2025-02-28@13:00:09 GMT
إجمالي نتائج البحث: 55

«Kawu Sumaila»:

    A ranar Litinin ne Jam’iyyar NNPP ɓangaren Kwankwasiyya a Kano, ta fitar da sanarwar dakatar da jiga-jigan ’yan siyasarta huɗu.  An dakatar da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, da sauran ’yan majalisar wakilai uku, da suka haɗa da Aliyu Sani Madakin Gini da Kabiru Alhassan Rurum da kuma Abdullahi Sani Rogo. Sai dai ba kowa ne ya san asalin mafarin rigimar ’yan majalisar da madugunnKwankwasiyyam Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba. Saɓanin ya faro ne a lokacin da Kwankwaso ya jagoranci fitar da shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli.   Yadda kasuwar buƙata ta haɗe su da Kwankwaso a 2023 Dama dai ana ganin Sani Rogo da Kawu Sumaila, asali ba su da gami da tafiyar siyasar Kwankwasiyya, amma saboda kasuwar buƙata ce,...
    Akwai makoma mai haske wajen raya sabon karfin samar da ci gaban ayyukan gona, wanda tabbas zai taimaka wa Sin da kasashen Afirka wajen gaggauta zamanantar da ayyukan gona, har ma da zamanantar da kasashensu baki daya.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Donald Trump ta kawo karshen wani shirin Amurka na bunkasa samar da wutar lantarki a Afirka, wanda aka kaddamar fiye da shekaru 10, in ji Bloomberg. Shirin wanda tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama ya kaddamar a shekarar 2013, yana da nufin samar da wutar lantarki ga miliyoyin gidaje a nahiyar Afirka, wanda Hukumar raya kasashe ta Amurka (USAID) ke tafiyar da shi. Wannan na daga cikin shirin Trump na rage kashe kudade na tarayya wanda ma’aikatar ingancin gwamnati ke jagoranta. Kusan dukkanin manufofin shirin “Power Africa” ​​an sanya su cikin jerin shirye-shiryen da za a kawar da su. A ranar 20 ga watan Janairu, ne shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka ta dakatar da...
    Shugabannin kasashen Afirka ta Kudu da Malesiya da kuma Colombia sun bukaci da a hukunta laifukan da Isra’ila ke yi na keta dokokin kasa da kasa. A makalar da suka rubuta a mujalar harkokin waje, shugabannin sun bayyana cewa “Zabin abu ne mai wuyar gaske: ko dai mu yi aiki tare don tilasta dokokin kasa da kasa ko kuma mu yi kasadar rugujewar sa.” Shugabannin sun kara da cewa “harin da ake kaiwa al’ummar Falasdinu ya yi daidai da ababe marasa dadi da munin tarihin da suka faru a cen baya kan kasashensu”, da suka hada da mulkin mallaka, yaki da ta’addanci da wariyar launin fata. “Muna iya fitowa daga nahiyoyi daban-daban, amma muna da tabbacin cewa rashin tsawatarwa na...
    Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.  Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...
    Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku kan zargin cin amanarta. Sauran waɗanda jam’iyyar kan zargin cin amana sun haɗa da Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.  
    Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na Beirut,bayan da aka dauki tsawon yau ana gudanar da jana’izarsa. Dubun dubatar mutanen Lebanon da kuma wasu daga wajen kasar ne su ka halarci taron jana’izar Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin da  aka gudanar a cikin birnin Beirtu. Tashar talabijin din al’mayadin ta bayyana cewa bisa kirdado adadin mutanen da su ka halarci jana’izar sun kai mutane miliyan daya da 400,000. Mahalarta jana’izar sun cika filin wasa na birnin Beirut da kuma manyan tituna ta yadda babu masaka cinke, da hakan ya sa motar da take dauke da makararsa da...
    Ƙaramin Ministan Gidaje da Tsara Birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya bayyana cewa ɗan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a Zaɓen 2023 Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara. Sai dai Ministan ya ce ƙaddarar hukunci daga Allah ne ya sanya a yanzu haka ba shi ke riƙe da madafan iko a Jihar Kanon ba. Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Ata ya faɗi hakan ne yayin da yake barazanar ficewa daga jam’iyyar APC muddin ake sake naɗa Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar Kano. Ministan ya ce kalaman da shugaban jam’iyyar ya riƙa furtawa su ne dalilin da Allah Ya ƙwace mulkin jihar...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta kasa da kasa. Wang, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babbar darektar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, a birnin Johannesburg, birni mafi girma kuma cibiyar hada-hadar tattalin arzikin Afirka ta Kudu. A nata bangaren, Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, a tsakiyar rudanin da duniya ke fama da shi, kasar Sin ta hau kan turba mai kyau,...
    A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD. Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu...
    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
    Binciken Ra’ayoyi Na CGTN: Watan Daya Da Dawowar Trump Mulki, Mutanen Duniya Sun Ce Da Wuya A Ce An Gamsu Da Salonsa
    Kamfanin mai na kasar Sin (CNPC) ya sanar a yau Alhamis cewa, ya kammala aikin hakar rijiyar man fetur mafi zurfi a yankin Asiya, yayin da rijiyar ta kai zurfin mita 10,910 a hamadar arewa maso yammacin kasar Sin. Rijiyar wacce aka fi sani da “Shenditake 1” da ke tsakiyar hamadar Taklimakan a cikin kwarin Tarim, a jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur, ta kasance wani gagarumin aiki na binciken kimiyya. Bayan neman albarkatun man fetur da gas, an kuma tsara aikin rijiyar don zurfafa nazarin juyin halittar duniya da kuma zurfafa ilimin binciken kasa. A cewar kamfanin CNPC, an fara aikin hakar rijiyar ne a ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2023, inda aka shafe fiye da...
    “Kungiyar malaman jami’o’i, reshen KASU na son sanar da jama’a cewa, majalisar zartaswarta ta kasa ta amince da bukatar reshen kungiyar na tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar, 18 ga Fabrairu, 2025.   “Majalissar ta yi watsi da alkawuran da gwamnatin jihar Kaduna ta dauka na rashin tabbaci, da cikakkun bayanai, da kuma lokacin da za a iya aiwatar da alkawuran kan biyan hakkokin mambobin kungiyar,” in ji sanarwar.
    Sakataren harkokin waje na kasar Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa kasashen Amurka da Rasha sun kuduri anniyar kawo karshen yakin Ukrai, banda haka zasu kara kyautata dankon zumunci da tattalin arziki a tsakaninsu. Shafin yanar gizo na labarai, Arabnews ta gwamnatin kasar Saudiya ya bayyana cewa, ya nakalto Rubio yana cewa kasashen biyu sun amince da sake bude ofisoshin jakadancin kasashen biyu a Washington da kuma Mosco, sannan zasu kafa kwamiti na musamman don kawo karshen yaki da kuma kyautata dangantaka tsakanin kasashen biyu. Daga karshen zasu yi aiki tare don bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Har’ila taron da kasar Saudiya ta dauki bakwancinsa a jiya Talata ya sami halattar tokwaransa na kasar Rasha Sergey Lavrov, kuma shi ne...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karɓar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. Domin sauke shirin, latsa nan
    Babban kwamandan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa: Sun sabunta hanyoyin da sojojin Iran zasu mayar da martani kan duk wani harin wuce gona da iri kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bada umarni Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdur-Rahim Mousawi ya bayyana cewa: Tun tsawon kwanaki da suka gabata jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana cewa: Idan Amurka ta farma tsaron al’ummar Iran, to lallai Iran za ta kai farmaki kan tsaronta ba tare da wata shakka ba, wannan ya kasance umarni ne bayyananne ga dakarun Iran, kuma kwamandojin sun sabunta shirinsu na aiwatar da wannan umarni, kuma a halin yanzu Iran a shirye take tsaf don gudanar da umarni a aikace. Manjo Janar...
    Shan ruwa hanya ce mafi sauwi wajen magance kumburin ido domin, ruwa yana wanke dauda a Ido. A samu cokulan karfe kamar biyar zuwa shida a saka a firiji na tsawon minti 10 zuwa 15 sannan a cire su, sai a rika shafawa a kumburin Ido har sai ido ya sabe. Ganyen shayi yana magance kumburin Ido: A jika ganyen shayi a ruwan dumi, sannan a cire a bari ya huce. Sai a kwanta a dora jikakkiyar jakar ganyen shayin a kan idanu sai a rufe idanu da kyalle mai tsabta. A bari ya tsaya a hakan na tsawon minti biyar zuwa goma sannan a cire. Wata hanyar magance kumburin ido ita ce: A samu gurji a yanka sannan a...
    Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida. Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta. Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Tsaron ruwa bai kamata ya zama kayan aikin matsin lamba kan kasashen waje ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Bai kamata tsaron teku ya zama wani makami na matsin lamba kan kasashen waje ba, sai dai ya zama sakamakon hadin gwiwa tsakanin kasashen yankin. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bude taron ministocin kasashen tekun Indiya karo na 8 a birnin Muscat na kasar Oman a yau Lahadi, Araqchi ya ce: A yau mun hadu a kasar da aka sani tsawon shekaru aru-aru a matsayin gada da ta hada tsakanin gabas da yamma, kuma tsakanin manyan wayewa da al’ummomi na kusa da na nesa. Ya kara da...
    Sannan a kudu maso kudu, masu goyon bayan sabbin jihohi suna son a samar da jihohin Ogoja, Warri, da Bori daga jihohin Kuros Ribas, Delta da Ribas, da kuma Jihar Obolo daga jihohin Ribers da Akwa Ibom na yanzu. Daga kudu maso yamma kuwa, akwai shawarwarin samar da sabbin jihohi shida. Jihohin da ake shirin kirkira sun hada da Toru-ebe da za a sassaka daga jihohin Delta da Edo da Ondo na yanzu, da kuma jihohin Ibadan da Lagoon da za a sassaka daga jihohin Oyo da Legas, bi da bi. Sauran sun hada da Jihar Ijebu da za a samar daga Jihar Ogun ta yanzu da kuma jihohin Oke-Ogun da Ife-Ijesha da za a kirkiro daga jihohin Ogu da...
    Sai dai kuma, bayan bayyana a taron da gwamnonin tafkin Chadi suka yi a Borno na cewa, tubabbun ‘yan ta’adda sama 5000 ne suka sake haduwa da iyalansu, Jabi ya ce; babu shakka wannan wani cin fuska ne ga fuskokin wadanda aka kashe da kuma jaruman sojojin da suka mutu. Haka nan, ya kuma sake bayyana hadewar komawar tasu cikin al’umma a matsayin wani babban kuskure wajen aiwatar da manufofin da suka dace. Ya kara da cewa, “Abin da ya kamata mu yi wa ‘yan ta’adda shi ne, mu tabbata sun girbi abin da suka shuka. Saboda haka, idan har da gaske muke wajen kawar da ta’addanci a fadin wannan kasa, ya kamata mu sanya ido yadda ya kamata....
    A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin. Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da ke Amurka (CGCC) da aka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka, Xie ya bayyana cewa, barazanar haraji ba za ta taba yin tasiri a kan Sinawa ba, a maimakon haka, masu yi za su buge ne da illata ginshikin yaki da miyagun kwayoyi da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kara tsadar kayayyaki ga iyalan Amurkawa da harkokin kasuwanci...
    Kwamandan sojan na Iran  Birgediya Janar Hamid Wahidi ya bayyana cewa, Iran tana da cikakken shirin na aiwatar da umaranin babban kwamandan sojin kasa, kuma akidarmu ta yaki, ta ginu ne akan kariya, amma kuma a lokaci daya za mu fuskanci duk wanda ya kawo mana hari, da karfi. Birgediya  janar Hamid Wahidi ya bayyana hakan ne dai a lokacin bikin kaddamar da lambobin yabo da sadaukarwa ga iyalan shahidai na sojan sama, inda ya ce: “A wannan lokacin da ake ciki, Muna cikin wani yanayi mai matukar hatsari a duniya, amma a ranar sojan sama jagoran juyin juya halin musulunci ya shata mana ka’idoji masu kima da za mu yi aiki da su da, kuma za su kasance wadanda...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya miƙa wa sabon Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi sandar sarauta, a wani biki da aka gudanar a filin wasa na garin Bama. A yayin bikin, Gwamna Zulum ya yi alƙawarin kammala titin Maiduguri zuwa Banki domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Najeriya, Kamaru da Chadi. Dokokin gyaran haraji sun tsallake karatu na biyu a majalisa An yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga a Kaduna Haka kuma, ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar da kammala Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya da ke Bama da kuma dawo da wutar lantarki a yankin. Zulum, ya ƙara da cewa za a ci gaba da tallafa wa masarautar da gyara gine-ginen da Boko Haram suka lalata. Hakazalika,...
    An cafke wani saurayi mai kimanin shekaru 13 bayan ya je rajistar layin wayar salula a yankin ’Yan Katako da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Rundunar ’yan sandan Filato ce ta yi wa manema labarai holen saurayin mai suna Umar Hashim tare da wasu mutum shida da ake zargi da garkuwa da kuma kisan wani mai suna Tasiu Abdullahi a ranar 20 ga watan Disamba. DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa An harbe ’yan sanda biyu a Yobe Sai dai da yake yi wa manema labarai jawabi, Hashim ya bayyana cewa jami’an tsaron har gida suka je suka kama shi da cewa an yi amfani da lambar wayarsa wajen karɓar kuɗin fansar...
    Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna da rubuce-rubuce daban-daban sun ce, dole ne kamfanin ya samar da mafita mai dorewa tare da maido da wutar lantarki a tashar wutar lantarki ta ‘Kwara Poly feeder’ da ke rarraba wutar ga al’ummomin yankin.
    An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano. An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka. Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka. Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka. ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi...
    Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano ya ba al’ummar yankin Sheka awa 24 su kawo wa rundunar sunayen manyan ’yan daban da ke addabar yankin. Rundunar ta ba da wannan wa’adin ne bayan matsalar ’yan daba ta ya ƙi ci ta ƙi cinyewa a yankin da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. A yayin wani zama na musamman da kwamishinan rundunar ta yi da al’ummar yankin ne aka ba su wannan sanarwar. Kwamishinan ’yan sandan, wanda ya samu wakilci DPO na yankin Dakata, ACP Yusha’u Mus’ud, ya ce muddin al’umma ba su taimaka da bayanan jagororin ’yan daban ba, ta ɓata-garin an kama su ba, babu yadda za a yi ɓata-garin su daina addabar yankin. Ɗan fashi ya yi wa ɗaliban jami’a uku...
      Ga Yadda zaku hada: Da farko za ku samu Tukunya sai ku zuba sukarin a ciki, ku dora shi a wuta ya narke ya yi zafi ya dan tafasa, sai ku kawo lemon tsami guda daya ku matse a ciki sai ku bar shi ya dan dahu sannan ku sauke. Sai ku samu roba me dan girma, ku zuba fulawar a ciki sannan ku kawo Baikin Fauda ita ma ku zuba sai ku zuba dan Gishiri kadan ba da yawa ba sai ku zuba Bota idan kuma ba kuda Bota za ku iya zuba mai ku kwaba da shi, sai ku kwaba sosai ku juya shi ya juyu sosai, sannan ku samu abin murzawa ku yi ta buga shi,...
    Su tsare tsaren anyi shirin tabbatar dukkan makarantu masu zaman kan su da na gwamnati za su fara amfani da tsarin a watan Janairu 2025. Sai dai kuma watan Janairu ya wuce ba tare da samun wani ci gab aba dangane da lamarin. Rahoto ya nuna har yanzu da akwai sauran Rina a Kaba, domin kuwa da akwai karancin makarantu wadanda basu da irin kayan da za ayiu amfani da su wajen aiwatar da sabon tsarin,da kuma yadda za a horar da Malamai, hakan ta sa aka bar masu ruwa da tsaki cikin shakku ko sabon tsarin ilimin za afara amfani da shi. Sabon tsarin ilimin an yi niyyar fara amfanni da shi inda za a koyar da yaddaake sabbin...
    A cikin daren nan aka dawo da wutar lantarki a Jihar Kaduna. Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kaduna (Kaduna Electric) ya dawo da wutar be bayan kwanaki babu ita. An dauke wutar ne sakamakon yajin aiki da ma’aikatansa suka shiga tsawon kwana biyar. Kaduna Electric ne ke ba da wutar lantarki a Jihar Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi. Ma’aikaran sun janye yajin aikin ne bayan Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya shiga tsakaninsu da kamfanin.
    Sakatariyar kwamitin JKS na babbar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta bayyana a taron hukumomin kwastam na kasar a ranar 7 ga wata cewa, darajar cinikin waje na kasar Sin ta zarce manufar da aka tsara ta yuan triliyan 43 a karon farko a shekarar 2024, inda ta karu da kashi 5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar 2023, kuma ta ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi girma a fannin cinikin kayayyaki a shekaru takwas a jere. A shekarar 2024, an fuskanci karuwar rashin tabbas da rashin zaman lafiya a waje, duk da haka hukumar kwastam ta samar da hidimomi mafi kyau domin saukake da sa kaimi ga inganci da daidaiton yawan...
    Kotun manyan laifuka a kasar Tunisiya ta daure Shugaban kungiyar al-Nahdha ta masu kishin musulunci Rashid al-Ganushi, zaman kurkuku na tsawon shekaru 20. Haka nan kuma an daure wata ‘yar Jarida Shahrizad Ukkasha wacce take wajen kasar, zaman kurkuku na tsawon shekaru 22. Wata ‘yar jaridar da ita ma ta sami hukuncin dauri, ita ce Shuza Bilhaj, wacce za ta yi zaman kurkuku na tsawon shekaru5. Shi kuwa tsohon minista Lutfi Zaitun an  yanke masa hukuncin zaman kurkuku na shekaru 35, sai kuwa mai magana da yawun ma’aikatar harkokin cikin gida Muhammad Ali al-Aruri, shekaru 13 a gidan kaso. Yayin da tsohon shugaban gwamnatin kasar Hisham al-Mashishi zai yi zaman shekaru 35 a gidan kurkuku. Tun a watan Disamba na...
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da asuba. Lakurawa sun kashe mutum 1 sun jikkata 6 a Kebbi Yadda bom din Boko Haram ya kashe mutane a hanyar kasuwa a Adamawa Aƙalla masallata 10 da suka haɗa da Limamin ne aka ce an yi awan gaba da su a yayin harin. Jaridar Punch ta ruwaito DSP Ahmed Rufa’i, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Sakkwato ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Juma’a....
    A yayin zaman, Dakta Balarabe ta jaddada tsananin tasirin da katsewar wutar lantarkin ke yi ga muhimman ayyuka, musamman harkokin kiwon lafiya da harkokin kasuwanci a fadin jihohin da abin ya shafa.   Ta bukaci ma’aikatan da ke yajin aikin da su maido da wutar lantarki yayin da ake ci gaba da tattaunawa don samun maslaha.
    Zulum Ya Jagoranci Dawowar Ƴan Gudun Hijira 7,790 Daga Chadi
    Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar  Ukrain. Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.
    Tshohon daractan hukumar kare hakkin bil’ada ta MDD Craig Mokhiber ya yi kira ga Amurkawa su dawo daga rakiyar gwamnatin Trump da kuma firai ministan HKI Benyamin Natanyahu, mashayin jinin Falasdiwa, a dai dai lokacinda yake ziyararsa ta farko zuwa kasar Amurka tun bayan da Trump ya sake dawowa fadar White House. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Craig Mokhiber ya na fadar haka a shafinsa na X a jiya litinin, ya kuma kara da cewa, irin tarban da gwamnatin Trump ta bawa Natanyahu, da kuma yadda wasu yan majalisar dokokin kasar suka himmatu, ya nuna cewa babu bambanci a tsakanin gwamnatin Joe Biden da kuma Trump idan an yi maganar dangantar Amurka da HKI. Yace dukaninsu...
    HKI tana son aiwatar da wani shiri don kara yawan yahudawa a kasar, a dai dai lokacinda take fama da karancin yahudawa a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta ce a baya dai gwamnatin yahudawan suna son kara yawan  yahudawa musamman a yankin yamma da kogin Jordan, ammam har yanzun shirin baya tafiyar kamar yadda take so. Labarin ya kara da cewa yawan Palasdinawa a cikin kasar Palasdinu da aka mamaye wata barazana ce babba ga gwamnatin kasar. Banda haka a cikin yakin watanni 15 da ta fafata da Mutanen yankin Gaza, wasu yahudawa sun fice daga kasar kuma da dama daga cikinsu sun sha alwashin ba za su sake dawowa kasarba. Wasu kuma sun kai...
    Da marecen jiya Lahadi ne dai shugaban Majalisar dokokin Iran  Mahmud Mashahadani ya iso Tehran domin fara ziyarar aiki da zai gana da jami’an gwamnatin kasar. Mataimakin shugaban Majalisar Shawarar musulunci ta Iran Hamid Ridha Haji Babbayi  da kuma shugaban kwamitin kawancen majalisun kasashen biyu ne su ka tarbi Mashhadani a filin saukar jiragen sama na “Mehrbad”
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5 Ya ce hukumar ta karɓo kuɗaɗen daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce kowanne mahajjaci ya samu Naira 61,080. Ya kuma ce an tura wa kuowa kuɗinsa kai-tsaye zuwa asusun bakinsu. “NAHCON ta mayar da waɗannan kuɗaɗen ne saboda matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru...
    Kawo yanzu Kano Pillars, wadda take mataki na 10 da maki 29 za ta fafata da Remo Stars a wasan mako na 23.
    A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
    Darakta-Janar na Hukumar yi wa kasa hidima ta kasa NYSC, Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya tabbatar wa masu yi wa kasa hidima a fadin kasar nan cewa ba za a tura su yankunan da ke da kalubalen tsaro ba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga matasa masu yi wa kasa hidima da ke samun horo a sansaninsu da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Darakta Janar na NYSC wanda ke rangadi a sansanin masu yi wa kasa hidimar a jihar Zamfara, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ak tsaurara matakan tsaro a sansanin. Ya jaddada cewa, tsaro da jin dadin matasan na da matukar muhimmanci ga hukumar. Birgediya Janar Ahmad ya jaddada bukatar...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana cewa; babbar matsalar da  duniyar musulmi ke fuskanta ta samo tushe ne daga yin isa daga koyarwar musuluncin, da babu abinda hakan ya haddasa sai rabuwar kawuna da sabani, ya kuma bai wa makiya kafar da za su shiga. Shugaban kasar ta Iran wanda ya aike da sako zuwa wurin rufe ‘gasar karatun akur’ani mai girma karo na 41 da aka yi a birnin Mashhad, ya bayyana cewa; Alkur’ani mai girma yana yin Magana ne da musulmi a matsayin al’umma daya dunkulalliya, yake kuma yin kira a gare su da su yi riko da igiyar Allah da hadinkai, domin hana rabuwar kawuna. Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Shakka babu, wani sashe...
    Shugaban Hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya, NYSC Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed ya tabbatar wa mambobin shirin da suke aikin yi wa ƙasa hidima na shekara ɗaya cewa za su fara karɓar Naira 77,000 daga watan Fabrairu. A daidai lokacin da aka sake duba mafi ƙarancin albashi da hauhawar farashin kayayyaki, gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin kuɗaɗen alawus ɗin daga N33,000 zuwa N77,000 duk wata, amma da dama sun nuna damuwarsu kan aiwatar da hakan. Gwamna Buni ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Tafkin Chadi ’Yan bindiga sun kashe mutum 3 sun sace 24 a Zamfara A shekarar bara wani jami’in shirin ya danganta jinkirin aiwatar da biyan kuɗin da rashin kuɗi. Amma yayin da yake bayani ga...
    Tsohon shugaban kamfanin Google Eric Schmidt, ya bayyana bullar kamfanin DeepSeek na Sin a matsayin wadda ta kawo muhimmin sauyi ga takara a fagen kirkirarriyar basira ta AI a duniya. Wannan na kunshe ne cikin wani sharhi da jaridar Washington ta wallafa ranar Talata, inda Eric Schmidt ya jaddada cewa, karfin Sin na yin takara da manyan kamfanonin fasaha ba tare da amfani da albarkatu mai yawa ba, ya nuna bukatar da Amurka ke da ita ta karfafa karfinta a bangaren. Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta DeepSeek kamfanin Sin ne dake mayar da hankali kan kirkirarriyar basira ta AI, wanda aka...
    Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15. Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai. A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda...
    Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Max Air na tsawon wata uku, bayan ɗaya daga cikin jiragen kamfanin, tayarsa ta yi bindiga yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a daren ranar Talata. Jirgin Max Air ƙirar Boeing 734 mai lamba 5N-MBD ne ya samu matsalar kamar yadda rahotanni suka bayyana. Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Dukkanin fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun kuɓuta cikin ƙoshin lafiya. Wannan shi ne karo na uku da jirgin Max Air ke fuskantar matsala cikin watanni uku da suka gabata. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), ta sanar da...
    Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci.   Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin.   Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin.   Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”
    Sama da ’yan Najeriya 5,000 da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, na fuskantar barazanar dawo da su gida. Daga cikinsu, kusan 1,500 ne ake tsare da su, wanda hakan na daga cikin matakin da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka na korar baƙin haure da masu neman mafaka ba bisa ƙa’ida ba. Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Alƙaluman da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE), ta fitar a watan Nuwamban 2024, sun nuna cewa akwai mutum miliyan 1.445 baƙin haure da ke zaune a ƙasar ba tare da takardun izini ba, ciki har da mutum 3,690...
    Shettima ya yi alkawarin cewa, bisa umarnin shugaban kasa, gwamnati za ta hada hannu da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), kan hanyoyin da hukumomin kula da zirga-zirgar ababen hawa, da ma’aikatun sufuri na tarayya da na Jihohi za su hada kai don dakile yawaitar hadurran tankar mai a fadin kasar.
    Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar. Labarin ya kara da  cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan  birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare,  da...
۱