2025-03-28@15:40:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 95

«nasarar juyin juya halin Musulunci»:

    A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da masu zuba hannun suka yi. Wannan ya nuna, savanin jimlar shiyar da aka yi hada-hadar ta kasuwar da ta kai Naira biliyan 1.818  sai kuma wata shiyar da ta kai ta Naira biliyan 47.226, wato wacce aka yi musayarta a makon da ya wuce wadda ta kai 64,222. Misali, manyan kamfanonin da suka yi hada-hada a kasuwar sune,  kamfanin Inshora na Sovereign Trust Insurance da...
    Aƙalla mutum 24 ne suka rasu a wata gobarar daji mai muni da ta auku a tarihin Koriya ta Kudu baya ga mummunar ɓarna da ta haddasa. Mukaddashin shugaban ƙasar ya sanar a ranar Laraba cewa wutar dajin ta rabu kashi daban-daban har fiye da goma tun ƙarshen mako, inda ta laƙume wasu yankunan kudu maso gabashin kasar. Ribas: Za mu ɗauki matakan da za su shafi tattalin arzikin Nijeriya — ’Yan ƙwadago Ban sani ba ko zan tsaya takara a 2027 — Atiku Har ila yau, ta kuma tilasta wa kusan mutum 27,000 ƙaurar gaggawa bayan ta datse tituna da kuma na’urorin sadarwa kamar yadda mazauna yankunan da ke neman tsira da rayukansu suka sanar. Wani jami’in Ma’aikatar Kare...
    Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda tun daga shekarar 2017, hada-hadar cinikayya ta duniya a fannin rarraba matsakaitan hajoji, ke kara dogaro kan kasar Sin sama da dogaronta ga yankin arewacin Amurka. Kazalika a shekarar 2023, dogaron sassan kasa da kasa kan kasar Sin ta fuskar samar da matsakaitan hajoji ya kai kaso 16 bisa dari, sama da na yankin arewacin Amurka mai kaso 15 bisa dari. Bugu da kari, rahoton...
    Ba wannan tarihi na kanfar iko da ayarin farko na “yan majalisun wannan kasa ke da shi ne abin kallo ko la’akari ba, cikakkiyar dama da suke da ita a yau, tare da turbude hancin bukatun masu zabe, shi ne babban abin nadama da kaico!!!. Idan a wancan lokaci za a ce Turawa sun rike musu kugu ne, ta yadda za a ga ba su da wani tasiri ko katabus, wajen zuwa da kyawawan manufofi, don ciyar da jama’arsu gaba. Yanzu kuwa, za a iya yi wa wadannan “yan majalisun uzuri?. Shin, suna da cikakken ikon gudanar da aiyukan nasu ko babu?. Babu shakka, duk wani irin iko da ake da bukata da tsarin mulki zai ba da, ya jima...
    “SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba. “Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam....
    A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata. Kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ita ma ta shaida wannan yanayi, a farkon watanni biyu na shekarar bana, yawan kudin kayayyakin da aka sayar a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 8 da...
    Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki. Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa ​​wuƙa ta mutu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda. Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin...
    Sai dai, a yayin da yake yanke hukuncin; mai shari’a Omotosho, ya yanke hukuncin cewa, ya yi watsi da karar tasu da suka shigar saboda rashin cancanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin sake farfaɗowa daga wannan masifa. ‘Za a fara biyan Naira 77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Maris’ Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus. Hukumomin yankin har zuwa yanzu ba su bayyana ainihin dalilin tashin gobarar ba, yayin da waɗanda abin...
    Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan...
    Haka kuma, a ranar 3 ga Fabrairu, jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutum uku da bindigogi 10 ƙirar AK-47, inda suka amsa cewa suna sayar da su ga masu aikata laifuka. Rundunar ‘yansanda ta ce za ta ci gaba da yaƙi da fasa-ƙwauri da safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, tare da kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata gobara da ta auku safiyar wannan Larabar ta laƙume kasuwar ’yan gwan-gwan da ke unguwar Dakata a Ƙaramar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano. Kasuwar wadda ake kira da Kwalema tana nan a kan titin Zango, daura da gidajen man Dominion da kuma Mobil da ke makwabtaka da ofishin Hukumar WAEC. Cire Gwamna Fubara ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki — Lauyoyi DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu na ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar da ke neman wuce gona da iri. Sai dai ya bayyana cewa duk da bincike ya soma gudana, amma kawo yanzu...
    Alkaluma daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin ko MIIT, sun nuna irin ci gaba bisa daidaito da sashen masana’antun dijital na kasar Sin ya samu a shekarar 2024 da ta gabata, inda a shekarar ta bara sashen ya samu karin kudin shiga da riba. Alkaluman da MIIT ta fitar a jiya Litinin, sun nuna a baran, sashen ya kudin da ya kai kudin Sin yuan tiriliyan 35, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 4.9, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 5.5 bisa dari a shekara. Kazalika, jimillar ribar da sashen ya samar ta karu da kaso 3.5 bisa dari a shekara, inda ya kai yuan tiriliyan 2.7. Bugu da kari, a shekarar ta 2024, karin kimar hajoji da manyan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan ayyuka da sufuri na kasar Lebanon Yusuf Rasamani ya bayyana cewa; Asarar da HKI ta jazawa kasar Lebanon a lokacin yaki ta kai dalar Amurka biliyan 14, tare da bayyana cewa kasar Rasha ta bijiro da cewa za ta taimaka. Rasamani ya fada wa Radiyon “Sputnik” na Rasha cewa; Suna ci gaba da aiki tare da babban bankin duniya, domin tantance barnar da yakin Isra’ila ya haddasa a Lebanon.” Bugu da kari ministan ayyukan na kasar Lebanon ya kuma ce; Ma’aikatar ta fara aikin debe baraguzai a cikin garuurwan da za su iya isa, wadanda babu sojojin HKI a cikinsu.” Haka nan kuma ya ce; Kasar ta Lebanon da kuma Bankin Duniya da Asusun bayar da Lamuni suna aiki...
    Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a wani taron sirri da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan mako kasar Rasha ta yi Allah-wadai da sabuwar  gwamnatin  kasar ta Syria dangane da kisan kiyashin da jami’anta suke yi a kan tsiraru a kasar. Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasar Syria (SOHR) ta sanar da kashe fararen hula 1,383, galibi ‘yan Alawite a cikin makon da suka gabata. SOHR ta ce yawancin wadanda aka kashe fararen hula ne, kuma jami’an da ke da alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne suka kashe su. Kasar Rasha ta yi gargadi kan karuwar ta’addanci a kasar Syria tare da kwatanta kashe-kashen...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya.  “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba. “tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?” “Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar  jama’a na duniya.” Inji jagoran. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a...
