2025-02-21@14:20:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 815
«sabon Sakataren Gwamnatin»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da zauna lafiya kuma a bai wa zukata haƙuri biyo bayan ƙazamin rikicin mallakar fili da aka yi tsakanin mazauna da kuma Jami’ar Bayero da ke Kanon. Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da ziyarci unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a ranar Talatar nan, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Za a kashe Naira biliyan 4.8 wajen yaƙi da cutar HIV a Nijeriya — Ministan Lafiya Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 “Dole ne mu yi wa waɗanda suka rasu a addu’a sannan mu jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa. Muna fatan wannan...
Ministan ya kara da cewa, za a kaddamar da kashin farko na gyaran madatsar ruwan a tsakanin watan Fabrairu zuwa Yulin 2025. Ya kuma kara jaddada muhimmancin wannan aiki na tabbatar da cewa ba a samu ambaliyar ruwa a jihar Borno a shekarar 2025 ba.
Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya soki ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Shugaban Bola Tinubu da cewa suna yi ne kawai domin neman mulki. Uba Sani ya bayyana cewa ’yan siyasar da ke yawan sukan Tinubu a baya-bayan nan ba su da wani abin da za magance matsalolin Najeriyar da suke suka shugaban kasan a kai. Ya kara da cewa masu sukan Tinubun su ne suke ta yabon shugaban kasar, amma yanzu da mulki ya bar hannunsu suka dawo suna zagin sa. A cewarsa, babu mutum daya a cikin taron masu kushe Tinubun da ke da nagartar da ta fi shugaban kasar, yana mai jaddada cewa Tinubu ya yi yaki kai da fata kuma har yanzu yana kare muradun...
Babban wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya gudanar da taron manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York, jiya Litinin bisa agogon birnin, domin gabatar da muhimman tsare-tsare na wa’adin shugabancin kasar Sin a kwamitin sulhu, na wannan wata. A cewar Fu Cong, a yayin wa’adin shugabancin kwamitin sulhu na MDD a watan nan, kasar Sin za ta mai da hankali kan ra’ayoyin bangarori daban-daban da gudanar da tsarin mulkin duniya, da kula da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma yanayin da ake ciki a wasu kasashen Afirka. Da aka tambaye shi game da samfurin kirkirarriyar basira ta DeepSeek, wanda wani kamfanin kula da fasahohin kirkirarriyar basira na kasar Sin ya fitar,...
Majalisar Zartarwa ta ware naira biliyan 4.8 domin yaƙi da yaɗuwar cutar HIV a Nijeriya. Wannan na daga cikin matsayar da aka cimma a taron Majalisar Zartarwa da ya gudana a ranar Litinin kamar yadda Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate ya tabbatar. Ma’auratan da aurensu ya mutu sau 12 a shekara 43 Dalilin da Tinubu ya ƙi amincewa da ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi a Adamawa Ministan ya ce wannan yana daga cikin manufofin gwamnatin na inganta kiwon lafiya a matakin farko. A cewarsa, an tsara kashe kuɗaɗen ne a fannin ɗaukar ma’aikatan lafiya da ba su horo domin samun ƙwarewa da kuma tabbatar da an bayar da kulawar da ta dace domin hana yaɗuwar cutar HIV a sassan ƙasar....
Haruna, mazaunin Unguwar Kanawa Dutse Abba, an rahoto cewa, ya jagoranci ‘yan bindiga uku – Shago Yaro, Tanimu Ayuba, da kuma Lamido Dantajiri zuwa gidan dansa, Alhaji Anas da misalin karfe 1 na dare, inda suka tarar ba ya gida, amma suka yi awon gaba da matansa biyu, ‘ya’yansa uku, kaninsa, da matar kaninsa. An tsare Iyalin har tsawon kwanaki 60 a tsakanin dajin Buruku da Sabo Birni. Da yake tabbatar da rawar da ya taka a wannan aika-aika, Haruna ya ce, “Ni manomi ne kuma dan banga. Gaskiya ni ne na kai ‘yan bindiga gidan Alhaji Anas. Anas dana ne – dan yayata. Na san daya daga cikin ‘yan fashin da ya ce in nuna musu gidan...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da asusun horar da ma’aikata ITF. Shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K Dagaceri ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban asusun horas da ma’aikata na yankin arewa maso yamma, Malam Aminu Abdu a ofishinsa. A cewarsa, gwamnatin jihar tana sane da muhimmancin da asusun ke da shi, musamman ga ma’aikatan da aka horas da su domin samun kwarewa a fanninsu. Dagaceri, ya tabbatar wa shugaban asusun cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon baya da hadin kai ga sabon ofishin na ITF da aka kafa a yankin Jigawa. Tun da farko, Shugaban Asusun na Arewa maso...
An shawarci gwamnonin jihohin Arewa da su yi koyi da gwamnatin jihar Neja wajen magance matsalolin rikicin makiyaya da manoma a yankin domin samun ci gaba mai dorewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah ta kasa MACBAN, Dokta Baba Usman Ngelzarman ne ya bayar da wannan shawarar a wajen wani taro na musamman na karramawa tare da tabbatar da lakabin gargajiya ga wasu fitattun Fulani guda biyu a jihar Neja, da aka gudanar a fadar Sarkin Minna. Dokta Baba Usman Ngelzarman ya bayyana cewa, hanyar da Gwamna Mohammed Umar Bago na Jihar Neja ya bi na samar da sakamako mai kyau, ta yadda za a rage yawan rikicin makiyaya da manoma a jihar abin a yaba ne matuka. A cewarsa hakan ya...
Daminar Bana: NiMet Ta Yi Hasashen Jinkirin Saukar Ruwan Sama A Jihohin Arewa
Babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa Iran za ta yi amfani da dukkan karfinta wajen kare shirinta na nukiliya cikin lumana. A yayin wata ziyara da ya kai wani baje kolin da ke nuna sabbin nasarorin da aka samu a masana’antar nukiliya a hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI) a ranar Litinin din nan, Ali Shamkhani ya sake nanata gaskiyar shirin nukiliyar Iran da kuma yadda kasar ke bin ka’idojin kasa da kasa. “Iran ba ta taba neman makaman nukiliya ba kuma ba za ta taba yin hakan ba,” in ji shi. “Duk da haka, tana kare hakkinta da dukkan karfinta.” Shamkhani ya ci gaba da cewa:...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Labanon ta shigar da sabon korafi kan yahudawan sahyuniya gaban kwamitin sulhu na MDD, inda ta yi Allah wadai da hare-haren baya-bayan nan da yahudawan sahyuniya suka kai kan kasar Labanon, da kuma keta hurimun ikon kasar, da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma yau fiye da watanni biyu. Wannan korafin, wanda aka mika ta hannun wakilcin Dindindin na Labanon a Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, ya jibanci yadda Isra’ila ta ci gaba da keta yarjejeniyar tun daga ranar 27 ga Nuwamba, 2024 ranar da tsagaita bude wuta ta fara aiki har zuwa yau Talata 4 ga Fabrairu. Lebanon Ta yi Allah wadai da ci gaba da kai hare-hare ta kasa da...
