2025-03-01@20:38:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1240
«ruwan kanwa»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An shiga ruɗani bayan Tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya koma majalisar tare da rakiyar ’yan sanda. An sauke Obasa daga muƙaminsa a ranar 13 ga watan Janairu kan zargin yin amfani da ofis ɗinsa ba daidai ba. An yi wa mutane damfarar Naira biliyan 52 ta banki —NIBSS Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa An maye gurbinsa da Mojisola Meranda, wanda hakan ya haifar da rarrabuwar kai a majalisar da kuma jam’iyyar APC mai mulki a Jihar. Rahotanni sun nuna cewa an matsa wa Meranda da ta sauka daga muƙaminta, bayan da ake zargin cewa Shugaba Bola Tinubu bai gamsu da sauke Obasa daga muƙaminsa ba. A safiyar ranar Alhamis, labari ya...
Damfarar da aka yi wa mutane ta hanyar tura kuɗi ta banki ya ninku sau uku zuwa Naira biliyan 52 a Najeriya. Alƙaluma ‘n Hukumar Kula da Tsarin Tura Kuɗi Tsakanin Bankuna (NIBSS) ya nuna a shekara huɗu da suka gabata aka samu wannan karin daga Naira biliyan 11 zuwa biliyan 52, Alƙaluman sun nuna a shekara shekarar 2024 an yi asarar Naira biliyan 52, kusan ninki biyar na Naira biliyan 11,2 da aka yi asara a shekarar 2020. Rahoton na NIBSS ya bayyana cewa masu damfarar sun yi yunƙurin sace Naira biliyan 86.4 a shekarar 2024. The figure is coming on the heels of the latest GDP figures released by the National Bureau of Statistics showing a fourth...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara. Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi. Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar. Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da...
Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa. Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka. Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba. Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa Ya ci gaba da cewa, “yanzu mun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za mu yi gwajin tashin helikwaftan farko ƙirar Najeriya.” Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa...
Hukumar bunƙasa ƙere-ƙere ta ƙasa (NASENI) ta bayyana cewa an kusa kammala aikin ƙera jirgin sama mai saukar ungulu na farko da aka yi a Nijeriya, kuma nan ba da jimawa ba za a fara gwajin tashinsa. Wannan ci gaba na daga cikin yunƙurin ƙasar wajen bunƙasa fasahar masana’antu da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje. Manajan Ayyuka na Cibiyar Bunƙasa Jiragen Sama ta NASENI, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa aikin yana kan hanya, inda ake amfani da dabaru na zamani don haɗa jirgin saman mai suna “Nigerian Chopper.” Ya ce hukumar ba wai tana ƙirƙiro wata sabuwar fasaha ba ne, sai dai tana inganta shirye-shiryen da aka fara tun farko, wanda ya...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya ce idan an gan shi, sai a mika bayanan ga Dagaci, Hakimi, Mai Unguwa ko Sarki mafi kusa domin sanarda Mai Alfarma Sarkin Musulmi. Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban wata, yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga daukacin...
Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a cikin dare inda suka ƙona wuraren ibada da gidaje da makarantu da shaguna a ƙauyen Kwapre da ke yankin Sabuwar Yadul a Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Gabanin Sallar Isha’ a ranar Talata ne mayaƙan suka far wa yankin da hari, inda suka yi ta cin karensu babu babbaka. Mazauna sun bayyana cewa maharan sun ƙona wuraren ibada da makarantu da gidaje da shaguna sannan suka sace dukiyoyin jama’a. Mai unguwar kauyen Kwampre da Joel Kulaha, ya tabbatar da aukuwar lamarin, amma ya ce ba a samu asarar rai ba. NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa Dangote ya rage farashin man...
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada. An gudanar da rabon kayan ne a ɗakin ajiyar abinci na gwamnatin jihar da ke Bulasa. Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a wajen rabon, ya gode wa gidauniyar bisa tallafin da ta ke bai wa mutanen jihar. Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince...
Shugaban Hafsan Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya zama Shugaban Kungiyar Sojojin Sama na Afrika-AAAF. Da yake jawabi a wajen taron shugabannin sojojin saman Afrika da aka gudanar a kasar Zambiya, Air Marshal Hasan Abubakar, ya jadadda bukatar samar da hanyoyin warware kalubalen tsaro da kasashen Afirka ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Vice Marshal Olusola Akinboyewa, ya fitar, hafsan hafsoshin ya bayyana muhimmancin hadin gwiwa tsakanin shiyya da dabarun hadin gwiwa wajen karfafa karfin jiragen na Afrika da kuma magance barazanar da ake fuskanta. Ya jaddada cewa, inganta hadin gwiwa tsakanin sojojin saman Afrika na da matukar muhimmanci wajen tunkarar kalubalen tsaro da ke...
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta sake jaddada aniyar ta na dakile yaduwar magungunan jabun a fadin kasar nan. Darakta Janar na Hukumar Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta bayyana hakan a yayin bikin bude taron wayar da kan jama’a na kwanaki biyu da aka gudanar a Kano. Farfesa Mojisola Christianah wacce Darakta Pharmacist, Pharmacist Bitrus Fraden ta wakilta ta ce NAFDAC ta bullo da wasu sabbin tsare-tsare guda uku da nufin inganta hanyoyin magance yaduwar magungunan jabu a kasar. Babban Daraktan ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su tallafa wa wadannan tsare-tsare, da nufin tabbatar da samar da ingantattun kayayyakin kiwon lafiya, masu inganci ga ‘yan Nijeriya. Ta ce Najeriya...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da shirin horas da makarantun firamare da kananan makarantun gwamnati 50 a fadin jihar domin su iya amfani da fasahar ziyyana shafin internet. Da yake gabatar da shirin a madadin Gwamna Abdulrahman AbdulRazaq a Makarantar Sakandare ta Bishop’s Smith Junior Ilorin, babban mai ba gwamna shawara na musamman, Alhaji Sa’adu Salau, ya ce shirin na dijital ya kasance don ƙarfafa fannin ilimi. A cewarsa shirin ya shafi sama da dalibai 150 a kowace makarantu 50 na gwamnati a matakin gwaji. Ya ce idan aka kafa harsashin tsarin zamani, yaran jihar Kwara ba za su koma baya a tsakanin takwarorinsu na duniya ba.” Gwamna AbdulRazaq yace sauran makarantun gwamnati da za su...
A kokarin da take yi na magance kalubalen muhalli da inganta ayyukan sarrafa sharar gida mai dorewa, gwamnatin jihar ta hana zubar da shara a filin titin kotu. Wannan shawarar na da nufin hana yaduwar cututtuka da kuma kare lafiya da amincin mazauna da masu wucewa. A yayin ziyarar da kwamishinan muhalli da sauyin yanayi na jihar Dr. Dahiru Muhammad Hashim ya kai wurin ya bayyana damuwarsa kan illar muhalli da kiwon lafiya daga zubar da shara. Ya jaddada kudirin gwamnati na samar da ingantattun dabarun sarrafa shara don kare lafiyar jama’a da muhalli. Dokta Hashim ya ba da umarnin kwashe sharar da suka taru a yankin, sannan ya shawarci mazauna yankin da su rika zubar...
Gwamnatin Jihar Nasarawa ya hori Kiristoci masu niyyar ziyarar su zama jakadu na gari tare dayin addu’ar zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba idan sun isa can. Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana haka a lokacin bankwana da masu ziyarar su 162 da zasu tashi zuwa Isra’ila. Gwamnan ya jaddada muhimmancin da’a a yayin tafiyar tasu, inda ya bayyana cewa su dauka su Allah ya nufa da wannan ziyarar a bana. Ya kuma tabbatar wa maziyartan jihar cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen kyautata rayuwarsu, tare da samar da matsuguni da abinci kyauta a tsawon tafiyarsu. Sakataren zartarwa na hukumar jin dadin hukumar kula da masu ziyarar kiristoci ta jihar Nasarawa, Davide Ayiwa, wanda ya yabawa...
Sai dai Bukar ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa ya sanar da shugabansa kuma ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a bi masa haƙƙinsa ba. Ya ce sau da dama an buƙaci ya kawo bayanan asusun ajiyarsa na banki don duba matsalarsa, amma babu wani canji. Duk da cewa shugaban makarantar ya wanke shi daga zargin guduwa daga aiki, har yanzu ba a mayar masa da albashinsa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa da dama a daidai lokacin da kungiyar Hamas ta mika gawarwakin ‘yan Isra’ila hudu ga kungiyar agaji ta Red Cross. Fursunonin sun isa birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan ne a kan motocin kungiyar agaji ta Red Cross bayan sun tashi daga gidan yarin Ofer da ke yankin da aka mamaye. Musayar ta karkare kashi na farko na musayar da aka faro tsakanin bangarorin biyu, wanda ke gudana a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka fara aiwatarwa a watan da ya gabata da fatan kawo karshen yakin kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta yi wa Gaza na tsawon watanni 15. Falasdinawan da aka sako na cikin fursunoni sama da 600, wadanda...
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.” Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin...
Kasashen Iran da kuma Saudiyya sun tattauna kan halin da ake ciki a yankin dama batun taron kungiyar kasashen Musulmi ta OIC da za’ayi a cikin kwanaki masu zuwa a Jeddah. Tattaunawar ta wakana ne ta wayar tarho tsakanin ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan da Abass Araghchi, ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran (RII). A yayin ganawar, bangarorin biyu sun yi nazari kan halin da ake ciki a yankin, tare da tattauna taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar OIC da za a yi a Jeddah. Dama a kwanan baya bangarorin sun tattauna kan shirin shugaban Amurka Donald Trump na kwace zirin Gaza dama tilasta wa falasdinawan yankin kaura zuwa Masar da Jordan, shirin da dukkan kasashen...
Gwamnatin Donald Trump ta kawo karshen wani shirin Amurka na bunkasa samar da wutar lantarki a Afirka, wanda aka kaddamar fiye da shekaru 10, in ji Bloomberg. Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kaddamar a shekarar 2013, yana da nufin samar da wutar lantarki ga miliyoyin gidaje a nahiyar Afirka, wanda Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke tafiyar da shi. Wannan na daga cikin shirin Trump na rage kashe kudade na tarayya wanda ma’aikatar ingancin gwamnati ke jagoranta. Kusan dukkanin manufofin shirin “Power Africa” an sanya su cikin jerin shirye-shiryen da za a kawar da su. A ranar 20 ga watan Janairu, ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta dakatar da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki a Najeriya ta zama ginshiƙin rayuwa da al’umma ba sa iya rayuwa ba tare da ita ba. A duk lokacin da aka ɗauke ta al’umma kan shiga matsanancin hali. Mutane da dama sun dogara ne da wutar lantarki wajen tafiyar da harkokinsu na yau da kullum, kai har ma da na kasuwanci. A kwanakin baya ne jihohin Kaduna, Sakkwato, Zamfara da kuma Kebbi suka fuskanci ɗaukewar wutar lantarki na tsawon kwanaki, wanda ya jefa al’ummar jihohi cikin halin ni-’yasu. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce Gwamna Umar Namadi ya amince da nadin sabbin jami’an cibiyoyi 27 da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025. Babban Daraktan Hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce, an zabo sabbin jami’an cibiyar ne daga dukkan kananan hukumomin jihar 27, kuma za su samu horo da jagoranci kan ayyukan da hukumar ta dora musu. Ya kuma bayyana cewa, tuni hukumar ta gudanar ta taron bita ga dukkan jami’an shiyyar da nufin sanar da jami’an irin ci gaban da aka samu a shirye-shiryen gudanar da aikin hajji mai zuwa. Alhaji Ahmed Umar Labbo, ya bayyana jin dadinsa kan yadda...
Hukumar fansho ta jihar Jigawa da kananan hukumomin jihar ta fara biyan sama da naira miliyan 733 ga ma’aikata sama da 280 da suka yi ritaya da kuma ‘yan uwan ma’aikatan da suka rasu. Shugaban hukumar Dakta Bilyaminu Shitu Aminu ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga wadanda abin ya shafa a ofishin fansho da ke Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa kudaden sun hada da na barin aiki, da na ma’aikatan da suka mutu. A cewarsa, ma’aikatan 281 sun hada da na jiha, da kananan hukumomi da na hukumar ilimi, wadanda suka yi ritaya na son rai ko kuma sun kai shekarun ritaya ko kuma wadanda suka mutu suna aiki. Dakta Bilyaminu Shitu...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 30 da gudanar da taron harkokin mata na duniya na Beijing. Kuma kasar Sin za ta ci gaba da amfani da damar da aka samu ta cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da shirin ayyuka, da yin kokari tare da kasahen duniya wajen sa kaimi ga raya sha’anin mata na duniya. Lin Jian ya bayyana cewa, a ranar 24 ga watan Fabrairu, an gudanar da taron tattaunawa kan murnar cika shekaru 30 da zartas da sanarwar Beijing da shirin ayyuka bisa bukatun Sin da wasu kasashen da abin ya shafa, a yayin da majalisar kare hakkin dan Adam ta...
A karshe kungiyar ta bayyana cewa sansanonin za su samar da hanyoyin samun kuɗi, wanda hakan zai samar da kuɗin shiga ga jihohin da kuma walwalar maniyyata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ukraine ta amince da wata yarjejeniya da Amurka kan haƙar ma’adinai da cinikayyar albarkatun ƙasa. Ana sa ran sanar da yarjejeniyar a hukumance a yau Laraba, inda za a ba wa kamfanonin Amurka dama su shiga harkar haƙar ma’adinai a Ukraine, ciki har da man fetur da iskar gas. Dangote ya rage farashin man fetur zuwa N860 a Legas Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Bisa ga bayanai, Amurka za ta samu wani kaso mai yawa daga ribar da za a samu, wanda zai iya kai wa Dala biliyan 500. Duk da cewa ba a bayyana batun tallafin tsaro a cikin yarjejeniyar ba, ministar shari’ar Ukraine, Olha Stefanishyna, ta ce akwai wasu muhimman batutuwa da...
A yau Laraba, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina bai wa Taiwan makamai, ta kuma guji yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin Taiwan. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa kullum, lokacin da aka tambaye shi game da rahotannin da ke cewa, gwamnatin Trump ta bayar da dalar Amurka biliyan 5.3 na taimakon da kasar ke bai wa kasashen waje da aka dakile a kwanan baya, wanda ya hada da dalar Amurka miliyan 870 da aka kebe a kan sha’anin tsaro na Taiwan. A cewar Lin, Sin ta damu matuka game da ire-iren wadannan rahotanni, yana mai...
Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu. Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko. Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau. A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana...
Sojojin kasar Iran sun kammala atisayen hadin giuwa mai suna Zolfaghar 1403 a jiya Talata tare da faretin sojojin Ruwa na kasar. Atisayen ya hada sojojin sama da na ruwa ne, saboda jarraba yadda bangarorin biyu zasu yi aiki tare a lokacin yaki, duk da cewa ko wani bangare yana aiki a inda ya kore, ya ke kuma da masaniya a kansa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, sojojin zasu hada kai don tabbatar da zaman lafiya a yankin Asiya ta kudu cikin ruwa da kan tudu tare. Manya-manyan kwamandojin sojojin kasar wadanda suka hada da Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin babban kwamnadan sojojin kasar a bangaren tsare-tsare. Da kuma Manjo Janar Abdulrahim Musavi babban kwamandan...
Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim ya gana da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arigchi da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Jami’an gwomnatin 2 sun je kasar Lebanon ne don halattan taron Jana’izar manya-manyan shahidan kungiyar kuma shuwagabannin kungiyar, Shahid Sayid Hassan Nasarallah, da kuma magajinsa Sayid Hashin Safiyyuddeen. Wadanda sojojin HKI suka kashe ko suka kaisu ga shahada a shekarar da ta gabata. Labarin ya kara da cewa jakadan kasar Iran a Lebanon Mujtaba Amani ya sami halattan taron inda bangarorin suka tattauna sabbin al-amura da suke tasowa a kasar da kuma yankin kudancin Asiya da...
Kungiyar Hamas wacce take iko da Zirin Gaza ta bada sanarwan cewa an kawo karshen takaddama da HKI dangane da jinkirin da tayi wajen sakin fursinonin Falasdinawa 620 a ranar Asabar da ta gabata bayan da ta saki fursinoni yahudawa har 6. Tashar talabijin ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto kakakin kungiyar Hazem Qassem yana fadar haka a yau Laraba, ya kuma kara da cewa, gwamnatin kasar Masar ce mai shiga tsakani, kuma ta lamuncewa kungiyar kan cewa shirin musayar zai sake komawa kan yadda aka tsara shi, sannan HKI zata sake wadannan fursinoni Falasdinawa. Banda haka labarin ya kara da cewa a gobe Alhamis ma kungiyar Hamas zata mika gawakin yahudawa 4 wadanda take tsare da su a...
A ranar 25 ga wata ne zaunannen wakilin kasar Sin a majalisar dinkin duniya Fu Cong, ya bayyana a taron kwamitin sulhu na MDD game da batun Isra’ila da Falasdinu cewa, tilas ne a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza baki dayanta, don tabbatar da tsagaita wuta mai dorewa. Ya kuma yi kira ga Isra’ila da ta dakatar da aikin soji a yammacin gabar kogin Jordan. Fu Cong ya bayyana cewa, dole ne mulkin Gaza bayan yakin ya bi ka’idar “Falasdinawa su yi mulkin Falasdinu”, kuma ya kamata kasashen duniya su ba da goyon baya ga sake gina Gaza. Kana kasar Sin ta yi kira ga al’ummomin kasa da kasa da su kara himma wajen kira ga...
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci samar da sabon ginin sakatariyar jam’iyyar na kasa, ya kuma bayyana irin kokarin da jam’iyyar ke yi na kula da mambobinta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 825 kan kowace lita a Jihar Legas. Yanzu haka dai an samu ragin Naira 65, daga farashin da ake siyarwa a kan Naira 890 a baya. Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Sabon farashin zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025. Matatar ta ce wannan matakin na nufin rage wa ‘yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta, yayin da azumin watan Ramadan ke ƙaratowa, tare da tallafa wa manufofin tattalin arziƙi na Shugaba Bola Tinubu. “Rage farashin man fetur wani ɓangare ne na ƙokarinmu na sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya,” in ji matatar Dangote. “Za...

Xi Ya Jaddada Cewa Dole Ne A Dauki Sabbin Nauyi Da Sabbin Ayyuka A Sabuwar Tafiya Ta Inganta Zamanintarwa Irin Ta Kasar Sin
Kwanan nan, mamban hukumar siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, kuma sakatarorin sakatariyar hukumar, da mamban kungiyar JKS na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC, majalisar gudanarwa kuma majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC, da kuma darektan kwamitin JKS na kotun jama’a ta koli kuma hukumar gabatar da kararraki ta koli, sun ba da rahotannin tantance nasarorin aiki ga kwamitin kolin JKS da kuma babban sakatarensa Xi Jinping. Xi ya duba rahotannin kuma ya gabatar da muhimman bukatu. Yana mai jaddada cewa, shekarar bana ita ce shekarar karshe ta shirin shekaru biyar-biyar na 14, kuma muhimmiyar shekara ce ta kara zurfafa yin gyare gyare. Dole ne a mai...
Matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa Naira 825 kan kowace lita a Jihar Legas. Yanzu haka dai an samu ragin Naira 65, daga farashin da ake siyarwa a baya. Na gaji bashin 8.9bn a matsayin shugaban APC — Ganduje Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Sabon farashin zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025. Matatar ta ce wannan matakin na nufin rage wa ‘yan Najeriya wahalhalun da suke fuskanta, yayin da azumin watan Ramadan ke ƙaratowa, tare da tallafa wa manufofin tattalin arziƙi na Shugaba Bola Tinubu. “Rage farashin man fetur wani ɓangare ne na ƙokarinmu na sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya,” in ji matatar Dangote. “Za mu ci gaba da...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na...
Shirin Rumbun Saukin zai fi bayar da da muhimmanci ne kan ma’aikatan gwamnati da dattijai masu shekaru 60 zuwa sama, inda kayan abincin za su kasance a nau’ikan ma’aunai daban-daban domin a dai-daita da bukatun iyalai da samun masu cin gajiya wanda za su yi rijista ta yanar gizo ko kuma ta cibiyoyin da aka tanada domin shirin. Danja, ya ƙara da cewa burin gwamnati shi ne faɗaɗa shirin zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar, tare jaddada himmatuwar gwamnatin Katsina na ci gaba da ɗaukar nauyin shirin domin rage matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Jam’iyyar APC mai mulki, ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar daban-daban. Duk da kasancewar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima a waje taron, wasu manyan shugabannin jam’iyyar ba su halarci taron ba. Ƙungiya ta raba wa marayu da mabuƙata kayan makaranta a Kano Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Daga cikin waɗanda ba su halarci taron ba akwai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi. Dalilin Rashin Halartar Buhari Dangane da dalilin da ya sa Buhari bai samu halartar taron ba, tsohon mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
Ƙungiyar Youths for Progressive Union (YUO), ta raba wa yara marayu da masu ƙaramin ƙarfi a unguwar Kofar Mata da ke Jihar Kano, kayayyakin makaranta. Kayayyakin sun haɗa da littattafai, alƙalami, jakunkuna, da sauran kayan koyo don taimaka wa yaran da iyayensu suka rasu ko kuma ba su da ƙarfi. Shugabannin APC sun gana gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sakataren ƙungiyar, Kwamared Usman Bello Kofar Mata, ya ce sun bayar da taimakon ne, domin rage yawan yara da ke gararamba a tituna, musamman marayu. “Mun ga yadda wasu yara ke shiga tsaka mai wuya bayan rasuwar iyayensu. “Wasu ba su da kowa da zai kula da su, sai...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da sama da Naira Biliyan Biyar domin biyan diyya ga wadanda aikin gina tituna a cikin gari ya shafa. Kwamishinan yada labarai da matasa da wasanni da al’adu na jiha Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse. A cewarsa, aikin titin ya shafi garuruwa musamman Fagam, da Kila da Jugwa, da Sakuwa, da Gwaram, da Sankara, da Ringim da Bulangu, da Kafin Hausa, da Gandun Sarki, da Hadejia, da Dansure, da Roni, da Aujara, da Jahun da kuma karamar hukumar Dutse, kamar yadda ma’aikatar filaye, da gidaje, da raya birane da tsare-tsare na yanki suka gabatar. Ya...
Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma. Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Ƙungiya ta rage farashin kayan marmari saboda Azumin Ramadan A cewar bayanai daga Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (FAO), Saudiyya ita ce ƙasa ta biyu mafi girma wajen samar da dabino na duniya, inda take samar da tan miliyan 1.61 na dabino. Masar ita ce ƙasa mafi girma wajen samar da dabino, inda...
A farko-farkon da masu dauke da makamai su ka kwace iko da birnin Halab, jami’an gwganatin Turkiya sun kaucewa yin Magana akan abinda yake faruwa. Sa dai kuma da yake mai kaza a aljihu ba ya jimirin cas, ba a je ko’ina ba, su ka fara furta kalaman da suke nuni da cewa, Da kawai rina a kaba. Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Fidan, ya yi tsokaci akan abinda yake faruwa a Syria, ya zargi tsohuwar gwamnatin Syria da cewa; Ba ta yi aiki da bangarorin yarjejeniyar Astana ba.” Sojojin Turkiya suna cikinm kasar Syria tun a farkon 2018, inda suke mamaye da kaso 10% na yankin wannan kasa. Kuma aiki a tare da masu adawa da gwamnatin Damascuss,musamman rundunar...
A yayin da jam’iyyar APC mai mulki ta shirya taron kwamitin zartaswa na kasa wanda ake sa ran za ta yi ranar Laraba, jam’iyyar ta musanta rade-radin da ake yi na cewa shugaba Bola Tinubu na iya neman shugaban jam’iyyar, Dakta Abdullahi Ganduje, ya sauka daga mukaminsa. Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Ajibola Basiru, ya karyata jita-jitar a wata hira da aka yi da shi, inda ya jaddada cewa, jam’iyyar ta saba gudanar da irin wannan taron, ba wai sai don shirin zabe ba. Amurka Za Ta Illata Kanta Bisa Tsara Matakan Kayyade Samar Wa Sin Sassan Na’urorin Laturoni Na Semiconductor Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa A halin da ake ciki, tsohon gwamnan jihar...
Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba. Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa. “A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane yake: ba za mu yi shawarwari cikin matsin lamba, barazana, da takunkumi ba.” “Saboda haka,” in ji ministan harkokin wajen Iran, “babu yuwuwar yin shawarwari kai tsaye tsakaninmu da Amurka kan batun nukiliya matukar dai ana ci gaba da yin amfani da mafi girman matsin lamba a yadda take a halin yanzu.” Misra Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da...
Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da kasa. A makalar da suka rubuta a mujalar harkokin waje, shugabannin sun bayyana cewa “Zabin abu ne mai wuyar gaske: ko dai mu yi aiki tare don tilasta dokokin kasa da kasa ko kuma mu yi kasadar rugujewar sa.” Shugabannin sun kara da cewa “harin da ake kaiwa al’ummar Falasdinu ya yi daidai da ababe marasa dadi da munin tarihin da suka faru a cen baya kan kasashensu”, da suka hada da mulkin mallaka, yaki da ta’addanci da wariyar launin fata. “Muna iya fitowa daga nahiyoyi daban-daban, amma muna da tabbacin cewa rashin tsawatarwa na...
An cimma matsaya tsakanin Isra’ila da Hamas kan sakin fursunomin Falasdianwan nan 206 da Isra’ila ta jinkira, bayan da Hamas ta saki ‘yan Isra’ila shida. An dai tsara sakin fursunonin a ranar Asabar data gabata, saidai Isra’ila ta jinkirta sakin falasdinawan bisa abinda ta kira rashin gamsuwa da cin wulakanta ‘yan kasarta gabanin sakin da kungiyar Hamas ke yi. Bayanai sun ce za’a saki falasdinawan su 206 a cikin sa’o’I 24 masu zuwa. Dangane da dakatar da sakin fursunonin, Hamas ta zargi Isra’ila da “saka dukkan yarjejeniyar tsagaita wuta a cikin hatsari mai tsanani” tare da yin kira ga kasashe masu shiga tsakani da su shiga tsakani. A nata bangaren, Hamas za ta mika wasu gawawwakin ‘yan Isra’ila hudu da...
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare da dama a kan wasu sansanonin soji a kudancin kasar Siriya, ciki har da wasu yankunan da ke wajen Damascus babban birnin kasar da kuma lardin Deraa da ke kudancin kasar. Hare-haren dai ya biyo bayan kiran da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi na karbe yankin kudancin Siriya baki daya.” Jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila ta kuma bayar da rahoton cewa, Tel Aviv ta fara aiwatar da wani shiri na “shiga kudancin Syria. Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare a kudancin Syria a daren Talata, yana mai cewa harin wani bangare ne na sabuwar manufar Isra’ila ta “kawar da ayyukan soji a kudancin Syria.” A cikin...

Amurka : Kungiyar DAWN Ta Bukaci ICC Ta Binciki Biden Kan Laifin Hada Kai Da Isra’ila A Laifukan Gaza
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta DAWN mai hedkwata a birnin Washington ta yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC da ta binciki rawar da tsohon shugaban Amurka Joe Biden da wasu jami’an Amurka suka taka wajen taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A bukatar da aka mika wa mai gabatar da kara na kotun ICC Karim Khan a ranar 19 ga watan Janairu, 2025, wacce ta bayyana a ranar Litinin, kungiyar mai zaman kanta ta Democracy Now for the Arab World (DAWN) ta zargi Biden, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, da sakatarensa na tsaro, Lloyd Austin, da taimakawa Isra’ila ta aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar kungiyar mai zaman kan ta,...
Baya ga Messi shi ma Luis Suarez ya fuskanci hukunci bayan tuhumarsa da laifin dukan Birk Risa a wuya duk dai a wannan karawar tsakaninsu da New York, Messi ya koma Inter Miami daga PSG shekaru biyu da su ka gabata, tun bayan zuwanshi Miami Messi ya zura kwallaye fiye da 20 sannan ya taimaka an zura kwallaye da dama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna. Natasha ta shigar da ƙarar ne gaban Babbar Kotun Tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick. Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Ta nemi Kotun Tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta diyyar naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara. Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya yi ƙorafi kan...