    Wani dan bindiga da ya karya yarjejeniyar sulhu a Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina mai suna Bala Wuta na Garin Mazanya, na can kwance rai-kwakwai-mutu-kwakwai bayan ya sha dukan kawo wuka. Tubabbun ’yan bindiga sun yi wa Bala wuta takakkiya ne har gida inda suka yi masa bugun dawa, bayan da ya yi garkuwa da wasu matafiya jim kadan bayan sulhun da aka yi, inda bayan sun lugwiwita shi, suka wajabta masa biyan tarar Naira miliyan uku. HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ana iya tuna cewa, a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2025 ne aka yi sulhun, wanda ya samu wakilcin sojoji da ’yan sanda...
    Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya. Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi mata haƙƙinta. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Natasha, ta ce dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Nijeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili. Taƙaddamar da ke tsakanin Sanata Natasha...
    Gwamnatin Najeriya a ranar Talata ta bayyana fatanta na ganin tattalin arzikin kasar zai karu da a kalla kashi 4.6 cikin dari a shekarar 2025, daga kashi 3.19 a shekarar 2024. Da yake kaddamar da wani cikakken tsarin tattalin arziki na samun ci gaba mai dorewa a babban birnin tarayyar Abuja, ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin kasar, Wale Edun, ya ce har yanzu daidaita sassan tattalin arzikin kasa shi ne abin da aka fi sa a gaba, tare da samun daidaito a darajar musayar kudi, da rarar cinikayya, da karuwar samar da man fetur da ke sanya kasar a matsayin kasa mai karfi a duniya. A sa’i daya kuma, hukumar kididdiga ta kasa a baya ta...
    Kimanin fararen hula 1,000 ne aka kashe tare da jikkata wasu daruruwa a hare-haren jiragen yaki marasa matuki a nahiyar Afirka, yayin da ake ci gaba da yin amfani da jirage marasa matuka a nahiyar. A cewar jaridar The Guardian, masu sharhi da nazari na cewa , daga shekara ta 2021 zuwa 2024, jami’an tsaro a kasashe daban-daban na nahiyar Afirka sun yi amfani da jiragen yaki marasa matuka wajen kai hare-hare, wanda kuma sau tari ana kashe fararen hula ne, maimakon masu aikata laifuka. Dole ne wannan ya kawo karshe, kuma dole ne kasashen duniya su dauki matakai da suka dace waje saka kaidoji kan amfani da jiragen yaki marasa matuka, domin rashin yin hakan zai ci gaba da...
    Manya-manyan Jiragen ruwan yaki na kasashen Rasha da China sun isa tashar Jeragen ruwa ta Chabahar dake kudu maso gabacin kasar Iran a bakin tekun india don fara atisayen soje a tsakanin kasashen uku, wanda aka sanyawa suna ‘damarar tsaro na shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan gagarumin atisayen sojojin ruwa tsakanin manya-manyan kasashen guda uku zai sami halattan wasu kasashe da dama a matsayin masu kallo. Labarin ya kara da cewa manya-manyan jami’an sojojin ruwa na sojojin Iran da kuma na dakarun IRGC ne suka tarbi jiragen ruwan yaki na wadannan kasashe. Sannan ana saran wakilai daga kasashen Azerbaijan, Iraki, Kazakhstan, Oman, Pakistan, Qatar, Afirka ta Kudu, Sri Lanka da Haddiyar...
    Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da tashin hankalin da ya farke a gabar tekun Syria a ranar Lahadin da ta gabata, a daidai lokacin da rahotanni ke nuna cewa an kashe wasu iyalai baki daya a wannan tashin hankali, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a matsayin “mai matukar tayar da hankali”. Babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike kan kisan kiyashin da masu dauke da makamai suka aikata, tare da hukunta wadanda suka aikata laifukan. Babban jami’in kare hakkin bil adama na MDD ya kara da cewa, “Muna samun rahotanni masu matukar tayar da hankali kan yadda ake kashe iyalai baki daya, da...
    Rahotanni sun bayyana cewa, ya kammala yunkurin komawa jam’iyyar SDP.   Da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ofishin yada labarai na Atiku ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar ya na nan dan jam’iyyar PDP na gaskiya.   Yayin da yake bayyana rahotannin a matsayin “karya”, ofishin yada labaran ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da rahoton sauya jam’iyyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Liberpool na shirin lashe Premier League na bana kuma na 20 jimilla, za ta yi kan-kan-kan da yawan wanda Manchester United ta dauka a tarihi kuma Liberpool ce ta daya a kan teburin Premier na kakar nan da maki 67, sai Arsenal ta biyu mai maki 54. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bakin duniya ya kiyasta cewa ana bukatar dala biliyan 11, domin sake gina Lebanon sakamakon barnar da hare haren Isra’ila suka haifarwa kasar. Bangaren gidaje na Lebanon ya fi fama da matsalar, inda aka kiyasta asarar da ta kai dala biliyan 4.6, yayin da masana’antar yawon bude ido ta yi asarar dala biliyan 3.6. “Sakamakon rikice-rikicen ya haifar da raguwa a ainihin GDP na Lebanon na 7.1 bisa dari a 2024,” in ji Bankin Duniya. Rahoton ya kara da cewa, “Ya zuwa karshen shekarar 2024, raguwar GDP na kasar Lebanon tun daga shekarar 2019 ya kusan kashi 40%, wanda hakan ya haifar da koma bayan tattalin arziki a bangarori da dama da kuma yin tasiri ga ci gaban tattalin arzikin...
    Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Legas da ta Yola, da Jihar Adamawa, sun yanke wa wasu dillalan miyagun ƙwayoyi huɗu da aka kama da safarar ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan 4.6 hukuncin ɗaurin shekaru 95 s gidan yari. Ɗaya daga cikinsu, Ogbuji Christian Ifeanyi, jami’an hukumar NDLEA sun kama shi a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas a bara, yana ƙoƙarin shigowa da hodar iblis ɗauri 817 mai nauyin kusan kilogram 20, wadda kuɗinta ya kai biliyan 46. Tinubu ya bai wa Farfesa Jega muƙami a gwamnatinsa PDP ta soki dakatar da Natasha, ta nemi a binciki Akpabio Sauran da aka kama sun haɗa da Iloduba Augustine Chinonye, Shuaibu Nuhu Isa (wanda aka fi sani...
    Gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan cewa kasar nan ta yi asarar tiriliyoyin naira sakamakon ayyukan masu hakar ma’adanai ta barauniyar hanyoyi musamman a jihohi. Gwamnatin ta kuma cafke da gurfanar da ‘yan kasan waje su hudu wadanda suka shiga harkar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu mutane 320 kuma aka cafke kan harkokin satar ma’adinai. A cewar gwamnatin, cikin wadanda aka kama 320, kusan mutum 150 a halin yanzu suna fuskantar shari’a kuma wasu guda tara an dauresu, inda su kuma mutum hudu ‘yan kasar wajen aka dauresu a gidan yari. Ministan bunkasa albarkatun kasa, Dele Alake, shi ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da manema labarai a karshen zaman majalisar zartarwa na tarayya...
    Rundunar hadaka ta jami’an tsaro da suka hada da ‘yan banga sun yi nasarar hallaka  wani kasurgumin jigon kungiyar Lakurawa da aka fi sani da  Maigemu a jihar Kebbi. Sanarwar da Daraktan Tsaron, Alhaji AbdulRahman Usman Zagga, ya fitar, ta ce an kashe Maigemu ne a ranar Alhamis a Kuncin Baba da ke karamar hukumar Arewa, bayan musayar wuta da jami’an tsoro. Sanarwar ta ce, wannan nasarar ta zo ne mako guda bayan da Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Nasir Idris ya ziyarci al’ummar Bagiza da Rausa Kade a yankin karamar Hukumar Arewa, domin jajantawa al’ummar yankin bisa kashe wasu mutane shida da ake zargin barayin shanun Lakurawa ne suka yi. An bayyana cewa, matakin da gwamnan jihar ya dauka kan...
    Alake ya bayyana cewa majalisar zartarwar ta amince da wani sabon shiri na inganta tsari da kuma dakile asarar kudaden shiga a fannin ma’adinai. A wani bangare na shirin, ya ce gwamnati za ta tura fasahar tauraron Dan’adam don sa ido kan muhimman wuraren hakar ma’adinai da kuma bin diddigin ayyukan ma’adani. Alake ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta karfafa aikin hadin gwiwa a tsakaninta da gwamnatin jihohi a yankunan da ake hakar ma’adinai domin dakile ayyukan masu haka ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da cewa kasar na morar albartun da Allah ya huwace mata. Da yake magana kan takardar da ya gabatar a gaban majalisar, ministan ya ce takardar ta tsara yadda za a shawo kan...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
    Wata mummunar gobara ta ƙone shaguna sama da 17 a ɓangaren ’yan teloli da masu hada-hadar kayan abinci a tsohuwar kasuwar garin Gombe. Gobarar, wadda ta fara da misalin ƙarfe 2:00 na dare, ta jefa ’yan kasuwa cikin jimamin asarar dukiya mai tarin yawa da aka kiyasta ta kai miliyoyin naira. Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu, sun bayyana cewa gobarar ta bazu cikin sauri, inda ta riƙa laƙume kaya da kadarori kafin ’yan kwana-kwana su iso wurin. Ko da yake ba a tabbatar da musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu ’yan kasuwar na zargin cewa matsalar wutar lantarki ce ta haddasa...
    Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin sakataren kwamitin wanda dama shi ne mataimakin darakta na hanyoyin ruwa na cikin gida a wannan ma’aikata. Ministan ma’aikatar tattalin arziki na ruwa, Adegboyega Oyetola ne ya kaddamar da kwamitin da zai yi aiki tukuru domin  kare hatsurran kwale-kwale da kananan jiragen ruwa a cikin kasar. Ministan da yake Magana a wurin kaddamar da wannan kwamitin a birnin Abuja, ya yi kira da a yi...
    Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya bayyana cewa matarsa ta taɓa kawo masa ƙorafi game da cin zarafin da ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi mata. A cewarsa, rikicin ya fara tun lokacin da Natasha ta tsaya takarar kujerar Sanata a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, inda ta nemi kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya. Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano A lokacin, Akpabio yana riƙe da mukamin Ministan Neja Delta. “Da kaina na je na same shi na buƙaci ya bai wa matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotar da ke tsakaninmu. “Bayan mun tattauna sai...
    Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mandalari da ke Konduga a Jihar Borno, ta hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama. Gobarar, ta tashi da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu, 2025, ta bazu zuwa yankunan da ke da cunkoson jama’a, inda ta cinye matsugunan wucin gadi da kuma kayayyaki masu tarin yawa. Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga Hukuma ta kama ciyaman kan zargin badaƙalar filin N100m a Kano Sojojin da aka jibge a Konduga, sun kai ɗauki nan take bayan samun labarin tashin wutar. Sun haɗa kai da jami’an agaji da kuma al’ummar yankin domin shawo kan gobarar. Duk da haka, akwai fargabar...
    Kakakin Majalisar dinkin MDD Stephane Dujarric ya bada sanarwan cewa yana makaranta a Gaza fiye da 100,000 suka fara karatu a makarantu a yankin a ranar 23 ga watan Fabrayrun da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jami’in MDD yana fadar haka a jiya Alhamis kwanaki huda da fara karatu a yankin na Gaza, bayan tsekon da aka samu saboda yakin da HKI ta dorawa kasar na tsawon shekara guda da watanni. Dujarric ya bayyana cewa a halin yanzu makarantu 165 suka bude kofofin su ga yan makaranta a gaza, kuma ga mafi yawansu wannan shi ne karo na farko da suka shiga aji a cikin watanni 16 da suka gabata. Jami’an gwamnati a Gaza...
    “A karkashin Shugabancin Dantsoho, ya taimaka wajen ganin ana sauke sundukan kayan da aka yo jigilarsu a cikin sauki, musamman a Tashar Lekki wanda hakan ya taimaka, wajen rage cunkso a Tashar.” A cewar Mahukuntan Mullar. Mahukuntan Mullar sun kara da cewa, sun zabo Dantso ne, ganin cewa, shi ne, na farko da aka zaba a mukamin Shugaba na Kungiyar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya PMAWCA, inda zabarsa, ta kara daga kima da darajar Nijeriya, a fannin harkokin tafiyar da Tashohin Jiragen Ruwa, a yankin. A yayin da yake karbar babbar lambar yabon Mullar Dakta Dantsoho ya bayar da tabbacin cewa, zai kara zage damtse wajen shugabantar Hukumar, daidai da tsare-tsaren Miniatan bunkasa...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar. Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci. Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan...
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90% na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar. Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci. Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan...
    Damfarar da aka yi wa mutane ta hanyar tura kuɗi ta banki ya ninku sau uku zuwa Naira biliyan 52 a Najeriya. Alƙaluma ‘n Hukumar Kula da Tsarin Tura Kuɗi Tsakanin Bankuna (NIBSS) ya nuna a shekara huɗu da suka gabata aka samu wannan karin daga Naira biliyan 11 zuwa biliyan 52, Alƙaluman sun nuna a shekara shekarar 2024 an yi asarar Naira biliyan 52, kusan ninki biyar na Naira biliyan 11,2 da aka yi asara a shekarar 2020. Rahoton na NIBSS ya bayyana cewa masu damfarar sun yi yunƙurin sace Naira biliyan 86.4 a shekarar 2024.   The figure is coming on the heels of the latest GDP figures released by the National Bureau of Statistics showing a fourth...
    Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce tattalin arzikin ƙasar ya haɓaka da kaso 3.84 cikin 100 a zango na 4 na shekarar 2024. A cewar rahoton da hukumar NBS ta fitar a yau Talata, bunƙasar ta ɗara kaso 3.46 da aka samu a zango na 3 na 2024. An naɗa Obasanjo mai shiga tsakani a rikicin Kongo Manoman tumatir na tafka asara saboda faɗuwar farashi Alƙaluman game da zango na 4 na shekarar 2024 sun kuma ɗara kaso 3.46 cikin 100 da aka ba da rahoton samu a zango na 4 na 2023. “Ɓangaren ayyuka ne kan gaba a bunƙasar ta zango na 4 na 2024, wanda ya ƙaru da kaso 5.37 cikin 100 tare da ba da gudunmawar...
      An bukaci Majalisar Dokoki ta Kasa da ta kafa doka wacce za ta tanadi hukuncin kisa ga masu safarar da kuma masu shan miyagun kwayoyi, domin kare rayuwar ‘yan kasa. Wannan kiran ya fito ne daga shirin KAKAKI na FRCN Kaduna FM, inda masu kira suka bayyana ra’ayoyinsu a yayin tattaunawa da mai gabatar da shirin. Masu magana sun nuna damuwa kan illar safarar miyagun kwayoyi a kasar, musamman yadda yake shafar matasa, wadanda ake kallon su a matsayin shugabannin gobe. Alhaji Gaddafi Rigasa da Hajiya Aisha Mando sun jaddada bukatar hukumomin tsaro su kara zage damtse wajen yaki da wannan matsala, domin inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewa. Sai dai sun kuma ba da shawarar a farfado...
      dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka: Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta. Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi. Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya....
    Jami’an Tsaro a Jihar Sakkwato, sun kama babban mai yi wa Bello Turji safarar makamai, mai suna Hamza Suruddubu. Rahotanni sun bayyana cewar ana zarginsa da yi wa wasu maharan safarar makamai a jihar. An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida Wata majiya, ta shaida wa Zagazola Makama cewa Suruddubu ɗan yankin Gabashin Sakkwato ne, kuma ya daɗe yana safarar makamai daga jihar Zamfara zuwa sansanonin ‘yan ta’adda a Gabashin Sakkwato. “Shi ne babban mai yi wa ƙasurguman ’yan bindiga irin su Bello Turji, Boka, da Halilu Buzu safarar makamai,” in ji majiyar. Bincike, ya nuna cewa ba makamai kawai Suruddubu ke safara ba, har da...
    Ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta yi iƙirarin cewa wasu ’yan bindiga sun sace sama da shanu miliyan huɗu na mambobinta musamman a yankin Arewa maso Yamma. Shugaban Ƙungiyar MACBAN na ƙasa, Baba Usman ne ya bayyana hakan a yayin ƙaddamar da sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙungiyar na jiha a Jihar Kebbi. ’Yan bindiga sun kashe mutum 12, sun sace wasu a Zariya Hisbah ta rufe gidajen rawa a Katsina Ya ce, ɓarayin shanu na yawan kai wa Fulani makiyaya hari, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. Usman ya jaddada cewa, ana yawan sauya fahimtar Fulani makiyaya da kuma yin kuskuren sanya su a matsayin masu tayar da fitina, inda ya buƙaci jama’a su riƙa ganin su...
    Gwmanatin Tarayya ta haramta wa tireloli masu ɗaukar man fetur da nauyinsa ya kai lita 60,000 aiki a Najeriya daga ranar 1 ga watan Maris mai kamawa. Hukumar Albarkatun Man Fetur ta Kasa (NMDPRA) ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin taƙaita yawan haɗuran tirelolin man fetur da ke sanadiyyar asarar ɗaruruwan rayuka da dukiyoyi na miliyoyin kuɗaɗe. Hukumar ta ƙara da cewa zuwa ƙarshen wannan shekara ta 2025 za a haramta wa motoci masu ɗaukar man fetur lita 45,000 hawa titunan Najeriya. Ta bayyana cewa bayan wani taron da aka gudanar kan yawan haɗuran tirelolin man fetur da irin asarar da hakan ke haifarwa, masu ruwa da tsaki a harkokin mai da sufuri hukumomin tsaro da sauransu...
    Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya NBS ta ce alƙaluman hauhawar farashi sun koma kashi 24.48 daga 34.8 cikin 100 a watan Janairun da ya gabata. Wannan ne karon farko da hukumar ta NBS ta fitar da rahoton bisa sabon tsarin tattara alƙaluma da ta fara amfani da shi, abin da ke nufin da wuya a iya gane haƙiƙanin raguwa ko hauhawa a yanzu. Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu Alƙaluman sun nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ta kai 26.08 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Da yake yi wa manema labarai jawabi shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya faɗa ranar Talata cewa sun sauya tsarin ne saboda...
    Ana fargabar cewa gobara ta yi ajalin wata uwa da ’ya’yanta biyu a yankin Onipakala da ke Ƙaramar Hukumar Ondo West a Jihar Ondo. Bayanai sun ce musibar ta auku ne da tsakar daren Lahadi yayin da jama’a ke sharar barci, lamarin da ya jefa makwabta cikin zullumi. Saudiyya ta bai wa Kano da Abuja tallafin dabino albarkacin watan Ramadana Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe Aminiya ta ruwaito cewa, zuwa wayewar gari Litinin, matar da ’ya’yanta —Bukola da Ifeoluwa— sun ƙone ƙurmus a sakamakon gobarar. Wani maƙwabcinsu da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce tun tsakar dare gobarar ta tashi amma ana ji ana gani ta rutsa da mutanen uku...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa kokarin da makiya suke yi na haifar da sabani a tsakanin al’ummar kasar ta hanyar yi musu barazana ya ci tura. Babban tattakin da al’ummar kasar suka yi a ranar 10 ga watan Fabrairu ya nuna cewa barazanar makiya ba ta da wani tasiri a kan wannan kasa da kuma al’ummarta. Jagoran ya yi ishara da irin gagarumar fitowar al’ummar kasar a cikin jerin gwano da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci, wanda ya hambarar da azzalumar gwamnatin Pahlavi ta tsohuwar gwamnatin Amurka. Ayatullah Khamenei ya sake ba da misali da irin dimbin abubuwan da suka faru a lokacin zagayowar nasarar...
    Wani jirgin sojin Najeriya ya jefa wa fararen hula bom inda ya kashe fararen hula bakwai a yankin Yani  da ke Ƙaramar Hukumar Safana ta Jihar Katsina. Mamatan sun hada da mutum shida ’yan gida ɗaya, kamar yadda wani shaida ya bayyana. Hakan na zuwa ne bayan wasu jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda biyu da wani jami’in Rundunar Tsaron Al’umma na jihar (CWC) sun kwanta dama a yayin musayar wuta da ’yan bindiga a Ƙaramar Hukumar a ranar Asabar. Wani mazaunin Gundumar Zakka da ke Ƙaramar Hukumar, yankin da abin ya faru, ya bayyana cewa an yi arangamar ne bayan zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar ranar Asabar, inda ’yan bindiga suka shirya kai wa...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa. Ya kara da...
    Nijeriya na shirin shiga cikin jerin ƙasashen da ke ƙera motoci masu amfani da lantarki. Hakan na zuwa ne a da kokarin tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi na buɗe cibiyar bincike ta Tukur Buratai gabarar yin bincike wajen samar da na’urorin da ba za su ringa amfanin da makamashi ba. Cibiyar ta Tukur Burutai ta haɗa hannu da da kasar Sin domin saukaka aikin tare da kuma inganta yanayin yadda za a gudanar da binciken. Gidauniyar Buratai Ta Taya Giwa-Daramola Murnar Zama Shugaban Kungiyar Tseren Kwale-kwale Na Ondo Kingibe Ya Yaba Wa Tsare-tsaren Bunkasa Ilimi Ga Matasa Na Buratai Babban Manajan Daraktan cibiyar, Moses Ayom, ya bayyana nasarar da kasar Sin ta samu wajen...
    Rahoton ya ce an fara badakalar ne a ranar 10 ga watan Disamba a lokacin da kamfanin harhada magunguna ya samu sakon imel dake nuna wani mai sayar da shi, Accent Pharma, yana neman a biya shi wani sabon asusun ajiya na banki. Ba tare da sanin sakon imel din na yaudara ne ba, ana zargin kamfanin harhada magunguna ya aika Rs 11.76 lakh, kamar yadda PUNCH Metro ta fahimci. Wakilinmu ya ruwaito cewa kamfanin ya gano cewa an yi kutse ne bayan an biya kudin da kuma tantancewa. Wannan ya haifar da kwakkwaran bincike daga sashin damfarar intanet na kasar. Rahoton ya kara da cewa, “Masu bincike sun binciki email din da aka yi wa kutse zuwa Nijeriya inda...
    Wasu magidanta da suka mallaki wani zakara (Ricco) jinsin Bantam daga Bourgoin-Jallieu a sashen Isère na kasar Faransa, sun karɓi sammaci domin bayyana a gaban kotu sakamakon korafin da wani makwabcinsu ya yi game da carar zakaran. Korafin da suka yi ya hada da, rashin barci saboda karar zakaran yake yi a yayin carar, kamar yadda mai gabatar da ƙara ya ambata, wanda ya gayyaci masu zakara (Ricco) zuwa kotu a watan Janairun 2025. Kasuwanci: Yadda matan Arewa ke samun arziki daga cikin gidajensu Gurgu mai mata huɗu da bai yarda da yin bara ba Mutumin, wanda ya fi son a sakaya sunansa, yana daya daga cikin makwabtan masu ikirarin cewa, carar zakaran ba za a iya jure ta ba...
    Kungiyar masu sana’ar samar da manyan injuna ta kasar Sin ta bayyana a yau Juma’a cewa, masana’antar ta samu ci gaba mai inganci a shekarar 2024, biyo bayan shirin kasar na daukaka ingancin manyan injuna da ma dabarun raya masana’antar da aka dauka. A shekarar 2024, ribar da manyan kamfanonin samar da manyan injuna suka samu ya karu kan na 2023 da kaso 6 cikin dari. Manyan kamfanonin na nufin wadanda suke samun kudin shigar da ya kai yuan miliyan 20 ko fiye, a shekara. A bara, na’urorin samar da lantarki daga iska ne suka mamaye fiye da rabin kayayyakin samar da lantarki a kasar. A shekarar 2024, cinikin motoci masu amfani da makamashi mai tsafta ne ya dauki kaso...
    Tawagar ta tattaro hukumomi da suka hada da hukumar kula da yanayi (NiMET), hukumar kula da ayyukan ruwa, da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa karkashin kulawar ofishin mataimakin shugaban kasa. Wannan yana tare da hadin gwiwar ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai (OCHA).   A duk duniya, OCHA, wacce ke kula da CERF da Asusun Kula da Ruwa na Kasa (CBPFs) irin su Asusun Ba da Agajin Gaggawa (NHF), tana jagorantar matakai don taimaka wa miliyoyin mutane ta hanyar magance annoba kamar ambaliyar ruwa, fari, da kwalara.   A watan Oktoban 2024, CERF ta saki Dala miliyan 5 domin a kara kaimi wajen magance ambaliyar ruwa da kuma magance muhimman bukatu a jihohin Borno da...
    Hukumar tara haraji ta jihar Kano (KIRS) ta sanar da wani gagarumin shiri na kara yawan kudaden shiga na jihar zuwa sama da Naira biliyan 100 nan da shekarar 2025.   Shugaban hukumar Dr. Zaid Abubakar ne ya bayyana hakan a yayin da hukumar ke bitar ayyukan hukumar na shekarar 2024 da kuma tsare-tsarenta na shekarar 2025.   A cewar Abubakar, KIRS ta bullo da tsare-tsare na matsakaita da kuma na dogon lokaci domin bunkasa kudaden shiga na jihar.   Shirin tara kudaden shiga na matsakaicin zango na nufin tara sama da Naira biliyan 100 a shekarar 2025, inda ake sa ran za ta haura Naira biliyan 200 a shekaru masu zuwa.   Musamman ma, gwamnatin jihar tace tana son...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
    Karon Farko A Shekarar 2025: Turken Rarraba Hasken Wutar Lantarki Ya Fadi A Nijeriya
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ta kama wani matashi tare da wasu mutum uku kan zargin safarar harsasai daga Jos zuwa Abuja. Matashin ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun biya shi Naira 50,000 domin ya karɓo harsasai daga Jos zuwa Abuja. Majalisa na neman rushe ƙudirin ƙara kuɗin kira da data Noman rani ne zai kawar da yunwa a Yankin Tafkin Chadi — Zulum “Ni mazaunin Abuja ne. Makonni biyu da suka wuce, wani mutum ya aike ni domin karɓo masa harsasai a Jos zuwa Abuja. “Ya tabbatar min babu wata matsala da zan fuskanta, amma a hanya jami’an tsaro suka kama mu ni da wasu mutum uku,” in ji matashin. Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, yayin da yake holen waɗanda...
    Iraniyawa mazauna kasar Burkina Faso sun gudanar da bukukuwan murnar cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Ouagadougou. A wannan karon, kasashen biyu sun daukaka kyakkyawar dangantakarsu da aka gina a shekarar 1984.   Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a birnin Ouagadougou, Mojtaba Faghihi, wanda ya halarci bikin, ya bayyana cewa juyin juya halin Musulunci a Iran a shekara ta 1979 ya ba da damar “yantar da mu daga tsoma bakin siyasa na kasashen waje da wawashe dukiyarmu”. A cewarsa, Iran ta samu nasarar dakile makircin makiya da kuma wuce gona da iri na sojojin kasashen waje, da takunkumi da kuma ta’addanci. A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya...
    Kungiyoyin da suke dauke da makamai sun kashe fararen hular da ba su gaza 55 ba a wani hari da su ka kai wa wasu kauyuka da sansanin ‘yan hijira a Arewacin DRC. Mahukunta a yankin na Arewacin DRC sun ambaci cewa wasu masu dauke da makamai na kungiyar CODECO sun kai wa wasu kauyuka da suke yankin Djaiba hare-hare a gundumar Ituri a  jiya litinin da dare. Bugu da kari masu dauke da makaman sun kai hari a cikin sansanin ‘yan hijira da suke a cikin wannan yankin kamar yadda shugaban sansanin Antoinnette Nzale ya fadawa manema labaru. Ita dai kungiyar CODECO  gamayya ce ta kungiyoyin da suke dauke da makamai da su ka fito daga kabiluar Landu, manoma....
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Sirrin nasarar da Iran ta samu shine haɗin kai da kasancewar mutane a cikin kowane fagen neman ci gaba Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa juyin juya halin Iran ya samu nasarar korar azzalumai daga kasar Iran ce, kuma sirrin ire-iren nasarorin da aka samu bayan nasarar juyin juya halin Musulunci shi ne kasantuwar kasa ta taka rawar al’umma da kyakkyawar hadin kai. Shugaba Pezeshkian ya kara da cewa a jawabin da ya gabatar a karshen jerin gwanon na tunawa da nasarar juyin juya halin Musulunci a birnin Tehran: Ba za su taba mika wuya ga kasashen waje ba. Ko da yake Iran bata neman yaki, amma tun ranar farko makiya suke...
    Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga wayewar garin jiya Litinin ne, al’umma sun fito kan manyan hanyoyi kasa a jihohi kasar tamkar kwararan kogi don gudanar da murnar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, tare da tabbatar da aniyarsu ta yi riko da manufofin juyin juya halin na Musulunci da kuma sabunta mubaya’arsu ga tsarin Jamhuriyar Musulunci.
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa wannan ziyara ta gwamnan, za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da Bankin na Duniya.   Cikin jawabin sa a wurin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa dangantakar ta Bankin Duniyar.   “Ina so in fara da nuna godiya ta ga Bankin Duniya game da tallafin da ya ke bayarwa a jihar mu. Mun jingina da manufofin Bankin Duniya wajen inganta rayuwar al’ummar mu kawar da talauci da ci gaban ayyukan inganta rayuwa.   “Muna sane da ƙalubalen da muka fuskanta, wanda ya shafi gudanar da ayyukan ci gaba a jihar Zamfara, musamman waɗanda suka samu matsala wajen aiwatarwa, sakamakon yanayin da aka shiga. Amma, lallai babu shakka muna...
    Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a gare shi) ya jagoranta, a cikin wadannan shekaru da dama, juyin juya halin Musulunci ya fuskanci makirce-makirce masu yawa da cikas, kuma ya samu gagarumar nasara, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne hambarar da gwamnatin sarki Shah da kasashen yammacin duniya suke goya masa baya, kamar yadda Iran bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci ta yi nasarar kafa gwamnati da samar da ginshikanta da...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya yi kira da a kafa kawancen duniya da dukkanin kasashen musulmi za su shiga ciki, domin taimakawa mutanen Gaza, da sake gina yanki, tare da cewa, kasashen musulmi kadai za su iya sake gina yankin na Gaza tare da dawo da rayuwa a cikinsa. A ganawar da ya yi da mambobin majalisar jagoranci ta kungiyar Hamas, anan Tehran ya yi jinjina ga shahidan kawancen gwagwarmaya, ya kuma yi murna akan nasarar da ‘yan gwgawarmaya su ka samu akan ‘yan sahayoniya. Shugaban kasar ta Iran ya kara da cewa; Nasarorin da mutanen na Gaza su ka samu, sun hana makiya ‘yan sahayoniya cimma manufofin da su ka shata, duk da cewa adadin shahidan da aka...
    A Nijar an yi bikin cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran a Yamai babban birnin kasar, bikin da ya samu halartar ‘yan siyasa da jakadu da jami’an diflomasiyya da ‘yan jarida. Manyan baki da suka halarci bikin sun hada da ministan harkokin wajen Nijar, magajin garin Yamai da kuma wakili na musamman na Firaministan Nijar. A yayin wannan biki, jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Nijar Ali Tiztak ya gabatar da jawabi, inda ya yi ishara da irin nasarorin da Tehran ta samu cikin shekaru arba’in da suka gabata. Ali Tiztak ya ci gaba da cewa, duk da takunkumin zalinci da kalubalen da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take fuskanta tun ranar farko bayan nasarar...
    “Ina so na fara da godiya ga Bankin Duniya kan tallafin da yake ci gaba da bai wa jiharmu. Mun daidaita manufofin ci gabanmu da manufar Bankin Duniya na kawar da talauci da inganta ci gaba mai dorewa.” “Mun kuma lura da kalubalen tsaro da a baya suka yi tasiri wajen aiwatar da ayyuka a jihar Zamfara, musamman wadanda suka kawo cikas ga cimma burin da aka sanya a gaba. Duk da haka, muna samun ci gaba yayin da ake fuskantar ƙalubalen, kuma abubuwa suna komawa daidai.” “Mun inganta matakan tsaro ta hanyar kwararan matakai da jihar ta dauka na inganta tsaro da kara daukar matakan dakile barazanar tsaro.” “Gwamnatinmu ta dukufa wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya gana ta tawagar shoura ta kungiyar Hamas a safiyar yau Asabar a nan Tehran inda ya bayyana cewa mayakan kungiyar sun sami nasara a kan Amurka da HKI a yakin da suka dora masu na tsawon watanni 15. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Imam Sayyid Aliyul Khaminae yana cewa tsagaita wuta da aka samu bayan wannan lokaci mai tsawo na fafatawa yayi dai-dai. Tawagar shuraa ta Hamas din dai sun hada da shugaban riko na kungiyar Khalil Al-Hayya, shugaban majalisar shoora ta kungiyar Muhammad Ismail Darwish da sauransu. Jagoran ya kara da cewa nasarar da mutanen Gaza suka samu a kan Amurka da kawayenta misdaki nan a...
    Madara muhimmin abinci ne da ake bukata domin samun sinadarai masu ginawa da ƙara ƙarfi da lafiyar jiki. Bincike ya nuna cewa mutane biliyan shida ne ke shan madara a duniya, wanda ya sa shan madarar saniya da kiwon dabbobi ya zama wani vangare na rayuwar ɗan adam. Dubban mata Fulani suna samun kuɗaɗen shiga ta hanyar sayar da madara ga ɗaiɗaikun mutane ko jama’a ko ’yan kasuwa, waɗanda suke sha ko sarrafa shi domin amfanin kasuwanci. Lura da muhimmancin madara ga rayuwar ɗan Adam da kuma ƙoƙarin rage haɗarin da ke tattare da shan ta, Hukumar Haɓaka Noma da Kiwon Dabbobi ta Jihar Kano (KSADP) ta zuba jarin Dala miliyan 8.03 don gina cibiyoyi 100 na tattara madara...
    Masana’antar kera kayayyakin laturonin sadarwa ta kasar Sin ta samu ci gaba mai sauri a shekarar 2024, inda karin darajar manyan kamfanoni a fannin ya karu da kashi 11.8 cikin dari bisa ta shekarar 2023, kamar yadda bayanai suka nuna a hukumance a jiya Alhamis. Adadin kudaden shiga na manyan kamfanoni na wannan fanni ya karu da kashi 7.3 cikin dari a bara, idan aka kwatanta da shekarar 2023 zuwa yuan triliyan 16.19 kimanin dalar Amurka tiriliyan 2.26. a cewar bayanai daga ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin. Hakazalika, alkaluman da aka fitar sun nuna cewa, a wannan lokaci, adadin ribar da wadannan kamfanoni suka samu ya karu da kashi 3.4 cikin dari bisa ta shekarar 2023 zuwa...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gana da tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da wata tawagar kwamandojin sojojin sama da na tsaron sararin samaniyar kasar na sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a safiyar yau Juma’a a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan tunawa da kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci. Taron na yau ya zo daidai da zagayowar kwanaki goma na samun nasarar juyin juya halin Musulunci, kuma taron tunawa da mubaya’a mai dimbin tarihi ga Imam Khumaini (Allah ya kara masa yarda) a ranar 8 ga watan Fabrairun shekara ta 1979. Don haka a safiyar...
    Wata gobara da ta tashi a Ƙauyen Zago da ke Ƙaramar Hukumar Danbatta a Jihar Kano, ta ƙone gidaje, amfanin gona, da dabbobi, lamarin da ya janyo wa mazauna ƙauyen asara mai tarin yawa. Gobarar, ta fara ne da safiyar ranar Laraba, inda ta ƙone gidaje da dama tare da lalata hatsi da sauran amfanin gona. An yi garkuwa da tsohon Shugaban Hukumar NYSC Janar Tsiga Ɗan firamare ya je makaranta da bindiga yana barazanar harbe ɗalibai Har ila yau, ta kashe shanu da sauran dabbobi mallakin mazauna ƙauyen. Wasu daga cikin mazauna ƙauyen, Hayyo Zago da Abdulrahman Zago, sun ce gobarar ta ci gaba da ci har zuwa rana kafin jami’an kashe gobara su iss, inda suka yi nasarar...
    Kasar Afirka Ta Kudu ta ga yadda Palasdinawa suka jajirce wajen kare kansu daga HKI ne, ya sa ta gurfanar da HKI a gaban kutun ICC don kawo karshen kissan kiyashin da yahudawan suke masu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya kara da cewa, kasar Afirka ta gudu dai tana dade tana goyon bayan masu gwagwarmayan neman yencinsu a duniya daga ciki da da kasar Falasdinu da aka mamaye. Har ila yau da kuma ganin tarihin da kasar take da shi, na yaki da wariyar launin fata a kasar, duk sun hadu sun karfafa ta wajen daukar wannan matakin kan HKI. Jakadan kasar Afirka ta kudu a nan Tehran, Francis Moloi ne ya fadawa kamfanin dillancin labaran ‘Iran...
    Bisa bayanan da aka samu daga wani dandali na shafin intanet, ya zuwa yau Talata, jimillar kudaden shiga da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a gidajen sinima a shekarar 2025 ta zarce kudin Sin yuan biliyan 11, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.5. Bugu da kari, adadin masu kallo a lokacin bikin bazara na shekarar 2025 ya zarce miliyan 170, wanda ya karya tarihin baya na yawan masu kallo da aka taba samu lokacin bikin bazara, a tarihin fina-finan kasar Sin. Har ila yau, bisa la’akari da yawan tikitin da aka sayar a shekarar 2025, yawan kallon fina-finan kasar Sin ya zarce na Arewacin Amurka, inda a halin yanzu ya zama na daya a duniya. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza...
    Alkaluman da ma’aikatar cinikayya ta Sin ta fitar baya-bayan nan na cewa, a shekarar bara, darajar shige da ficen cinikayyar ba da hidimomi ta Sin ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 7.5, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.034, wanda ya karu da kashi 14.4 cikin dari bisa makamancin lokaci na shekarar 2023, ma’aunin ya kai wani sabon matsayi a tarihi. Shugaban hukumar kula da cinikayyar ba da hidimomi ta cibiyar nazarin hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki na kasa da kasa ta ma’aikatar kasuwanci ta kasar, Li Jun, ya bayyana cewa, al’adun Sin masu kayatarwa na ci gaba da jawo hankalin masu yawon bude ido su zo kasar Sin don yawon shakatawa, da alamar zai inganta habaka ma’aunin cinikayyar ba...
    Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.14, wanda ya kafa sabon tarihi. Ya zuwa yanzu dai, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a 2025 yana kan gaba a kasuwar fina-finan duniya da jimillar yuan biliyan 10.121, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.4 (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
    La’anannen dan siyasar Sweden din nan mai kyamar addinin Islama, Rasmus Paludan, ya sake tozarta kur’ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark. Paludan mai shekaru 43 shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Denmark Stram Kurs, ya sake haifar da cece-kuce ta hanyar aikata wannan aika aika a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Denmark. Wani faifan bidiyo da aka watsa a dandalin sada zumunta ya nuna Paludan yana wulakanta kur’ani mai tsarki, matakin da ya yi matukar bakanta ran musulmin duniya. Matakin na Paludan ya zo ne bayan kisan da aka yi wa wani dan kasar Iraki mai suwan Salwan Momika wanda ya walakanta Al’Kur’ani a gidansa da ke birnin Sodertalje a ranar 30 ga watan Janairu. Matashin mai...
    Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024 da Hisbah ta yi sanarwar zuwa yanzu, an samu ɓullar aƙalla bidiyoyi 10 daga jihar da suka tayar da kura a kafofin sada zumunta, musamman TikTok, ciki har da na tsiraici. Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara Ɓullar bidiyon tsiraicin fitattun ’yan Tiktok irin su Hafsat Babaiana da Hafsat...
    Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran,  shekaru 46 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Asabar ce shugaban kasar Iran, Masuod Pezeshikyan tare da majalisar ministocinsa suka kara sabonta bai’a wato marigayi Immam Khomani (q).   Labarin ya kara da cewa Sayyid Hassan Khomani, jikan Imam(q) wanda kuma yake kula da hubbaren nasa ne, ya tarbi shugaban kasar ya kuma jagorance su zuwa hubbaren kakansa Imam Khumaini(q). Imam Khomani (q) ne ya jagoranci mutanen kasar...
    Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga  babban birnin kasar Kinsasha. Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu  ita ce, muna yin yaki ne saboda kishin Congo, ba muna yaki ne saboda samun ma’adanai ba, babu wani dalili na daban da ya sa muke yaki.” Da akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa, ‘yan tawayen na M 23 sun kama hanyar zuwa Bukavu, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a yankin. Nangaa ya ce babu wata gwamnati tsayayya a kasar Congo, domin Tshikedi ya riga ya...
    Bugu da ƙari, Naira miliyan 267.6 an ware su domin shirye-shiryen Addinin Musulunci da tallafa wa waɗanda suka Musulunta, yayin da Naira miliyan 589 za a yi amfani da su wajen bincike kan harkokin tsaro da kuma yaƙi da bara a tituna. Jimillar kasafin kuɗin Jihar Kano na shekarar 2025 ya kai Naira biliyan 719.75, wanda ya karu da kashi 31 daga asalin kuɗin da aka gabatar da farko, kuma ya fi na shekarar 2024 da kashi 65.
    Alkaluma daga ma’aikatar kudi ta kasar Sin sun nuna cewa, kudin shigar kamfanoni mallakin gwamnatin Sin ya karu da kaso 1.3 a shekarar 2024. A cewar ma’aikatar, kamfanonin sun samu karuwar yuan triliyan 84.72, kwatankwacin dala triliyan 11.7 na kudin shiga a 2024. Jimilar ribar da suka samu a shekarar 2024 kuma, ta karu da kaso 0.4 zuwa triliyan 4.35 a kan na shekarar 2023. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Al’ummar kasar Iran sun fara gudanar da bukukuwan cika shekaru 46 da juyin juya halin Musulunci na shekara ta 1979, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya, wanda ya kai ga kafuwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Kamar kowace shekara, ana fara bukukuwan ne da karfe 9:33 na safe, na ranar 1 ga Fabrairu, 1979, ga jirgin saman Air France da ya dawo da Imam Khumaini gida daga gudun hijira na sama da shekaru 14 wanda ya kai ga kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. A yayin bukukuwan al’ummar Iran suna halartar taruka daban-daban har zuwa zagayowar ranar 22 ga watan Bahman wato 10 ga watan Fabrairu, wato ranar tunawa da juyin juya halin Musulunci. Juyin juya halin Musulunci ba wai kawai...
    Hukumar kwastam ta kasar Sin ta ce an samu ci gaba sosai a yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashe da yankuna 160 na duniya a shekarar 2024. Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta fitar ya karu da kaso 7.1 a shekarar, wanda ya kai yuan triliyan 25.45, kimanin dala triliyan 3.55, shekaru 8 a jere ke nan ana samun wannan ci gaba. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Adadin jigilar fasinjoji da jiragen kasa masu zirga zirga cikin biranen kasar Sin suka yi a shekarar 2024, ya karu da kimanin biliyan 2.8 ko kuma kaso 9.5 a kan na shekarar 2023. A cewar ma’aikatar kula da sufuri ta kasar, a baran, jimilar jigilar fasinjoji da jiragen suka yi ya kai biliyan 32.24. Zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2024, tsawon tafiyar da jirage 325 suka yi a fadin birane 54 na kasar Sin, ya kai kilomita 10,945. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya. Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu. Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje A ranar Talata kuma, shugaban Angola...
    An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC. Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare. Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye. DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen...
    An zaƙulo gawarwakin mutane 19 bayan wani jirgin fararen hula da jirgin sojoji sun yi karo a sararin samaniya a ƙasar Amurka. A cikin daren Laraba ne wani jirgin Kamfanin American Airlines dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwaftan sojojin Amurka, ƙirar Black Hawk, mai ɗauke da mutane a birnin Washington DC. Jiragen da suka yi karo sun auka a cikin kogin Potomac, inda a halin yanzu ake aikin ceto, tun baya aukuwar hatsarin jiragen daga misalin ƙarfe 9 na dare. Jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa jirgin fasinjan na dauke da iyalai da kuma tawagar ’yan wasa Skating, bayan sun kammala atisaye. DR Congo: Sojoji sun ƙaddamar da gagarumin hari kan ’yan tawayen...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna. Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi hare-hare. Sojoji sun ƙwato tarin makamai a Zamfara Tankar mai ta sake fashewa a Neja Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja a ranar Talatar nan, mai magana da yawun rundunar, Benneth Igweh, ya ce sun samu nasarar ce ta hanyar bayanan sirri, inda suka cafke wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Igweh ya bayyana...
    Wani katafaren wurin zubar da shara da aka tanada a wajen Kaduna ya koma wata babbar sana’ar kasuwanci inda ‘yan gwangwan ke amfani da gurbataccen ruwan najasa domin amfanin Noma.     Wata Kungiyar ‘yan jarida ta ziyarci al’ummar Katanga da ke karamar hukumar Chikun a jihar Kaduna inda aka fara gudanar da wannan aiki inda suka gano cewa kimanin ‘yan gwangwan 150 ne suka tsunduma kansu domin karfafa tattalin arziki a wurin da ake jibge sharar.   Jama’a na yin tururuwa zuwa wurin zubar da sharar na Katanga wanda shi ne babban wurin da gwamnatin jihar ta amince da sharar don tabbatar da tsaftar muhalli.   Mallam Zubairu shi ne shugaba, ya shaidawa tawagar ‘yan jarida da sauran kungiyoyin...
    A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano Shugaba Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) kuma shugaban kwamitin tsakiya na sojojin kasar ya kara da cewa, “a cikin shekarar dabbar Dragon, mun nuna kuzari da ruhi mai karfi na iya aiwatarwa. Mun...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
۱