Sakamakon sanarwar da Amurka ta fitar kwanan baya a kan kara haraji na kashi 10 cikin dari a kan daukacin kayayyakin kasar Sin da ake kaiwa kasar tare da kafa hujja da wasu batutuwa irin su maganin Fentanyl, a yau Talata, ma’aikatar cinikayya da takwararta ta kudi ta kasar Sin sun fitar da wata sanarwa cewa, Sin ta dauki matakan mayar da martani a kan Amurka tare da fara aiwatarwa. Matakan da suka jibanci lamarin sun hada da cewa, da farko, kasar Sin za ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, daga ranar 10 ga Fabrairu. Sannan na biyu, kasar Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH...
Da yake tabbatar da harin, wani mazaunin T/wada Garmadi, Rumaya Kwassam, Mista Joel Ahada, ya yi Allah wadai da wannan danyen aikin, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin mutunta hakkin dan Adam da kare lafiyar mazauna karkara. Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Shugaba Bola Tinubu ya ƙi rattaba hannu kan ƙudirin kafa Jami’ar Ilimi ta Tarayya a Numan da ke Jihar Adamawa. Hakan na ƙunshe cikin wata wasiƙa da ya aike wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas wadda mataimakinsa, Benjamin Kalu ya karanta a yayin zaman majalisar na yau Talata. Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja Wasiƙar shugaban ta kare matakin da ya ɗauka na ƙin amincewa bisa la’akari da tanadin da sashe na 22 da ke cikin ƙudirin kafa jami’ar ya yi. Ya yi bayanin cewa sashen ya yi tanadin cewa filin da za a gina jami’ar zai kasance a ƙarƙashin ikon Gwamnatin...
Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da tsohon uban gidansa kuma magabacinsa Malam Nasir El-Rufai. Uba sani ya ce babu kamshin gaskiya a maganganun da ke yawa cewa shi da tsohon gwamnan El-Rufai suna zaman doya da manja. Ya bayyana haka ne a yayin hirar da kafar tala bijin ta TVC ta yi da shi a ranar Litinin, inda ya ce “alakarmu tana nan yadda ta ke, babu wata matsala, kamar yadda ake rade-radi.” Am fara tunanin cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin Uba da El-Rufai ne bayan da gwamnati mai cin ya yi zargin Gwamnatin El-Rufai da barin masa bashin biliyoyin Naira da kuma karkatar da wasu kudade. Yau Majalisar za ta ci...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, an kashe sojoji 2 a yankin kusa da Tubas dake Arewacin yammacin kogin Jordan. Kafafen watsa labarun sun kuma ce, maharin ya isa wani shinge na soja dake kusa da Tayasir, ya kuma boye a cikin hasumiyar da masu tsaro ke zama a ciki, sannan ya bude wa sojoji wuta daga sama. Har ila yau maharin ya yi bata-kashi da sojojin da suke a wajen, sai dai a karshe sun ci karfinsa, da hakan ya yi shahadarsa. A bayanin da kungiyar Hamas ta fitar ta jininawa maharin tare da cewa, abinda hakan yake nufi shi ne cewa hare-haren da ‘yan sahayoniya suke kai wa ba za su tafi haka kawai ba tare da...

Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa. Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.” A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai...
Ministocin harkokin wajen 5 na kasashen larabawa tare da hadin gwiwar jami’an Falasdinawa sun rubuta wa ministan harkokin wajen Amurka Marco Antonio Rubio wasiki da a ciki suke nuna kin amincewa da shirin korar Falasdinawa zuwa wajen Falasdinu. Kasashen da su ka rubuta wasikar sun kunshi Saudiyya, HDL, Katar, Masar da Jordan, sai kuma mai bai wa shugaban gwamnatin Falasdinu shawara Husain Sheikh, sun kuma mika wannan wasikar ne ga mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Amurka mai kula da yankin gabas mai nisa. A ranar 25 ga watan Janairu da ya shude, shugaban kasar Amurka ya gabatar da shawarar cewa kasashen Masar da Jordan su karbi bakuncin Falasdinawa daga Gaza. Tare da cewa Trump din ya ce zaman na...

Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa A Shirye Take Ta Fara Tattaunawa, Marhala Ta Biyu Na Tsagaita Wuta A Gaza
Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Aston Villa ta kammala ɗaukar tsohon ɗan wasan Real Madrid Marco Asensio daga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. Asensio wanda ya bar Real Madrid a shekarar 2023 ya na ɗaya daga matasan ƴan wasa da tauraruwarsu ke haskawa a harkar ƙwallon ƙafa a yanzu. PSG Na Neman Dauko Lamine Yamal Daga Barcelona A Kan Yuro Miliyan 200 Wannan Ita Ce Shekarata Ta Karshe A PSG —Mbappe Aston Villa ta wallafa a shafinta na kafar sadarwa cewa Asensio ya rattaɓa hannun komawa ƙungiyar a matsayin aro daga PSG har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. Asensio ne ɗan wasa na biyu da Villa ta ɗauka aro bayan Marcus...

Sojojin Iran Sun Fara Atisayen Soje Karu Na Biyu Mafi Yawa A Bangaren Garkuwan Sararin Samaniyar Kasar
Sojojin JMI sun bada sanarwan fara isayen soje karo na biyu a yankun tsakiya da kuma kudancin kasarTashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa za’a fara wannan atisayen ne a yau Talata 04 ga watan Fabrairu, kuma atisayen zai fi maida hankali ne a kan garkuwan tsaron kasar , wanda kuma ya kasance daga cikin shirye-shiryen kasar na shirin kare sararin samaniyar kasar ta sama. Labarin ya kara da cewa a wannan karom ma sojojin Iran da kuma dakarun juyin juya halin musulunci zasu yi atisayen hadin giwa ne don gwada karfin sojojin kasar da kuma IRGC na kare sararin samaniyar kasar. Kafin haka dai sojojin sun gwada karfinsu a bangarori daban daban na sojojin kasar don...

Wani Tsohon Ma’aikacin MDD Ya Yi Kira Ga Amurkawa Su Dawo Daga Rakiyar Gwamnatin Amurka Da Natanyahu
Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wasu mutum biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin lashe wata dattijuwa mai shekara 67, kan zargin ta da maita. Kotun ya yanke musu hukuncin kisa ne a ranar Litinin bayan samun su da laifin kiran dattijuwar mai suna Ɗahare Abubakar, mayya sannan suka daɓa mata wuka har lahira. Mai Shari’a Usman Maido, ya bayyana cewa masu gabatar da ka to sun gabatar da gamsassun hujjoji da suka tabbatar da laifin wadanda aka gurfanar. Waɗanda kana yanke wa hukuncin kisan su ne Da’luta Ibrahim, Abdulaziz Yahaya, Faisal Yahaya, Ibrahim Abdu da Ayuba Abdulrahman. Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano Rikicin rusau ya yi ajalin mutum...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mutanen da ke da sha’awar shiga harkar noma don sama wa kansu abin da za su ci ko kuma don samun kuɗaɗen shiga na fuskantar ƙalubale. Wannan ƙalubale ya haɗa da ƙarancin ilimin noman, da na irin shuka, da rashin gonaki da dai sauran su. NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan batu tare da samar da hanyoyin noma ba tare da kashe kuɗi masu yawa ba. Domin sauke shirin, latsa nan
An yi kiyasin adadin tafiye-tafiyen fasinjoji tsakanin yankuna zai kai biliyan 4.8 a duk fadin kasar Sin daga ranar 14 ga watan Janairu zuwa ta 2 ga watan Febrairu, wato rabin farko na kwanaki 40 na zirga-zirgar bikin bazara. Adadin ya nuna karuwar kashi 7.2 cikin dari bisa makamancin lokaci na bara, a cewar tawagar aiki ta musamman da aka kafa don saukake ayyukan da suka shafi zirga-zirgar bikin bazara, wanda aka fi sani da chunyun. Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba Bisa Ka’ida Ba A Kuje Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Zirga-zirgar fasinjoji ya karu tun daga ranar 30 ga watan Janairu, inda adadin tafiye-tafiyen ya zarce miliyan 300 a...
Mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 13 suka jikkata a sanadiyyar wani mummunan hatsari da ya auku a hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Aminiya ta ruwaito cewa hatsarin ya rutsa da tireloli uku waɗanda suka yi karo da juna ’yar tazarar mitoci ƙalilan zuwa garin Agaie. Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar Ebola Wani mazaunin yankin, Baba Yakubu ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tirelolin da lamarin ya shafa ta ɗauko lodin dabbobi da suka haɗa da shanu da awaki Shi ma Darekta Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullah Baba Arah, ya...
A yayin da rikici ya kaure cikin dare tsakanin jami’an tsaro da masu gine-gine a unguwar Rimin Zakara, mutane sun cinna wa gidan mai garin wuta. Da farko dai an samu rikici tsakanin mahukunta da mutanen yankin, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane huɗu tare da ƙone gidan mai unguwar. NCDC ta tsaurara matakan shige da fice a Nijeriya saboda fargabar Ebola EU ta yaba wa Gwamna Zulum kan farfaɗo da Jihar Borno Aƙalla wasu mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙazamin rikicin da ya hautsine tsakanin mahukunta da mazauna unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano. Bayanai sun ce an harbe mutanen huɗu ne yayin da suka fito tirjiya...
Majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da wani kudirin doka da za ta ci tarar naira N25, 000 ga duk wanda aka samu ya yi fitsari, bahaya, zubar da shara ko kuma zubar da majina a kan titi ko kuma a ƙarkashin gada a jihar. Hakan ya biyo bayan dokar da majalisar ta zartar wanda zai bai wa hukumar da ke ƙawata birane damar kula da wuraren shakatawa. Abinda Ya Kamata Ku Sani Dangane Da Wasan Athletico Madrid Da Getafe Sin: Kasar Amurka Ce Ta Haifar Da Matsalar Miyagun Kwayoyi A Cikin Gidanta A zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan zaman majalisar na yau Litinin, shugaban ma su rinjaye na majalisar, ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawal...
A yayin da aka bude wasannin lokacin sanyin na Asiya karo na 9 a birnin Harbin na arewacin kasar Sin a ranar Litinin ta hanyar gabatar da tseren kunna fitila, mai dauke da fitilar, kuma mamban kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa (IOC), Yu Zaiqing, ya bayyana cewa, gasar za ta sa kaimi ga kara yawan wasannin lokacin sanyi a nahiyar Asiya. Yu ya kara da cewa, tseren fitilar na dauke da ruhin Olympics, wanda ke sanya karin mutane samun zurfin fahimtar wasannin, yana mai cewa, wannan shi ne karo na biyu da Harbin ya karbi bakuncin wasannin lokacin sanyi na Asiya, bayan na karo na 3 da ya gudana a shekarar 1996. Ana matukar sa ran samun ingantattun...
Bisa kididdigar da hukumar kula da harkokin fina-finai ta kasar Sin ta fitar, ya zuwa karfe 6:30 na yammacin ranar 3 ga watan Febrairun 2025, agogon Beijing, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finai wato box office na sabuwar shekarar bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ya kai yuan biliyan 8.257, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.14, wanda ya kafa sabon tarihi. Ya zuwa yanzu dai, yawan kudaden da aka samu daga kallon fina-finan kasar Sin a 2025 yana kan gaba a kasuwar fina-finan duniya da jimillar yuan biliyan 10.121, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.4 (Mai fassara: Mohammed Yahaya)

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Bayyana Cewa: Makamai Masu Linzaminsu Zasu Kai Duk Inda Makiya Suke
Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husaini Salami ya tabbatar da cewa: Makamai masu linzami na Iran suna da karfin kai hari kan duk wani wuri da ke da alaka da makiya a yankin da kuma fatattakar makamai masu linzami, yana mai jaddada cewa; sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna da karfin kalubalantar makiya a kowane lokaci. Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da jawabi ne a wajen bikin “Malik Ashtar” karo na 14 a safiyar yau Litinin, inda ya ce...

Kasar Iran Ta Bayyana Cewa: Tana Goyi Bayan Duk Wata Gwamnati Da Ke Samun Goyon Bayan Al’ummar Siriya
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya gudanar ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu dangane da batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma huldar diflomasiyyar Iran. Baqa’i ya tabo batun ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya kai zuwa kasar Qatar, inda ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne bisa tsarin alakar diflomasiyya ta al’ada tsakanin kasashen biyu....

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce; Kasashen Iran Da Iraki Zasu Kare Kungiyoyin Gwagwarmaya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf a wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Iraki Mahmoud al-Mashhadani, ya bayyana cewa: Kasashen Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Iran da kawarta Iraki sun kuduri aniyar marawa bangaren gwagwarmaya baya domin kare Musulunci da martabar al’ummar musulmi. Baqir Qalibaf ya kara da cewa: Sun ba da muhimmanci wajen raya hanyar layin dogo, musamman sabuwar...
Gwamnatin mamayar Isra’ila ta tantance hanya ta musamman da jirgin da ya dauki fira ministan mamayar Isra’ila zuwa Amurka saboda tsoron kama shi! A wani mataki da ke nuni da yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke kara nuna damuwa, jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar ta watsa rahoton cewa: Jirgin da ke dauke da fira ministan haramtacciyar kasar, Benjamin Netanyahu zuwa birnin Washington na Amurka, ya dauki wata hanya ta musamman, domin ya gwammace ya kaucewa wucewa ta sararin samaniyar kasashe wadanda suka tabbatar da cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen aiwatar da sammacin kama Netanyahu idan ya shiga sararin samaniyarsu. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba...
Masu zanga-zanga a birnin Kinshasa fadar mulkin kasar Dimokaradiyyar Kongo sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashe da suka hada da Amurka da Faransa Masu zanga-zangar sun kai hare-hare a wasu ofisoshin jakadanci a birnin Kinshasa, fadar mulkin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, a lokacin da suke gudanar da zanga-zangar a makon da ya gabata, don nuna adawa da yadda ake ci gaba da ruruta wutar rikici a shiyar gabashin kasar. Shafin sadarwa na yanar gizo na Russia Today ya bayyana cewa: Al’ummar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da suke cikin fushi sun kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashen Rwanda da Faransa da Belgium da kuma Amurka, yayin da hayaki ke tashi daga ginin ofishin jakadancin Faransa. Masu zanga-zangar sun kona tutar Amurka tare...
“An zargi Asibitin da yin aiki ba tare da rajista ba da kuma yin ayyukan likitanci a cikin wani gidan haya da ake ganin bai dace da ayyukan kiwon lafiya ba. “Bincike na farko ya nuna cewa, wani dattijo kuma shugaban Al’umma ya rasu sakamakon tiyata da aka yi masa a Asibitin, yayin da wasu rahotanni suka nuna cewa, majinyata da dama sun tsira da kyar daga bisani aka kai su wasu Asibitoci don samun kulawar gaggawa. “Da isar su, tawagar binciken ta gano asibitin a cikin wani mawuyacin hali da rashin tsafta,” in ji shi.
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna. Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da...
Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum. An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Gasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere. A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin...
Wani mahayin keken hawa, Samuel Fastuma, ɗan asalin Jihar Benue, ya kammala balaguronsa a kan keken hawa daga Legas zuwa Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a cikin kwanaki 8 kacal. A cewar Fastuma, ya fara wannan tafiya ce a ranar Lahadi 19 ga watan Janairu, 2025 bisa ƙudirinsa na nuna fatan alheri ga daukacin masu yaƙi da fatara da masu yaƙi da muggan ƙwayoyi da kuma neman hadtin kai da zaman lafiya a tsakanin al’ummar Nijeriya. Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Alawar yara mai sanya maye ta shiga gari —NDLEA Da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan isar sa birnin na Maiduguri, Fastuma ya ce, ya fara wannan tafiya ce domin yi wa...
A kwanan nan, kasar Amurka ta sanar da sanya karin harajin kwastam da ya kai kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin ke fitar da su zuwa kasuwannin Amurka. Wannan mataki ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda kuma zai lalata huldar dake tsakanin Sin da Amurka a fannin cinikayya. Yanzu haka, kasar Sin ta ce za ta kai kara ga kungiyar WTO, gami da daukar matakan da suka wajaba wajen kare moriyarta. A ganin kwararru masu nazarin al’amuran duniya, dalilin da ya sa sabuwar gwamnatin kasar Amurka daukar matakin nan na sanya karin haraji shi ne domin neman tilastawa sauran kasashe su biya kudi, ta yadda kasar Amurka za ta samu damar sassanta matsalar tattalin arziki da...
Hukumar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA ta ce an yi wa wani mutum mai shekara 59 tiyata domin ciro sunƙin hodar ibilis 57 cikin guda 81 da ya haɗiye kwanaki bakwai da suka gabata a Addis Ababa da ke kasar Habasha. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ta ce an kama mutumin ne a lokacin da ake tantance fasinjoji bayan isar su filin jirgin sama na Murtala Muhammad daga Habasha a ranar 26 ga watan da ya gabata. Kakakin hukumar ya ce bincike ya gano cewa mutumin wanda ya yi iƙirarin ɗan kasuwa ne a yankin Oshodi da ke jihar Lagos, ya tafi Addis Ababa inda ya haɗiyi sunƙi...
Ƴansanda Sun Kashe Mutum Ɗaya Kan Zargin Garkuwa Da Mutane A Adamawa
Uwargidan Gwamnan Jihar Jigawa, Hajiya Hadiza Umar Namadi ta kaddamar da wani katafaren wurin shan shayi da taliya na zamani a karamar hukumar Maigatari ta jihar. Hajiya Hadiza Namadi ta ce, wurin sayar da shayin da taliyar da aka zamanantar da shi wani yunkuri ne na karamar hukumar ta Maigatari. Ta kara da cewa, an tsara wannan wurin na zamani ne domin samar da yanayi mai kyau da inganci ga mutane, inda za su ci abinci cikin gamsuwa, tare da bunkasa kasuwanci a yankin. Hajiya Hadiza ta kuma kaddamar wani tallafi ga mata 300 a karamar hukumar Maigatari. An bayar da naira dubu talatin kowannensu, domin bunkasa kananan sana’o’i. Gidan rediyon Najeriya ya ruwaito cewa,...
Mutum biyu sun rasu sakamakon bullar cutar zazzabin Lassa a Jihar Filato. Kwamishinan Lafiya na Jihar Filato, Dakta Cletus Shurkuk, ya sanar cewa mutum na uku da ya kamu da cutar yana samun kulawa a asibiti. Ya bayyana cewa mamatan sun kamu da cutar ne a Karamar Hukumar Kanam, na ukun da ke raye kuma a Karamar Hukumar Shendam. Daya daga cikin majinyatan ya rasu ne a Shendam na biyun kuma a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano Kwamishinan ya bayyana cewa gwamanatin jihar tana aiki tare da Cibiyar Yaki da Yaduwar Cututtuka...
Gwamnatin Tarayya ta sanar das shirye-shiryenta na sake kara kudin wutar lantarki nan da watanni masu zuwa. Ta bayyana cewa ana tsara karin ta yadda zai zo da tallafi ga masu karamin karfi cikin masu amfani da wutar. Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Makamashi, Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan a Babban Taron Shugabannin Lantarki na Kasashen Afirka da ke gudana a Dar es Salaam, hedikwatar kasar Tanzania. A yayin taron ta gabatar wa mahalarta da shirin na Najeriya na kashe Dala biliyan 32 domin inganta wutar lantarki zuwa shekarar 2030. Batun karin na zuwa ne bayan a bara gwamnatin ta yi ninka kudin wuta sau uku ga kwastomomi da ke amfani da Band A. A yanzu kuma kamfanonin rarraba...
Shuwagabannin kasashen turai guda uku wato EU3 sun bayyana cewa daukewa Iran takunkuman tattalin arzikin da aka dorawa kasar ya fi karfinsu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran yana fadar haka a wata hira ta musamman da ta hada ta da tashar. Mohammad Eslami ya ce kasashen turan guda uku wadanda suka hada da Jamus, Faransa da Ingila sun aiko masa da sako inda suke tabbatar haka. A cikin shugaban Muhammad Eslami ya fadawa tashar talabijan ta Presstv irin ci gaban masu yawa wadanda JMI ta samu a cikin shekarun da suka gabata. Shugaban ya kara da cewa sakon da EU3 ya nuna irin yadda rikicin shirin Nukliyar kasar Iran...

Iran Da Pakisatan Sun Jaddada Bukatar Samar Da Harkokin Kasuwanci Na Akalla Dalar Amurka Billiyon $10 A Tsakaninsu
Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a kasar ta Pakistan. Ya kuma ce dole ne shuwagabannin kasashen biyu tsara yadda hakan zai kasance. Muqaddam ya kuma kara da cewa gwamnatocin kasashen biyu suna da dangantaka ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da kasuwanci, al-adu, addini da tsaro da sauransi. Cibiyar kasuwanci da kuma kamfanoni a kasar Pakistan yana daga cikin cibiyoyin kasuwanci mafi girma a kasar ta Pakistan. Daga karshe Jakadan...

Wasu Hukumomi A MDD Sun Bada Sanarwan Cewa HKI Ta Fadada Yaki Kan Falasdinawa Daga Gaza Zuwa Dukkan Kasar Falasdinu
Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Nan Ba Da Dadewa Ba Zai Kara Kudin Fito Na Kayakin Da Ake Shigo Da Su Amurka Daga Kasashen Turai
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara da cewa zai dorawa hatta kayakin da suke shigowa Amurka daga kasashen Turai, nan gaba, sai dai bai sanya lokaci ba. Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa zai dorawa kasar Canada kashi 25% kan dukkan kayakin da suke shigowa kasar. Sai mna Desel, inda zai sanya kashi 10% kacal.