Gwamnatin Tarayya ta ce ta gano irin muhimmiyar gudunmuwar da kungiyoyin hadaka ke takawa wajen bunkasa tattalin arziki da ci gaban al’umma, da kuma karfafa jama’a a kasar. Karamin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana hakan yayin kaddamar da shirin horo na musamman ga shugabanni, kwamitocin gudanarwa, da manajoji na kungiyoyin hadaka a Najeriya, wanda aka shirya a Kaduna. A cewar Kungiyar Hadaka ta Duniya (International Cooperative Alliance), sama da kashi 12% na al’ummar duniya suna cikin daya daga cikin kungiyoyin hadaka miliyan 3 a duniya. Kungiyoyin hadaka suna nada muhimmiyar gudunmuwa wajen bunkasa tattalin arziki mai dorewa, inda suke samar da ayyukan yi da damammaki ga mutane miliyan 280, wanda...
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage farashin kayan marmari kamar dankalin Turawa da karas da kukumba da latas da koren tattasai da ake fataucin su daga wasu jihohin Arewa zuwa Kudancin kasa. Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno “Za mu yi ragin ne daidai gwargwado daga cikin ribar da muke samu saboda albarkar...
Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan ya faɗo daga benen wani katafaren kanti. Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Cikin wani dogon saƙo da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin. “Muna baƙin ciki da samun labarin mutuwar Abubakar Lawal. Wannan lamari ne...
Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun yi fashi da makamin wasu kwale-kwalen kamun kifi guda takwas a hannun masunta a Doron Baga da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa ta Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a ƙauyen Kaimo da ke da tazarar kilomita huɗu daga garin Doron Baga. DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Mutum 10 sun mutu a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ‘yan ta’addan dauke da muggan makamai da ba a tabbatar da adadinsu ba, sun mamaye ƙauyen inda suka tara masuntan waje guda. Majiyar ta ce “sun iso ne da makamai, inda suka...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi alkawarin kara bunkasa huldar Iran da Rasha ta hanyar kara kaimi wajen ga yarjejeniyoyin da ke tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da mu’amala da cudanya mai ma’ana kan harkokin yankin. A yayin ganawar da ya yi da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da ke ziyara a kasar, Pezeshkian ya bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da cewa tana kara habaka, tare da jaddada bukatar gaggauta aiwatar da yarjejeniyoyin da ke tsakaninsu, musamman ma cikakkiyar yarjejeniyar hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu. Ya ce, “Iran da Rasha suna da rawar gani da za su iya takawa domin inganta hadin gwiwarsu, kuma mun kuduri aniyar karfafa huldar dake tsakanin Tehran da...
Kungiyar Hamas ta yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na sanya takunkumin hana masu ibada shiga masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta yi ishara da umarnin da ‘yan sandan Isra’ila suka bayar na ba wa masu ibada 10,000 kawai damar gudanar da sallar Juma’a a harabar masallacin Al-Aqsa, tana mai cewa matakin wani lamari ne mai matukar hadari da ke da nufin tauye ‘yancin addini. Hamas ta ce, umarnin ‘yan sandan Haramtacciyar Kasar Isra’ila cin zarafi ne ga dukkan ka’idoji, yarjejeniyoyin da kuma dokoki na kasa da kasa, sannan kuma hakan tsokana ce kai tsaye ga musulmi. Sanarwar ta kuma jaddada cewa, irin wadannan tsare-tsare ba za su...
An naɗa wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin ’yan tawayen M23 da gwamnatin Dimokuraɗiyyar Congo. Kungiyoyin raya kasashen gabashi (EAC) da kudancin nahiyar Afirka (SADC) ne suka naɗa tsoffin shugabannin Habasha da Kenya da Nijeriya domin sanya idanu a kan batun sulhu a Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo inda yaki ya kazanta a gabashin ƙasar. Shugabanin kasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi nadin a wani yunƙuri na kawo karshen yaƙin basasa a gabashin Congo, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin ’yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A bisa tafarkin addini da kuma al’ada, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi? DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su. Domin sauke shirin, latsa nan
Sakamakon binciken da kwamitin ya yi, zai tantance matakin da za a dauka na gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central. Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan. Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano. Bugu da kari, babban daraktan...
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati. Ya furta haka ne a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa ta shirya a cibiyar bunkasa ma’aikata dake Dutse. Ya jaddada cewa, gaskiya, da rikon amana, su ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari. Barista Salisu Abdu, ya...
Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun ‘yan talla da masu kananan sana’o’i. Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar. Mohammed Umar Bago wanda ya yi Allah-wadai da yadda ake karbar kudade ba bisa ka’ida ba a hannun kananan ‘yan kasuwa, ya umurci shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da su kara sa ido tare da tabbatar da ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka nan take. Ya tunatar da su cewa gwamnatin jihar Neja tana da tsarin bai daya da ya hana karbar haraji dafa masu kananan sana’o’i...
Gwamnatin jihar Jigawa ta nemi hadin kan al’umma don gina kasa bisa gaskiya da rikon amana, tare da kaucewa cin hanci da rashawa ba. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) ta shirya a Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewa, taron na da nufin wayar da kan manyan jami’an gwamnati kan ayyukan hukumar da sauran batutuwan da suka shafi hakan. “Wannan shiri yana da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da yadda gwamnati ta jajirce wajen ci gaba da inganta dukkan ka’idojin gudanar da mulki.” Gwamna Namadi ya ce, cin hanci...
Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware. Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe. Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala. Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne yayin da wata motar dakon kaya maƙare da siminti ta yi ƙundumbala ta faɗa wani rami. Wata majiya ta ce fasinjoji 13 ne a cikin motar wanda 10 daga ciki suka mutu nan take yayin da ragowar ukun suka jikkata.. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Yobe, SP Dungus...
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da biyar na kananan hukumomi ashirin da uku a matsayin doka. Shugaban Majalisar, Alhaji Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana cewa an kara kasafin kudin zuwa sama da naira biliyan dari da ashirin da uku. Yayin gabatar da kudirin a zauren majalisa don amincewa, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi da Aiwatarwa, Yunusa Shehu Pambegua, ya bayyana cewa a baya bangaren zartaswa ya mika kasafin kudi na sama da naira biliyan dari da goma sha biyar na kananan hukumomi ashirin da uku na jihar. Yunusa Shehu Pambegua ya bayyana cewa yayin kare kasafin kudinsu, shugabannin wasu kananan hukumomi...
Dalibban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura na daf da fara Jirage da Motoci Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ne ya bayyana haka lokacin da yake magana da Radio Nijeriya Kaduna a ofishinsa na Daura. Ya kara da cewa Jami’ar Sufurin da Gwamnatin Tarayya ta Samar na da manufar Samar da dalibbai masu hazaka da zasu kasance masu kirkire kirkire da manufar ganin ana yaye dalibbai da zasu dogaro da kansu dama taimakawa wajen habakar tattalin arzkin kasa. Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ya Kara da cewa baya ga ilmantar da dalibbai Jami’ar tsaye take wajen ganin sun Samar da dalibbai masu tarbiyya da zasu kasance abin alfahari cikin al’umma. Hakama Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa yanzu...
Kotun Majistire da ke zama a Sabo a unguwar Yaba ta Jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad. Mai Shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya karanta hukuncin ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad. Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo Haka nan ma kotun ta sallami Oodunni Ibrahim, wanda ake kira Primeboy da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde. Sai dai hukuncin ya ce za a gurfanar da ma’aikaciyar jinyar da ta...
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a ranar Litinin ya halarci bikin kaddamar da gina yankin masana’antu da kasar Sin ta zuba jari, inda ya bayyana shi a matsayin wani ci gaba na bunkasa masana’antu a kudancin Afirka. Kamfanin Xintai Resources na kasar Sin ne ya zuba jarin dala biliyan 3.6 a yankin masana’antu musamman na makamashi da karafa na kogin Palm da ke Beitbridge na lardin Matabeleland ta kudu, kuma za a aiwatar aikin a matakai biyar cikin shekaru 12, da nufin samar da kayayyakin da ake amfani da su na chromium da coke. Mnangagwa ya ce, “Ina fatan aikin wannan yankin masana’antu na musamman, zai taka rawa a matsayin wani muhimmin tubali ga ci gaban masana’antu da zamanantar da...
An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri. Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai lauyan masu shigar da kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’ar tare da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali. Mai shari’a Osiagor ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a, sannan ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana sayar da kwando daya na tumatir a kan Naira 3,500, yayin da ake sayar da babban kwando a kan Naira 10,000. 40% na matan Kano sun fuskaci cin zarafi a gida —Shugaban Majalisa Dan kwallon Najeriya ya mutu bayan fadowa daga bene a Uganda Wani manomin tumatir, Isah Bello Abba ya bayyana cewa, wannan yanayi ya sa manoma cikin fargaba saboda sun kashe kudade masu...
Waɗanda Suka Yi Nasara 1. Aliyu Usman Adam – Matsayi na Ɗaya Aliyu Usman Adam, ɗan asalin Zariya, Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a 2008. Bayan hidimar ƙasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014. A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TV Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu. 2. Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu Zainab Muhammad,...
Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, ya bayyana cewa mutum hudu a cikin kowane mata 10 a Jihar Kano sun fuskanci cin zarafi a gidajensu. Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa akalla kashi 35 na matan Najeriya sun fuskanci cin zarafi, lamarin da ya ce ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma. Ya bayyana wa taron wayar da kai game da illar ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma cin zarafi a cikin gidaje cewa, “abin ya fi muni a yankin Arewa maso Yamma, inda a Jihar Kano matan da ake cin zarafinsu a cikin gidajensu sun kai kashi 40 cikin 100.” Game da yawa masu ta’mmali da miyagun kwayoyi kuwa, Shugaban Majalisar Wakilan, wanda dan yankin ne, ya bayyana cewa an...
Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba. Kafafen watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na baya, kafin barkewar yaki, kuma kungiyar ta koyi darussa daga yaki da sojan kasa na Isra’ila a baya.” Jaridar “Badiot Ahranot” wacce ta dauki labarin ta kuma ce; Har yanzu Hamas ba ta fito da dukkanin mayakanta a filin daga ba, da adadinsu ya kai 30,000, kuma tana ba su albashi ta hanyar kudaden harajin da take karba. Wani sashen na bayanin kafafen watsa labarun...
Shugaban kungiyar ‘al-Hikimah” na kasar Iraki Ammar Hakim ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi. A yayin ganawar Ammar Hakim ya jaddada muhimmancin taimaka wa kokarin da Masar take yi na ganin an hana korar falasdinawa daga yankunansu zuwa wajen Falasdinu. Ammar Hakim ya kuma ce, a yayin wannan ganawar na bayyana wa shugaban kasar jinjinawarmu akan yadda Masar ta kasance mai taimaka wa Falasdinawa.” Haka nan kuma mun nuna goyon bayanmu ga kokarin Masar al’umma da gwamnati na hana tilasatawa Falasdinawa yin hijira da kuma kare hakkokin Falasdinawa da riko da kasarsu. Har ila yau Ammar Hakim ya ce ganawar tasu ta tabo batutuwa da su ka shafi halin da ake ciki a wannan yankin da kuma wajabcin...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta ce za ta fara gudanar da bincike kan kocin Fenerbahce Jose Mourinho bayan da ta zarge shi da furta kalaman wariyar launin fata bayan da ƙungiyoyin suka tashi 0-0 ranar Litinin. Zuwa yanzu dai ba a bayyana irin kalaman da Galatasaray ke nufin Mourinho da furtawa ba, da yake magana a taron manema labarai bayan kammala wasan derby na Istanbul, Mourinho ya ce kujerar da ya zauna a filin wasan Galatasaray ba ta zama kurum, ta na tsalle kamar biri idan aka zauna kanta, ya kuma sake nanata sukarsa ga alƙalan wasan Turkiyya, yana mai cewa da an tafka babban kuskure idan akayi amfani da wani alkalin wasan ƙasar a wasan. An Dakatar Da...
Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda. Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar tasa da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene. Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers da ke kasar, inda ya fara wasa tun shekara 2022, kafin nan ya...
Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya. A yayin jawabin da ya yi a ranar Litinin, a babban taro na 2025 kan kwance damara, a hedkwatar MDD dake Geneva, Mr. Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da MDD da su ba da fifiko kan batun kawar da makaman nukiliya. Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa “dole ne kasashen duniya su tilastawa Isra’ila bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi (NPT) don kawar...
Fiye da mutane 7,000 da yawancinsu fararen hula ne aka kashe a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango tun daga watan Janairu, in ji Firaminista Judith Suminwa Tuluka a ranar Litinin. Mambobin kungiyar M23 da ke samun goyon bayan kasar Rwanda sun kwace iko da yankunan gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo masu arzikin ma’adinai da suka hada da manyan biranen Goma da Bukavu da ke gabashin kasar. Firayim Minista Judith Suminwa Tuluka ta yi gargadin cewa, halin da ake ciki na tsaro a gabashin DRC ya kai matsayi mai daukar hankali, yayin da take jawabi ga kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva. Ta ce mutanen da suka mutu sun hada da “fiye da gawarwaki 2,500 da aka binne...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da Amurka ta zartas kan rikicin Rasha/Ukrain duk kuwa da kauracewar kasashen Turai kwamitin ya kada kuri’ar amincewa da kudurin na Amurka da nufin kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru uku ana yi tsakanin Ukraine da Rasha. Kuri’u 10 ne suka amince da kudurin, sabili da haka babu wanda ya ki, ko da yake kasashen Turai biyar a majalisar – Denmark, Faransa, Girka, Birtaniya da Slovenia – sun zabi su kauracewa zaben. Wannan kudurin dai ya tuna da muhimmin kudurin MDD na wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya, tare da yin kira da a warware takaddama cikin lumana da samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin kasashen...
Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa. Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna. Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance. Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira...
’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta. Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?...
nkin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...
Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata zargin da tsohon abokinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2031. A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa. A yayin hirar da aka yi da shi a cikin dare a kafar Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa sun raba jiha da tsohon abokin nasa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Sanata Uba Sani, yanzu duk ba abokansa ba ne. Amma martaninsa, a cikin sakon da ya fitar jim kaɗan...
Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe ba. Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa, daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga tabbatar da hakkin dan Adam a duniya shi ne amfani da matakan tilastawa kasashe. Ya kara da cewa wadannan matakan suna da illa ga fararen hula kuma ba adalci ne ba ga marasa galihu kamar mata, yara, tsofaffi da masu nakasa. Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya bayyana jin dadinsa a wannan...
Gwamnatin Trump ta saka sabbin takunkumai kan wasu mutane da ke da alaka da wani kamfanin fitar da mai na Iran. Takunkuman sun shafi mutane 22 da jiragen ruwa 13 da ke da alaka da masana’antar mai ta Iran. Wadannan takunkumin wani bangare ne na matsin lamba na shugaban Amurka Donald Trump kan Iran. Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta sanar da cewa, takunkumin na da nufin gurgunta harkokin hada-hadar kudi da kuma cinikin man fetur na Iran, da nufin takaita shirinta na nukiliya. Iran dai na mai kakkausar suka kan takunkuman na Amurka, tana mai kallonsu a matsayin sabawa ka’idojin kasa da kasa.
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya bayanna cewa, Turawa za su iya shiga cikin shirin warware rikicin Ukraine, yayin da kungiyar EU ke fargabar cewa za a mayar da ita saniyar ware tun bayan fara tattaunawar kai tsaye tsakanin Moscow da Washington. “Turawa, amma har da sauran kasashe, suna da hakki kuma suna da damar shiga, Kuma zamu mutunta hakan, ”in ji Vladimir Putin a wata hira da aka yi da shi ta talabijin. Ya nanata cewa kasashen Turai ne suka yanke alaka da Rasha bayan da ta fara kai hari kan Ukraine shekaru uku da suka gabata, Don haka “Shigowarsu a cikin tsarin tattaunawar ya zama dole. Vladimir Putin ya dage kan cewa tattaunawar da Rasha da Amurka suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ko kun san sunan dabinon da kuka fi so ku ci a lokacin shan ruwa? Dan Agadas ne, ko Ruwa-Ruwa, ko Annakhiyl? NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi A yayin da ake shirye-shiryen tarbar watan Ramadana, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nau’ukan dabino da alfanunsa ga dan Adam, musamman mai azumi. Domin sauke shirin, latsa nan
Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.” Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki. Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji...
Ya kuma zargi NSA da nuna sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa a 2031, don haka yake kokarin kawar da duk wanda zai zamar masa kalubale a kan hanyarsa. Cikakken bayani na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda ya samu wakilcin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya ce shirin samar da tallafin a mazabu zai kara inganta manufofi 12 na gwamnatin jihar wadanda suka hada da karfafawa al’umma don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a kowane mataki. Ya yi fatan wannan karimcin zai yi kyakkyawan tasiri ga mutane 1,200 da suka ci gajiyar tallafin. A jawabinsa, dan majalisa...
Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a. A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna. Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina A yayin da mu’amala tsakanin jinsi ɗaya ta halasta a wasu yankunan ƙasar mafi rinjayen musulmi a duniya, sai ɗabi’ar ta haramta a lardin Aceh da aka ayyana dokokin shari’ar Musulunci. Tun a watan Nuwamban bara ne dai ’yan sanda masu ɗabbaka shari’a suka kama mazajen biyu da ke karatu a wata jami’a suna aikata wannan alfasha a wani...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp