2025-03-31@02:44:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 233

«da rashawa ta»:

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye. Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian ya tabbatar da cewa an isar da martanin Iran ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump ta hanyar Oman. Ya jaddada cewa, yayin da Iran ta yi watsi da tattaunawar kai tsaye, ba ta taba rufe kofar yin shawarwarin kai tsaye ba matukar dai aka cimma wani abu da bai yi karo da manufofin Iran ba. Ya kara da cewa, “Kamar yadda Jamhuriyar Musulunci ta Iran...
    Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24. A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon jiragen yakin na Amurka da kuma sauran jiragen da suke ba shi kariya a cikin tekun “Red Sea”. Kakakin sojan na kasar Yemen ya kuma ce; Sun kai wa jiragen na Amuka hare-hare ne da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta. An shiga makwanni na uku kenan da sojojin na Yemen suke mayar da martani akan hare-haren da sojojin Amurka da...
    Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira gudun tayar da hargitsi a Jihar Kano. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya Gabanin yanzu dai, Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da shi kansa Sarki Aminu sun ɗaura azama ta gudanar da haye-hayen sallah bana. Sai dai da yake magana da manema labarai a ranar Alhamis, Kurawa...
    Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda abin ya shafa a garin Majia. Ya bayyana cewa, zuwa yanzu, an tara Naira miliyan 839 daga hannun manyan ‘yan kasuwa, da  kamfanoni, da sauran jama’a domin tallafawa waɗanda  lamarin ya shafa. Gwamnan ya bayyana cewa za a ba da Naira dubu dari biyar a hannu, yayin da za a tura Naira miliyan uku da rabi kai tsaye zuwa asusun bankinsu. “Kamar yadda aka...
    Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, Tehran tana kan bakanta na maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kai kan wasu wurare a nan Iran daga cikin har da wani barikin sojoji a nan birnin Tehran a shekarar da ta gabata. Safari ya kara da cewa, jinkirin da aka samu na maida-martani yana da hikima a...
    Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa da HKI da dukkan kilomita don maida mutanen kaza zuwa can. Wasu ma’aikatan MOSAD biyu, da kuma wani jami’in gwamnatin Amurka sun fadawa shafin labarai na yanar gizo Axios, kan cewa tun sun rika sun tattauna da kasashe Somalia da Sudan ta kudu da kasar Indonasia da wasu da dama dangane da wannan batun. Ya zuwa yanzu dai gwamnatin HKI ta kashe fiye da mutanen...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir da shi ne. Haka nan kuma ya yi ishara da nauyin da ya rataya akan wuyan Majalisar Dinkin Duniya da kuma sauran kasashen da suke cikin sa-ido da ‘yarjeneniyar tsagaita wutar yaki, haka nan kuma ya yi kira zuwa ga kungiyoyin kasa da kasa da su dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen maimaita keta tsagaita wutar yaki da ‘yan sahayoniyar suke yi. Har ila...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta Mayarwa Shugaban kasar Amurka Donal Trump amsar wasikarsa ga kasar danagne da shirinta na makashain Nulkiya ta hanyar kasar Omman. Aragchi ya bayyana haka a jiya Alhamis a lokacinda yake hira da kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran. Ya kuma kara da cewa a cikin wasikar dai gwamnatin JMI bayyanawa shugaban kan cewa tana ganin bazata iya shiga tattaunawa gaba da gaba da Jami’an gwamnatin kasar Amurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya ba, saboda halayen gwamnatocin Amurka a baya dangane da shirin. Daga ciki Iran ta dauke shekaru biyu cutar tana tattauna batun wannan shirin da manya-manyan kasashen duniya daga ciki har da kasar Amurka,...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka taru a Tel Aviv domin nuna adawa da mulkin firaministan kasar Benjamin Netanyahu. Masu zanga zangar sun kuma bukaci a tsagaita bude wuta da kuma sako fursunonin da ake tsare da su a Gaza. Sun rike alluna masu dauke da hotunan wadanda  ake tsare da su a Gaza ko kuma allunan neman tsagaita bude wuta da Hamas cikin gaggawa. Gamayyar kungiyoyin da ke adawa da shugaban majalisar ministocin ne suka shirya zanga-zangar da ta barke a makon da ya gabata, wanda suke zarginsa da matakin korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gida wato Shin Bet, Ronen Bar. Wata Kuri’ar jin ra’ayin jama’a a isra’ila ta nuna cewa yawancin ‘yan Isra’ila na adawa...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kira hadin kan kasashen duniya domin nuna goyon baya ga Falasdinu gabanin ranar Kudus ta Duniya. Kungiyar ta yi kira da a samar da hadin kai a kasashen duniya a ranar Juma’a da Asabar da Lahadi masu zuwa domin nuna goyon baya ga Gaza da Kudus, yayin da Isra’ila tare da goyon bayan Amurka ke ci gaba da yakin kisan kare dangi da suke yi wa Falasdinawa. A cikin sanarwar da ta fitar, Hamas ta yi kira da a gudanar da gagarumin jerin gwano na hadin gwiwa a dukkan birane da manyan birane na duniya. “Muna kira ga daukacin al’ummar Falasdinu, kasashen Larabawa da na Musulunci, da dukkan al’ummarmu masu son ‘yanci na...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya bayar da gudummawar Naira miliyan 27 da buhunan shinkafa 300 ga mutanen da gobara ta shafa a ƙananan hukumomi uku da ke mazaɓarsa a Jihar Yobe. Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Machina, Nguru, da Yusufari. An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Sanata Lawan, ya jajanta wa mutanen da suka yi asarar dukiya sakamakon gobarar. Ya ce haƙƙinsu ne su taimaka wa juna, kuma zai ci gaba da ƙoƙari don ganin cewa wadanda abin ya shafa sun samu tallafin da ya dace. Ya bayyana cewa wannan tallafin zai ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin da...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na Duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhummanci a makon da ya gabata, dangane da siyasa tattalin arziki zamantake tsaro da sauran, sannan mu yi masu karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////.. Madallah, masu sauraro shirinmu na yau zai yi dubi dangane da “ranar Qudus ta Duniya’ wacce aka rayata a jiya Jumma’a ce 27 ga watan Ramdan shekara ta 1446 wanda yayi dai-dai da 28 ga watan Maris shekara ta 2025 miladiyya ne aka gudanra da ranar Qudus ta duniya, a nan kasar Iran da kuma...
    Kwamitin tallafawa marayu da masu karamin karfi na kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah wa Ikamatis Sunnah dake karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa ya tallafawa gidajen marayu da masu karamin karfi da kayan abinci na kusan naira miliyan 9. Shugaban kungiyar Sheikh Hassan Sabo Musa ya bayyana hakan yayin rabon kayan da aka gudanar a karamar hukumar Babura.   Yace, an sami gudunmawar  kudade da kayan abinci daga al’umma da kungiyoyi. Sheihk Hassan Musa ya kara jadadda bukatar cewar, ya zama wajibi a rika jibintar al’amuran marayu domin samun falala daga Allah.   A jawabinsa, shugaban kwamitin tallafawa marayu,  Malam Nura Sale ya ce wannan shine karo na goma Sha biyu na shirin. Ya godewa wadanda suka bayar...
    Bayan gazawar tattaunawar da hukumar ta IAEA ta yi da Tehran, babban daraktan hukumar Rafael Grossi ya jaddada muhimmancin komawa kan teburin shawarwari nan gaba don tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba. Hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta ce tattaunawar da ta yi da wani babban jami’in kasar Iran a baya-bayan nan, ba a samu wani ci gaba kadan ba a cikin binciken nukiliyar da aka shafe shekaru ana yi kan kasar Iran, yana mai jaddada bukatar gaggauta warware takaddamar diflomasiyya da ke tsakanin Tehran da Washington. A wata hira da Bloomberg babban darektan hukumar Rafael Grossi ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai koma Tehran domin ci gaba...
    Bayan shafe sa’o’i 12 na tattaunawar sirri da aka yi a Saudiyya, jami’an Amurka da na Rasha sun kammala tattaunawa kan rikicin Ukraine a ranar Litinin. Hukumomin Rasha sun ruwaito cewa fadar White House da Kremlin za su fitar da sanarwar hadin gwiwa yau Talata kan tattaunawar da suka yi, wanda Moscow ta bayyana tun da farko a matsayin “mai wuyar gaske.” Tattaunawar yanzu tana mai da hankali kan yiwuwar tsagaita wuta a tekun Black Sea, domin ba da damar komawa kan yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar fitar da hatsin da yake da muhimmanci ga samar da abinci a duniya. Ministan tsaron Ukraine Rustem Umerov ya bayyana ganawar da suka yi da Amurkawa a ranar Lahadi a matsayin...
    Rahotanni daga Falasdinu na cewa akalla Falasdinawa 61 ne sukayi shahada a cikin sa’o’i 24 da suka gabata, in ji ma’aikatar lafiya ta Gaza. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ma’aikatar ta ce an gano gawarwaki hudu a karkashin baraguzan gini, sannan an kwantar da mutane 134 da suka jikkata a asibiti cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Adadin wadanda suka mutu a zirin Gaza ya kai 50,082, yayin da mutane 113,408 suka samu raunuka tun bayan fara yakin kisan kare dangi na Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba, 2023. Har ila yau, a ranar litinin, sojojin Isra’ila sun kai harin bam a asibitin Nasser, mafi girma a kudancin Gaza, da ke Khan Younis, harin da ma’aikatar...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.  A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
    Shugqbqn kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen sayyed Abdulmalik Badaruddin Huthi ya bayyana cewa tura wani kataparen jirgin ruwan yaki zuwa gabas ta tsakiya wanda shugaban kasar Amurka yayi wata gazawace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalti Alhuthi yana fadar haka yau Lahadi a wani jawabin da ya gabatar ,inda yake bayyana irin halin da ake ciki a yakin da sojojin kasarsa suke fafatawa da gwamnatin kasar Amurka.  Ya kuma kara da cewa jiragen yakin ruwa na kasar Amurka sun zama matsala ga gwamnatin Amurka maimakon su taimaka mata. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan cewa zata aiko da jirgin ruwan yaki mai suna USS Carl Vession zuwa tekun Maliya don karfafa USS Harry Truman...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
    An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye. Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya. Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne. A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana....
    A kokarin Gwamnatin Jihar Jigawa na karfafa ayyukan noman rani tare da samar da wadataccen abinci da inganta rayuwa, ta kaddamar da shirin noman rani na Lallashi da ake amfani da rijiyoyin burtsatse a Karamar Hukumar Maigatari ta jihar. Rahoton na nuna cewa, an yi aikin ne domin canza salon noman rani da sauran ayyukan noma a yankunan da galibi hamada ce. A cewar rahoton, wannan shiri ana yin amfani da makamashin hasken rana da kuma amfani da na’urori masu rahusa tare da dabarun noman rani don samar da harkokin noman rani mai inganci cikin sauki. Dakatar da Gwamnan Ribas zubar da ƙimar Nijeriya ne a idon duniya — Jonathan An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum...
    KAmfanin dillancin labarun “al-Somariyya Newas” ya ambato jagoran ‘yan hamayyar siyasa na kasar Turkiya Uzgor Auzal yana fadin cewa: A daren jiya juma’a adadin wadanda su ka fito Zanga-zangar nuna kin jinin shugaba Rajab Tayyib Urdugan sakamakon sauke da kama ‘yan hamayyar siyasa da ya yi kaga kan mukamansu da su ka hada da magajin garin birnin  Istanbul. Magajin garin Istanbul Imam Uglu ya yi watsi da duk wata tuhuma da aa yi masa ta hannu a cin hanci da rashawa. Kamfanin dillancin labaran “Reusters” ya nakalto wata majiyar shari’a tana cewa Imam Uglu ya yi watsi da dukkanin thume-tuhumen da aka yi masa masu alaka a cin hanci da rashawa. Shi dai Imam Uglu zai tsaya takarar shugabancin kasa...
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya mika sakon gaisuwar idin Nowruz na sabuwar shekarar hijira Shamsiyya ga jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan Nowruz, na  shigowar bazara da kuma sabuwar shekara ta Farisa. Putin ya kuma aike da sakon fatan alheri ga shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar a ranar Juma’a. Nowruz, wanda ke nufin Sabuwar Rana, ita ce ranar farko ta watan Farvardin na kalandar Farisa. Ranar  a mafi yawan lokuta tana kamawa ne a ranar 20 ga Maris amma a duk bayan shekaru tana tana kamawa  daidai da 21 ga Maris. Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ranar Nowruz ta duniya a...
    Dubban mutane ne a birnin Amman babban birnin kasar Jordan suka gudanar da zanga-zanga bayan sallar Juma’a domin yin Allah wadai da sake dawo da laifukan da Isra’ila ke aikatawa a Gaza. A rahoton factjo, dubban mutane sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Gaza a wani gagarumin maci na wannan Juma’a. Mahalarta tattakin sun yi Allah wadai da hare-haren da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan masallacin Al-Aqsa a cikin watan Ramadan.  A cikin wannan maci da aka gudanar bisa gayyatar Harkar Musulunci da kwamitin Tallafawa Falastinawa suka kira, dubban mutane sun halarta da suka hada da wakilai na siyasa, jam’iyyu, da kungiyoyin kwadago, da sauran jama’ar kasa, inda suka yi ta rera taken la’antar ayyukan zalunci na gwamnatin...
    Daruruwan Falastinawa fararen hula ne suka yi shahada tun bayan da Isra’ila ta dawo da hare-haren kisan kare dangi a kan al’ummar yankin zirin gaza, matakin day a yi hannun riga baki daya da yarejejeniyar dakatar da bude wuta da aka rattaba hannu a kanta karkashin jagorancin Amurka, Masar da kuma Qatar. Dakarun mamaya na Isra’ila sun kaddamar da wani farmaki mai matukar muni da manyan makamai a ranar Juma’a a kan yankunan arewa maso yammacin Gaza da suka hada da Sudaniya, al-Karamah, da kuma Beit Lahia, wanda hakan ya yi sanadin shahadar fararen hula masu yawa da suka hada da mata da kananan yara, yayin da kuma wasu daruruwa suka jikkata. Sojojin Isra’ila sun yi gargadi ga dukkanin Falasdinawa...
    A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Iran ta yi Allah wadai da Kwamitin Sulhun na MDD na rashin tabaka komai wajen  dakatar da ayyukan Amurka da Isra’ila wanda Iran din ta bayyana da abin kunya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen da kuma yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai wa Falasdinawa hari a zirin Gaza, tare da yin Allah wadai da rashin daukar wami mataki daga kwamitin sulhu na fuskantar wadannan munanan ayyukan. Esmaeil Baghaei, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana matukar na dama kan yadda ake kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara da ba su ji ba...
    Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma  Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga doron kasa. Tun ranar Asabar da ta gabata ce sojojin Amurka da Burtaniya wadanda suke da jiragen yakinsu a cikin tekun maliya da wasu wurare a yakin suka fara kaiwa kungiyar hare-hare saboda goyon bayan ga HKI. Kafin haka dai kungiyar Ansarullahi ta bawa HKI kwanaki huda ta kawo karshen kofar ragon da ta yiwa falasdinawa kimani miliyon biyu a gaza, inda suka hana shigowar...
    Rahotanni daga Gaza na cewa hare haren Isra’ila a baya bayan nan sun yi sanadin shahadar mutane kusan 1,000 a baya bayan nan wanda ke nuna irin girman barnar da gwamnatin sahayoniyan ke aikatawa a zirin. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sabon danyen aikin da Isra’ila ta yi ya kai ga kashe akalla mutane 970 cikin sa’o’i 48. Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta bayyana cewa, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kaddamar a ranar Talata, sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 970. Wasu rahotanni na daban ce mutane 356 ne suka mutu a harin da aka kai ta sama, a cikin sa’a huda sannan akalla Falasdinawa 1,000 ne suka samu raunuka. Wani...
     Rahotanni daga sansanin ‘yan hijira na Nablus a yammacin kogin Jordan sun ambaci cewa sojojin mamayar HKI sun tilasta wa iyalai 10 ficewa daga gidajensu. Sojojin na HKI suna shirin kaddamar da wani gagarumin hari na tsawon kwanaki uku a cikin sansanin “Ayn.” Dake Nabilus. A gefe daya, kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa; Sojojin Amurka suna da shirin kai hare-hare ta kasa a cikin yankin Gaza. Jaridar “Wall Street Journal” ta bayyana cewa; Sojojin na mamaya za su ci gaba da zama a yankunan da su ka shiga a cikin Gaza, sannan kuma su kai wasu sabbin hare-hare ta kasa.
    A yunkurin da gwamnatin jihar Jigawa ke yi na sauya fasalin harkar noma, majalisar zartaswa ta jihar ta amince da ware sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyar domin fara aiki da sabon Kamfanin injinan noma na jihar. Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan ga manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, an kafa kamfanin ne domin rage tsadar sarrafa kayayyakin amfanin gona a fadin jihar. Ya kara da cewa, majalisar ta kuma amince da fitar da sama da naira miliyan dari tara da sittin da tara domin ci gaba...
    A ranar Juma’a, fadar Kremlin ta ce Shugaba Putin ya aike saƙo zuwa ga Trump ta hannun manzon Amurka na musamman, Steve Witkoff, yana bayyana cewa Rasha tana nazarin batun tsagaita wuta amma tana taka-tsantsan. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce yana fatan wannan tattaunawa za ta kai ga samun mafita, amma ya jaddada cewa dole ne Rasha ta mayar da yankunan da ta ƙwace. Tun a shekarar 2014, Rasha ta ƙwace yankin Crimea, sannan a shekarar 2022 ta mamaye wasu yankuna huɗu na gabashin Ukraine. Yanzu dai ana fatan wannan tattaunawa za ta kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana ci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Rundunar ’yan sandan Adamawa ta cafke wani ƙani da yayansa — Aliyu Abdulmalik da Ibrahim Abdulmalik — kan zargin yanke kan wani almajiri ɗan shekara 10, Abdallah Lawali. Bayanai sun ce ’yan uwan junan biyu sun aikata wannan ta’asa ce a ranar 7 ga watan Maris a unguwar Sarkin Yamma da ke Ƙaramar Hukumar Jada. Majalisar Ribas ta soma shirye-shiryen tsige Gwamna Fubara Trump zai tuntuɓi Putin kan yaƙin Ukraine Sanarwar da rundunar ’yan sandan ta fitar ta ce an kama ababen zargin ne da gangar jikin almajirin a cikin wani buhu, yayin da aka ƙwaƙulo kansa a cikin wani rami da suka binne a harabar gidansu. Rundunar wadda ta ce yanzu haka bincike ya kankama a kan lamarin, ta...
    Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa hare-haren ta’adanci wadanda sojojin Amurka da Burtaniya suka kai kan yankuna da dama a kasar ba zasu hana mutanen kasar ci gaba da kare Falasdinawa a Gaza ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Al-huthi yana fadar haka a wani jawabin da ya gabata a jiya Lahadi da yamma. Ya kuma kara da cewa sojojin kasar zasu ci gaba da kai hare hare kan katafaren jirgin ruwan yaki mai daukar jiragen saman yaki na Amurka dake cikin Tekun maliya. Sannan zasu ci gaba da kai hare hare kan jiragen HKI da na Burtania da na Amurkan masu wucewa ta tekun malia kamar yadda ta bayyana...
    Gidauniyar Aliko Dangote, a cikin shirye-shiryenta na 2025, na bayar da tallafin abinci ga ‘yan Nijeriya, ta ƙaddamar da rabon abinci, inda ta ware kimanin Naira Biliyan 16 domin tallafa wa talakawa ‘yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu nakasa. Shirin da fiye da mutum miliyan ɗaya ne za su rabauta da tallafin buhunhunan shinkafa mai nauyin kilo 10 daga wannan tsarin na gidauniyar Aliko Dangote. NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya El-Rufai ya nemi afuwa ko mu maka shi a kotu — Gidauniyar Ɗahiru Bauchi Da yake jawabi a wajen taron kaddamarwar, Shugaban gidauniyar Aliko Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce an tsara yin rabon shinkafar buhu miliyan ɗaya ne ga ‘yan Nijeriya...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa kofar JMIa bude yake ga kasashen Turai don tattaunawa da fahintar juna kan matsalolin da bangarorin biyu suke sabani a kansu, tare da mutunta hurumin Juna. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiyaAsabar a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Netherlands Caspar Veldkamp a jiya Asabar. Ministan ya kara da cewa dangantakar diblomasiyya tsakanin Dutch da Iran tsohuwar dangantaka ce. Sannan Iran tana da nufin fadada shi. A Nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Netherlands yay aba da yadda dangantaka tsakanin kasashen biyu yake bunkasa. Sannan dangane da tsabirin kasar Iran guda uku, Abu Musa, Tumbe kucek da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baka’e ya tir da kungiyar kasashe 7 masu karfin tattalin arziki a duniya,wato G7. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Baghaee yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma yi All..wadai da zarge zagren kungiyar wadanda suka hada da zargin Iran da kokarin mallakar makamin Nukliya, da hadsa fitina a kudancin Asia. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran yace dukkan wadannan zarge-zarge basa da toshe. Sannan ya zargi kasashen kungiyar na G7 da goyon bayan HKI a kissan kiyashin da ta aikata a Gaza. Kafin haka dai kasashen kungiyar ta G7 sun kammala taronsu a kasar Canada a ranar jumma’ar da ta gabata inda suka, suka fidda bayanin bayan...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa. Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen. Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran. bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya –...
    Rahotannin dake fitowa daga Falasdinu na cewa wani hari da Isra’ila ta kai a arewacin zirin Gaza ya kashe akalla Falasdinawa tara, ciki har da ‘yan jarida uku a cikin gida, in ji ma’aikatan lafiya. An kai harin ta sama a wata mota a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin yau Asabar. A cewar likitocin, mutane da dama sun samu munanan raunuka, tare da jikkata a ciki da wajen motar. “An kai shahidai tara zuwa asibiti, da suka hada da ‘yan jarida da dama da ma’aikata daga kungiyar agaji ta Al-Khair, sakamakon harin da aka kai wa motar da wani jirgi mara matuki a garin Beit Lahia, tare da luguden wuta a yankin,” in ji kakakin hukumar tsaron farar...
    Mai bai wa shugaban Daular Hadaddiyar Daular Larabawa da ya kawo ziyara Iran ya bayyana cewam ganawarsa da ministan harkokin wajen Iran ya yi kyau. Mai bai wa shugaban daular ta Hadaddiyar Daular Larabawa shawara, Muhammad Anwar Karkush ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa:  Muna kimanta ttataunawa mai amfani da kuma  aiki tare.” Baya ga batutuwan da su ka shafi alaka a tsakanin kasashen biyu,  da kuma abubuwan da suke faruwa a cikin wannan yankin, Anwar Karkash ya zo da wasiki daga shugaban kasar Amurka Donald Trump.
    Jakadan JMI na din din din a MDD Amir Saeed Iravani ya yi tir da HKI kan yadda take amfani da Kalmar “ta’addancin Addinin musulunci’ don rabawa addinin ayyukan ta’addanci. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Iravani yana fadar haka, a taron yaki da kin addinin musulunci a kasashen yamma da kuma kasashen da suke fama da karancin sanin addinin musulunci a duniya. Iravani ya kara da cewa, shekaru uku da suka gabata ne babban zauren MDD ya samar da kuduri mai lamba 73/254 don yaki da kin musulmi da addinin musulunci a duniya. Jakadan ya yi tir da Banyamin Natanyahu Firai ministan HKI da yawan amfani da kalmomi wadanda suke rabawa addinin musulunci ayyukan ta’addanci. A...
    Takardar da aka yi nazari a karshen watan Janairu ta nuna cewa a watan Fabrairun 2025, an ware shirin samar da mai na kan naira zuwa jirgin dakon mai hudu ne kawai, rukuni hudu zalla, kuma a watan Maris, dakon man biyu ne kawai aka yi da ya kai ganga 950,000 (ganga miliyan 1.9 ga watan). Wannan yana wakiltar rabon ganga 61,290 a kowace rana kasa da makasudin 385,000 bpd a karkashin tsarin. Karancin samun danyen mai ya tursasa wa matatar man Dangote garzaya wa kasashen waje domin neman danyen man. A baya-bayan nan kamfanin ya samu gangar danyen mai miliyan 12 daga Amurka. Duk da dai har yanzu matatar Mai ta Dangote ba ta fito a hukumance ta yi...
    Na hudu, kudurin Sin shi ne inganta hadin gwiwa ta hanyar tattaunawa, tare da adawa da neman kwamitin sulhu na MDD ya shiga tsakani. Bugu da kari, ministan ya ce Sin za ta tsaya kan dabarar daukar matakai daya bayan daya da saka alheri da alheri, da neman cimma matsaya ta hanyar tattaunawa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan shiri ya nuna tsantsar halin nuna jinkai da kulawar Alhaji Aliko Dangote wajen kawar da yunwa da fatara a Nijeriya. Gwamnan wanda mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta, ya ce za a raba buhun shinkafar guda dubu 120, mai nauyin kilogram 10 a daukacin kananan hukumomi 44 dake fadin jihar Kano. A jawabinta ga manema labarai, Babbar Darakta kuma Babbar jami’ar gudanarwar gidauniyar Aliko...
    Sabon kocin Ingila, Thomas Tuchel ya cire ɗan wasan bayan Ingila Harry Maguire cikin jerin ƴanwasan Ingila da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026. Cikin jerin ƴan wasa 26 da sabon kocin ƙasar Thomas Tuchel ya fitar, ranar Juma’a ya sanar da sunan Marcus Rashford bayan cire shi a wasannin baya. Haka ma kocin ya saka sunan tsohon ɗan wasan Liverpool da ke taka leda a ƙugiyar Ajax, Jordan Henderson cikin tawagar. A karon farko mai tsaron ragar Burnley, James Trafford da ɗan wasan bayan Liverpool, Jarell Quansah za su iya samun damar buga wa babbar tawagar Ingila ƙwallo ba a ke cikin tawagar A ranar Juma’a, 21 da watan Maris ne tawagar Ingila...
    Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki.   Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau.   A cewar Gidan-Goga, Ministan ya zabi bayar da kudi ne maimakon kayan abinci, saboda tuni wasu ‘yan siyasa a jihar suka raba wa magoya bayansu hatsi.   Ya kuma jaddada cewa tallafin kudi zai baiwa magoya bayan jam’iyyar APC damar siyan wasu muhimman abubuwan da ake bukata a cikin watan Ramadan.   “A wannan karon,...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce ya karbi  wata wasika daga shugaban kasar Amurka Donald Trump ta hannun manzon kasar Hadaddiyar Daular Larabawa. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Araghchi ya bayyana cewa, na karbi bakuncin Anwar Gargash mai baiwa shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa shawara kan harkokin diflomasiyya. Baya ga tattaunawa kan huldar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwan yankin, na samu wasikar shugaban kasar Amurka. Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa, tuni aka mika wannan wasika ga jagoran juyin juya hali domin yin nazari a kanta, da kuma daukar matakin da ya dace dangane da wasikar. Wasu bayani na cewa wasikar dai tana kunshe ne da wani sako...
    A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare. Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i.   Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana cewa, matakin ya yi daidai da kudurin wanda ya kafa na rage radadin tattalin arziki a tsakanin marasa galihu.   Ya bayyana cewa an zabo mutane 12 da suka ci gajiyar tallafin daga kowace karamar hukumar jihar 23 da suka hada da zawarawa 10 ko marayu mata da kuma nakasassu biyu a kowace karamar hukumar.   Ya ce kowane wanda ya ci gajiyar shirin zai...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya.  “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga yarjejeniyar da aka sanya wa hannu,” kamar yadda jagoran ya bayyana yayin da yake jawabi ga taron dalibai a birnin Tehran a jiya Laraba. “tunda mu ka ga baya girmama yarjejeniya, menene ma’anar yin shawarwari kuma ?” “Saboda haka, kiraye-kirayen yin shawarwarin da tattaunawa na da nufin yaudarar  jama’a na duniya.” Inji jagoran. Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce “Idan manufar tattaunawar ita ce a...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da matakin da kasar Yemen ta dauka na haramtawa jiragen ruwan Isra’ila shiga tekun Bahar Maliya Bayan sanarwar da kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta fitar na cewa za ta dawo da haramcin da ta yi wa jiragen ruwan Isra’ila na tsallakawa tekun Bahar Rum, Hamas ta fitar da sanarwa inda ta yi maraba da matakin. ta bayyana wannan mataki a matsayin wanda ke nuna hakikanin matsayin al’ummar Yemen da gwamnatin kasar na goyon bayan gwagwarmayar al’ummar Falastinu. Har ila yau kungiyar ta yi kira ga dukkanin kasashen Larabawa da na Musulunci da kuma ‘yantatun kasashe a duniya da su kara zage damtse wajen matsin lamba ga ‘yan mamaya da magoya bayansu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata kungiyar kare hakkin bil’adama a kasar Bahrain ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta kara yawan kama mutane yan adawa daga ciki har da yara kanana saboda shiga cikin zanga-zanga, ko kuma bayyana ra’ayinsu na siyasa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar kare hakkin bil’adama ta ” The Americans for Democracy & Human Rights in Bahrain (ADHRB), ta kuma kara da cewa, bayan afwar da gwamnatin Bahrain ta yi wa yan adawar kasar kimani 1,584 a cikin watan Afrilun shekara ta 2024 da ya gabata, daga ciki har da yara 40, amma daga baya ta fara kama yan adawan tana  tsaresu. Suna kama dukan wanda ya nuna  kiyyarsa, ko ya bayyana ra’ayinsa na siyasa, ko kuma...
    Shugaban kwamatin duba rabon abincin azumi na majalisar dokokin jihar Jigawa a shiyyar Dutse kuma mataimakin Shugaban Majalisar, Alhaji Sani Isiyaku Abubakar ya bukaci masu aikin dafa abincin a karamar hukumar Gwaram da su dauki wannan aiki a matsayin turbar samun lada daga Allah Madaukakin Sarki ba wai hanyar neman riba kadai ba. Alhaji Sani Isayku Abubakar ya yi wannan kiran ne lokacin da ya jagoranci Yan kwamatin domin duba aikin dafawa da kuma rabon abincin azumi a unguwar Sabon Layi da ke karamar hukumar Gwaram. Ya ce rangadin duba rabon abincin azumi na daga aikin majalisa na duba ayyuka da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da inganci da kuma shugabanci nagari. Alhaji Sani Isayku Abubakar tare da Yan kwamatin sun...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci  ba. “Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata. “Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.” Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump,...
    Shugaban ofishin yada labarai a Gaza Salama Marouf, ya yi Allah wadai da ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi, saboda kin janyewa daga yankin Salahul Din a kudancin Gaza da kuma ci gaba da kutsawa da da kai hare-hare a cikin Rafah. Marouf ya yi gargadin cewa wadannan ayyuka na nuni da irin mummunan nufi da haramtacciyar kasar Isra’ila ke da shi da kuma yadda take ci gaba da aikata laifuffuka kan al’ummar Palasdinu. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Marouf ya bayyana cewa, a cikin kwanaki goman da suka gabata, sojojin Isra’ila sun kara zafafa hare-hare,  duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Ya yi nuni da lamari na baya-bayan...
    Kasar Yemen ta sanar da cewa za ta ci gaba da kai hare-haren soji kan jiragen ruwan Isra’ila a wasu muhimman yankunan teku da ke gabar tekun kasar bayan cikar wa’adin da ta gindaya wa Isra’ila na ta sake bude mashigar zirin Gaza tare da bayar da damar kai agaji cikin yankunan Falasdinawa da yaki ya daidaita. Rundunar sojin Yaman ta fitar da sanarwar a cikin daren jiya, inda ta ce za a ci gaba da kai hare-hare kan duk wasu jiragen ruwa masu alaka da ISra’ila kamar yadda Abdul-Malik al-Houthi shugaban kungiyar gwagwarmayar Ansarullah ta kasar ya bada umurni. Tunda farko Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya bai wa gwamnatin Isra’ila kwanaki hudu ta bude hanyoyin kai kayan agaji Gaza...
    Kasar Ukraine ta bayyana aniyarta ta amincewa da shawarar da Amurka ta gabatar, game da dakatar da bude wuta nan take tsakaninta da Rasha har tsawon kwanaki 30, biyowa bayan fara tattaunawa da tawagar Amurka a birnin Jeddah na kasar Saudiyya. Wata sanarwar hadin gwiwa tsakanin wakilan Ukraine da na Amurka da aka fitar a jiya Talata ce ta tabbatar da hakan, bayan sassan biyu sun shafe sa’o’i suna tattaunawa. Sanarwar ta ce akwai yiwuwar tsawaita yarjejeniyar, kuma Amurka za ta tuntubi Rasha kasancewar amincewarta zai tabbatar da cimma nasarar matakin. Baya ga hakan, Amurka ta amince da dage matakin dakatar da musayar bayanan sirri, kuma za ta ci gaba da baiwa Ukraine tallafin tsaro, yayin da kuma sassan biyu...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da kayayyakin jin kai da bukatun yau da kullum a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ya zama “laifi na yaki da kuma hukuncin gama-gari.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta ce matakin rufewar ya saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta watan Janairu ne. “Irin wannan matakin keta dokokin kasa da kasa da na jin kai, da yarjejeniyar Geneva, kuma laifukan yaki ne da hukuncin gama-gari da ke barazana ga rayukan fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.” Hamas ta ce rufewa da kuma hana shigar da kayan agaji sama da kwana 10 a jere yana kara tsananta radadin da...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi Allah-wadai da matakin da gwamnatin Amurka ta dauka na haramtawa  al’ummar Iraki ‘yancinsu na samun wutar lantarki, da ma wasu ababen more rayuwa. “Muna tare da al’ummar Iraki, kuma mun tabbatar da alkawarinmu ga gwamnatin Iraki na ba da hadin kai wajen tinkarar matakan da Amurka ta dauka ba bisa ka’ida ba,” in ji Araghchi a wani sakon da ya wallafa a shafin X. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani babban jami’an makamashi  a kasar Iraki yana cewa, a halin yanzu Iraki ba ta da wasu hanyoyin da za su maye gurbin makamashin da ake shigowa dashi  daga kasar Iran, lamarin da zai haifar da babban kalubale wajen biyan bukatar wutar...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi imanin cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake dawo da yaki a zirin Gaza ba ta da amfani, tana mai cewa tattaunawar tsagaita bude wuta ce hanya daya tilo da Isra’ila za ta iya ceto rayukan ‘yan kasarta da take garkuwa ranar Litinin 10 ga watan Maris, kungiyar ta ce Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu na kawo cikas ga aiwatar da yarjejeniyar saboda wasu dalilai na rajin kansa da kuma na siyasa kawai. Hamas ta kuma kara jaddada aniyar ta na aiwatar da yarjejeniyar, inda ta bayyana aniyar ta na kaddamar da shirin tsagaita wuta a mataki na biyu ba tare da bata lokaci ba. Har ila yau kungiyar ta ce gwamnatin Isra’ila...
    Majalisar Dinkin Duniya, ta yi tir da matakin Isra’ila na kate wutar lantarki a Gaza, tana mai matukar gargadi game da ilan da hakan zai janyo wa Zirin. Matakin da Isra’ila ta dauka na katse wutar lantarki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya zai hana yankin Falasdinawa samun “ruwa mai tsafta,” in ji wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan yankunan Falasdinawa da aka mamaye. Francesca Albanese ta fada a ranar Litinin cewa shawarar da Isra’ila ta dauka na yanke wuta a Gaza na nufin tsaida hanyoyin samar da ruwa a zirin. Albanese ta kuma yi Allah wadai da rashin daukar mataki kan hakan daga kasashen duniya. A ranar Lahadin da ta gabata ne, kafofin yada labaran Isra’ila...
    Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya isa kasar Saudiyya domin ganawa da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin wata muhimmiyar ganawa tsakanin tawagogin Ukraine da na Amurka domin share fagen shawarwarin zaman lafiya da Rasha a nan gaba. Taron dai na nuni da wani gagarumin yunkurin diflomasiyya na magance rikicin da ke faruwa a Ukraine kuma zai iya ba da damar tsagaita bude wuta a cewar rahotanni. Tattaunawar da za a yi a Jeddah ita ce ganawa ta farko tsakanin jami’an Ukraine da Amurka tun bayan ziyarar da Zelensky ya kai fadar White House a karshen watan Fabrairu da ya gabata, wanda ya haifar da cacar baki baki mai zafi tsakaninsa da shugaban Amurka Donald Trump. Tun bayan...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa tattaunawa tare da barazana ba tattaunawa ake kiransa ba, sai dai tursasawa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmael Baghaie  ya na fadar haka a yau litinin a jawabin mako-makon da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin. Baghaei ya kara da cewa JMI ba zata taba tattaunawa da Amurka tare da barazana da kuma takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba.  Zabin tattaunawa ko kuma yaki, ba  tattaunawa sai dai tursasawa. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa JMI ba ta da zabi, ko ta shiga tattaunawa da Ita Amurka ko kuma ta shiyawa yaki. Kakakin ma’aikatar...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce shirin makamashin Nukliyar kasar Iran, na zaman lafiya ne, kuma babu wani shiri na samar da makaman Nukliya a cikinsa, sannan ya kara da cewa Iran ba za ta taba shiga tattaunawa da kasar Amurka mai cin zalin wasu kasashe ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi ya na fadar haka a shafinsa na X a yau Litinin, ya kuma ce wannan ita ce martanin Iran a kan sakon da Amurka ta ce aikawa jami’an gwamnatin kasar Iran, na cewa su zabi tattaunawa ko yaki. Kafin haka Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana hakan, ya kuma kara da cewa, kasashen yamma musamman...
    Masu rajin kare hakkin bil’adama a birnin Sao Paulo na kasar Brazil, sun ratsa tsakiyar birnin tare da makeken tutar kasar Falasdinu inda suke kira zuwa ga cikekken yenci ga Falasdinawa da kuma dakatar da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a can. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, a dai dai lokacinda ake kira zuwa ga goyin bayan mutanen gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi a fagen kasa da kasa, mutanen Brazil sun fito kwansu da kwarkwartansu a birnin Sao Paulo don tabbatar da wannan kiran. A halin yanzu dai ana kokarin samarda kawance ta kasa da kasa, wacce zata game ko ina a duniya, don goyon bayan mutanen Falasdinu da kuma korar yahudawa yan...
    Gwamnatin Isra’ila ta tura wa tawaga zuwa kasar Qatar a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin Isra’ilar da masu shiga tsakani ciki har da Amurka. Wannan ya biyo bayan tattaunawar kai tsaye da ba a taba yin irinta ba tsakanin Hamas da wakilin Amurka Adam Boehler dake kula da mutanen da akayi garkuwa da su. Wakilin na Amurka ya sha bayyanawa a baya baya nan cewa Ya yi imanin cewa za a iya cimma yarjejeniya a makonni masu zuwa. Ya kuma ce Hamas ta shirya tsagaita bude wuta na tsawon shekaru biyar zuwa goma sannan kuma kungiyar ta kwance damara. Tunda farko dai kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “suna kira ga masu...
    Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan  fararen...
    Shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Muhammad Bakir Kalibaf, ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi Iran ta zauna teburin tattaunawa da gwamnatin Amurka alhali tana yi ma ta barazana. Har ila yau ya ce zancen bayan nan na shugaban kasar Amurkan akan tattaunawa manufarsa ita ce yaudara da kuma kokarin raba Iran da karfinta. A yau Lahadi ne shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya bayyana haka, yana mai kara da cewa; Kasarsa ba ta jiran wani sako  daga Amurka, kuma za ta dakile dukkanin takunkuman da ta kakaba mata ta hanyar dogaro da karfin tattalin arzikinta da kuma alakarta ta kasa da kasa. Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kuma ce; Yadda Donald Trump ya yi...
    Abin da ya sa wannan tsari ya yi daban shi ne ba wai domin irin tsarin gine-gine da za a yi ba; akwai allunan batun siyasa da kuma ‘yancin Falasdinawa. A jawabinsa a wajen taron, shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi ya yi kira da a samar da tsare-tsare guda biyu da za su tafi lokaci daya wanda aka fi sani da tsarin kasa biyu – kasar Falasdinawa da kuma ta Isra’ila. Larabawa da kuma sauran mutane na ganin wannan itace kadai hanyar samar da mafita ga rikicin da aka dade ana fama da shi, sai dai Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kawayensa sun yi watsi da batun. Wannan sabon tsari ya bayyana cewa Gaza za ta zauna karkashin kulawar “gwamnatin...
    Manyan kasashen Turai, da suka hada da Burtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya, sun goyi bayan shawarar Masar na sake gina Gaza a matsayin mai adawa da shirin “riviera” na shugaban Amurka Donald Trump wanda ke ba da shawarar korar Falasdinawa da karfi daga yankin. Duk da goyon bayansu da kuma wanke ayyukan kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tun farkon yakin a watan Oktoban 2023, ministocin harkokin wajen Birtaniya, Faransa, Jamus, da Italiya sun sanar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar cewa sun amince da shirin Masar wanda zai inganta “mummunan yanayin rayuwa da Falasdinawa suke ciki a Gaza.” Sanarwar ta kara da cewa, “Shirin ya nuna wata hanya ta sake gina Gaza idan aka...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce dagewar da wasu kasashe masu cin zarafi suka yi na yin shawarwari da Iran na yi ne don neman amfanin kansu. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manyan jami’ai na bangarori uku na gwamnati a ranar Asabar. Jagoran ya ce “Dagewar da wasu gwamnatoci suka yi kan yin shawarwari ba wai don warware al’amura ba ne, a’a yana nufin aiwatar da abin da suke so.” Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: ” Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta amince da abin da suke tsammani ba.” Wadannan gwamnatocin da suke cin zalin ba sa neman yin shawarwari kan batun nukiliya...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Imam Ayatullah sayyid Aliyul Kahaminae, ya bayyana cewa tursasawa kasar Iran ta shi tattauna da gwamnatin Amurka ba abin amincewa ba ne, kuma yin hakan ba zai warware matsalolin da ke tsakaninsu ba. Tashar talabijinta Presstv a nan Iran ta nakalto Jagoran ya na fadar haka a yau Asabar a lokacin da yake ganawarsa, da shugaban kasa Masoud Pezeshkiyan da alkalin al-kalan kasa Muhsen Ejei da kuma shugaban majalisar dokokin kasar Muhammad Bakir Qalibof da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar da dama a gidansa. Jagoran ya kara da cewa ba matsalar makamashin Nukliya ne suke bukatar tattaunawa da Iran ba, sai dai suna su tilastawa kasar Iran ra’ayinsu, a cikin dukkan al-amuran...
    A dai dai lokacinda ake bukukuwan ranar mata ta duniya kungiyar Hamas wacce take iko da Gaza, ta yi allawadi da HKI saboda kissan mata kimani 12.000 a gaza a cikin yakin tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar Hamas na fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa kasashen yamma musamman Amurla da kasashen Turai, idan magana ta zo kan matan Falasdinawa wadanda HKI ta kashe, suna nuna faska biyu. Kashe mata Falasdinawa ba take hakkin mata ne ba, tunda HKI ce ta kashe su. Kungiyar ta kara da cewa HKI ta kashe mata 12,000 sannan ta raunata wasu dubbai, haka ma ta kori wa su da dama daga godajensu.
    Ofishin jakadancin JMI dake MDD a birnin New York na kasar Amurka ya bada sanarwan cewa bai karbi wani sako daga shugaban kasar Amurka Donal Trump ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakoto Jaridar Axios ta Amurka na cewa Shugaban kasar Amurka ya aikawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Ayatullahi Khaminae wasika, inda a ciki yake kiransa zuwa tattaunawa da Amurkan a kan shirin makamashin Nukliyar kasar Iran. Har’ila yau shugaban ya bayyana haka wa tashar talabijin ta Fox news. Iran dai ba ta son tattaunawa kai tsaye da Amurka saboda rashin gaskiya a cikin al-amuransu. Musamman shi Donal Trump, sabo da shine ya fidda kasarsa daga yarjeniyar JCPOA tun farko sannan ya dage sai...
    Majaliar Dattawa ta ce ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne saboda saɓa dokokin majalisar da ta yi, ba don zargin cin zarafin da ta yi wa shugaban majalisar ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Bamidele Opeyemi ne bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a madadin majalisar. Kotu ta saki tsohon shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol Ramadan: Hisbah ta rufe shagon caca a Kano A cewarsa, dakatar da Sanata Natasha, mataki ne da duka majalisar ta ɗauka, saboda saɓa dokokinta da ta yi kamar yadda kwamitin ɗa’a da ladabtarwa ya tabbatar. “An dakatar da ita ne saboda yadda take keta dokoki da ƙa’dojin majalisa, da nuna rashin ɗa’a a majalisar, wannan shi ne...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya sake jaddada kin amincewa da matakin samar da kasashe biyu a matsayin samar da mafita ga rikicin falasdinu, yana mai cewa hakan ba zai tabbatar da hakkokin Falasdinawa ba, a maimakon haka ya ba da shawarar samar da “kasa dimokuradiyya guda daya” a matsayin mafita daya tilo. Da yake jawabi yayin taron musamman na ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC, a birnin Jeddah na kasar Saudiyya da aka kira don magance cin zarafi da laifukan da Isra’ila ke yi kan al’ummar Falasdinu, Araghchi ya jaddada matsayar Iran kan Falastinu tare da bayyana goyon bayan da Tehran ke yi wa Falasdinawa a matsayin abin da ba za a iya...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a birnin Tehran ya bayyana cewa; Tattaunawa da Amurka kaskanci ne, ga shi kuwa al’ummar Iran tana da tunani ne irin na Ashura, ba ta karbar kaskanci. Limamin na Tehran ya yi ishara da yadda duniya ta ga yadda Donald Trump ya wulakanta shugaban kasar Ukiraniya, don haka ya kamata masu dogaro da Amurka su kwana da sanin cewa, haka makomarsu za ta kasance, domin haka halayyar girman kai take.” Haka nan kuma limamin na Tehran ya ce; tare da cewa jagoran juyin musulunci na Iran ya sha jaddada cewa, babu aiki da tunani a cikin tattaunawa da Amurka, kuma ba abu ne na girma ba, sai dai kuma da akwai wadanda ba su nuna...
    Bangaren soja na kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ya ce a shirye yake kan komi ma, kuma zai ci gaba da kasancewa cikin “kyakyawan shiri”, yana mai jaddada cewa barazanar da Isra’ila ke yi na sake yaki a zirin Gaza da aka yi wa kawanya ba zai sa a sako Isra’ilawan da aka yi garkuwa da su ba. Abu Ubaida, kakakin kungiyar al-Qassam Brigades, ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a faifan bidiyo a ranar Alhamis, yana mai jaddada cewa, abin da ‘yan mamaya suka kasa cimma ta hanyar “makamai da yaki” ba za a taba samun shi ba ta hanyar “barazana da yaudara ba.” Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan da shugaban Amurka...
    Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu. Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya. A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’ila Bakai, ya ce, Iran tana kokarin ganin cewa an gudanar da taron kungiyar kasashen musulmi domin tattauna batun barazanar tilasta mutanen Gaza yin hijira. Haka nan kuma ya ce, wannan tunanin na korar falasdinawa daga Gaza, ba wani abu ba ne sai cigaba da kisan kiyashi, ta hanyar amfani da makamin siyasa.
    Bayan haka, ƙungiyoyi da jama’a da dama sun buƙaci a yi bincike kan lamarin, wanda ya kai ga Majalisar Dattawa ta buƙaci Sanata Natasha ta bayyana kanta da kuma gabatar da ƙorafi a hukumance. Sanata Natasha Ta Gabatar Da Ƙorafinta A ranar Laraba ta gabatar da ƙorafin, Sanata Natasha ta isa majalisar ne tare da mai gidanta, sannan ta yi magana kai-tsaye ga Shugaban Majalisar. Ta ce: “Ina gabatar da ƙorafi kan Shugaban Majalisar Dattawa, mai girma Sanata Godswill Akpabio, bisa cin zarafi, tursasawa da ƙoƙarin daƙile min aikina a matsayin ƴar majalisa.” Daga nan, ta sauka daga kujerarta zuwa gaban Akpabio, inda ta rusuna tare da miƙa takardun ƙorafinta. Martanin Akpabio Sanata Akpabio ya karɓi ƙorafin Natasha, amma ya...
    Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul  tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa. Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse. Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita. Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa  tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban...
    Mataimakin ministan harkokin wajen a kan al-amuran siyasa, dole ne Amurka ta daukewa kasarsa wadannan takunkuman tattalin arziki wanda suke cutar da mutanen kasar Iran da al-adunsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto TakhtaRawanchi yana fadar haka a shafinsa na X ko twitter a da, a kuma  jiya Talata, Mataimakin ministan ya kara da cewa, takunkuman tattalin arzikin da kasashen Amurka da Turai suka dorawa kasar Iran ya zuwa yanzu ya shafi rayuwar mutanen kasar da dama wanda kuma take hakkinsu ne. Labarin ya kara da cewa a shekaru fiye da 40 da suka gabata, gwamnatocin Amurka kadai sundorawa kasar Iran takunkuman tattalin arziki mafi muni, kuma nau’ii daban-daban. Haka ma ta dade tana wa kasar barazanar...
    Gwamnatin hadin kan kasa dake yammacin Libya ta kore labarun da kafafen watsa labarun yammacin turai suke watsa na cewa, za ta karbi bakuncin Falasdinawa –akarkashin shirin Trump na korar mutanen Gaza. Sanawar gwamnatin wacce ofishin shugabanta Abduhamid al-Dubaibah ya fitar ya bayyana cewa; Libya tana jaddada matsayarta akan cewa, hakkin Falasdinawa ne su rayu a cikin kasarsu. Sanarwar da aka wallafa a shafin ‘facebook’ ta kuma ce; Wancan labarun na karya ne babu kamshin gaskiya a cikinsu, tare da bayyana wadanda su ka watsa su da cewa, ba su yi aiki da mafi karancin ka’ida ta aikin watsa labaru ba, kuma manufar ita ce wasa da hankalin mutane. Haka nan kuma ta ce wanda ya rubuta rahoton Jerome Kersey...
    A Wani taron manema labarai da fadar Kremlin ta saba yi kowace rana, mai magana da yawun shugaba Putin ya bada amsar tambayar da aka yi masa kan martani Rasha na matakin da Amurka ta dauka na dakatar da bai wa Ukraine tallafin soji Kakakin na shugaban na rasha Dimitry Peskov Ya ce:  ya kamata mu yi dubi kan lamarin, “Idan har da gaske ne, to wannan shi ne mataki da zai sanya Kyiv ta nemi cimma yarjejeniyar zaman lafiya.” Peskov ya kara da cewa Da ma Amurka ce ke sahun gaba wajen samar wa da Ukraine makamai. “Don haka idan ta daina ko ta dakatar da bai wa Ukraine agajin soji, to shi ne abin da yafi dacewa  kuma...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta rage tsawon lokacin aikin ma’aikatanta nan take albarkacin watan Ramadan. Gwamna Umar Namadi ya dauki matakin ne domin ba wa ma’aikata damar samun hutut da kuma  gudanar da ibada a wannan wata mai albarka. Shugaban Ma’aikata na jihar, Muhammad Kandira Dagaceri, ya sanar da cewa ce daga yanzu lokacin aiki ya koma karfe 9 na safe zuwa 3 na yamma a ranakun Litinin zuwa Alhamis. Sanarawar ta kara da cewa ranar Juma’a kuma za a rika tashi aiki karfe 1 na rana har zuwa karshen watan azumin. Ya kuma yi kira ga ma’aikata da su yi amfani da watan ibadar wajen yin addu’o’in samun sauki a fannin tattalin arziki da zaman lafiya a Jihar Jigawa da...
    Kasashen larabawa sun yi kakkausar suka ga matakin da Isra’ila ta dauka na dakatar da shigar da duk wani kayan agaji a zirin Gaza, suna masu bayyana hakan a matsayin keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas da kuma dokokin kasa da kasa. Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya a cikin wata sanarwa ta ce “Masar ta yi Allah-wadai da kuma yin tir da matakin da gwamnatin Isra’ila ta dauka na dakatar da agajin jin kai ga Gaza, tare da yin amfani da shi a matsayin wani makami na cin zarafi da azabtarwa.” Masar ta kuma yi Allah wadai da matakin da Isra’ila ta dauka na hana shigar da duk wani agajin jin kai a zirin Gaza a matsayin “ketare iyaka”...
    Kungiyar ECOWAS, ta sanar da cewa tawagarta da ta je Guinea Bissau, ta bar kasar bayan barazanar data fuskanta daga shugaban kasar. A wata sanarwa da ta fitar, tawagar ta ce ta bar kasar “da sanyin safiyar Asabar sakamakon barazanar korar da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya yi.” Tawagar kungiyar ECOWAS ta ziyarci kasar Guinea-Bissau tsakanin ranakun 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu domin taimakawa wajen warware rikicin siyasar kasar dangane da sanya ranar gudanar da zaben shugaban kasa. ECOWAS ta ce ta bar kasar ne don gujewa wannan wulakanci. Kafin hakan dai shugaban kasar ya gana da tawagar ta masu shiga tsakani na kungiyar ta ECOWAS a ranar Litinin da ta gabata.  Amma daga bisanio ya zarge su da...
    Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira. Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa. Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967. A ranar Talata...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da shawarar da Isra’ila ta gabatar na tsawaita matakin farko na yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, inda ta yi kira ga kasashen duniya da su matsa wa gwamnatin mamayar lamba don ci gaba da mataki na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara tun farko. Yau Asabar ne dai matakin farko na yarjejeniyar ke kaow karshe. Kakakin kungiyar Hamas Hazem Qassem ya bayyana a wata hira da gidan talabijin na Al Araby cewa, ba za a amince da tsawaita matakin farko na yarjajjeniyar kuma gwamnatin mamaya na da cikakken alhakin gazawar fara shawarwari a mataki na biyu na tsagaita wuta a zirin Gaza. Qassem ya kuma lura da cewa, maganar da...
    Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu. Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance  matsalar da Falasdinawa suke...
    Shuwagabannin Afrika ta Kudu, Malasiya da kuma Colombia sun jaddada matsayinsu nah ana jiragen ruwa dauke da makamai zuwa HKI tsayawa a tashishin jiragen Ruwan kasashen su. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ta nakalto shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa, Firaiministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim da Shugaban kasar Colmbia Gustavo Petro suna fadar haka a wani rubutun hadin guiwa da aka buga a mujallar ‘Foreign Policy’ na wannan makon. Shuwagabannin sun bayyana cewa yakin da HKI ta durawa Falasdinawa a Gaza, ya nuna yadda tsarin dokokin kasa da kasa suna gaza tabbatar da adalci a duniya. Labarin ya kara da cewa : Ko mu hada kai mu tabbatar da dokokin kasa da kasa, ko kuma dukkan...
    Kamfanin Microsoft ya kori ma’aikata biyar bayan da suka nuna rashin amincewa da kwangilar da kamfanin ya kulla da sojojin Isra’ila. A rahoton cibiyar yada labarai ta Falasdinu, ma’aikatan sun gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar Microsoft da ke Redmond a birnin Washington, sanye da riguna masu dauke da taken nuna adawa da amfani da fasahar kamfanin wajen kai wa Falasdinawa hari. Matakin ya zo ne bayan da aka buga wani rahoto da ke nuna cewa an yi amfani da bayanan sirri na wucin gadi da na’urar tantance gajimare na Microsoft wajen ayyukan sojojin Isra’ila. Bayan wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya yi a baya-bayan nan, ya bayyana cewa kamfanonin fasahar kere-kere na Amurka sun taimaka...
    Kasar Masar ta ce an fara tattaunawa tsakanin Isra’ila da Hamas kan mataki na gaba na tsagaita wuta a Gaza. Ma’aikatar yada labaran kasar Masar ta fada a jiya Alhamis cewa, tawagogin Isra’ila, Qatar da Amurka na birnin Alkahira domin tattaunawa mai zurfi kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. “Bangarorin da abin ya shafa sun fara tattaunawa mai zurfi don tattaunawa kan matakai na gaba na yarjejeniyar tsagaita wuta, a ci gaba da kokarin tabbatar da aiwatar da fahimtar juna da aka amince da su a baya,” in ji sanarwar. Ta kara da cewa, masu shiga tsakani suna tattaunawa kan hanyoyin da za a iya “inganta isar da kayayyakin jin kai” zuwa yankin Falasdinu da yaki ya daidaita. A...
    Rundunar sojin Isra’ila ta amince da “cikakkiyar gazawarta” dangane da harin da kungiyar Hamas ta kai a kudancin kasar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023, wanda ya haifar da yaki a zirin Gaza, bisa sakamakon wani binciken da aka gudanar. A binciken da sojojin Isra’ila suka yi na cikin gida kan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba, 2023, jami’an sojin sun amince da cewa sun kasa cika aikinsu a ranar da Hamas ta kai wa Isra’ila hari. Wani jami’in soji ya shaidawa gidan radiyon RFI cewa sojojin sun “kasa cika aikinsu na kare fararen hula Isra’ila” a harin na ranar 7 ga Oktoba, 2023, yayin da aka fitar da babban sakamakon binciken. Ya kara da cewa...
    Jamhuriyar musulunci ta Iran tana shirin aiwatar da shirinta na gina sabbin cibiyoyin samar da wutar lantarki ta hanyar fasahar Nukiliya da kuma fadada wadanda take da su a yanzu. Shugaban hukumar makamashin Nukiliya ta Iran Muhammad Islami  ne ya bayyana hakan, yana mai kara da cewa: “ Za mu  kara  yawan wutar lantarkin da muke samarwa da  megawati 2000 a kowace sa’a daya  daga nan zuwa karshen zangon na bakwai na tsare-tsaren ci gaba da ake yi a kowace shekara 5. Zangon dai zai kare ne a cikn watan Maris 2029. Salami ya ce za a kara megawati 1,000 a cikin kowace sa’a da hakan zai mayar da abinda ake samarwa zuwa megawati 3,000 a cikin kowace sa’a.
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta kira yi Isra’ila da ta gaggauta dakatar da siyasar amfani da karfi na yi wa Falasdinawa karfa-karfa a yammacin kogin Jordan. Hakan nan kuma ta yi kira ga HKI da ta daina ayyukan da za su iya zama azabtar da al’umma kaco kau. Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta kuma bayyana cewa, irin wannan siyasar da Isra’ilan take amfani da ita, ta tilasata wa Falasdinawa 40,000 yin hijira daga yammacin kogin Jordan. Hukumar ta “Amnesty” ta sanar a yau Alhamis cewa; Falasdinawa mazauna “Budhum” a Musafir suna fuskantar hatsarin korarsu a kurkusa saboda yadda ‘yan share wuri zauna suke kai musu hare-hare a karkashin kariyar hukumar ‘yan sahayoniya....
    Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya sanar da rage kashi 90 na tallafin rabon kayan abinci don ƙarfafa dogaro da kai a tsakanin mazauna jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake ƙaddamar da rabon kayan abinci ga magidanta 25,000 gabanin watan Ramadan a Maiduguri, Jere da sauran sassan jihar. Helikwaftan farko ƙirar Najeriya zai fara aiki —NASENI Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan A cewar Zulum, gwamnatin jihar za ta ba da fifiko ga hanyoyin samar da ci gaba na tsawan lokaci a kan matakan agaji na gajeren lokaci kamar rabon tallafin abinci. Ya kuma bayyana irin gagarumin jarin da gwamnatinsa ta yi wajen tallafa wa manoma sama da miliyan...