2025-02-26@01:40:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1301

«ga kasar Sin»:

    An gudanar da taron dandalin ciniki tsakanin Sin da Habasha kana taron sa kaimi ga dandalin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na kasa da kasa wato CISCE karo na 3 a jiya Litinin a Addis Ababa, hedkwatar kasar Habasha. Kwamitin sa kaimi ga cinikin Sin da ketare da kwamiti mai kula da harkar zuba jari na Habasha da kungiyar kasuwanci da kungiyar sana’o’in Habasha sun gudanar da taro mai taken “Shiga Habasha: Habaka hadin gwiwar tsarin samar da kayayyaki tsakanin Sin da Afirka” cikin hadin kai. Inda wakilai fiye da 200 daga bangarorin gwamnatoci da ciniki da tattalin arziki da kafofin yada labarai da sauransu suka halarci taron. Jakadan Sin dake Habasha Chen Hai ya gabatar da wani jawabi,...
    Biyo bayan umarnin da hukumar kula da aikin hajji ta kasa ta bayar, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta kara wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau yayin taron bita ga  ma’aikata da jami’an Alhazai na kananan hukumomi a Otal din Grand Central. Alhaji Danbappa ya bayyana cewa za a ci gaba da karbar kudaden  maniyyata har zuwa ranar daya ga watan Ramadan. Ya kuma bayyana cewa, ya zuwa yau 25 ga watan Fabrairun 2025, hukumar ta bada sama da naira biliyan 22 ga hukumar alhazai ta kasa a madadin Alhazan jihar Kano. Bugu da kari, babban daraktan...
    Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci  hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba. Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati. Ya furta haka ne a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa ta shirya a cibiyar bunkasa ma’aikata dake Dutse. Ya jaddada cewa, gaskiya, da  rikon amana, su ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari. Barista Salisu Abdu, ya...
    Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa  masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun  ‘yan talla da masu kananan sana’o’i. Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar. Mohammed Umar Bago wanda ya yi Allah-wadai da  yadda ake karbar kudade ba bisa ka’ida ba a hannun kananan ‘yan kasuwa, ya umurci shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da su kara sa ido tare da  tabbatar da ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka nan take. Ya tunatar da su cewa gwamnatin jihar Neja tana da tsarin bai daya da ya hana karbar haraji dafa masu kananan sana’o’i...
    Ministar harkokin wajen Madagascar Rasata Rafaravavitafika ta bayyana a Tananarive, hedkwatar kasar jiya Litinin cewa, ana godiya ga Sin da ta dade take tura tawagogin likitanci zuwa kasar cikin shekaru 50 da suka gabata, don ba da tallafin jinya na zamani a yankuna masu nisa na Madagascar, da ceton rayuka na miliyoyin mutane dake wuraren. Rasata ta bayyana hakan ne yayin halartar bikin sa hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar tawagogin likitanci ta Sin tsakanin Sin da Madagascar. Ji Ping, jakadan Sin dake Madagascar da Randriamanantany Zelyarivelo, ministan kiwon lafiyar jama’a na Madagascar, suka sa hannu a kan yarjejeniyar. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Bisa labarin da aka bayar, an ce, gwamnatin Trump ta kasar Amurka tana tsara wasu tsauraran matakan kayyade samar wa kasar Sin sassan na’urorin hada laturoni na semiconductor, da kara matsin lamba ga kasashen kawacenta, tare da bukatarsu da su tsaurara dabaibayi a kan sha’anin samar da fasahar matattarar bayanai ta microchip ga kasar Sin. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya yi nuni a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau 25 ga wannan wata cewa, kasar Sin ta riga ta sanar da matsayinta ga kasar Amurka kan batun kayyade samar da sassan na’urorin laturoni na semiconductor ga kasar Sin sau da dama. Ya ce, Amurka ta siyasantar da batun tattalin arziki da cinikayya da...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta nemi  hadin kan al’umma don gina kasa bisa gaskiya da rikon amana, tare da kaucewa cin hanci da rashawa ba. Gwamna Umar Namadi ya yi wannan kiran a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) ta shirya a Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewa, taron na da nufin wayar da kan manyan jami’an gwamnati kan ayyukan hukumar da sauran batutuwan da suka shafi hakan. “Wannan shiri yana da matukar muhimmanci idan aka yi la’akari da yadda gwamnati ta jajirce wajen ci gaba da inganta dukkan ka’idojin gudanar da mulki.” Gwamna Namadi ya ce, cin hanci...
    Har ila yau, kwamishinan ma’aikatar Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda ya bukaci iyaye da daliban makarantun da su tabbatar sun koma makaranta a ranar da aka ware.   Ya yi gargadin cewa, za a dau matakin ladabtarwa a kan Daliban da suka gaza bin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An tabbatar da mutuwar mutum 10 a sakamakon wani haɗari da ya auku a  babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri a Jihar Yobe. Haɗarin wanda ya jikkata mutum uku ya auku ne shingen binciken ababen hawa da jami’an tsaro suka kafa a daidai garin Warsala. Babu hannun Naira Marley a mutuwar Mohbad — Kotu Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS Bayanai sun ce haɗarin ya auku ne yayin da wata motar dakon kaya maƙare da siminti ta yi ƙundumbala ta faɗa wani rami. Wata majiya ta ce fasinjoji 13 ne a cikin motar wanda 10 daga ciki suka mutu nan take yayin da ragowar ukun suka jikkata.. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Yobe, SP Dungus...
      Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da kudirin kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da biyar na kananan hukumomi ashirin da uku a matsayin doka.   Shugaban Majalisar, Alhaji Yusuf Dahiru Liman, wanda ya jagoranci zaman, ya bayyana cewa an kara kasafin kudin zuwa sama da naira biliyan dari da ashirin da uku.   Yayin gabatar da kudirin a zauren majalisa don amincewa, Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi da Aiwatarwa, Yunusa Shehu Pambegua, ya bayyana cewa a baya bangaren zartaswa ya mika kasafin kudi na sama da naira biliyan dari da goma sha biyar na kananan hukumomi ashirin da uku na jihar.     Yunusa Shehu Pambegua ya bayyana cewa yayin kare kasafin kudinsu, shugabannin wasu kananan hukumomi...
    Dalibban Jami’ar Sufuri ta Gwamnatin Tarayya dake Daura na daf da fara Jirage da Motoci Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ne ya bayyana haka lokacin da yake magana da Radio Nijeriya Kaduna a ofishinsa na Daura. Ya kara da cewa Jami’ar Sufurin da Gwamnatin Tarayya ta Samar na da manufar Samar da dalibbai masu hazaka da zasu kasance masu kirkire kirkire da manufar ganin ana yaye dalibbai da zasu dogaro da kansu dama taimakawa wajen habakar tattalin arzkin kasa. Shugaban Jami’ar Farfesa Umar Adam Katsayal ya Kara da cewa baya ga ilmantar da dalibbai Jami’ar tsaye take wajen ganin sun Samar da dalibbai masu tarbiyya da zasu kasance abin alfahari cikin al’umma. Hakama Shugaban Jami’ar ya bayyana cewa yanzu...
    Kotun Majistire da ke zama a Sabo a unguwar Yaba ta Jihar Legas ta wanke mawaƙi Abdulazeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley da abokin aikinsa Samson Balogun Eletu, wato Sam Larry daga zargin hannu a mutuwar mawaƙi Aloba Oladimeji IleriOluwa, wanda aka fi sani da Mohbad. Mai Shari’a Ejiro Kubenje, wanda ya karanta hukuncin ya ce babu wata ayar tambaya kan mutanen biyu game da rasuwar Mohbad. Tattalin arzikin Nijeriya ya haɓaka da kashi 3.84 — NBS An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo Haka nan ma kotun ta sallami Oodunni Ibrahim, wanda ake kira Primeboy da tsohon manajan Mohbad, Opere Babatunde. Sai dai hukuncin ya ce za a gurfanar da ma’aikaciyar jinyar da ta...
    Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a ranar Litinin ya halarci bikin kaddamar da gina yankin masana’antu da kasar Sin ta zuba jari, inda ya bayyana shi a matsayin wani ci gaba na bunkasa masana’antu a kudancin Afirka. Kamfanin Xintai Resources na kasar Sin ne ya zuba jarin dala biliyan 3.6 a yankin masana’antu musamman na makamashi da karafa na kogin Palm da ke Beitbridge na lardin Matabeleland ta kudu, kuma za a aiwatar aikin a matakai biyar cikin shekaru 12, da nufin samar da kayayyakin da ake amfani da su na chromium da coke. Mnangagwa ya ce, “Ina fatan aikin wannan yankin masana’antu na musamman, zai taka rawa a matsayin wani muhimmin tubali ga ci gaban masana’antu da zamanantar da...
    An gurfanar da wadanda ake zargin ne bisa laifuka daban-daban, da ke da alaka da laifukan zamba ta yanar gizo, mallakar wasu takardu da ke dauke da shaidar karya, da kuma satar bayanan sirri.   Dukkansu sun ki amsa laifin da ake tuhumar su da su a lokacin da aka karanta musu tuhumar, sai dai lauyan masu shigar da kara, Nnaemeka Omewa, ya bukaci kotun da ta dage zaman shari’ar tare da tsare wadanda ake kara a gidan gyaran hali.   Mai shari’a Osiagor ya dage sauraron karar zuwa ranar 23 ga watan Yunin 2025 domin ci gaba da shari’a, sannan ya bayar da umarnin a tsare su a gidan gyaran hali. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024. A cewar rahoton da hukumar NBS ta fitar a yau Talata, bunƙasar ta ɗara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024. An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi Alƙaluman game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma ɗara kaso 3.46 cikin 100 da aka ba da rahoton samu a zango na 4 na 2023. “Ɓangaren ayyuka ne kan gaba a bunƙasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya ƙaru da kaso 5.37 cikin 100 tare da ba da gudunmawar...
    Waɗanda Suka Yi Nasara 1. Aliyu Usman Adam – Matsayi na Ɗaya Aliyu Usman Adam, ɗan asalin Zariya, Jihar Kaduna, an haife shi a shekarar 1984. Ya kammala karatunsa na firamare da sakandare a Zariya, sannan ya samu digiri a harshen Hausa daga Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a 2008. Bayan hidimar ƙasa a Jihar Edo, ya yi aiki a kamfanin SAN Yoghurt da kuma Alhuda Center School daga 2011 zuwa 2014. A 2014, Aliyu ya koma aikin jarida, inda ya yi aiki da jaridar RARIYA a Abuja har zuwa 2017. A halin yanzu, shi ne Manajan shirye-shirye (Content Manager) a Nishadi TV Abuja. Yana da mata da ‘ya’ya biyu. 2. Zainab Muhammad (Indian Girl) – Matsayi Na Biyu Zainab Muhammad,...
    A yau Talata ne dai ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya karbi bakuncin takwaransa na Rasha Sergey Lavrov wanda ya fara ziyarar aiki a nan Tehran. Bangarorin biyu dai sun tattauna akan batutuwa da dama da suka shafi halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, da kuma na kasa da kasa. Bugu da kari bangaroin biyu sun tattauna akan alakar kasashen biyu da hanyoyin bunkasa ta.
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi mu zauna kan teburin tattaunawa da mutumin da yake fitowa fili yana yi mana barazana, kuma ya sa hannunsa a wuyansa ya sheke mu. Shugaban kasar ta Iran wanda ya gana da ‘yan majalisa masu wakiltar gundunar Hamadan a daren jiya Litinin ya ce;  Mu mutane ne da mu ka yarda da tattaunawa,kuma a halin yanzu abinda ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci yake yi kenan da kasashen makwabta. Da ya tabo batun takunkuman da Amurka take kakaba wa Iran kuwa, shugaban kasar ta Iran  ya ce, babu yadda za a yi a kakaba takunkumin ya yi tasiri akan kasar da take da iyaka mai tsawo da...
    Kafafen watsa labarun HKi sun ambato jami’an soja na cewa, mayakan Hamas sun sake gina kansu ta hanyar daukar dubban mayaka, kuma suna nan a arewacin Gaza ba su fita daga ciki ba. Kafafen  watsa labarun na HKI sun kuma kara da cewa; mayakan da kungiyar take da su a yanzu, sun rubanya mayakanta na baya, kafin barkewar yaki, kuma kungiyar ta koyi darussa daga yaki da sojan kasa na Isra’ila a baya.” Jaridar “Badiot Ahranot” wacce ta dauki labarin ta kuma ce; Har yanzu Hamas ba ta fito da dukkanin mayakanta a filin daga ba, da adadinsu ya kai 30,000, kuma tana ba su albashi ta hanyar kudaden harajin da take karba. Wani sashen na bayanin kafafen watsa labarun...
    Shugaban kungiyar ‘al-Hikimah” na kasar Iraki Ammar Hakim ya gana da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-sisi. A yayin ganawar  Ammar Hakim ya jaddada muhimmancin taimaka wa kokarin da Masar take yi na ganin an hana korar falasdinawa daga yankunansu zuwa wajen Falasdinu. Ammar Hakim ya kuma ce, a yayin wannan ganawar na bayyana wa shugaban kasar jinjinawarmu akan yadda Masar ta kasance mai taimaka wa Falasdinawa.” Haka nan kuma mun nuna goyon bayanmu ga kokarin Masar al’umma da gwamnati na hana tilasatawa Falasdinawa yin hijira da kuma kare hakkokin Falasdinawa da riko da kasarsu. Har ila yau Ammar Hakim ya ce ganawar tasu ta tabo batutuwa da su ka shafi halin da ake ciki a wannan yankin da kuma wajabcin...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray ta ce za ta fara gudanar da bincike kan kocin Fenerbahce Jose Mourinho bayan da ta zarge shi da furta kalaman wariyar launin fata bayan da ƙungiyoyin suka tashi 0-0 ranar Litinin. Zuwa yanzu dai ba a bayyana irin kalaman da Galatasaray ke nufin Mourinho da furtawa ba, da yake magana a taron manema labarai bayan kammala wasan derby na Istanbul, Mourinho ya ce kujerar da ya zauna a filin wasan Galatasaray ba ta zama kurum, ta na tsalle kamar biri idan aka zauna kanta, ya kuma sake nanata sukarsa ga alƙalan wasan Turkiyya, yana mai cewa da an tafka babban kuskure idan akayi amfani da wani alkalin wasan ƙasar a wasan. An Dakatar Da...
    Wani dan kwallon Najeriya mai suna Abubakar Lawal daga Jihar Sakkwato ya rasu bayan fadowa daga bane a kasar Uganda, inda yake taka leda. Rahotanni sun bayyana cewa Abubakar Lawal mai shekaru 29 ya gamu da ajalinsa ne bayan ya fado daga hawa na uku na wanin babban kantin sayar da kayayyaki a Kampala, babban birnin kasar Uganda. Rasuwar tasa ta haifar haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito. Da farko an alakanta rasuwar tasa da hatsarin babur, kafin daga bisani jami’an tsaro su bayyana cewa ya fado ne daga bene. Marigayin dan wasan gaba ne a kungiyar kwallon kafa ta Vipers da ke kasar, inda ya fara wasa tun shekara 2022, kafin nan ya...
      An bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta kafa doka wacce za ta tanadi hukuncin kisa ga masu safarar da kuma masu shan miyagun kwayoyi, domin kare rayuwar ‘yan kasa. Wannan kiran ya fito ne daga shirin KAKAKI na FRCN Kaduna FM, inda masu kira suka bayyana ra’ayoyinsu a yayin tattaunawa da mai gabatar da shirin. Masu magana sun nuna damuwa kan illar safarar miyagun kwayoyi a kasar, musamman yadda yake shafar matasa, wadanda ake kallon su a matsayin shugabannin gobe. Alhaji Gaddafi Rigasa da Hajiya Aisha Mando sun jaddada bukatar hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen yaki da wannan matsala, domin inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. Sai dai sun kuma ba da shawarar a farfado...
      Masu sharhi kan harkokin kudi a Cowry Asset Management suna tsammanin Naira za ta ci gaba da kasancewa kan yadda take a wannan makon, tare da hana matakan hana rugujewar ta a kasuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta bakin Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ta shaidawa taron kwance damarar makamai na Majalisar Dinkin Duniya a Geneva cewa, makaman kare dangi na gwamnatin Isra’ila da suka hada da makaman nukiliya na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin da ma duniya baki daya. A yayin jawabin da ya yi a ranar Litinin, a babban taro na 2025 kan kwance damara, a hedkwatar MDD dake Geneva, Mr. Araghchi ya yi kira ga kasashen duniya da MDD da su ba da fifiko kan batun kawar da makaman nukiliya. Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa “dole ne kasashen duniya su tilastawa Isra’ila bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman kare dangi (NPT) don kawar...
    Mutanen unguwa sun kama wani magidanci mai shekara 45 kan zargin sa da lalata wani yaro ɗan makarantar firamare ta hanyar luwadi a yankin Zariya ta Jihar Kaduna. Al’ummar yankin sun ce dama ana zargin mutumin da yi wa yara maza fyade, don haka suke ta bibiyar motsinsa, kuma yaron ya faɗa da bakinsa cewa kusan sau uku mutmin yana ɗaukar sa. Wanda ke zargin yana sana’ar sayar da rake ne a Bakin Dago Tudun Jukun a Karamar Hukumar Zariya Jihar Kaduna. Aminiya ta ziyarci xibiyar da ke kula da cin zarafin mata da ƙananan yara da ke Asibitin Gambo Sawaba Kofar Gayan Zariya domin samun sahihin bayani kan lamarin a likitance. Magidanci ya sari matarsa da adda har lahira...
    ’Yan sanda sun cika hannu da wani magidanci bayan da ya sari matarsa da adda a kai, ta ce ga garinku nan. ’Yan sanda sun kama magidancin ne bayan samun rahoton aika-aikan da ya yi wa mai dakin tasa a sakamakon takaddamar da suka samu a tsakaninsu. Lamarin ya faru ne a sabuwar unguwar Upper Mission da ke garin Benin, hedikwatar Jihar Edo. Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Moses Yamu, ya ce ko da ’yan sanda daga babban ofishinsu da ke yankin Aduwawa suka isa wurin, sun iske matar kwance cikin jini, da mummunan sara a kanta. Ya daɓa wa yayansa wuƙa saboda Naira 700 NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa Da Shi?...
    nkin.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...
    Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙaryata zargin da tsohon abokinsa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi masa na neman takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2031. A wata hira da aka yi da El-Rufai cikin dare ne tsohon gwamnan Kadunan ya yi zargin cewa Nuhu Ribadu yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa. A yayin hirar da aka yi da shi a cikin dare a kafar Arise TV ranar Litinin, El-Rufai ya bayyana cewa sun raba jiha da tsohon abokin nasa Nuhu Ribadu da kuma Gwamnan Kaduna mai ci kuma magajinsa, Sanata Uba Sani, yanzu duk  ba abokansa ba ne. Amma martaninsa, a cikin sakon da ya fitar jim kaɗan...
    Rundinar kare juyin juya halin musulinci ta Iran, ta bayyana bikin jana’izar sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai rasuwa Sayyed Hassan Nasrallah da kuma Sayyed Safiedinne da aka gudanar a matsayin wani babban sako na ‘yan gwagwarmaya ga duniya baki daya. Wannan babban taron da akayi a Beirut abun tarihi ne ga duniyar musulmi, ya kuma nuna cewa kungiyar Hizbullah, na da karfinta da kuma akidar kyamar sahyoniyawan. Sanarwar ta kara da cewa: “Bikin da ya samu halartar miliyoyin mutane, a daidai lokacin da ake barazana da jiragen yakin Isra’ila, ya zama wata alama ta karfin Musulunci da cikakken hadin kan al’ummar kasar Labanon. Sanarwar ta yi nuni da cewa, gagarumin taron makoki daga kasashe daban-daban, addinai da kabilu, da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran, ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da hakkin dan adam a matsayin abun matsin lamba na siyasa ko tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashe ba. Abbas Araghchi, ya bayyana hakan ne a zaman kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya jaddada cewa, daya daga cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas ga tabbatar da hakkin dan Adam a duniya shi ne amfani da matakan tilastawa kasashe. Ya kara da cewa wadannan matakan suna da illa ga fararen hula kuma ba adalci ne ba ga marasa galihu kamar mata, yara, tsofaffi da masu nakasa. Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araghchi ya bayyana jin dadinsa a wannan...
    Kasashen nan guda uku mambobin kungiyar kawancen Sahel (AES) da suka balle daga kungiyar ECOWAS, sun kaddamar da tutarsu ta bai daya. An kadaddamar da tutar ne a yayin haduwar ministocin harkokin wajen kasashen jiya Asabar a Bamako babban birnin kasar Mali mai rike da shugabancin kungiyar na farko. Firaministan Mali, Janar Abdoulaye Maïga ya bayyana a yayin bikin, cewa “Tutar kungiyar AES, launin kore, tana dauke da tambarin kungiyar a tsakiyarta.”  Ya jaddada cewa launin kore yana nuna alamar bege da wadata, wanda ke wakiltar dukiya da karfin tattalin arziki. Wannan sabuwar alamar ta kunshi hadin kai da muradin bai daya na kasashen uku, inda suka kuduri aniyar yin aiki tare domin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar yankin inji...
    Ranar 21 ga watan Fabrairu ne aka cika shekaru 53 da shugaban kasar Amurka na lokacin Richard Nixon ya kawo ziyara kasar Sin a shekara ta 1972, ziyarar ta sauya tarihin duniya, ta kuma samar da tushen ci gaban yankin Asiya da tekun Pasifik cikin lumana. Lokacin da tunanin yakin cacar baka ya yi kamari a Amurka, Nixon ya fahimci muhimmancin jamhuriyar jama’ar kasar Sin a ci gaban Asiya da duniya baki daya. Nixon, ya kasance dan siyasa mai ra’ayin mazan jiya wanda ya girma cikin yakin cacar baka, amma duk da haka ya keta shingayen mulkin mallaka, danniya da babakere na wancan lokaci don fahimta da sauke alhakin da ke kansa na tarihi, ta hanyar hadin gwiwa da tuntuba,...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin bayar da tallafi a mazabun  jihar da su yi amfani da damar da suka samu domin dogaro da kai. Ya bayyana hakan ne a wajen kaddamar da shirin da majalisar da ke wakiltar mazabar Kaugama ya yi. Malam Umar Namadi wanda ya samu wakilcin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin, ya ce shirin samar da tallafin a mazabu zai kara inganta manufofi 12 na gwamnatin jihar wadanda suka hada da karfafawa al’umma don bunkasa zamantakewa da tattalin arziki a kowane mataki. Ya yi fatan wannan karimcin zai yi kyakkyawan tasiri ga mutane  1,200 da suka ci gajiyar tallafin. A jawabinsa, dan majalisa...
    Wata kotu a lardin Aceh da ke ƙasar Indonesia ta yanke wa wasu ɗalibai maza biyu hukuncin bulala a bainar jama’a. A ranar Litinin ce kotun ta yanke wa mutanen biyu hukuncin bayan samun su da laifin luwaɗi da juna. Uwa ta jefo jaririnta daga saman bene mai hawa biyu An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina A yayin da mu’amala tsakanin jinsi ɗaya ta halasta a wasu yankunan ƙasar mafi rinjayen musulmi a duniya, sai ɗabi’ar ta haramta a lardin Aceh da aka ayyana dokokin shari’ar Musulunci. Tun a watan Nuwamban bara ne dai ’yan sanda masu ɗabbaka shari’a suka kama mazajen biyu da ke karatu a wata jami’a suna aikata wannan alfasha a wani...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Tinubu ya ce Najeriya ta dauki wani muhimmin mataki na gudanar da kidayar jama’a da gidaje da aka jima ba a yi ba, inda  ya tabbatar da cewa za a gudanar da aikin cikin inganci ta hanyar amfani da fasahar zamani. Shugaban ya ba da wannan tabbacin ne a wata ganawa da ya yi da jami’an hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) a fadar gwamnati, shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin kidayar jama’a ga tsare-tsare na kasa, tare da jaddada aniyarsa na tabbatar da tattara bayanai masu inganci. Shugaba Tinubu ya bayyana shirin kafa kwamitin da zai duba kasafin kidayar jama’a da kuma gano hanyoyin samun kudade. Ya kuma jaddada bukatar hukumar kula da tantance ‘yan kasa...
    Mai magana da yawun kwamitin sa kaimi ga cinikayya tsakanin Sin da ketare ya amsa tambaya da manema labarai suka gabatar masa kan takardar bayani a kan manufar “Zuba jari a Amurka ta zamanto farko” a gun taron manema labarai da aka gudanar a jiya Lahadi. Inda ya ce, bangaren masana’antu da kasuwancin Sin na matukar kin yarda da matakin da Amurka ta dauka, wanda ya yi gamin-gambiza da batun tsaron kasa wuri guda, sannan ya yi hannu riga kwata-kwata da tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Kakakin ya kara da cewa, Amurka ta tsaurara matakan tsaro da nufin fakewa da guzuma ta harbi karsana a kan shigo da jari daga bangaren Sin a fannin kimiyya da manyan ababen rayuwa da...
    Shugaba Xi ya kuma yi nuni da cewa, a watan Satumban bara, Sin da Brazil, tare da wasu kasashe masu tasowa, sun kafa kungiyar abokan zaman lafiya game da rikicin kasar Ukraine, don samar da sarari da kuma ingantattun sharudda domin karfafa warware rikicin a siyasance. (Abdulrazaq Yahuza Jere)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta  yi alkawarin horar da matasa da ke aikin noman alkama a karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba gonakin alkama a yankin. Ya yabawa Shugaban karamar hukumar Birnin Kudu, Dr Muhammad Uba Builder bisa wannan shiri da ya bayyana a matsayin wata hanya ta samar da aikin yi ga matasa da bunkasa harkar noma. Kazalika, a yayin ziyarar gani da ido, Malam Umar Namadi ya kuma ba da umarnin gaggauta gina katanga da kuma gina ofishin jami’an tsaro a sabuwar tashar bada ruwan sha mai amfani da hasken rana ta garin Birnin Kudu. Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar, Alhaji Ibrahim Garba Hannun Giwa, ya shaida...
    Wani jariri sabuwar haihuwa ya riga mu gidan safiyar Litinin bayan mahaifiyarsa ta jefo shi ta tagar wani otel a birnin Paris. Jami’an tsaro da ke shigar da ƙara sun ce an tsinci gawar jaririn wanda ko cibiyarsa ba a yanke ba. An yi zanga-zangar kisan ɗalibi a Jami’ar FUDMA da ke Katsina NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Wata majiya ta ce uwar jaririn mai shekaru 18 ta jefo shi ne ta tagar ɗakin wani otel daga hawa na biyu a Kudancin Faransa. An bai wa jaririn kulawar gaggawa amma a ƙarshe ya ce ga garinku nan kamar yadda majiyar ta tabbatar. ’Yan sanda sun ce jaririn ya mutu da misalin ƙarfe 7:45 na safiya...
    Ma’aikatar kula da muhallin halittu ta kasar Sin ta gudanar da taron manema labarai a yau Litinin 24 ga wata, inda wani jami’inta ya nuna cewa, ingancin iska da muhallin kasar sun kyautatu a shekarar da ta gabata, lamarin da ya shaida cewa, kasar Sin ta cimma burin magance gurbatar yanayi a shekara ta 2024. Jami’in ya kara da cewa, a shekara ta 2024, yawan kwanakin da aka samu kyakkyawan ingancin iska ya kai kaso 87.2%, adadin da ya karu da kaso 1.7% idan aka kwatanta da na shekara ta 2023. Kazalika, yawan kwanakin da aka samu mummunar gurbatar yanayi ko fiye da haka, ya kai kaso 0.9%, adadin da ya ragu da kaso 0.7%. A Beijing, wato fadar mulkin...
    Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce kungiyar ta saki fursinoni yahudawa  6, kuma take fatan HKI za ta saki falasdinawa 620 kamar yadda yake cikin yarjeniyar tsagaita wuta, amma ta ki yin hakan, da dalilin cewa wai kungiyar Hamas ta wulakanta daya daga cikin fursinoni 6 da ta saka. Jami’in na Hamas ya ce tawagar tattaunawar...
      Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci.   Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na haɗin gwiwa a Laddauga, wurin kiwon dabbobi na Kachia a Jihar Kaduna.   Ya bayyana cewa, manufar wannan shiri ita ce tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai na makarantun makiyaya.   Sakatare Janar ya ƙara da cewa kashi 60 na waɗanda za su amfana ‘yan mata ne, kuma shirin zai ƙarfafa ilimin kyawawan ɗabi’u a fannin abinci mai gina jiki, tsafta, tsabtace muhalli, da kuma...
    Sojojin Iran sun gwada amfani da sabbin jiragen yakin na zamani da suka kera a cikin gida, a cikin atisayen Zulfikar 1403 da ke gudana a kudancin kasar, wanda kuma ya hada rundunonin sojojin kasar daban-daban. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar atisayin na cewa sojojin sun gwada amfani da jirgin saman yaki samfurin Yak-130 a cikin atisayen. Inda suka tabbatar da ingancinsa. Ana gudanar da atisayen Zulfikar 1403 ne a yankin Tekun Omman da kuma wani bangare na yankin Tekun farasa daga kudancin kasar Iran. Bugediya Janar Alireza Sheikh kakakin atisayen ya fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa wannan bangare kadan ne daga atisayen, amma a yau sun...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
    Ministan ya yi zargin cewa, furucin Shugaban na daya daga cikin dalilan da suka sa Allah ya karbe mulki daga jam’iyyar duk da nasarar da ta samu a zaben gwamna na 2023.   Amma da yake mayar da martani, Abbas ya yi zargin cewa Ata ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023, kuma sun bayyana haka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.   Abdullahi Abbas ya ce, “A gare mu ‘yan APC Yusuf Ata ba dan jam’iyyar APC ba ne. Ba mu ma san dalilin da ya sa aka nada shi minista ba. Duk fadin jihar Kano a karamar hukumarsa ne muka zo na uku a zaben 2023.   “Ba mu san cewa an nada shi minista ba. Mun...
    Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza  a jiya Lahadi. Ya kara da...
    A yau Litinin ce aka sanya Sayyid Safiyyuddeen shugaban kungiyar Hizbullah wanda yayi shahada a hannun sojojin HKI a yakin Tufanul Aksa a makwanccinsa ta karshe a garinsu Deir-Qannoon Al-nahr dake kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dubban duruwan mutane ne suka halarci Jana’izar sa, sannan mutanen kauyuka a yankin da dama sun halarci jana’izar. Mutane daga kasashen duniya da dama wadanda suka halarci jana’izar a jiya Lahadi a Beirt sun  halarci jana’izar Sayyid shahid Hashim safiyyudeen a yau a kudancin kasar ta Lebanon.
    Hukumar tsaro ta farin kaya  (NSCDC) reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin sojan gona ga aikin hukumar. Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC reshen jihar Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce mutanen biyu, Muhammad Sarari da Madaki Zaharaddeen,   masu shekaru 43 da 32, mazauna Goron Dutse ne, a karamar hukumar Dala, da Hotoro kwatas a karamar hukumar Nassarawa. A cewar jami’in hulda da jama’an, wadanda ake zargin suna zuwa hukumomin da ma’aikatun gwamnati ne, inda suke yaudarar manyan ma’aikata tare karbar kudade daga hannunsu. “Dubunsu ta cika ne a lokacin da suka yi yunkurin tsoratar da...
    A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun tsayar da su domin tuhuma bisa zargin cewa masu yi wa ’yan bindigar daji leƙen asiri ne. NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji Wannan harbin da suka yi ya yi sanadiyar mutuwar wannan ɗalibi mai suna Saidu Abdulkadir. Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya an kama wani ɗalibin jami’ar yana safarar makamai....
    To, ma iya cewa kasar Amurka ta riga ta fusata dukkan kasashen duniya. Idan an sa wata kasar dake nahiyar Afirka fuskantar matakin da kasar Amurka ta dauka ita kadai, to, za ta ji akwai matsin lamba. Sai dai yanzu za a saki jiki, saboda ko da yake kasar Amurka ta kan ci zarafin sauran kasashe, amma ba ta da karfin cin zarafin dukkan kasashe a sa’i daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a wajen taron aikin tsaro na Munich da ya gudana a kwanan nan, cewa bai kamata a ji tsoron aikace-aikacen kasar da ta ke ta nuna fin karfi a duniya ba, saboda galibin kasashen duniya dake...
    Babbar kotun tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga tsige Honarabul Aliyu Ango Kagara, dan majalisar APC mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/GSCS/10/2025 da Kagara ya shigar kan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara,  da Kakakinta, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC). Ta ce shari’ar da mai shari’a Salim Olasupo Ibrahim ya jagoranta ta kalubalanci tsige Kagara da shugabannin majalisar suka yi. A cewar sanarwar, kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na hana INEC gudanar da zaben cike gurbi na mazabar...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
    Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.  Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...
    Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya. Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Waɗanda aka dakatar sun hada da Kawu Sumaila (Sanatan Kano ta Kudu), Ali Madakin Gini (Dala), Sani Rogo (Rogo/Karaye), da Kabiru Rurum (Rano/Kibiya). Dungurawa ya ce waɗannan ‘yan majalisa sun samu tikitin NNPP ne, amma daga baya suka fara aikata abubuwan da suka sabawa jam’iyyar. Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  Jam’iyyar NNPP Daya INEC Ta Amince Da Ita – Shugaban Jam’iyyar  Ya ce misali, Sanata Sumaila ya ƙaddamar da...
    Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku kan zargin cin amanarta. Sauran waɗanda jam’iyyar kan zargin cin amana sun haɗa da Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.  
    Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen iko da birnin el-Obeid na yankin kudancin ƙasar na kusan shekaru biyu da dakarun RSF suka yi. Wannan nasara na zuwa ne ‘ƴan sa’o’i bayan da RSF ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar siyasa a Nairobi da ke ƙasar Kenya na kafa gwamnatin aware a yankunan da ke ƙarƙshin ikonta. Tun dai shekarar 2023 ne rundunar RSF da sojojin Sudan ke fafatawa, inda dubban fararen hula ke mutuwa sannan da dama na barin gidajensu. Rikicin dai ya raba ƙasar ɓangarori biyu, inda sojoji ke iko da arewa da gabashi, yayin da su kuma RSF ke iko da mafi yawancin yankin Darfur da ke yammaci da wasu sassan kudanci. Birnin El-Obaid dai wanda shi ne...
      Barazanar Ata Kan Ficewa Daga APC A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, Minista Yusuf Ata ya yi magana da magoya bayansa, yana mai cewa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, to zai fice daga jam’iyyar. “Muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi,” in ji Ata. Ya ƙara da cewa, “Idan suka dawo da shi, za mu fice, kuma na rantse da Allah jam’iyyar za ta sake faɗuwa a zabe.” Wannan rikici na ƙara nuna rabuwar kai a cikin APC a Kano, wanda ka iya shafar ƙarfi da tasirin jam’iyyar a jihar nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Babban Jami’in Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Emeka Onumajuru, ya bayyana cewa saura kiris su gama da jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji. Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba. “Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka. Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa. Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin...
    Babban Jami’in Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Emeka Onumajuru, ya bayyana cewa saura kiris su gama da jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji. Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba. “Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka. Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa. Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin...
    Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci. Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo. Basaraken  ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta. Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba. “Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin da ke da nufin kusantar da jama’a ga gwamnati, zai kuma tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen da aka aiwatar sun dace da  muradin al’umma. Don haka Namadi ya yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka rungumi ayyukan da gwamnatin jihar ke  aiwatarwa hannu bibbiyu, tare da yin alwashin ci gaba da samar da ingantattun ayyuka. Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, zai yi nazarin...
    An gurfanar da wata matar aure a kotu kan zargin ta da cinna wa mijinta wuta a Jihar Kano. Ana zargin matar ta watsa wa mijin nata fetur sannan ta cinna masa wuta ne saboda ya shiga dakin sabuwar amaryarsa, suna tattaunawa da ita. Shaidu sun bayyana cewa wadda ake zargin ta yi aika-aikan ne bayan ta nemi mijin nata ya fito daga dakin amaryar tasa amma ya ƙi amincewa. Magidancin ya samu munanan kuna a sakamakon wutar da matar tasa ta yi masa. Lauyar Gwamantin Jihar Kano, Saima Garba, ta karanta wa matar takardar tuhumar aikata kisa da ake mata, amma ta musa. Daga nan alƙalin kotun Majistare mai Lamba  25, Halima Wali, ta ba da umarnin tsare matar...
    Iran ta yi kakkausar suka kan ta’addancin Isra’ila game da keta hurumin kasar Lebanon, bayan da jiragen yakinta suka yi shawagi a yankin da ake gudanar da jana’izar tsoffin shugabannin kungiyar Hizbullah. A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a daren Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta shiga wani sabon yanayi na kara tabbatar wa duniya da cewa ita bata bin dokokin kasa da kasa. Baghaei ya ce jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kokarin tarwatsa dubban daruruwan ‘yan kasar Lebanon da wasu da suka taru domin nuna girmamawa ga jarumtansu, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da mataimakinsa da suka nada Sayyed Hashem Safieddine. Baghaei ya...
    Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta. Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa. “Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar...
    Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran). Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a wata ganawa da ya yi da shugabannin jami’an diflomasiyyar Afirka a birnin Tehran ya bayyana cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da nahiyar Afirka, na daya daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya a gaba. Aref ya kara da cewa, shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar...
    Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta hana wani yunƙurin ‘hari da ‘yan bindiga suka kai kan jami’an NSCDC a kan hanyar Dutsinma-Kurfi a ƙaramar hukumar Dutsinma. Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025. Bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:57 na dare, ‘yansanda daga ofishin Dutsinma suka gaggauta kai ɗauki, wanda ya haifar da musayar wuta da ‘yan bindigar. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mutum Tare Da Sace Mutum Biyu A Kaduna Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata A sakamakon haka, ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka samu gawar ɗaya daga cikinsu...
    Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (murabus) ya bayyana dalilin da ya hambarar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a 1985. Janar Babangida ya bayyana dalilin da gwamnatinsa ta karya darajar Naira da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta yi bayan kifar da Buhari. Babangida, wanda shi ne babban hafsan sojin kasa a lokacin Buhari, ya taka rawar gani a juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Shehu Usman Shagari a 1983 da kuma na 1985 da ya kawo shi kan karagar mulki. Ya ba da cikakken bayani game da abubuwan da suka faru a cikin littafin tarihin rayuwarsa da ya ƙaddamar a makon jiya. Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi NAJERIYA...
    A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu. Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da ingantacciyar murya guda ta kasashe masu tasowa. Wang ya bayyana a yayin taronsu cewa, kasar Sin a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwar cin moriyar juna tsakaninta da kasar Afirka ta kudu, da kara gaggauta bunkasuwar kasashen biyu, da kuma kara yin hadin gwiwa don kara daukaka murya da wakilci na kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka a cikin ajandar kasa da kasa. Wannan...
    Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda. Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya. Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya ce dubun dan shekara 65 din mai suna Nehemiah Sunday Udo ne a ranar Asabar baya al’ummar kauyen Ekpene Obo da ke Ƙaramar Hukumar Esit Eket sun ritsa shi. John ya ce bayan samun kira daga al’ummar yankin ne ’yan sanda suka kai samame inda suka samu mutanen sun kai wanda ake zargin fadar basaraken yankin. Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
    Kungiyar Hamas ta jinjina da irin babbar gudunmawa da tsayin dakan da Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine suka yi wajen goyon bayan Palastinu, da kuma shahadar da suka yi a kan wannan tafarki. A cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da jana’izar shahidan biyu, kungiyar Hamas ta ce, muna addu’ar Allah ya jikan su da rahama, tare da mika ta’aziyyarmu ga al’ummar kasar Labanon da dukkanin al’ummar mu Larabawa da musulmi. Kungiyar ta tabbatar da cewa, laifuffukan Haramtacciyyar Kasar Isra’ila da kuma kisan gillar da ta yi wa shugabannin gwagwarmaya a Falasdinu, Labanon da sauran su, ba za su dakatar da tafarkinmu ba. Har ila yau sanarwar ta bayyana matsayin shahid Sayyid Hassan Nasrallah da jajircewarsa da...
    Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun gana da shugaban kasar Labanon Joseph Aoun. Bayan nan kuma tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri, sannan ta ci gaba da tattaunawa da sauran jami’ai da suka hada da firaministan kasar Labanon Nawaf Salam. Ghalibaf da sauran jami’ai sun tafi kasar Lebanon a safiyar Lahadi don halartar jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah, da kuma magajinsa  Sayyed Hashem Safieddine, wadanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kashe su a karshen shekarar da ta gabata. Da yake...
    Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin  Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya. Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Jos ta Arewa da Bokkos da Shendam da Mangu da kuma Kenke. Ko waɗanne irin matakai ya kamata al’umma su ɗauka don kauce wa kamuwa da wannan cuta? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...
    Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron  kasar nan. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a na gwamnatin jihar Jigawa da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. A cewar sa, kiran ya zama wajibi domin karfafa tsaro a fadin Najeriya. Alhaji Badaru Abubakar, ya yi nuni da cewa an samu ingantuwar harkokin tsaro a fadin kasar cikin ‘yan watannin nan. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi iya bakin kokarinta wajen yaki da rashin tsaro, kuma za ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofin da ake so. Ministan ya...
    Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi. A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma ba tare da wata matsala ba lokacin Chunyu da aka kammala jiya Asabar, alkaluman bana sun nuna an samu karuwar kashi 7.1 cikin dari a kan adadin da aka samu na daidai irin wannan lokacin a shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)  
    Matakin Amurka Na Takaita Zuba Jari Zai Cutar Da Wasu Da Ita Karan Kanta
    Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce har yanzu Najeriya na neman shugabanni nagari da za su fifita jin daɗin al’umma maimakon mayar da hankali kan wajen tara wa kansu dukiya. Ya bayyana hakan ne yayin bikin karramawa da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Firamare ta Sultan Bello (SUBOPA), ta shirya domin girmama wasu mambobinta biyu – Manjo Janar Abdulmalik Jibrin (mai ritaya) da Birgediya Janar Abdulkadir Gumi (mai ritaya), bisa sababbin muƙaman da suka samu a gwamnati. Arewa na buƙatar haɗa kai da Kudu Maso Kudu don ceto Najeriya — El-Rufai Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP An naɗa Manjo Janar Jibrin a matsayin Sakatare na Hukumar...
    Kasar Sin Ta Zayyana Muhimman Ayyukanta Na Zurfafa Gyare-gyare A Yankunan Karkara Da Inganta Raya Su
    Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi, Yunusa Umar, ya jagoranci mambobi fiye da 7,500 zuwa jam’iyyar PDP. Cikin waɗanda suka sauya sheka har da Shugaban Matasa na APC a yankin, Yusuf Inuwa Bora, da Sakatare mai kula da jin daɗin mambobi, Isah Zakaria. An karɓi waɗannan sabbin ‘yan jam’iyyar ne a hukumance a ranar Lahadi, inda Shugaban PDP na ƙaramar hukumar Dass, Hon. Yusuf Sabo, da Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Mohammed Abubakar Jibo, suka tarɓe su. Umar ya bayyana cewa kyakkyawan shugabancin Gwamna Bala Mohammed ne ya sa suka bar APC. Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu...
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin ya yi Allah wadai da kasar Australia bisa yadda ta zargi kasar Sin da yin atisayen soja bisa doka a tekun dake kusa da kasar ta Australia. Kakakin, Wu Qian ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin kafofin watsa labaru game da zargin na Australia cewa jiragen ruwan yaki uku na kasar Sin sun yi atisayen soja a tekun dake kusa da kasar Australia. Wu Qian ya bayyana cewa, zargin da kasar Australia ta yi ba shi da tushe balle makama, domin yankin tekun da jiragen ruwan yakin na kasar Sin suka yi atisayen soja yana can nesa da layin teku na kasar Australia, kuma yanki ne da ba ya cikin mallakar wata kasa....
    Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki. Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da sojojin zaman lafiya da za su kai 30,000 daga cikin har da na kasar Switzerland. Sai dai kuma aiwatar da shirin na turai yana da alaka ne da yadda Donald Trump zai amince da kasarsa ta taka rawa, idan har Rasha ta kai wa turawan hari, ko ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda jaridar ta ambato wani jami’in turai din yana fada. Jaridar ta...
    Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na Beirut,bayan da aka dauki tsawon yau ana gudanar da jana’izarsa. Dubun dubatar mutanen Lebanon da kuma wasu daga wajen kasar ne su ka halarci taron jana’izar Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin da  aka gudanar a cikin birnin Beirtu. Tashar talabijin din al’mayadin ta bayyana cewa bisa kirdado adadin mutanen da su ka halarci jana’izar sun kai mutane miliyan daya da 400,000. Mahalarta jana’izar sun cika filin wasa na birnin Beirut da kuma manyan tituna ta yadda babu masaka cinke, da hakan ya sa motar da take dauke da makararsa da...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. A ranar lahadi 23  ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar Hibullah, sayyid Hassan nasaralla, da kuma magajinsa na tsawon kwanaki 6 Sayyid Hashim safiyyuda deen, kafin haka shi ne shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah.   An haifi sayyid Hassan nasaralla (r ) a ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1960  a wani kauye a kudancin kasar Lebanon, Sayyid ya tashi a cikin gida mai saukin rayuwa, ya fara karatu kamar yadda ko wani...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana Shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, jagora ne na musamman na al’ummun larabawa da musulmi kuma shugaban gwgawarmaya. A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da Shahid Hashim Safiyuddin, inda ya bayyan cewa: A wannan rana muna yin ban kwana da jagora na tarihi na musamman wanda kuma yake a matsayin alkiblar ‘yantattun na duniya. Sheik Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah ya kasance wanda ‘yan gwgawarmaya suke kauna, wanda Falasdinu da birnin Kudus ne manufarsa, ya kuma taka rawa wajen farfado da batun kare hakkokin Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid...
    Wanda ya wakilci jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a wajen jana’izar Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Safiyuddin Hashim, ya gabatar da jawabi da a ciki ya bayyana cewa: Jagoran jihadi mai girma, kuma shugaban gwgawarmaya a cikin wannan yankin, Sayyid Hassan Nasrallah ( Allah ya daukaka matsayinsa)  ya kai matsayi na koli na daukaka da izza. Sayyid Mujtaba al-Husainy ya kuma ce; A wannan lokacin za a binne gangar jikin Sayyid a cikin kasar da ya yi jihadi saboda Allah akanta, amma ruhinsa da kuma tafarkinsa na gwgararmaya zai kara daukaka fiye da kowane lokaci a baya. Sayyid Mujtaba al-Husaini ya kuma ce:Makiya su kwana da sanin cewa, gwgawarmaya za ta cigaba da...
    Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane su ka halarci jana’izar yana nuni da cewa, gwgawarmayar musuluncin ta sake jaddada kanta. Sheikh Ibrahim Yakub Ibrahim El_Zakzaky ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah yana a matsayin takaitaccen hoton al’ummar musulmi ne, kuma  gudanar da jana’izar da na gani yana nuni da cewa; Ruhinsa yana nan a raye cikin fagen daga. Har ila yau jagoran ja harkar musulunci a Nigeria ya ce, abokan gaba ‘yan sahayoniya sun zaci cewa ta hanyar kisan gilla za su kawo karshen gwgawarmaya,amma abinda yake faruwa a yau, yana nuni da cewa gwgawarmaya ta kara sabunta kanta, kuma da...
    Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka
      dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka: Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta. Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi. Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya....
    Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics
    Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Cigaba Da Zama Shugaban APC A Kano, Zan Fita – Ata