2025-03-12@17:01:57 GMT
إجمالي نتائج البحث: 123

«a wannan atisayen»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    Bisa kididdigar da aka samu daga dandalin yanar gizo, adadin kudaden da aka samu daga fina-finan kasar Sin da suka yi zarra a kasuwa wato box office a 2025 ya zarce yuan biliyan 5.047, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 696, wanda ya zarce rawar da manyan fina-finan Arewacin Amurka suka taka a kasuwa, wanda ya kasance a matsayi na daya na wucin gadi a kasuwar fina-finan duniya. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
    Aston Villa na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke son ɗauko ɗan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford, ɗan wasan mai shekaru 27 bai taka leda a United ba tun lokacin da babban kocin ƙungiyar Ruben Amorim ya ajiye shi a wasan Manchester derby a ranar 12 ga watan Disamba. Amorim ya ce a ranar Laraba yana jin ƙungiyarsa za ta fi kyau da Rashford a ciki, amma ɗan wasan bai cika ƙa’idojin da ya buƙata ba, wakilan Rashford sun gana da wasu manyan ƙungiyoyin Turai a cikin ‘yan makonnin da suka gabata a ƙoƙarinsu na ganin ya bar Manchester. Mece Ce Matsalar Manchester United? AC Milan Ta Kammala Ɗaukar Kyle Walker Daga Manchester City A Matsayin...
    Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin. Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da falsafa. Limamin juma’ar na Tehran wanda yake jawabi dangane da zagayowar cikar shekaru 46 daga dawowar Imam Khumaini Iran bayan zaman hijira na shekaru 15 a kasashen waje, ya ce abin alfahari ne yadda wannan rana ta zagayo a daidai wannan lokacin da kungiyoyin gwgagwarmayar musulunci suke kara bunkasa da daukaka a duniyar musulunci. Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma bayyana cewa abinda yake...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka hada da na tattalin arziki siyasa, zamantakewa, tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan mu ji Karin bayanani daga bakin masana gwagwadon lokacinda muke da shi. Dafan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///..Madalla, masu sauraro, shirimmu nay au za iyi Magana dangane da ‘abinda ya sa ranar 9 ga watan Day ko kuma 29 ga watan Decemba yake da matukar muhimmanci ga Iraniyawa ko JMI?. A nan Iran ranar 9 ga watan Day na ko wace shekara tun shekara ta 2009, wanda...
    Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis. Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan. Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
    An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce, shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed al-Sharaa (al-Jolani) ya gabatar da jawabi na samun nasara bayan ganawa da shugabannin bangarorin soja a birnin Damascus fadar mulkin kasar, a gaban dandazon bangarori da dakarun Siriya. A yayin jawabinsa na nasara, Al-Sharaa ya ce: A yau kasar Siriya tana bukata abubuwa fiye da kowane lokaci, yana cewa, kamar yadda suka kuduri aniyar ‘yantar da kasar a baya, wajibi...
    Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron gaggawa game da batun Kongo(Kinshasa) da kwamitin sulhu ya kira jiya Talata cewa, a halin yanzu, yankin gabashin Kongo(Kinshasa) yana cikin yanayi mai hadari. Ya ce Sin na goyon bayan mambobin kwamitin sulhu su hada kai tare da daukar kwararan matakai, ta yadda za a samar da dabarun hana yanayin ya ci gaba da tsanani da kuma inganta warware batun a siyasance. Fu Cong ya bayyana cewa, kwanan nan, yanayin Kongo(Kinshasa) ya shiga matsanancin yanayi ciki sauri, inda kungiyar M23 ta kai hari birnin Goma, hedkwatar jihar Kivu ta arewa dake kasar, lamarin da ya sanya fararen hula da yawa barin gidajensu, inda kuma hadarin barkewar rikici...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
    Kalaman shugaban Amurka na cewa zai tsarkake Zirin Gaza na Falasdinu ta ruda kawayen kasarsa na Larabawa tare da hargitsa su Wani mai sharhi na jaridar Washington Post David Ignatius ya ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na tsarkake Gaza da mika Falasdinawa zuwa Masar da Jordan ya sanya kasashen Larabawa da suke kawancen da Amurka cikin halin fargaba da dardar. Shafin watsa labaran Al-Quds Al-Arabi, ta yi nuni da cewa Trump ya gabatar da tunaninsa domin hanyar gabatar da shawarwari da tunani tana da dama tare da sabani da siyasa a aikace. Ta ce Trump na fuskantar daukan matakin yin kasadar da zai lalata kyawawan ra’ayinsa da bayyana munanan tunaninsa. Jaridar ta kara da cewa: shugaban na Amurka zai...
    Yau Talata ana bikin tunawa da aiko ma’aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa wato Yaumil Mab’as. Ranar Mab’as 27 Ga Rajab rana ce ta murna da farin ciki saboda saukar Mala’ika Jibril (a.s) a kogon Hira dauke da sakon ayoyin farko na Kur’ani zuwa ga (Annabi) Muhammad ibn Abdullah (s.a.w) a lokacin yana dan shekara 40. Babbar manufar gudanar da wannan biki ita ce tunawa da ranar aiko manzon Allah Nuhammad (SAW), wanda ya zo wa dan adam da sako tsira daga halaka da kuma fita daga duhun kafirci da jahilci. Manzon Allah (SAW) ya kasance mutum na musamman a cikin larabawa, wanda dukkanin al’ummar da ke tare da shi ta yi masa shedar gaskiya da rikon amana da karamci...
    Haka kuma, an naɗa Muhammad Yahaya Liman a matsayin sabon Daraktan Akanta. Ya samu ƙwarewa a fannonin rahoton kuɗi da sarrafa kuɗi, ana sa ran zai taimaka wajen ƙara ƙarfin tsarin kuɗi na jihar. An kuma naɗa Akibu Isa Murtala, wanda a baya ya kasance Mataimaki na Musamman a Ofishin Shugaban Ma’aikata, a matsayin Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Gudanarwa. Aikin sa shi ne kula da gudanar da ayyukan ma’aikatu. Injiniya Abubakar Sadiq kuma an naɗa a matsayin Mataimakin Manajan Darakta na Hukumar Samar da Ruwa da Tsabtace Muhalli a Ƙauyuka (RUWASA). An ɗora masa alhakin inganta samar da ruwa da tsabtace muhalli a yankunan karkara. Haka kuma, an kafa kwamiti na musamman domin farfaɗo da Hukumar Sufuri...
    Dubban daruruwan Falasdinawa da suka rasa matsugunansu sun fara komawa yankin arewacin zirin Gaza da yaki ya daidaita bayan da aka cimma matsaya tsakanin Hamas da Isra’ila. Tuni kungiyar Hamas ta yaba da komawar Falasdinawan zuwa arewacin Gaza wanda ta danganta a abun tarihi. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas bayan shafe watanni 15 ana gwabza kazamin yaki a Gaza. An fara aiwatar da kashin farko na yarjejeniyar a ranar 19 ga watan Janairu, kuma ana sa ran za’a saki Falasdinawa sama da 1,890 da ‘yan Isra’ila 33, wadanda ke cikin 240 da kungiyoyin Hamas ta yi garkuwa dasu a harin ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2023. Tun lokacin yakin ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 47,306,...
    Real Madrid za ta fafata da Leganes, yayin da Barcelona za ta je Valencia a zagayen kwata fainal a Copa del Rey, bayan da aka raba jadawali ranar Litinin. Wani wasan da zai yi zafi shi ne tsakanin Atletico Madrid da Getafe, yayin da za a yi tata-ɓurza tsakanin Real Sociedad da Osasuna. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu Ana sa ran buga wasannin da za a gudanar ranar 5 ga watan Fabrairu. A jadawalin ya bayar da damar sake buga El Clasico wato karawar hamayya tsakanin Real da Barcelona a wasan ƙarshe da suka daɗe ba su haɗu a gasar tsawon shekaru. An haɗu...
    Kociyan Manchester United, Ruben Amorim ya faɗa cikin fushi cewa watakila wannan ce kaka mafi muni a tarihin ƙungiyar a Gasar Firimiyar Ingila. Hakan ya biyo bayan shan kashin da ƙungiyar ta yi a gida a hannun Brighton da ci 1-3 a karawar mako na 22 na gasar Firimiyar. Hakan ya kai United matsayi na 13 a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 26. Ga jerin rashin ƙoƙarin ƙungiyar a shekarun baya: Bayan da Brighton ta yi nasara a kan United a Old Trafford, karo na shida ke nan da aka doke ƙungiyar a gida a wasa na 12 tun bayan 1893/94. United ta ƙare a ƙarshen teburi, lamarin da ya kai ga ta bar buga gasar ta...
    Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
    Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai  miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
    Hukumar kula da gandun daji na Hadejia ta ce wuraren shakatawa na kasa suna taka rawar gani ta fuskar kiyaye halittu, da magance matsalolin sauyin yanayi, da inganta bincike, da ci gaba, gami da samar da ayyukan yi a Najeriya. Mukaddashin jami’in kula da gandun dajin, Mista Jonah Moses ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar neman shawarwari ofishin wayar da kan jama’a na kasa da ke Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya nanata cewa al’umma za su kara fahimtar fa’idojin irin wadannan wurare ne kadai idan Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa NOA, ta taimaka wajen fadakarwa ko ilmantar da jama’a. Jonah Moses ya bayyana cewa, sun kawo ziyarar ce domin ganawa da masu ruwa...
    Hukumar Kula Da Taswira Ta Jihar Kebbi (KEBGIS), ta tsara wani gagarumin shiri na samar da kudaden shiga na sama da Naira biliyan daya a shekarar 2025.   Babban Manajan Hukumar, Bashiru Saidu Bakuwai, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan tabbatar da nadinsa a matsayin babban Manaja, ya ce hakan ya nuna kwazon hukumar a karkashin ma’aikatar filaye da gidaje na tallafa wa tattalin arzikin jihar.   Malam Saidu Bakuwai, ya ba da karin haske kan ayyukan hukumar da suka hada da alhakin duk wasu takardu da suka shafi filaye, tsarawa da bayar da takaddun kowane gida, sake tantancewa, daidaitawa, da kuma tsarin rajistar kadarorin.   Sauran su ne Gudanarwa da Rajista...
    Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar Iran ya bayyana cewa: Atisayen sojin mai take “‘Manzon Allah Mai Girma na 19” ya bayyana ƙarfin sojojin Iran Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Muhammad Baqir Qalibaf ya bayyana cewa: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19” a cikin ruwan Tekun Fasha ya bayyana Alamar da ƙarfin sojojin Iran suke da shi. Mohammad Baqir Qalibaf ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar shawarar Musulunci a yau Lahadi: Atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19″ na sojojin ruwa da ke karkashin dakarun kare juyin juya halin Musulunci suka yi a cikin ruwan tekun Fasha, da kuma makaman tsaro da aka mika wa sojojin kasa na sojojin Iran, wanda a lokacin aka yaye shamakin...
    Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.