2025-04-19@17:10:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 373
«shugaban kasar Rasha»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga/Billiri a Jihar Gombe, Ali Isa JC, ya raba wa Musulmai da Kiristoci 2,000 kayan abinci don rage wahalar Azumin watan Ramadan da na Kiristoci. Ali JC ya bayyana cewa wannan tallafi yana da muhimmanci don sauƙaƙa wa jama’a gudanar da ibadarsu cikin sauƙi. An samu tsohon shugaban hukumar tsaron Faransa da zamba WHO za ta bai wa Nijeriya magungunan cutar kuturta “Buƙatar kayan abinci tana ƙaruwar a irin wannan lokaci, kuma muna ƙoƙarin taimaka wa mutanen mazaɓarmu su samu sauƙin rayuwa,” in ji shi. Baya ga kayan abinci, ya kuma raba babura 10 da babura masu kafa uku guda 20 domin tallafa wa mutane 200 a Jihar Gombe, inda kashi 50 cikin 100 aka...
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar da fara atisayen sojan ruwa na hadin gwiwa da kasashen Rasha da Iran, wanda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa a kusa da tashar ruwa ta Chabahar ta kasar Iran. Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa, kasashen Sin, Rasha da Iran sun fara atisayen jiragen ruwa na hadin gwiwa daga tashar ruwan Chabahar ta Iran ne domin karfafa hadin gwiwa na tsaro tsakanin wadannan kasashe guda uku. Kwanaki biyu da suka gabata, Beijing ta mayar da martani ga kalaman sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth na cewa kasarsa a shirye take domin shiga kowane irin yaki, kuma idan muna son dakile Sinawa ko wasu, dole ne...
Sunana Zainab Zeey Ilyas Jihar Kaduna: Muhimmancin sadaka na da yawa baya ga kariya da take yi, sadaka tana hana bambancin da ake yi tsakanin mai kudi da kuma talaka, sadaka tana hada kan al’umma musulmi guri daya, tana taimakawa marayu, masu takaba da manya wadanda suka manyanta wajen nuna musu cewar suma suna da gata, tana kuma kusanto mutum da Allah ta’alla. Wadanda ya kamata a bawa sadaka; Marayu, iyalai masu karamin karfi, masu takaba, ‘yan gudun hijra, dalibai da sauransu. Hanyoyin bada sadaka na da dumbin yawa kamar; bada sadaka ta hanyar bada kudi, yinta ta hanyar dauke abu daga kan hanya wanda zai cutar da dan’Adam, hada kungiya ko kirkirar kungiya ko bada gudunmawa a kungiyar...

Binciken Jin Ra’ayin Jama’a Da CGTN Ta Gudanar Ya Shaida Gamsuwar Al’ummun Duniya Da Salon Diflomasiyyar Sin
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu kwararru a fannin na aikin noman, sun alakanta samun wannan karuwar, saboda dauki daban-daban da gwamnatin tarayya ta samar ga fannin, musamman wajen kokarinta na rage kalubalen rashin tsaro. Daga cikin wannan daukin na gwamnati, sun hada da kirkiro da shirin jami’an tsaro na sintiri sama da 1,000 da aka tura zuwa kanannan hukumomi 19 a 2024, don bai wa manoma da amfanin noma da aka shuka kariya, inda shirin ya taimaka wajen kara bunkasa aikin noma. A cewar Hukumar ta ‘NBS’, fannin aikin noma ya samar da kashi 25.59 wajen habaka fannin tattalin arzikin kasar, wato ma’ana, a zango na uku na 2023, gudunmawar da fannin ya samar ga tattalin arzikin kasar, ya tsaya ne a kashi 26.11,...
Sojojin Isra’ila sun kai farmaki kan wasu masallatai a birnin Nablus da ke gabar yammacin kogin Jordan a ranar Juma’a ta farko ta watan Ramadan. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, a safiyar ranar Juma’a sojojin gwamnatin Isra’ila sun kutsa kai cikin wasu masallatai shida na birnin Nablus, inda suka hana gudanar da salla. Har ila yau, sun kame wasu Falasdinawa uku a lokacin da suke kutsawa cikin Nablus. Rahotanni sun ce sojojin na Isra’ila sun harba harsasai masu rai, da gurneti da bama-bamai masu guba a yayin da dakarunsu suka mamaye wasu unguwanni a birnin. Ko a ranar Alhamis din da ta gabata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ci...
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, ta rufe wani shagon da ake yin caca na zamani, wanda aka fi sani da “betting. Mataimakin kwamandan hukumar a Kano, Sheikh Mujahideen Aminudeen, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Kano. Kotu ta yanke wa dillalan ƙwayoyi hukuncin ɗaurin shekaru 95 Kisan malami: Shugabannin Kiristocin Kudancin Kaduna sun yi Allah-wadai Ya ce sun ɗauki wannan mataki ne bisa dokokin Jihar Kano, kuma hukumar ta kai samame wajen kafin ta rufe shagon gaba ɗaya. Aminudeen ya nuna damuwa kan yadda wasu Musulmai ke shiga harkar caca, musamman a lokacin azumin watan Ramadan. A watannin baya hukumar ta haramta yin cacar “betting” lamarin da ya sanya ta fara farautar wuraren...
“NNPC na amfani da kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje domin yin gogayya da matatar Dangote, a maimakon ta dukufa amfani da matatunta na mai da suke cikin kasar nan. Wannan lamarin na shafan dorewar musayar kasuwanci kuma zai kara janyo damuwowi ne kawai ga tattalin arzikin kasar nan,” Iledare ya shaida. Wani masanin makamashi kuma shugaban NES, Farfesa Adeola Adenikinju, ya ce akwai bukatar hukumomi su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da wadatar mai da kuma saukinsa a kasuwanni. Ya kuma lura da cewa akwai bukatar magance dakile gasar rashin adalci domin a samu yin ciniki sosai a tsakanin masu mai. Mataimakin shugaban IPMAN, Hammed Fashola, ya nuna farin ciki da rage farashin litar...
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, shugabannin Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatissunnah, musamman Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, da duk al’ummar Musulmi gaba ɗaya. Daga ƙarshe, ya yi addu’a ga Allah da ya gafarta wa marigayin, ya kuma saka masa da Aljannatul Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu alkaluma da suka fito daga Babban Bankin Nijeriya CBN sun suna cewa, a 2024, Asusun ajiyar Nijeriya rufe ne a kan Dala biliyan 40.877. Wani masani a fannin tattalin arziki da ke da zama a jihar Legas Ibukun Omoyeni, a wani hasashe da ya yi kan shekarar 2025 ya bayyana cewa, Nijeriya ta fuskanci wasu bin ka’dojin yarjejeniyar karbar bashi, inda ya kara da cewa, baya ga batun kafin a shiga shekarar 2026, akwai wasu basussuka na waje Nijeriya ta ciwo wandanda kuma, ba su riga sun gama nuna ba, wanda akalla zai iya kai wa Dala biliyan 1.33 a duk shekara ko kuma sama da haka wadanda suka hada da biyan kudin ruwa na rancen, inda mai yuwa,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da iyalin su al’ada. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shin ko mene ne matsayin buɗa-baki tare da iyali a watan Ramadana? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da...
Don haka, Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida saboda saba ka’idojinta na majalisar dattawa. Bugu da kari, majalisar ta bukaci Natasha da ta maido da duk wani abu mallakin majalisar ga mai kula da Majalisar har sai lokacin dakatarwar ya cika. Sanata Imasuen ya bayyana cewa, “A madadin kwamitin majalisar dattawa kan da’a, gata, da kuma sauraron kararrakin jama’a, muna godiya ga shugaban kasa da manyan abokan aikinmu bisa damar da aka ba mu na yi wa ‘yan Nijeriya hidima ta hanyar wannan kwamiti. Mun gabatar da shawarwarinmu cikin girmamawa don tantancewa da amincewa. Na gode.” Bayan doguwar muhawara kan rahoton da kwamitin ya gabatar, Sanatocin sun amince da dukkan shawarwarin...
Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
Jami’ai a Ukraine sun ce mutane huɗu sun mutu, 29 da suka jikkata, a wani harin makami mai Linzami da Rasha ta kai kan wani Otel a birnin Kryvyi Rih – Mahaifar shugaba Zelensky. Masu aikin ceto na ƙoƙarin zaƙulo masu sauran numfashi a ɓaraguzan gine-gine. Wannan hari na zuwa ne sa’o’i bayan Amurka ta tabbatar da cewa ta daina musayar bayanan sirri da Ukraine — wanda haka zai kasance ƙalubale matuƙa ga Ukraine wajen iya daƙile hare-haren Rasha. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce masu aikin sa kai daga wata ƙungiyar bayar da agaji daga Amurka da Birtaniya na daga cikin waɗanda harin ya rutsa da su a daren jiya. Hakazalika, an kai wasu hare-haren...
Yayin da watan Ramadan ya shiga kwana na 6, masu lura da al’amura da dama na kokawa kan tsadar kayan marmari a Kano, wanda suke ganin wani muhimmin bangare ne na karin kumallo da ake yi a sahur da kuma lokacin buda baki. Malam Bello Ibrahim da Abdulmajeed Baba, masu amfani da ’ya’yan itatuwa musamman a lokacin azumin Ramadan, a wata tattaunawa da suka yi da gidan rediyon Najeriya, sun bayyana rashin jin dadinsu da tashin gwauron zabi. ‘Ya’yan itatuwa na da matukar muhimmanci ga lafiyar mu a lokacin azumi, amma farashin na kara zama wanda ba zai iya jurewa ba,” in ji su. Malam Ado Shehu, jami’in hulda da jama’a na kasuwar ‘ya’yan itacen Naibawa,...
An yi kira ga al’ummar musulmi da su kara yawan ruwa da ‘ya’yan itatuwa a lokacin azumin watan Ramadan domin inganta sinadaran jiki. Wani kwararre a fannin lafiya a Jami’ar Ilorin, Farfesa AbdulRahman Afolabi ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin, jihar Kwara. Ya ce a lokacin azumi da ake tsananin zafi a hankali ruwan jiki yana raguwa. A cewarsa karuwar cin ‘ya’yan itatuwa daban-daban zai yi matukar amfani ga musulmi mai azumi. Farfesa Afolabi ya bayyana cewa a lokacin azumin watan Ramadan musulmi sun kaurace wa abinci da abin sha, tare da hana jikinsu cin abinci da suka saba. Ya ba da shawarar a kara amfani...
Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta ga gwamna Inuwa Yahaya kan rabon kayan abinci da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar a matsayin tallafin azumin watan Ramadan. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar Abdulkadir Ahmad ya fitar a Gombe. Jam’iyyar ta caccaki gwamnatin jihar kan rashin amincewa da rawar da gwamnatin tarayya ta taka, wanda hakan ya sanya ake yaudarar jama’a wajen ganin cewa tallafin na jiha ne kawai. Jam’iyyar adawa ta ba da shawarar cewa yin shiru ya sa ayar tambaya game da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da kayayyakin agaji. Ta kuma yi zargin cewa sukar da Gwamnan ya yi a...
Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe. Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya raba kayayyakin agaji na watan Ramadan na sama da Naira miliyan 200 ga al’ummar mazabarsa. Ya yi hakan ne da nufin tallafa wa al’umma domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, duba da halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki. A wajen bikin kaddamar da rabon, Yusuf Dahiru Liman, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Bashir Adamu Nababa, ya jaddada aniyarsa ta rage wahalhalun da al’ummar mazabarsa ke fuskanta. Ya bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani bangare na alkawarin da ya dauka na inganta walwalar jama’a a yayin yakin neman zabe. Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki, Isiyaku Adamu Nababa, ya jaddada cewa shirin ya...
Dubban Falasdinawa ne suka halarci masallacin al-aksa a cikin kwanakin Ramadan da suka wace. Inda yawansu yake kaiwa kimani 80,000. Mafi yawansu matasa ne wanda suke sallar asham da isha’I wannan duk tare da bincike mai tsananin da HKI take yi a kan hanyoyin shigar masallacin. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, halartan Falasdinawa sallah a masallacin a cikin wannan watan mai al-farma yana raya al-amuran addini a cikinsa, duk tare da gwamnatin yahudawan suna sanya shingaye masu yawa don hana Falasdinawa raya masallacin. Sheikh Ikramah Sabri limamin masallacin ya na kwadaitar da Falasdinawan kan halattar sallah a masallzacin don raya shi. Banda matsayin masallacin a addinin musulunci dai, haduwar falasdinawa a masallacin alamace ta hadin...
Gwamna Umar Namadi ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar Jigawa a wannan lokaci na azumin watan Ramadan na shekarar 2025. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri ya sanyawa hannu, aka kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse. “Ma’aikatan jihar za su je aiki karfe 9 na safe sannan su tashi da karfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis maimakon zuwa karfe 5 da ake kai wa a baya, sai ranar Juma’a ma’aikatan za su je aiki da karfe 9 na safe su tashi da karfe 1 na rana kamar yadda aka saba”. Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, an yi wannan karimci ne da nufin samarwa ma’aikatan...
Kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto a jiya Talata cewa, shugaba Vladmir Putin ya amince da zama mai shiga tsakanin Iran da Amurka. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amanci cewa, kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto majiyar fadar mulkin kasar “Kremlin” na cewa shugaba Vladmir Putin zai zama mai shiga tsakanin Iran din da Amurka. Haka nan kuma kafafen watsa labarun na Rasha sun ce; Rasha da Amurka sun amince su yi wata tattaunawa ta daban akan Iran”. Mataimakin shugaban kasar Rasha ya ambaci cewa, a yayin zaman da kasashen biyu su ka yi a Riyadh na Saudiyya, sun tattauna akan abinda yake da alaka da Iran. Majiyar ta kuma ce abinda kasashen biyu suke son yin Magana...
A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce: ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa kuma...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis. Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin. Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da...
Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu. “Farawa daga yanzu, ma’aikatan gwamnati a jihar za su rika fara aiki da karfe 9:00 na safe kuma su tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis, raguwar awanni biyu daga tsohon lokacin rufewa na karfe 5:00 na yamma. A ranakun Juma’a kuwa, ma’aikata za su fara aiki da karfe 9:00 na safe su kuma tashi da karfe 1:00 na rana, kamar yadda aka saba.” A...
A cewar ‘yansandan Ukraine, hare-haren Rasha sun raunata mutane a yankin Donetsk, sannan a ƙaramar hukumar Kherson, mutum biyar sun mutu, yayin da 13 suka jikkata, ciki har da ‘yansanda da suka je ɗauko gawar wani mutum. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku a bikin “Kharazmi” na shekara-shekara karo na 83. Shugaban wannan shirin na samar da maganin Farajallah Mehna zadeh ya fada wa kamfanin dillancin labarun Fars cewa; Daya daga cikin magungunan shi ne “Topiramate”, sai dai an sami sabon salo na yin magani wanda zubin sanadarorin da ake hada shi ya banbanta da na baya.” Farajallah Mehna Zadeh ya kuma ci gaba da cewa: Mun fara...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) za ta gudanar da taron shekara-shekara daga ranar 4 zuwa ta 10 ga Maris a nan birnin Beijing, a cewar wani kakaki a yau Litinin. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da shirin ciyarwa a watan Ramadan na shekarar 2025 a hukumance, da nufin samar da abincin buda baki ga mabukata 91,000 a fadin jihar. Shirin wanda zai dauki tsawon kwanaki 27 yana daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi na tallafawa dimbin al’ummarta a watan na Ramadan. Mataimakin gwamnan jihar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda kuma shi ne shugaban shirin, ya kaddamar da shirin a hukumance a cibiyar Dandali dake karamar hukumar Fagge. Ya nuna jin dadinsa da yadda aka gudanar da shirin cikin kwanciyar hankali, tare da yin kira ga kamfanonin da abin ya shafa da su tabbatar da isar da abinci cikin lokaci da inganci a dukkanin cibiyoyin ciyar da abincin. Za...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari. Hakan wani muhimmin mataki ne na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa. A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya ya ce, gwamnan ya bayyana cewa, aikin da ake amfani da shi ta hanyar amfani da hasken rana da kuma amfani da dabarun noman rani, yana yana taimakawa wajen yin noma a kowane lokaci na shekara tare da bunkasa tattalin arzikin manoma. A cewarsa, shirin mai fadin hekta 10 wanda aka samar da rijiyoyin burtsatse na zamani guda hudu do tallafa wa kananan manoma...
Babban sakataren dakarun Asa’ibu Ahlul Hakki na kasar Iraki ya karyata zancen cewa za’a kwance damarar dakarun Hashdu sha’abi na kasar ta Iraki Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Qais Al-Khaz’ali ya na karyata wannan labarin, ya kuma bayyana haka ne a wani shiri a tashar talabijin ta Al-Irakiyya na kasar ta Iraki a jiya Lahadi. Al-Khaz’ali ya kara da cewa makaman da suke karkashin kula na Hashdu sha’abi suna karkashin kula mai kyau, don haka babu tsaron cewa za’a yi amfani da su a inda bai dace ba. Ya kuma kara da cewa, tsarin tsaro na kasar ta Iraki yana da matukar muhimmanci garemu. Sannan ya kammala da cewa kwance damarar dakarun Hashdu Ashabi zagon kasa...
Masu fasahar gina jiragen sama a kasar Iran sun samar da wani sinadari wanda ake kira ‘Smart Magnesium’ wanda ake iya rage nauyin jiragin sama da shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto masu binciken na cewa sun samar da wani sinadari wanda baya sanya ‘magnesium Alloy’ a jikin jiragen sama tsatsa, kuma idan an rufe jikin jirgi da shi zai rage nauyinsa. Banda haka zai kyautata yanda jirage zasu sarrafa makamashin jirgin. Rahoton ya kara da cewa wannan kirkirar ya na da muhimmanci a kamfanonin kera jiragen sama, da kuma samar da injuna, saboda zai kara dadewar jikin jiragen sama, kafin yayi tsatsa. Har’ila yau ya kuma taimaka wajen rage nauyin jikin jirgin. Banda haka sabon...
Archbishop Okoh ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da bin hanyoyin doka domin shawo kan lamarin. Ya ce CAN ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an samar da daidaito a tsarin ilimi, ba tare da nuna bambancin addini ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan Ramadan, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin mai cike da falala, tausayi, da zaman lafiya. A sakon da MDD ta fitar ta hannunsa, Guterres ya ce, “Ramadan lokaci ne da ke karantar da kyawawan ɗabi’u na tausayawa, taimakekeniya, karamci, da mutunta juna. Wannan wata dama ce ta ƙara hada kai, sada zumunta, da gina al’umma mai cike da zaman lafiya.” Ya kuma jaddada muhimmancin tunawa da waɗanda suke cikin hali na ƙunci, musamman ’yan gudun hijira da waɗanda ke fama da rikice-rikice a wurare kamar Gaza, Sudan, da yankunan Sahel. Guterres ya bayyana damuwarsa kan halin da suke ciki, yana mai cewa, “Ina tare...
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Wannan ta’addanci ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba. Gwamna Nasir Idris ya bayar da tabbacin inganta a tsaro jihar. Ganin yadda mutane ke cikin tsoro, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar jaje ƙauyukan a ranar Asabar. Ya tabbatarwa da al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin shawo kan matsalar tsaro, musamman...
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Wannan ta’addanci ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba. Gwamna Nasir Idris ya bayar da tabbacin inganta a tsaro jihar. Ganin yadda mutane ke cikin tsoro, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar jaje ƙauyukan a ranar Asabar. Ya tabbatarwa da al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin shawo kan matsalar tsaro, musamman...
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA, ta yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci na watan Ramadan wajen tunanin abubuwan da za su amfani kasa baki daya. Kodinetan hukumar na jihar Jigawa Mallam Ahmed Tijjani Ibrahim ya yi wannan kiran a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Malam Ahmed Tijjani ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi addu’ar zaman lafiya, da tsaro da ci gaban jihar da kasa baki daya. Ya bayyana watan Ramadan a matsayin wata mai alfarma da ake son musulmi su kara kusanta ga Allah SWT, ta hanyar tsarkake zukatansu. Don haka Tijjani ya umarce su da su zama ’yan...
Bisa labarin da shafin intanet na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC ya fitar, za a gudanar da taron manema labarai na taro na uku na NPC karo na 14, a zauren taron manema labarai na babban dakin taron jama’a, da karfe 12 na safiyar ranar 4 ga watan Maris, inda mai magana da yawun taron zai amsa tambayoyi daga ‘yan jaridun kasar Sin da na kasashen waje kan batutuwan da suka shafi ajandar taron da kuma ayyukan NPC. Shafin ya kuma bayyana cewa, ana maraba da ‘yan jaridun kasar Sin da na kasashen waje su halarci taron na manema labarai. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su. Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da...
Hukumar Hisba ta Jihar Kano, ta kama wasu matasa da ba su yi azumi a ranar farko ta watan Ramadan ba. Mataimakin Kwamanda Janar na Hukumar, Dokta Mujahideen Abubakar ne, ya tabbatar da kama matasan. Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi Hakazalika, ya tabbatar da cewa jami’an Hisba sun cafke su yayin sintiri da suka yi a sassa daban-daban na Kano. Har ila yau, hukumar ta kama wasu matasa ku san 60 bisa laifin askin banza, wanda ta ce ya saɓa wa dokokin addini da al’ada. Bugu da ƙari, an kama wasu direbobin Adaidaita Sahu da ake zargi da cakuɗa maza da mata a cikin abin hawa, abin da hukumar...
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga kowa. Ina taya mu murnar zuwan watan Ramadan mai alfarma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga kowa. Ina taya mu murnar zuwan watan Ramadan mai alfarma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan harkokin wajen kasar Ali Muhammad Umar ya bayyana cewa; Somaliya za ta iya rattaba hannu akan takardun fahimtar juna da za su bai wa Habasha izinin amfani da tashar ruwa da take a gabar tekun Indiya daga nan zuwa watan Yuni. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai Fira ministan kasar Habasha Abi Ahmed ya kai ziyara zuwa kasar Somaliya inda ya gana da shugaban kasar Hassan Sheikh Mahmud, kuma bangarorin biyu su ka tattauna hanyoyin bunkasa alaka a tsakanin kasashensu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha Nebiat Gatachewa ya ce; kokarin da ake yi na bunkasa alaka a tsakanin Addis Ababa da Magadishu ya haifar da da, mai ido musamman a siyasance da kuma ta hanyar...
Bismillahir Rahmanir Rahim Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya isar da komai. Tsira da amincin Allah su tabbata bisa ga Annabi (S.A.W) da kuma bayinsa zababbu. Bayan haka. Wannan wani dan takaitaccen sako ne nake so na isar da shi ga ’yan uwa Musulmi, na ciro hujjojinta daga littafin Allah (S.W.T) da kuma sunnar Manzo (S.A.W) da kuma zantukan maluma magabata da magada. Sai na ambaci sunan littafin: “RAMADANIYYA” Ina ba da kyauta ga kowane Musulmi da Musulma wato mai Azumi, maza da mata. Ina rokon Allah Ya sanya shi a cikin mizanin kyawawan ayyukanmu a ranar saduwa da Shi da Aljannar ni’ima. Allah Ya sa haka. Ina rokon duk wanda ya ga wadansu kurakurai ya aikomin don...
Wani jami’in ya ce yarjejejeniyar za ta ba da dama ga Zelenskyy da Trump su tattauna batun ci gaba da bayar da tallafin soji ga Ukraine, dalilin da ya sa Kyib ke son kammala yarjejeniyar. Trump ya kwatanta wannan matsaya da aka cimma a matsayin “babbar yarjejeniyar,” wacce za ta kai ta tiriliyan na daloli. A wani labarin kuma, Kasar Ukraine ta bayyana cewar hare-haren da Rasha ta kai wa garuruwan dake kusa da filin daga a gabashin kasar sun hallaka akalla mutum 5 tare da raunata wasu 8 ‘yan sa’o’i bayan wani mummunana harin jirgi mara matuki kusa da birnin Kyib. Gagarumin ruwan wutar da jiragen saman Rasha marasa matuka suka kai cikin dare sun hallaka mutum 2 a...
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza. Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. » Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. » Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga...
Sunana Aisha T. Bello daga Jihar Kaduna: Rashi ramadan basket nasa a kore saurayi saboda ‘yan mata sun maida ramadan basket dole. Shawara ta ga al’ummar musulmi duniya shi ne; mu yi amfani da wannan dama gun rokon Allah, saboda in Allah ya nuna mana wanan mu gani ba lallai bane mu ga wani watan Ramadan din ba, kuma mu sa kasar mu cikin addu’a Allah ya bamu dacewa. Sunana Abubakar Ahmad, daga Jihar Nassarawa: Ga me hali ya kan shiryawa gajiyayyu marasa hali, wanda kuma Allah bai hore masa ba ya shiga sahun wanda sai dai a dauka a basu su wadannan ba sa shirya komai face yawan salloli da addu’o’i da neman taimakon ubangiji Allah ya fitar...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan. Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan. “Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar. “Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.” Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar...
Daga cikin Kasashen da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan. A nan Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai...
Ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Jihar Kano, ya bai wa jihar da wasu jihohin Arewa kyautar dabino katan 1,250, a matsayin wani ɓangare na shirin tallafin Ramadan na kowace shekara. Wannan shiri na cikin ayyukan jin-ƙai da Cibiyar Sarki Salman (KSrelief), ke gudanarwa don tallafa wa masu buƙata da kuma ƙarfafa dangantakar Saudiyya da Najeriya. Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn Yayin bikin rabon dabinon, Jakadan Saudiyya a Kano, Khalil Admawy, ya gode wa Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima Mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da tallafa wa al’ummar Musulmi a faɗin duniya. Ya jaddada aniyar Saudiyya na ci gaba da...
Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027. Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasar. Kazalika, ya yaba wa Shugaban Kwamtin kan gundunmawar da ya bayar wajen gainin an samar da wadannan ayyuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Saɓanin shekarun baya, azumin watan Ramadan na bana ya zo a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa farashin kayan abinci na sauka a sassan Najeriya. Kayayyakin masarufi irinsu shinkafa da wake da fulawa na daga cikin waɗanda aka fi sarrafawa a watan na Ramadan, kuma su ne masu gwaggwaɓan kaso a faɗuwar farashin. Farashin kayan masarufi na sauka a wannan karo ne baya kimanin shekara biyu a jere suna tashi a ƙasar. Haka kuma, ana iya cewa ’yan Najeriya sun saba ganin tashin farashin kaya, musamman na abinci, a gabnin watan Ramadan. Duk da mutane suna nuna jin daɗinsu da saukar farashin a wannan karon, amma wasu na cewa hakan bai kawo sauƙi ga talaka ba, a wannan lokaci...
Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka. 2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata. 3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya....
Azumin watan Ramadan na daga cikin shika-shikan Musulunci, kuma Allah ne Ya wajabta shi a kan bayinsa. Wannan wata yana da falala da lada mai yawa, domin Allah Ya keɓe shi da girma da ɗaukaka. Ga wasu daga cikin falalar azumin watan Ramadan: 1. Ana buɗe kofofin Aljanna, ana rufe ƙofofin wuta, kuma ana ɗaure shaiɗanu. Wannan yana taimaka wa zuciyar Musulmi wajen yin alheri da kauce wa munanan ayyuka. 2. Yin azumi da tsayuwar sallar Tarawihi saboda Allah da neman lada, ana gafarta zunuban bawa da suka gabata. 3. Akwai daren Lailatul-Kadari, wanda ya fi wata dubu daraja. Duk wanda ya yi ibada a wannan dare yana mai imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya....
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC), ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki. Ana zargin cewa Mohammed, ya sayar wa wani kamfani mai suna Mahasum filin. An ga watan Ramadan a Najeriya An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya An gano cewar an tura kuɗin filin Naira miliyan 100 a asusun banki na shugaban. Mai magana da yawun ƙaramar hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kama Mohammed. Ya tabbatar da cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025, a asusunsa. Sai dai hukumar ta ce ta karɓo kuɗaɗen haba ɗaya....
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin ranar Juma’a, wanda hakan ke nufin ranar Asabar, 1 ga watan Maris, ita ce daya ga watan Ramadan 1446 Hijira a Najeriya. A cikin wata sanarwa da Sarkin Musulmi, ya karanta a fadarsa, ya bayyana cewa an samu sahihan bayanai daga kwamitocin ganin wata da shugabannin addinin Musulunci a sassa daban-daban na kasar nan. An ga watan Ramadan a Najeriya —Sarkin Musulmi Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara a dalilin haka, ya ayyana fara azumin watan Ramadan daga safiyar Asabar. Haka nan, hukumomin Saudiyya ma sun tabbatar da ganin watan, inda suka ayyana Asabar a matsayin daya ga...
Fadar mai alfarma sarkin Musulmi, ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen Juma’ar nan a Sakkwato. Cikin wata sanarwa da Mai Alfarma Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban. Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446. Nasiru Malami/Sakkwato
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Sergei Shoigu, sakataren majalisar tsaro ta kasar Rasha, a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, Sin da Rasha sun kasance masu tuntubar juna a dukkan matakai, da aiwatar da matsayar da suka cimma da shugaba Putin da hadin gwiwa mai muhimmanci da moriyar juna tare da zurfafa hadin gwiwarsu a kai a kai, domin taimakawa muradunsu na bai daya na samun ci gaba da farfado da kasashen biyu. Ya kara da cewa, ya kamata kasashen 2 su karfafa hadin kai a harkokin da suka shafi yanki da ma duniya, su kuma goyi bayan rawar da kasashen BRICS da kungiyar hadin kai ta Shanghai suke takawa, tare da...
Hukumomi a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin yau Juma’a. Hakan na nuni da cewa azumin bana zai fara a ranar Asabar, 1 ga watan Maris, 2025. Shafin Haramain Sharifain ne, ya tabbatar da wannan sanarwa, yayin da aka ga jinjirin watan a wurare daban-daban na ƙasar. Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano Wannan na nufin cewa Musulmai a Saudiyya za su fara azumi a ranar Asabar. Hakazalika, ƙasashen Qatar da Oman sun sanar da cewa za su fara azumin Ramadan a wannan ranar Asabar. A yayin da ake shirin shiga wannan wata mai alfarma, an yi kira ga Musulmai...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma Babban Sakataren Tsare-Tsare, Salisu Mustapha, kan badaƙalar zaftare albashin ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba. An umarci Mustapha da ya sauka daga muƙaminsa na Babban Sakataren Tsare-Tsare a Ofishin Shugaban Ma’aikata domin ba da damar gudanar da bincike. A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura Gwamna Abba ya amince da naɗa Malam Umar Muhammad Jalo, Muƙaddashin Babban Sakataren REPA, a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan jihar har zuwa lokacin da za a kammala binciken lamarin. Matakin gwamna ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da dama da ma’aikatan gwamnati suka yi kan rage albashi ba bisa...
Shugaban Rasha Vladimir Putin da Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo sun tattauna a fadar Kremlin, yayin da ‘yan adawar Guinea-Bissau suka sha alwashin gurgunta kasar gabanin zabe. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, sun yi shawarwari a fadar Kremlin, a wani sabon salo na yunkurin da Moscow ke yi na kulla huldar tattalin arziki da tsaro da kasashen yammacin da tsakiyar Afirka. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya habarta cewa, hamshakin attajirin nan na Rasha Oleg Deripaska ya halarci tattaunawar da shugabannin biyu suka yi. Kafofin yada labarai sun ambato wani minista a Guinea-Bissau, ya ce, Kamfanin aluminium na Rasha Rusal yana sha’awar gina layin dogo da tashar jiragen ruwa a kasar, da kuma...
Sama da litattafai 73,000 na koyarwa da kayan wasanni, gwamnatin jihar Kwara ta raba wa daliban makarantun firamare da kananan sakandare a fadin jihar. Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da yake jawabi a wajen taron raba kayayyakin a Ilorin, ya ce sauran kayayyakin da za a raba sun hada da dakunan karatu na firamare 12,780; guda 100 na kayan ilimi na musamman; 260 na Kula da Yara da sauransu. Gwamna AbdulRazaq wanda ya samu wakilcin kwamishiniyar ilimi da ci gaban jama’a ta jihar, Hajiya Sa’adatu Modibbo Kawu, ta ce wannan wani shiri ne a cikin jerin shirye-shiryen da gwamnatin ke yi wanda ke nuni da fifikon da take da shi na samar da ilimin boko a jihar. A cewarsa...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Lin Jian ne ya jaddada cewa, alakar da take a tsakanin Rasha da China ba ta tasirantuwa da shiga tsakanin wani bangare na uku, sannan kuma ya ce, kokarin da Amurka take yi na haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu ba zai yi nasara ba. A wani taron manema labaru da kakakin ma’aikatar harkokin wajen na China ya gabatar, ya bayar da jawabi akan tambayar da aka yi masa akan maganar da ta fito daga bakin ministan harkokin wajen Amurka Marco Robio cewa; Rasha ta dogara ne China, kuma kasashen biyu za su iya hada kai su yi fada da Amurka. Li Jian ya kuma ce; Ba tare da la’akari da sauye-sauyen da za su...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025. Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara. Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi. Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar. Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da...
Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Saad Abubakar ya yi kira ga al’ummar Musulmin kasar nan da su fara neman ganin jinjirin watan RAMADAN a gobe Juma’a 28 ga watan Fabrairu 2025, daidai da kalandar Musulunci 29 ga watan Sha’aban1446AH. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addinin musulunci na jihar Sokoto, Farfesa Sambo Wali Junaidu, Wazirin Sokoto ya ce idan an gan shi, sai a mika bayanan ga Dagaci, Hakimi, Mai Unguwa ko Sarki mafi kusa domin sanarda Mai Alfarma Sarkin Musulmi. Sanarwar ta ci gaba da cewa, duban wata, yana fayyace kalandar Musulunci a cikin shekara guda, wanda hakan ya sa ganin watan Ramadan ya fi karbuwa ga daukacin...
Gidauniyar Sarki Salman ta Saudi Arabiya ta bayar da tallafin kayan abinci ga marasa ƙarfi 2,450 a Jihar Kebbi ta hannun hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA). An gudanar da rabon ne a Birnin Kebbi, inda aka raba buhuhunan shinkafa da wake mai nauyin kilo 25, garin masara kilo 2, da man gyada. An gudanar da rabon kayan ne a ɗakin ajiyar abinci na gwamnatin jihar da ke Bulasa. Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris a wajen rabon, ya gode wa gidauniyar bisa tallafin da ta ke bai wa mutanen jihar. Amurka Da Rasha Sun Kammala Tattaunawar Kawo Ƙarshen Yakin Yukiren A Ƙasar Saudiyya Hajjin 2025: Kamfanin Saudiyya Ya Amince...
Masar ta yi watsi da shawarar da jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya gabatar na cewa Alkahira, maimakon kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta karbi ragamar zirin Gaza na wucin gadi, tana mai danganta irin wadannan tsare-tsare da cewa “ba za a amince da su ba.” Kamfanin dillancin labarai na MENA ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen Masar Tamim Khalaf yana cewa, “Duk wani ra’ayi ko shawarwari da suka saba wa matsayar Masar da Larabawa (a kan Gaza) an yi watsi da su kuma ba za a amince da su ba.” Kakakin ya nanata kiran da Masar ta yi na janyewar Isra’ila daga yankunan Falasdinawa da ta mamaye, da kuma goyon bayanta ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin...
Jami’an diblomasiyyar kasashen Rasha da Amurka zasu sake haduwa a gobe Alhamis 27 ga watan Fabarayru a birnin Istambul na kasar Turkiyya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yana fadar haka a kasar Qatar, ya kuma kara da cewa a haduwarsu na gobe kasashen biyu zasu maida hankali ne wajen sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a kasashensu. Ministan ya kara da cewa, dangantaka tsakanin Rasha da Amurka bai taba yin kyau ba tun lokacin tarayyar Soviet, amma ta dan kyautata a lokacin shugabancin Trump na farko. Sannan bayan sake dawowan Trump da alamun dangantakar zata yi kyau. A gobe Alhamis dai bangarorin biyu zasu dubu abubuwan da suke hana...
Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwa Masu Hada-hadar Kayan Marmari a Jihar Oyo, Walin Ibadan, Alhaji Dauda Shehu ya ce, kungiyar za ta rage farashin kayan marmari domin samun sauƙi ga al’ummar Musulmi a cikin watan Azumin Ramadan. Ya ce, “kamar yadda muka saba yi a baya a irin wannan lokaci, a bana ma za mu rage farashin kayan marmari kamar dankalin Turawa da karas da kukumba da latas da koren tattasai da ake fataucin su daga wasu jihohin Arewa zuwa Kudancin kasa. Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar ɗan wasan Nijeriya a Uganda Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno “Za mu yi ragin ne daidai gwargwado daga cikin ribar da muke samu saboda albarkar...
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati. Ya furta haka ne a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa ta shirya a cibiyar bunkasa ma’aikata dake Dutse. Ya jaddada cewa, gaskiya, da rikon amana, su ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari. Barista Salisu Abdu, ya...
Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware. Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yau Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Sergey Lavrov wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran. Bangarorin biyu dai sun tattauna akan batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma na kasa da kasa. Bugu da kari bangaroin biyu sun tattauna akan alakar kasashen biyu da hanyoyin bunkasa ta.

Gwamnatin Iraki Ta Kokawa Sabuwar Gwamnatin Siriya Dangane Da Barazanar Mayakan Daesh Da Suka Rage A Kasar
Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza a jiya Lahadi. Ya kara da...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...
dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka: Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta. Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi. Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya....
Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo. Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai. A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani...
Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai fam miliyan (£300m) a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa sannan ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe sama da fam biliyan biyu (£2bn), ko kuma a yi wa tsohon filin wasa na Old Trafford kwaskwarima da zai ci Fam biliyan 1.5. Manchester United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai Fam miliyan 113.2 daga ranar 30 ga watan Yunin 2024 kuma kawo yanzu kungiyar tana mataki na 15 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24. Amma kuma har yanzu kungiyar tana buga gasar cin...
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza. Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman,...
Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun kungiyar Rapid Support Forces, wadanda a halin yanzu mayakan ‘yan tawayen suke fama da karancin kayayyakin aiki. Sojojin Sudan sun kai farmaki kan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke kusa da gadar Soba, wadda ta hada kudancin Khartoum da gabashin Nilu a kan hanyar kogin Blue Nile, inda suka kwace iko da sansanonin dakarun ‘yan tawayen. A yayin da Dakarun kai...
Mutane 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Neja
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...

Kungiyar Hizbullah Ta Lebanon Ta Jaddada Rashin Amincewarta Da Mika Kan Kasar Ga Amurka Da Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da barazanar kai hari kan filin jirgin saman Lebanon da sauran muhimman wuraren kasar ba. Sheikh Damoush ya jaddada a cikin hudubarsa ta Juma’a cewa “ya zama wajibi gwamnati ta magance matsalar jiragen Iran zuwa kasar Lebanon, domin wannan batu na farko da na karshe yana da alaka ne da ‘yancin kai da kuma martabar kasar Lebanon, kuma hakan na nuni da kwace ‘yancin matakin da...
