwan al’ummar Iran suna halartar taruka daban-daban har zuwa zagayowar ranar 22 ga watan Bahman wato 10 ga watan Fabrairu, wato ranar tunawa da juyin juya halin Musulunci. Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi. Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa. Shekara guda bayan binne shi,...
    Da yake magana ta cikin shirin siyasa na talabijin Channels, ministan ya ce, shugaban kasa bai yi wasu tafiye-tafiyen da suka isa ba. “Har yanzu wannan gwamnatin sabuwa ce. An rantsar da shi a 2023. Ta fuskancin duniya har yanzu shi sabon shugaban kasa ne. Yana bukatar tattaunawa da ganawa da takwarorinsa domin gina alaka mai kyau a tsakaninsu, sannan kuna iya ganin amfanun irin wadannan tafiye-tafiyen. “Za ka sake tafiya ka samu zuba jari na dala biliyan 2 kamar yadda ya yi a Brazil. A zahiri, ba mu ma yi tafiye-tafiyen da suka isa ba. Ina ba da shawarar mu sake yin wasu karin tafiye-tafiyen. “Nijeriya tana da dinbin dukiya. Nawa ne tafiyar zai lakume idan aka kwatanta da...
    “Da na tambaye shi dalili, sai ya ce al’ummominmu suna fama da barnar ‘yan bindiga da hakan ke janyo asarar rayuka da garkuwa da mutanenmu tsawon shekaru zuwa yanzu ba tare da samun mafita da shawo kan lamarin ba.” Gwamnan ya ce bayan rokon, ya zauna da masu ruwa da tsaki ciki har da mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, kafin daga karshe suka amince da fito da shirin yin sulhun. Ya kara da cewa matakin na zuwa ne bayan da ‘yan fashin dajin suka sako mutane 200 da suka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari. Gwamnan ya nuna fatansa na cewa matakin zai dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar...
    Shekara 18 da fara aikin gina babban asibitin kwararru mai gado 300 a unguwar Sabuwar Kaduna (Millennium City) amma har yanzu aikin bai kammalu ba. Aikin wannan katafaren asibiti, wanda ake hasashen babu irinsa a fadin yankin Yammacin Afirka, ya yi zamani da gwamnoni biyar, kowannensu na sa lokacin kammala shi, amma har yanzu abin ya gagara. Sau hudu gwamnonin jihar daban-daban suna sa wa’adin kammalawa da kaddamar da wannan katafaren asibiti, ba tare da haka ba ta cimma uwa ba. A shekarar 2007 tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Muhammad Namadi Sambo tare da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci na Duniya suka assasa aikin ginin asibitin da wa’adin kammala shi a cikin shekara biyar, wato 2012. An yi fatan zai kasance...
    A nata jawabin, babbar mai shari’a ta Jihar Gombe, Mai Shari’a Halima S. Mohammed, ta bayyana cewa an shigar da kararraki guda 616 wadanda suka shafi manya da kananan laifuka da kuma cin zarafi a babbar kotun jihar, daga cikinsu 555 an kammala shari’arsu, inda wadanda suka rage ba su kai 70 ba. Ta bayyana godiya ga Gwamna Yahaya bisa ba da kwangilar biliyoyin naira na gina babbar sakatariyar kotun da sauran taimako da dama. Babban Lauyan gwamnatin jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barrister Zubairu Muhammad Umar, ya bayyana cewa gwamnatin Yahaya ta taka rawar gani wajen samun nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a yunkurinta na ciyar da sashin shari’a gaba.
    Kungiyar Hamas ta sanar da sunayen mutum uku da za ta mika wa kasar Isra’ila a Gaza a ranar Asabar a ci gaba da musayar fursunonin yaki tsakaninsu. Bayan sako ’yan Isra’ila uku da ’yan kasar Thailand biyar a ranar Alhamis, Rundunar Qassam , sashen sojin Hamas ta sanar ranar Juma’a cewa wadanda kungiyar za ta sako su ne Ofer Kalderon da Keith Siegel da kuma Yarden Bibas. Hakan na zuwa ne bayan a cikin dare jiragen yakin Isra’ila sun kashe Palasdinawa 10 a sansanin ’yan gudun hijira na Jenin da ke garin Tammun da ke yankin Yammacin Kogin Jordan. Kazailka ’yan sandan Isra’ila sun kama Palasdinawa 12 a yankin Gabashin Birnin Kudus a yayin da suke murnar sako ’yan...
    Kotu ta daure wata matar aure da wani magidanci a gidan yari kan aikata lalata da juna. Kotun Majistare da ke Gwagwalada a Abuja ta yanke wa zawararwan hukuncin ɗaurin wata uku kowannensu ne bayan samun su laifin aikata zina da junansu. Matar mai shekaru 25 da bazawarin mai shekara 30 sun amsa laifin a lokacin da aka karanta musu takardar tuhumar a gaban kotun. Zawarawan sun kuma buƙaci kotun ta yi musu sassauci. Da farko alƙalin ya ba da umarnin tsare su har sai sun kawo shaida da za su yi rantsuwa cewa su mutanen kirki ne, amma suka kasa. Daga bisani Alƙali Olatunji Oladunmoye, ya yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin wata uku ko biyan tarar Naira 25,000. Tun...
    Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa. Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami. Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar cewa wata shida bayan kammala ba su horo da sauya tunanin tsofaffin mayaƙan, amma har yanzu babu labarin ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya yi tubar muzuru. Shugabar Sashen Daƙile Rikice-rikice Masu Alaƙa da Tsattsauran Ra’ayi (PVEA)  ta Cibiyar, Ambasada Mairo Musa Abbas, ce ta bayyana haka a yayin taron gwamnonin yankin Tafkin Chadi a Maiduguri, Jihar Borno. NAJERIYA...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada aniyar Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a dukkan fannoni Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi nuni da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Iran da Qatar, yana mai jaddada aniyar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na bunkasa alaka da kasar Qatar a fannoni daban daban. Wannan ya zo ne a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi a birnin Doha a jiya Alhamis, tare da fira ministan Qatar kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al- Thani. Taron ya tattauna batutuwa da dama da suka shafi bangarorin biyu, da suka hada da ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma ci gaban yankin,...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace. Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci...
    Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin Qatar, Doha a jiya Alhamis. Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, tawagar kungiyar ta hada da shugabannin Khalil Al-Hayya, Hussam Badran, Izzat Al-Rishq da Basem Na’im. Darwish ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tallafa wa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yancin kai, yana mai jaddada cewa: “Harin Daukan Fansa naAmbaliysar Al-Aqsa Mai Albarka” wani ci gaba ne a yunkurin al’ummar...
    Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan mamayar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Za ta yi aiki da dukkan karfi da azamarta har sai ta raba fursunonin Falasdinawa da gidajen yarin ‘yan sahayoniyya, tare da yin nuni da cewa, za ta ci gaba da kokarinta ba tare da wata matsala ba, domin kubutar da su ta kowace hanya. Kungiyar Hamas ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a a yayin bikin sakin wani sabon rukunin fursunonin Falasdinu, tana jaddada cewa: Hamas ta sake sanar da babban alfahari da girmamawa ga al’ummar Falastinu masu tsayin daka,...
    Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa. A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara...
    Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis. Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina...