2025-03-31@23:40:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 887

«Jami ar Yakubu Gowon»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A ranar litinin da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu kan dokar dorawa kayakin kasar China da suke shigowar kasar Amurka da kudaden fito na kasha 20%. A maida martani na farko kasar China ta ce kara kudin fito kan kayakin kasarta ba tare da wani dalili karbabbe ba zai maida duniyar ta zama sai mai karfi yake rayuwa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar China Wang Yi yana fadar haka a yau Jumma’a a birnin beigin, ya kuma kara da cewa , bai kamata kasar Amurka ta maida alkhari da sharriba, saboda hakan zai maida duniyar kamar rayuwar dabbobi. Yace bai kamata kasashen duniya su nunawa kananen...
    Yansanda a birnin Lagos na kudancin kasar sun kama wasu yan kasar Pakistan biyu wadanda suke da hannu dumu-dumi a cikin aikin kamawa don neman kudaden fansa daga hannun wani dan kasar ta Pakistan dan shekara 48 a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran sun nakalto daga kafafen yada labaran kasar wadanda suka ji kakakin yansan na jihar Lagos Chief Superintendent Benjamin Hundeyin yana cewa, yan kasar Pakisatn da suka kama a wani dauki da suka wanda aka sace don neman kudaden fansa sun kama a ranar 5 ga watan maris akwia Roman Gull dan shekara 19 da kuma Aftab Ahmed dan shekarera 28 a duniya kuma yan asalin kasar Pakistan ne, wadanda suka hada kansu da wasu...
    Kakakin babban sakataren MDD ya bayyana damuwarsa kan abubuwan da suke faruwa a yankin yamma da kogin Jordan, inda sojojin HKI suke ci gaba da rusa gidaje, da bata yanyuyi da kuma dukan Faladinawa da suka hadu da su a yankin arewacin yamma da kogin na Jordan. Tashar talabijin ta Presstva anan Tehran ya nakalto Stephane Dujarric kakakin babban sakataren MDD yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa, wakilan Majalisar a yankun sun bada rahoton yadda sojojin HKI suka kutsa a cikin sansanin yan gudun hijira na al-Arroub wanda yake cikin yankin Shuyukh al-Arrub, inda suka daki wani matsayi da kasar bindiga har suka fasa masa bakinsa suka kuma karya masa kafa. Har’ila yau rahoton ya...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hadisi ya tabbatar da yadda cin abinci tare yana ƙara danƙon zumunci da ƙaunar juna da albarka a tsakanin al’umma. Mai yiwuwa wannan ne ya sa akan samu ƙarin kusanci da shaƙuwa a tsakanin duk iyalan da kan zauna su ci abinci. Ko kafin watan azumi dai, wasu magidantan kan mayar da cin abinci tare da iyalin su al’ada. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur Ba? DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shin ko mene ne matsayin buɗa-baki tare da iyali a watan Ramadana? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan irin alfanun da...
    A kasuwar Ariaria da ke Aba, NAFDAC, sun gano jabun magunguna da kudinsu ya kai na miliyoyin Naira. Bugu da kari, a kasuwar Idumota da ke a jihar Legas, NAFDAC sun garkame Shanguna sama da 3,000 bayan sun gano Shagunan shake da jabun magunguna. A kasuwar kan Gadar Onitsha, nan ma Hukumar ta sun kama manyan motoci goma shake da jabun magungana, inda a bayan kamen dilolin magungunan suka yi yunkurin bai wa jami’an na NAFDAC cin hancin Naira miliyan 135. Har ila yau, a kasurgumar kasuwar Cemetery da ke Aba, nan ma NAFDAC ta kama tare da kwace jabun magunguna da kudinsu ya kai na sama da Naira miliyan biyar. Bisa batun gaskiya, irin wannan bakar hada-hadar jabun magunguna,...
    Gwamnatin Syria ta ayyana dokar ta-baci a yankuna da dama na kasar bayan da aka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yadda gwamnatin kasar ke kara murkushe fararen hula. An sanya dokar ta-baci a birnin Tartus da ke arewa maso yammacin kasar da kuma daukacin lardin Homs a daren Alhamis. An kuma sanar da dokar hana fita a Latakia har zuwa karfe 10:00 na safe agogon kasar ranar Juma’a. Dokar hana fita ta biyo bayan zanga-zangar da ‘yan Alawiyyawa da mabiya Shi’a suka yi, wadanda suka yi Allah wadai da ta’addancin gwamnatin. Sun zargi gwamnatin rikon kwarya ta Syria da fifita mulki kan sake gina al’ummar kasar. Majalisar koli ta addinin musulunci ta Alawite a kasar Syria ta fitar da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya tafi kasar Saudiyya domin halartar taron ministocin kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, domin tattauna matakan da za a dauka na tinkarar shirin Amurka na tilastawa mutanen Gaza gudun hijira. A yammacin ranar Alhamis ne Araghchi ya tashi zuwa birnin Jeddah na kasar Saudiyya inda za a gudanar da taron a yammacin ranar Juma’a, in ji ma’aikatar harkokin wajen Iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya ce Iran ta bukaci taron ne domin jawo hankalin kungiyar OIC, a matsayinta na babbar kungiya a duniyar musulmi, kan batun da ya shafi al’ummar musulmi da kasashen musulmi. Shirin shugaban Amurka Donald Trump na raba Falasdinawan Gaza da kasarsu ta asali...
    “Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a lokacin da lamarin ya faru, mun yi magana da manema labarai, inda muka fayyace cewa ba da gangan ba ne, illa hatsari ne. Kasancewar Hafsan Sojin Sama a Zamfara na nuna ƙwarewa da kulawa ta musamman. Gwamnan ya bayyana cewa rundunar sojin saman Nijeriya na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙar ‘yan bindiga a Zamfara, Arewa maso Yamma, da ma kasa baki ɗaya. “Ina godiya da...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa yadda ta nuna damuwarta kan harkokin tsaro a jihar. Mataimakin Sufeta na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya, AIG Ahmed Ammani, ya bayyana haka a lokacin da ya kai wa Gwamna Umar Namadi ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse babban birnin jihar Jigawa. AIG Ammani ya yaba da dimbin tallafin da Gwamna Namadi ke bai wa ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ke aiki a jihar. Ya bayyana jihar Jigawa a matsayin daya daga cikin jihohin kasar nan masu zaman lafiya. A cewarsa, tun da ya samu mukamin AIG mai kula da shiyya ta 1, bai taba samun rahoton manyan laifuka daga...
    Kwanaki 29 ke nan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutane. An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna garin su tara, a wata ranar Laraba. An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan Janar ɗin da aka sace domin neman kuɗin fansa na Naira miliyan 250m. Wata majiya ta kusa da dangin ta shaida wa wakilinmu cewa, har yanzu ana ci gaba da...
    Maj.-Gen. Kangye ya kara da cewa dakarun da ke yaki da satar mai sun kwato lita 452,396 na danyen mai da aka sata, lita 224,175 na Man gas da aka tace ba bisa ka’ida ba, da kuma lita 1,920 na man fetur. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ziyarar wani bangare ne na tsarin Gwamna Dauda Lawal na tabbatar da ingantattun ayyuka a faɗin jihar da kuma tabbatar da kammala ayyukan a kan lokaci.   “A ranar Talata ne Gwamna Dauda Lawal ya fara ziyarar aiki domin duba ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa.   “An fara ziyarar ne da Babban Asibitin Gusau, ɗaya daga cikin manyan asibitocin da aka gyara, tare da samar mata da kayan aiki a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.”   A lokacin da yake duba aikin filin jirgin sama na Zamfara, Gwamna Lawal ya ce, gwamnatinsa ba wai kawai tana gina kowane irin filin jirgin saman ba ne, amma ana ginin ne na zamani wanda zai...
    Shugaban kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN Ali Muhammad Ali ya ce manyan taruka biyu na kasar Sin wato taron NPC da CPPCC sun zama muhimmiyar hanya ta fahimtar manufofin da gwamnatin Sin ke dauka da yadda take daidaita harkokinta da basirarta na zamanantar da al’ummar Sinawa. Ali Muhammad ya bayyana haka ne yayin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya kara da cewa, “Da farko mun zura ido kan nagartattun manufofin da Sin take dauka na daidaita harkokinta, wadanda tarukan biyu suka gabatar da su da sakamakon da take samu dangane da hakan a fili, manufofi kuma sun sauke nauyin dake wuyansu. Musamman ma a halin da duniya ke ciki na fuskantar manyan sauye-sauye, dabaru da...
    Yayin da tattalin arzikin kasar Sin ke kara samun tagomashi, masana daga sassa daban daban, na ganin hakan dama ce ta ci gaban duniya baki daya. Kamar dai yadda sakamakon wani bincike, na asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna yadda bunkasar tattalin arzikin kasar Sin ke shafar ci gaban tattalin arzikin duniya baki daya. Binciken ya nuna bunkasar tattalin arzikin Sin da karin kaso daya bisa dari, yake haifar da matsakaicin bunkasar tattalin arzikin sauran sassan kasa da kasa da kaso 0.3 bisa dari. Duba da haka, ma iya cewa duniya za ta ci gaba da shan romon bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, yayin da kasar ke ta kara fadada manufofinta na bude kofa ga sassan duniya....
    Da yammacin yau Alhamis ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar, kana shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, ya ziyarci mambobin taro na uku na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa wato CPPCC karo na 14 ta kasar Sin, wadanda suka zo daga kungiyar dimokuradiyya ta kasar Sin, da kungiyar raya dimokuradiyya ta kasar Sin, da kuma bangarorin ilimi. Shugaban na Sin ya kuma halarci taron kungiyar hadin gwiwa na CPPCC, domin sauraron ra’ayoyi da shawarwari. Yayin ziyartar mambobin majalisar ta ba da shawara kan harkokin siyasa, Xi ya jadadda cewa, ya kamata a karfafa amfani da ilmi don inganta kimiyya da fasaha da kuma kwararru, ta yadda za a kafa wani yanayi...
    Majalisar Dokokin ECOWAS, ta kafa wani kwamiti na musamman domin tattaunawa da shugabannin kasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar da suka fice daga kungiyar, tare da kokarin magance matsalolin siyasa a yankin Yammacin Afirka. Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, wanda mamba ne a Majalisar ECOWAS, ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai. Ya ce an yanke wannan shawara ne bayan wani taro da aka gudanar a Legas. A cewar Sanata Barau, manufar kwamitin ita ce tattaunawa da shugabannin kasashen AES don fahimtar juna da jaddada muhimmancin ci gaba da kasancewa cikin ECOWAS, musamman idan aka yi la’akari da dangantakar tattalin arziki da zamantakewa da ke tsakanin jama’ar yankin. Shugabar Majalisar Dokokin...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya bai wa manema labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, matakin na zuwa ne bayan wani kwakkwaran bincike da kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Bello Abdulkadir Fanini ya gudanar. “Rahoton kwamitin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Bashir Kazaure, biyo bayan sanarwar  batun biyan mafi karancin albashi...
    Dubban al’ummar Musulmi ne suka halarci jana’izar Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Izala na Ƙasa, Sheikh Hassan Jingir, a garin Jos. An gudanar da sallar jana’izar ne a ranar Alhamis a unguwar Anguwan Rimi da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato. Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na watanni 6 An sako ɗaliban jami’ar da aka yi garkuwa da su a Binuwai A cewar sakataren yaɗa labaran JIBWIS, Ahmad Ashiru, Sheikh Jingir ya rasu yana da shekara 70. Ya rasu a gidansa da ke Jos bayan fama da rashin lafiya. Ya rasu ya bar mata biyu da yara sama da 40. Ga hotunan yadda aka yi jana’izar:
    Har ila yau, jim kadan bayan ficewar Zelenskyy daga Washington, shugabannin kasashen Turai da suka hada da na Jamus da Faransa da Italiya da kuma Birtaniya suka yi gaggawar mara masa baya, yayin da wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka yi kakkausar suka ga Ukraine wanda a cewar Sanata Lindsey Graham na jam’iyyar Republican ta South Carolina, “sanadiyyar wannan ganawar da ta bar baya da kura, ka iya kawo karshen goyon bayan Washington ga Kyiv.” Shin abin tambaya a nan, da gaske ne wannan yunkurin na Amurka don kawo karshen rikici ne a tsakanin Ukraine da Rasha ko kuwa don amfanin kanta ne? Me ya sanya gwamnatin Trump ta fara wani gangamin tonon silili mai zafi kan Zelenskyy? Kwanakin baya...
    Kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ, FRCN Kaduna Chapel, ta jaddada kudirinta na inganta jin dadin mambobinta ta hanyar bullo da sabbin tsare-tsare da shirye-shiryen tallafi. Shugaban kungiyar, Kwamared Umar Adamu Sarikin Fada ne ya bayyana haka a lokacin rabon kayan abinci na Ramadan ga ‘yan kungiyar a Kaduna. Umar Adamu Sarikin Fada ya bayyana cewa shirin rabon kayayyakin na daga cikin dabarun da kungiyar ta keyi na dakile tasirin tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan. Ya tabbatar da cewa sama da ‘yan uwa Musulmi dari da hamsin ne suka ci gajiyar shirin na watan Ramadan na bana, inda ya jaddada cewa su ma Kirista na kungiyar sun samu irin wannan tallafi a lokacin bukukuwan Kirsimeti na 2024. Shugaban ya kuma...
    Kasar Tunisiya ta shiga cikin sabuwar dambaruwar siyasa saboda yadda ake yi wa wasu fitattun ‘yan siyasa, lauyoyi da kuma ‘yan jarida 40 shari’a, bisa zargin cewa suna yi wa kasa makarkashiya. An jibge jami’an tsaro masu yawan gaske a bakin kotun, yayin da a wajenta kuma masu fafutuka suke bayar da taken nuna kin amincewa da shari’ar, suna bayar da taken; ‘Neman ‘ ‘yanci, da kuma zargin ma’aikatar shari’a da zama ‘yar koren gwamnati. Lauya a cikin kwamitin lauyoyi masu bayar da kariya ga wadanda ake yi wa shari’ar, Lamia Farhani ta bayyana cewa; Abin ban mamaki shi ne shugaban kasa wanda ya rantse zai kare shari’a, wanda kuma shi kwararre ne akan tsarin mulki shi ne na farkon...
    Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya. Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan kasar ya zama abin dariya ba, kamar a kwanaki kadan da su ka gabata da ya mike a gaban majalisa ya yi barazanar aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya. Haka nan kuma ta zargi Fira ministan kasar da cewa za su yi amfani da batun kara yawan taimakon soja ga Ukiraniya domin kara haraji a cikin gida. Tun bayan da aka yi cacar baki a...
    Wakilin ɗan wasan, Jorge Mendes, ne ya tabbatar da batun sabon kwantiragin, yana mai cewa, duba da yadda Yamal ke taka leda a halin yanzu, yana da muhimmanci ya ci gaba da kasancewa tare da Barcelona. Ƙungiyoyi da dama sun nuna sha’awar ɗaukar Yamal, amma Barcelona ta dage cewa ba za ta bari ya bar ƙungiyar ba. Sabuwar yarjejeniyar za ta ƙara masa ƙarin kuɗin shiga da kuma kariya daga ƙungiyoyin da ke zawarcinsa. Yanzu dai abin jira shi ne ranar da ɗan wasan zai saka hannu kan sabon kwantiragin domin tabbatar da amincewarsa da ci gaba da taka leda a Camp Nou. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
    Shugaban kungiyar marubuta wasanni ta kasa SWAN, Kwamared Isaiah Benjamin, ya bukaci sabon kwamitin hadin gwiwar SWAN da aka kaddamar da su farfado da kungiyar ta hanyar jawo masu zuba jari don tallafa wa marubutan wasanni a fadin kasar nan.   Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin kwamred Isaiah Benjamin ya jaddada mahimmancin karfafa kudi ga ‘yan jaridun wasanni, yana mai baiwa kwamitin ‘yancin gudanar da aiki yadda ya kamata.   “Aikin da ke gaba yana da girma, amma ina da yakinin iya karfin ku na karfafa tattalin arzikin marubutan wasanni a Najeriya ta hanyar hadin kai. Kuna da cikakken goyon bayanmu, ”in ji shi.   Ya bayyana cewa zaben ‘yan kwamitin wanda shugaban kungiyar SWAN na jihar Nasarawa,...
      Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Yakubu Sani Haidar a matsayin babban shugaban ma’aikatan jihar Zamfara.   Nadin wanda ke fara aiki nan take, ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ta bakin babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Sulaiman Ahmad Tudu.   A cewar sanarwar, Haidar ya gaji Ahmad Liman, wanda ya yi ritaya a ranar 28 ga Fabrairu, 2025.   Haidar, wanda ya kammala karatunsa na kimiyyar siyasa a shekarar 1989 a Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, an nada shi Babban Sakatare a shekarar 2012, kuma ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi gwamnati da dai sauransu.   Gwamna Lawal ya bayyana...
    ’Yan sanda sun kama wani korarren jami’in shige da fice a yayin da yake kokarin sayar da makamai Ga ’yan ta’adda. Kwamishinan ’Yan Sanda na Babban Birnin Tarayya, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa an kama jami’in ne a hanyarsa ta kai wa ’yan ta’addan bindigogi a yankin Zuma da ke Ƙaramar Hukumar Bwari. Da yake jawabi a hedikwatar rundunar, CP Olatunji Rilwan, ya bayyana cewa dubun korarren jami’in tsaron ta cika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu, 2025. Ya bayyana cewa jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ƙarƙashin jagorancin OC Mustapha Muhammad ne suka kama shi, bayan samun bayanan sirri. NAJERIYA A YAU: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Su Ga Ragi A Farashin Man Fetur...
    Shugaban ma’aikatan Tsaron kasar Amurka ko Pentagon Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka a shirye take ta shiga yaki da China, bayan da Beijing ta tabbatar da cewa zata tunkari kasar Amurka da dukkan karfinta kan ko ta ina ta fito mana a adawar da take nunawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hegseth yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake hira da shirin labarai na tashar talabijin ta Foxnews na Amurka. Seketarin tsaron tsaron ya kara da cewa dok wanda yake son zaman lafiya to ya shiryawa yaki. Don haka kasar Amurka, inji Hegseth dole ta tabbatar da tana da sojojin masu karfi da makamai masu inganci don shiriwa ko ta kwana, saboda...
    Jakadan JMI a hukumar makamashin Nukliya Mohsen Naziri ya bayyana cewa sabbin takurawar da kasashen yamma, musamman Amurka suke wa kasarsa ba zasu yi tasiri ba. Banda hakan zasu cutar da wadanda suka dora mana su, Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Naziri yana fadar haka a Jawabin da ya gabatar  a taron gwamnoni hukumar ta IAEA a birnin Geneva a jiya Laraba. Ya ce kasashen yamma ne suka jagoranci karin takunkuman tattalin arziki a kan Iran, ko kuma bayyana cewa Iran bata bada hadin kai da ta dace ga hukumar makamashin Nukliya ta duniya wato IAEA. Da kuma zargin kasar Iran da cewa tana kokarin mallakan makaman Nukliya. Naziri ya zargin kasashne yamma kan rashin cika...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Fiye da wata guda ke nan bayan da Matatar mai ta Ɗangote ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 890 zuwa naira 825 kowace lita. Bayan wannan ragi ne dai shi ma Kamafanin Mai na Kasa (NNPCL) ya sanar da rage nasa farashin. Sai dai  har yanzu ba a ga ragin a gidajen mai  ba. NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Ba Mu Bayar da ‘Ramadan Basket’ Ba DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan wannan lamari. Domin sauke shirin, latsa nan
    Gwamna Mallam Umar Namadi na jihar Jigawa ya karbi lasisin yin hada hadar kasuwanci na kasa da kasa, wato kasuwanci maras shinge a kan iyakar  Maigatari a hukumance, wanda hukumar kula da sarrafa kayayyaki ta Najeriya NEPZA ta bayar kwanan nan. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa, kwamishinan kasuwanci, da masana’antu, Alhaji Aminu Kanta ne ya mika wa Gwamna Umar Namadi lasisin a ofishinsa. Hamisu Mohammed Gumel ya bayyana cewa, tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati mai ci ta dukufa wajen gudanar da aikin karbar lasisin aikin daga NEPZA A cewarsa, wannan ya nuna karara da kudurin gwamnati na...
    A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa. Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da...
    A gefe guda, Akpabio ya musanta duk zarge-zargen da ta ke yi masa, yayin da Majalisar Dattawa ta tura Akpoti-Uduaghan zuwa kwamitin ladabtarwa saboda taƙaddamar da ta shiga tsakaninta da Shugaban Majalisar kan batun sauya wajen zama. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da yammacin yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bitar rahoton aikin gwamnatin kasar, na tawagar lardin Jiangsu, a taro na uku na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14. Xi ya jaddada cewa, a matsayinsa na lardi mai karfin tattalin arziki, dole ne lardin Jiangsu ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaban kasar Sin, musamman ma a fannin sa kaimi ga inganta kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha, da dunkulewar masana’antu, da sa kaimi ga inganta zurfafa yin gyare-gyare, da bude kofa ga kasashen waje, da shigewa gaba wajen aiwatar da manyan tsare-tsare na ci gaban kasar, da kuma ba da misali a fannin samar da wadata ga jama’a baki daya. (Safiyah Ma) Daga...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York. Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.” Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya...
    Kasar Afrika ta Kudu, ta yi Allah wadai da yadda ta ce Isra’ila ke amfani da yunwa a matsayin makamin yaki a Gaza ta hanyar toshe agajin jin kai ga Zirin tun ranar Lahadi. Isra’ila na “amfani da yunwa a matsayin makamin yaki” a Gaza ta hanyar toshe inji Afirka ta Kudu a wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar yau Laraba 5. “Ta hanyar hana shigowar abinci a Gaza, Isra’ila na ci gaba da amfani da yunwa a matsayin makamin yaki,” in ji Pretoria, wacce dama tun tuni ta shigar da korafi kan Isra’ila akan kisan kiyashi a Gaza a gaban kotun duniya. Afirka ta Kudu ita ce kasa ta baya-bayan nan da ta yi Allah-wadai da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da shirin sake gina Gaza na Masar da aka amince da shi a wani taron gaggawa na kasahen Larabawa da aka yi a birnin Alkahira. Hamas ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, taron na birnin Alkahira ya nuna wani muhimmin mataki na daidaita alaka tsakanin Larabawa da Musulunmi da Falasdinu, musamman a ci gaba da hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da yi a zirin Gaza, da yammacin kogin Jordan da kuma al-Quds. Kungiyar ta yabawa shugabannin kasashen Larabawa da suka yi watsi da yunkurin raba Falasdinawa da kasarsu, tana mai danganta da sako mai cike da tarihi. Hamas ta yi marhabin da kiran tana mai bayyana shi a matsayin “tsari...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan wannan jawabi, Sanata Natasha ta gabatar da ƙorafi bisa dokar majalisar, imda ta zargi Akpabio da cin zarafinta da kuma amfani da matsayinsa ba daidai ba. Ta kuma nemi izinin miƙa ƙorafin ga majalisar a hukumance. Majalisar ta tura ƙorafin zuwa Kwamitin ladabtarwa domin ci gaba da bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya raba kayayyakin agaji na watan Ramadan na sama da Naira miliyan 200 ga al’ummar mazabarsa. Ya yi hakan ne da nufin tallafa wa al’umma domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, duba da halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki. A wajen bikin kaddamar da rabon, Yusuf Dahiru Liman, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Bashir Adamu Nababa, ya jaddada aniyarsa ta rage wahalhalun da al’ummar mazabarsa ke fuskanta. Ya bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani bangare na alkawarin da ya dauka na inganta walwalar jama’a a yayin  yakin neman zabe. Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki, Isiyaku Adamu Nababa, ya jaddada cewa shirin ya...
    Shuwagabannin kasashen Turai da wakilai daga kasashe 19 na Kungiyar, sun kammala taro a birnin Lodon, inda suka nuna goyon bayansu ga kasar Ukraine, musamman kan yadda ya dage wajen kare kasarsa da kasashen Turai  a gaban Donal Trum a ranar Jumma’an da ta gabata, ya waste ba tare da kasashen sun bayyana abinda zasu iya yiwa Ita Ukraine a yakin da take ci gaba da fafatawa da Rasha ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa matsalolin da suka taso dangane da dogaron da kasashen turai suke yi kan kungiyar Tsaro ta NATO yana daga cikin manya-manyan al-amura da suka tattauna. Yakin cacarbakin da shugaba Trump na Amurka yayi da shugaban kasar Ukraine ya zama masomin...
    Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza. Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba. Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci...
    ’Yan sanda sun ceto wani mutum mai shekaru 48, Alhaji Samaila Muhammed, da aka yi garkuwa da shi a ƙauyen Lano da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba ta Jihar Gombe. An gudanar da aikin ceton bisa tsari tare da haɗin gwiwar ‘yan banga na yankin, lamarin da ya tabbatar da cewa mutumin ya shaƙi iskar ’yanci salin-alin. Gobara ta ƙone shaguna 17 a tsohuwar kasuwar Gombe Mijina bai hana ni waƙa ba sai dai… – Fa’iza Badawa Wakilinmu ya ruwaito cewa, mahukunta sun tabbatar da ƙoshin lafiyarsa sannan daga bisani aka sada shi da ’yan uwansa. Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Gombe, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar, ya tabbatar da aniyarsu ta ci gaba...
    Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
    Kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto a jiya Talata cewa, shugaba Vladmir Putin ya amince da zama mai shiga tsakanin Iran da Amurka. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya amanci cewa, kafafen watsa labarun Rasha sun nakalto majiyar fadar mulkin kasar “Kremlin” na cewa shugaba Vladmir Putin zai zama mai shiga tsakanin Iran din da Amurka. Haka nan kuma kafafen watsa labarun na Rasha sun ce; Rasha da Amurka sun amince su yi wata tattaunawa ta daban akan Iran”. Mataimakin shugaban kasar Rasha ya ambaci cewa, a yayin zaman da kasashen biyu su ka yi a Riyadh na Saudiyya, sun tattauna akan abinda yake da alaka da Iran. Majiyar ta kuma ce abinda kasashen biyu suke son yin Magana...
    Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje.   Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar yabo ta kasa ta jami’in tsaro na Tarayya (OFR) kuma ya yi fice a Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabaru (NIPSS).   Hukumomin tsaro tuni suka fara gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi masa, inda ake kokarin zakulo wadanda suka aikata laifin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area 1 da ke babban birnin ƙasar. Masu garkuwa sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice a Abuja Tinubu ya naɗa Babatunde Ogunjimi Akanta Janar na Tarayya Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh ta fitar a yammacin wannan Talatar, ta ce tsohon babban jami’in Hukumar Shige da Ficen ya mutu ne a ɗakin wani otel...
    Sai dai, Firaministan Ukraine Denys Shmyhal ya ce, har yanzu Kyiv na da isassun makamai da za ta kai wa dakarunta dake yaki a gaba-gaba.   “Taimakon kayayyakin Soji na Amurka yana da mahimmanci kuma yana ceton dubban rayuka, don haka, Kyiv za ta yi duk mai yiwuwa don ganin ta ci gaba da alaka da Washington”. In ji Shmyhal   Shmyhal ya kara shaida cewa, “Muna da mafita ɗaya kawai – nasara don tsira. Ko dai mu ci nasara, ko kuma wani ya rubuta mana shiri na biyu.”   A nata bangaren, fadar Kremlin ta Rasha ta ce, katse tallafin soji ga Ukraine shi ne matakin da ya fi dacewa don samar da zaman lafiya. Daga kanmu, magana...
    A ko da yaushe kasar Sin na tsayawa tare da kasashe masu tasowa a matsayinta na kasa mai tasowa kuma mamba na wadannan kasashe. Kakakin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin karo na 14, Lou Qinjian ne ya bayyana hakan a ranar Talata a taron manema labarai, inda ya ce, kasar Sin za ta rika shiga a dama da ita, kuma za ta kasance mai bayar da shawarwari kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa. Da yake tsokaci game da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigar da su daga kasar Sin, Lou ya ce, daukar matakin da Amurka ta yi bisa radin kai ya saba wa ka’idojin kungiyar...
    Rahotanni sun nuna cewa kasar Yamen ta gargadi isra’ila game da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a gaza, kana ta yi alkawarin fadada hare-harenta a tel Avivi matukar ta dawo da kai hari kan alummar falasdinu, Tace: matakin da isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin agaji da jin kai a yankin gaza, da kuma rufe dukkan mashigar dake isa zuwa yankin,  take dukkan dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar da aka cimma. Ana sa bangaren shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar yamen sayyid Abdul malik Hutsi ya bayyana cewa matukar Isra’ila ta dawo da kai hari a yankin Gaza to za ta mayar da martani mai tsananin a ko ina a Israila...
    Kamfanin dillancin labarun “Sana” na kasar Syria ya ambaci cewa; jiragen yakin HKI sun kai hare-haren a wani wuri dake gefen garin Tartus, sai dai babu rahoto akan asarar rayuka har yanzu. Kamfanin dillancin labarun “ Sana” ya ci gaba da cewa; Ma’aikatan agaji suna kokarin gano hakikanin inda aka kai wa harin. Su kuwa sojojin  HKI sun  sanar da kai hari ne akan wani rumbun makamai dake yankin “Kardaha’. Wannan ba shi ne karon farko da sojojin na HKI su ka kai hari a garin Tartus ba,  a ranar 16 ga watan Disamba ba sun kai wannan irin harin.
    Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna  a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya  Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja. Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa;               “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa...
    Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya Litinin. Ya kuma kara da cewa, akwai alamun Natanyahu Firai ministan HKI yana son ya sake komawa yaki a Gaza. Hamdan ya ce, kafin haka gwamnatin HKI ta dakatar da aikin aiwatar da yarjeniyar da suka kulla da ita, yana son ya yi watsi da ita, sannan ya bukaci a sake tattaunawa kan sauran abubuwan da suka zo a cikin yarjeniyar. Jami’in na Hamas y...
    Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin . Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar. Wannan har’ila yau zai kara fadin kasuwar kasashen kungiyar ta SADC. Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.
    Haka kuma, an sake zaɓar Mojisola Meranda a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar bayan sauka daga matsayinta na kakakin majalisar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
    Hukumar kula da gandun daji da filayen ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, namun dajin kasar ta Sin sun karu yadda ya kamata ba tare da cikas ba. Adadin manyan dabbobin Panda ya karu daga kimanin 1,100 a shekarun 1980 zuwa kusan 1,900 a yau, yayin da yawan damisar dusar kankara ya kai fiye da 1,200. Sai kuma adadin giwayen daji nau’in na Asiya da ya karu daga fiye da 150 zuwa sama da 300. A fannin shuke-shuke da tsirrai na daji kuwa, an samu nasarar dawo da nau’o’in halittunsu fiye da 200 dake cikin hadarin bacewa bat a duniya, kuma yawancin jinsunansu sun farfado tare da samun kariya yadda ya kamata....
    Ministan harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya ce shirin sake gina Gaza wanda ya baiwa Falasdinawa yancin ci gaba da zama a kasarsu, za a gabatar da shi a taron gaggawa na kasashen Larabawa da za a yi a wannan mako. Abdelatty a wani taron manema labarai a ranar Lahadin nan ya jaddada cewa shirin sake gina ba zai kasance na Masar ne kawai ko kuma na Larabawa ba amma zai nemi goyon bayan kasa da kasa don tabbatar da aiwatar da shi cikin nasara. Abdelatty ya ce “Za mu yi tattaunawa mai zurfi tare da manyan kasashe masu ba da taimako da zarar an amince da shirin a taron kasashen Larabawa mai zuwa.” Abdelatty ya ce bayan taron gaggawa...
    Wani mutum wanda aka bayyana a matsayin Abdulrashid Usman, ya yanke jiki ya mutu a yayin da yake buɗa-baki a yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida mai suna Suleiman Bala, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da aka ɗauki azumi, lokacin da mamacin da abokansa suke buɗe-baki a majalisarsu da ke yankin Kutunu a Ƙaramar Hukumar Gwagwalada. Ya ce Usman da abokansa suna zaune a kan benci suna cin ’ya’yan itatuwa ne ya yanke jiki ya faɗi, rai ya yi halinsa. Nan take abokan suka garzaya da shi zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa. A cewarsa, marigayin, wanda yake cikin koshin lafiya, ya dawo daga Kaduna ganin buɗa-baki, daga nan ya je...
    Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin noman rani ta hanyar amfani da rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Maigatari. Hakan wani muhimmin mataki ne  na samar da abinci da zamanantar da noma a jihar Jigawa. A cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan Hamisu Mohammed Gumel ya rabawa gidan rediyon Najeriya ya ce, gwamnan ya bayyana cewa, aikin da ake amfani da shi ta hanyar amfani da hasken rana da kuma amfani da dabarun noman rani, yana yana taimakawa wajen yin noma a kowane lokaci na shekara tare da bunkasa tattalin arzikin manoma. A cewarsa, shirin mai fadin hekta 10 wanda aka samar da rijiyoyin burtsatse na zamani guda hudu do  tallafa wa kananan manoma...
    Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wa ta sabon tattaunawa da kuma sauya yarjeniyar tsagaita wuta da aka cimma da HKI dangane da yaki a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mahmoud al-Mardawi wani babban jami’in kungiyar yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa ‘ba zamu tsawaita kashi na farko na yarjeniyar ba, haka ma ba za mu amince da gabatar da sauye –sauye a cikin yarjeniyar ba. Mardawi yace HKI za ta karbi fursinonin da suka rage a hannun Hamas kadai ne, ta hanyar ko tsarin da yarjeniyar ta amince da shi. Ya ce: Benyamin Natanyahu yana, cikin dimwa...
    Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta gargadi HKI da kuma Amurka kan cewa, tana sanya ido a kan yadda suke sabawa yarjeniyar budewa juna wuta da suka cimma da su. Musamman yadda HKI ta sabawa yarjeniyar a mashigar Rafah na barin abinci ya shiga Gaza, da kuma bukatar sake tattauna wasu al-amura a yarjeniyar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran nakalto Hazem Al-asad mamba a majalisar siyasa ta kasar Yemen, yana fadar haka, ya kuma kara da  cewa, kungiyar a shirye take ta sake shiga yaki da Amurka, a duk lokacinda suka yi kokarin cutar da mutanen Gaza. Al-Asad ya gargadi gwamnatin Amurka da masu goyon bayan HKI a duk wata cutarwa da zata yiwa mutanen Gaza. Har’ila yau,...
    Archbishop Okoh ya buƙaci jama’a da su zauna lafiya tare da bin hanyoyin doka domin shawo kan lamarin. Ya ce CAN ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen ganin an samar da daidaito a tsarin ilimi, ba tare da nuna bambancin addini ba.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mahukuntan Saudiyya sun buɗe shafi na musamman domin yin rajista ga masu sha’awar yin ibadar Itikifa a watan Ramadan da muke ciki a ƙasar. A ranar Lahadi, 1 ga watan Ramadana ne aka sanar da buɗe shafin ga masu sha’awar yin Itikafi ’yan asalin ƙasar da kuma baƙi. Sanarwar ta bayyana ka’idojin da masu sha’awar za su cika domin samun gudanar da ibadar a kwanaki 10 ma ƙarshen watan Ramadan a masallatan Haramin Makkah da Madina da sauransu masallatan ƙasar. Bayanan da ake buƙata sun hada da: Ɓacewar bindigogi 4,000: Sakaci ne dalili —’Yan sanda NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan MDD ta taya Musulmi murnar zuwan watan Ramadan 1- Ƙasar mutum: Ta asali...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ɗora laifin ɓacewar bindigo 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu game da kula da makamai. Da take ƙarin bayani kan yawaitar ɓacewar bindigon, rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba su san ciwon kansu ba wajen aiki. Rundunar ta bayyana takaicinta ne a wata takardar cikin gida daga “TERROFOR ABUJA” wanda wakilinmu ya yi katarin samu a ranar Lahadi. Takardar ta fito a yayin da Majalisar Dattawa take gudanar da bincike kan rahoton Babban Mai Binciken Kudi na Tarayya da ya nuna manyan bindigon ’yan sanda 3,907 sun ɓace. A kan haka ne Kwamitin Majalisar...
    ’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina. ’Yan bindigar sun sace daliban ne a ɗakunan kwanansu da ke yankin Paris Quarters a garin na Dutsinma. Maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kutsa yankin ne da misalin ƙarfe 4 an asubahin ranar Lahadi, suka yi awon gaba da ɗaliban. Jami’an tsaro sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa, amma kafin su isa wurin ’yan bindigar sun riga sun riga sun tsere da ɗaliban. Dutsinma na daga cikin ƙananan hukumomin Jihar Kastina da suka fi dama da matsalar ’yan bindiga da ke satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, duk kuwa da matakan da gwamnati da kuma hukumomin...
    Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a ci gaba da yaki. Sergey Lavro ya kuma ce; tunanin aikewa da dakarun zaman lafiya zuwa Ukiraniya wauta ce. Lavrov ya bayyana shugaban kasar Ukiraniya Zelenskiy  da cewa dan Nazi ne, wanda ya ha’inci al’ummarsa.”
    A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka yi jana’izar  Sam Nujoma wanda shi ne ya samo wa kasar  ‘yanci bayan tsawon shekaru na gwgawarmaya. Mahalarta jana’izar ta Nujoma sun kunshi iyalansa, mata,’ya’yan da jikokin, sai shugabannin kasashen Afirka na da, da masu ci. A yayin jana’izar an bayyana Nujoma a matsayin wani gwarzo na fada da mulkin mallaka da tsarin wariya da ya kare nahiyar ta Afirka.” Shugaban kasar Namibia mai ci a yanzu ya bayyana Nujoma da cewa; Gwarzo ne da za a rufe shi a cikin makabartar da gwarazan kasar suke kwance. Kuma shi na musamman ne daga cikin ‘ya’yan wannan kasa, sannan kuma dan juyin juya hali. Mahalarta jana’izar dai sun fito ne daga...
    Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar. Walid Junbilat  wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma bakin Isra’ila a cikin harkokin wannan yankin, musamman abinda yae faruwa a kudancin Syria. Dan siyasar na kasar Lebanon  wanda ya yi taron manema labaru a jiya Lahadi ya yi gargadi akan yanayin da ake ciki a yankin “Jabalu-Duruz” da tsoma bakin HKI domin haddasa rashin tsaro a cikin wannan yankin. Haka nan kuma ya yi tuni da yabo akan tarihin gwgawarmayar ‘yan Duruz’ da...
    ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Wannan ta’addanci ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba. Gwamna Nasir Idris ya bayar da tabbacin inganta a tsaro jihar. Ganin yadda mutane ke cikin tsoro, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar jaje ƙauyukan a ranar Asabar. Ya tabbatarwa da al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin shawo kan matsalar tsaro, musamman...
    ’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha Girke-girken Azumi: Yadda ake yin Tsiren Dankali Wannan ta’addanci ya jefa mazauna yankin cikin tsananin fargaba. Gwamna Nasir Idris ya bayar da tabbacin inganta a tsaro jihar. Ganin yadda mutane ke cikin tsoro, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kai ziyarar jaje ƙauyukan a ranar Asabar. Ya tabbatarwa da al’ummar yankin cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin shawo kan matsalar tsaro, musamman...
    Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo da ya gabatar ga taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, kasancewar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Sin da Amurka a duniya, abu ne da ya zama wajibi kuma nauyi ne dake kan wuyansu. Xie Feng ya jaddada cewa, idan kasashen biyu suka dauki juna a matsayin abokan hamayya, kuma suka shiga mummunar gasa, kasashen za su yi rashin nasara, kuma duniya za ta sha wahala. Amma idan suka zama abokan huldar juna, da samun nasara tare, za su samu ci gaba tare, da kuma amfanar da duniya baki daya. Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin...
    Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su. Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da...
    ’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki. Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi. Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan Ramadana Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.” ’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi...
    Kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa sojoji a shirye suke su shiga cikin rikicin da ya barke a garin Jarmana dake kusa da birnin Damascuss na kasar Syria domin kare ‘yan Duruz. Ofishin Fira ministan HKI Benjemine Netanyahi ya fitar da sanarwa a jiya Asabar da marece, yana ce; Netanyahu da ministansa na yaki Yesra’il Kats sun bayar da umarni ga sojojin kasar da su kasance cikin shiri domin kare ‘yan Duruz a garin Jarmana dake bayan binin Damascuss. Ofishin watsa labarai na ministan yakin na HKI ya ce; Nauyi ne a wuyanmu mu kare ‘yan’uwanmu Duruz a cikin Isra’ila, da kuma hana a cutar da su a cikin Syria, don haka za mu dauki duk wani mataki...
    Shugaban kasar Ukrain Volodomyr Zelesky ya samu tarba mai kyau a kasar Burtaniya bayan ya isa birnin London a jiya Asabar kuma bayan cacan baki mai zafi da yayi da shugaban Amurka Donal Trump a fadar White House dangane da yakin Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa shugaba Zeleski ya gana da firaiministan kasar Burtania Keir Starmer, wanda ya yaba masa kan yadda ya tsayawa kasarsa da kuma kasashen turai a gaban shugaban Amurka Donal Trump da mataimakinsa a ranar jumma’an da ta gabata. Labarin ya kara da cewa shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya zanta da shuwagabannin biyu, wato Trump da kuma Zeleski don kwantar da hankali. A yau Lahadi ce za’a gudanar da taro na musamman...
    Rundunar Basij a yankin kudu maso gabacin kasar Iran ta bada sanarwan shahadar dakarunta guda biyu a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran, ya nakalto rundunar IRGC na yankin ya na bada sanarwan shahadar Hojjatoleslam Sadeq Mahmoudi da kuma Milad Damankesh a lokacinda suke komawa gida daga wurin aiki a cikin wata mota tasu. Labarin ya kara da cewa shahidan biyu sun hadu da ajalinsu ne a lokacinda wasu yan ta’adda suka bude wuta a kan motarsu a lokacinda suke wucewa a wata unguwa zuwa gidajensu. Lardin Sitan Baluchistan wanda ke kan iyaka da kasar Pakistan dai ya dade yana fada da kungiyoyin yan ta’adda wadanda suke shigowa kasar daga kasar Pakistan, wadanda kuma suke samun taimako...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta bayyana a jiya Juma’a cewa, tashar jirgin ruwa ta Tanga da kasar Sin ta inganta yanzu tana jigilar sama da tan miliyan 1.2 na kaya a duk shekara, adadin da ya karu daga jigilar tan 400,000 a kowace shekara. “Habaka tashar ta Tanga ya inganta ayyukanta.” a cewa Hassan a jawabinta ga kasar a karshen ziyararta a yankin Tanga. Tana mai cewa, babban kamfanin gine-gine mallakin kasar Sin wato China Harbor Engineering Compnay, shi ne ya yi aikin inganta tashar ta Tanga. Ta kara da cewa, inganta tashar da aka yi ya kuma samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da shirye-shiryen mayar da tashar ta zama cibiyar jigilar takin zamani da...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba jaddada cewa, kasar Sin ta girmama ikon mallakar kasa da cikakken yanki na kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik, da girmama bukatunsu da al’adun kabilunsu da kuma hadin gwiwarsu wajen samun ci gaba da kansu. A kwanakin baya, yayin da firaministan kasar tsibiran Cook Mark Brown yake hira da wakiliyar babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG, ya bayyana cewa, Sin ta kiyaye girmama kasashen tsibirai na yankin tekun Pasifik a fannoni 4. Firaminista Brown ya yi nuni da cewa, kasarsa ta tsibiran Cook ta dora muhimmanci ga girmamawar da Sin ta nuna mata, kasar Sin ta kiyaye yin hakan tun da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu....
    Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma. Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan. Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma. Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan. “Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar. “Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.” Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar...
    A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar. Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA)’ ta haramta amfani da iran wadannan tankunan man ne daga yau Asabar 1 ga watan Maris, saboda ceton rayukan mutanen kasar. Dokar dai zata shafi ayyukan mutanen, don wasu zasu rasa ayyukansu. Dokar ta kara da cewa, daga yau tankunan man masu daukar lita 45,000 zuwa kasa ne kawai za’a a barisu dauki man fetur zuwa wasu wurar daga deport. Sai kuma kungiyar...
    Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa kasar Yemen a shirye take ta sake shiga yaki idan yarjeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu ta wargaje. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar ta hotunan bidiyo a jiya 28 ga watan Fabrairun shekara ta 2025. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bayyana cewa birnin Tel’aviv wato Yafa, zai zama babban wurin da makaman kungiyar zasu nufi idan hakan ya faru. Huthi ya ce “Idan yaki ya sake barkewa za mu kai hare-hare a ko ina a HKI sannan birnin Tel’aviv zai za ma babbar manufar makamammu. Yace: Kasar Yemen ta na kallom yadda al-amura suke tafiya...
    Ya bayyana cewa rundunar ta damu matuka da faruwar lamarin, kuma ta himmatu wajen tabbatar da an yi adalci, yana mai cewa “Muna hada kai da hukumomin makarantar da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo wadanda ake zargin tare da kama su. Za a sanar da ci gaban lamarin a kan lokaci,” in ji shi. Tun da farko dai, jaridar PUNCH Metro ta ruwaito cewa, a ranar Litinin din da ta gabata ne mahukuntan jami’ar suka rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da dalibai suka yi kan kisan abokin aikinsu. Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa wakilinmu a Katsina a safiyar ranar Litinin cewa, “wasu jami’an CJTF sun bindige dalibai biyu ne bisa kuskure, suna tunanin...
    Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Lokacin harin, mutum biyu sun jikkata, yayin da ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya rasa ransa sakamakon harbin da wani daga cikin mutanensa ya yi. Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace...
    Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya. Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan. A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan. A nan  Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai...
    Bayanai Hudu Da Ya Kamata A Sani Dangane Da Kiwon Kifi A Nijeriya: 1- Kimanin Kashi 40 Kacal Ake Iya Cimma Bukatar Samar Da Shi A Nijeriya: A cewar wata kididdiga ta Bankin Duniya, Nijeriya a 2018, ta samar da yawan Kifin da ya kai kimanin 1,169,478, wanda ya kai kimanin kashi 40 cikin 100, wanda bukatarsa da ake da ita a Nijeriya a shekara daya, ta kai kimanin tan miliyan 3.4, inda sauran wanda ake bukatar fitarwa waje ya kai kashi 60 cikin 100. 2- Kamun Tarwada A Nijeriya Fitacciyar Sana’a Ce: Samar da Tarwada a Nijeriya, ya karu daga tan miliyan 21,700 a 1999 zuwa tan miliyan 316,700 a 2015, wanda ya karu da sama da kashi 1,400...
    Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027. Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasar. Kazalika, ya yaba wa Shugaban Kwamtin kan gundunmawar da ya bayar wajen gainin an samar da wadannan ayyuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta duba yiwuwar inganta cibiyar lafiya tare da kafa makarantar sakandare a garin Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu. Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da gidan marayu da makarantar islamiyya, wanda dan asalin yankin Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya ya gina a matsayin wakafi ga mahaifinsa. Malam Umar Namadi ya bayyana jin dadinsa bisa wannan  kokari na Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya. Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan matakin domin amfanin talakawa da marasa galihu a cikin al’umma. Ya  jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da irin wadannan mutane...
    Alkaluman da hukumar kididdga ta kasar Sin ta bayar a yau Jumma’a sun shaida cewa, yawan mutanen kasashen waje da suka shigo babban yankin kasar Sin ba tare da biza ba a bara, ya kai miliyan 20.12, adadin da ya karu da kaso 112.3%. Bisa ga alkaluman, yawan baki masu yawon shakatawa da suka shigo babban yankin kasar a bara ya kai miliyan 131.9, wanda ya karu da kaso 60.8%, kuma daga cikinsu miliyan 26.94 ’yan kasashen waje ne, sauran kuma sun fito daga yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin. Sa’an nan, kudin da baki masu yawon shakatawa suka kashe ya kai dala biliyan 94.2, wanda ya karu da kaso 77.8%. Ban da haka, yawan mazauna...
    Bankin na CBN ya sanar da cewa, daukacin Bankunan, ana sa ran su bi wannan umarnin nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shadidan Hizbullah kimabi 130 ne aka yi jana’izarsu a yau jumma’a a kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran tanakalto kungiyar Hizbullah na fadar haka, ya kuma kara da cewa kungiyar ta gabatar da shihidar da dama saboda kare kasarsu, saboda kare kasar Lebanon daga mamayar HKI. Labarin ya kara da cewa an gudanar da jana’izar ne a garuruwan Aitarun da kuma Aita shaab. Inda mutanen da dam dagayankin zuka halarta . Labarin ya kara da cewa Shahidan sun kai ga shahada ne a hare-haren da sojojin HKI suka kai kan kudancin kasar ta Lebanon a cikin watannin Octoba da kuma Nuwamba na shekara ta 2024. Labarin ya kara da cewa a yakin dai mutanen leabin kimani...
    Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da Sergei Shoigu, sakataren majalisar tsaro ta kasar Rasha, a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, Xi Jinping ya ce, Sin da Rasha sun kasance masu tuntubar juna a dukkan matakai, da aiwatar da matsayar da suka cimma da shugaba Putin da hadin gwiwa mai muhimmanci da moriyar juna tare da zurfafa hadin gwiwarsu a kai a kai, domin taimakawa muradunsu na bai daya na samun ci gaba da farfado da kasashen biyu. Ya kara da cewa, ya kamata kasashen 2 su karfafa hadin kai a harkokin da suka shafi yanki da ma duniya, su kuma goyi bayan rawar da kasashen BRICS da kungiyar hadin kai ta Shanghai suke takawa, tare da...
    Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya yi wani kakkausan gargadi game da rahotannin rashin biyan albashi da rashin biyan ma’aikatan jihar, inda ya bayyana hakan a matsayin tauye hakkin ma’aikata da kuma cin amanar jama’a.   Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da kwamitin bincike mai mutane bakwai, karkashin jagorancin Hon. Abdulkadir Abdussalam, domin gano musabbabin sabanin.   Sakataren gwamnatin jiha Alhaji Umar Faruk ya wakilta, ya ce kwamitin ya hada da manyan jami’an gwamnati da masana harkokin kudi da wadanda suka kware a tsarin biyan albashi.   Yace Membobin Kwamitin sune Abdulkadir Abdussalam_ – Shugaban, Kwamishinan Karkara da Ci gaban Al’umma Dr. Bashir Abdu Muzakkari – memba, mai ba da shawara na musamman kan...
    A 2024, rundunar ‘yansanda ta Abuja, sun kama wani mai suna Nuhu Ezra, a yanikin Lugbe dauke da Kokon kan mutum da Kasuwansa, inda wanda ake zargin, ya yi ikirarin cewa, ya ci karo da Kokon kan mutum da Kasuwan ne, a yayin da yake yin farauta a cikin Dajin Kuje. Kazalika, duk dai a 2024, rundunar ‘yansanda ta jihar Ondo, sun cafke wani mai suna Yusuf Adenoyin, a yankin Isua, na karamar hukumar Akoko ta kudu maso gabas dauke da Kokon kan bil Adama guda takwas. A Jihar Oyo ma, rundunar ‘yansanda ta jihar ta kama wasu mutane biyu a yankin Amuloko da ke garin Ibadan, bisa zargin samun dauke da danyen Kokon kan wata mata , da ba...
    An bude cibiyar tattarawa da yada labarai game da manyan taruka biyu na kasar Sin na shekara-shekara, a otel na Media Center dake birnin Beijing a jiya Alhamis. Za a kaddamar da taro karo na 3 na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 ne a ranar 5 ga watan Maris, yayin da za a bude taro na 3 na majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 14, a ranar 4 ga watan na Maris. Sama da ‘yan jarida 3,000 ne suka yi rajistar daukar rahotannin tarukan biyu na bana, wanda zai kawo karshen wa’adin tsarin raya kasa karo na 14 da wa’adinsa ya fara daga shekarar 2021 zuwa 2025. Daga cikin ‘yan jaridar, sama da...
      Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.   Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.   Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da bukatar zuwa Hajji su tuntubi jami’an hukumar a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar ko su ziyarci hedikwatar hukumar dake kan titin Katsina, a cikin garin Kaduna.   Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa mutum dubu uku da dari hudu da sittin (3,460) ne suka biya kudin Hajji ta hannun hukumar.   Ya kuma kara da cewa kudin Hajji ya kama naira...
    A ranar 27 ga wata ne babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya kaddamar da gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya a birnin Beijing. Babban daraktan CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, masana’antar mutum-mutumin inji ta zama wata muhimmiyar alama ta auna matsayin wata kasa ta fuskar kimiyya da fasahar kere-kere da kuma masana’antar kere-kere na babban mataki. Kasar Sin ta zama kasa mafi grima a duniya wajen kera mutum-mutumin inji da yin amfani da su. Ta hanyar dogaro da babban dandalin watsa labaru mai karfi, gasar basira ta mutum-mutumin inji ta duniya ta CMG za ta nuna nasarorin da aka samu wajen kera mutum-mutumin inji ta kowane bangare, ta yadda za a hada karfin...