2025-04-04@21:23:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 354
«a safiyar yau»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya. Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano. A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko...
Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar. Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka rasa rayukansu fararen hula ne. A ranar Talatar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wani otel da ke birnin Baledweyne da wata mota da aka shakare da bama-bamai, kafin daga bisa suka shiga cikin otal din suka kai farmakin da ya dauki tsawon yini guda. Majiyoyin ‘yan sandan sun tabbatarwa kamfanin dillanmcin labaran Reuters cewa, hudu daga cikin ‘yan ta’addan...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed a fadar gwamnati, inda suka yi wata ganawar sirri. Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters Duk da cewa dalilin ziyarar bai fito fili ba, ana hasashen cewa yana da alaƙa da shirin siyasar 2027, inda ake ta raɗe-raɗin haɗakar ‘yan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Taron ya ƙara hura...
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu. Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar. Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi. Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar da yanayin na zafi kan haifar a jihohi goma sha tara na ƙasar daga yankin arewa ta tsakiya da yankin gabashin ƙasar. Kan haka ne muka tuntuɓi likita domin ya yi mana ƙarin bayani game da cututtuka biyar da aka fi kamuwa da su a lokacin zafi da kuma hanyoyin kare kai. Sanƙarau – Dakta Hassan Ibrahim, likita a asibitin Biba da ke jihar Kaduna ya...
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya NAJERIYA A YAU: Ladan Da Mai Aikin Ƙarfi Yake Samu A Lokacin Azumi Shin yin sulhu da ’yan fashin daji ita ce mafita? Kuma yaya halin yankunan da suka ƙulla irin wannan yarjejeniya yake a yanzu? Shirin NAJERIYA A YAU, zai yi duba kan yadda wasu al’umma ke ƙoƙarin tsira daga matsalar tsaro ta hanyar yarjejeniya...
Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton ya kuma bayyana cewa, a shekarar 2025 gwamnatin kasar za ta kara zage damtse wajen raya kauyukan dake rabe da birane da gyara gine-ginen da suka tsufa. Ga duk wanda yake shiga yankunan kauyuka da ke cikin birane (kamar unguwannin masu karamin karfi) ko wadanda suke rabe da su zai ga ba su da kyawun gani, domin kayayyakin alatu da kayatattun gine-gine da ababen more...
Hakika yadda kasar Amurka ta dakatar da tallafi a wannan karo ya nuna ra’ayin shugaba Donald Trump dangane da kasashen Afirka. Wanda za a iya fahimta bisa ganin yadda ya bayyana kasar Lesotho a matsayin “kasar da ba a san ta ba”, wacce ba ta cancanci tallafin da ake ba ta ba, a kwanakin baya, yayin da yake magana da ‘yan majalisun kasar Amurka. Sai dai shugaban bai san sauye-sauyen da kasashen Afirka suka samu ba, wadanda tun tuni suka daina dogaro da kasashen yammacin duniya. A daura da haka, ana iya ganin fahimtar matsayin kasashen Afirka mai dacewa, a cikin maganar da ministan wajen kasar Sin Wang Yi ya fada a kwanan baya, yayin da yake amsa tambayar da...
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya. Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba. ‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas. Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da daruruwan fasinjoji a ranar Talata a wani yunkurin ci gaba da ta da hankali da wata kungiyar ’yan aware ke yi a Kudu maso yammacin Pakistan. ’Yan bindigar sun raunata direban jirgin kasan a kokarinsu na kwace iko da jirgin a yankin Balochistan mai duwatsu da ke iyaka da Afghanistan da kuma Iran. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa Wani babban jami’in gwamnati mai kula da harkokin sufurin jiragen kasa Muhammad Kashif ya shaida wa AFP cewa adadin mutane da aka yi garkuwa da su ya kai 450. Sai dai kuma shafin jaridar rnz na intanet ya ruwaito cewa, daga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
An kora Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester United gida a Gasar cin Kofin FA na bana, bayan Fulham ta doke ta da ci 2-1 har gida a filin wasanta na Old Trafford a makon da ya wuce. Manchester United ta yi bankwana da gasar ne alhali ita ce ke mai riƙe da Kofin FA da ta lashe a bara, bayan nasara a kan Manchester City, lamarin da ya ba ta damar buga Gasar Europa a kakar bana. ‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’ An hana tashe bana a Kano — Nalako Kungiyar Old Trafford ta koma matsayi na 14 a kasan teburin Firimiya da maki 34, bayan da ta ci...
Shugaban kasar Ghana, John Darmani Mahama ya nemi kungiyar Ecowas da ta amince da kungiyar kawancen kasashen Sahel din nan guda uku da suka balle daga cikinta. Mista Mahama, ya bayyana hakan a kafofin sada zumunta a ranar Litini jim kadan gabanin ya ziyarci kasar Burkina faso, bayan ya kai irin wanan ziyara kasashen Mali da Nijar. Ci gaba da huldar tattalin arziki da kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso, na daga cikin jigon rangadin da shugaban Ghana ya kai a kasashen na AES. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta...
Rundunar ‘Yan sanda a jihar Kwara ta ce ta fara bincike kan kisan da aka yi wa Alhaji Idris Abubakar, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) na jihar. A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi ya fitar, ya ce an harbe shugaban ne a ranar 8 ga Maris, 2025 a kofar gidansa da ke Oke-Ose, a unguwar Ilorin. A cewar sanarwar Jami’an ‘yan sanda sun garzaya inda lamarin ya faru nan take, inda suka gano kwamson harsashi guda biyar da aka yi amfani da su wajen yin harbin. Ya bayyana cewa Hukumar Binciken Laifukan Jiha (SCID) ta fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin. Ta kuma bada...
Ƙungiyar SERAP, mai fafutukar haƙƙin ɗan Adam da yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya, ta buƙaci Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da ya gaggauta janye dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. SERAP ta ce dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha ba komai ba ne illa tauye mata ’yancinta na faɗin alabarkacin baki, wanda Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya ba ta. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Tsohon Mataimakin Gwamnan Kogi Patrick Adaba ya rasu Cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta fitar a ranar 8 ga watan Maris, SERAP ta ce muddin ba a kiyaye wannan gargaɗi ba za ta ɗauki matakin shari’a nan da sa’o’i 48. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun matamaikin shugabanta,...
Shugabana kasar Ghana John Dramani Mahama, ya ziyarci kasashen Mali da Nijar a wani bangare na ran gadin diflomatsiyya da ya fara a kasashen sahel din nan uku da suka balle daga kungiyar Ecowas. Bayan birnin Bamako a ranar Asabar, shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya je birnin Yamai a ranar Lahadi, inda wasu rahotanni ke cewa ya je ne da nufin dinke barakar da ke tsakanin kungiyar ta raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kasashen uku na Sahel. Saidai a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na Nijar, hukumomin kasar sun tabbatar da cewa kasashen sun tabbatar da aniyarsu ta karfafa dangantakar abokantaka da hadin gwiwa a tsakanin kasashensu a fannonin siyasa, tattalin...
Kasar Qatar ta bukaci hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa da ta sanya ido kan cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta bayyana cewa, Doha ta bukaci hukumar ta (IAEA) da ta sanya damar gudanar da bincike da ka’ida daga hukumar ta MDD, kan dukkanin cibiyoyin nukiliyar Isra’ila. Jakadan dindindin na Qatar a Majalisar Dinkin Duniya, Jasem Yacoub al-Hammadi, ya bukaci gwamnatin Isra’ila da ta rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Qatar ta fitar ta ce “Al-Hammadi ya jaddada bukatar kasashen duniya da cibiyoyinta su tabbatar da alkawurran da suka dauka a karkashin kudurorin kwamitin sulhu na MDD, da babban taron...
Bayanai da kungiyar dake sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar, sun ce rikicin baya-bayan nan tsakanin bangarorin da ke dauke da makamai da suka hada da kungiyar Hayat Tahrir al-Sham (HTC) da kungiyoyin dake da alaka da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad, ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 1,000 a cikin kwanaki biyu kacal. Wannan tashin hankalin, ya fi shafar yankin yammacin Syria, wanda ya kara ta’azzara halin da ake ciki. A baya dai kungiyar ta bayar da rahoton cewa, an kashe akalla mutane 237 da suka hada da 142 wadanda ba mayakan ba ne a yankin gabar ruwan kasar ta Syria, tun bayan fara kazamin fada a ranar Alhamis din da ta gabata....
Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan fararen...
Ofishin jakadancin kasar Sin dake Nijeriya, ya shirya taro domin bikin ranar mata ta duniya da ake gudanarwa a ranar 8 na watan Maris din kowacce shekara. Taron mai taken “Labarinta, Makomarta” wanda ya gudana ranar Juma’a a cibiyar raya al’adu ta kasar Sin dake birnin Abujan Nijeriya, ya hada mata daga dukkan bangarorin rayuwa, inda suka yi waiwaye kan ci gaban da suka samu da ma tsara hanyar tabbatar da daidaiton jinsi. Da yake jawabi yayin taron, jakadan Sin a Nijeriya Yu Dunhai, ya nanata muhimmancin bikin na wannan shekara kasancewar ya zo daidai da cikar Yarjejeniyar Beijing ta tabbatar da daidaiton jinsi ta MDD, shekaru 30 da kulluwa. A Mai Da Duniya Ta Zama Ta Kasa Da Kasa...
Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu. A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23. Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za...
Abin haka yake, akwai kasashe sama da 190 a duniyarmu, idan kowace kasa na bin manufar ba kanta fifiko, to nuna fin karfi zai zama a ko ina a duniyarmu, kuma kasashe masu karamin karfi su ne za su fi fuskantar matsalar. Amma abin farin ciki shi ne, har yanzu akasarin kasashen duniyarmu na rungumar adalci da zaman daidaito, kuma karin kasashe na rungumar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama. A sa’i daya kuma, kasashe masu tasowa na kara karfinsu, inda suka riga suka zama muhimmin karfin da ke kiyaye zaman lafiya da sa kaimin ci gaban duniya. Mutanen kasashen yamma su kan ce, “Moriya ta fi zumunta muhimmanci da dorewa”. Amma a ganin Sinawa, ya kamata abota...
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Syria ta bayar da rahoton cewa, adadin fararen hula da aka yi kisan kiyashin na baya-bayan nan daga tsiraru ‘yan Alawite ya kai mutane 1,018 tun daga ranar alhamis zuwa wannan Lahadi. Kungiyar sa ido ta ce jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria da kuma kungiyoyin da suke kawance da su da suka da alaka da alkaida, sun kashe fararen hula 745 na Alawi a cikin kwanaki uku da suka gabata, wanda ya haura adadin da aka sanar a lokutan baya. Sai dai Fox News ta buga misali da wata ‘yar Alawiyya, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa sama da mutane 4,000 ne aka kiyasta an kashe...
Wasu ’yan bindiga sun harbe shugaban ƙungiyar makiyaya Fulani ta Miyetti Allah reshen Jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Asabar yayin da maharan suka biyo sawunsa suka harbe shi a ƙofar gidansa da ke yankin Oke Ose na birnin Ilorin. Malaman Tsangaya Sun Bai wa Gwamna Inuwa Lambar Yabo Ta ‘Khadimul Qur’an’ Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Muhammad Abdullahi, wani hadimin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq kan hulɗa da al’umma da harkokin Fulani, ya tabbatar da faruwar lamarin. “Eh, an kashe shi jiya da daddare. Wasu ’yan bindiga ne suka harbe shi. “A yanzu haka ana shirin yi masa jana’iza, amma tun a jiya ’yan...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
A karon farko alkaluman ta’addaci a yankin Sahel da ke nahiyar Afirka ya zarce na jimillar sauran sassan duniya, a cewar rahoton cibiyar GTI mai bincike kan ta’addanci a matakin duniya. Rahoton ya nuna yawan kashe-kashe masu alaka da ta’addanci a Sahel, “ya zarce rabin jimillar adadin a duniya.” Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano Alkaluman sun nuna an kashe mutane 3,885 a yankin daga cikin mutane 7,555 da aka kashe a fadin duniya a dalilin ta’addanci. Rahoto ya kara da cewa a yayin da adadin a matakin duniya ya ragu daga kimanin 11,000 a shekarar 2015, lamarin ya ninku sau 10 a yankin daga shekarar 2019,...
Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara. “Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara. Farashin abinci da ya hauhawa a baya yana sauka. “Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.” Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da...
A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
5. Damfara da Alkawurra na Bogi: Wasu na bayar da alkawurran aure da ba su da gaskiya don cimma wasu burika nasu. Yadda Za Ka Kare Kanka • Ka guji aika hotuna na sirri ko bidiyo ga wanda ba ka sani sosai ba. • Kar ka yarda da duk wani alkawari da ba ka tabbatar da gaskiyarsa ba. • Ka duba asalin mutum kafin ka yi amanna dashi da bayanan ka. • Yi taka-tsantsan da sakwannin da kake fitarwa a yanar gizo. • Ka daina amfani da intanet wajen yin mu’amala da wanda ba ka da isasshen sani a kansa. • Idan kana fuskantar barazana, ka sanar da hukuma ko wani da ka yarda da shi. Labari Domin Karfafa Gwiwa...
Wasu alkaluma da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya CBN sun suna cewa, a 2024, Asusun ajiyar Nijeriya rufe ne a kan Dala biliyan 40.877. Wani masani a fannin tattalin arziki da ke da zama a jihar Legas Ibukun Omoyeni, a wani hasashe da ya yi kan shekarar 2025 ya bayyana cewa, Nijeriya ta fuskanci wasu bin ka’dojin yarjejeniyar karbar bashi, inda ya kara da cewa, baya ga batun kafin a shiga shekarar 2026, akwai wasu basussuka na waje Nijeriya ta ciwo wandanda kuma, ba su riga sun gama nuna ba, wanda akalla zai iya kai wa Dala biliyan 1.33 a duk shekara ko kuma sama da haka wadanda suka hada da biyan kudin ruwa na rancen, inda mai yuwa,...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Ta buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba. A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma. Ta tunatar da mahalarta...

Wang Yi: Diflomasiyyar Kasar Sin Ta Samar Da Kwanciyar Hankalin Da Ake Bukata A Duniya Mai Cike Da Rikici
Har ila yau Wang Yi, ya ce Sin da Amurka za su kasance a doron duniya na tsawon lokaci, don haka dole ne su nemi yadda za su yi zaman jituwa cikin lumana. A cewar Wang Yi, mutunta juna muhimmiyar ka’ida ce ta hulda kasashen biyu. Da yake tsokaci game da matakin Amurka na sanya karin haraji kan kayayyakin kasar Sin bisa fakewa da batun Fentanyl, Wang Yi ya ce, bai kamata Amurka ta saka alheri da sharri, ko kuma kakaba haraji ba. Yana cewa, tu’ammali da maganin Fentanyl a Amurka, matsala ce da ya kamata kasar ta warware da kanta. Ya kara da cewa, ba zai yiwu a yi tunanin za a danne kasar Sin, sannan kuma a ci...

China Ta Yi Gargadin Cewa Duniyar Zata Zama Ba Doka Da Oda Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Yakin Kudaden Fito Da Ta fara
A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...

Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka
Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...

Kasar Chaina Ta Yi Gargadin Cewa Duniyar Zata Zama Ba Doka Da Oda Idan Amurka Ta Ci Gaba Da Yakin Kudaden Fito Da Ta fara
A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...

Karin Kudin Lantarki Da Na Kira: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shirya Zanga-zanga A Fadin Nijeriya
Kungiyar ta yi tir da tsarin da hukumar kulawa wutar lantarki ta yi,wanda take neman ta ba masu amfani da wuta, nau’i- nau’in da suke ko ta kai su,ba domin komai ba don wata magana ta kara bunkasa samun wutar lantarki fiye da irin halin da ake ciki yanzu. Kamar dai yadda kungiyar tace tsarin Hukumar wani kokari ne na karin kudin wutar lantarki na sauyawa masu amfani da wuta daga tsarin da suka saba amfani da shi mai sauki zuwa ga wanda zai kasance wanda yake mai tsada. A sanarwar da aka fitar Shugaban kungiyar da Sakatarenta Kwamrade Joe Ajaero Komrade Emmanuel Ugboaja wadda ta ce tsarin da ake shirin yi tamkar “yin laifi ne ga tattalin arzikin kasa.”...
“Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne. Kasancewar Hafsan Sojin Sama a Zamfara na nuna ƙwarewa da kulawa ta musamman. Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da...
Da yammacin yau Alhamis ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, ya ziyarci mambobin taro na uku na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC karo na 14 ta kasar Sin, wadanda suka zo daga kungiyar dimokuradiyya ta kasar Sin, da kungiyar raya dimokuradiyya ta kasar Sin, da kuma bangarorin ilimi. Shugaban na Sin ya kuma halarci taron kungiyar hadin gwiwa na CPPCC, domin sauraron ra’ayoyi da shawarwari. Yayin ziyartar mambobin majalisar ta ba da shawara kan harkokin siyasa, Xi ya jadadda cewa, ya kamata a karfafa amfani da ilmi don inganta kimiyya da fasaha da kuma kwararru, ta yadda za a kafa wani yanayi...
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya jaddada kudurin Najeriya na aiwatar da cikakken yarjejeniyar biyu da aka kulla tsakanin China Media Group da manyan gidajen watsa labarai na gwamnati a Najeriya – Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) da Hukumar Rediyon Tarayyar Najeriya (FRCN) a taron hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka gudanar a Beijing. Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi Jakadan Sin a Najeriya, Mista Yu Dunhai, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa a yau alhamis. Ya ce, wadannan yarjejeniyoyi sun ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa a fannin watsa labarai da sadarwa, domin inganta dangantakar Najeriya da Sin. Ya bayyana cewa yarjejeniyoyin sun shafi...
Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a. Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da suka shafi fursunonin, Adam Boehler, da shugabannin Hamas, a yunkurin cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza. Trump ya ambaci haka ne bayan ganawa da fursunoni shida da aka sako a wani bangare na matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Wani babban kusa na kungiyar Hamas ya shaidawa Al Mayadeen cewa, taron na baya-bayan nan ya bar wa bangaren Amurka...
Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu. Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya. A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su...
Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.” Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy? Kwanakin baya...
Gwamnatin Jihar Kano, ta ƙulla yarjejeniya da kamfanin Stata Logistics Limited domin kafa sabon tsarin sufuri na zamani da za a dogara da amfani da CNG (Compressed Natural Gas) a jihar. A taron da aka gudanar a Ma’aikatar Sufuri ta Kano, Daraktan Kamfanin Stata Logistics, Chuks Nwani, ya bayyana cewa shirin zai rage cunkoson ababen hawa a titunan Kano. Majalisar Dattawa na shirin dakatar da Natasha na wata 6 An yanke wa masu fyaɗe 3 hukuncin dandanƙewa da rataya a Kaduna Hakan zai samu ne ta hanyar maye gurbin ƙananan motoci da sabbin bas-bas na zamani masu amfani da CNG. Waɗannan bas-bas za su iya ɗaukar fasinjoji da kashi 120 sama da motocin sufuri na yanzu, wanda zai samar da...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su, Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba. Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya. Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika...
Hakika, kasar Sin ta nuna bajinta a kan habakar da take samu a fagen kere-keren mutum-mutumi musamman ma a yayin bikin bazara na shekarar 2025 inda aka jero wasu mutum-mutumi 16 suka gudanar da raye-raye masu kayatarwa a wani bangare na shagulgulan jajibirin bikin. Yadda mutum-mutumin suka rika kwarkwasa da rawa da juyi ya yi matukar birge ’yan kallo na ciki da wajen kasar. Bugu da kari, a karon farko, mutum-mutumi za su shiga a dama da su a wasan gudun fanfalakin da za a gudanar cikin watan Afrilu mai zuwa a Beijing, babban birnin kasar Sin, inda ake sa ran mutum-mutumin nan da aka saka masa fasahar kirkirarriyar basira ta AI, Tian Kung wanda cibiyar bunkasa kere-keren mutum-mutumi masu...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta cafke wani matashi Safiyanu Dalhatu, mai shekara 20, kan zargin kashe mahaifiyarsa har lahira a unguwar Abujan Kwata. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya ce ’yan Kwamitin Tsaro na Unguwar ne suka kai rahoton lamarin ofishin rundunar na ‘A’ Division da ke Bauchi. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio Babu abin da zai hana mu zama jam’iyya ɗaya da Kwankwaso — Shekarau Bincike ya nuna cewar mahaifiyar matashin, Salama Abdullahi, mai shekara 40, ta samu karaya a hannayenta biyu sakamakon dukan da ya mata bayan sun samu saɓani. Bayan samun rahoto, jami’an rundunar ƙarƙashin jagorancin CSP Abdullahi Muazu, sun garzaya wajen da lamarin ya faru. Sun kai Salama Asibitin...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi, ta fara bincike kan mutuwar wata mata mai shekaru 20, Hajara Isa, wadda aka tsinci gawarta a gidan mijinta aure. Kakakin rundunar, Mohammed Ahmed Wakil, ya bayyana cewa sun samu rahoton rasuwar matar a ranar 3 ga watan Maris, 2025. Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio EFCC ta tsare tsohon Gwamnan Akwa Ibom kan almundahanar Naira biliyan 700 Sai dai ya ce ’yan uwan mamaciyar suna zargi kishiyarta da hannu a mutuwarta. Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa Muhammad, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin. Binciken farko ya kai ga kama kishiyar mamamciyar, mai suna Fatima Mohammed, mai shekaru 28. Da aka tambaye...
Ya kuma bukaci kwamitin da ke da alhakin rabon kayayyakin da su hada kai da shugabannin al’umma da na addini a yankunansu domin ganin an raba kayan abincin yadda ya kamata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tunin Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya umarci babban baturen ɗansanda a C Division da ya jagoranci tawaga ta musamman da za su gudanar da bincike kan lamarin a tsanake. A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, yunkurinsu a halin yanzu ya kai ga kama Fatima Mohammed, kishiya ga mamaciyar wacce a halin yanzu take tsare a hannunsu. “Bincike na farko ya nuna cewa, akwai zargin Fatima Mohammed na da hannu a mutuwar Hajara. A yayin da ake yi mata tambayoyi, an ce ta amince ta shaƙe ta har lahira, sannan ta yi yunƙurin ɓoye laifin ta hanyar zuba mata tafasasshen ruwa tare da ƙona jikinta da buhun da ke narkewa,” in ji CSP Wakil A...
Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba shakka Sin na matukar adawa da shi, kuma ba za ta zura ido ta rungume hannu tana ta kallo kawai ba. A wannan ranar kuwa, Sin ta mayar da martani, inda da farko ta kai kara a gaban kunigyar cinikin duniya ta WTO kan matakin da Amurka ke dauka, daga baya ta kara kakabawa Amurka harajin kwastam kan wasu kayayyakin da za...
Yayin da al’ummar Musulmai a Najeriya da duniya ke fara azumin watan Ramadan, Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta aike da sakon fatan alheri, tana kira da a yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen sabunta zukata da nuna tausayi da karfafa hadin kai a kasa. A cikin wata sanarwa da Daraktan Janar na gidauniyar, Abubakar Gambo Umar ya sanya wa hannu, ta jaddada bukatar kyautata dabi’u da wanzar da zaman lafiya da adalci a kasuwanci a lokacin azumi. Gidauniyar ta yi kira ga malaman addini da su ci gaba da yada sakonnin tsoron Allah da hakuri da kaunar juna, domin karfafa darussan Ramadan na sabunta imani da hadin kan al’umma. Hakazalika, gidauniyar ta...
Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ta bayyana cewa saɓani ne ya shiga tsakanin matashin da mahaifiyarsa, wanda ya haifar da tashin hankalin. Majiyoyi daga unguwar sun ce matashin yana shaye-shaye, kuma mahaifiyarsa ta faɗa masa ya daina, wanda hakan ne ya fusata shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bayar da umarnin gudanar da bincike, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida wa kotun cewa mutumin ya yi yunƙurin aika-aikan ne bisa zargin matarsa da kama kuruwar ɗansu da ya jima yana fama da rashin lafiya. Magidancin da ke zaune a ƙauyen Gawo da iyalin nasa ya musanta tuhumar da ake masa, don haka, Alƙali Nura Ahmad ya ba da umarnin tsare shi a gidan yari. Bidiyon batsa: Kotu ta ɗaure ’yan Tiktok a gidan yari a...

Hamas Ta Ce Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ne Kadai Za Ta Kubutar Da Fursinonin Yahudawa Daga Hannun Kungiyar
Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa, akwai alamun Natanyahu Firai ministan HKI yana son ya sake komawa yaki a Gaza. Hamdan ya ce, kafin haka gwamnatin HKI ta dakatar da aikin aiwatar da yarjeniyar da suka kulla da ita, yana son ya yi watsi da ita, sannan ya bukaci a sake tattaunawa kan sauran abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar. Jami’in na Hamas y...
Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin . Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar. Wannan har’ila yau zai kara fadin kasuwar kasashen kungiyar ta SADC. Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.
Cocin Christ Evangelical & Life Intercessory Ministry da ke yankin Sabon Tasha a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, ya raba wa makarantun Islamiyya Musulmi masu ƙaramin ƙarfi akalla 1,000 hatsi albarkacin watan Ramadan. Shugaban Cocin, Fasto Yohanna Buru, ya ce sun yi haka ne domin yauƙaƙa dangantaka da kuma wanzar da zaman lafiya a tsakanin Musulmi da makwabtansu mabiya wasu addinai a yankin. Ya ce, “muna mayar da biki ne bisa alherin da Hajiya Ramatu Tijjani, wadda ta tsaya kai da fata wajen rabon shinkafa, kuɗi, da tufafi ga marayu da zawarwan cocinmu a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara da kuma Ista.” Fasto Buru, ya ce cocin janyo irin wannan rabon abinci ga Musulmi a jihohi biyar a tsawon...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce ake wa laƙabi da Masu Gida ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Wasan wanda aka fara da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ya na daga cikin manyan wasanni masu zafi da ke ɗaukar hankalin masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Nijeriya. Kano Pillars Ta Dakatar Da Kocinta Na Tsawon Makonni Uku Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi? Rabiu Ali da Jerry Alex ne su ka jefa wa Pillars ƙwallayensu biyu a wasan, da wannan sakamakon Sai Masu Gida su ka koma matsayi na 4 akan teburin gasar Firimiyar Nijeriya. Ƙungiyar ta Kano ta dakatar da kocinta Usman...
An kaddamar da cibiyar likitancin gargajiya na Sin ta farko, ranar Juma’a a Freetown, babban birnin kasar Saliyo, wadda ta zama muhimmin mataki a yunkurin kasar na amfani da likitancin gargajiya na Sin domin amfanawa al’umma. Kadammar da cibiyar ta biyo bayan kammala wani aikin binciken kiwon lafiyar al’umma a kasar wanda likitocin kasar Sin suka jagoranta, wanda ke da nufin tallafawa kasar inganta matakan kariya da maganin cututtuka gama gari kamar hawan jinni da ciwo mai tsanin. Da yake gabatar da jawabi yayin bikin kaddamar da cibiyar, mataimakin ministan lafiya na kasar Saliyo Charles Senessie, ya yabawa dangantaka mai karfi dake tsakanin Sin da Saliyo a bangaren kiwon lafiya, musammam wajen amfani da likitancin gargajiya na Sin. Ya ce...
Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila lamba da ta dakatar da matakin da ta dauka na yunkurin halaka mutane fiye da miliyan 2, inda ta kara da cewa, bayanin Netanyahu dangane da tsawaita matakin farko wani yunkuri ne na kaucewa yarjejeniyar, da kuma kaucewa shiga tattaunawa a mataki na biyu. Tun da farko a ranar Lahadin da ta gabata, Isra’ila ta sanar da dakatar da duk...
Kungiyar Hamas ta yi kira ga masu shiga tsakani na kasa da kasa da su yi matsin lamba akan ‘yan mamaya su dakatar da azabatar da fiye da mutane miliyan daya da suke yi ta hanyar hana shigar da kayan agaji. Kungiyar ta Hamas wacce ta fitar da sanarwa a yau Lahadi ta ce, matakin da Netanyahu ya dauka na dakatar shigar da kayan agaji cikin Gaza, wata tsokana ce, kuma laifin yaki ne sannan uwa uba keta yarjejeniyar datakar da wuta da musayar fursunoni ce. Bugu da kari, kungiyar ta Hamas ta ce bukatar da Netanyahu ya gabatar na tsawaita zango na farko na yarjejeniyar, wani yunkuri ne na gujewa aiwatar da ita kanta yarjejeniyar. Haka nan kuma Hamas...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. » Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga...
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance matsalar da Falasdinawa suke...
Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru. Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu. Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya...
Hukumar abinci ta duniya ( FAO) ta sanar da cewa bisa la’akari da yadda adadin mutanen Afirka yake karuwa da kaso 2.3% a kowace shekara, hakan yana nufin cewa amfani da alkama zai karu. Bugu da kari hukumar abincin ta duniya ta ce da akwai wasu dalilan da za su sa Rashan ta kara yawan kai alkamar zuwa nahiyar Afirka da su ne fari da ake fama da shi Arewacin Afirka da kuma ambaliyar ruwan sama a yankin Sahel.
Hukumar bada lamuni ta Duniya IMF da kuma bankin duniya, manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya sun ce ba zasu bada kudade don sake gina kasar Lebanon ba, sai sun cika wasu sharudda zuwa wani lokaci. Kuma sune samar da huldar jakadanci da HKI da kuma kwance damarar kungiyar Hizbullah. Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta nakalto shugaban hukumar IMF Kristalina Georgieva ta fadawa gwamnan babban bankin kasar Lebanon na riko, Wassim Mansouri a wata haduwa da suka y ikan cewa kasarsa zata sami kudaden sake gidan kasar dag wajenta ne, tare da sharudda. Rahoton ya kara da cewa kasashen Lebanon da Siriya zasu sami kudade daga cibiyoyin biyu ne kawaii dan sun samar da dangantakar diblomasiyya da HKI. Sannan kasar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“PDP jam’iyyar siyasa ce, kuma muddin kuka ci gaba da kai mata hari, ba za ku samu ci gaba ba. Ba za ku iya daukar nauyin ‘yan baranda na siyasa da farfaganda don lalata mana kima ba don kawai burge Shugaba Bola Tinubu saboda ajandar ku ta 2027. “Ba wani dan Arewa mai hakali da zai yi wa APC yakin neman zabe a Arewa. Kasancewar wasu ’yan siyasa suna yi wa jam’iyyar shigo ba zurfi ne domin su sami abun sawa a bakin salati ne kadai amma ba wai za su zabe ta a 2027 bane. “Bai kamata Uba Sani ya bar wasu ‘yan siyasa suna yaudararsa, wadanda ba za su iya amfanar da siyarsa da komai ba. “Saboda haka,...
A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu. An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli. Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023 Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al’ummar Musulmi na yin azumi ne bisa dalilan addini kamar yadda Allah Ya yi umarni don samun lada. Sai dai daga baya binciken masana kimiyya ya gano cewa bayan lada da ake samu daga yin azumi, akwai wasu alfanu da mai azumi ke samu ga lafiyar jikin shi da suka haɗa da inganta ƙarfi da zurfin tunani zuwa fitar da gurbatattun abubuwa da jiki ba ya bukata. A taƙaice dai, ba kawai lada mai azumi ke samu ba, har da samun lafiyar jiki da na ƙwaƙwalwarsa. NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa...
An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau ranar 27 ga wannan wata cewa, kasar Sin za ta ci gaba da maida batun samun bunkasuwa a matsayin batu mafi muhimmanci a cikin ajendar kasa da kasa, da bin tunanin raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama, da zama babbar kasa mai ba da muhimmiyar gudummawa a duniya, don tabbatar da bunkasar tattalin arzikin duniya yadda ya kamata. Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin ta kiyaye sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya. A matsayin kasa ta biyu mafi ci gaban tattalin arziki a duniya, kasar Sin ta ba da gudummawar kashi 30 cikin dari ga bunkasuwar duniya, kana ita ce muhimmiyar abokiya ta...
Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa. Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka. Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba. Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa Ya ci gaba da cewa, “yanzu mun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za mu yi gwajin tashin helikwaftan farko ƙirar Najeriya.” Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa...
Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama na Afrika-AAAF. Da yake jawabi a wajen taron shugabannin sojojin saman Afrika da aka gudanar a kasar Zambiya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jadadda bukatar samar da hanyoyin warware kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar, hafsan hafsoshin ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin shiyya da dabarun hadin gwiwa wajen karfafa karfin jiragen na Afrika da kuma magance barazanar da ake fuskanta. Ya jaddada cewa, inganta hadin gwiwa tsakanin sojojin saman Afrika na da matukar muhimmanci wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke...
Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross. Fursunonin sun isa birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan ne a kan motocin kungiyar agaji ta Red Cross bayan sun tashi daga gidan yarin Ofer da ke yankin da aka mamaye. Musayar ta karkare kashi na farko na musayar da aka faro tsakanin bangarorin biyu, wanda ke gudana a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka fara aiwatarwa a watan da ya gabata da fatan kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza na tsawon watanni 15. Falasdinawan da aka sako na cikin fursunoni sama da 600, wadanda...
Ukraine ta amince da wata yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai da cinikayyar albarkatun ƙasa. Ana sa ran sanar da yarjejeniyar a hukumance a yau Laraba, inda za a ba wa kamfanonin Amurka dama su shiga harkar haƙar ma’adinai a Ukraine, ciki har da man fetur da iskar gas. Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Bisa ga bayanai, Amurka za ta samu wani kaso mai yawa daga ribar da za a samu, wanda zai iya kai wa Dala biliyan 500. Duk da cewa ba a bayyana batun tallafin tsaro a cikin yarjejeniyar ba, ministar shari’ar Ukraine, Olha Stefanishyna, ta ce akwai wasu muhimman batutuwa da...
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa. Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da aikin soji a yammacin gabar kogin Jordan. Fu Cong ya bayyana cewa, dole ne mulkin Gaza bayan yakin ya bi ka’idar “Falasdinawa su yi mulkin Falasdinu”, kuma ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga sake gina Gaza. Kana kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su kara himma wajen kira ga...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar. Ya...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da kungiyar Hamas ke yi. Bayanai sun ce za’a saki falasdinawan su 206 a cikin sa’o’I 24 masu zuwa. Dangane da dakatar da sakin fursunonin, Hamas ta zargi Isra’ila da “saka dukkan yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin hatsari mai tsanani” tare da yin kira ga kasashe masu shiga tsakani da su shiga tsakani. A nata bangaren, Hamas za ta mika wasu gawawwakin ‘yan Isra’ila hudu da...
Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren. Rasata ta bayyana hakan ne yayin halartar bikin sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tawagogin likitanci ta Sin tsakanin Sin da Madagascar. Ji Ping, jakadan Sin dake Madagascar da Randriamanantany Zelyarivelo, ministan kiwon lafiyar jama’a na Madagascar, suka sa hannu a kan yarjejeniyar. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda. Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar tasa da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene. Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers da ke kasar, inda ya fara wasa tun shekara 2022, kafin nan ya...
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa. Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna. Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance. Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira...
’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta. Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.” Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki. Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
Kungiyar Hamas ta jinjina da irin babbar gudunmawa da tsayin dakan da Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine suka yi wajen goyon bayan Palastinu, da kuma shahadar da suka yi a kan wannan tafarki. A cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da jana’izar shahidan biyu, kungiyar Hamas ta ce, muna addu’ar Allah ya jikan su da rahama, tare da mika ta’aziyyarmu ga al’ummar kasar Labanon da dukkanin al’ummar mu Larabawa da musulmi. Kungiyar ta tabbatar da cewa, laifuffukan Haramtacciyyar Kasar Isra’ila da kuma kisan gillar da ta yi wa shugabannin gwagwarmaya a Falasdinu, Labanon da sauran su, ba za su dakatar da tafarkinmu ba. Har ila yau sanarwar ta bayyana matsayin shahid Sayyid Hassan Nasrallah da jajircewarsa da...
Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. A ranar lahadi 23 ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar Hibullah, sayyid Hassan nasaralla, da kuma magajinsa na tsawon kwanaki 6 Sayyid Hashim safiyyuda deen, kafin haka shi ne shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah. An haifi sayyid Hassan nasaralla (r ) a ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1960 a wani kauye a kudancin kasar Lebanon, Sayyid ya tashi a cikin gida mai saukin rayuwa, ya fara karatu kamar yadda ko wani...

Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20
A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...