2025-03-02@21:52:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 243
«kungiyar kwallon kafa ta»:
Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila lamba da ta dakatar da matakin da ta dauka na yunkurin halaka mutane fiye da miliyan 2, inda ta kara da cewa, bayanin Netanyahu dangane da tsawaita matakin farko wani yunkuri ne na kaucewa yarjejeniyar, da kuma kaucewa shiga tattaunawa a mataki na biyu. Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Isra’ila ta sanar da dakatar da duk...
Salah ya kasance danwasa na farko a gasar Premier da ya ci ya kuma bayar aka ci a wasanni daban-daban har goma a kaka daya. Sannan shi ne danwasa na farko da ya yi haka a daya daga cikin manyan gasar Turai biyar tun bayan Lionel Messi da ya yi wannan bajinta a kakar 2014-15, inda ya yi wa Barcelona hakan da kwallo 11. Sai dai babban abin da yake gaban kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ko kuma yake ci mata tuwo a kwarya shi ne kasancewar a karshen wannan kakar kwantiragin Muhammad Salah zai kare kuma har kawo yanzu bai sake sabon kwantiragin ba, tunda har yanzu ba su cimma wata yatrjejeniya ba wadda za ta saka ya ci...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza. Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. » Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga...
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance matsalar da Falasdinawa suke...
Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru. Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu. Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya...
Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan kai alkamar zuwa nahiyar Afirka da su ne fari da ake fama da shi Arewacin Afirka da kuma ambaliyar ruwan sama a yankin Sahel.
Kazalika, wannan kimiyya abar maraba ce ga masu kiwon Shanu, musamman ga wadanda ke bukatar fadada samar da ingantacciya kuma wadatacciyar Madara a guraren kiwonsu. Kirkirar kimiyyar, ta zo kan gaba duba da kokarin niyyar da Ma’aikatar Bunkasa Kiwon Dabbobi ta sanya a gaba, ta zamanantar da kiwon dabbobi da kuma habaka samar da wadatacciyar Madarar Shanu a kasar nan. Ana dai ci gaba da bukatar ingantacciyar Madarar Shanun a fadin wannan kasa, sai dai ana ci gaba da fuskantar kalubalen lafiyayyun Shanun, musamman a kasa irin Nijeriya. Sabuwar kimiyyar za ta bayar da damar saurin sanya ido kan yadda kiwon lafiyarsu ke tafiya, saurin gano ko sun harbu da wata kwayar cuta da kuma kula da lokacin nakudanarsu. “Wannan...
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban hukumar IMF Kristalina Georgieva ta fadawa gwamnan babban bankin kasar Lebanon na riko, Wassim Mansouri a wata haduwa da suka y ikan cewa kasarsa zata sami kudaden sake gidan kasar dag wajenta ne, tare da sharudda. Rahoton ya kara da cewa kasashen Lebanon da Siriya zasu sami kudade daga cibiyoyin biyu ne kawaii dan sun samar da dangantakar diblomasiyya da HKI. Sannan kasar...

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta ‘Euro-Med Monitor’ Ta Ce Ta Sami Shaidu Wadanda Suka Tabbatar Da Cewa HKI Tana Azabtar Da Fulasdinwa
Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta wacce take da cibiya a birnin Geneva na kasar Swizlanta ta bada sanarwan cewa ta sami cikekken shaidu wadanda suke tabbatar da cewa gwamnatin HKI tana azabtar da falasdinawa wadanda take tsare da su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana bada wannan sanarwan a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa Jami’an gidajen yari da kuma sojjin HKI suna dukan kawo wuka kan falasdinawa da suka shiga hannunsu, sannan suna azabtar da su sosai, daga ciki har tare da yanke yanke wasu gabban jikinsu. Kungiyar ta kara da cewa, mutum yana iya ganin alamun duka da kuma kumburan wurare da dama a jikin Falasdiwa. Banda haka Falasdinawan...
Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah na fadar haka, ya kuma kara da cewa kungiyar ta gabatar da shihidar da dama saboda kare kasarsu, saboda kare kasar Lebanon daga mamayar HKI. Labarin ya kara da cewa an gudanar da jana’izar ne a garuruwan Aitarun da kuma Aita shaab. Inda mutanen da dam dagayankin zuka halarta . Labarin ya kara da cewa Shahidan sun kai ga shahada ne a hare-haren da sojojin HKI suka kai kan kudancin kasar ta Lebanon a cikin watannin Octoba da kuma Nuwamba na shekara ta 2024. Labarin ya kara da cewa a yakin dai mutanen leabin kimani...
“PDP jam’iyyar siyasa ce, kuma muddin kuka ci gaba da kai mata hari, ba za ku samu ci gaba ba. Ba za ku iya daukar nauyin ‘yan baranda na siyasa da farfaganda don lalata mana kima ba don kawai burge Shugaba Bola Tinubu saboda ajandar ku ta 2027. “Ba wani dan Arewa mai hakali da zai yi wa APC yakin neman zabe a Arewa. Kasancewar wasu ’yan siyasa suna yi wa jam’iyyar shigo ba zurfi ne domin su sami abun sawa a bakin salati ne kadai amma ba wai za su zabe ta a 2027 bane. “Bai kamata Uba Sani ya bar wasu ‘yan siyasa suna yaudararsa, wadanda ba za su iya amfanar da siyarsa da komai ba. “Saboda haka,...
Cibiyar Bunƙasa Ayyukan Bincike za ta gudanar da gangami domin nazarin dokokin da suka shafi zamantakewar Musulmi a jihohin da ta ke aiki, domin inganta haƙƙoƙin mata da ƙananan yara. Shugaban tawagar cibiyar, Dokts Taofik Abubakar daga Jami’ar Bayero Kano ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da suka kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, a fadarsa da ke Zariya. Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki Dokta Taofik, ya ce sun je fadar ne, domin neman albarka da shawarwari kan hanyoyin magance cin zarafin mata. Ya kuma bayyana cewa cibiyar ta ɗauki nauyin malamai da limamai zuwa Jami’ar Al-Azhar da ke Masar...
Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023, jami’an sojin sun amince da cewa sun kasa cika aikinsu a ranar da Hamas ta kai wa Isra’ila hari. Wani jami’in soji ya shaidawa gidan radiyon RFI cewa sojojin sun “kasa cika aikinsu na kare fararen hula Isra’ila” a harin na ranar 7 ga Oktoba, 2023, yayin da aka fitar da babban sakamakon binciken. Ya kara da cewa...
A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu. An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli. Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023 Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce,...
An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...

Bankin Raya Afirka ( AFDB) Ya Bayyana Kasashen Da Tattalin Arzikinsu Yake Bunkasa Da Sauri A Cikin Nahiyar
Bankin Raya Afirka ya sanar da wasu kasashe 10 da ya ce, su ne tattalin arzikinsu yake bunkasa da sauri a cikin nahiyar, tare da yin hashashen cewa gabashin Afirka zai zama sama da sauran yankunan nahiyar a cigaba. Ana hasashen cewa a cikin rabin kasashen nahiyar za a sami habakar jumillar kudaden shiga ( GDP) daga 4.4% da ya kasance a 2024, ya koma 6.1% a cikin 2026. Sai kuma a cikin kasashen Rwanda, Uganda, Sudan Ta kudu, Habasha, Tanzania da Kenya mafi karancin karuwarsa zai zama kaso 5.% a 2025. A cikin yankin yammacin Afirka kuwa, an tsinkayo cewa tattalin arzikinsu zai tashi daga 4.1% a 2024,zuwa 4.6% a 2025, kuma kasashe irin su Togo, Benin, Cote De...
Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa. Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka. Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba. Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa Ya ci gaba da cewa, “yanzu mun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za mu yi gwajin tashin helikwaftan farko ƙirar Najeriya.” Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa...
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada. An gudanar da rabon kayan ne a ɗakin ajiyar abinci na gwamnatin jihar da ke Bulasa. Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a wajen rabon, ya gode wa gidauniyar bisa tallafin da ta ke bai wa mutanen jihar. Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince...
Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama na Afrika-AAAF. Da yake jawabi a wajen taron shugabannin sojojin saman Afrika da aka gudanar a kasar Zambiya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jadadda bukatar samar da hanyoyin warware kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar, hafsan hafsoshin ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin shiyya da dabarun hadin gwiwa wajen karfafa karfin jiragen na Afrika da kuma magance barazanar da ake fuskanta. Ya jaddada cewa, inganta hadin gwiwa tsakanin sojojin saman Afrika na da matukar muhimmanci wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke...
Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross. Fursunonin sun isa birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan ne a kan motocin kungiyar agaji ta Red Cross bayan sun tashi daga gidan yarin Ofer da ke yankin da aka mamaye. Musayar ta karkare kashi na farko na musayar da aka faro tsakanin bangarorin biyu, wanda ke gudana a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka fara aiwatarwa a watan da ya gabata da fatan kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza na tsawon watanni 15. Falasdinawan da aka sako na cikin fursunoni sama da 600, wadanda...
Ukraine ta amince da wata yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai da cinikayyar albarkatun ƙasa. Ana sa ran sanar da yarjejeniyar a hukumance a yau Laraba, inda za a ba wa kamfanonin Amurka dama su shiga harkar haƙar ma’adinai a Ukraine, ciki har da man fetur da iskar gas. Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Bisa ga bayanai, Amurka za ta samu wani kaso mai yawa daga ribar da za a samu, wanda zai iya kai wa Dala biliyan 500. Duk da cewa ba a bayyana batun tallafin tsaro a cikin yarjejeniyar ba, ministar shari’ar Ukraine, Olha Stefanishyna, ta ce akwai wasu muhimman batutuwa da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arigchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron Jana’izar manya-manyan shahidan kungiyar kuma shuwagabannin kungiyar, Shahid Sayid Hassan Nasarallah, da kuma magajinsa Sayid Hashin Safiyyuddeen. Wadanda sojojin HKI suka kashe ko suka kaisu ga shahada a shekarar da ta gabata. Labarin ya kara da cewa jakadan kasar Iran a Lebanon Mujtaba Amani ya sami halattan taron inda bangarorin suka tattauna sabbin al-amura da suke tasowa a kasar da kuma yankin kudancin Asiya da...
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa. Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da aikin soji a yammacin gabar kogin Jordan. Fu Cong ya bayyana cewa, dole ne mulkin Gaza bayan yakin ya bi ka’idar “Falasdinawa su yi mulkin Falasdinu”, kuma ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga sake gina Gaza. Kana kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su kara himma wajen kira ga...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar. Ya...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da kungiyar Hamas ke yi. Bayanai sun ce za’a saki falasdinawan su 206 a cikin sa’o’I 24 masu zuwa. Dangane da dakatar da sakin fursunonin, Hamas ta zargi Isra’ila da “saka dukkan yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin hatsari mai tsanani” tare da yin kira ga kasashe masu shiga tsakani da su shiga tsakani. A nata bangaren, Hamas za ta mika wasu gawawwakin ‘yan Isra’ila hudu da...

Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A bukatar da aka mika wa mai gabatar da kara na kotun ICC Karim Khan a ranar 19 ga watan Janairu, 2025, wacce ta bayyana a ranar Litinin, kungiyar mai zaman kanta ta Democracy Now for the Arab World (DAWN) ta zargi Biden, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, da sakatarensa na tsaro, Lloyd Austin, da taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar kungiyar mai zaman kan ta,...
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar Juma’a a harabar masallacin Al-Aqsa, tana mai cewa matakin wani lamari ne mai matukar hadari da ke da nufin tauye ‘yancin addini. Hamas ta ce, umarnin ‘yan sandan Haramtacciyar Kasar Isra’ila cin zarafi ne ga dukkan ka’idoji, yarjejeniyoyin da kuma dokoki na kasa da kasa, sannan kuma hakan tsokana ce kai tsaye ga musulmi. Sanarwar ta kuma jaddada cewa, irin wadannan tsare-tsare ba za su...
An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo. Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo inda yaki ya kazanta a gabashin ƙasar. Shugabanin kasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi nadin a wani yunƙuri na kawo karshen yaƙin basasa a gabashin Congo, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da...
An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe. Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala. Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne yayin da wata motar dakon kaya maƙare da siminti ta yi ƙundumbala ta faɗa wani rami. Wata majiya ta ce fasinjoji 13 ne a cikin motar wanda 10 daga ciki suka mutu nan take yayin da ragowar ukun suka jikkata.. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Yobe, SP Dungus...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda. Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar tasa da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene. Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers da ke kasar, inda ya fara wasa tun shekara 2022, kafin nan ya...
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa. Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna. Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance. Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira...
’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta. Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.” Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki. Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda ya samu wakilcin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya ce shirin samar da tallafin a mazabu zai kara inganta manufofi 12 na gwamnatin jihar wadanda suka hada da karfafawa al’umma don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a kowane mataki. Ya yi fatan wannan karimcin zai yi kyakkyawan tasiri ga mutane 1,200 da suka ci gajiyar tallafin. A jawabinsa, dan majalisa...
Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce kungiyar ta saki fursinoni yahudawa 6, kuma take fatan HKI za ta saki falasdinawa 620 kamar yadda yake cikin yarjeniyar tsagaita wuta, amma ta ki yin hakan, da dalilin cewa wai kungiyar Hamas ta wulakanta daya daga cikin fursinoni 6 da ta saka. Jami’in na Hamas ya ce tawagar tattaunawar...
Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci. Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na haɗin gwiwa a Laddauga, wurin kiwon dabbobi na Kachia a Jihar Kaduna. Ya bayyana cewa, manufar wannan shiri ita ce tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai na makarantun makiyaya. Sakatare Janar ya ƙara da cewa kashi 60 na waɗanda za su amfana ‘yan mata ne, kuma shirin zai ƙarfafa ilimin kyawawan ɗabi’u a fannin abinci mai gina jiki, tsafta, tsabtace muhalli, da kuma...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran). Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a wata ganawa da ya yi da shugabannin jami’an diflomasiyyar Afirka a birnin Tehran ya bayyana cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da nahiyar Afirka, na daya daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya a gaba. Aref ya kara da cewa, shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar...
Kungiyar Hamas ta jinjina da irin babbar gudunmawa da tsayin dakan da Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine suka yi wajen goyon bayan Palastinu, da kuma shahadar da suka yi a kan wannan tafarki. A cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da jana’izar shahidan biyu, kungiyar Hamas ta ce, muna addu’ar Allah ya jikan su da rahama, tare da mika ta’aziyyarmu ga al’ummar kasar Labanon da dukkanin al’ummar mu Larabawa da musulmi. Kungiyar ta tabbatar da cewa, laifuffukan Haramtacciyyar Kasar Isra’ila da kuma kisan gillar da ta yi wa shugabannin gwagwarmaya a Falasdinu, Labanon da sauran su, ba za su dakatar da tafarkinmu ba. Har ila yau sanarwar ta bayyana matsayin shahid Sayyid Hassan Nasrallah da jajircewarsa da...
Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...

Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20
A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...
Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai fam miliyan (£300m) a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa sannan ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe sama da fam biliyan biyu (£2bn), ko kuma a yi wa tsohon filin wasa na Old Trafford kwaskwarima da zai ci Fam biliyan 1.5. Manchester United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai Fam miliyan 113.2 daga ranar 30 ga watan Yunin 2024 kuma kawo yanzu kungiyar tana mataki na 15 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24. Amma kuma har yanzu kungiyar tana buga gasar cin...
Shugaban Majalisar Wakilai, Dokta Abbas Tajudeen ya ce Kasafin Kuɗin Nijeriya na baɗi zai ba da damar kafa ƙarin makarantu na matakin Tarayya a mazaɓarsa ta Zariya. Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara-shekara karo na 31 da 32 na ƙungiyar bunkasa ilimi ta Zariya, watau ZEDA da aka gudanar a Zariya. Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe An kama mutum biyu kan kisan wata mata saboda maita Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun haɗa da makarantar firamare da sakandare na yara masu buƙata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo. Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafin na musamman ga ɗaliɓin da ya fi...
Sama da magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham 1,000 ne suka yi zanga-ganga kan shugaban kungiyar, Daniel Leby kafin wasa da Manchester United a Premier ranar Lahadin da ta gabata. An yi ta kuwa da cewar ”Leby ya bar kungiyar da kuma ”Enic ya bar Tottenham” yayin da magoya baya suka rinka daga tuta a kusa da filin wasa, wadanda ke kiraye-kirayen a kawo canji. An kuma tsara yin zaman dirshan da zarar an tashi wasan Premier a karawa da United, inda magoya baya suka bukaci da kowa ya tsaya a filin wasan Tottenham. An kafa kyalle a wajen zaman masu gida da wajen zaman baki da aka rubuta sakon cewar ”lokacin canji ya yi” domin ”shekara 24 an...
Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed. Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da...
Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya bayyana aniyar kafa karin makarantu a Zaria. Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya ce za a kafa karin makarantu a mazabar tarayya ta zaria a kasafin kudin shekarar 2026. Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara karo na 31 da 32 na kungiyar bunkasa ilimi ta zaria, watau ZEDA da aka gudanar a Zaria. Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun hada da makarantar firamare da sakandare na yara masu bukata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo. Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafi na musamman ga dalibin da ya fi kowa kwazo a fannin koyon ilimin kwamfuta da kuma...
Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta kasa da kasa. Wang, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babbar darektar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, a birnin Johannesburg, birni mafi girma kuma cibiyar hada-hadar tattalin arzikin Afirka ta Kudu. A nata bangaren, Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, a tsakiyar rudanin da duniya ke fama da shi, kasar Sin ta hau kan turba mai kyau,...

Yake-Yaken Kasa Da Kasa Ne Suka Mamaye Taron G20 Na Ministocin Harkokin Wajen Kungiyar A Afirka Ta Kudu
A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu. Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba. Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na tattalin arziki a duniya sannan suna...
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA) da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), sun fara raba kayayyakin tallafi ga mutum 507 da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar a 2024. An gudanar da rabon kayayyakin a ranar Juma’a a Ƙananan Hukumomin Kibiya da Madobi, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya miƙa kayayyakin ga waɗanda suka ci gajiyar shirin. Ɗan Abacha ya kare mahaifinsa bayan ƙaddamar da littafin IBB Sibil Difens ta cafke mutum 17 kan aikata sata a Yobe Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya ne, ya wakilci gwamnan. Gwamnan, ya gode wa NEMA bisa goyon bayan da ta ke bai wa jihar, tare da yaba wa SEMA saboda jajircewarta wajen...

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da barazanar kai hari kan filin jirgin saman Lebanon da sauran muhimman wuraren kasar ba. Sheikh Damoush ya jaddada a cikin hudubarsa ta Juma’a cewa “ya zama wajibi gwamnati ta magance matsalar jiragen Iran zuwa kasar Lebanon, domin wannan batu na farko da na karshe yana da alaka ne da ‘yancin kai da kuma martabar kasar Lebanon, kuma hakan na nuni da kwace ‘yancin matakin da...

Sojojin Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Luguden Wuta Kan Gabar Yammacin Kogin Jordan
Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke arewacin gabar yammacin kogin Jordan a jiya Juma’a. Yanzu kusan wata guda ke nan da Netanyahu ya ba da umarnin tsananta hare-haren kan sansanin ‘yan gudun hijiran na Tulkram, kamar yadda ofishinsa ya bayyana, kwana guda bayan tashin bama-bamai kan motocin bus-bus a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila. Ofishin fira ministan ya bayyana cewa: Kwanan nan...
Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref da jakadun kasashen Afirka a Tehran. Baghaei ya bayyana cewa, taron ya nuna aniyar Iran na karfafa alaka da fadada hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban-daban na moriyar juna. A yayin ganawar, Aref ya bayyana cewa, dabarun gwamnatin Iran, karkashin shugaba Masoud Pezeshkian, ya yi daidai da ainihin manufofin Iran na inganta alaka da kasashen Afirka. Ya jaddada manufar karfafa hadin gwiwa tsakanin...
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”. A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya...
Arangama Tsakanin NLC Da Gwamnatocin Soji Ga duk mutumin da yai duba na tsanaki ga hakikanin manufofin samar da wannan kungiya ta NLC, la-budda, wajibi ne a rika samun sa-toka-sa-katsi tsakaninta da gwamnatoci musamman irin na Soja. Ba kawai gwamnatocin soja ba, da tafiya ta kara nikatawa kamar yadda za a gabatar nan gaba cikin wannan dan rubutu, an wayigari hatta gwamnatocin farar hula ma ba sa wanyewa lafiya da wannan madigar kungiya ta NLC. A mabanbantan lokutan gwamnatocin Soji a wannan Kasa, an sha yin kwalli da kai farmaki tare da kame shugabannin wannan kungiya ta NLC, inda za a ga cewa, gwamnatocin, sun fi yin amfani ne da jami’an tsaro na farin kaya (DSS), wajen kai hare haren...
Bugu da kari, ministan ya ce bana lokaci ne na Afrika, duba da cewa za a gudanar da taron kolin G20 a nahiyar Afrika a karo na farko tun bayan da AU ta zama cikakkiyar mamba. Ya ce ya kamata a saurari kiraye-kirayen nahiyar, a kuma yi la’akari da damuwarta, kana a taimakawa ayyukanta da samar da damar wanzar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar. Ministan ya kuma tabbatar da cewa, kasar Sin na goyon bayan jama’ar nahiyar su warware matsalolin da kansu, kuma tana adawa da kasashen waje su rika tsoma baki cikin harkokin kasashen Afrika. (Fa’iza Mustapha)
Kungiyar wasan Kareti ta Iran ta zama ta daya a nahiyar Asiya, yayin da Iraki ta zo ta biyu sai kuma Tajikistan ta uku. An yi wannan gasar ne ta Asiya a garin Calus dake Arewacin Iran wanda ya sami halartar kasashe da dama. Daga cikin kasashen da su ka shiga gasar wasannnin da akwai Iraki, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman sai kuma Tajikistan. An bude wannan gasar ne dai daga ranar 19 ga watan nan na Febrairu, kuma za a rufe ta zuwa gobe 22 gare shi. Da akwai ‘yan wasa 120 na cikin gida da waje da su ka shiga cikin gasar, da ‘yan kallo 700 a cikin dakin wasa.

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...

Wasu Motocin Bas-Bas Sun Tarwatse A Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yankin Bat Yam A Kudancin Tel-Aviv
Motocin bas-bas guda uku sun tarwatse a birnin Tel Aviv, lamarin da ya haifar da rudani a tsakanin yahudawan sahayoniyya Motocin bas-bas guda uku sun fashe da yammacin jiya Alhamis a wurare daban-daban a yankin Bat Yam da ke kudancin birnin Tel Aviv a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila. Kafofin watsa labaran haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana cewa: Ma’aikatan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila ta “Shin Bet ta fara binciken wadanda ake zargin dasa ababen fashewa da suka yi sanadiyyar tarwatsewar motocin bas-bas din, kuma sun ba da rahoton zargin cewa; An samu wasu bama-bamai guda biyu wadanda ba su fashe ba. Har ila yau, kafofin watsa labaran ‘yan mamayar sun ruwaito cewa: An dakatar da zirga-zirgan jiragen kasa gaba...
Gwamnatin jihar Jigawa ta yi alkawarin ci gaba da gudanar da ayyukan kiwon lafiya da aka gudanar karkashin hadin gwiwarta da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), da shirin samar da rigakafin cututtuka a kasashe masu tasowa(GAVI) a cikin shekaru uku da suka gabata. Haɗin gwiwar wanda aka fara shi da yarjejeniyar fahimtar juna da aka rattaba hannu a shekarar 2022, an yi shi ne don haɓaka tsarin bada lafiya na jihar, da inganta tsarin rigakafi ta hanyar samar da kayan aiki da wadatattun ma’aikatan lafiya. A wajen mika kayan aikin da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, Gwamna Umar Namadi ya ce shirin ya bayar da gudunmawa musamman wajen samar da inshorar lafiya...
Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya. Bayan neman albarkatun man fetur da gas, an kuma tsara aikin rijiyar don zurfafa nazarin juyin halittar duniya da kuma zurfafa ilimin binciken kasa. A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da...
Ƙungiyar Masu Nakasa ta ƙasa reshen Jihar Gombe (JONAPWD), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta kuma Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Masu Nakasa ta Jihar, Dokta Isiyaku Adamu. Ƙungiyar ta shirya taro na musamman tare da iyayen yara da suke fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. NNPP ta rasa Ɗan Majalisa na farko da ya koma APC Harin ’Yan bindiga: Mun yi asarar shanu sama da miliyan 4 – Miyetti Allah Wannan taron na musamman, wanda aka gudanar a ofishin JONAPWD da ke Gombe, ya zama wata muhimmiyar dama don tattauna matsaloli, musayar ƙwarewa da kuma ƙarfafa fafutuka don kare haƙƙoƙin yara masu fama da matsala irin ta nakasar jiki da kuma ta taɓin hankali. A...
Gidauniyar Tunawa Da Sir Ahmadu Bello Za Ta Gudanar Da Taronta Karo Na 11 A Bauchi.Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za ta gudanar da bikin tunawa da Sir Ahmadu Bello na shekara karo na 11 a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, a Bauchi, Jihar Bauchi. Taron, wanda aka shirya tare da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Bauchi, zai girmama marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato kuma Firaministan tsohuwar Yankin Arewa. A bana, taken laccar shi ne “Arzikin Halitta: Juya Albarkatun Yankin Arewa Zuwa Ci Gaban Tattalin Arziki Mai Dorewa.” Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yadda za a yi amfani da albarkatun noma da ma’adanai da ruwa don bunkasa ci gaban tattalin arzikin...
Kwamandan dakarun juyin juya halin Musulunci na rundunar sararin samaniya ya jaddada cewa; Babu shakka Iran zata kaddamar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila na alkawarin gaskiya na 3 Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na rundunar Sojin sararin samaniyar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, ya jaddada cewa za a gudanar da farmakin daukan fansa na Alkawarin Gaskiya na 3 idan Allah Ya yarda, amma Iran ba zata barnatar da kwarewarta a banza kamar yadda ya faru a harin alkawarin Gaskiya ta 1 da ta 2 ba, don haka babu shakka za a gudanar da harin daukan fansa kan haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya kara da cewa: Yankin yammacin Asiya ya samu ci gaba da dama, kuma...
Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
Jarin da kasar Sin ke zubawa wajen inganta lafiyar muhalli mai dorewa a duniya ya nuna muhimmiyar rawar da take takawa ta wannan fuskar. A shekarar 2024, kasar ta jagoranci duniya wajen zuba jarin sauya makamashi, inda ta zuba dalar Amurka biliyan 818 a wannan bangare. Wannan jarin ya sanya kasar Sin ta zama cibiyar samar da makamashi mai tsafta a duniya domin ita ke da kusan kashi 50 cikin dari na tasoshin samar da man “hydrogen” mara gurbata muhalli a duk duniya. Kasar Sin ta nuna wa duniya kyakkyawan misali abin koyi kamar yadda Shugaba Xi na kasar ke ci gaba da yayata muhimmancin kiyaye halittun doron kasa da kuma maye makamashi mai gurbata muhalli da mai tsafta. Shi...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na gaba na musayar fursunoni. Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya...
Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...
Jagoran juyin juya halin Musulunci A nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya gana da shuwagabannin kungiyar Jihadul Islami na kasar Falasdinu da aka mamaye a jiya Talata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa Ziyad Nakhalah shugaban kungiyar ne ya jagoranci tawagar kungiyar zuwa ganawa da jagoran. Labarin ya nakalto Jagoran juyin juya halin musulunci ya fadar cewa a halin yanzu babu wani abunda HKI zata yi a gaza sai idan kungiyoyi masu gwagwarmaya suna sun abin ya faru, saboda kekkyawar riko da suka yiwa yankin. Imam Seyyed Ali Khamenei, ya yabawa kungiyoyin falasdinawa kan hadin kai da suka nuna a yankin da ya gabata. Ziyad al-Nakhalah, babban sakataren kungiyar Jihad Islami, ya bayyana cewa sun...
Gwamnatin Jumhuriyar Nijer daga jiya Talata ta fara aikin hana yan Najeriya dauke da Passport na kungiyar ECOWAS shiga kasar. Kafin haka dai mutane daga kasashen ECOWAS suna shiga kasashen kungiyar ba tare da bukatar visar shiga ko wace kasa daga cikin kasashe kungiyar ba. Amma bayan da kasashe 3 Nijer, Burkina Faso da kuma Mali suka fice daga kungiyar sannan suka samar da sabon Passport a tsakanin kasashen uku, sai al-amura suka fara sauyi tsakaninu da Ecowas. Sun fara hana wadanda suke rike da Passpory na kasashen ECOWAS shiga kasashen ba tare da visa ba. Gwamnatin Nijer bata bada sanarwan fara aiki da wannan dokar ba. Kuma wani jami’in shige da fice na Niger ya ce umurnin ne aka...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya aikata duk abin yake so Shugaban Amurka Donald Trump ya yi nuni da wa’adin da ya bayar dangane da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma sakin fursunonin, yana mai cewa ya shaidawa fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya aika duk abin da yake so. Trump ya tabo batun mataki na gaba – ana sa ran za a fara tattaunawa nan ba da jimawa kan kashi na biyu na yarjejeniyar – ya ce: “Ya rage ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan mataki na gaba, tare da tuntubarsa.” An kuma tambayi Trump ko jinkirin jigilar makamai zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila a karkashin Shugaba Biden zai “hana tsagaita...

Jaridar Maariv Ta Isra’ila Ta Bayyana Wasu Daga Cikin Hasarorin Da Yakin Gaza Ya Janyo Wa Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya
Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji. Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa. Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa. A wata wasika da...
A ranar Asabar din da ta gabata ne shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka AU, suka zabi shugaban kasar Angola Joao Lourenco, a matsayin sabon shugaban karba-karba na kungiyar da kuma ministan harkokin waje da hadin gwiwar kasa da kasa na Djibouti, Mahamoud Ali Youssouf, a matsayin sabon shugaban hukumar gudanar da ayyukan kungiyar, wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a kasashe biyu masu matukar muhimmanci a nahiyar, wato Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo (DRC) da kasar Sudan. Rikicin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kara kamari, bayan samun galaba a wasu yankunan kasar da ‘yan tawayen M23 suka yi, na baya-bayan nan shi ne kwace iko da muhimman wurare da dama a birnin Bukavu, hedkwatar...
Iran ta bayyana cewa za ta aike da tawaga a matakin koli zuwa jana’izar mirigayi babban sakataren kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon Hassan Nasrallah. Da yake sanar da hakan kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce kasar za ta halarci gagarumin bikin mai matukar muhimmanci, Tunda farko dai kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa tawagogin kasashe 79 za su halarci bikin tunawa da marigayi babban sakataren kungiyar Sayyid Hassan Nasrallah da kuma shugaban majalisar zartarwarta Sayyid Hashem Safieddine. Sheikh Ali Daher, kodinetan babban komitin jana’izar Nasrallah da Safieddine, ya bayyana cewa bikin da aka shirya yi a ranar 23 ga watan Fabrairu, zai kasance “ranar tunawa da shugaban wanda aka zalunta a kan...
Bangaren kungiyar Hamas da ke dauke da makamai ya tabbatar da shahadar wani daga cikin jami’in kungiyar a wani harin Isra’ila. Muhammad Ibrahim Shaheen, ya yi shahada ne a wani harin da wani jirgin yakin Isra’ila ya kai a Sidon. Kassam Brigades ta bayyana shi a matsayin wanda ya yi tsayin daka kan zalincin Isra’ila, ciki har da lokacin yakin Gaza. Ita ma Isra’ila ta tabbatar da kashe jami’in na Hamas a harin da ta ce ta kai kan a Lebanon Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin ta sama a Sidon, inda suka ce sun kashe wani “dan ta’adda” Bafalasdine. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kokarin ganin yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma...
’Yan sanda sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargi da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 12 fyaɗe a kauyen Jalingo da ke Ƙaramar Hukumar Tarmuwa a Jihar Yobe. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya fitar a Damaturu ranar Litinin. Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina Yadda na yi wa budurwar da muka haɗu a Facebook gunduwa-gunduwa —Matashi Ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na yammacin ranar 15 ga watan Fabrairu, inda waɗanda ake zargin suka kai yarinyar wani kango a jeji suka keta mata haddi. Rahoton na cewar, “Hedikwatar ‘yan sandan jihar reshen Ƙaramar Hukumar...

Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Da Hamas Sun Yi Tirsa Da HKI Kan Azabtar Da Falasdinawa A Gidan Yarin Ofer
Kungiyoyin Hamas, Jihad Isalami da kuma sauransu a kasar Falasdinu da aka mamaye sun bayyana yi allawadi da HKI saboda yadda suke zazabtar da fursinonin Falasdinawa a gidan yarin Ofer, kamar yadda labari ya ke isa daga ca. Tashar talabijin ta Presstv na takalto cewa gidan yarin ofer ya na yammacin birnin Ramallah, a yankin yamma da kogin Jordan. Kungiyoyin sun bayyana cewa, wannan shi ne halin ta’addanci da kuma kekacewar zuciya yahudawan sahyoniyya. Daga karshe kungiyoyun sun yi kara da wadanda abin ya shafa su rika sanya ido sannan su aikata abinda ya dace don kawo karshen wahalar falasdinawa a gidajen yarin Ofer.
Najeriya ta nuna adawa da wani yunkuri na sake fasalin Sashen Harkokin Siyasa, Zaman Lafiya da Tsaro na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) (PAPS), saboda damuwa game sanadin da ka iya tabarbarewar hanyoyin zaman lafiya da siyasa na kungiyar. Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar ne ya sanar da wannan matsayi a madadin Shugaba Bola Tinubu, a lokacin da ake tattaunawa kan ssauye-sauyen kungiyar AU. Shugaban na Najeriya ya kuma yabawa shugabanin kasashen Ruwanda Paul Kagame da William Ruto na Kenya, bisa shawarwarin da suka gabatar na kawo sauyi da nufin ganin kungiyar ta AU ta kara zage damtse wajen magance matsalolin mambobin kungiyar. Shugaba Tinubu ya bayyana goyon bayansa na samar da kwamitin sa ido kan shugabannin kasa da...
Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa. Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma...
Shugaban gwamnatin kasar Jamus Olaf Scholz ya gargadi Amurka da cewa, turai a shirye take ta kalubalanci barazanar da take yi mata, duk da cewa dai tana fatan fahimtar juna. Shugaban gwamnatin kasar ta Jamus; Duk wanda yake son nahiyar turai ta shiga cikin batun zaman lafiya, to dole ne ya yi tarayya da ita cikin daukar matakan da su ka dace.” Shugaban gwamnatin na kasar Jamus dai yana mayar da martani akan batun kawo karshen yakin Rasha da Ukiraniya ba tare da bai wa kasashen na turai damar bayyana ra’ayinsu akan batun ba. Dangane da batun kara kudaden fito akan hajar da kasashen turai ke shigarwa Amurka, Olaf Scholz ya ce, Turai tana da karfin da za ya iya...
A wani zanga-zangar lumana da suka gabatar a jiya Asabar masu goyon bayan kungiyar Hizbullah sun yi kira ga gwamnatin kasar Lebanon kada ta bari Amurka da HKI su zama su ne ke jajjuya al-amuran kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmood Qamati shugaban kwamitin siyasa na kungiyar Hizbullah ya na fadar haka a jiya Asabar, a kan babban titin da ya ke zuwa tashar jiragen sama na birnin Beirut babban birnin kasar kasar, wato Rafiqul Hariri INT. Airport, inda mabiya kungiyar suka yi gaggami, don nuna rashin amincewar da hana jiragen saman Iran sake sauka a tasahar. Qamati ya kara da cewa bai kamata HKI tayiwa jiragen saman Iran masu zuwa beiru barazana, sannan ita...
Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin yaki na ” Drone” ya cilla kan wata mota a kan titi a garin Jarjoun da Iqlim Attuffah inda suka kashe mutane 3 sannan wasu kusa da motar guda 4 sun ji rauni. Majiyar yahudawan ta bayyana cewa sun kashe wani kwamandan kungiyar Hizbullah ne, amma shaidu a yankin sun tabbatar da cewa duk wadanda HKI ta kashe ba mayakan kungiyar Hizbullah ne ba. Wannan...
Ya ce Jihar Kogi ce ta gudanar da taron domin tana da shugabannin kungiyar a matsayin gwamna da mataimakinsa, inda ya ce Gwamna Usman Ododo na daya daga cikin jami’ansa a Jihar Neja sannan kuma mataimakin jami’in kungiyar malamai ta Nijeriya (NUT). Ya ce, “Don haka muna son mu yi wannan taron ne domin mu saurare ku don sanin abin da aka yi da abin da ba a yi yadda ya kamata ba, don haka mu dauka mu kai musu. “A gare mu, kamar zuwan gida ne. Muna so mu zo mu yi hulda da su don gano ko suna yin abubuwan da muke sukar wasu.” Kan haramta kungiyoyin kwadago a kwalejojin jihar da gwamnatin baya ta Yahaya Bello ta...
An zabi dan takarar kasar Djibouti Mahamoud Ali Youssouf a matsayin sabon shugaban kwamitin gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika ta AU. An zabe shi ne a yayin zaman taron kungiyar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha da yammacin yau Asabar. Ya samu nasara ne a zagaye na 7 da kuri’u 33 daga cikin 49. Dan shekaru 59 da haihuwa, wanda shi ne ministan harkokin wajen kasar Djibouti zai gaji Moussa Faki Mahamat na Chadi wanda wa’adinsa na biyu kan shugabancin kungiyar zai kare a ranar 15 ga watan Maris. Manyan kalubalen dake gaban sabon shugaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ta AU sun hada da rikicin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango da Sudan da kuma matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya...

Ministan Tattalin Arziki Na Kasar Iran Ya Kama Hanyar Kasar Saudiya Don Halattar Taron Tattalin Arziki
Ministan kudi da tattalin arziki na kasar Iran yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiya don halattar wani taro mai muhimmaci na tattalin arziki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan tattalin yana fadar haka a shafinsa na X, ya kuma kara da cewa, yana zuwa wannan taron ne tare da gayyar tokwaransa na kasar Saudiya da kuma kum ashugaban hukumar lamuni ta duniya, wato IMF. Abdulnaser Himmati ya bayyana cewa manufae taron itaa ce tattauna hanyoyin bukasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa . Har’ila yau taron tana son kyuatata dangantakar tattalin arziki a kasashen yankin Asia da kuma aiki tare da sauran kasashen duniya sabota ci gaban kasashen duniya gaba daya. Taron na kwanaki biyu, wata...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa kungiyar tattalin arziki ta BRICS ta mutu, saboda barazanar da yayi na karawa dukkan mambobin kungiyar kudin fito ko haraji na 100% na kayakin kasashensu dake shiga kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, maganar shugaban zai kara sabani a cikin kasashen kungiyar, ta BRICS wanda suke ganin Amurka ta mamaye al-amuran tattalin arziki a duniya. An kafa kungiyar BRICS ne a shekara 2009 kuma kasashen da suka fara kafata sune, Brazil, Russia, India, da kuma China, amma daga baya kungiyar ta kara fadada, inda kasashen Afirka ta kudu, Iran, Habasha, da kuma Hadaddiyar daular Larabawa. Bayan da kasar Rasha ta karbi shugabancin kungiyar na...
Sojojin HKI sun kaseh Falasdinawa 4 a yankin yamma da kogin Jordan a lokacinda suke fadada hare-haren da suke kaiwa kan falasdinawa wanda kuma yake daukar rayukar Falasdinawa a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar WAFA ta falasdinwa wacce ta nakalti majiyar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin tana cewa sojojin yahudawan sun kashe Adel Abdel Bashkar a sansanin yan gudun hijira na Askar a kusa da garin Nablus bayan albarusai sun sameshi a kirjinsa. Labarin ya kara da cewa bayan an kai shi asbine sai yace ga garinku, ko kuma yayi shahada. Har’ila yau majiyar ta kara da cewa Falasdinawa matasa uku ne suka yi shahada a lokacinda sojojin yahudawan suka kai hari a sansanin...
Duk da kasancewar Malam Murtala Abubakar nakasasshe mara kafafu, amma bai lamunci yin bara ba. Hasali ma, ya rabu da matarsa ta fari saboda dabi’arta ta yin bara. Shekaru 50 da suka wuce Malam Muratala ya rasa kafafunsa, tun yana dan shekara bakwai a duniya. A haka ya ci gaba da rayuwarsa, inda a halin yanzu yake kula da iyalansa, mata hudu wadanda dukansu nakasassu ne da ’ya’yansu 15. A haka yake fadi-tashin daukar dawainiyarsu, domin tsare mutuncinsa, saboda ya yi imanin cewa, “Bara tana rage daraja da kimar mutum.” Wannan ne ma ya sa ya rabu da matarsa ta farko saboda dabi’ar bara. Rayuwar Malam Murtala, wanda a lokacin da yake dan shekara bakwai yake takawa da kafafunsa zuwa...
Cibiyar bincike kan fasahar sadarwa ta kasar Sin (CAICT), ta bayyana a yau Juma’a cewa, adadin wayar salula da Sin ta samar ya karu da kaso 22.1 a watan Disamban bara, zuwa kusan guda miliyan 34.53. Cibiyar wadda ke karkashin ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, ta ce zuwa watan Disamban, wayoyi masu sadarwar 5G ne suka dauki kaso 88.1 na adadin, inda jimilarsu ta kama miliyan 30.43, karuwar kaso 25.8 a kan na makamancin lokacin a shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Limamin da ya jagoranci sallar Jumu’a a birnin Tehran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani ga shugaban Amurka ta hanyar gudanar da bikin tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci Limamin da ya jagoranci sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun mayar da martani da kakkausar murya ga kalamai da kuma matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka ta hanyar halartar gagarumar zanga-zangar tunawa da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar Iran. Ayatullah Khatami ya kara da cewa: A yau daga mimbarin Juma’a da ke birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran yana tabbatar da cewa: Miliyoyin Iraniyawa ne suka halarci...

Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa
Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...