2025-02-28@20:44:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 140

«cinikayya da»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Sojojin Sudan sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar Rundunar sojin Sudan ta sanar a yau jiya Talata cewa: Sojojinta da mayakan da suke goya musu baya sun kwace iko da birnin Al-Kamlin da ke jihar Aljazira a tsakiyar kasar, kuma babban hafsan hafsoshin rundunar sojin kasar Janar Abdul-Fattah Al-Burhan ya yi alkawarin samun nasara a nan kusa kadan kan wadanda ya kira ‘yan tawaye. Sojojin Sudan sun watsa labarin ta hanyar kafofin Facebook da Instagram tare da wallafa faifan bidiyon yadda al’ummar birnin suka fito kan tituna suna bayyana murnarsu da ‘yantar da birninsu daga hannun ‘yan tawaye tare da bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba ga sojojin Sudan. A nasa...
    Wata gobara da ta tashi a wata makarantar tsangaya da ke Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda a Jihar Zamfara, ta yi ajalin almajirai 17. Dukkanin almajiran sun ƙone ƙurmus, ta yadda ba a gane kowa a cikinsu ba. Saura ƙiris Bello Turji ya zo hannu – Ministan Tsaro Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta farq ne cikin daren ranar Talata, kuma ta ɗauki kimanin sa’o’i uku tana ci. Rahotanni sun bayyana cewar wasu almajirai 16 sun samu munanan raunuka a gobarar. Wani mazaunin yankin, Abdulrasaq Bello Kaura, ya bayyana cewa gobarar ta fara ne sakamakon kamawar wasu itatuwa da aka ajiye. Wani ganau ya shaida cewar, “Abin ya faru ne a makarantar Malam Ghali,...
    Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya bayyana cewa sun kusa da kama ƙasurgumin ɗan ta’addan nan da ya addabi yankin Arewa Maso Yamma, Bello Turji. Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya tana da tabbacin cewa matsalar tsaro za ta zama tarihi kafin ƙarshen shekarar 2025. Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya  Tinubu ya ƙara kasafin kuɗin 2025 zuwa N54.2trn “Shugaban ƙasa na cewa yaushe matsalar tsaro za ta ƙare, saboda lokacin da ya kamata ta ƙare ya yi. “A wani zama da muka yi da shi da shugabannin hafsoshin tsaron, an tattauna sosai, kuma shugaban ya ce su faɗa masa yaushe matsalar za ta ƙare, suka ce da yardar Allah zuwa ƙarshen shekarar nan,” in ji shi....
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Shugaban kasar Amurka donal Trum ya bayyana anniyarsa na aiki tare da kungiyar kasashen masu arzikin man fetur don rage farashin man fetur a duniya. Shugaban ya bayyana cewa zai yi aiki da kasar Saudiya UAE da sauransu don rage farashin man man fetur a duniya. Kuma daga nan yana ganin aka iya kawo karshen yakin da ke faruwa a kasar  Ukrain. Shugaban ya fadi haka ne a jawabinda da ya gabatar a taron tattalin arzikin da aka gudanar a Davos na kasar Swizziland. Duk tare da tattaunawa ta abokantaka da kuma bukatar a a kara yawan man fetur a kasuwannin duniya, zuwa dalar Amurka triliyon guda.
    Kungiyar Hamas wacce take iko da yanin zirin gaza ta bada sanarwan cewa a shirye take, masu shiga tsakanin, wato kasar Masar ta fara tattaunawa marhala ta biyu na tattaunawar tsagaita wuta a Gaza. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin laran AFP na kasar Faransa yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, wani jami’in kungiyar wanda baya son a bayyana sunansa ya ce kungiyar a shirye take a fara tattaunawar.. A wannan tattaunawa dai ana saran za’a fayyace filla-filla kan yadda al-amura zasu kasance a nan gaba a zirin gaza. Labarin ya kara da cewa jami’an Hamas sun bayyana haka ne a ranar da aka yi musayar fursinoni da HKI a garin Khan Yunus....
    Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husaini Salami ya tabbatar da cewa: Makamai masu linzami na Iran suna da karfin kai hari kan duk wani wuri da ke da alaka da makiya a yankin da kuma fatattakar makamai masu linzami, yana mai jaddada cewa; sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna da karfin kalubalantar makiya a kowane lokaci. Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da jawabi ne a wajen bikin “Malik Ashtar” karo na 14 a safiyar yau Litinin, inda ya ce...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya gudanar ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu dangane da batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma huldar diflomasiyyar Iran. Baqa’i ya tabo batun ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya kai zuwa kasar Qatar, inda ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne bisa tsarin alakar diflomasiyya ta al’ada tsakanin kasashen biyu....
    Jakadan kasar Iran a Pakisatan ya bayyana bukatar shuwagabannin kasashen biyu su kara yawan musayar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, zuwa dalar Amurka biliyon $10. Tashar talabijian ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Reza Amiri Moghadam yana fadar haka a wani taro da aka gudanar tsakanin Jami’an kasashen biyu a cibiyar kasuwanci ta Rawalpindi a kasar ta Pakistan. Ya kuma ce dole ne shuwagabannin kasashen biyu tsara yadda hakan zai kasance. Muqaddam ya kuma kara da cewa gwamnatocin kasashen biyu suna da dangantaka ta hanyoyi da dama, wadanda suka hada da kasuwanci, al-adu, addini da tsaro da sauransi. Cibiyar kasuwanci da kuma kamfanoni a kasar Pakistan yana daga cikin cibiyoyin kasuwanci mafi girma a kasar ta Pakistan. Daga karshe Jakadan...
    Jakadiyar MDD na musamman kan al-amuran Falasdinawa, ta bada sanarwan cewa HKI ta fadada aikin kissan kare dangi da take yi a Gaza zuwa dukkan kasar Falisdinu, ta kuma kara da cewa wannan halin ya nuna cewa HKI tana son ta kara fadada kissan kiyashin zuwa garin Jenin da kuma yankin yamma da kogin Jordan gaba daya. Francesca Albanese ta bayyana haka ne a shafin ta na X, a jiya Lahadi, ta kuma yi kira ga kasashen duniya su shigo cikin al-amarin don kawo karshen kisan kare dangi da kuma rusa gidajen Falasdiwa da ta fara a yankin Jeneen. Daga karshe Jami’ar ta MDD ta bayyana cewa a halin yanzu kissan kiyashi da rushe-rudhen gidajen falasdinawa bai tsaya kan Gaza...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura. Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna. ’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5 Ya ce hukumar ta karɓo kuɗaɗen daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON). Ya ce kowanne mahajjaci ya samu Naira 61,080. Ya kuma ce an tura wa kuowa kuɗinsa kai-tsaye zuwa asusun bakinsu. “NAHCON ta mayar da waɗannan kuɗaɗen ne saboda matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru...
    Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a taron shugabannin ƙasashen Afrika kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya, inda Nijeriya ta gabatar da shirin dala biliyan 32 na faɗaɗa samar da wuta zuwa shekarar 2030. An Sace Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki 18 A Cikin Kwanaki 6 – TCN Jami’in Kenya: Fasahar Sin Na Ingiza Samar Da Wutar Lantarkin Kenya Ta ce duk da...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta nuna adawa da rashin amincewa da matakin da Amurka ta dauka na sanya karin harajin kashi 10 cikin dari kan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasar Sin, kuma za ta dauki matakan da suka dace don kare halaltattun hakkokinta da moriyarta. Kakakin ya jaddada cewa, “Kasar Sin tana tsaye kan matsayinta ba ja da baya. Babu wanda zai yi nasara a yakin cinikayya da haraji.” Yana mai cewa, karin harajin bangare daya na Amurka ya sabawa ka’idojin WTO. Kuma wannan matakin ba zai iya magance matsalolin Amurka na gida ba kuma mafi mahimmanci, ba zai amfanar da kowane bangare ba,...
    A jiya Asabar kasar Amurka ta sanar da kakaba karin harajin kwastam na kaso 10% kan kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa Amurka. Dangane da batun, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta bayyana rashin jin dadi da kin amincewa daga bangaren Sin. Cikin sanarwar da ma’aikatar ta gabatar, ta ce matakin Amurka ya keta ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, wanda ba zai ba da damar daidaita matsalar da kasar Amurka ke fuskanta ba, maimakon haka, zai lalata huldar hadin gwiwa tsakanin kasashen 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Ban da haka, ma’aikatar kasuwanci ta Sin ta ce, kasar Sin za ta kai kara ga kungiyar cinikayya ta duniya, da daukar matakai don mayar da martani ga matakin Amurka....
    Haduwar farko shine wanda AC Milan ta yi nasara da ci 3–2 tsakaninta da Internazionale Milan a gasar Italian Football Championship a ranar 10 January, 1909.   Wanda yafi yawan jefa kwallaye: Andriy Shevchenko kwallaye 14.   Nasara mafi girma: inter Milan 0–6 Ac Milan a gasar Serie A (11 May 2001).   Dan wasan dayafi buga wasan Derbi Madonnina Paolo Maldini wasanni 56.   Haduwar da akafi jefa kwallaye Inter Milan 6-5 Ac Milan (6 Nuwamba 1949).   Dan wasan da yafi yawan kwallaye a wasa guda José Altafini kwallaye 4 (27 Maris 1960).   Dan wasa mafi shekaru daya jefa kwallo a wasan Zlatan Ibrahimović Shekaru 39 (26 Janairu 2021).   Gaba daya a tarihi, kungiyoyin biyu...
      Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu.   Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane mahajjati ya karɓi sama da naira dubu sittin da ɗaya a asusunsa bakinsa.   Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne saboda katsewar wutar lantarki a lokacin da maniyyata ke Muna, wanda ya shafi tsarin sanyaya iska kuma hakan ya janyo musu matsala.   Hukumar Alhazai na Jihar Kaduna ta ta yaba da hakurin wadanda har yanzun basu same...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Aragchi yana bayyana matakan da sabuwar gwamnatin Amurka zata dauka idan har tana son sake samun yardar samun yardar kasar Iran. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a lokacinda yake hira ta musamman da tashar talabijin ta Al-jazeera ta kasar Qatar a birnin Doga. Ministan ya kara da cewa gwamnatocin Amurka da suka shude daga ciki har da gwamnatin Trumps suka yi a baya musamman ficewarta su daga yarjeniyar JCPOA.  Abbas Argchi ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci wanda dole ne Amurka ta yi idan tana son jawo hankalin iran dangane da tattaunawa da ita shi ne sako kudaden ta masu yawa wadanda ta hana a yi amfani...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    A wani bayani da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana alhininta na shahadar babban hafsan mayakan rundunar “Kassam” ta kungiyar Hamas Muhammad Dhaif  tare da wasu abokan aikinsa, tare da bayyana rawar da  suka taka a fagen gwagwarmaya. Kungiyar ta Hizbullaha ta mika sakon ta’aziyya da kuma barka akan shhadar Muhammad Dhaif ga kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas da sauran kungiyoyin Falasdinawa da kuma al’ummar Falasdinu. Haka nan kuma kungiyar ta Hizbullah ta mika sakon ta’aziyyar ga iyalan shahidan. Kungiyar gwgawarmayar musuluncin ta Lebanon ta kuma ambaci cewa, Muhammad Dhaif ya tafiyar da dukkanin rayuwarsa ne wajen fada da ‘yan sahayoniya da kwankwasar kansu, musamman ma dai a yayin farmakin Aksa, da ya kasance daya daga cikin fitattun wadanda...
    An bayyana dangantakar cinikayya tsakanin kasar Sin da Afrika a matsayin wadda ta taimaka wajen gaggauta ci gaba da samar da irin zamanantarwar da nahiyar ke bukata domin ta kasance cikin takara a duniya. Muya Guo, shugabar sashen Sin a bankin Stanbic na Kenya ne ta bayyana haka yayin wata hira a Nairobin Kenya, inda ta ce dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Afrika tare da jarin da kasar ta nahiyar Asiya ke zubawa, sun dora nahiyar kan tafarkin samun ci gaba, yayin da ta zamanantar da muhimman bangarori kamar na kere-keren kayayyaki. ‘Yan Adawa Sun Caccaki Buhari Kan Kalamunsa Na Cewa, ‘Allah Ne Kadai Zai Iya Gyara Nijeriya’ Fatara Da Talauci Na Yi Wa ‘Yan Nijeriya Miliyan 13 Barazanar Fadawa...
    Masu haƙar zinare aƙalla mutum 10 sun mutu wasu da dama sun ɓace bayan zaftarewar ƙasa a kansu a wani filin haƙar ma’adinai yankin Koulikokro na ƙasar Mali. Hukumomin yankin sun bayyana cewa mata ne yawancin masu haƙar zinaren da abin ya rutsa da su mata ne, kuma an kasa ciro gawarwakinau, “saboda tsananin sarƙaƙiyar yanayin.” Gwamnatin yankin ya bayyana cewa ajali ya rutsa da su ne a ƙauyen Danga, a cikin wani rami mai ruwa da laka, wanda zaftarewar ƙasar ta binne su a ciki a ranar Laraba. Ta bayyana a shafinta na Facebook cewa “abin takaicin shi ne babu ko mutum ɗaya da ya tsira a cikin su.” Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya...
    A nata jawabin, babbar mai shari’a ta Jihar Gombe, Mai Shari’a Halima S. Mohammed, ta bayyana cewa an shigar da kararraki guda 616 wadanda suka shafi manya da kananan laifuka da kuma cin zarafi a babbar kotun jihar, daga cikinsu 555 an kammala shari’arsu, inda wadanda suka rage ba su kai 70 ba. Ta bayyana godiya ga Gwamna Yahaya bisa ba da kwangilar biliyoyin naira na gina babbar sakatariyar kotun da sauran taimako da dama. Babban Lauyan gwamnatin jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barrister Zubairu Muhammad Umar, ya bayyana cewa gwamnatin Yahaya ta taka rawar gani wajen samun nasarorin da ma’aikatarsa ta samu a yunkurinta na ciyar da sashin shari’a gaba.
    A ranar Litinin, hukumar Tsaro ta DSS da Majalisar Ulama sun kira Sheikh Bin Uthman da AY Maikifi don tattaunawa. Majalisar Ulama ta shawarci Sheikh Bin Uthman da ya koma masallacinsa na asali, amma har yanzu ba a san ko zai amince da hakan ba.
    Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kori kwamishinoni guda biyar daga muƙamansu. Wannan ma cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Architect Samuel Jatau, ya fitar da yammacin ranar Alhamis. Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai Sanarwar ta bayyana cewa sauke kwamishinonin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka, sai dai ba a bayyana dalilin korarsu ba. Sanarwar ta bayyana cewa korar kwamishinonin ba zai rasa nasaba da gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba, musamman ganin yadda suka kwashe shekara guda wajen gudanar da ayyukansu. A cewar wata majiya, gaza yin aiki yadda ya kamata ne ya sa aka cire su daga...
    Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis. Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da wadanda suke da rai zuwa neman gawaki kawai, tunda ana ganin da wuya a sami wani da rai a cikin fasinjojin jirgin. Ya zuwa yanzu dai an tsamo gawakin mutane 30, kuma suna ci gaba da aikin gano wasu karin gawakin. Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa jirgin fasinjar ya rabu zuwa kasha ukku sannan ya fada cikin wani ruwa mai zurfin mita 7....
    Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu. A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji. A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana...
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun cafke Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, bayan kai sumame a gidansa da ke Abuja. Aminiya ta tabbatar da cewa jami’an EFCC ɗauke da makamai sun isa gidansa da misalin ƙarfe 4:46 na yammacin ranar Laraba, inda suka kama shi a gaban matarsa da ’ya’yansa. Mutum 20 sun rasu a hatsarin jirgin sama a Sudan ta Kudu Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Sai dai har yanzu ba su bayyana dalilin cafke shi ba. Wata majiya ta bayyana cewa an kama tare da tafiya da Farfesa Yusuf zuwa wani waje da ba a bayyana ba. Duk da cewa hukumomi ba...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce karamin yankin Gaza ya durkusar da gwamnatin Isra’ila duk da makaman da ta ke dasu da kuma cikakken goyon bayan Amurka. Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa : tsayin daka da aka fara a Iran din, ya jawo farkawar wasu al’ummar musulmi kuma durkusar da Isra’ila a Gaza da Labanon misali ne. Jagoran ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ganawa da jakadun kasashen musulmi a birnin Teheran, a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan zagayowar ranar aiko da sakon annabta ga Manzon Allah Muhammad (SAW). Jagoran ya ce “A yau, bayanin da muke bayarwa na mulkin mallaka da girman kai yana bayyana gaba daya...
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayyana cewa gwamnatin jihar na hada rijistar manoma da masu rike da mukaman siyasa a cikin shirinta na inshorar lafiya domin tabbatar da ayyukan kiwon lafiya ga daukacin ‘yan kasa.   Gwamnan ya bayyana haka ne a Minna, a lokacin da ya karbi bakuncin abokan hulda na ci gaba daga kungiyar Global Alliance for Vaccine Immunisation GAVI, UNICEF da WHO da suka je jihar domin bikin rufe taron GAVI da ke tallafawa tsarin karfafa tsarin PHC a jihar Neja.   Umar Bago ya ce manoma da masu rike da mukaman siyasa da makiyaya za a yi musu rajista ta ma’aikatar makiyaya sannan ya nuna cewa duk ma’aikatan gwamnati da masu rike da...
    Kungiyar masu ruwa da tsakin masana’antu a fannin mai ta Najeriya NEITI da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, na kokarin kwato kusan dala biliyan shida da kuma wani naira biliyan 66 da gwamnatin tarayya ke bin gwamnatin tarayya bashin.   Sakataren zartarwa na hukumar Mista Orji Ogbonnaya Orji, wanda ya bayyana haka a lokacin kare kasafin kudin 2025 a gaban kwamitin majalisar kan albarkatun man fetur.   Mista Orji Ogbonnaya, ya bayyana cewa tuni hukumar ta gabatar da dukkan rahotannin da ta ke a masana’antar hako mai ga majalisar a wani bangare na matakan tabbatar da samun nasarar kwato kudade daga hukumomin gwamnati.   Ya ce wasu daga cikin abubuwan da hukumar ta sa a...
    Sakatare Janar Na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres ya bayyana damuwarsa game da matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da taimakon kasashen waje daga Amurka yayin da sabuwar gwamnatin Amurka ke aiwatar da sabbin manufofinta na ketare, kamar yadda mai magana da yawun Guterres ya bayyana. “Ya yi kira da a yi la’akari da halin da ake ciki don tabbatar da ci gaba da samar da muhimman ayyukan ci gaba da na jin kai ga al’ummomin da ke da rauni a duniya,” in ji Stephane Dujarric ga manema labarai. ” Ya ce akwai al’umomin da suka dogara da wannan tallafin,” inda ya kara da cewa Amurka na “daya daga cikin manyan masu ba da agaji” a duniya....
    Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Nijeriya na da wadataccen arzikin da za ta ci gaba da ɗawainiyar duk wasu tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu zuwa ƙetare. A bayan nan dai ’yan Nijeriya na ci gaba da bayyana damuwa kan yawan tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi a kai-a kai zuwa ƙetare la’akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a ƙasar. Da kuɗin hayar gidana da ke Kaduna nake sayen abinci a yanzu — Buhari ’Yan sanda sun yi ƙarin haske kan barazanar harin ’yan ta’adda a Kano Ana kuma ci gaba da jefa ayar tambaya ko shin tafiye-tafiyen da shugaban ƙasar ke yi suna haifar da ɗa mai ido ta hanyar kalato wa ƙasar wata riba. Sai dai...
    Ana fargabar cewa wani mutum mai shekaru 30, Rabiu Sani, ya mutu a wani kududdufi da ke unguwar Kunture a Ƙaramar Hukumar Ungogo da ke Jihar Kano. Mai magana da yawun rundunar hukumar kwana-kwana, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin. ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike NAJERIYA A YAU: Dabarun Bunƙasa Kasuwanci Ta Intanet Ya bayyana cewa ofishin karɓar koken gaggawa ne ya samu kira daga wani Silas Munkhaila dangane da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa jami’ansu sun isa kududdufin inda suka tsamo gawar mutumin wanda ya je ɗebo wa mahaifinsa ruwa. Ya ƙara da cewa sun miƙa gawar mamacin a hannun mai unguwar Kunture, Uba Abdulkadir. Kazalika,...
    Ana zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa sun ɓullo da sabon salon cin hanci inda suke tatsar jami’o’i da sauran manyan cibiyoyin ilimi na tarayya. Kafar yaɗa labarai ta Premium Times ta ruwaito cewa ’yan majalisar suna barazana ga kowane shugaban jami’a ya ba su cin hancin Naira miliyan takwas kafin sun amince da kasafin makarantarsa na shekarar 2025. Binciken ya gano cewa kwamitin manyan makarantu da na Asusun Tallafin Manyan Makarantu (TETFUND) a Majalisar Wakilai da ta Dattawa sun buƙaci kuɗaɗen ne daga shugabannin manyan makarantun kafin su amince da kasafinsu na 2025. ’Yan majalisar sun nemi kowanne daga cikin shugaban Jami’o’in Tarayya 60 da ke ƙasar nan ya ba su Naira miliyan huɗu ga kwamitin majalisar dattawa da...
    Wani magidanci mai suna Rabiu Sani mai shekaru 30 ya rasa ransa bayan ya zame cikin wani tafki a lokacin da yake diban ruwa a garin Kunture da ke karamar hukumar Ungogo.   Jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullah, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Kano.   A cewarsa, hukumar ta samu kiran gaggawa daga jami’in ‘yan sanda, Silas Munkaila, inda nan take aka tura tawagar ceto zuwa wurin.   Saminu ya yi nuni da cewa, duk da kokarin da suka yi, an tabbatar da rasuwar Rabiu.   Haka zalika, wata budurwa mai suna Binta da ke fama da damuwa da tabin hankali ta rasa ranta bayan ta fada rijiya...
    Wasu jami’an MDD sunn bayyana cewa, a cikin halin da ake ciki a kudancin kasar Lebanon ba ya yuwa mutane yankin su koma gidajensu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ba bayyana cewa a yau ne wa’adin kwanaki 60 na ficewar sojojin HKI daga kudancin kasar Lebanon kamar yadda ya zo a cikin yarjeniyar da suka cimma da gwamnatin kasar Lebanon watanni biyu da suka gabata. A safiyar yau ne sojojin HKI suka kashe mutan akalla 15 sannan wasu kimani 83 suka ji rauni a lokacinda suka yi kokarinn komawa gidajensu da ke kudancin kasar Lebanon wadanda sojojin HKI suke mamaye su. Wakilin MDD na musamman a kan al-amuran kasar Lebanon Jeanine Hennis-Plasschaertand da kuma shugaban rundunar UNIFEL ta...
    “Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu. “Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu. “Saboda haka,...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi. Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.