2025-04-05@03:39:34 GMT
إجمالي نتائج البحث: 903
«a Jihar Taraba»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Shugaban kotun tafi da gidanka na jihar Taraba, Useni Galadima, ya tasa keyar wasu mutane shida gidan yari bisa samunsa da laifin karya dokar zartarwa mai lamba biyar, 2023, wanda gwamna Agbu Kefas ya bayar. Wanda ake zargin, Suleiman Musa mai shekaru 30, daga Jos, jihar Filato; Adamu Umar mai shekaru 40 daga Bauchi, jihar Bauchi; Usman Umar Danburam, 35, daga Darazo, Jihar Bauchi; Ibrahim Abdullahi, mai shekaru 50, daga Mina, Jihar Neja; Aminu Mohammed, 40; da Adamu Abdul’aziz mai shekaru 46 daga jihar Taraba, an kama su ne a ranar 17 ga watan Janairun 2025. An same su dauke da kayayyaki dama da kuma wasu duwatse ake zargin masu daraja ne a wani sansani hakar ma’adinai dake...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
Bayan tsawon shekaru 40 a tsare, shugaban fursunonin Falasdinawa, Mohammed Al-Tous, ya samu ‘yancinsa Kungiyar kula fursunonin Falasdinawa da suke tsare a gidan yarin haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta saki Muhammad al-Tous, wanda shi ne fursuna mafi tsufa a hannunta, tare da tasa keyar shi tare da wasu fursunoni 69 zuwa kasar Masar, a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni tsakaninta da kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas. A ranar Asabar din da ta gabata ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta saki fursunonin Falasdinawa 200 a madadin wasu mata sojoji hudu da kungiyar Hamas ke tsare da su a Zirin Gaza. Al-Tous (mai shekaru 69) yana tsare tun 1985 kuma yana cikin kungiyar Fatah an yanke...