Sheikh Na’im Kassim: Za A Yi Jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah A Rana 23 Ga Febrairu Da Ake Ciki
Bbaban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Lahadi ya bayyana cewa; Za a yi jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah tare da Shahid Sayyid Hashim Safiyuddin. Sheikh Na’im Kassim ya kara da cewa, za a binne Shahid Sayyid Hassan Nasrallah a wani wuri dake kusa ba filin saukar jiragen sama na birnin Beirut, yayin da shi kuma Sayyid Hashim Safiyuddin za a binne shi a mahaifarsa ta Deir-Kanun dake kudnacin Lebanon. Wani bayanin da Sheikh Na’im Kassim ya yi, shi ne cewa bayan shahadar Sayyid Hassan Nasrallah an zabi Sayyid Safiyuddin Hashim, saidai gabanin su sanar da kwanaki shi ma ya yi shahada. Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce, taken...
Ma’aikatan Agaji suna ci gaba da fito da gawawwakin shahidan Falasdinawa da Isra’ila ta rushe gidaje akansu, a tsawon lokacin yaki,wasu kuma akan hanyoyi. Wani jami’in agaji ya ce, bayan gushewar fiye da shekara daya na yaki, da wuya suke iya samun cikakkiyar gawar wani daga cikin shahidai, sai dai rabi da rabi, a wasu wuraren ma dai sai dai kasusuwa. Ya zuwa yanzu dai an sami gawawwakin da sun kai 458 kamar kakakin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu Dr. Khalil Dakran ya ambata. Ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinawa tana kirdadon cewa za a iya samun gawawwakin da suke tsakanin 4000, zuwa 5000 a karkashin baraguzai a fadin Falasdinu.
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a jiya Lahadi Fira minista Benjamin Netanyahu ya bayar da umarnin a rushe gidajen na Falasdinawa. Kafafen watsa labarun HKI sun bayyana cewa wannan shi ne hari irinsa na farko da aka rushe gidaje 100 a lokaci kadan. Masu bin diddigin abinda yake faruwa suna cewa, da alama HKI tana son shafe sansanin ‘yan hijirar na Jenin ne baki daya. Kungiyoyin Falasdinawa da su ka hada da Hamas sun yi kira da a takawa HKI akan wannan irin barna da take yi.
Hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ta sanar da cewa ta kwato mutane 23 da masu garkuwa da mutane su ka kama a cikin dajin Kajuru da ke karamar hukumar Kajuru. Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ya sanar a jiya Lahadi cewa sun kwato mutanan ne a ranar 2 ga watan Febrairu, 2025. Jami’in ‘yan sandan ya ce sun sami nasarar kwato mutanan ne bayan da su ka sami bayanai na sirri akan kai da komowar masu garkuwa da mutanen. Haka nan kuma Hassan ya ce, an yi taho mu gama ne da masu garkuwa da mutanen a kusa da kauyen Doka dake karamar hukumar ta Kajuru. Barayin suna kokarin sauya wa mutanen...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5 Ya ce hukumar ta karɓo kuɗaɗen daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce kowanne mahajjaci ya samu Naira 61,080. Ya kuma ce an tura wa kuowa kuɗinsa kai-tsaye zuwa asusun bakinsu. “NAHCON ta mayar da waɗannan kuɗaɗen ne saboda matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru...
Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta cafke wasu matasa a yankin Sheka bayan ɓarkewar rikici tsakanin ƙungiyoyin ƴan daba. Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, yana mai cewa rikicin ya fara ne bayan mutuwar wani matashi mai suna Yusuf Aminu, ɗan unguwar Sheka Babban Layi, wanda ake zargi da aikata fashi da sauran laifuka. Dabaru Irin Na Sin A Kan Daidaita Harkokin Duniya A 2024 An Yi Taro Don Tattauna Dabarar Aiwatar Da Shawarar Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya A MDD Rahotanni sun nuna cewa marigayin mamba ne na ƙungiyar ‘Yan Shida,’ wacce ta addabi yankin Sheka da aikata fashi da tashin hankali. Wasu mazauna unguwar sun kama shi, suka kakkarya masa ƙafa tare da...
Arsenal ta doke Manchester City a wani yanayi mai ban mamaki a filin wasa na Emirates dake birnin Landan, ƙwallaye da Odegaard, da Partey, da Skelly, da Harvertz da Nwaneri suka jefa ya sanya Man City cikin garari. Tun minti na 2 da fara wasan kyaftin ɗin tawagar Arsenal Martin Ordegaard ya jefa ƙwallo a ragar Manchester City bayan da ɗan wasan baya Nathan Ake ya tafka kuskure. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara Gaban Kotu Arsenal Ta Matsawa Liverpool Ƙaimi Bayan Doke Tottenham A Emirates Duk da ƙwallon da Haaland ya ci bai hana Arsenal raga raga da City a wasan mako na 24 na gasar Firimiyar ba, wannan sakamakon ya sanya magoya bayan ƙungiyar sa...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Manchester City ta ci 5 da 1 a Gasar Firimiyar Ingila. Ƙungiyoyin biyu sun ɓarje gumi da yammacin ranar Lahadi a filin wasa na Emirates, a mako na 24 na gasar. Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Ɗan wasan tsakiyar Arsenal, Martin Ordeegard ne ya fara jefa ƙwallo a minti na biyu da fara wasa. Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Erling Haaland, ya warware ƙwallon da Arsenal ta jefa wa Manchester City, a minti na 55. A minti ma 56 Thomas Partey ya ƙara jefa wa Arsenal ƙwallo ta biyu. A minti...
Masana’antar shirya fina-finai ta kasar Sin ta kafa wani sabon tarihi a hutun bikin bazarar 2025, inda daga ranar 29 ga watan Janairu zuwa ranar 1 ga Fabrairu, kudaden da aka samu daga kallon fina-finai ya kai biliyan 5.75 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 802, wanda ya zarce mafi yawan kudin da aka samu a baya na yuan biliyan 5.73 a shekarar 2021. Wannan adadi shi ne mafi yawan kudi da aka samu daga kallon fina-finai a lokacin bikin bazara a tarihin sinima ta kasar, kuma ya tabbatar da matsayin kasar Sin na kasancewa jagora wajen samun mafi yawan kudade daga kallon fina-finai wato box office a shekarar 2025, wanda ya zarce Arewacin Amurka. Gwamna Buni Ya Jaddada Bai Wa Sojoji...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da ci gaban da Iran ta samu a fagage daban-daban, yana mai cewa kasar ta samu bunkasa a dukkan bangarori cikin shekaru 40 da suka gabata. Iran ta yau ba Iran ce ta shekaru 40 da suka gabata ba – mun ci gaba ta kowane fanni,” in ji shi. Jagoran ya jaddada cewa “Abin da ya bambanta Iran da sauran al’ummomi da yawa shi ne jajircewar mutanen kasar na yin Allah wadai da Amurka a matsayin mai zalunci, makaryaciya, mayaudariya da girman kai.” Jagoran ya bayyana hakan ne a wata ganawa yau Lahadi tare da mahardatan musabaka ta Al’kur’ani mai tsarki karo na 41 da aka gudanar...
Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon. “Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa ido da masu shiga tsakani don dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” in ji shi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin dazu. Sheik Qasem ya ce kungiyar Hizbullah na taka-tsan-tsan don bai wa gwamnatin Lebanon damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Faransa da Amurka suka shiga tsakani...
Kungiyar Hamas ta yi Allah-wadai da kalaman shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da mazauna Gaza zuwa kasashen Masar da Jordan dake makwabtaka da ita. A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban kungiyar Hamas Sami Abu Zuhri ya yi tir da irin wadannan shawarwari a matsayin “abin dariya kuma maras amfani,” yana mai cewa, “Abin da mamayar Isra’ila ta kasa cimma da karfi, ba zai samu ta hanyar makircin siyasa ba.” Abu Zuhri ya kara da cewa, “Sanarwar da Amurka ta nanata na raba Falasdinawa da gidajensu da nufin sake gina yankin zirin Gaza na nuni da yadda kasar ke da hannu wajen aikata laifukan da suka shafi yanki.” Kana, ya yi gargadin cewa, “aikin kwashe mazauna Gaza” wani...
Rahotanni sun ce gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na matsawa kasar Ukraine lamba domin gudanar da zabuka a karshen wannan shekara a daidai lokacin da ake kokarin kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Kiev da Moscow. Wakilin Trump na musamman kan Ukraine da Rasha, Keith Kellogg, ya fada a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa zabukan shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Ukraine da aka dakatar a yakin da ake yi da Rasha, suna bukatar a gduanar da su. “Yawancin kasashen dimokuradiyya suna gudanar da zabe a lokacin yakinsu. Ina ganin yana da mahimmanci su yi haka,”in ji Kellogg. Kamfanin dillancin labaran reuters ma ya rawaito wasu jami’an fadar White House sun tattauna batun matsawa...
La’anannen dan siyasar Sweden din nan mai kyamar addinin Islama, Rasmus Paludan, ya sake tozarta kur’ani mai tsarki a birnin Copenhagen na kasar Denmark. Paludan mai shekaru 43 shugaban jam’iyyar adawa ta kasar Denmark Stram Kurs, ya sake haifar da cece-kuce ta hanyar aikata wannan aika aika a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Denmark. Wani faifan bidiyo da aka watsa a dandalin sada zumunta ya nuna Paludan yana wulakanta kur’ani mai tsarki, matakin da ya yi matukar bakanta ran musulmin duniya. Matakin na Paludan ya zo ne bayan kisan da aka yi wa wani dan kasar Iraki mai suwan Salwan Momika wanda ya walakanta Al’Kur’ani a gidansa da ke birnin Sodertalje a ranar 30 ga watan Janairu. Matashin mai...
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a taron shugabannin ƙasashen Afrika kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya, inda Nijeriya ta gabatar da shirin dala biliyan 32 na faɗaɗa samar da wuta zuwa shekarar 2030. An Sace Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki 18 A Cikin Kwanaki 6 – TCN Jami’in Kenya: Fasahar Sin Na Ingiza Samar Da Wutar Lantarkin Kenya Ta ce duk da...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace don kare halaltattun hakkokinta da moriyarta. Kakakin ya jaddada cewa, “Kasar Sin tana tsaye kan matsayinta ba ja da baya. Babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya da haraji.” Yana mai cewa, karin harajin bangare daya na Amurka ya sabawa ka’idojin WTO. Kuma wannan matakin ba zai iya magance matsalolin Amurka na gida ba kuma mafi mahimmanci, ba zai amfanar da kowane bangare ba,...
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Nijeriya da ke buga wasa a ƙungiyar Galatasaray Victor Osimhen, ya shigar da ƙarar wani ɗan jaridar Turkiya Tolga Bozduman bisa zargin ɓata masa suna. A cikin wani saƙo da wani makusancin Osimhen ya wallafa a shafinsa na X, ya ce za a fara sauraron ƙarar da ɗan wasan ya shigar bayan da ɗan jaridan ya zarge shi da naushin sa. Wannan dai na zuwa ne bayan da ɗan jarida Bozduman ya zargi Osimhe da cin zaraginsa, bayan tashi wasa 3-3 tsakanin ƙungiyarsa ta Galatasary da kuma Dynamo Kyiv. Yanzu haka dai Osimhen na fuskantar bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kai. A makon da ya gabata ne...
Kasashen 3 na yankin sahel sun kafa ta su kungiyar mai suna “Kawancen Sahel” (AES). Yadda ficewar Nijar da Mali da Burkina Faso daga Ecowas ka iya raunata kungiyar Ficewar kasashen Mali da Nijar da Burkina Faso daga kungiyar Ecowas a ranar Laraban nan bayan kwashen fiye da shekara guda ana zaman tankiya tsakanin kungiyar da kasashen guda uku, wani abu da ke nuni da rashin tabbas ga cigaba da kasancewar kungiyar ta Ecowas. A ranar ta 29 ga watan Janairun 2024 ne kasashen guda uku da shugabannin mulkin soji ke jagoranta suka sanar da kungiyar Ecowas a hukumance dangane da bukatar ficewar tasu. To sai dai bisa dokokin Ecowas, kasashen na bukatar sanar da kungiyar shekara guda kafin amincewa...
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar da sanarwa da a ciki ta bukaci Isra’ila da ta janye sojojinta daga kudancin Lebanon tana mai cewa wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci. Ministan harkokin wajen kasar ta Masar Badar Abdulatif ya ce, wajibi ne ga Isra’’ila da ta janye sojojin nata daga Lebanon ba tare da wani sharadi ba, domin ba za a kyale ta akan koda taku daya na kasar Lebanon ba. A karkashin sharadin tsagaita wutar yaki da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba na 2024, Isra’ila za ta janye sojojinta daga cikin kasar ta Lebanon a ranar 26 ga watan nan na Janairu. Ya zuwa yanzu dai an tura sojojin Lebanon da kuma na MDD...
Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909. Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14. Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001). Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56. Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949). Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960). Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021). Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
A wani mataki na tsaro da Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano ya fitar saboda magance barazanar tsaro da yake fuskanta, ya fara aiwatar da dokar hana motoci masu baƙin gilas wato tinted glass shiga harabar asibitin. Mahukuntan asibitin sun bayyana cewa, motocin da ke ɗauke da marasa lafiya ko ma’aikata za su iya shiga, amma sai an bi ka’idojin tsaro na musamman. Mahaifin ma’aikacin Aminiya ya rasu Majalisar Matasa ta Ƙasa ta goyi bayan taron Kur’ani A wata sanarwa da Daraktan Gudanarwa na asibitin, Usman Rabiu Mudi ya fitar, ya ce, an kafa dokar hana motocin masu baƙin gilashi shiga ne saboda wasu munanan abubuwan da suka faru. Ya bayyana irin munanan ababen kamar yunƙurin sace mutane...
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya sha alwashin ci gaba da shirin kasar na kera makaman nukiliya har sai baba ta gani. Kafar yada labaran kasar ta rawaito Mista Kim ya kai ziyara cibiyar da ake kera makaman, inda ya ce shekarar da muke ciki na da matukar muhimmanci a tsarin da kasar ke yi na karfafa shirin makaman nukiliya, da kuma fito na fito da duk kasashen da suka nemi tsoma baki a harkar kasarsa. Kalaman Kim na zuwa ne bayan gwajin makaman da Pyongyang ta yi a ranar Asabar da ta wuce, domin tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro, shi ne gwaji na farko tun bayan shugaban Amurka Donald Trumo ya sha rantsuwar kama...
Ministocin harkokin waje da wasu jami’an gwamnatocin kasashen sun ki amincewa da korar Falasdinawa daga kasarsu kamar yadda shugaban AMurka Donal Trump ya bada shawara. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ya nakalto ministoci da jami’an gwamnatin kasashen kungiyar kasashen larabawa suna fadar haka, a wani taron hadin giuwa a cibiyar kungiyar dake birnin Alkahira na kasar Masar. Labarin ya kara da cewa taron ya sami halattar ministocin harkokin waje na kasashe Masar, Jordan, Saudia, Qatar, da gwamnatin Palestinian Authority, sannan da wakilia daga sauran kasashen kungiyar ta ‘Arab League’ . Kungiyar ta bayyana cewa kasashen kungiyar basy amince da duk wani kokari na canza yadda kasashen larabawa suke ciki don tabbatar da samuwar HKI a yankin ba, kamar...
Kungiyoyin kare bil’adama ta Falasdinawa guda biyu sun bada rahoton cewa gwamnatin HKI tana azabta falasdinawa da suke tsare da su. Sun kuma kara da cewa sojojin HKI tana wulakanta Fursinonin Falasdinwa suna kuma azbtar da su, musamman bayan sakin 183 daga cikinsu, a musaya ta huda. Inda Falasdinawa suka mika masu fursinoni 4 da ke hannunsu. Hukuma mai kula da fursinoni Falasdinawa ko (PPS) ta bayyana cewa a marhala ta 4 Falasdinawar 183 yahudawan suka sallama, ammam 111 daga cikinsu wadanda sojojin yahudawan suka tsare a lokacinda ake yaki na watanni 15 da su ne. Har’ila yau daga cikin wadanda aka sallama a jiya Asabar 18 daga cikinsu ta yanke masu hukuncin daurin rai da rai ne, har mutuwa....
Jami’ar Michigan ta Amurka ta dakatar da karatun wasu daliban jami’ar saboda rawar da suka taka, a zanga-zangar goyon bayan Gaza a yakin watanni 15 da suka yi da HKI. Kamfanin dillancin labaranSahab ya nakalto kamfanin dillancin labaran Mehr yana fadar haka, ya kuma kara da cewa, hukumar Jami’ar Michigan ta kori wasu daliban daga karatu har na tsawon shekaru biyu. Labarin ya nakalto hukumomin Jami’ar na cewa, wadannan daliban sune suka shirya zanga-zanga a cikin Jami’ar, inda suka maida ita cibiyar goyon bayana Falasdinawa a Gaza. Ta kuma kara da cewa wannan kin kabilar samiyawa ne. Jami’ar ta sa an kama wasu malaman jami’ar, ta kuma dakatar da wasu daga karantarwa, sannan wasu kuma an koresu daga jami’an kwatakwata....
Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu. Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa, suna yaba wa shugabannin Musulunci da suka shirya wannan taro kamar su Sarkin Musulmi, Imam Dahiru Usman Bauchi da Sheik Karibullah, da kuma Sheik Bala Lau. Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja Dangote ya karya farashin man fetur Ya ce, irin wannan taro na masu kishin Kur’ani, wanda ba a taɓa yin irinsa ba a Nijeriya,...
A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya akalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kudin fansa. Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba. Sannan, shin su wa ke amfani da kudaden fansar da ake biya ga masu garkuwa da mutanen? Hasashe ya nuna cewa, mai yiwuwa a yi amfani da kudaden don kara sayen bindigogi da sauran makamantansu. Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Bukatar Warwarewa A cikin wannan rudani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati...
Iyalai da dama da ’yan fashin daji suka raba da matsugunansu a wasu jihohin Arewa-maso-Yamma da Arewa-maso-Gabas sannan daga bisani kuma aka kore su daga birnin Abuja, inda suka samu mafaka a halin yanzu, suna wani hali a wasu sassan Jihar Nasarawa da ke makwaftaka da Babban Birnin Tarayya Abuja. Binciken da wakilinmu ya yi ya nuna cewa, ’yan gudun hijirar sun fito ne daga sassan jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sakkwato a yankin Arewa-maso-Yamma da jihohin Adamawa da Borno da Yobe a yankin Arewa-maso-Gabas. Dangote ya karya farashin man fetur An miƙa wa Majalisar Kano ƙorafin ƙara wa’adin manyan ma’aikatan gwamnati A yanzu haka galibinsu sun fada barace-barace da kananan ayyuka ko sana’o’in da ba...
Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja. Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa. Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi...
Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba. Musa ya ce, illa kawai dai suna taimakon kansu da kuma na kusa da su, wanda kuma ba haka ya dace a ce suna yi ba, dalili kuwa shi ne, har yau babu wani daga cikin masana’antar tamu da ya taba samun wani mukamin gwamnati, ya taimaka wa ita kanta masana’antar, illa kalilan daga cikinmu. A bangaren abokanan fada kuwa a Masana’antar Kannywood, Mai Sana’a...
Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
An miƙa wa Majalisar Dokokin Kano ƙorafi kan abin da aka bayyana a matsayin ƙarin wa’adin aiki na wasu manyan jami’an gwamnati ba bisa ƙa’ida ba. A ƙunshin ƙorafin an yi zargin cewa ana ƙara wa manyan jami’an wa’adin aiki ta hanyar amfani da Dokar Zartarwa Ta 1 ta 2025, wadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanyawa hannu. A cikin wata wasika mai kwanan wata 6 ga Janairu, 2025, Sani Usman DanAbdullo, Esq., Daraktan Gudanarwa da Harkokin Gabaɗaya na Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Jihar Kano (KSACA), ya buƙaci Majalisa da ta kare doka da oda, tare da dakatar da abin da ya bayyana a matsayin rashin amfani da ikon zartarwa yadda ya kamata. An aike da ƙorafin ne...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kaddamar da sabbin na’urori masu linzami da na tsaro Babban sakataren rundunar da ke sa ido kan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya sanar da kaddamar da wasu sabbin na’urori masu linzami da na tsaro a cikin tsarin baje kolin “Malik Ashtar”, wanda za a gudanar a ranar Litinin mai zuwa a kasar. Birgediya Janar Hamid Bazmashahi ya kara da cewa a wani taron manema labarai a yau Asabar, za su yaye shamakin makaman dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kare karfinsu bisa tsarin baje kolin. Ya yi nuni da cewa, baje kolin zai hada da, a karon farko, baje kolin jami’an tsaron da ke sintiri da jiragen ruwa...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu. Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane mahajjati ya karɓi sama da naira dubu sittin da ɗaya a asusunsa bakinsa. Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne saboda katsewar wutar lantarki a lokacin da maniyyata ke Muna, wanda ya shafi tsarin sanyaya iska kuma hakan ya janyo musu matsala. Hukumar Alhazai na Jihar Kaduna ta ta yaba da hakurin wadanda har yanzun basu same...
Aƙalla matasa 150 masu kirkire-kirkire daga yankin Arewa sun hallara a Kano don halartar “Innovate North” Business Development and Innovation Hackathon, wani shiri da ke da nufin ƙarfafa harkokin kasuwanci da sauya fasalin dijital. Yayin da take jawabi a taron, Maryam Lawan Gwadabe, wacce ta shirya gasar kuma ita ce wanda ta kafa Blue Sapphire Hub, ta jaddada mahimmancin shiryawa da ba da jagora ga matasa domin bunkasa basirarsu. APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara “Yawancin matasa masu kirkire-kirkire ba su da jagora ko kuma wanda zai taimaka musu su sauya tunaninsu zuwa kasuwanci mai ɗorewa,” in ji ta. Gwadabe ta bayyana gasar a matsayin babbar...
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa bayyanar irin girman da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suke da shi ya sanya makiya takaici. Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Manjo Janar Baqiri ya aike da sakon murna ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Hossein Salami, a yau Asabar, dangane da bukukuwan watan Sha’aban, ciki har da zagayowar ranar haihuwar Imam Husaini (a.s), wanda ya zo daidai da ranar dakarun kare juyin juya halin Musulunci. Yana mai jaddada cewa; Yana da...
Kasar Kenya na amfani da damar ci gaban fasahar kasar Sin don kara dogaro da samar da wutar lantarki a kasar. Darektan ma’aikatar kula da harkokin rarraba wutar lantarki ta kasar Joseph Siror ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Nairobi, babban birnin kasar Kenya cewa, ababen more rayuwa a fannin samar da wutar lantakin kasar na kunshe da dimbin kayayyakin aiki daga kamfanonin kasar Sin irin su Huawei da rukunin Yocean. An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa Ƴansanda Za Su Fara Tilasta Yin Insuran Motoci Daga 1 Ga Fabrairu “Sashen wutar lantarki na Kenya ya kuma ci moriyar musayar fasaha da...
‘Yan gwagwarmayar Siriya sun sanar da fara kaddamar da hare-haren daukan fansa kan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila Sojojin mamayar Isra’ila sun yifuruci da cewa; Sun fuskanci bude wuta daga yankin kudancin Siriya, wanda kungiyar gwagwarmayar al’ummar Siriya ta yi ikirarin kai harin wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da sojojin mamaya suka kutsa kai cikin yankunan Siriya bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad. Sojojin mamayar Isra’ila sun tabbatar da kai wani farmaki kan rundunar sojinsu a kudancin Siriya a jiya Juma’a. A jiya ne sojojin mamayar Isra’ila suka kai farmaki kauyen Taranja da ke yankin Quneitra a kudu maso yammacin kasar Siriya, inda suka kame mutane biyu. Wakilin gidan rediyon sojojin mamayar Isra’ila ya...
Sojojin Sudan sun kwace iko da wani birni da ke arewacin Kordofan daga hannun ‘yan tawayen kasar na Rapid Support Forces Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta sake kwace iko da birnin Umm Rawaba, birni na biyu mafi girma a arewacin jihar Kordofan da ke kudancin kasar daga hannun dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce: Godiya ta tabbata ga Allah da yardarSa, sojojin sun tsarkake birnin Umm Rawaba daga hannun mayakan dakarun kai dauki gaggawa da sojojin hayarsu, tare da janyo musumunanan hasarori masu yawa. A cewar shafin yanar gizo na Arabi 21, Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun mamaye birnin...
Ga kuma yadda za ku hada: Da farko za ku wanke tsamiya sai ku dafa ta ku tace ta, sannan ku wanke danyar citta, sai ku nikata ku samu roba mai kyau ku tace tsamiyar tare da cittar ku sanya suga da filebo sai ku juya sosai ku sanya a firij ko ku sanya masa kankara. Asha dadi lafiya. Hade-haden Lemon Shayi: Abubuwan da za ku tanada: Kankana, Kwakwamba, Sitoru Beri Na Ruwa, Lemo, Tea Bag, Danyar Citta, Abarba, Lemon Juice, Na’a na’a: Yadda za ku hada: Da farko za ku wanke kankana da danyar citta sai ku nika su sannan ku tace ku zuba a cikin tukunya sai ku dora akan wuta sannan ku wanke abarba...
A jiya Jamu’a, wakilin CMG ya samu labari daga ofishi mai kula da aikin ceton mutane daga bala’in girgizar kasa da ya abku a gundumar Tingri karkashin birnin Shigatse na kasar Sin cewa, yanzu haka, an kafa gidajen wucin gadi 7733, da tantuna 9941, tare da tsugunar da mutane 47787 da bala’in girgizar kasa ya ritsa da su. Wadannan alkaluma sun nuna cewa, an riga an kammala aikin tsugunar da dukkan mutanen wurin bisa wani mataki na wucin gadi. A ranar 7 ga watan Janairun da ya gabata ne dai, aka samu abkuwar girgizar kasa da karfinta ya kai maki 6.8 a gudumar Tingri ta birnin Shigatse dake jihar Xizang ta Sin. Kana a halin yanzu, ban da mutanen da...
Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar. Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar. Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Sun nemi a ɗauki mataki a kan Aregbesola saboda zargin kafa ƙungiyoyin da ke raba kan jam’iyyar da yin haɗin gwiwa da jam’iyyun adawa don raunana APC a Osun. A cikin wata wasiƙa da kwamitin zartarwa na APC na Osun ya aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana cewa Aregbesola ya kafa wata ƙungiya mai...
Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024 da Hisbah ta yi sanarwar zuwa yanzu, an samu ɓullar aƙalla bidiyoyi 10 daga jihar da suka tayar da kura a kafofin sada zumunta, musamman TikTok, ciki har da na tsiraici. Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara Ɓullar bidiyon tsiraicin fitattun ’yan Tiktok irin su Hafsat Babaiana da Hafsat...
Kwamitin zai bincike kamar yadda aka bada sharuddan da za ta ayi amfani da su lokacin bincike, domin ta gano ta yaya lamarin maganganun da ake yadawa,da ake zargin abubuwan da suke da alaka da badana wanda mataimakin shugaban jami’ar ne aka ce akwai kokarin da ya yi domin ya sayi mukaman Bursar da rajistara, kana agano dalilin da yasa aka dauki maganar wadda yanzu ta zama abar maganar ta kafofin sadarwa na zamani. Hakanan ma kwamitin an ba shi alhakin da ya yi bincike kan maganar da ake ta yadawa cewa shi Injiniya.Adebayo, musamman ma zargin da ake yi na shi mataimakin shugaban jami’ar a sake duba dukkan kokarin da aka yi da matakin da aka dauka wanda ‘yansanda,...
A wannan hirar, Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatuil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya yi magana game da cece-ku-ce kan ɗaukar nauyin wani taron Al-Ƙur’ani da aka shirya. Da yake magana jim kaɗan bayan wata lacca ta musamman a sakatariyar JIBWIS ta ƙasa da ke Abuja a wannan makon, shugaban ya bugi ƙirji da cewa al’ummar Musulmi na da kuɗin da za su iya shirya taron. Aminiya: Za mu ka yi mana bayani kan mahimman abubuwa game da taron Al-Kur’ani da aka shirya? Amsa: Taron Al-Qur’ani mai zuwa a ranar 22 ga Fabrairu ya shafi gabatar da karatun Al-ƙur’ani mai girma, inda makaranta da mahaddata za su taru a bisa jagorancin Sarkin Musulmi na Sakkwato. Majalisar Ƙoli...