2025-02-22@21:47:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1174

«shugaban kasar»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”. A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kwango, matakin ya “hana shawagi da sauka a cikin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, saboda dalilai na rashin tsaro da ke da nasaba da rikicin masu dauke da makamai.” A taswirorin zirga-zirgar jiragen sama na duniya, jiragen sama daga Kigali na kasar Rwanda, yanzu haka na kaucewa shiga sararin samaniyar Kongo. Bayanai sun ce wani jirgin da ya tashi daga babban birnin kasar Rwanda zuwa birnin Landan na kasar Birtaniyaa ranar Talata, an tilas ya sauya hanyarsa don yin aiki da dokar, wanda a yanzu ya shafi “dukkan jiragen...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rediyo na daga cikin kafofin da al’umma da dama suka dogara da su don jin labarai, shirye-shirye da kuma samun nishadi. Rediyo na taka muhimmiyar rawa wajen wayar wa da al’umma da dama kai musamman duba da yadda aka bayar da shaidar cewa tafi kowace kafa saurin yaɗa bayanai ba a cikin birane ba, har ma da yankunan karkara. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Sai dai a wannan gaɓa ana ganin gidajen rediyo a Arewacin ƙasar nan na samun koma baya, la’akari da yadda a wasu lokutan wasu suke rufe harkokinsu su ɓace...
    Har ila yau, ga irin su Apple, Microsoft, da Google da duk sun samu gindin zama a kasar Sin tare da bude ofisoshi da ressan masana’antu a biranen Shanghai, Beijing, da Shenzhen. Haka nan sauran kamfanoni irin su Coca-Cola, da PepsiCo duk sun tsayu da kafafunsu sosai a kasar. Bugu da kari, ga kamfanonin harkokin biyan kudi ta fasahar zamani kamarsu Amazon da PayPal da su ma suka samu hadin kan kamfanonin kasar Sin don fadada kasuwancinsu a cikin kasar. Duka wannan yana nuna yadda Sin ke fada da cikawa ne a kan manufofinta na kara bude kofa ga duniya. Kuma ya dace Amurka ta nuna sanin ya kamata a kan bahaguwar fahimtarta da sake lale kan matakanta na haddasa...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
    A yau Laraba, kafar yada labarai ta CGTN ta hada gwiwa da tashar watsa labarai ta lardin Heilongjiang na kasar Sin ta kamfanin CMG, wajen shirya wani bikin musayar al’adu na kasa da kasa, wanda ya shafi gasar wasannin kankara ta nahiyar Asiya dake gudana a Harbin, gami da bikin fitilu na gargajiyar kasar Sin. Mahalartar bikin sun hada da ‘yan wasa da ‘yan jaridu na kasashen nahiyar Asiya daban daban. (Bello Wang)  
    Fitaccen ɗan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, ya ce ya yi nadamar mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2023. Yayin da yake zantawa da Aminiya ta wayar tarho, Kwamanda ya ce Shugaba Tinubu ya watsar da waɗanda suka sha wuya a kansa, duba da halin da ƙasa ke ciki a yanzu. Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta Ya bayyana cewa, a duk tsawon rayuwarsa, bai taɓa yin nadamar wani abu kamar yadda ya yi nadamar mara wa Tinubu baya ba. “Da ciwo, amma dole a faɗi gaskiya. Ni cikakken ɗan jam’iyyar APC ne,...
    Ƙungiyar na buƙatar kamfanonin su dawo wa Nijeriya da kuɗaɗen da suka kwashewa ‘ƴan ƙasa. Kamfanin sadarwa na MTN ya fara amfani da sabon tsarin ƙarin kudin awanni kaɗan bayan da majalisar wakilai ta kasa ta bukaci gwamnati da ta dakatar da ƙarin.
    Taro kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da ya gudana a Paris na Faransa, ya ja hankalin duniya. Masu rattaba hannu 61 ciki har da Faransa da Sin da India, sun fitar da wata sanarwa cewa za su nace wajen raya wannan fasaha bisa ka’ida ba tare da rufa rufa ba, kuma ta kowane bangare. Kimiyya ba ta da iyaka. Idan muka waiwayi ci gaban bil adama, ba a taba raba kowace nasara da aka samu a binciken kimiyya da kirkire kirkiren fasaha da hadin gwiwa da musaya tsakanin kasa da kasa ba. Gwamnatin Sin na goyon bayan ci gaban kimiyya da fasaha ta kowane bangare, kuma a shirye take ta gabatar da gogewarta a fannin ga duniya. DeepSeek, samfurin...
    Alkaluma daga hukumar kula da jigila da sayen kayayyaki ta kasar Sin sun nuna cewa, darajar jigilar kayayyakin jama’a da aka yi a kasar Sin a shekarar 2024, ya karu da kaso 5.8 zuwa yuan triliyan 360.6, kwatankwacin dala triliyan 50.28, idan aka kwatanta da 2023. Zuwa karshen 2024, kasar ta samar da cibiyoyi 151 na jigilar kayayyaki na kasa da sama da wuraren ajiyar kayayyaki 2,500 a kasashen waje. Haka kuma ta bude sabbin hanyoyi 168 na jiragen dakon kayayyaki na kasa da kasa a baran. A cewar Hu Han, jami’i a cibiyar tattara bayanan da suka shafi jigila ta kasar, ingantawa kayayyakin aiki da suka shafi jigila da daukaka tsarin hanyoyin jigila sun bunkasa ware albarkatu ga bangaren...
    A karshe ya ce yana neman afuwa ga al’umma saboda tallata gwamnatin Tinubu da ya yi akan za ta yi abin kirki amma sai aka samu akasin haka.