Kwamatin lura da kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa ya kaddamar da rangadi na yini biyu a karamar hukumar Jahun, domin tantance kwazon karamar hukumar ta fuskar gudanar da ayyukan raya kasa da sha’anin mulki da kashe kudade. Shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Gwiwa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce ziyarar na daga cikin ayyukan majalisa da suka hada da duba kasafin kudi da yin doka da kuma tantance abubuwan da gwamnati ta ke gudanarwa kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. Ya ce a lokacin wannan ziyara, kwamatin zai tantance kundin bayanan ayyukan raya kasa da rahoton zangon shekara da bayanan tarukan kwamatin tsaro da na gudanarwa. Ya ce kwanitin zai kuma tantance bayanan ayyukan majalisar kansiloli da kuma alkaluman...

Tashar Jiragen Sama Ta Rafikul Hariri Int. Na Birnin Beirut Yana Ciki Da Masu Shiga Kasar Saboda Jana’izar Shaheed Nasarallah
Tashar jiragen sama ta birnin Beirut tana cike da masu shiga kasar daga kasashen daban-daban don halattar jana’izar Shahidai kuma shuwagabannin kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah da kuma Magajinsa Shahid Sayyid Hashimi Safiyyuddeen wanda za’a gudanar a ranar 23 ga watan Fabarairu da muke ciki. Kamfanin tafiye-tafiye na “Ajuz Travillin Agency’ ya fadawa tashar talabijin ta Almanar kan cewa tun yawan jiragen sama masu zuwa daga kasashen waje suka nin nink tafiye-tafiyensu zuwa Beiru, daga cikinsu, akwai Iraq Air wanda yake zuwa Beiru har sau biyu. Amma daga yau ya kara shi zuwa har sau ukku. Kamama Egypt Air ya ninka zuwasa Beirut har sai yu. Da kuma Tarksih Air shi ya ninninka ta fiyasa zuwa kasar. Labarin ya kara...

Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata. Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki...
Jami’an diblomasiyya da dama daga kasashen kungiyar G20 ne suka isa birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu, don halattar taro na kwanaki biyu. Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya isa birnin Johannesburg a jiya Alhamis kwanaki biyu kacal da ya gana da tokwaransa na kasar Amurka a birnin Riyad na kasar Saudiya. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ yace ana saran kasashen turai zasu kara jaddada goyon bayansu ga kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da kasar Rasha. Duk tare da cewa gwamnatin kasar Amurka tana son kawo karshen yakin ba tare da su ba. Kasashen Burtaniya , Faransa, Jamus da kuma tarayyar Turai EU gaba daya suna goyon bayan Ukraine a yakinta da Rasha....
Ta ƙara da cewa wannan shiri yana nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hulɗa kai-tsaye da jama’a. Za a fara jerin tarukan ne da gabatarwar Ministan Raya Kiwo, Mukhtar Maiha; da Ministan Cigaban Yankuna, Injiniya Abubakar Momoh. Ma’aikatar ta gayyaci ‘yan jarida, masu ruwa da tsaki, da jama’a gaba ɗaya don halartar wannan muhimmiyar tattaunawa da nufin bayyana wa jama’a irin cigaban da gwamnati ke samu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky da “mai mulkin kama karya,” yana mai bukatarsa da ya gaggauta daukar matakin tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Rasha ko kuma ya yi kasadar rasa kasarsa. Trump ya yi wadannan kalamai ne, kwana guda bayan da ya zargi Ukraine da haddasa yakin Rasha, yana mai cewa hakan ya janyo Washington cikin rikicin na shekaru uku. An shirya wa’adin shekaru biyar na Zelensky zai kare a watan Mayun 2024, amma saboda dokar soja da aka kafa a watan Fabrairun 2022, ba za a iya gudanar da zabe ba. Kalaman na Trump sun jawo martani cikin gaggawa daga jami’an Ukraine, inda ministan harkokin wajen kasar Andrii Sybiha ya jaddada cewa...
A karshe dai, ya nanata muhimancin raya karfin kasa da kasa ta hanyar aiwatar da ayyuka masu alaka da hakan. Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana fatan yin hadin gwiwa da sassa daban daban, domin bude sabon babin raya huldar cude-ni-in-cude-ka, tare da kafa tsarin gudanar da harkokin kasa da kasa mai inganci. Bayan taron, ya kuma amsa tambayoyin ‘yan jaridu, game da yadda kwamitin sulhu na MDD zai karfafa kwarewarsa ta gudanar da ayyuka, da matsayin kasar Sin kan batun Gaza da dai sauransu. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki. Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau. Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki. Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kan zanga-zangar yunwa, ya gano cewa mutum 10 sun rasa rayukansu, yayin da wasu mutum bakwai suka samu munanan raunuka. Rahoton ya kuma bayyana cewa an yi asarar dukiya da ta kai Naira biliyan 11, sakamakon ƙone-ƙone, sace-sace, da lalata kadarorin gwamnati da na ’yan kasuwa a faɗin jihar. Mutum 11 sun kuɓuta daga hannun Boko Haram a Borno USAID: Amurka za ta yi bincike kan ɗaukar nauyin Boko Haram Da yake jawabi a taron majalisar zartaswar ta jihar karo na 25 a ranar Talata, Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi rahoton daga shugaban hannun kwamitin, Mai shari’a Lawan Wada (ritaya). Ya tabbatar da cewa za a fitar...
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na gaba na musayar fursunoni. Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya...