2025-03-25@03:25:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 507

«a Falasdinawa»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Kungiyar kwamishinonin kudi ta kasa ta jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Jigawa na bunkasa Ilmin ya’ya mata. Shugaban kungiyar kuma kwamishinan kudi na jihar Ekiti, Mr Akim Oyebode ya bayyana hakan a lokacin da suka ziyarci Gwamna Umar Namadi a gidan gwamnati dake Dutse. Mr Akim Oyebode ya ce kungiyar tana alfahari da ayyukan raya kasa da Gwamna Umar Namadi ya aiwatar tun hawansa karagar mulki, a sassan jihar ta Jigawan. Yana mai cewar sun ziyarci jihar Jigawa ne domin yi wa Gwamnan ta’aziyyar rashin da aka masa. A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya yaba musu bisa wannan ziyara tare da fatan za su koma jihohinsu lafiya.   Usman Mohammed Zaria
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane  300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
    Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa. Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin daga lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, kamar yadda ƙungiyar Halo Trust ta ruwaito. Jami’an tsaron White Helmets na Syria sun bayyana wa BBC cewa yawancin waɗanda suka rasu manoma ne da suka fara komawa gonakinsu. Hassan Talfah, wanda yake jagorantar sashen tsince bama-bamai a arewa maso yammacin ƙasar, ya ce nau’in UXO waɗanda ba a ƙarƙashin ƙasa suke ba,...
    Majalisar dokokin jihar Jigawa ta jaddada aniyar ta na hada kai da ofishin kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF domin samun nasarar aiwatar da tsare-tsare da za su inganta rayuwar yara da marasa galihu a jihar.   Mataimakin kakakin majalisar, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya bada wannan tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin tawagar ofishin UNICEF na Kano karkashin jagorancin Hajiya Fatima Adamu.   Ya lura cewa irin wannan haɗin gwiwa tsakanin majalisa, Action Against Hunger da Save the Children International sun haifar da sakamako mai kyau ta hanyar tallafawa matakan majalisa ta hanyar fasaha da ba da shawara don tsara manufofin da sauran tsare-tsaren a Jigawa.   Alhaji Sani Isyaku Abubakar ya bada tabbacin ci gaba...
    Falasdinawa sun gudanar da wata gagarumar liyafar tarbar fursunonin Falasdinawa 114 a Ramallah da aka sako daga gidan yarin ‘Yan sahayoniyya Daruruwan jama’a a birnin Ramallah da ke gabar yammacin kogin Jordan sun gudanar bikin tarbar fursunoni 114 da aka sako daga gidan yarin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a wani bangare na biyu na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya, yayin da wasu fursunoni 16 daga cikinsu suka isa birnin Zirin Gaza. Jama’ar garin Ramallah sun dauki fursunonin da aka sako a kafadarsu a matsayin alamar nasara. Fursunonin sun bayyana godiyarsu ga ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa kan jajurcewar da suka yi a Gaza, kuma har ta kai ga kulla yarjejeniyar musayar. A yayin bikin,...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.