2025-04-13@10:23:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 366

«Falasdinawa a yankin»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A gobe Litinin 24 ga watan Maris ne tawagogin masu tattaunawa na kasashen Amurka da Rasha zasu hadu a birnin Rayida na kasar Saudiya don ci gaba da tattaunawan da suka fara a yan makonnin da suka gabata dangane da yakin da ke faruwa a Ukraine, shekaru fiye da 3 da suka gabata, da kuma dangantaka a tsakanin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto Yury Ushakov mai bawa shugaba Putin shawara kan al-amurin siyasa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa Sanata Georgy Karasin ne zai jagoranci tawagar masu tattaunawa ta kasar Rasha sannan ta kasar Amurka an rika an samar da tawagar, wasu zata hadu da na Rasga a gobe litin a birnin...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
    A kwanakin baya, bankin Deutsche, banki mafi girma na kasar Jamus ya yi bayani game da yanayin kashe kudi ta kasar Sin cewa, karin Sinawa suna kara son kashe kudi. Bisa sabon rahoton da bankin ya gabatar, an ce, idan aka kwatanta da na shekarar bara, yawan masu kashe kudi na kasar Sin yana karuwa, kashi 52 cikin dari na wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu a binciken sun ce suna son kara kashe kudi, adadin da ya kai matsayin koli a shekara daya da ta gabata. Kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta gabatar ita ma ta shaida wannan yanayi, a farkon watanni biyu na shekarar bana, yawan kudin kayayyakin da aka sayar a kasar Sin ya kai Yuan triliyan 8 da...
    An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne. A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana....
    KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin  Istanbul. Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aa yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa. Kamfanin dillancin labaran “Reusters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa. Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa...
    “Bayan nazari da tattaunawa da gwamnati, Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad ya amince da gudanar da wannan gagarumin biki,” in ji shi. Sanarwar ta ƙara da cewa za a fitar da cikakken jadawalin shirye-shiryen hawan nan gaba kaɗan, tare da fatan Allah Ya sanya ayi bikin lafiya. A tarihi, Hawan Daushe yana da muhimmanci sosai a al’adun Bauchi, inda sarakuna da masu riƙe da mukamai ke hawa dawakai cikin shiga ta alfarma, tare da nuni da al’adun gargajiya. Hakan yana jan hankalin jama’a da yawon buɗe ido daga sassa daban-daban. Masarautar Bauchi ta jaddada cewa ba a bayyana haƙiƙanin labari ba, kuma kwamitin da ke kula da hawan ne ya nemi a soke bikin da farko. Sai dai bayan shawarwari, yanzu...
    Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta. Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema a Amahoro. Wasan shi ne zagaye na biyar a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya da za a buga a shekarar 2026, Nijeriya na matsayi na 4 a rukunin C na gasar da maki 6 a wasanni 5, sai Afrika Ta Kudu dake jan ragamar rukunin, ƙasar Benin ta biyu sai Rwanda dake matsayi na uku. Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An gudanar da Sallar Juma’a a mako na uku na watan Ramadan a Masallacin Al-Aqsa, duk kuwa da tsauraran takunkumin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta dauka, tare da halartar Palasdinawa 80,000. Kamfanin dillancin labaran Al-Naba y bayar da rahoton  cewa, dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma’a ta uku na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa, duk da matakai na kawo cikas da sojojin mamaya na Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka dauka da kuma yanayin sanyi da ruwan sama a birnin Kudus. Hukumar kula da lamurran addinin Musulunci a birnin Kudus ta bayar da bayanin cewa, masallata 80,000 ne suka gudanar da sallar Juma’a ta uku na watan Ramadan a masallacin Al-Aqsa. Sheikh Khalid Abu Juma, limamin masallacin Al-Aqsa, ya...
    Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu da gaggauta janye dakatarwar da ya yi wa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin jihar. Da yake magana a madadin ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya ce babu wani dalili da ya dace da zai sa shugaban ƙasa ya ayyana dokar ta-ɓaci a jihar. Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Ya bayyana cewa, kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadi ayyana dokar ta-ɓaci ne kawai a lokuta na matsanancin rikici kamar yaƙin basasa, ko rushewar doka da oda, wanda a cewarsa babu ɗaya daga cikinsu da ya faru a Jihar Ribas. NEF, ta zargi Gwamnatin Tarayya...
    Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar. Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata. Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa...
    Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma  cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da ka’idojin shari’a a  kotunan manyan laifuka na kasar. Har ila yau cibiyar ta ce, bayan kammala tattara bayanai a zango na farko, za kuma ta bude shafi na gaba domin kara samun wasu bayanan da za su tabbatar da cewa an yi wa Isra’ilawan hukunci a cikin kasashen duniya, musamman masu dauke da zama ‘yan kasashe biyu. Wani shiri da wannan cibiyar take da shi,shi...