    A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama ce ta hadin kan mutanen kasar Iran, har’ila yau jawabi ne ga barazanar da makiya JMI suke mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka bayan ya zagaya ya ga sabbin makamai wadanda masana’antun makamai na kasar suka kera. Ya kuma yaba da irin ci gaban da masana’antun suka samu. Imam Khaminae ya kuma yaba da ayyukan da masu...
    Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ta dauki alhakin harin da aka kai a lardin Kunduz na arewacin kasar Afganistan, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 5 da kuma raunata wasu da dama. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto “Daesh Khorasan” tana fadar haka a shafinta na sadarwa, bayanda wani dan ta’adda ya tarwatsa kansa a kusa da wani banki a garin Kunduz, wanda ya halaka shi ya kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla guda biyar. Labarin ya kara da cewa an kai harin kunan bakin wakenne da misalign karfi 8:35 na safe a yau Laraba, wato 4:05 na safe agogin GMT. Mai gidan bankin da kuma wasu mutane 4 daga cikin akwai fararen hula da kuma wani...
    Jakadan kasar Rasha a nan Tehran Alexey Dedov ya bayyana damuwarsa da yadda kasar Amurka take son ta maida kasashen Rasha da China gefe a tattaunawar shirin Nukliyar kasar Iran, in har za a tattauna, ya kuma jaddada muhimmancin samuwar kasashen biyu a tattaunawar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dedov ya na cewa rashin halartar kasashen Rasha da China a cikin duk wata tattaunawa dangane da shirin Nukliyar kasar Iran, zai kawo gibi mai yawa a harkokin siyasa da tsaro a yankin Asiya. Jami’in diblomasiyyan ya kara da cewa kasahen yamma suna son maida kasashen biyu gefe a cikin tattaunawar, a yayinda kasancewarsu a cikin taron yana da matukar muhimmanci saboda al-amarin zai shafi yankin gaba...
    Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya kara jaddadawa Sarkin Jordan Abdullahi II kan shirinsa na kwace yankin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan ya maida shi wurin shakatawa, da kuma kan cewa kasar Jordan da Masar ne zasu dauki nauyin kula da Falasdinawa kimani miliyon 2 a Gaza a cikin kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Trump yana fadar haka a ganawarsa da Sarkin a birnin Washington a yau Laraba. A nashi bangaren Sarkin kasar ta Jordan ya bayyana cewa yana ganin kasashen larabawa zasu dauki mataki guda ne a cikin wannan al-amarin, sannan zasu ji ta bakin Yerima Muhammad  bin Salman na kasar Saudiya da kuma Shugaba Abdul Fattah Assisi na kasar Masar, wadanda suke...
    Hukumar kula da ‘yan sama jannati na kasar Sin (CMSA), a yau Laraba, ta bayyana sunayen tufafin ‘yan sama jannati da motar zirga-zirga a duniyar wata na aikin binciken wata na kasar. CMSA ta ce, an sa ma tufafin na ‘yan sama jannati suna Wangyu, wanda ke nufin kallon duniyar sama, kuma ya yi daidai da sunan tufafin da ‘yan sama jannati su kan sa lokacin da suka fita daga tashar sararin samaniya, wato Feitian, wanda ke nufin tashi zuwa sararin samaniya. Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Yawan Motocin Da Sin Ta Fitar Zuwa Ketare A 2024 Ya Karu Da Kaso 23% Kazalika, sunan motar zirga-zirga a duniyar wata shi...
    Kungiyar Hamas a Gaza ta godewa kasashen duniya musamman kasashen Jordan da Masar dangane da kin amincewarsu da korar Falasdinawa a Gaza. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya ce zai kwace zirin Gaza daga hannun Falasdinawa, sannan zai tsugunar da su a kasashen Masar da kuma Jordan, suna so ko basa so. Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto kungiyar tana fadar haka a yau Laraba. Ta kuma kara da cewa. Mutanen gaza basa son rabuwa da kasarsu, ta kaka da kakanni. Kuma suna maraba da dukkan shawarorin da kasashe larabawa da sauran kasashe duniya zasu bayar, don ganin  an sake gina Gaza ba tare da an kori falasdinawa daga kasarsu ba. A wani Labari...
    Karon Farko A Shekarar 2025: Turken Rarraba Hasken Wutar Lantarki Ya Fadi A Nijeriya
    Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama. A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi. Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Haka kuma, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Bama da kuma dawo da wutar lantarki a yankin. Zulum, ya ƙara da cewa za a ci gaba da tallafa wa masarautar da gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata. Hakazalika,...
    Al’ummar Jihar Jigawa sun yi kira ga Gwamnan Jihar Malam Umar Namadi da ya yi amfani da kyawawan tsarin da gaskiya wajen zabar wadanda za su ci gajiyar shirye-shiryen bada tallafin karfafa sana’o’i. Sun kuma bukaci gwamnatin jihar da ta yi amfani da tsarin bayar da tallafin karfafa al’umma ma gwamnatin tarayya na (FADAMA) a  dukkan shirye shiryenta ta bada tallafi,  domin ganin al’ummar jihar sun ci gajiyar ayyukan gwamnati. Wani shugaban al’ummar yankin Walewale a karamar hukumar Garki, Malam Haruna Abdullahi, ya ce, hanyar da shirin FADAMA na gwamnatin tarayya ya yi amfani da ita ya tabbatar da cewa tallafin ya isa ga masu bukata. A cewarsa, tsarin ya kawar da son zuciya da siyasa, wanda...
    Dokokin Gyaran Haraji sun tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai, bayan tafka muhawara mai zafi a tsakanin ’yan majalisar. Tun da farko, an gabatar da ƙudirorin guda huɗu wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar, amma an haɗe su zuwa guda ɗaya domin sauƙaƙa nazari a kansu. An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC Jagoran majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere ne, ya jagoranci tattaunawar, inda ya jaddada buƙatar sauta tsarin harajin Najeriya. Ya ce dokokin za su sauƙaƙa biyan haraji, cire harajin kayayyakin buƙatu na yau da kullum kamar abinci da kiwon lafiya, tare da samar da rangwame ga ma’aikata masu ƙaramin ƙarfi. Yawancin ’yan majalisar...
    Kasar Sin Ta Yi Kiran Samar Da Ci Gaba Da Tsaro Bai-daya A Fannin Fasahar AI
    Mazauna Ungwan Ate da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun fito kan tituna domin yin zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da satar jama’a da suka addabi yankinsu. Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Ungwan Ate zuwa Ungwan Mission da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia. Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Sun kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don kare rayukansu da dukiyoyinsu. Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da Aminiya, ya ce ’yan bindiga sun shiga Ungwan Ate a daren ranar Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cin karensu...
    Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci a kan lamarin.   Har ila yau, ya yi kira ga hukumar makarantar da ma Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), da su girke tudu-tudu na rage gudu a kusa da makarantar domin kaucewa irin hatsarin nan gaba.
    Mazauna Ungwan Ate da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna, sun fito kan tituna domin yin zanga-zanga kan yawaitar hare-haren ’yan bindiga da satar jama’a da suka addabi yankinsu. Masu zanga-zangar sun toshe hanyar Ungwan Ate zuwa Ungwan Mission da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Kachia. Ɗan majalisar Kebbi ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Sun kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa don kare rayukansu da dukiyoyinsu. Wani daga cikin masu zanga-zangar da ya zanta da Aminiya, ya ce ’yan bindiga sun shiga Ungwan Ate a daren ranar Talata, inda suka shafe sama da sa’o’i biyu suna cin karensu...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Besse/Maiyama daga Jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Koko, ya sanar da wannan mataki ne cikin wata wasiƙa da ya aike kuma aka karanta a zauren majalisa. N50,000 aka biya ni don safarar harsasai zuwa Abuja – Matashi Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum Ya bayyana rikicin cikin gida a jam’iyyar PDP a matsayin dalilin da ya tilasta masa barin ta. Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan ficewar wani ɗan majalisar Kaduna, Amos Gwamna Magaji, wanda shi ma ya fice daga PDP sabida rikice-rikice. Sai dai shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya musanta zargin jam’iyyar na fama da rikice-rikice....
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum “Ni mazaunin Abuja ne. Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja. “Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum “Ni mazaunin Abuja ne. Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja. “Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda...
    Ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta fara rangadin tantancewa a kauyukan jihar, gabanin shirin wayar da kan al’umma game da yaran da ba su zuwa makaranta. Ziyarar na da nufin gano musabbabin wannan matsala tare da nemo mafita ta hanyar hada kai tsakanin al’umma. Kididdigar da Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar na nuna da cewa, Kano tana da kimanin yara 837,479 da ba sa zuwa makaranta, adadi mai ban mamaki da jihar ke kokarin magancewa.   Tawagar tantancewar, karkashin jagorancin jami’a mai kula da ilimin yara mata ta jihar, Hajiya Amina Kassim, ta ziyarci kauyuka da dama, inda ta tattauna da iyaye, da shugabannin gargajiya, da malaman addini. “Tawagar ta gano muhimman abubuwan da...
    Majalisar Wakilai ta buƙaci Hukumar Kula da Sadarwa (NCC) ta janye ƙarin kashi 50 na kuɗin waya da data da ta amincewa kamfanonin sadarwa su yi. Wannan dai na zuwa ne a yayin da ɗan majalisar daga Jihar Bayelsa, Oboku Oforji ya gabatar da ƙudirin kan lamarin. Majalisar ta ce ƙarin bai kamata ba a wannan lokacin, saboda har yanzu babu tsayayyen layin waya mai sabis mai kyau a cikinsu. Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su A don haka ne majalisar ta buƙaci NCC da Ministan Sadarwa, Bosun Tijani, su dakatar da ƙarin saboda matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya...
    Iran ta yi kakkausar suka kan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na yin amfani da karfi a kan kasar, inda ta bayyana hakan a matsayin barazana da rashin da’a. A cikin wata wasika da ya aike a wannan Talata zuwa ga shugaban Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhu na dindindin jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saïd Iravani, ya bayyana cewa kalaman na Trump na tada hankali sun sabawa dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin MDD. Trump ya ce zai gwammace ya kulla yarjejeniya da Iran maimakon “harba mata bam fiye da kima,” a wata hira da manema labarai a ranar Asabar. “Na fi son kulla yarjejeniya da ba za ta cutar...
    Kasar Aljeriya ta yi marhabin da shirin Iran na gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC a zirin Gaza, wanda shugaban na Amurka ya ce yana son karbe iko tare da raba al’ummar kasar baki daya. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya gabatar da shawarar gudanar da wani zama na musamman na kungiyar OIC a ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Aljeriya Ahmed Attaf, a wani bangare na tuntubar da yake yi da ministocin harkokin wajen kasashen musulmi kan Gaza. A yayin tattaunawar tasa, Mista Araghchi ya yi cikakken bayani kan shawarwarin da ya yi a baya-bayan nan da shugabannin kasashen musulmi, da kuma babban sakataren kungiyar OIC, Hussein...
    Kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana a wannan Talata a yayin wani taron manema labarai cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan ma’abuta girman kai, da kuma shahidan bil’adama a kan mulkin mallaka”. Ya kara da cewa jana’izar za ta ci gaba da zaburar da mutane masu ‘yanci a duniya shekaru da dama masu zuwa.” Daher ya yi nuni da cewa bikin zai dauki...
    Iraniyawa mazauna kasar Burkina Faso sun gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Ouagadougou. A wannan karon, kasashen biyu sun daukaka kyakkyawar dangantakarsu da aka gina a shekarar 1984.   Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Ouagadougou, Mojtaba Faghihi, wanda ya halarci bikin, ya bayyana cewa juyin juya halin Musulunci a Iran a shekara ta 1979 ya ba da damar “yantar da mu daga tsoma bakin siyasa na kasashen waje da wawashe dukiyarmu”. A cewarsa, Iran ta samu nasarar dakile makircin makiya da kuma wuce gona da iri na sojojin kasashen waje, da takunkumi da kuma ta’addanci. A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jaddada buƙatar samar da manyan gonakin gudanar da noman rani domin yaki da matsalar karancin abinci a Yankin Tafkin Chadi. Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin taron Gwamnonin Tafkin Chadi da aka gudanar makon da ya gabatar a garin Maiduguri fadar Jihar Borno karo na biyar, inda ya jadadda cewar, Allah SWT ya azurta wannan Yanki na Tafkin Chadi da dimbin filayen noma wanda idan aka yi amfani da su yadda ya kamata, na iya ba da gudummawa sosai wajen samar da abinci a yankin har ma da yankuna makwabta. Zulum ya bayyana muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnonin yankin da abokan haɗin gwiwa da Majalisar Dinkin Duniya domin kafa gonakin noman...
    Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabbatar da cewa Shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ba zai gaza ba duk da ƙoƙarin yaɗa jita-jita da wasu ke yi. Kwankwaso, ya musanta wani rahoto da ke cewa mahajjata na iya rasa zuwa aikin Hajjin 2025, inda ya bayyan cewar wannan ƙarya ce da aka shirya don yaudarar jama’a da kuma ɓata sunan shugaban NAHCON. An yi wa kashi 25 na matan Nijeriya kaciya Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya Ya buƙaci jama’a, musamman maniyyatan da za su yi aikin Hajjin 2025, da su yi watsi da wannan rahoto, inda ya Farfesa Pakistan yana da...
    Jaridar Daily Telegraph ta watsa labarin cewa: Shugabannin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Khamenei da ya janye fatawarsa kan haramcin mallakar makamin nukiliya Jaridar Daily Telegraph ta kasar Birtaniya ta watsa rahoton cewa: Shugabannin sojojin Iran sun bukaci Jagoran juyin juya halin Musulunci Sayyid Ali Khamenei ya yi watsi da haramcin mallakar makaman nukiliya da ya fitar da fatawa kanta a farkon takaddamar Shirin makamashin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Jaridar ta ruwaito a cikin wani rahoton da wakilinta na musamman Akhtar Muhammad Makoy ya fitar cewa: Manyan jagororin sojojin Iran sun ce dole ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya soke fatawar da ta haramta kera makaman nukiliya matukar gwamnatin Iran na son ci gaba...
    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Sake gina Gaza na bukatar kudi sama da dala biliyan 53 Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya fada a ranar Talata cewa: Sake gina yankin Zirin Gaza da yakin haramtacciyar kasar Isra’ila ya lalata yana bukatar kudi sama da dala biliyan 53, ciki har da sama da dala biliyan 20 cikin shekaru uku na farko. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya rubuta a cikin wani rahoto da aka shirya bisa bukatar babban zauren Majalisar Dinkin Duniya cewa: Adadin kudaden da ake bukata don farfado da sake gina yankin a cikin gajeren lokaci, matsakaita da kuma dogon lokaci a Zirin Gaza “an kiyasta kimanin dala biliyan 53 da miliyan 142. A cikin...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
    Duk da haka, da alama cewa, waɗannan binciken ƙila ba su da isasshen ikon gano bindigogin da suka ɓace.   A yanzu haka dai, kwamitin majalisar dattawa yana zaune a Abuja domin ci gaba da bincike kan lamarin.
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
    Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula, musamman kananan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Wadannan kalamai sun zo ne a yayin wani taron tattaunawa da kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar, inda aka yi karin haske kan rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, wanda ya yi sanadiyyar raba mutane kimanin miliyan 12 da matsugunan su. Yakin dai ya kawo cikas wajen kai agajin...
    An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin.   An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin.   Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa ​​mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
    Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba.   “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu yana da yawa, farashin sa yana sauka da kan sa.”   Ministan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannin tsaro, inda ya ce a shekarar 2024 jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 8,000, sun kama mutum 11,600, tare da ƙwato makamai fiye da 10,000.   Ya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ake yi yana sa hanyoyi na ƙara...
    An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba. DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa An harbe ’yan sanda biyu a Yobe Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Sin Ta Ayyana Matakan Bunkasa Harkokin Sayayya Da Zuba Jarin Waje
    “Wannan shi ne dalilin da ya sa Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a cikin takardar yaƙin neman zabensa gabanin zaben 2023 cewa batun tsaro ne zai sa a gaba, inda ya yi alƙawarin aiwatar da matakan shawo kan lamarin. “A halin yanzu an shaida cewa Gwamna Lawal ya cika alƙawarin. “Gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta ba da fifiko kan harkokin tsaro a jihar Zamfara, kuma ta ɗauki matakin da ya dace tun farko cewa sulhu da ‘yan bindiga ba komai ba ne illa ‘je ka na yi ka’. “A cikin hirarraki da manema labarai daban-daban, gwamnan ya sake bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta yo sulhu da ‘yan bindigar da ke addabar jihar ba. “Ya kamata a bayyana...
    Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da rahoton dake da alaka da rarrabuwar iko tsakanin kasashen duniya na taron tsaro na Munich, yana cewa, bisa binciken da taron ya yi, kasa da kasa sun kara amincewa da kasancewar iko tsakanin kasashe daban daban a duniya. Kuma bangaren Sin ya yi imanin cewa, ba za a iya dakile wannan ci gaban da duniya ta samu ba. Da ya tabo batun sanya na’urar Buoy da Sin ta yi cikin ruwa don duba yanayin cikin tekun da batun ya shafa, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan ya dace da dokokin cikin gida...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun harbe wasu jami’an ’yan sanda biyu a ofishinsu da ke Kolere a Ƙaramar Hukumar Fune ta Jihar Yobe. Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Janairun da ya gabata ne gungun wasu ’yan ta’adda suka harbe DSP Ali Pindar, wani jami’in ɗan sanda da ke ofishin. Netanyahu ya bai wa Hamas wa’adin sakin Isra’ilawan da take garkuwa da su Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman Bayanai sun ce tun farko dai marigayi DSP Pindar shi ne ya jagoranci tawagar jami’an da ta cafke wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami amma daga bisani aka bayar da belinsa. Wata majiya ta ce bayan bayar da belin nasa...
    An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
    A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin bunkasa noman dabino a jihar. Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya, wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse. Babban makasudin ziyarar ita ce tattaunawa...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
    Shugaban Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gargaɗi Hamas da ta yi gaggawar sakin Isra’ilawan da take tsare da su a hannunta. Netanyahu ya ce ya bai wa ƙungiyar wa’adin zuwa ranar Asabar da ta saki Isra’ilawan da take garkuwa da su kamar yadda aka amince a yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu ta tanada. Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman ‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’ Netanyahu ya ce ya yi ganawa ta awa huɗu da majalisar yaƙinsa inda kowa ya bayyana kaɗuwa da halin da mutane uku da Hamas ta saka ranar Asabar suka kasance. “Dukkanin mu mun yi maraba da buƙatar shugaba Trump na sakin mutanen zuwa ranar Asabar da...
    Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
    Kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin CPCA, ta ce bangaren fitar da motoci daga kasar Sin zuwa kasashen ketare, ya ci gaba da samun tagomashi a shekarar 2024. A cewar CPCA, kasar Sin ta fitar da jimilar motoci miliyan 6.41 zuwa kasashen waje a bara, adadin da ya karu da kaso 23 bisa dari a kan na shekarar 2023. Kasashen da ke kan gaba, wadanda aka kai wa motocin na kasar Sin sun hada da Rasha da Mexico da Hadaddiyar Daular Larabawa, yayin da kasashen da suka ingiza ci gaban da Sin ta samu wajen fitar da motocin suka hada da Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa da Brazil da Belgium da Saudiyya. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Har kullum, na kan ce, ci gaban kasar Sin wata dama ce ba kalubale ba. A matsayin ’yar Afrika, ci gaban kasar Sin daidai yake da ci gaban nahiyar Afrika domin duk wata nasara da ta samu, ba ta kyashin kai wa Afrika, kuma burinta shi ne ta ga nahiyar ta amfana, ta samu ci gaba, kuma al’umma sun kasance cikin walwala. Kamata ya yi wannan ra’ayi na kasar Sin na neman ganin ci gaban kowa, ya kasance ra’ayin kasashe manya masu son ganin ci gaban duniya, sai dai yayin da ake fafatukar ganin haka, manyan kasashen su ne ke kokarin dankwafe duniya daga samun irin ci gaban da al’umma ke muradi. (Faeza Mustapha)
    Tafida, ya bayyana godiyar Gwamna Nasir Idris ga Sakatarorin kan irin gudunmuwar da suka bayar ga inganta bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi da kuma goyon baya ga gwamnatinsa a kan jagorancin al’ummar jihar.   Daga karshe, Gwamnan ya gode wa Sakatarorin kan irin yadda suka sadaukar da kansu wajen kawo cigaba a bangaren Ilimi a matakin kananan hukumomi 21 na fadin jihar tare da yi musu fatan alkairi a rayuwarsu ta gaba.
    Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka da suke yankin Djaiba hare-hare a gundumar Ituri a  jiya litinin da dare. Bugu da kari masu dauke da makaman sun kai hari a cikin sansanin ‘yan hijira da suke a cikin wannan yankin kamar yadda shugaban sansanin Antoinnette Nzale ya fadawa manema labaru. Ita dai kungiyar CODECO  gamayya ce ta kungiyoyin da suke dauke da makamai da su ka fito daga kabiluar Landu, manoma....
    Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu da shirin na shugaban kasar Amurka akan mutanen Gaza. Ministan harkokin wajen Saudiyya Faysal Bin Farhan ya ce, Saudiyya tana da matsaya tabbatacciya da ita ce kin amincewa da duk wani shiri na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza zuwa wata kasa.” Ministan na Saudiyya ya nuna goyon bayansa ga kiran da Iran ta yi na yin taron kungiyar kasashen musulmi domin tattaunawa wannan batu....
    Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta na kafa Hukumar Kula da Masu Buƙata ta Musamman a wani mataki na tabbatar da adalci a tsakanin al’ummar jihar. Kwamishiniyar Mata da Yara masu bukata ta musamman, wacce Daraktar Jin Daɗi ta ma’aikatar, Binta Muhammad Yakasai, ta wakilta, ta bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na yini guda da masu ruwa da tsaki kan kafa Hukumar Kula da Mutanen da ke da Bukatu na Musamman (PWDs) a Jihar Kano. Tana jaddada aniyar gwamnati na ƙarfafa PWDs, Yakasai ta ce, “Wannan taro ba kawai haɗuwar ra’ayoyi ba ne, amma wani mataki ne na tabbatar da adalci, haɗawa da ƙarfafa wani muhimmin ɓangare na al’ummarmu.” Ta bayyana manyan dalilai guda biyar da ke nuna bukatar kafa...
    Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa. BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC Alƙaluman ƙasashe mafi cin hanci da rashawa a duniya ya nuna yadda Nijeriya ta koma matsayin ta 140 daga ta 145 da take a baya a sahun ƙasashe 180 mafiya cin hanci da rashawa a duniya Rahoton wanda ya yi nazari kan ƙasashen ya yi amfani...
    Nijeriya ta zama ƙasa ta 140 a cikin jerin ƙasashen da aka fi tafka cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2024 a cewar ƙungiyar Transparency International. A cikin rahoton wanda ta fitar a yau, Transparency ta ce Denmark ce ƙasar da ta kasance wadda ba ta fuskantar matsalar ta cin hanci da rashawa. BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC Alƙaluman ƙasashe mafi cin hanci da rashawa a duniya ya nuna yadda Nijeriya ta koma matsayin ta 140 daga ta 145 da take a baya a sahun ƙasashe 180 mafiya cin hanci da rashawa a duniya Rahoton wanda ya yi nazari kan ƙasashen ya yi amfani...
    An ce, tsakanin shekarar 2000 zuwa 2023, kasar Sin ta samar da rance da yawansa ya kai kimanin dalar Amurka biliyan 43 ga kasashen Afirka, don su raya bangaren samar da wutar lantarki. Kana a shekarun nan, kamfanonin kasar Sin sun gudanar da dimbin ayyukan samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka, kamarsu madatsar ruwa ta Souapiti ta kasar Guinea, da madatsar ruwa ta Djibloho dake kasar Guinea Bissau, da dai sauransu. Gaba daya an gudanar da ayyukan a kasashe da yankuna fiye da 40 na nahiyar, wadanda suka kara samar da wutar lantarki na kilowatt miliyan 120, da karin layin wutar lantarki mai tsawon kilomita dubu 66. Har ila yau, kasar Sin ta sanar da shirin gina wasu manyan...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban Birnin Jihar. Ya bayyana cewar, Gwamnatin a shirye take ta yi aiki tare da kowace kungiya da ke da niyyar tallafa wa jin daɗin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar jigawa. Malam Umar Namadi ya kara da cewar a zancen ma dai da ake yi a halin yanzu, Jihar Jigawa ta shahara wajen noman dabino kuma ita ce ta daya a noman...
    Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata. A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu sun fito ne daga Jihar Ogun. An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero
    ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN ya ce wannan sabon tsari zai ƙarfafa shigar da sabbin ATM a faɗin ƙasa tare da tabbatar da cewa bankuna suna cajin kuɗin da ya dace.
    Kafafen watsa labarun HKI sun ce; Barazanar da ake yi wa kungiyar Hamas ba ta wani tasiri a gare ta. Kafafen watsa labarun na HKI suna yin tambaya akan yadda Hamas din take isar da sakwanni a fakaice ga Isra’ila a yayin bikin mika fursunoni da take shiryawa. Tashar talabijin din ta 12: ta ambaci cewa; A cikin wannan yanayi mai tsanani da ake ciki, ko wane sako ne kungiyar ta Hamas take son isarwa ta hanyar shirya biki a yayin sakin fursunoni? Shi kuwa mai yi tashar sharhi, Ohad Hamu, ya ce kungiyar ta Hamas ta isar da sako da harshen Hebrew da take mahana da Isra’ilawa, sai kuma turanci da take Magana da gwamnatin Amurka, da hakan yake...
    Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar cewa matukar Falasdinawa ba su saki fursunonin  Isra’ila ba daga nan zuwa Asabar, to za a kawo karshen tsagaita wutar yakin da aka yi, da komawa yaki. Shugaban kasar ta Amurka ya shata wa’adin 12: 00 Na ranar Asabar a matsayin lokacin karshe na mika fursunonin. Shugaban kasar ta Amurka wanda yake Magana da ‘yan jarida a ofis dinsa dake fadar White House, ya sake jaddada tsohuwar barazanar da ya yi tun kafin a rantsar da shi, na ce wa zai bude kofofin jahannama idan ba a mayar da fursunonin ba daga Gaza.” Donald Trump ya kara da cewa, ya yi Magana da Benjamin Netanyahu akan wa’adin na karshe a ranar Asabar...
    Ɗan Majalisar PDP Ya Sauya Sheka Zuwa APC
      Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi.     Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa, zai hada da jerin tattaunawa da ayyukan da zasu mayar da hankali wajen magance kalubalen tattalin arzikin yankin.     Taken taron na bana, “Alherin Duniya: Sauyw Albarkatun Halitta na Arewa zuwa Cigaba Mai Dorewa”, na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar karin damuwa kan talauci da rashin aikin yi da rashin ci gaba duk da kasancewar Arewa na da yalwar albarkatun halitta.  ...
    Jami’ar Bayero Ta Shirya Bikin Yaye Ɗalibai Karo Na 39
    Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya  bayyana cewa kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
    Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata. A watan Janairu ne Allah Ya yi wa Onanuga rasuwa. Dukkansu sun fito ne daga Jihar Ogun. An kama ’yan ina-da-kisa 47 a Kwalejin Tarayya a Kebbi
    Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata.
    Abin Kunya Ne Nijeriya Har Yanzu Ba Ta Iya Ciyar Da Kanta – Gwamna Bala
    ’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300. Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki. Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama. Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero Gwamnan Zamfara ya...
    Dalibai 179 za su samu shaidar Digiri Mai Daraja ta Ɗaya a yayin bikin yaye ɗalibai na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK). Shugaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Abba, ya bayyana cewa dalibai 4,402 ne za a yi bikin yaye su a ranar farkon, inda a za a ba su shaidar kammala Digirin farko da Difloma da sauran makamantansu. Bikin yaye ɗaliban shi ne karo na 39 da za a gudanar a jami’ar ta BUK. Bikin na kwana huɗu ya kunshi jawabai da laccoci da taruka da kuma bayar da kyaututtuka da takardun shaida a matakai daban-daban. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Matan Arewa Karantar Ilimin Kimiyya? Farfesa Sagir Abbas ya bayyana cewa a rana ta biyu za a...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci shi ne kasantuwar kasa ta taka rawar al’umma da kyakkyawar hadin kai. Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa a jawabin da ya gabatar a karshen jerin gwanon na tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Tehran: Ba za su taba mika wuya ga kasashen waje ba. Ko da yake Iran bata neman yaki, amma tun ranar farko makiya suke...
    Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata rana. Trump ya kara da cewa a yayin zantawarsa da Tashar talabijin ta Fox News; Suna da kasa mai kimar gaske mai dauke da ma’adanai na musamman da man fetur da kuma iskar gas, da sauran abubuwa. Trump ya ci gaba da cewa: Yana son dukiyarsu ta kasance cikin aminci, domin suna kashe daruruwan biliyoyin dalolia cikin kasar. Ya karkare furucinsa da cewa; Za su...
    Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da rusa ababen more rayuwa a birnin Tul-karam da sansanoninsa na Falasdinu tare da kama Falasdinawa da tilasta wa jama’a yin gudun hijira Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai hare-hare kan birnin Tul-Karam da sansanoninsa guda biyu Tul-karam da Nourul- Shams a rana ta 16 a jere, a daidai lokacin da sojoji ke ci gaba da barnata kayayyakin more rayuwa da kadarorin jama’a da kuma kame jama’a gami da tilastawa dubban mazauna sansanonin biyu gudun hijira. Sojojin mamayar suna ci gaba da killace sansanonin Tulkaram da Nourul Shams, sannan kuma suna kara yawan sintirin motocinsu da na tankokin yakinsu da kuma sintiri da kafa a yankuna da unguwannin su, a daidai lokacin...
    Wani sanatan Amurka yana barazana ga shugaban kasar Tunisiya da neman rusa nasarar dimokuradiyyar kasar Sanatan Amurka Joe Wilson, dan majalisar wakilai daga shiyar kudancin jihar Carolina, ya kaddamar da hari kan shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id, inda ya dauke shi a matsayin “dan mulkin kama karya” tare da yin kira da a kakabawa Tunisiya takunkumi har sai ta dawo kan tsarin dimokiradiyya. Maganganun Wilson, wanda ya shahara da kare matakan muggan laifukan yahudawan sahayoniyya da kuma tsantsar kiyayya ga kungiyoyin gwagwarmaya da dukkan gwamnatocin Larabawa da na Musulunci da suka ki amincewa da Shirin daidaita alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila, ya fuskanci mayar da martani mai yawa a tsakanin ‘yan siyasar Tunisiya da masu fafutuka kare hakkokin dan Adama,...
    Kamfanin Dangote na Peugeot Automobiles Nigeria Limited (DPAN), wanda ke kera wa da tallata motocin Peugeot a Nijeriya, ya fara tarawa da haɗa sabuwar Peugeot 3008 GT a masana’antarsa da ke Kaduna. Peugeot 3008 GT, mai injin 1.6-lita turbo mai ƙarfi, ya ƙara yawan jerin motocin da ake haɗawa a masana’antar DPAN, wanda ya ya ke samar da 301 sedan da Peugeot 5008 mai kujeru bakwai. Wannan sabon samfurin yana da Faisal kamar fitilun, da hasken rana mai iya buɗewa, da tayoyin 17-inch alloy. Matatar Dangote Ta Bai Wa Ɗalibai 473 Tallafin Karatu Zanga-zanga: Ku Kawo Ƙarshen Rashin Wutar Lantarki Da Ta Addabi Jihohi- Gwamnatin Kaduna  Hakanan, an samar da fasahar ABS don hana birki shanye wa, ESP don hana...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta jinkirta sakin sauren karin ‘yan Isra’ila da take garkuwa dasu “har sai an ga abinda hali ya yi”, saboda keta dokar da Isra’ila ta yi na tsagaita wuta a Gaza. Sanarwar da bangaren soji na Hamas ta fitar bakin kakakinta Abu Obeida, ta bayyana cewa ‘’fiye da mako uku makiya sun gaza wajen cika yarjejeniyar da suka cimma’’. Hamas ta ce ‘’sakin karin wasu yahudawa na ranar Asabar 25 ga wata an jingine shi, sai nan gaba, yayin da suke jiran makiya su mutunta yarjejeniyar da aka fara aiwatarwa makkonin da suka gabata. Tuni dai Isra’ila ta mayar da martani dangane da sanarwar ta Hamas inda a wata sanarwa da ministan tsaron kasar ya...
    Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu. A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya  ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan. Tunda farko...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa shirin korar  al’ummar Zirin Gaza zai hada da kwace ‘yancinsu na komawa kasarsu. Trump ya fada a wata hira da tashar Fox News cewa shirin da yake yi a kan Gaza ya kunshi fitar da daukacin al’ummar yankin da kuma sake gina abin da ya kira ‘’Sake farfado da Gabas Ta Tsakiya’’ Ya kara da cewa za a iya samun wurare daban-daban har guda shida don Falasdinawa su zauna a wajen zirin Gaza. Ya kuma ce za’a gina wa Falasdinawa gidaje masu kyau da inganci nesa da wajen da suke, saidai bai bayyana takamaiman wuri ba. A wani labarin kuma Donald Trump ya fada a ranar Litinin din nan cewa cewa “watakila” zai...
    Gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya yi kira da a gaggauta sakin hambararen shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum da matarsa ​​Hadiza. Tun a watan Yulin 2023 ne ake tsare da Bazoum ​​a wani reshe na fadar shugaban kasar da ke Yamai, inda Likitansa ne kawai aka yarda ya ziyarce shi. A cewar gungun aiki na Majalisar Dinkin Duniya kan tsare mutane ba bisa ka’ida ba, Mohamed Bazoum da matarsa ​​Hadiza ana tsare da su ba bisa ka’ida ba, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa. Su ma lauyoyin Mohamed Bazoum A cikin wata sanarwa, sun tunatar da cewa tsohon shugaban da matarsa ​​”an hana su mu’amala da kasashen waje” dangi, abokai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
    Kamfanin kula da sufurin layin dogo na kasar Sin, ya ce jarin manyan kadarori da kasar ta zuba a bangaren layin dogo ya kai yuan biliyan 43.9, kwatankwacin dala biliyan 6.12, a watan Janairun bana. A cewar kamfanin, adadin ya karu da kaso 3.7 bisa dari idan aka kwatantan da makamancin lokacin a bara. A wannan lokaci, an gudanar da manyan ayyuka, ciki har inganta layin dogo mai saurin tafiya tsakanin biranen Chengdu da Chongqing. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Kano, Umar Farouk Ibrahim. An dai rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka gudanar ofishin gwamnan. ’Yan bindiga sun kashe fasto a Gombe An shiga nuna wa juna yatsa tsakanin Hamas da Isra’ila Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Kano, Barista Haruna Isa Dederi ne ya ba shi rantsuwar kama aikin. Naɗin sabon Sakataren Gwamnatin na zuwa ne watanni biyu bayan sauke Dokta Abdullahi Baffa Bichi daga muƙamin da wasu kwamishinoni 5 da shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan. Wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan na Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce an zaɓi sabon Sakataren Gwamnatin ne...
    Kungiyar kula da harkokin jigilar kayayyaki da sayen kayayyaki ta kasar Sin ta samar da adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin a watan Janairun da ya gabata cewa, wanda ya nuna cewa, yawan bukatun ajiye kaya a Sin ya bunkasa cikin sauri duba da karuwar bukatun sayayya a lokacin bikin sabuwar shekara, kuma sana’o’in adana kayayyaki na ci gaba da samun bunkasuwa. Adadin sana’o’in adana kayayyaki na Sin ya kai kashi 52.5%, a watan Janairun da ya wuce, wanda ya karu da kashi 1.9% bisa na watan Disamban da ya gabata, adadin da ya kai koli a cikin watanni 10 da suka gabata. Sakamakon manufofin tabbatar da tattalin arziki da ingiza bunkasuwa, da ma yadda aka koma aiki bayan hutun...
    A kokarinta na karfafa hadin gwiwa da tabbatar da gaskiya da rikon amana, hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa (JG-PCACC) ta kai ziyarar ban girma ga takwararta da ke Abuja. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na JG-PCACC Alhaji Yusuf Suleiman ya bai wa gidan rediyon Najeriya a birnin Dutse na jihar Jigawa. A cewarsa, sun kai  ziyarar ce karkashin jagorancin shugaban PCACC, Barista Salisu Abdu,  da zummar tantancewa da kuma cudanya da masu ruwa da tsaki a hukumar, tare da lalubo hanyoyin hadin gwiwa  tsakanin bangarorin biyu. Barista Salisu Abdu ya jaddada mahimmancin hadin gwiwar t domin hana cin zarafi da rashin adalci a...
    ’Yan bindiga sun kashe wani fasto, Rabaran Bala Galadima yayin harin da suka kai garin Lubo da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan bindigar sun kuma yi fashin kuɗi har Naira dubu 300 a yayin harin da suka kai cikin dare wayewar gari Lahadi. Wani mazaunin garin ya bayyana cewa maharan, waɗanda sun kai takwas, sun kai farmakin ne da misalin karfe 1 zuwa 3 na dare, inda suka firgita jama’a da harbe-harbe kafin su kutsa cikin gidan wani mutum mai suna Musa Puma. Majiyar ta ce maharan sun rutsa matar gidan da bindiga inda suka karbi kuɗi naira dubu dari 300 tare da yin garkuwa da ɗaya daga cikin ’ya’yansu da kuma...
    NUC Ta Dakatar Da Bayar Da Lasisin Gina Sabbin Jami’o’i Masu Zaman Kansu
    Hamas ta sanar da yanke shawarar jinkirta sakin fursunonin Isra’ila nan gaba har sai abin da hali ya yi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta fitar tana mai cewa an ɗauki matakin ne a matsayin mayar da martani ga keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi. Dalilin da na ziyarci Obasanjo — Atiku Gwamnan Zamfara ya gindaya sharaɗin sulhu da ’yan bindiga Sanarwar da ɓangaren sojin Hamas ɗin ya fitar ta ce “fiye da mako uku, shugabacin ƙungiyar na bibiyar yadda maƙiya suka gaza cika ka’idojin yarjejeniyar da suka cimma. “Karya wannan ƙa’ida, har da jinkirta dawowar waɗanda suka rasa muhallansu zuwa Arewacin Gaza, inda ake fakon su tare da harbin su, da...
    A yau Litinin, kasar Sin ta sanar da sabbin ka’idojin kyautata kare sirrikan jama’a yayin kare tsaron al’umma. Firaministan kasar Sin Li Qiang ne ya rattaba hannu kan wata dokar majalisar gudanarwar kasar, domin fitar da ka’idojin, wadanda za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu. Ka’idojin na da nufin tafiyar da harkokin da suka shafi kula da tsare-tsaren kyamarorin da aka kafa domin tsaron al’umma da kare sirrika da hakkoki da muradu da ma bayanan daidaikun mutane. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)