2025-02-27@04:20:35 GMT
إجمالي نتائج البحث: 216
«da suka yi ritaya»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ya ce al’ummar kasar Labanon ba za su manta da irin goyon bayan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Iraki ta yi musu ba a lokacin da Isra’ila ke kai musu hare-hare. Sheikh Naim Qassem ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa kai tsaye a yammacin jiya Litinin. “Nasarar Gaza ta al’ummar Falasdinu ce, da al’ummomin yankin da suka tallafa musu da kuma duk masu neman ‘yanci a fadin duniya.” Inji shi. Sheikh Qassem ya jaddada cewa tsayin daka wani zabi ne na siyasa, kasa da kuma jin kai don fuskantar mamayar Isra’ila da ‘yantar da yankunan da ta mamaye. Ya bayyana cewa an cimma manufofin da ke tattare da...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, Sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan “jajircewar mutanen kudancin kasar Lebanon fuskantar sojojin HKI’ yan mamaya’ wanda ni tahir amin. ///…A Jiya lahadi be wa’adin ficewar HKI daga yankuna da garuruwan da suka mammaye a kudancin kasar Lebanon, amma karfe 4 da safe yana cika mutanen wadannan yankuna suka kwarara zuwa gidajensi, amma ko da suka isa sai suka ga cewa sojojin kasar Lebanon sun sha shinge don hana mutane wucewa zuwa wadannan wurare, don har yanzun akwai sojojin HKI a yankin suna iya kashe su. Banda haka sojojin HKI sun kara wayoyin wasu daga cikin mutanen wadannan yankuna, suna fada masu cewa kada su kuskura su shiga wadannan yankuna. Amma...

Sanarwar Yiwuwar Kai Harin Ta’addanci Kano Lokacin Maulidi: Mun Cafke Wani Da Bama-bamai – Kwamishina
Ya bayyana cewa, wadanda ake zargin sun tsere daga jihar biyo bayan tona musu asiri, amma an cafko daya an dawo da shi Kano bayan ya tsere da farko. CP Dogo, ya jaddada mahimmancin samun rahoton leken asiri wajen dakile barazanar da ake iya fuskanta, tare da yin cikakken bayani kan yadda ‘yansanda suka hada kai da masu ruwa da tsaki don inganta tsaro a lokacin taron.
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta yi ƙarin haske dangane da barazanar harin ’yan ta’adda da ta yi gargaɗin aukuwarsa a bayan nan. Da yake yi wa manema labarai jawabi, Kwamishinan ’Yan sandan Kano, Salman Dogo Garba, ya ce sun ɗauki matakan da suka dace biyo bayan barazanar harin ’yan ta’adda musamman a yayin taron Maulidin Shehu Ibrahim Inyass na ƙasa da aka gudanar ranar Asabar a jihar. Ɗan shekara 30 ya mutu a kududdufi a Kano ’Yan majalisa sun nemi cin hancin N480m kafin amincewa da kasafin jami’o’i —Bincike “Mun ankarar da jama’a sannan muka ɗauki matakan da suka dace domin tunkarar lamarin,” in ji CP Garba. Ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargin dangane da lamarin...
Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
Gomman sojoji da mayaƙan sa-kai na Sibiliyan JTF sun kwanta da dama a wata arangama da mayaƙan Boko Haram a yankin Mai-saleh da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe. Majiyoyin tsaro sun bayyana ce ’yan na Boko Haram sun kai wa jami’an tsaron hari ne bayan da jami’an tsaron sun kwace wani babban sansaninsu da ke Mai-Saleh a tsakanin jihohin biyu. Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro mai barin gado, Manjo-Janar Edward Buba, ya tabbatar da rasuwar sojoji 22 a harin. “Jimillar sojoji 22 ne suka rasu wasu da dama sun jikkata a yayin artabun,” in ji Edward Buba. Amma wasu majiyoyi sun ce sojojin da suka kwanta dama sun haura 27. Mace ta rasu, wasu sun jikkata yayin da...
Bayan da jami’an tsaro a kasar Burtania suka kama wani fitaccen mai gwagwarmayar kare hakkin Falasdinawa da kuma goya masu baya, a kwanakin da suka gabata. Wasu yan kasar sun gudanar da taro don tattaun makomar incin fadin albarkacin baki a kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wadanda suka yi magana a taron a yau Lahadi, suna cewa batun encin fadin albarkacin baki, da kuma kare hakkin b il’adama yana kara tabarbarewa a kasar. Labarin ya kara da cewa a ranar asabar da ta gabata ce, masu zanga-zanga a manya manyan birana a kasar Burtaniya suna fito kan tituna inda suke, goyon bayan al-ummar Falasdinu, sun bukaci a kawo karshen mamayar kasar Falasdinu, a kawo karshen...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu. SERAP ta maka Tinubu da NCC a kotu kan kara kudin kiran waya da data Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai. Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan...
Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26. Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...
Majiyoyin leken asirin da suka tabbatar da harin, sun kara da cewa maharan sun kai hari sansanin ne dauke da muggan makamai, inda suka ce ‘yan ta’addan sun lalata gine-gine da dama da kuma motocin aikin soji a yayin harin.
Mutane Na Yawan Tambaya Ta Yaushe Zan Yi Aure – Firdausi Yahaya
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Ruben Amorim ya yi amai ya lashe kan kalaman da ya yi cewar ƙungiyarsa ta Manchester United ta kakar nan ita ce mafi muni a tarihi. Sai dai ya ce ba zai yi yaudara ba da cewar ba su da manyan matsaloli ba a kasa. Amorim ya ce ya yi kuskure da ya samar da baraka lokacin da ya fuskanci ƴan wasa nan take, bayan tashi karawar da Brighton ta yi nasara 3-1 a Premier League. Hakan ya sa ya gana da ƴan jarida cikin fushi da ta kai ya faɗi wasu kalaman. An tambaye shi ko ya san cece-kucen da batunsa ya haifar kafin fuskantar Rangers a Europa League, Amorin sai ya ce yana magana da kansa ba da...