2025-03-03@21:23:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 54
«abincin buɗa baki»:
Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki domin tallafa wa mabuƙata a wannan wata mai albarka na Ramadana. Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya ƙaddamar da rabon abincin a cibiyar Dandali da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a jihar. HOTUNA: Tinubu ya karɓi baƙuncin Shugaban Saliyo a Abuja NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki Bayanai sun ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta ƙaddamar da wannan shiri tana da burin raba abincin buɗa-baki ga mabuƙata masu azumtar watan Ramadana. Gwamnatin ta ce an tanadi cibiyoyi 91 domin raba wa mabuƙata 91,000 abincin buɗa-baki duk rana nan da tsawon kwanaki 27 masu zuwa. Domin tabbatar da samun nasara, gwamnatin ta...
Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa. Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa. A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina. ’Yan bindigar sun sace daliban ne a ɗakunan kwanansu da ke yankin Paris Quarters a garin na Dutsinma. Maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kutsa yankin ne da misalin ƙarfe 4 an asubahin ranar Lahadi, suka yi awon gaba da ɗaliban. Jami’an tsaro sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, amma kafin su isa wurin ’yan bindigar sun riga sun riga sun tsere da ɗaliban. Dutsinma na daga cikin ƙananan hukumomin Jihar Kastina da suka fi dama da matsalar ’yan bindiga da ke satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, duk kuwa da matakan da gwamnati da kuma hukumomin...
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki. Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi. Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan Ramadana Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.” ’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi...
Wata kotun majistare da ke zamanta a Ago Iwoye, Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 21, Adebanjo Segun, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kaza. Jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar tsaro ta Civil Defence , Dyke Ogbonnaya ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. An ce an fara samun matsalar ne a ranar Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025, kan Adebanjo mai shekara 21 a lokacin da aka kama shi da laifin satar kaza. Zulum ya rage adadin tallafin rabon abinci da kashi 90 a Borno An shiga ruɗani bayan Obasa ya koma majalisar Legas da ’yan sanda Ogbonnaya ya bayyana cewa, “Bayan an yi nazari...
An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda. An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba. An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa An maye gurbinsa da Mojisola Meranda, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar kai a majalisar da kuma jam’iyyar APC mai mulki a Jihar. Rahotanni sun nuna cewa an matsa wa Meranda da ta sauka daga muƙaminta, bayan da ake zargin cewa Shugaba Bola Tinubu bai gamsu da sauke Obasa daga muƙaminsa ba. A safiyar ranar Alhamis, labari ya...
Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan ya faɗo daga benen wani katafaren kanti. Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Cikin wani dogon saƙo da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin. “Muna baƙin ciki da samun labarin mutuwar Abubakar Lawal. Wannan lamari ne...
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...
Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a. A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna. Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina A yayin da mu’amala tsakanin jinsi ɗaya ta halasta a wasu yankunan ƙasar mafi rinjayen musulmi a duniya, sai ɗabi’ar ta haramta a lardin Aceh da aka ayyana dokokin shari’ar Musulunci. Tun a watan Nuwamban bara ne dai ’yan sanda masu ɗabbaka shari’a suka kama mazajen biyu da ke karatu a wata jami’a suna aikata wannan alfasha a wani...
A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun tsayar da su domin tuhuma bisa zargin cewa masu yi wa ’yan bindigar daji leƙen asiri ne. NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji Wannan harbin da suka yi ya yi sanadiyar mutuwar wannan ɗalibi mai suna Saidu Abdulkadir. Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya an kama wani ɗalibin jami’ar yana safarar makamai....
Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda. Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya. Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya ce dubun dan shekara 65 din mai suna Nehemiah Sunday Udo ne a ranar Asabar baya al’ummar kauyen Ekpene Obo da ke Ƙaramar Hukumar Esit Eket sun ritsa shi. John ya ce bayan samun kira daga al’ummar yankin ne ’yan sanda suka kai samame inda suka samu mutanen sun kai wanda ake zargin fadar basaraken yankin. Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan...
Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai mai hankali da zai goyi bayan APC a zaɓen 2027. PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani kan zargin cewa Sanata Lawal Adamu, Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, baya aikin komai sai ɗumama kujera. Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Haka kuma, ana zargin gwamnatin Jihar Kaduna da dakatar da rarraba kayayyakin koyarwa da Sanata Lawal Adamu ya saya domin amfanin makarantun jihar. Yusuf Dingyadi, Mataimaki na Musamman na Shugaban PDP kan Yaɗa Labarai, ya ce ya kamata gwamnatin jihar ta haɗa kai da wakilan jama’a don ci...
Wani ginin ajujuwa a Kwalejin ’Yan Mata ta Kimiyya da Fasaha (GGTC) Potiskum ya rufta, inda daliba ɗaya ta rasu kuma wasu da dama suka jikkata. Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ɗalibai ke tsaka da karatu. An rufe Jami’ar Kogi saboda zanga-zangar ɗalibai EFCC ta gargaɗi ciyamomi kan amfani da kuɗaɗen jama’a a Gombe Gini ya faɗa kansu ne ba zato ba tsammani, lamarin ya haddasa mummunan tashin hankali tare da jefa ɗalibai da dama cikin baraguzan gini. Bayan aukuwar lamarin, an yi gaggawar ceto ɗaliban, inda aka garzaya da su zuwa Asibitin Ƙwararru na Potiskum domin ba su kulawa. Duk da an samu nasarar ceto da dama daga cikinsu, wata ɗaliba ta rasa ranta...
Hukumomin Jami’ar Tarayya da ke Lokoja a Jihar Kogi, sun rufe jami’ar har zuwa wani lokaci domin daƙile ci gaba da asarar rayuka da dukiya. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun magatakarda kuma sakatariyar majalisar Jami’ar, Dokta Rebecca Aimiohu Okojie, a ranar Alhamis kuma ta bayyanawa manema labarai a Lokoja. Jihar Gombe na ƙarfafa haƙƙoƙin yara masu nakasa — Ƙungiyar JONAPWD NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Hukumar Jami’ar ta yi zargin cewa, ɗaliban sun tare babbar ƙofar shiga jami’ar ne tun bayan haɗarin da ya yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’ar biyar a ranar Litinin, wanda ya sa shiga harabar jami’ar ke da wuya. “Rufewar jami’ar ya biyo...
Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
Gwamnatin Amurka ta ƙudiri aniyar gudanar da bincike kan yadda gwamnatocin da suka gabata suka riƙa sarrafa kuɗaɗen da aka fitar domin bai wa Nijeriya da wasu ƙasashen tallafi. Hakan dai ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurkan, Donald Trump ya ɗauka a watan Janairu na dakatar da duk wani tallafi da Amurkan ke bayarwa a ƙetare har na tsawon kwanaki 90. DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji Shugaba Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta gudanar da binciken ne a dalilin ruɗanin da ya dabaibaye duniya wanda ke cin karo da muradun Amurkan. Haka kuma, Shugaba Trump ya ce za a...
An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal a Jihar Ogun. Marigayin, wanda ke aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi a Jihar Legas. NAFDAC ta gano wajen da ake sabunta magungunan da suka lalalce a Abiya Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro Ya je otal ɗin Super G Royal da ke rukunin gidaje naAnthony Uzum tare da wata mata da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar. Da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar washegari ne, manajar otal ɗin, Deborah Adejobi, ta gano cewar ɗakin da suka kama ba a kulle yake ba. Lokacin da ta shiga, sai ta tarar da ɗan sandan a kwance babu rai, kuma matar da...
Babban Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya sake jaddada cewa ƙasashen waje ne ke tallafa wa ’yan ta’addan Boko Haram da kuɗi da makamai. A wata hira da ya yi da Al Jazeera, Janar Musa ya nuna damuwa kan yadda ƙungiyar ke ci gaba da aikata ta’addanci sama da shekaru 16, duk da ƙoƙarin da sojojin Najeriya ke yi na daƙile. Gwamnatin Yobe Ta Ɗauki Jami’an Kiwon Lafiya 42 Aiki Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Ya bayyana cewa an kama wasu ’yan Boko Haram ɗauke da maƙudan kuɗaɗe da ke da alaƙa da ƙasashen ƙetare. Ya nuna cewa akwai ƙasashen da ke taimaka wa ƙungiyar daga waje. Janar Musa ya yi tambaya cewar: “Ta...
Wani ɗan Nijeriya ɗan asalin Jihar Yobe, Saidu Abdulrahman, ya lashe kambun lambar yabo ta Kundin Bajinta na Duniya a matsayin wanda ɗaukar hotuna kai tsaye cikin sa’a ɗaya. Bayanai sun ce a cikin mintuna 60 Sa’idu Abdulrahman mai shekara 28, ya ɗauki hotuna 897 masu ɗaukar hankali a watan Satumba na bara, lamarin da ba shi damar doke wanda ya lashe kambun na bara da hotuna 500. Makwabta sun kai karar ma’aurata saboda carar zakaransu Kasuwanci: Yadda matan Arewa ke samun arziki daga cikin gidajensu Da wannan ƙwazo ne Kundin Bajinta na Duniya wata Guinness World Records (GWR) ya karrama matashin da lambar yabo. Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, matashin ya bayyana cewa, “ina...
Hukumomin Jami’ar Nnamdi Azikiwe (Unizik) da ke, Awka a Jihar Anambra ta kori ɗalibar nan mai suna Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cin kwalar wani malamin jami’ar Dakta Chukwudi Okoye. A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga Goddy-Mbakwe ta far wa malamin jami’ar, Dakta Chukwudi bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani wuri da ke harabar jami’ar. An ɗage taron mahaddata Qur’ani da za a yi a Abuja Asabar za a yi zaɓen ƙananan hukumomin Katsina A cikin takardar korar ɗalibar da jami’ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wanda muƙaddashin magatakardar jami’ar, Ɓictor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin korar ne...
Rahotanni sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur’ani da ake yi wa laƙabi da Qur’anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu wanda za a gudanar a Abuja kamar yadda BBC Hausa ta bayyana. An dai ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 a matsayin ranar da za a gudanar da taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur’ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya. ‘Asabar ne zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Katsina’ Mutum 23 sun mutu da raunata wasu a haɗarin mota a gadar Kano Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa, “tun daren jiya Alhamis aka ɗage...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram. Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis. Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare ayankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula. Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin. A yayin zaman wanda ya mayar da hankali...
Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su. Lardin Balochistan mai albarkar ma’ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.
Wata ɗalibar a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, Faith Aluko Adesola, ta rasa ranta bayan da wata babbar mota ta murƙushe ta. Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, Alhaji Rabi’u Muhammad ne, ya tabbatar da faruwar lamarin. Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025 Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ya ce Adesola ɗaliba ce da ke ajin farko (ND1) a Sashen Koyon Aikin Jarida na makarantar. A cewarsa, tana kan ɗan acaba domin zuwa makaranta lokacin da babbar motar ta yi awon gaba da babur ɗin a kusa da kofar shiga makarantar, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta. “Da muka samu labarin, tawagar makaranta da suka haɗa da shugaban tsaro...
An yi jana’izar fitaccen ɗan siyasar nan kuma Shugaban Hukumar Kwashe Shara na Jihar Kano (REMASAB), Alhaji Ahmadu Haruna Zago, a Ƙofar Kudu da ke Fadar Sarkin Kano. Haruna Zago, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Miƙa makaman ’yan bindigar Katsina ya bar baya da ƙura Dubban mutane ne suka halarci jana’izar fitaccen ɗan siyasar, daga ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi. Sauran jami’an gwamnatin Kano da manyan ’yan kasuwa na daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar marigayin. Ga hotunan yadda jana’izar ta wakana: ...
Wata Babbar Kotu a Abuja, ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar bayar da belin Tsohon Shugaban Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, wanda ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Yusuf a gidan gyaran hali na Kuje har zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu. Sojoji sun doki ’yan sanda kan kama ‘mai laifi’ Fitaccen ɗan siyasa Ahmadu Haruna Zago ya rasu A lokacin ne kotun za ta yanke hukunci kan buƙatar bayar da belinsa. Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), na zargin Yusuf da karkatar da kuɗaɗen gwamnati lokacin da yake jagorancin NHIS a shekarar 2016. Ana...
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
An tafi da shi tare da wasu mutane uku da suka haɗa da ɗan uwansa da matarsa da ɗansa a yayin harin. An tattaro cewa, jigon na APC ya kai ziyara gidan ɗan uwansa ne lokacin da ‘yan bindigar suka kai harin. Sai dai, an tsinci gawar matar dan uwansa mai suna, Madam Esther, a kusa da unguwar Ijah-Gbagyi da ke karamar hukumar Tafa a jihar Neja da safe.
Ya ce: “A baya, muna da wasu hukumomi da ke ƙayyade farashin kayan abinci, amma domin kasuwanci na ’yanci da bunƙasa harkokin noma, gwamnati ba ta ga dacewar ci gaba da hakan ba. “Yanzu abin da gwamnati ke yi shi ne ta tabbatar da cewa ana samar da isassun kayan abinci, domin idan abu yana da yawa, farashin sa yana sauka da kan sa.” Ministan ya kuma bayyana nasarorin da aka samu a fannin tsaro, inda ya ce a shekarar 2024 jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda da ’yan bindiga sama da 8,000, sun kama mutum 11,600, tare da ƙwato makamai fiye da 10,000. Ya tabbatar da cewa ƙoƙarin da ake yi yana sa hanyoyi na ƙara...
An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba. DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa An harbe ’yan sanda biyu a Yobe Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
Sojojin Najeriya sun tarwatsa babbar maɓoyar ƙasurgumin ɗan Bello Turji da ke ƙauyen Garin Fakai a Jihar Zamfara. Wanann nasarar zai gurgunta harkokin ƙasurgumin ɗan ta’addan, wanda a halin yanzu ke wasan ɓuya da jami’an tsaro. Ƙauyen Fakai shi ne babbar mafakar Bello Turji, ɗan ta’addan da ke addabar yankin Zamfara da sassan Jihar Sakkwato. Dakarun rundunar Tsatsa Daji III, sun kuma ƙwato tarin makamai a yankin bayan ’yan ta’addann sun cika bujensu da iska. ’Yan daba sun ƙona gine-ginen makaranta a Binuwai ’Yan gida daya sun yi wa ma’aurata dukan kawo wuka a Kano Sojojin sun yi wannan nasara ne a yayin samamen da suka kai bayan samun bayanan sirri, inda daga bisani suka karasa zuwa mafakar ’yan ta’addan...
Kotu ta tsare wani ɗan fashi da ya yi wa ɗalibai mata uku na Jami’ar Jihar Kwara fyaɗe. Matashin da dubunsa ta cika yi wa ɗaliban fyade ne a yayin wani fashi a ɗakunan kwanan ɗalibai mata a cikin dare. Ya yi musu wannan aika-aika tare da yunƙurin kisa ne a daƙinsu kwanan ɗalibai mata da ke wajen harabar jami’ar a yankin Malete a ranar 2 ga watan Disamba, 2024. A yayin gurfanar da matashin a gaban Kotun Majiatare ta Jihar Kwara da ke birnin Ilorin, an tuhume shi da yin amfani da makami wajen yi wa ɗaliban munanan raunuka, tare da yi musu fyaɗe da kuma sace wayoyin iPhone 13 PronMax da iPhone 11 Pro Max. ’Yan sanda na...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ’yan matan. ’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Mazauna yankin sun ce, maharan da suke da yawa sun shiga cikin unguwar ne daga yankin Birnin Gwari, ta Kwalejin fasaha ta Mamman Kontagora da ke Pandogari. Majiyoyi sun ce an kai ’yan matan da...
Ma’aikata a Jihar Alaska da ke Amurka sun bazama neman wani ƙaramin jirgin sama na kasuwanci a ranar Juma’a da ya ɓace ɗauke da mutum 10. Kamar yadda hukumomin yankin suka ce, a wani sabon afkuwar da ya afku ta jirgin Amurka. Magungunan Jabu: ’Yan majalisa sun nemi yin hukuncin ɗaurin rai da rai Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Rundunar ’yan sandan Jihar Alaska ta sanar da cewa, jirgin samfurin Cessna Caraɓan mai fasinjoji tara da matuƙin jirgi ɗaya ne, an samu rahoton ne ranar Alhamis. Jirgin da ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da ƙarfe 4:00 na yamma agogon Alaska (0100 GMT) da ya ɓace. Biranen biyu suna da nisan mil 146 (kilomita 235)...
Majalisar Wakilan Tarayya ta buƙaci babban lauyan gwamnatin tarayya da ya gabatar da gyare-gyare ga dokokin da ake da su da nufin zartar da hukunci mai tsauri da suka haɗa da ɗaurin rai da rai ga waɗanda ke da hannu wajen sarrafawa da shigo da magungunan jabu. Da kuma gaggarumin tara ga ’yan kasuwar da aka samu da laifin yin mu’amala da jabun kayayyaki. ’Yan bindiga sun mamaye masallaci da awon gaba da masallata a Sakkwato Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Hakan ya biyo bayan wani ƙuduri kan muhimmancinsa ga jama’a da ɗan majalisa, Tolani Shagaya ya gabatar a zauren majalisar a ranar Alhamis. Ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kafa dokar ta-ɓaci kan...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...
An kama wani ɗalibin firamare mai shekara 13 ɗauke da bindiga a makaranta, inda yake barazanar harbe abokan karatunsa da ita. Bayan nan ne jami’an tsaro suka yi nasarar kama shi a Makarantar Firamare ta St. Paul da ke ƙauyen Ikot Ibiok a Ƙaramar Hukumar Eket a Jihar Akwa Ibom. A safiyar Alhamis ne kakakin runduanr ’yan sandan jihar, DSP Timfon John, ta sanar da kama yaron. DSP Timfon John ta bayyana cewa, a yayin bincike sun gano cewa yaron ya shafe kimanin wata uku yana zuwa da bindigar makaranta. An kashe wa ma’aurata ’ya’yansu uku an ɓoye gawarsu a firinji Zargin Tinubu: Gaskiya Naja’atu ta fada kan Nuhu Ribadu —El-Rufai NAJERIYA A YAU: Tasirin Yankan Angurya A Rayuwar Mata...
Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom, ta yanke wa Farfesa Ignatius Uduk hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari kan laifin sauya sakamakon zaɓe. An gurfanar da Farfesan kan tuhume-tuhume uku da suka haɗa da gazawa wajen aiwatar da aikinsa, sauya sakamakon zaɓe, da kuma yin rantsuwar ƙarya a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe. Ɗan sanda ya harbe kansa har lahira a Nasarawa Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Lamarin ya shafi zaɓen ‘yan majalisar jiha da aka gudanar a Essien Udim a shekarar 2019. A ranar Laraba ne, Mai shari’a Bassey Nkanang ya same shi da laifin sauya sakamakon zaɓe da yin rantsuwa bisa ƙarya. Hakan ya sa alƙalin ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku...
Hukumar ICPC ta samu gurfanar da Mohammed Idris, wani jami’i a ƙofar shigen shiga wurin Hajji da ɗiban kaya na filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Lagas, kan laifin bayar da bayanan ƙarya da kuma cin da kuɗaɗen haram. A gaban Mai shari’a O.A. Fadipe na kotun laifuka ta musamman da ke Ikeja, lauyan ICPC, Yvonne Williams-Mbata, ta gabatar da shaida kan yadda bincike ya gano ɓacewar kuɗi har Naira miliyan goma sha ɗaya da dubu ɗari biyu da talatin da huɗu (N11,234,000) a ƙarƙashin kulawar wanda ake tuhuma daga watan Fabrairu 2001 zuwa Afrilu 2021. Yadda Tayar Jirgin Saman Max Air Ta Kama Da Wuta Yayin Sauka A Kano Fashewar Tayar Jirgi A Kano: Gwamnatin Tarayya Ta...
Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna. A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da ɗan wasan ya shigar bayan da ɗan jaridan ya zarge shi da naushin sa. Wannan dai na zuwa ne bayan da ɗan jarida Bozduman ya zargi Osimhe da cin zaraginsa, bayan tashi wasa 3-3 tsakanin ƙungiyarsa ta Galatasary da kuma Dynamo Kyiv. Yanzu haka dai Osimhen na fuskantar bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kai. A makon da ya gabata ne...
A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron. Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya? Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli...
Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester. Mece Ce Matsalar Manchester United? AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin...
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55 mai suna Yusuf Garba wanda aka fi sani da Gana kan zarginsa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi. Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali Garba wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa. Shekara guda bayan binne shi,...
Kotu ta daure wata matar aure da wani magidanci a gidan yari kan aikata lalata da juna. Kotun Majistare da ke Gwagwalada a Abuja ta yanke wa zawararwan hukuncin ɗaurin wata uku kowannensu ne bayan samun su laifin aikata zina da junansu. Matar mai shekaru 25 da bazawarin mai shekara 30 sun amsa laifin a lokacin da aka karanta musu takardar tuhumar a gaban kotun. Zawarawan sun kuma buƙaci kotun ta yi musu sassauci. Da farko alƙalin ya ba da umarnin tsare su har sai sun kawo shaida da za su yi rantsuwa cewa su mutanen kirki ne, amma suka kasa. Daga bisani Alƙali Olatunji Oladunmoye, ya yanke wa kowannensu hukuncin ɗaurin wata uku ko biyan tarar Naira 25,000. Tun...
Aƙalla mutane 20 ne ska rasu a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a Jihar Unity da ke Sudan ta Kudu. Rahoton gidan rediyon Miraya, na tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ƙasar, ya bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne jim kaɗan bayan tashinsa daga wata rijiyar mai a Unity, inda ya ɗauki hanyarsa ta zuwa babban birnin ƙasar, Juba. An dakatar da Max Air na tsawon wata 3 bayan hatsari a Kano Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Jirgin yana ɗauke da fasinjoji 21 da kuma ma’aikatan jirgin lokacin da hatsarin ya auku. Rahotanni sun tabbatar da cewa matuƙin jirgin ya rasu, yayin da mutum ɗaya kacal ya tsira da ransa, sai dai yana...
Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare. Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru. Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin. Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare. “Daidai lokacin da tayar ta...
Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa. A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya samu rauni a gwiwar dama a lokacin atisayen safiyar Talata, wanda ya hana shi tafiya Spain don buga wasan da ƙungiyarsa ke neman cancantar shiga zagayen 16 na ƙarshe. Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya Gwamnan Bauchi Ya Sanya Hannu Kan Dokar Da Za Ta Daƙile Satar Yara A Bauchi Duk da cewa kulob ɗin bai bayyana tsawon lokacin da Lookman zai...
Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar. Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari ’Yan sanda sun yi ƙarin haske kan barazanar harin ’yan ta’adda a Kano Ana kuma ci gaba da jefa ayar tambaya ko shin tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi suna haifar da ɗa mai ido ta hanyar kalato wa ƙasar wata riba. Sai dai...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada. Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni. Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na...
Ruben Amorim ya yi amai ya lashe kan kalaman da ya yi cewar ƙungiyarsa ta Manchester United ta kakar nan ita ce mafi muni a tarihi. Sai dai ya ce ba zai yi yaudara ba da cewar ba su da manyan matsaloli ba a kasa. Amorim ya ce ya yi kuskure da ya samar da baraka lokacin da ya fuskanci ƴan wasa nan take, bayan tashi karawar da Brighton ta yi nasara 3-1 a Premier League. Hakan ya sa ya gana da ƴan jarida cikin fushi da ta kai ya faɗi wasu kalaman. An tambaye shi ko ya san cece-kucen da batunsa ya haifar kafin fuskantar Rangers a Europa League, Amorin sai ya ce yana magana da kansa ba da...