    An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa.   Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin.   A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa.   Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
      Cibiyar Bincike Kan Harkar Noma (IAR) tare da hadin gwiwar Hukumar Yada Sakamakon Bincike da Wayar da Kan Manoma ta Kasa (NAERLS), Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, sun shirya taron kwana guda a Kaduna domin masu ruwa da tsaki kan aikin bunkasa noman dawa a Najeriya.   Taken taron shi ne: “Gabatarwa da Tattaunawa Kan Amfanin Sabbin Nau’ikan Dawa Masu Jure Sauyin Yanayi Domin Rage Talauci da Inganta Abinci a Najeriya.”   Daga cikin manyan abokan aikin akwai Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Kungiyar Manoman Dawa da Masara ta Najeriya, da Tarayyar Turai (EU), da sauransu. A jawabin sa, Mataimakin Daraktan NAERLS, Farfesa Muhammad Musa Jaliya, ya ce babban burin taron shi ne tabbatar da dorewar sabon...
    Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa babu wata gamayyar ’yan adawa da za ta iya hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu lashe wa’adi na biyu a zaɓen 2027. Ya yi wannan jawabi ne domin mayar da martani ga sabuwar haɗakar ’yan adawa da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da wasu shugabanni suka kafa. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas A yayin taron manema labarai da Atiku ya gudanar a Abuja a ranar Alhamis, ya soki yadda Tinubu ke tafiyar da mulki, musamman batun ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka...
    Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe mulki daga hannun jam’iyya mai ci. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati Da yake jawabi ga manema labarai tare da wasu ’yan adawa a zauren taro na ‘Yar’adua Center da ke Abuja a ranar Alhamis, Atiku ya ce an yi taron ne don sake samar da wasu ‘yan adawa kafin babban...
    Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A Ribas? Ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas yana nufin Gwamnatin Tarayya ta ƙwace ikon jihar, kuma hakan na iya kawo cikas ga harkokin siyasa da ci gaban jihar. Masana doka da ‘yan adawa na ganin cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama wata hanya ta take haƙƙin masu mulki da aka zaɓa a jihar. Tun bayan ɗaukar wannan mataki,...
    Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan...
    Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da jiragen ruwan yake daga tekun medeteranina sun cilla wuta kan garuruwan Beit –Lahia, Rafah da kuamKhan Yunus inda suka kashe da dama ko suka kaisu ga shahada. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun sake mamayar yankin Netzarim wanda ya raba arewa da kudancin zirin gaza a yau Alhamis. Ya zuwa yanzu yawan falasdinawa da suka yi shahada ya kai 49,547 tun...
    Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma  Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga doron kasa. Tun ranar Asabar da ta gabata ce sojojin Amurka da Burtaniya wadanda suke da jiragen yakinsu a cikin tekun maliya da wasu wurare a yakin suka fara kaiwa kungiyar hare-hare saboda goyon bayan ga HKI. Kafin haka dai kungiyar Ansarullahi ta bawa HKI kwanaki huda ta kawo karshen kofar ragon da ta yiwa falasdinawa kimani miliyon biyu a gaza, inda suka hana shigowar...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa duk abinda HKI da babbar kawarta Amurka zasu yi don fiddasu daga kasarsu ba zai kai ga nasara ba da yardar All… Tun shekara 1948 ne kasar Burania a lokacin, wacce ta mamaye kasar Falasdinu ta mikawa yahudawan Sahyoniyya kasar Falasdinu, sannan suka kara mamayar kasar bayan yakin shekara 1967. Inda yahudawan suka mamaye har da gabacin birnin Qudus sannan sun ginawa yahudawa...
    A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun jama’a, da sauran dabaru da tsare-tsare na kwarewar aiki da za a samar a jihar. Hakika wannan kawance zai fa’idantar sosai saboda yadda yankin na arewa ya kwashi tsawon wasu shekaru yana kaka-ni-ka-yi da matsalolin dake tarnake ci gabansa sakamakon mummunar matsalar tsaro musamman ma a jihar Zamfara wadda ta zama babbar tungar ’yan bindiga. Kwararru a fannin sha’anin tsaro, sun sha nanata cewa matukar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    MAfi yawancin mambobin kwamitin tsaron sun yi tir da harin da sojojin HKI su ka kai wa mutanen Gaza a cikin daren shekaran jiya wanda ya yi sanadiyyar shahadar fiye da Falasdinawa 400.  Wakilin kasar Rasha a MDD  ya bayyana cewa; Sake bude yaki a Gaza, yana nufin korar Falasdinawa daga kasarsu” ya kuma jaddada cewa; “  Wajibi ne ga kwamitin tsaro ya yi duk abinda zai iya yi, domin sake tsayar da wutar yaki, bai kuma kamata a ce an sake maimaita kurakuren baya ba. Shi kuwa wakilin kasar Aljeriya a MDD, ya bayyana ya zargi HKI da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki, yana mai jaddada cewa; Wannan lokaci ne da hukunta masu laifi, domin babu wanda...
     Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu. Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus. A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa; Sojojin Amurka suna da shirin kai hare-hare ta kasa a cikin yankin Gaza. Jaridar “Wall Street Journal” ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya za su ci gaba da zama a yankunan da su ka shiga a cikin Gaza, sannan kuma su kai wasu sabbin hare-hare ta kasa.
    Shugaban Majalisar Dattawan Arewa (NEF), Farfesa Dahiru Ango Abdullahi Yakawada, ya yi murabus daga sarautar Magajin Rafin Zazzau. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ya yi murabus ne daga sarautar Magajin Rafin Zazzau saboda shekarunsa da suka ja. Hamas ta ɗora alhakin harin da Isra’ila ta kai a kan Amurka Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji Wakilinmu ya ruwaito cewa a yanzu ƙaninsa, Alhaji Shehu Abdullahi Yakawada ne zai gaje shi a wannan kujera ta hakimanci. Farfesa Ango Abdullahi yana ɗaya daga cikin mazan jiya da suka yi ragowa a Nijeriya. Farfesa Dahiru Ango Abdullahi ɗaya ne daga cikin dattawan da al’umma suke buƙata musamman a wannan zamani. Yana ɗaya daga cikin masu bayyana ra’ayin su a kowanne irin yanayi...
    A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar. Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba...
    HKI ta keta yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a jiya inda ta kai hare-hare masu yawa, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 300 ya zuwa safiyar yau. Tashar talanijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a kan yankunan zirin Gaza da dama, kuma yawan mutanen da suka yi shahada ya zuwa yanzu ya kai 342 kumamafi yawansu mata da yara ne. Labarin ya kara da cewa a garin Khan Yunus na kudancin Gaza jiragen yakin HKI sun kashe falasdinawa 77 sannan falasdinawa akalla 20 suka kashe a birnin Gaza. SAMA kamfanin dillancin labaran Falasdinawa ya bayyana cewa daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu, kuma har yanzun ana neman wasu a wuraren...
    A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa dole ne Rasha ta mayar da yankunan da ta ƙwace. Tun a shekarar 2014, Rasha ta ƙwace yankin Crimea, sannan a shekarar 2022 ta mamaye wasu yankuna huɗu na gabashin Ukraine. Yanzu dai ana fatan wannan tattaunawa za ta kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana ci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
     Rahotanni Daga Gaza sun ce adadin Falasdinawan da su ka yi shahada da safiyar yau sun haura 200 Wata sanarwar da ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta fitar a yau Talata ta ce; Adadin shahidan sanadiyyar sabbin hare-haren HKI sun kai  244.  Sai dai har yanzu ba a kammala tantance adadin adadin shahidan ba, da kuma wadanda su ka jikkata. Gabanin wannan harin na safiyar yau, an bayyana cewa fiye da Falasdinawa 150 ne su ka yi shahada tun bayan tsagaita wutar yaki. Babban jami’i mai kula da harkokin watsa labaru a yankin Gaza Isma’ila Sawabita ya sanar da cewa; Tun daga tsagaita wutar yaki a ranar 19 ga watan Janairu zuwa yanzu adadin Falasdinawa da su ka yi shahada...
    Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali. Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada. Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu. Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta...
    Sojojin HKI sun ci gaba da keta hurumin yarjeniyan tsagaita budewa juna wata tsakaninta da Gaza inda a jiya Lahadi kadai ta kashe Falasdinwa 14 a wurare daban daban a yankin. Tashar talabijin ta Almayadden ta kasar Lebanon ta bayyana cewa yawan shahidai a kan tafarkin Kudus a Gaza ya kai 48,872 da kuma wadanda suka ji rauni tun fara yakin ya karu zuwa 112,032. Dan rahoton tashar al-mayadeen ya bayyana cewa a jiya Lahadi bafalasdiniya guda ta yi shahada a cikin gidanta a sansanin yan gudun hijira na Nusairat a lokacinda sojojin yahudawan suka bude wuta a kan gidanta. Rahoton ya kara da cewa wani jirgin yakin da ake sarrafa shi daga nesa ya bude wuta kan wasu Falasdinawa...
    Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa. Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Dangote. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, Shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan ɗaya ne ga ‘yan Nijeriya...
    An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare da kafa wuraren bincike domin magance matsalar rashin tsaro da ta biyo bayan kisan wata amarya mai shekaru 22, Zainab Ibrahim. An yanke wannan shawara ne a taron da aka gudanar a Hadejia, wanda ya haɗa jami’an majalisar masarautar da hukumomin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kirikasamma. Sojoji sun kashe ’yan bindiga 31, sun lalata sansaninsu a Katsina HOTUNA: NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye a cikin carbi da takalma Manufar taron ita ce samo mafita ga matsalolin tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Da yake jawabi a madadin majalisar masarauta, Galadiman Hadejia, Usman Abdul’aziz, ya nuna damuwa matuƙa game da yawaitar hare-haren da ake kai wa jama’a....
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran tana da nufin fadada shi. A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands yay aba da yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake bunkasa. Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da...
    Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta  Hamas ta yi Allawadai da Hare-haren Amurka da Birtaniya akan kasar Yemen Kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas ta fitar da bayani na yin tir da hare-haren da jiragen yakin Amurka da Birtaniya su ka kai wa Birnin San’aa a jiya Asabar da dare. Ita ma kungiyar Jihadul-Islami ta fitar da bayani na yin Allawadai da Amurka saboda harin da ta kai wa Yemen din, tana mai bayyana abinda ta aikata da cewa abin kunya ne da nuna goyon bayan ga laifukan da HKI take aikatawa akan al’ummar wannan yankin. Kungiyar Jiahdul-Islami ta kuma yi jinjina ga kasar Yemen saboda yadda su ka tabbatar da jarunta ta asali irin ta Larabawa da musulmi wajen nuna goyon bayan...
    Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya. An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar. A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar. “An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar...
    Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
    Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya. Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci. A...
    Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu. Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta. A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin...
    Takardar da aka yi nazari a karshen watan Janairu ta nuna cewa a watan Fabrairun 2025, an ware shirin samar da mai na kan naira zuwa jirgin dakon mai hudu ne kawai, rukuni hudu zalla, kuma a watan Maris, dakon man biyu ne kawai aka yi da ya kai ganga 950,000 (ganga miliyan 1.9 ga watan). Wannan yana wakiltar rabon ganga 61,290 a kowace rana kasa da makasudin 385,000 bpd a karkashin tsarin. Karancin samun danyen mai ya tursasa wa matatar man Dangote garzaya wa kasashen waje domin neman danyen man. A baya-bayan nan kamfanin ya samu gangar danyen mai miliyan 12 daga Amurka. Duk da dai har yanzu matatar Mai ta Dangote ba ta fito a hukumance ta yi...
    Gwamnatin Jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, ta dauki nauyin dalibai sama da 500 a wani mataki na tsara makomar matasa a fannin fasahar zamani. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan yayin bikin kaddamar da shirin da kuma mika takardun shaidar karatu ga wadanda suka ci gajiyar shirin fasahar zamani na Innovation Development and Effectiveness in the Acquisition of Skills (IDEAS) a Jihar Jigawa. Malam Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatinsa na karfafawa matasa ta hanyar kirkire-kirkire a fannin fasahar zamani da kuma koyon sana’o’i don habaka tattalin arziki. “A yau, mun kammala horar da dalibai 240 da suka koyi yadda za su bunkasa  harkokinsu na kasuwanci don tabbatar da ci gaba mai dorewa,” in ji gwamnan. “Haka...
    Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya. Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano. A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko...
    Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Samar da Dokar Shirye-Shiryen Matasa Da Ayyukan   Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na karfafa matasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar nan.   Ministan ya ce ziyarar da ya kai jihar Sokoto na da nufin kara cudanya da matasa a cikin watan Ramadan da bayar da tallafi mai mahimmanci.   Olawande, wanda ya samu rakiyar Seyi Tinubu, ya jaddada mahimmancin shirye-shiryen da suka shafi matasa, ciki har da samar da dandalin tattaunawa kan ci gaban matasa na kasa.   Ya yi nuni da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Ahmed Aliyu suna da manufa daya na ci gaban matasa, ta yadda za...
    Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.   Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.   A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi.   Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan.   “A wannan karon,...
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya ziyarci Gwamna Bala Mohammed a fadar gwamnati, inda suka yi wata ganawar sirri. Matashi Ya Kashe Mahaifiyarsa Da Taɓarya A Bauchi Gwarzon Ɗan Kasuwa Na Shekarar 2024: Benedict Peters Duk da cewa dalilin ziyarar bai fito fili ba, ana hasashen cewa yana da alaƙa da shirin siyasar 2027, inda ake ta raɗe-raɗin haɗakar ‘yan adawa domin ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki. Taron ya ƙara hura...
    Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i.   Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu.   Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar.   Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
    Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai ta dakatar da CBN daga ƙara kuɗin cajin ATM Ba abin da zai faru idan aka tsige Fubara – Wike Bayanai sun ce dakarun tawagar sun ƙwato bindigogi, harsasai, babur, tare da ceto wasu fasinjoji da aka sace. Wani direba da aka ceto, Malum Ari, ya bayyana yadda maharan suka tare hanyar: “Sun karɓe motata suka tilasta mana kwanciya a ƙasa. “Amma da suka hango...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya.  “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba. “tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?” “Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar  jama’a na duniya.” Inji jagoran. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ganin halin da fasinjojin ke ciki, sojojin suka yi kukan kura kan yan ta’addan, inda hakan ya tilasta suka saki fasinjojin da suke yunkurin garkuwa dasu tare da arcewa zuwa cikin daji.   Hakan ya sanya Sojojin kutsa kai cikin dajin domin farautar yan ta’addan, al’amarin da ya basu nasarar halaka wasu yan ta’adda da kwato makamai da babura.   Bugu da kari kuma, babu ko mutum daya a cikin ayarin da ya samu rauni ko kwalzani, amma daga bisani sun kubutar da fasinjojin guda 7. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci  ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata. “Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.” Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump,...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na tabbatar da gaskiya da adalci a shirin ciyarwa na azumin watan Ramadan da ke gudana a fadin jihar. Shugaban kwamitin duba rabon abincin buda baki kuma wakilin mazabar Kiyawa, Alhaji Yahaya Muhammad Andaza, ya bada tabbacin haka lokacin da ya kai ziyarar bazata a wasu cibiyoyin ciyarwar. A yayin ziyarar, kwamitin ya duba yadda ake gudanar da shirin a kananan hukumomin Birniwa da Kirikasamma da Guri da Hadejia, inda aikin kwamatin ya mayar da hankali ga tantance nasarar shirin da gano matsalolin da ke bukatar gyara. A karshen ziyarar, Alhaji Yahaya Andaza wanda shi ne mataimakin mai tsawatarwa na majalisar, ya bayyana damuwa kan wasu kura-kurai da aka samu a cibiyar...
    Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi ƙarar Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Godswill Akpabio a Majalisar Ɗinkin Duniya. Ta gabatar da kokenta a zaman taron mata da aka gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) a birnin New York, inda ta nemi ƙungiyoyin kare dimokuraɗiyya na duniya su bi mata haƙƙinta. Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa Jihohi 12 da za a fuskanci tsananin zafin rana — NiMet Natasha, ta ce dakatar da ita daga Majalisar Dattawan Nijeriya da aka yi ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma ta nuna damuwa kan cewa za a iya ƙoƙarin tsare ta saboda yin magana a fili. Taƙaddamar da ke tsakanin Sanata Natasha...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a yau Talata, 11 ga watan Maris. Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya Litinin. Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato Cikin wata sanarwa da shugaba, Maryam Abdullahi da kuma sakataren ƙungiyoyin, Kwamared Musa Yakubu suka sanyawa hannu, sun alaƙanta yajin aikin a matsayin martani da halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna kan buƙatunsu. Dangane da hakan gamayyar ƙungiyoyin ke kiran dukkan mambobinta da su tsunduma yajin aikin na sai baba...
    Shugaban Kwamitin Tallafa wa Marayu na Riyadissalihin Funtua, Alhaji Lawal Mekaji (Madugun Kasuwar Funtua), ya yi kira ga al’umma, musamman iyaye da masu hannu da shuni, da su bada gudunmawa wajen tallafa wa marayu da inganta rayuwarsu. Ya yi wannan kira ne yayin da yake raba kayan sutura da abinci ga marayu a Funtua a wani bangare na kokarinsa na yada albarkar watan Ramadan. A cewarsa, kula da marayu ba kawai nauyin zamantakewa ba ne, amma wata gagarumar ibada ce da ke karfafa kyawawan dabi’u a cikin al’umma. Da yake jawabi yayin taron rabon kayan, sakataren gidauniyar, Bashir Muhammad King, ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin da su yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace. Ya...
    Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin. Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya. A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
    Da yake jawabi a wurin taron, Maj.-Gen. Waidi Shuaibu, kwamandan OPHK, ya ce matakin na daga cikin kokarin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma dawo da wadanda rikicin Boko Haram ya shafa.   Shuaibu ya jaddada aniyar rundunar na dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas ta hanyar kawar da barazanar masu tada kayar baya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...
    ’Yan sanda sun cafke wasu mutum uku bisa zargin lalatawa da kuma satar wayoyin lantarki a ƙauyen Bororo da ke Ƙaramar Hukumar Michika ta Jihar Adamawa. An cafke ababen zargin ne da wayoyin lantarkin yayin wani sintiri da jami’an ’yan sanda suka gudanar a ranar 9 ga wannan wata na Maris. Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matashi a Kano Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ababen zargin da ke hannu sun yi iƙirarin aikata laifin da ake zarginsu da shi. Sai dai ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike gabanin ɗaukar matakin da ya ce nan gaba...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Jigawa, sun fara horas da mata 600 kan inganta muhalli ta hanyar bola jari. Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Jigawa JISEPA, Alhaji Adamu Sabo ya bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar mata ta duniya da kuma fara horaswar da aka gudanar a Dutse. Alhaji Adamu Sabo ya ce, baya ga  jajircewa, da juriya, da nasarorin da mata suke da, bikin ya yi duba kan irin rawar da mata suke takawa wajen dorewar muhalli da bunkasar tattalin arziki. Ya jaddada cewa ta hanyar shirin bola jari, watiWaste to Wealth Initiative, za su iya baiwa mata damar kare muhalli da kuma samar...
    Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan  fararen...
    Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta. A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako  daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa. Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi...
    Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci daya wanda aka fi sani da tsarin kasa biyu – kasar Falasdinawa da kuma ta Isra’ila. Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan itace kadai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka dade ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kawayensa sun yi watsi da batun. Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin...
    Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...
    A yammacin ranar Alhamis da ta gabata ce sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka aukawa Falasdinawa masu ibada bayan sun gudanar da sallar tarawihi a masallacin Al-aqsa, inda suka kore su daga masallacin da karfi, tare da hana su yin I’itikafi a cikin masallacin. Da yake tsokaci a cibiyar yada labaran Falasdinu, Ziad Abhais, mai bincike kan al’amuran birnin Kudus, ya jaddada cewa, matakin da gwamnatin sahyoniyawa ta dauka na hana masu ibadar I’itikafi a cikin masallacin Al-Aqsa wani mataki ne na cin zarafi da kuma muzgunawa hakkokinsu na addini. Ya kara da cewa: Sojojin yahudawan sahyoniya suna amfani da hakan ne don shimfida ikonsu a kan masallacin Al-Aqsa, domin kuwa a shekara ta 2015 an ba da izinin yin I’itikafi...
    Kasashen Jamus, Faransa, Birtaniya da Italiya “sun yi maraba” da shirin kasashen Larabawa na sake gina Gaza.  A cikin wata sanarwa ta hadin guiwa da ministocin harkokin wajen kasashen suka fitar a birnin Berlin, sun ce shirin idan an aiwatar da shi zai bada damar gaggauta warware mummunan halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza. A yayin taron da suka gudanar ne a ranar Talata data gabata a Masar kasashen Larabawan suka gabatar da wani shiri da zai lakume dalar Amurka Biliyan 53 na sake gina Gaza cikin fiye da shekara biyar inda shirin zai mayar da hankali kan taimakon gaggawa,dawo da ababen more rayuwa da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Shirin na kasashen Larabawa tamakar neman maye...
    A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
    Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar. “An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot. A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata masu dogaro da Amurka su kwana da sanin cewa, haka makomarsu za ta kasance, domin haka halayyar girman kai take.” Haka nan kuma limamin na Tehran ya ce; tare da cewa jagoran juyin musulunci na Iran ya sha jaddada cewa, babu aiki da tunani a cikin tattaunawa da Amurka, kuma ba abu ne na girma ba, sai dai kuma da akwai wadanda ba su nuna...
    An Bukaci ‘yan fansho suyi gangami ganin jinkirin da ake samu wajen biyan su kudaden su. An shawarci kungiyar ’yan fansho ta tarayya da ta zaburar da mambobinta kan jinkirin rage basussukan da gwamnatin tarayya ta amince da su. Jami’in hulda da jama’a na kungiyar ’yan fansho na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, Alhaji Muhammad Mamman, ya bayar da wannan shawarar a matsayin martani ga rahotannin da ke cewa an dakatar da zanga-zangar da ake shirin yi kan lamarin, biyo bayan rokon da PTAD ta yi na a ba da damar tattaunawa. Alhaji Muhammad Mamman wanda ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawa da wa’adin makonni hudu da hukumar NIPOST reshen kungiyar ‘yan fansho ta kasa ta bayar ya ba da shawarar...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta bayyana dakatar da ita da Majalisar Dattawa ta yi, a matsayin rashin adalci. An dakatar da ita ne biyo bayan ta ƙaddamar da ta ɓarke tsakaninta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, kan tsarin zama a zauren majalisa a ranar 20 ga watan Fabrairu. Doyin Okupe: Tsohon kakakin shugaban ƙasa ya rasu Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 Daga baya, ta zargi Akpabio da cin zarafinta, amma ya musanta hakan. Kwamitin Ladabtarwa da Ɗa’a na majalisar, ya yi watsi da koken nata, inda ya bayyana cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙorafin ba. Duk da haka, Natasha ta jaddada cewar ita Sanata ce, kuma za...
    Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da rusa gidaje, da bata yanyuyi da kuma dukan Faladinawa da suka hadu da su a yankin arewacin yamma da kogin na Jordan. Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ya nakalto Stephane Dujarric kakakin babban sakataren MDD yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, wakilan Majalisar a yankun sun bada rahoton yadda sojojin HKI suka kutsa a cikin sansanin yan gudun hijira na al-Arroub wanda yake cikin yankin Shuyukh al-Arrub, inda suka daki wani matsayi da kasar bindiga har suka fasa masa bakinsa suka kuma karya masa kafa. Har’ila yau rahoton ya...
    “Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne. Kasancewar Hafsan Sojin Sama a Zamfara na nuna ƙwarewa da kulawa ta musamman. Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar. Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar Jigawa. AIG Ammani ya yaba da dimbin tallafin da Gwamna Namadi ke bai wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar. Ya bayyana jihar Jigawa a matsayin daya daga cikin jihohin kasar nan masu zaman lafiya. A cewarsa, tun da ya samu mukamin AIG mai kula da shiyya ta 1, bai taba samun rahoton manyan laifuka daga...
    Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare da kokarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai. Ya ce an yanke wannan shawara ne bayan wani taro da aka gudanar a Legas. A cewar Sanata Barau, manufar kwamitin ita ce tattaunawa da shugabannin kasashen AES don fahimtar juna da jaddada muhimmancin ci gaba da kasancewa cikin ECOWAS, musamman idan aka yi la’akari da dangantakar tattalin arziki da zamantakewa da ke tsakanin jama’ar yankin. Shugabar Majalisar Dokokin...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya shaidawa kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas cewa zai ba da izinin sake kai sabbin hare-hare a zirin Gaza muddin kungiyar bat a saki sauran Isra’ilawan da ta yi garkuwa da sub a. Barazanar ta Trump ta zo ne a wata tattaunawa kai tsaye a Doha tsakanin wakilinsa kan al’amuran da suka shafi fursunonin, Adam Boehler, da shugabannin Hamas, a yunkurin cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni a Gaza. Trump ya ambaci haka ne bayan ganawa da fursunoni shida da aka sako a wani bangare na matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Wani babban kusa na kungiyar Hamas ya shaidawa Al Mayadeen cewa, taron na baya-bayan nan ya bar wa bangaren Amurka...
    Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu. Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya. A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani da makamin siyasa.
    Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar. Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni. “Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya...
    Gwamnan ya jaddada cewa yana da burin ganin an kammala waɗannan ayyuka domin amfanin al’umma, musamman hanyoyi da filin jirgin sama da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
    “A kan batun kafafen yada labarai, muna son mu yi taka-tsan-tsan don kada mu wuce gona da iri. Al’amari ne da ke cikin Majalisar Dattawa, kuma yin hakan ta hanyar kafafen yada labarai na iya daukar mana hankali. Zauren kwamitin zai iya ɗaukar mutane da yawa, kwamitin yana da mambobi kusan 23 ko 24. Muna son mu mai da hankali kan lamarin da ke gabanmu, kada wani lamari ya dauke mana hankali.”   Ya ba da tabbacin cewa za a yi wa Sanata Akpoti-Uduaghan adalci, inda ya ce: “Mai girma Sanata Natasha na da gata kamar kowane Sanata, kuma za a kare gatanta. Za ta samu adalci a wannan al’amari matukar ina wannan mukami. Kawata ce, kuma ba wanda zai...
    Fa’iza Muhammad wacce aka fi sani da Fa’iza Badawa, daya ce daga cikin mawakan Kannwood. Ita ta yi wakar fim din Oga Abuja, daya daga cikin finafinan suka yi tashe, ya kuma fito da basirar mawakiyar. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Mai barkwanci ya yi kuskuren liƙe bakinsa da sufa-gilu Kasancewar ta yi aure, mutane sun ɗauka ta daina harkar waƙa baki ɗaya. Sai a hirarta da wakilinmu Ibrahim Musa Giginyu, Fa’iza ta ce ba haka ba ne. Yaushe kika yi aure? Na yi aure ne a ranar 8 watan Afrilun shekar 2017, kuma ina zaune lafiya da mijina da kuma haihuwa daay da Allah Ya bamu, kuma aure ne na so ada kauna da kuma kyakkyawar kulawa. Kuma yana...
    Tun ranar 4 ga watan nan da muke ciki, Amurka ta fake da batun maganin Fentanyl, da nufin kakabawa Sin karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin kirar kasar Sin da za ta shigar da su kasar Amurka. Game da wannan mummunan mataki mai sabawa ka’idar cinikin duniya da karya lagon tsarin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, ba shakka Sin na matukar adawa da shi, kuma ba za ta zura ido ta rungume hannu tana ta kallo kawai ba. A wannan ranar kuwa, Sin ta mayar da martani, inda da farko ta kai kara a gaban kunigyar cinikin duniya ta WTO kan matakin da Amurka ke dauka, daga baya ta kara kakabawa Amurka harajin kwastam kan wasu kayayyakin da za...
    Kungiyar kasashen larabawa ta kawo karshen taron musamman da ta yi a birninn alkahira akan Gaza, tana mai amincewa da shawarar kasar Masar akan yadda za a sake gina yankin na Gaza. Bayanin bayan taron kungiyar ya kunshi cewa, shirin sake gina Gaza, yana nufin sake hade yankin da yammacin kogin Jordan a karkashin iko daya. Haka nan ya ambaci cewa abu mai muhimmanci a wannan lokacin shi ne tabbatar da tsagaita wutar yaki,wanda yake fuskantar keta shi –daga Isra’ila. Mahalarta taron na Masar sun kuma nuna kin amincewarsu da duk wani shiri na dauke mutane Gaza zuwa wani wuri na daban. Shi kuwa Fira ministan Falasdinu Muhammad Mustafa ba bayyana fatansa na ganin ai an aiwatar da  shirin na...
    Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
    A yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda a yayin taron, wani dan jarida ya gabatar da tambaya game da matakin Amurka, na sake kakabawa Sin karin harajin kashi 10 cikin dari, bisa fakewa da batun sinadarin kashe radadi na Fentanyl. Game da hakan, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin ya riga ya sha fayyace matsayinsa na nuna adawa da matakin. Ya ce, har kullum jama’ar kasar Sin suna adawa da nuna fin karfi, da yin matsin lamba, da tilastawa, da kuma barazana, saboda hakan ba hanya ce da ta dace a bi yayin mu’ammala da kasar Sin ba. Ya kara da cewa, idan bangaren Amurka...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa  kuma...
    Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa, akwai alamun Natanyahu Firai ministan HKI yana son ya sake komawa yaki a Gaza. Hamdan ya ce, kafin haka gwamnatin HKI ta dakatar da aikin aiwatar da yarjeniyar da suka kulla da ita, yana son ya yi watsi da ita, sannan ya bukaci a sake tattaunawa kan sauran abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar. Jami’in na Hamas y...
    Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar Larabawa ta Masar ta yi watsi da duk wani mataki da ke kawo barazana ga hadin kan Sudan, ciki har da yunkurin kafa gwamnatin ‘yan adawa, saboda hakan zai kara dagula al’amuran siyasa da kuma kawo cikas ga kokarin hada kan kasar. Alkahira ta bukaci dukkan bangarorin da su yi aiki mai inganci tare da cikakken tsari na siyasa, da nufin cimma daidaito da kuma...
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bada rahoton cewa sojojin HKI sun kashe akalla yara 16 tun farkon wannan shekara ta 2025 a yankin yamma da kogin Jordan. Tashar talabijin ta Presstv  a nan Tehran ta nakalto Ayed Abu Eqtaish, daraktan kungiyar ‘ The Defense for Children International’ a yankin yamma da kogin Jordan yana fadar haka. Ya kuma zargi manya manyan kasashen duniya da kyale gwamnatin HKI tana aikata irin wadannan laifuka kan Falasdinawa a gaban idan kowa. Eqtaish ya kara da cewa, rashin magana da kuma takawa gwamnatin yahudawan birki yana sa ta kara yawan kashe yara Falasdinawa a duk sanda ta ga dama. Kafin haka wani rahoton MDDya bayyana cewa idan ba’a hana...
    Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa a jiya Asabar ce motocin Buldoza na HKI suka shiga unguwar Almanshiya suka rusa gidajen wasu Falasdinawa, sannan suka bata hanyoyi a unguwar. Kamfanin dillancin labaran Abadulu na kasar Turkiya ya nakalti Ashawish yana cewa, sojojin HKI su kan tilastawa Falasdinawa fita daga gidajensu sannan su rusasu a gabansu. Tare da umurnin su fice...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance  matsalar da Falasdinawa suke...
    Fira ministan hakar Habasha  Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu. Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta Habasha ya kulla yarjejeniya da yankin Somaliland akan tashar jirgin ruwa. Ita dai kasar ta Habasha ba ta da iyaka da ruwa, don haka take son amfani da mashigar ruwan kasar ta yankin Somaliland. Habashan dai tana son gina wani yanki na kasuwanci a gabar ruwan  ta yankin Somaliland.  Yankin Somaliland na kasar Somaliya ne wanda Mogadishu  take daukar cewa ba kasa...